Ganin ido complete - Chapter 77
Ganin ido complete Chapter 77: Ganin ido complete Chapter 77. " Arhaam and Aryaan are thesame as always Daddy. Duk abunda ya tsara, to nima hakan ne a…
3,146 words
" Arhaam and Aryaan are thesame as always Daddy. Duk abunda ya tsara, to nima hakan ne a wurina..."
Wani irin washe baki ya yi yana ta farin ciki yana musu addu'a, ni dai mamakin duniya ya ishe ni.
"To kun samu budurwar ne?"
"A'a, tukunna dai Daddy. But na ji Aryaan na zancen Siyama ta gidan Mummy Hairiyyah.."
Jinjina kai ya yi yace.
"Wow! Wannan tunanine mai kyau, kuma kunga za'a ƙara ƙulla zumunci ya ƙara ƙarfi....da wuri zamu fara shirye-shiryen auren nan domin komai ya tafi a daidai.."
Kallon Aliyu na yi na ce.
"Shin wai ba za ku tashi ku tafi Islamiyya ba ne? Sai kun ga biyar ta yi ku fara mini muzurai ko?"
Miƙewa ya yi yana faɗin.
"Daman na kambala, I'm sorry my Maami, watsa ruwa kawai zan yi sha-shaf na zura uniform...ke fa Zarah?"
Ya ambata daga ƙarshe yana kallon inda Zarah take zaune kusa da Daddynta.
Itama dai miƙewa ta yi tana faɗin.
"Ni dai bana son wanka yanzu sai na dawo."
Jinjina kaina na yi na ce.
"To na ji! Wuce ki canja kayan. Ke kika sani, Allah ya tsare."
Sai da ya rakasu har mota yana mai jawa drivern na su kunne wanda kullum inda sabo to ya saba da wannan jan kunnen na ya lallaɓa da su a hankali.
Daga can bai dawo gidan ba sai da ya yi sallar isha sannan ya shigo.
Har muka yi shirin kwanciya bacci ni dai maganar nan tana nan ta tsaya mini a raina. Ganin yanda na ke ta wani iri yasa ya janyoni murya a ƙasa sosai ya ce.
"Why are you silent Bibi?"
Kallon idonsa na yi na ce.
"Amma ka ji fa zancen yaran nan? Har kuma kake biye su.."
Murmushi ya yi sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya yi twisting hannunsa a nawa softly ya ce.
"Bibi..wannan fa ba abun damuwa ba ne, dan Allah ki kwantar da hankalinki kuma ki godewa Allah da ya baki shiryayyun 'ƴa' ƴa. Ni fa haka nake ganin baiwar su kamar ke ɗin nan. Komai suna yin sa da lissafi da kuma hangen nesa. Ni ko a yanzu suka ce suna son auren tabbas zan yi musu shi. Domin they lack nothing, abun da ya kamata ki yi farin ciki kuma ki goya musu baya kiyi musu addu'a...."
"Shikenan! Allah yasa albarka ya nuna mana lokaci lafiya. Amm! Cewa na yi, ko dai za ka tafi kai ɗaya ne tun da one week ne za ka yi Kaga sai..."
"No, we are going together. Ai taron na rana ɗaya ne kawai, kinga zamu iya ziyartar Baba Ustaz, daman tun da kinga tsawon 3yrs ake magana bamu ziyarce su ba...Ga auren Suhaima ma, ɗiyar Engineer Abdulqadeer....."
Zaro ido na yi na ce.
"Da gaske?"
"Uhm! Daman cewa na yi kar a sanar miki, domin da wahala idan zamu iya attending.."
"Suhaima fa Daddyn Abdallah! Gaskiya gwanda da Allah yasa na ji wannan maganar, domin ya cancanci mu je. Yanzu da kake zancen auren su Aryaan ɗin idan ba su zo za ka ji daɗi?"
Hannu ya kai ya ja hancina yana murmushi ya ce.
"Ayi haƙuri to, na yi kuskure. Sai mu shirya mu tafi, Kinga muna kambalawa sai mu wuce kawai, daga can ko kwana ɗaya ne sai mu yi a Sokoto."
"Uhm! Hakan ya yi, Allah ya nuna mana."
"Amin. Ki rage gudun Acn nan sosai, sanyin na ji ya mini yawa."
"Ok,"
ta shi na yi na je na kashe sa gabaɗaya sannan na rage hasken fitilar na zo na kwanta.
******
Muna isa muka wuce gidan Baba Ustaz ɗin kamar yanda muka tsara shi kuma ya tafi wurin yin taron da ya kawo sa.
Baba ya yi farin cikin ganinmu sosai wanda sai da muka kwana biyu sannan muka wuce Kaduna gidan Nadeeyah muka wuni sannan muka wuce Gusau inda a yanzu Aunty Labiba ce kaɗai ke zaune a nan. Gidanmu muka shige muna ta hidiman Suhaima sannan daga nan muka samu time muka ziryaci Ya Hafiz inda a nan Mummy Zaliha take zaune wacce ta yi farin cikin ganinmu, sai kuka take tana ta mana addu'a. Daga nan muka wuce gidan Maman Fakiha wanda su ma yanzu sun canja gida muka gaishe ta sannan washe gari bayan an wuce da Amarya Kano mu kuma muka wuce Sokoto.
Duk wanda na shaida wa zancen auren nan da suka yi sai dai ya yi dariya, ya yi musu fatan alheri. To itama Ammie dai dariya ta yi sosai sannan ta kalle su ta ce.
"ikon Allah! Kamar jiya ne fa aka haife ku a gidannan!"
Arhaam ne ya ce.
"To ai farin ciki za ki yi, kin samu dama har guda biyu,...kinga na farko kina a duniyar aka haifemu, sannan na biyu kina a duniyar zamu yi aure."
Jinjina kai ta yi ta ce.
"Alhamdulillah! Na godewa Allah, Allah ya nuna mana lokaci lafiya ya bamu aron rai da lafiya mai amfani. Kunga baku gado Uncle ɗin ku ba, shi da sai da ya yi kamar ba zai yi auren ba sannan ya yi daga ƙarshe..."
Aryaan ya ce.
"Kin ga fa sai da na faɗawa Daddy cewa mu je Lagos gidan Uncle Bahrain ɗin, amma Maami ta ce wai lokaci ya ƙure mu bari next time."
Kallon sa na yi na ce.
"Akwai abu mai Muhimmanci ne da nake targeting shiyasa bana so mu ɓata lokaci a nan."
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"Ai na fahimta Maami, ba komai....Grandma ina Abbu ne?"
"Abbu Yana Bunza tun jiya, amma dai yau ɗin nan zai dawo. Ina Jadda?"
"Jadda lafiyanta ƙalau tana can tana fama da glass."
"Mummy Kausar fa?"
"Kausar tana school..."
Murmushi na yi ina kallonta na ce.
"Shikenan Ammie kin hana Kausar ta ɗaga ko'ina? Kin fi so tayi karatun a nan?"
"Wallahy fa Beenafah am, bana son abin da zai sa ta yi nisa dani, duk kun mini nisa daga ke har Bahrain ɗin, hakan yasa ba zan iya bari ta yi nesa dani ba. Zuwa 6pm za ku ga ta dawo."
"Mama Asma'u dai itama jiki yaƙi daɗi?"
"Hmm! Ai yanzu ma kam jiki Alhamdulillah! Ta ji sauƙi sosai ba kamar can baya ba."
"To Allah ya ƙara afuwa, yasa kaffara ne."
"To amin."
Daga haka ta tashi ta shiga hidima da su, komai kawo musu take yi tana ta farin ciki da ganin su.
Sai da muka kwana biyu sannan muka koma gida.
Bayan mun koma sai da ya yi kwana biyu ya huta a gida, sannan ya raka Zarah Birthday party ɗin ƙawarta da Shi da Abdallah da Haidar sannan ya shirya washe gari ya tafi majalisa.
Bayan ya dawo ne yake shaidamin cewa, akwai tafiyar da zai yi ƙasar amma daga ni sai Zarah zamu rakashi saboda yanayin karatunsu.
Na so ya ɗaga tafiyar bisa wani dalili amma ya ce min ta gaggawa ce kuma mai muhimmanci. Hakan yasa dole na haƙura.
Fira muka zauna yi har ƙarfe ɗaya na dare akan cewa zai yi kewar su saboda haka su tsaya su mi shi fira,sannan daga ƙarshe ya rakasu wurin baccinsu sannan ya dawo muka kwanta.
Washegari koda suka dawo daga masallacin asuba ni har na gama shiryawa domin cewa ya yi da wuri yake so mu isa.
Bayan na gaishe shi na ce.
"Kai ne fa kace da wuri zamu fita, amma shi ne sai yanzu ka dawo? Wataƙila kuma ka sha'afa ne?"
Girgiza kansa ya yi camly ya ce.
"Wasu bayin Allah ne dai suka tsayar da ni a masallacin bayan na kambala Azhkar..."
"Allah sarki! Wata ƙil sun yi ta zuwa basa samun ka?"
"Haka dai suka ce, to amma ai ba dole sai ɗin ba,.."
"Ai kasan halin mutanen ne, dole duk abinda za'a faɗa musu ba za su gamsu ba, sai dai sun gan ka ɗin ido da ido. Allah ya ƙara maka tsawon rai mai albarka ya ci gaba da dafa maka akan komai."
"Haka ne kuma....kinga, na ji kaina ya ɗan saramin kaɗan, ki kawo min Tea Mai ɗumi da maganina dan Allah, idan na sha sai in ɗan kwanta nasan abubuwa ne suka mini yawa, amma in sha Allah daga zaran mun dawo wannan tafiyar zamu tafi huta mai nisan zango."
Cike da tausayawa na ce.
"Eyyah! Sannu. To ko dai na kira likita? Sosai yake ma ciwo?"
Hannuna ya riƙo ya sumbata sannan ya yi mini murmushi ya ce.
"Relaxed please...ji duk yanda kika wani ruɗe. Lafiya lau nake kin ji ko. Ki kawo min Tea ɗin yanxu."
Murmushin na yi sannan na sauke ajiyar zuciya a hankali na lumshe idanuna na buɗe sannan na ce.
"Ok! In sha Allah zai daina....bari na je yanzu zan kawo maka."
Sai da na shiga wurin Jadda na dubata sannan na yi mata sallama akan zamu ɗan yi tafiya sannan na fito na je da kaina na haɗa masa Tea ɗin na je ɗaki na buɗe locker na ɗauko masa magani sannan na dawo ina tashinsa akan ya tashi.
Kiransa nake amma ko alamar motsawa bai yi ba. Hakan yasa na ajiye abun da ke hannuna ɗin kan wani glass table dake gefe Sannan na matsa na ce.
"Kar ka ce har ka yi bacci Daddyn Abdallah? Daman ina yawan ce maka ka riƙa hutawa sosai amma kullum cikin hidimar mutane ka ke baka hutawa,...Amma ni na san mi zan yi a wannan karon...Daddyn Abdallah! Dayaa! Ya Mohaa!!"
A ruɗe na faɗa jikinsa duk na bi na gigice ina faɗin.
"Dayaa please, ka amsa ni dan Allah...Masoyina..ka duba ni, gani na kawo maka Tea ɗin fa. Please.."
Wani irin abu ne mai nauyi na ji ya motsa a zuciyata, ganin da gaske bai motsa ba, bai kuma amsa ba. Zuciyata ce na ji ta karye, da ƙarfi na shiga kawar da tunanin da zuciyata da ƙwaƙwalwata suke har ba mini domin hakan ba za ta faru ba, kiransa nake da ƙarfi amma babu amsa...ji na yi wani irin kuka ya zo mini, amma still na dage ina ta jijjigasa ina ihun kiran sunansa.
Da gudu na fito ina ƙwala kiran su Aryaan a gigice na ce musu su kira likitan babansu kamar ya suma.
Ina gama faɗamusu na je na kira Uncle Mu'aƙƙib amma sai yake faɗa mini wata magana wacce ta girmewa ji na da ganina wai Dayaa ya tafi ya bar duniyar.
Wata irin super na yi na haye jikinsa tamkar na haukace ina faɗin.
"A'a...wallahy bai mutu ba, domin munyi alƙawarin cewa a tare zamu mutu. Dayaa ba zai taɓa mini haka ba. Ya yi alƙawari ba zai taɓa bari na ba. Dan Allah ka tashi ka faɗa masa cewa kai ɗin ba za ka taɓa bari na ba...Daddyn Abdallah dan Allah!!! Dan Allah kada ka barni... "
Shigowar su Arhaam ce na ji suna ta faɗin.
" Innalillahi wa inna ilaihi! Daddy ya rasu? No... Please doctor go and check on him. Ta yi yu dai wani abun ne na daban...mutuwa dai? Haba! A'a kam!"
Janyewa na yi tare da zubawa likitan ido da gaske, sai kace shi ne wanda zai hana sa mutuwar.
Sai dai bayan ya gama duk wani gwajin sa ya kalle mu inda muke tsaitsaye cirko-cirko muna Kallonsa ya ce.
" I'm sorry..."
Wata irin faɗuwa na yi tare da keta wani irin ihun tashin hankali kamar wata mahaukaciya ina faɗin.
"A'a...aa dan Allah! Ku daina! DAYAA na yana raye Ƙarya ne ba zai mutu ba. Ya yi mini alƙawari fa...Sai da fa ya tabbatar min cewa lafiyarsa ƙalau. Taya yanxu zaku ce min wai ya rasu.??"
Wani irin kuka ne muka shiga yi tare da daddafe gawar sa daga ni har 'ƴa'ƴanmu kamar hakan zai dawo da shi duniyar.
Faɗin nake.
"Mutuwa miyasa? Miyasa yanzu mutuwa? Mi nai miki da kika zaɓi rabani da masoyina...kin san wanene mijina a gare ni kuwa? Shi ɗin duniya ta ne! Shi ɗin komai na ne.."
"Subhanallah! Haba Beenafah! Ki yi haƙuri kada ki aikata saɓo mana..."
Gyaɗa kaina na yi da sauri ina faɗin.
"To na bari Uncle Mu'aƙƙib. Amma dan Allah kace masa ya bar wasa ya tashi...munyi alƙawari da juna..mummun.."
Faɗuwa na yi a jikinsa na some tsabar kaɗuwa.
*******
Kafin ka ce mi, Oumdurman ta girgiza da mutuwarsa, dangi kowa ya shiga tashin hankali da gigita jin labarin mutuwar da ba bu labarin ciwo ko wani accident ko wani abu da zai sa ace ai ya yi wata jinya.
Har aka masa sutura na kasa yarda cewa wai ya mutu, Su Aunty Labiba su Hajiya wacce ke zaune da Emraan a Yanzu, duk sai da suka iso sannan aka yi shirin binne sa.
Bana cikin hayyacina, na ɗimauta, na gigita, na ji gabaɗaya kowa da komai yake cikin duniyar nan ya fice mini a rai. Babu abinda nake so da ji da gani idan ba mijina.
Yara ma duk sun gigice har Zarah da take ƙarama a cikinsa ta gigita da mutuwar mahaifin su.
Bayan an gama shiryasa muka tsaya jikin gawar sa, na sumbaci goshin sa na ƙarshe, ina mai jin wata irin ƙuna a raina na ce.
"Mutumin kirki! Mijina ka tafi ka barni da yaranka masu ƙaunar ka, ka tafi ka barmu a lokacin da rai da tunani ba su tsammata ba, kai ne wanda ya yi min alƙawari, amma a yau wannan alƙawarin ya karye, kai ne mijin da ya fi kowane miji a duniya, Mijin Beenafah mahafinsu Arhaam, ina son ka ina ƙaunarka, na yafe maka duniya da lahira...zan kula da amanar 'yayanka. I will raise your children with honor, I will protect your name, I will continue your dream but ba zan taɓa daina son ka ba har abada. Kai ne masoyina na farko kuma na ƙarshe...Allah ya gafarta maka, Allah yasa mutuwa ta zamto hutu a gareka, Allah ya yalwata makwancinka yasa ka a Aljanna maɗaukakiya..."
Kwantawa na yi akan jikinsa na sake fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi. Ganin bani da niyyar ɗagawa yasa Ammie ta zo tana mai share hawayenta daƙyar ta iya nasarar ɓanɓareni akan gawar tasa.
Ina kallo aka fita da shi wanda bani da iko ko kuma zarafin hana faruwar hakan. Haƙiƙa mutuwa, tana da ɗaci, mutuwa tana da maye, mutuwa tana da tsananin ƙuna da raɗaɗi.
Kowa sai haƙuri yake bani ana ta lallashi na, musamman Jadda wace ke ta kuka tana faɗin dama mutuwar ita ce wacce ta ɗauka ta bar mini Hammodina.
Na shi wani irin yanayin da ko maƙiyina ya kalle ni sau ɗaya sai ya tausaya mini.
Kalamansa da dama idan na tuna suna nakasa zuciyata in riƙa jin ina ma ace mutuwar nima ta zo yanzu ta ɗauke ni na je na tarar da shi. Haƙiƙa mutuwa tai mana gaggawa. Miyasa ba ta barshi ya cika burin shi na aurar da En biyun sa ba?
Haka muka zauna zaman makokin da ko ruwa wannan bana iya haɗiye wa sai idan Ammie ce ta matsamin.
Hmm! Tabbas ba za ka taɓa sanin zafi da raɗaɗin mutuwa ba sai idan an ɗanɗana maka ita. Ƙarfi da yaji nake neman rasa hankalina wanda sai da aka dangana dani ga likita depression na nema ya kamani. Duk abunda nake shi nake gani, tunaninsa ko na minti ɗaya ya kasa barin ƙwaƙwalwata. Mutuwa ba ki yi mini adalci ba.
Ina jin yanda Su Ammie suka hau kaina wurin haɗa baki ko Allah zai sa na iya fahimta amma sai na ji yanda wani abu ya taso ya rufe mini zuciya a lokaci ɗaya. Gabaɗaya ganina da ji na suka ɗauke, ina mai ganin wani irin duhu akan idanuna.
A tsaye nake amma haka na ji na fara tafiyar a hankali na zube ƙasa ba numfashi a tare dani.
✍️ *OUM-AMEER*. ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 60*
"BIBI...BIVILOVE...BIBINA..."
A hankali na motsa daga position ɗinda nake akan gadon, sannan na shiga buɗe idanuwana slowly ina mai jin yanda Kai na yake wani irin sara min da amsar kuwwar Kalmomin da mutum ɗaya ne kawai yake da dama da ikon sarrafasu a kaina a duk lokacin da yaso. Kalma ce wacce nake fata da burin sake jinta ko da sau ɗaya ne a cikin rayuwa ta.
Sai dai kuma, Ammie na gani tsaye a gefena ita da Aunty Labiba suna mini wani kallon mai ɗauke da tsananin tausayi. Kallon da ya sarar mini da gwiwata ya kuma ƙara tabbatar mini da cewa na makara, domin dai ta tabbata cewa har yanzu dai ma mafarki nake ba, Dayaa na ya tafi ya barni har abada.
Duk da haka, Kalmomin da na ji su a kaina ne na shiga maimaitawa tare da yunƙurawa na hau dube-dube ina faɗin.
"Daaya na amsa maka...kana ina?"
Sai kuma na kalli Ammie na ce.
"Wallhy ina ji yanda yake kirana ko ku ba kuji ba ne?"
Kuka ne ya ƙwacewa Aunty Labiba wanda har yasa ta juya ta fice daga ɗakin ba shiri, domin ji take zuciyarta ba za ta iya ɗauka ba. Mutuwa mai yankan ƙauna. Kalli yanda kowa ya rasa nutsuwarsa dan Allah,ƙannensa, 'ƴa'ƴansa, iyayensa kowa ya ɗimauce.
Ammie kuwa, itama share hawayen ta ta yi tare da samun wuri a gefen gadon ta zauna ta kamo hannuna a hankali ta ce.
"Kin san me Beenafah? Rayuwa gaskiya ce, soyayya gaskiya ce, samun 'ƴa' ƴa samun farin ciki gaskiya ne,riskar yanayin baƙin ciki ma a cikin rayuwa gaskiya ne, dangi da abokai gaskiya ne, komai na duniya da kika yarda da gaske yana existing kamar yanda Ubangiji ya tsara mana....to itama MUTUWA gaskiya ce. Allah fa ya yi alƙwari da kansa kuma ya tabbatar da cewa, Wallahy dukkan wata rayuwa lallai mai ɗanɗanar mutuwa ce. Kafin mijin ki ya mutu...sai da Mahaifinki ya mutu, sai da Yayan mahaifinki ya mutu, sai da ƙaninki ya mutu, sai da kakarki da kanki suka mutu, sannan Mijin ki ya mutu, muma a haka watarana duk zamu mutu ɗin, sai dai mutuwa ba ta bada notice, duk lokacin da Allah yace ka bar duniyar...wallahy za ka barta ko ka shirya ko baka shirya ba. Za ki mutu, zan mutu, kowa ma zai mutu Beenafah, domin wannan duniyar ba ma tabbata ba ce, lahira ita ce gida na gaskiya wanda kowa a can zai tafi kamar yanda mijin ki ya tafi. Ki buɗe zuciyarki ki amshi gaskiya Beenafah,Ki yarda wanda ya mutu baya dawowa, abin da ya kamata ki yi haƙuri, ki ɗabbaka haƙuri mai kyau, in sha Allahu za ki zama mai nasara a rayuwa.... "
Wani irin kuka nake yi wanda matuƙar Kanada zuciya a ƙirjinka...to tabbas sai ka zubar da naka hawayen. Kuka nake ina girgiza kai na na ce.
" Ammie ashe da ciwo haka? Da ciwo sosai Ammie...Na kasa yarda cewa wai da gaske ya mutu! Ammie ina zan saka raina? Ya tabbatar min da cewa lafiyansa ƙalau, tafiya muka shirya a ranar zuwa ƙasar Lebanon..Ammie ya saka burin aurar da su Aryaan..."