Kenza eBookz

Ganin ido complete - Chapter 73

Ganin ido complete - Chapter 73

Ganin ido complete Chapter 73: Ganin ido complete Chapter 73. Murmushi Ammie ta yi ta ce.

3,373 words

Murmushi Ammie ta yi ta ce.

"Waɗannan sarakan cin abincin ina Nono zai ishesu. Harda Madara ake basu..."

"Kai Ammie...."

"Wallahy kuwa, yini suke shan Nono da cin abinci idan dare ya yi ma haka. Shiyasa ga su nan sun yi barakallah kamar waɗanda suka shekara.."

"Kai Ammie kyauwu kika gani. Kuma nasan har kin fara jin kewa, domin za su miki tawaye."

"Allah ya tsare hanya. Ina nan ai kujera nake, ina zaune za'a dawo a same ni. Hassana kawo min jikar tawa na gani mana."

Da sauri na miƙa hannu na karɓeta ina dariya na ce.

"Ni ce nan uwar ta, saboda ni zan fara ɗaukanta ba ke ba."

Dariya suka kwashe da ita sannan Ammie ta ce.

"Ba komai. Ni ko cewa akayi ba zan ɗauke ta sai in tsaya daga gefe in yi addu'a."

Fira muka sha sosai wanda har Ya Hafiz sai da ya dawo gidan muka zauna kamar komai bai taɓa faruwa a tsakaninmu ba. Sai da aka yi mana abinci muka ci wanda Mummy ta ji daɗin hakan sosai, sannan misalin ƙarfe uku muka shiga gidan su Fakiha.

Koda muka shiga an gama shirya gida an tsara komai ana jiran masu kawo lefen Fakihar idan an yi sallar Asr.

Cikin farin Mama ta karɓe su Arhaam ta goya ɗaya a bayanta ta rungume ɗaya tana faɗin burinta ya cika.

Cikin jindaɗin yanda Mamar ta ba ta muhimmanci Ammien ta ce.

"Wato dai lefen nan sai da kika hana a kawo shi ɗin sai idan ina nan?"

Zaunawa tayi a ƙasa yayin da Ammie ke kan kujera a zaune tana facing ɗinta ta ce.

"Hajiya Nana Hauwa! Wallahy tallahy ni a duk duniyar nan dai a yanxu...bani da tamkar ki. Hajiya kika bai wa Mijina Million huɗu...million huɗu fa a zamanin nan, kika ɗauki ɗana kika mayar na ki, ki ka riƙesa matsayi ɗaya da Bahrain kuka saka shi a makaranta...kalle shi..kalle shi ki ga yanda ya canja ya dawo ɗan gayu da shi ga kuma tarbiyya..auren Fakiha ya tashi kin zunguro mana manyan kuɗaɗe kin ce gashi nan mu saya mata kayan ɗaki...mu da ko dubu ɗari ta kanmu bamu da ita, amma ta sanadinki, rayuwa sai dai muce Alhamdulillah!"

Girgiza kanta tayi tare da zubo da hawaye ta ce.

" Hajiya Wallahy ba ki san yanda nake jin ki a raina ba. Allah dai ya ƙara mana lafiya ya kuma ya ƙara mana tsawon rai mai amfani. Amma auren Fakiha ko shekara goma za'a yi, na gama yankewa sai ranar da kika zo za a yi shi."

"Allah sarki! To ai gani na zo. Allah ya kaimu ranar auren lafiya."

"Amin."

"Ta so mu je kiga kayayyakin da aka haɗa musu..."

A tare suka fice suka barni daga ni sai Fakiha, bayan su ma su Ya Hamza sun fita.

Kallonta na yi na sheƙe da dariya na ce.

"Amarya Amarya...kin ga kyaunki kuwa?"

Itama dariyar tayi tana mai matsowa kusa dani ta shafa fata ta tana faɗin.

"Ai kece amarya. Ji yanda jikinki ke ta wani sheƙi yana walwali...ko ni nan da za a yiwa auren wani sati kin fini haɗuwa.

Wata dariyar na ƙara yi harda buga ƙafa sannan na ce.

"Ke! Billahillazy raba kanki da ni. Na ƙuna bani tarar ƙauri,a tsime nike nan ciki da waje in gaya miki. Giwa ta Mohaa Uwargida mai Capacity. harkar ba irin taku ba ce ku en yara, magana ake ta matan aure uwayen gida..."

Dariya ce ta ƙwace mata tare da yin mini wani kallon mamaki ta ce.

"Beenafah! Haka kika dawo ashe?"

"Af! Tsaya kallon ruwa kwaɗo ya miki ƙafa. Mummy Sameera ta fi wata tana gyara ni tamkar wani bakanike a cikin garage...."

"To ai ni kin goge mini harda yau Beenafah. Na rantse da Allah daman wanda ya ke shiru-shiru idan ya tashi burgewa ya fi burgaggen kan famfo haukacewa..."

"Oho dai! Kema nan watarana haka za ki yi. Ina nan ina lissafi yau saura kwana biyu mu dawo haka..ki bari zan ɗiba miki turaruka In Sha Allahu idan na buɗe kayana.."

Na faɗa ina mai ɗaga mata ystsuna guda biyu da na yi twisting.

Shigowar su Hafsa ita ce ta katse mana firar, sannan muka tashi muka yi sallar Asr ɗin.

Bayan mun kambala muna zaune muka ji ana ta keta guɗa ana ta arerewa ana farin ciki masu kawo lefe sun zo.

Muna nan gida saida aka gama sallar Isha bayan an kammala komai sannan muka koma gida.

Washegari kuma muka shirya muka tafi gidan su Yaya Ashiru kamar yanda na roƙi Ammie tun muna Sokoto.

Koda muka shiga gidan yana nan a gyare tsab kamar yanda suka saba. Gidan ba kowa da alama yaran suna makaranta kasancewar Lahadi ce.

Ayya ce ta fara fitowa sannan Umma. Yanda suka tarbemu ne ya bamu mamaki baki ɗayanmu. Cikin farin ciki suka baza mana tabarma a bakin bishiyar mangoron wacce ke ta kaɗa iska mai sanyi da daɗi.

Bayan mun gama gaisawa Ayya ta ce.

"Allah sarki! Hajiya ashe haka abubuwa suka yi ta kasancewa ko?"

Ɗan murmusawa Ammie ta yi tace.

"Wallahy fa! Al'amarin Allah kenan?"

"Masha Allah! Beenafah ke ce mai tagwaye? Naga kansu ɗaya, kamar su ɗaya."

Cewar Umma tana mai miƙo hannu ta karɓi Arhaam daga hannun Ammie wacce itace ta amsa mata da cewa Eh.

"Allah sarki! Allah ya raya su ya yi musu albarka."

Ammie ce ta amsa da amin sannan ta ce.

"Ina Ashiru yake Maman Fa'iza?"

"Ashiru yana Kano. Tun da ya tabbatar cewa da gaske an yi auren Beenafah ya wuce bai dawo garin nan ba har yau ɗin nan. Yana can ya na ta kasuwancinsa."

"Allah sarki! Allah ya ci gaba da dafa masa ya zaɓa mishi mafi alheri."

Ayya ce ta karɓe zancen tace.

"Amin ya Allah. Ai auren sa da Sabila ma sati biyu ne suka rage in sha Allahu. Ai tuni ya cire Beenafah a rai tare da yi mata fatan alheri."

Duk firar da suke ina nan zaune na yi shiru tare da saukar da kaina a ƙasa ina chart da Abbansu Arhaam. Yayinda kuma can ƙasan raina nake tanyasa farin cikin auren da aka ce zai yi. Hmm! Allah sarki rayuwa! Yanda nake farin ciki da mijinda na aura ina masa Addu'a shima ya samu farin ciki da kwanciyar hankali da matar da zai aura. Allah ya basu zuria ɗayyaba ya ƙara yalwata masa arzikinsa.

Cikin farin ciki Ammie ta ce.

"Kai Alhamdulillah! Wallahy na yi farin ciki da jin wannan labarin. Daman aure ɗaya ne zai tsayar da ni zuwa wani satin. Amma yanzu kam dole na tsaya domin shi ma Ashiru ɗa na ne, ina farin ciki da wannan labarin, Allah ya nuna mana lokaci lafiya ya sanya alheri."

Bayan sun ɗan ƙara taɓa fira nace Ya Hamza ya shigo musu da siyayyar da nayo musu sannan ba su kuɗi dubu ɗari biyar sannan itama Ammie ta basu kuɗi wanda ban san ko nawa ba ne sannan muka musu sallama muka fito.

Bayan mun koma gida muka shiga tattara kayanmu wanda komai Ammie ta sake gyara mana. Sannan ta zauna ta ƙara mini nasiha da jan kunne, muka yi ta tattauna har kusan ɗaya na dare sannan muka kwanta bacci.

*******

Washe gari tun misalin ƙarfe shida na yamma Su Aunty Labiba suka iso gidanmu tare da Aunty Ziza da Suwara wacce ke ɗauke da yaron ciki a jikinta.

Daman koda suka iso mun riga mun gama shiryawa ni da su Aryaan, sai kuma en rakiyarmu wato, Su Aunty Hassana da kuma Maman Fakiha waɗanda su ne mutanen da muke da su a faɗin Gusau.

Bayan an gama gaggaisawa an yi fira kaɗan muka fito. Hamshaƙan Motoci ne jere guda uku na gani a ƙofar gate ɗin namu.

Kallon Aunty Labiba na yi na ce.

"Aunty Labiba sai ka ce za'a kai Amarya? Ni wallahy dama bari ku ka yi Mijina ya zo ya tafi dani duk ya fiye mini wanna..."

Wata irin shewa sukayi sannan suka fashe da dariya Aunty Ziza ta ce.

"Lallai ma matar nan! To idan kika yi haƙuri yanzu mintuna kaɗan ne za su sadaki da Mijin naki.."

Hannu na saka na toshe bakina ina dariya na ce.

"Auh! Shin duk Auntyies ɗina ne a nan ko? Na ɗauka Su Fakiha ne kuyi haƙuri.."

Dariya sukayi sannan Aunty Labiba ta ce.

"Yi abun ki ƙanwata kuma Auntyna, lokacin ne kuma damar ki ce. Wallahy banga laifin ki ba."

"Shin wai sai an kira sallar magrib sannan za ku shiga ko yaya? Mts! Ku da yake in dai mata ne tseguminku ba ƙarewa yake yi ba."

Ɗan wara ido na yi ina kallon mutumin da ya leƙo kansa daga cikin mazaunin driver yana magana.

Dariya Aunty Labiba ta yi ta ce.

" leƙa fuskar sa da kyau ki gani. Barrister ne da kansa. Daman ya ce shi ne yau wanda zai mayar dake sannan ya baki haƙuri akan korar ki da ya taɓa yi daga gidansa, wanda yanzu abin ya dame sa..."

Dariya na yi na ce.

"Lah! Ai ba shi ne da godiya ba Aunty Labiba ni ce. Wallahy ni ce da godiya, domin da ace bai koreni ba a ranar, da yanzu ban je gidanku har na haɗu da Abbansu Arhaam ba,dan Allah ki tayani godiya."

Sai da muka gama dariya sannan muka shiga motocin muka tafi. Koda na shiga na tarar da Biba da wasu mata masu aiki guda biyu.

Basu wani jima ba suka tattara suka fece wanda Fakiha ce kaɗai wacce ta tsaya akan cewa sai na bata alƙawarinta domin ba lallai wannan zumuɗin da nake ya bari ta ƙara ganina ba. Daman na faɗamata ba zan tsaya bukinta ba tun jiya da muka yi waya da dare.

Kwalayen kayan ƙamshin na buɗe na zazzaɓa mata sannan na kira Biba na bata na ce ta samu kwali ta jera mata su.

Ina cikin rufe kayan ta kalle ni don bata da kunya ta ce.

"Sauran kayan matan ko?"

Wani kallon banzan na yi mata sannan na ce.

"Nima da za'a kai ni gidana sanda aka mini auren ba'a bani kayan matan ba, kayan ƙamshi kaɗai aka bani...tashi ki wuce dan Allah. Kinga yanxu an gama sallar magariba, daga zaran an yi Isha dawowa zai yi. Dan Allah ki wuce ki barni na shirya masa. Ke wallahy gidan Haya ce da ba'a kwashewa lafiya da ke."

Wata uwar dariyar ta sheƙe da ita sannan ta ce.

" Allah ya baki haƙuri to, na tafi sai da safe."

"Yauwa! Allah ya bamu alheri."

Har bakin Main door ɗin na rakota Sannan ta karɓi kwalin daga Hannun Biba ta wuce.

Kallon Bibar na yi na ce.

"Kin gama shiryawa su Arhaam ɗin?"

"Eh! Na gama tun ɗazu."

"Ok tau, ki ci gaba da kulawa da su,ina zuwa yanzu."

Sai da na gama duba abincin da suka shirya sannan na wuce na yi sallar Isha na shiga na tsala wanka na fito na kashe lokaci sosai na shirya cikin wani musulmin Lace na kashe ɗauri na fito sak Amarya ta. Sai murmushi na ke yi wanda ni kaina farin da zuciyata take ciki ban san yanda zan misalta shi ba.

*******

Ya Mohaa kuwa, sai da ya gama sallar Isha sannan ya fito daga masallacin zuwa gida.

Ɗan tsayawa ya yi daga nesa yana kallon mutumin da ke tsaye ɗan nesa da gidan kaɗan.

Sai da ya gama ƙare masa kallo sannan ya ƙarasa inda yake tsaye ya ce.

"Malam ya dai?"

Tun da ya iso garin ko minti goma bai ƙara cikakke ba ya fito ya zo gidanta bayan Fakiha ta tabbatar masa da cewa Beenafah tana garin bayan ya tambayeta.

Sai da ya iso ƙofar gidan sannan ya shiga tunanin yanda zai yi ya shiga gidan. Gabaɗaya basirarsa ta ɓace. Dama ya sani ya ɗauko Hamza ko Bahrain sun zo ko zai samu ya yi nasarar aiwatar da aikinsa. Ga shi tsawon wata huɗu da ya je gidansu ya kasa cika aikin nasa, kuma yau wannan damar ita ce kaɗai yake sa wacce daga ita muddin dai bai yi nasara ba to yasan faɗuwa ta tabbata gare sa ta har abada.

Yana cikin neman mafita kuma sai ga mai gidan ya rutsa sa yana tambayar sa wai ya dai?

"Tambayar ka nake, lafiya? Waye kake jira a nan?"

A rikice ya fara ƙyafta murya yana faɗin.

"Daman...Daman...ahm daman.."

Wani murmushin gefen baki ya yi sannan ya ƙara ɗaure fuska tamkar bai taɓa sanin yanda ake dariya ba ya jinjina kansa ya ce.

"Kasan wani abu? Tun ina da ƙurciyata wallahy tallahy ban taɓa sha'awar Zina ba. Duk irin jarabawar da na shiga ban taɓa jin cewa ina sha'awar bin wata macen ba ballantana in riƙa bibiyar matar aure. Ba wai ina alfahari ba ko wani abu, domin na san cewa ban fi ƙarfin jarabawa ba. Amma tambaya ta ɗaya ce a gare ka...Miyasa kake bibiyar Matata? Laifin me ta yi maka ko kuma ni wane laifin na yi maka da cancanci wannan hukunci da har yasa kake bibiyarta tsawon lokaci?"

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

*PAGE 58*

Wani irin matsanancin tsoro ne ya dabaibaye masa zuciya a lokaci ɗaya, domin yanda yaga wani irin ɓacin rai da ya bayyana ƙarara akan fuskar Ya Mohaa ɗin ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba.

Wato a irin wannan mugun yanayin da ake ciki, ko wuƙa a ka ɗora masa akan maƙogoransa yasan cewa ba zai iya faɗar wai dalilin da yasa yake bibiyarta ba.

Cewa zai yi don yana sonta yake bibiyar ta ko me? Ko kuma cewa zai yi yaga shi ɗin bai cancanceta ba sai ga shi? Hmm! Wai aka ce wuya makarantar Kare.

Da ya buga ya buga yaga cewar dai he has no way to escape yasa ya zube akan gwiwoyinsa murya cike da zallar magiya ya ce.

"Sharrin shai ɗan ne kawai...wallahy sharrin shaɗain ne. Dan Allah ka yi haƙuri,wallahy daga yau ba zan sake ba."

Girgiza kansa ya yi yana faɗin.

"A'a kam! Duk tsawon lokacin da ka kwashe kana bibiyar ta, taya ya rana ɗaya za ka ce mini ka daina kawai in yarda da kai. Yan da ka jure ka ke ta wahala haka na zaman bibiyarta dole dai kana da wani dalilin da yasa kake bibiyantan."

"Wallahy tallahy, na rantse da Allah, billahillazy ba komai, kawai sharrin shai ɗan ne..."

"Shi ne wanda yake ƙawata maka matar tawa ko? Hmm! Ka kuwa san rayuwar waye kake bibiya? Duk da da cewa a wannan lokacin ka samu ka kuɓuta da ƙyar wato ashe bai ishe darasi ba. Mata ta itace komai ta wa, duk wanda yace zai raɓeta da wani sharri kuma! To tabbas mutuwa za ta fiye masa alheri a cikin rayuwarsa."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Dan Allah yallaɓai ka yi haƙuri..."

Bai san ya akayi ba, cikin en daƙiƙu kaɗan yaga sojojin sa sun zagaye da bindiga suna jiran umarni.

Cikin gidan ya wuce direct ya bar su a nan ba tare da yi musu wani bayani ba.

Ni kuwa, ina nan na zauna parlour tare da twins ɗina inda muka ci uban gayu sai farin ciki muke. Suna nan na zaunar da su duk da cewa zaman bai gama nuna ba da kayan wasan su wanda Bahrain da Ya Hamza basa gajiya da zuwa kasuwa wurin siyowa, wata haukar ma sai ta baka dariya, yi ni suke wasa da su matuƙar dai suna gida ba su fita ba. Shiyasa Ammie ke cewa da a nan za su ci gaba da zama har su yi wayau da tabbas su Ya Hamza sun haukatar da su.

Ina ganin shigowarsa sai da na ji wani abu mai sanyi ya ratsa cikin xuciyata wanda ya saka na lumshe idanuna sannan na buɗe su a hankali na taka na je na rungume shi na ce.

"Welcome home my LOVE. Na saba yi maka barka da zuwa a duk lokacin da ka dawo gida....yau kuma da ni da yaranmu muke maka barka da zuwa...Welcome home DADDY."

Tun da ya ɗaura ƙwayar idonsa a kanmu, sai da ya ji wani sanyi ya ratsa duk wata gaɓa da jijiyar jikin sa. Wai shi ne a yau ya dawo gidansa ya tarar da matarsa da 'ƴa'ƴansa? Ashe akwai irin wannan lokacin da zai zo a gareshi watarana. Tabbas komai yana da lokaci muddin ka yi haƙuri ka saka Allah a cikin al'amarinka...

"Why are you quite?"

Saukar ɗumin hawayensa na ji a gefen wuyana. Sannan ya ɗago fuskata a hankali ya kalli ƙwayar idanuwana sai kuma ya kalli su Arhaam sannan ya sake kallona cikin wani irin yanayi ya ce.

"farin ciki ne Ya hanani Magana Bibi. Wani irin yanayin farin ciki na ke ji na a ciki wanda ban san ma abin da zance ba...Kin haskaka rayuwata kin sauya mini duniya. You are different Bibi!"

Murmushi na yi masa na ce.

"Alhamdulillah Ala kulli-hal!"

Maimaita kalmar ya yi sannan ya kalle ni a nutse ya ce.

"Bibi...na san Jafaru, nasan irin alaƙarku ta maƙotaka da kuma irin zumuncin da ya ƙulli har yanzu a tsakaninku. Amma ina so ki faɗa mini da bakin ki gaskiyar abin da yasa yake bibiyar ki daga baya....bai kamata Sam ace zancen sa ya shigo a cikin rayuwarmu a irin wannan lokacin da muke tsaka da farin ciki ba. Amma kamawa ta yi ki yi haƙuri. "

Ban san lokacin da wasu hawayen baƙin ciki suka wanke mini fuska ba. Cike da takaicin sa na yi masa bayanin komai da ya wakana tun wancan zuwan har ranar da akace ya zo nemana a daren suna.

Hmm! Wato wani irin mummunan yanayi ne ya bayyana akan fuskarsa wanda sai da ya saka na ji a raina dama ban faɗa masa ba.

Wani irin zafi ne ya ji yana ratsa ƙirjinsa har zuwa fatar jikinsa tsabar yanda ya ji kalaman masu kama da feshin wuta a cikin kunnuwansa.

Wayarsa naga ya ciro yana faɗin.

"Ku yi masa mugun dukan da sai kamanninsa sun sauya sannan ku rufe mini shi..."

Wayar na karɓe jikina na wata irin ciccira na ce.

"Ku harbe min shi! Ku saka bindiga a tsakiyar kansa ku harbesa, kafin ku aiwatar ku faɗa masa cewa saƙo ne daga Beenafah..."

Da sauri ya fisge wayar yana mai mini wani kallon mamaki ya yi sauri ya ce.

"No, don't kill him. Kui masa duka sannan ku rufe mini shi..."

Wasu zafafan hawayene suka biyo saman kumatuna domin sam ni wannan decision ɗin bai mini ba, na so ace an kasheshi domin sam na san har abada ba zai daina bibiyata ba tunda shi ɗin jahili ne, munafuki mai fuska biyu. Jin da gaske ya sauya hukuncina yasa na karye wuyana still da hawaye a fuskata na ce.

"To don Allah kada a bar mini shi a cikin gidannan, domin idan har ya kwana a nan to burinsa ya cika na kwana a inuwa ɗaya da ni. A yi nesa da shi dan Allah."

Jinjina kansa ya yi ya ce.

"Idan kuka gama dukansa..take him to police station, ayi masa azaba mai tsanani."

Yana kashe kiran ya je ya ɗauki Arhaam wanda yake wasa da kuka a lokaci ɗaya alamar ya gaji da zaman, Aryaan na ɗauka nima na fashe da dariya ganin da yake ta wani diri yana dariya na kalli Arhaam na ce.

" Kaga Aryaan yafi ka wayau, domin dariya yake yana welcoming Daddy kai kuma sai wani taɓe baki kake kana kuka.."

Dariya ya yi tare da ware ɗayan hannun sa muka shige ya zagayemu yana faɗin.

"Shi ma ai haka ne a wurinsa. Alhamdulillah! Da sabuwar rayuwar da zamu shiga. Allah ya amintar damu ya bamu zaman lafiya."

"Amin yah ubangiji."

Haɗa masa su na yi sannan na je na kawo mana kayan abincin na baje su a nan,muka zauna muka ci. Bayan na dawo ne ina haɗa musu madara yana ta kallona na yi murmushi na ce.

"Ya dai?"

Jinjina kansa ya yi yace.

"Kin yi kyau sosai. Ban ga wata mace mai kyaunki ba a duniya Bibina.."

Dariya nayi sannan na ce.

"Duk Mazan duniya haka kuke cewa..."

"And every man Idan kika ji ya faɗi haka, to ki yarda cewa shi abinda yake hannun sa, yake zuciyar sa kaɗai ne ya yarda da shi."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull