Ganin ido complete - Chapter 76
Ganin ido complete Chapter 76: Ganin ido complete Chapter 76. Tsayawa ya yi cak yana kallon su ɗaya bayan ɗaya da wani irin maɗaukakin mamaki a fuskar sa.…
3,361 words
Tsayawa ya yi cak yana kallon su ɗaya bayan ɗaya da wani irin maɗaukakin mamaki a fuskar sa. Sannan sai kuma ya waigo ya kalleni still harshensa ya kasa bashi haɗin kai wurin ganin ya furxo da abinda yake zuciyarsa.
Ganin haka yasa na kama hannun sa na sumbata ina murmushi na jinjina masa kaina na ce.
"This is true love...this is your legacy and you deserve everything Mijina..Happy birthday to you, ina maka addu'ar Allah ƙara bulbulawa rayuwarka albarka, ya ƙara maka lafiya da tsawon rai mai amfani, ya shiryar maka da 'ƴa'ƴanka yasa ka yi kyakkyawan ƙarshe. You are the best Husband, domin kai ne rayuwa ta. Ina maka fatan alheri....Happy 5th years Anniversary of happiness...And a matsayin jajirtaccen ɗan kasuwa wanda ya yi aiki tuƙuru ya gina kansa da en uwansa da ma mutanen duniya da dama ya zamto kafaɗar dogaronsu...Happy 25Yeras of Golden pathways."
Muryar su Aryaan Ya ji suma suna faɗin.
" Happy Birthday to our super hero Daddy...we love you Daddy."
Hawaye ne masu sanyi suka ƙwace masa, domin sam ko a mafarkin sa bai taɓa kawo wannan ranar za ta zo masa irin haka ba. Yasan cewa kamfaninsa ya cika shekaru ashirin da biyar and yasan cewa anniversary ɗinmu na cika 5yrs ya zo amma bai taɓa tunaninsa ta wannan hanyar ba.
Hugging ɗina ya yi a hankali ya ce.
"Thank you so much Bibi...thank you for everything. Haƙiƙa yau kin sanyani farin ciki wanda bai san ta ya zan misalta miki shi ba. Allah ya saka miki da alheri ya ƙara zaman lafiya da farin ciki."
Tafi wurin ya ɗauka kowa ya shiga tayamu murna sannan daga ƙarshe aka shimfiɗa mana blue carpet mai tsawo muka shiga takawa cikin manyan flowers masu kyau sosai har zuwa cikin babban Hall ɗin resort ɗin.
Muna shiga aka saki wani sassayan kiɗan mai ɗauke da English song na weeding anniversary har muka je inda table ɗinmu yake muma tsaya.
Muryar MC ɗin ce ta karaɗe wurin da cewa.
"please Welcome....the king and Queen of tonight...Mr. And Mrs. Mohaa."
Bayan mun zauna aka shiga Family Parade inda kowane dangi suka faro isowa inda muke domin taya murna da fatan alheri.
Su Jadda ne suka fara zuwa wanda har suka tsaya a gabanmu bai daina mamakin ganin su ba. Wai to ta ya ma suka san da duk wannan har suka shirya suka zo. Tsofaffi da su sai neman rigima.
"Hammodi....Ina muku addu'a da fatan alheri...Beenafah, babu abin da zan ce miki sai dai mun gode miki da kika dawo da farin ciki cikin rayuwarsa wanda muke fata ya ci gaba da ɗorewa har abada.."
Dariyarsa da farin cikin sa sun kasa ɓoyuwa a wannan lokacin. Babu abinda yake idan ba dariya da murmushi ba.
Jaddi kuwa, hannunsa ya kama yana faɗin.
" Kai ɗin na musamman ne a wurin kowa Hammodi, har a wurin matarka kai ɗin na musamman ne. Fatana ɗaya ne, watarana ka zo ka ci gaba da rayuwa a kusa dani, ko da ba za ka yi siyasa ba."
Yanzu kam sai da ya ji hawaye a idonsa, jinjina kansa ya yi ya ce masa.
" In sha Allah, watarana tabbas zan cika wannan mafarkin naka Grandpa. Na gode sosai."
Daga nan sai su Abiyh wanda har da Sanda yake ɗan dogarawa suma suka zo suka mana addu'a sannan Annie wacce take ta murmushi ta ce masa.
"You took care of our daughter like a queen...a ko'ina nuna ta kake yi da kuma yin alfahari da ita. Allah ya ƙara muku shekaru masu albarka ya ji ƙan iyayenku ya albarka wannan zumuncin."
Daga nan sai su Hajiya da su Aunty Labiba suka yo ƙungiya guda suna ta farin ciki suna tayamu murna sannan daga ƙarshe Aunty Labiba ta ce.
"Listen everyone..Beenafah is literally the best thing that ever happened to our brother, and to our super Daddy...muna muku fatan alheri, muna ƙaunar ki sosai a cikin rayuwarmu, har abada ba zamu manta alherinki a garemu ba."
Hannuna Hairi ta jimƙe tana murmushi ta ce.
" Happy Anniversary Mummy...Haƙiƙa ke da Aunty Labiba...Ku ne allon kwaikwayona..har abada ina alfahari da ku. Fatan farin ciki."
"Na gode favorate...na ji Jadda na sanar mini ranar kin ƙara buɗe wani shagon a Suq Rania.."
Dariya ta yi tace.
"Mafarkina ya cika Aunty Beenafah, har abada ba zan daina godewa Daddy da IG Suhaib ba da kuma su Jaddi."
"Masha Allahu, Allah ya taimaka yasa albarka."
"Amin."
Ammie itama bayan kowa ya koma ya zauna ne ta zo ita da Abbu da Bahrain ta bani wata sarƙa sannan ta bai wa Dayaa Agogo, sai kuma Bahrain da ya yi presenting ma su Aryaan wasu manyan toys waɗanda na ji yana cewa wata ƙasa yaje na musamman ya siyo su.
"Ina tayaku murna, Allah ya ƙara albarka a cikin rayuwar auren ku."
Cewar Abbu sannan itama Ammie ta yi mana addu'a tare da Bahrain suka wuce.
Bayan nan kuma abokan arziki da abokan kasuwanci suka shiga tayamu sannan daga ƙarshe aka shiga gudanar da wasannin yara kamar yanda na tsara daga nan aka kuma aka juya zuwa ga wani bango mai ɗauke da hotunanmu waɗanda wasu ma bai san da su ba, domin tun farko-farkon aurenmu nake ajiyar su, dana haihuwar Su Aryaan ga su kala-, kala. Wasu a jirgi, wasu a gida, wasu a Sudan wasu nigeria, da sauran su.
Daga haka na saka gasar fassara hotuna da videon da ke yawo a majigin. Haka aka yi ta nishadi da farin ciki kowa sai faɗin albarkacin bakinsa yake yi. Bayan an gama muka wuce bakin teku domin yin dinner ta ban mamaki wacce kowa sai da ya yaba. Wata banner ce ta musamman wacce akayi hoton kamfanin da kuma Hotonsa a jiki wanda aka yi rubutu da fitilu masu ɗaukar hankali. The CEO Golden pathway company.
Bayan an gama cin abincin ya hau saman stage ɗin wurin ya kalle ni ya jinjina kansa sannan ya kira kowa yake wurin ya yi godiya sannan ya ce.
"Tonight...it's not about me only...it's about the woman who rebuilt my heart. It's about a wife who gave me peace. Ita ɗin garkuwa ta ce, Mafarkina da Allah ya cika min,I love you more than the life itself. En Uwa da abokanan arziki. Ina godiya sosai da kuka haɗa kai wurin bani wannan bazata da bazan taɓa mantawa da ita ba. Haƙiƙa yau na yi farin ciki, kuma na tabbatar cewa ina da mata wacce ke matuƙar ƙaunata da yin alfahari da ni. Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya, mun gode sosai."
Daga nan na hau stage ɗin muka yanke cake ɗin tare da su Aryaan. Aka yi hotuna cike da nishaɗi sannan kowa ya koma gefe da wanda yake so aka yi ta fira wanda ni ina tare da Ammiena wacce ke ɗauke da 'ƴar ta Kausar wacce ta haifa a gidan Dr. Basheer shekara biyu da suka wuce, yarinyar da nake matuƙar ƙaunar ta a raina. A duk lokacin da na kalleta, hoton fuskar Sajjad ke dawo mini. Bahrain dake saɓe da Abdallah ne ya ce.
"Ina ƙara tayaki murna Aunty Beena....kalli yanda Daddy ke farin ciki. Raayuwa kenan.."
Murmushi na yi na ce.
"Na gode Bahrain..To kai wai yaushe zaka yi auren?"
Dariya ya yi ya kalli Ammie sai kuma ya kalleni ya ce.
"Idan na cika miki mafarkinki, na zamo jagoran WazeerMed, in sha Allah zan yi aure..."
"Kana da budurwa?"
Wata uwar dariya ya yi sannan ya ce.
"Budurwa kuma Aunty Beena? Noo! Not yet. 3years ya rage na haɗa Degree na, ko bayan na kambala, zan yi service na shekara ɗaya, sannan in fara aiki a Matsayin CEO, sai na yi kamar 2years haka, sannan na nemi budurwar. Kinga idan na fara tun yanzu, na rantse miki da Allah kuɗina kawai za ta riƙa sheƙewa tana cin duniyarta da tsinke..."
Da gani har Ammie da Abbu bamu san lokacin da muka fashe da dariya ba sannan daga ƙarshe na ce.
"To ai ita ce rayuwar..."
"No..ban yarda ba. Misali da ke. Koda kuka yi aure da Daddy bai ma taɓa ganin ki ba kema kuma haka, and ki kalla yanda kuke farin ciki rayuwarku na ta albarka. Ya Hamza haka Nimrah ta dinga tatsarshi in gaya miki ta dinga wanke shi, to wallahy bai samu sukuni ba sai da akayi auren nan. Amma kinga Ya Jafaru babu budurwarda take cin kuɗinsa. Tun da ya koma makaranta bayan wannan rigimar bai ƙara kula mace ba har yau. Yanzu haka ya zama barristernsa aikin sa kawai yake yi sai kula da su Mama."
Jinjina kaina na yi na ce.
"uhmm! Ya zaɓa abu mai kyau.."
Wani kallon ya mini da cewa.
"Aunty Beena cewa fa kika yi ya zaɓa abu abu mai kyau? Zaɓar yin rayuwa kai kaɗai shi ne abu mai kyau? Oh no! This is a very bad idea. Da iyalin dai...rayuwar za ta fi cika daidai."
"Bahrain...aure sunna ce mai ƙarfi, amma kuma ba dole ba ne matuƙar za ka kiyaye dokokin Allah. Tunda har yaga hakan ya fi masa fine! Let him be. Rayuwarsa ce, nobody will force him."
Girgiza kai Ammie ta yi cike da takaici ta ce.
"Jafaru ya ɓata rayuwar shi, sam bai kyautawa kansa da iyayen sa ba. Hatta ni ɗin nan ya daina magana da ni, yana da wata irin zuciya wacce ni dai ban taɓa ganin ɗan Adam kwatankwacinsa ba a duniyar nan. Iyayen sun yi sun yi, sai dai yace musu idan lokaci ya yi zai yi. To abinda bai gane ba shi ne, shi fa Allah duk abinda ya ga dama shi ne zai tabbata a cikin rayuwarka, idan kayi farin ciki a kowane yanayi ka gode masa...To sai ya ƙara maka kamar yanda ya yi alƙawari. Amma idan ka butulce...to tabbas za ka yi ta ganin ba daidai ba a rayuwarka. Amma kinga Ashiru! Ashiru ya kai ɗa wallahy, ya riƙemu har yanzu tamkar komai bai faru ba, yakan zo har Sokoto tare da matarsa idan dama ta samu muyi zumunci su koma. Ni da wannan ma na yi shawara da Dr. Cewa zamu ɗora shi a FruitWave wanda suka sakar mana, kinsan tun da ya dawo mallakinmu gabaɗaya, har yanzu ba'a yi wani yunƙuri ba. To In Sha Allahu zamu tattauna yanda ya kamata sai mu gani."
Cikin farin ciki na ce.
" Gaskiya na ji daɗin hakan sosai. Yaya Ashiru ya cancanta Ammie. Allah ya taimaka ya bada sa'a yasa ace gwamma da akayi."
Fira muka yi ta yi har misalin ƙarfe huɗu na asuba, sannan a hankali kowa ya watse muka yi sallama wanda da gari ya waye kowa zai koma gida inda ya fito. Nan na ce Ammie ta wuce da su Aryaan da Abdallah domin daman na yi plan ɗin ciresa daga Nono idan ta zo ta wuce da su, su yi mata ko one month ne sannan su dawo.
Washegari sai da na tabbatar kowa ya watse sannan na ce mishi ya shirya akwai surprise na gaba.
Sai da muka fito ya ga ba kowa daga ni shi ne muka rage.
"Ina su Arhaam Bibi.?"
Hannun shi na kama ina murmusawa na ce.
"Sun tafi gidan Ammie mu ɗan shaƙata..."
"Har da Abdallah?"
"Eh, a lissafinmu na cire a nono ai yau ne ya kama.."
Shiru ya yi alamar nazari sannan daga ƙarshe ya jinjina kansa yana kallona ya ce.
"Ke ɗin ta musamman ce. Tabbas yau ne date ɗin. Kin yi manipulating ɗina kinsa na manta komai....five years in marriage, and I still choose you everyday, over and over Bibina."
"And I will always choose you for ever Mijina."
Sai da muka yi sati biyu muka ɗai a nan muka shaƙata sannan muka koma gida.
Watarana ina zaune ina yanka masa fresh fruit ya kalleni yana ta murmushi ya ce.
"Har yau na kasa manta bukin bazatan da kika shirya mini Bibina. Na mutu da matuƙar mamaki domin komai ya tafi a sai ti..."
Wata irin dariya na yi sannan na ce.
"Oh! Wato ka za ta kai kaɗai ne mai kuɗi ko kuma kai kaɗai ne mai watau ko?"
"Wane ni! Ai ke ɗin kuwa ke ce mai kuɗi Bibi, domin an narka dukiya ba kaɗan ba. Kuma na san ba kuɗi ba ne..."
Dariyar na ƙara yi na ce.
"Ai zan zare su ne na dawo da kayana a hankali."
Dariyar ya yi shima sannan ya ce.
"ba komai. Ai komai nawa mallakin ki ne. Amma ina faɗa miki na ji daɗi sosai a raina. Ina son ki"
"Ni ma haka Dayaa na."
Bayan wata ɗaya muka je Qatar auren Shuraih daga nan muka dawo da su Aryaan muka ci gaba da tafiyar da rayuwa kamar yanda ubangiji ya tsara mana.
********
15years later....
A shekara sha biyar....abubuwa da yawa sun faru na daɗi da kuma akasin sa. Rayuwarmu ta canza sosai inda muka samu ci gaban da sai dai muce Alhamdulillah! Kamar yanda ya yi wa Jaddi alƙawari kafin rasuwarsa...ya dawo Oumdurman da alhalinsa wanda ya gina mana katafaren gida muke rayuwa Muda 'ƴan' ƴan mu. A yanzu shi ɗin shugaba ne kuma jagora kamar yanda Jaddin yake mafarki a koda yaushe inda yake a matsayin Minister kamar yanda Jaddi ya kasance a baya.
Ya kasance mutum mafi daraja da girma da ake ji da shi a faɗin Sudan ɗin, domin ya zamto abin dogaro, ƙashin bayan al'umma wanda baya gajiya da tallafa musu da kuma jin kokensu a koda yaushe.
Aryaan da Arhaam sun girma sosai wanda a yanzu suke aji ɗaya a jami'a yayin da Abdallah yake a SS2. Sai Aliyu Haidar da ke Jss1 sannan autata Zarah da ke primary 3.
Rayuwar dai, duk da tana cike da ƙalubale da jarabawowi, Alhamdulillah a kowane irin yanayi, duk da cewa kakan nasa baya raye, sosai suka ci gaba da haɗe kansu tare da su Uncle Mu'aƙƙib wanda a yanzu daga shi sai Ya Mohaan ke jagorantar iyalin na su da sauran yara da jikoki.
Gidan yana sa ka ji ba daɗi idan ka tuna da Jaddi wanda shi ne haske kuma annurin gidan na su. To amma a rayuwa, mutuwa ba ta da gwani, sannan bata barin wani don wani. A duk lokacin da Allah ya yi za ka bar duniyar to lallai ba makawa sai ka tafi.
Ko a Qatar Abiyh ne kaɗai ya rage wanda ya tsufa sosai, lokacin da masoyiyarsa Ammah ta rasu, ya yi kuka wanda sai da ya baiwa kowa tausayi. A hannunsa ta rasu a gadon asibiti, ashe duk ihun da ake, ɗan lokaci ne kaɗan a tsakaninsu wanda shekara goma kaɗai suka yi a tare ta rasu ta bar shi.
A yanxu na kasance Uwa, shugaba, jagorar Al'umma kamar yanda mijina ya kasance. Kuka da farin cikin iyalina shi ne kan gaba da komai nawa. A duk lokacin da zan kalle su suna farin ciki, sai na riƙa tunawa shekarun baya, wanda babu abu ɗaya da muka saka cewa zai faru irin haka, musamman Ya Mohaa da ya cire rai da farin ciki da kuma Mafarkin samun iyali.
Shi ne yau yake da manyan 'ƴa'ƴa. Masu nutsuwa da cikar kamala. Shi ne kullum za'a ce masa Daddy kaza, Daddy ya kamata ayi kaza, Daddy ya kamata ace kaza kaza ne. Daddy a biya mini kuɗin registeration, Daddy ni yaushe za'a yi walima ta,Daddy ni kuɗi kaza za'a bani domin zamu yi get together a school, Daddy we love you.
Waɗannan sune kalmomin da yake yawan faɗamin cewa suna saka shi farin ciki kuma suna saka shi jin cewa shi ɗin yanzu mutum ne, uba kamar yanda ya yi mafarki.
Siyasar sa...bata hana masa lokacinmu, domin ba don kuɗi yake yi ba, yana yi ne domin cika alƙawarin kakansa wanda ya mutu da farin cikin cewa burinsa ya cika domin Hammodinsa ya dawo ya kuma ɗauka daga inda ya tsaya wurin taimakon jama'a. kamar yanda ya saba cewa, shi ka ɗai ba zai iya ba sai da taimakon su Uncle Mu'aƙƙib, to haka ma ya tabbatar cewa ko bayan ya mutu Uncle Mu'aƙƙib ba zai iya shi kaɗai ba dole taimakon Ya mohaa.
Da wannan yake yawan tafiye-tafiye. Duk da cewa muna shirye-shiryen yin 20years anniversary a cikin watan nan, hakan bai hana shi shirya tafiyar da suka tsara ba, tafiyar ta ministoci ce da za su yi taro a Nigeria wanda ya ce mu shirya har mu zamu tafi.
Yau ma tun ƙarfe huɗu ya dawo gidan ba tare da na sani ba. A parlournsa na tarar da su suna cin abinci har da Aliyu wanda dawowarsa kenan daga school shi da Zarah.
Kallonsu na yi ina mai dire musu tray ɗinda yake hannuna na ce.
"Ai sai ku sanar mini cewa kun dawo,.."
"Mami mun ga kina da baƙi ne shiyasa."
Cewar Abdallah yana mai kai hannu ya ɗauki glass cup ya tsiyaya lemu. Duƙawa na yi na ɗauki cup ɗin na zubawa babansu ina miƙa masa na ce.
"To kai miye ya hana ka kirani a waya?.."
Kallona ya yi sannan ya ce.
"Na fa aika har sau biyu aka ce kina da baƙi.."
Jinjina kaina na yi sannan na ce.
" Uhm! To sannu da dawowa...tukunna wai ina ma ka tsaya tun ɗazu bayan ya kamata ace kana gidan nan tun 2pm?"
Kallon su Aryaan ya yi sai kuma ya kalli gefen su Abdallah sannan ya dawo da kallon guna yana murmushi ya ce.
"Har na kamo hanya, sai Aryaan ya kirani yace sun kambala lectures, sai na je school ɗin, daga nan kuma sai muka ga lokacin tashin su Zarah ya yi sai muka wuce..."
Rausayarda kaina na yi gefe na ce.
"But miyasa wai kullum kake son stressing kan ka ke akan yaran nan? Musamman su Aryaan da Abdallah fisabilillahi! Su ɗin fa a yanzu they are not kids anymore..."
Wani murmushin ya yi mini tare da girgiza kansa yana kallona ya ce.
"Bibi....kema ke san ba zan iya ba. Ko na ce ba zan sake ba, sai na ƙara ɗin...su ɗin rayuwa ta ne wanda idan babu su tamkar rasa numfashi ne..."
Zarah ce ta ce.
"Daddy next week birthdayn Ƙawata Hala kuma gashi bama nan, kuma ni I don't want miss the party, and so nake mu tafi tare kamar wancan time ɗin ka ji dan Allah Daddy.."
Wani kallon Aliyu ya mata sannan ya ce.
"Komai Hala komai Hala! Sai ka ce ita wani son ki take.."
Wata uwar hararar ta ɗana masa sannan ta kalle ni ta ce.
"Dan Allah Maami ko ranar ba sun zo ita da Mum ɗin su suka duba Jadda ba?"
Kaina na jinjina mata ina murmushi na ce.
"Share shi wasa yake miki.."
"Kuma ma ai ta zo ranar da Daddy ya dawo daga Dubai, sannan ta ce tana son Maamina kuma tana son Ya Arhaam.."
Lokaci ɗaya kallonmu ya koma kanta dukkanmu, sannan sai kuma muka kalli Arhaam ɗin wanda ya zaro ido alamar mamaki sai kuma ya ajiye spoon ɗin hannunsa ya yi dariya ya ce.
" eyyah! Ga shi ni kuma ta mini ƙarama da aure. "
Sake Kallonsa muka yi ni da Daddynsu na ce.
"What?"
Jinjina kansa ya yi hankalinsa kwance ya ce.
"Maami da gaske nike faɗamuku. Yanzu ina da 19yrs, karatuna 5yrs ne, kinga ina kammalawa zai kama 24yrs to a 25 zan yi aure..."
Wani irin mamaki ne da al'ajabi ya cika mini zuciya. Kallon Daddyn na su na koma yi don in ji mai zai ce. Kawai sai naga yana dariya cike da farin ciki yace.
" Gaskiya wannan tunani ne mai kyau. And kuma na goya baya ɗari bisa ɗari...."
"Haba Daddyn Abdallah! Wai biye shi za ka yi?"
"Bibi...miyasa ba zan biye shi ba? There is nothing wrong dangane da maganar da ya yi,kin fa ji plan ɗinsa, kuma plan ne mai kyau, akayi aure da 20yrs ma ballantana 25yrs. Yana da nutsuwa, yana da kuɗi, yana da gidan da zai ajiye ta sannan yana da sana'arsa, to mine ne zai dame ki?... "
Waigawa ya yi ya kalli Aryaan wanda tun ɗazu ya ajiye spoon ɗin yana duba wayarsa ya ce.
" Kai fa Aryaan? Miye ra'ayinka?"
Arhaam ɗin ya kalla sai kuma ya kalleni sai kuma ya kalli Baban yace.