Ganin ido complete - Chapter 78
Ganin ido complete Chapter 78: Ganin ido complete Chapter 78. "Dukkan wani ɗan Adam da buri a rayuwarsa yake mutuwa Beenafah. A da ya kasance a duniyarsa…
3,314 words
"Dukkan wani ɗan Adam da buri a rayuwarsa yake mutuwa Beenafah. A da ya kasance a duniyarsa shi kaɗai wanda ya cire rai da tsammanin cewa zai yi aure a rayuwar nan, a lokacin kuma yana da buri da addu'ar ko auren ne dai ya samu ya yi ko shi kaɗai ya yi Allah ya cika masa burinsa. kwatsam sai Allah ya haɗa ku kuka yi aure, sai kuma ya fara buri da fatan samun haihuwa wacce yake ji ai da ya samu haihuwar burinsa ya gama cika a duniya. Ya samu yaran, ya yi farin ciki, ya yi dariya ya yi kuka a tare da su, ya taka matsayi da rawar da duk wani nagartaccen uba yake taka wa. Bayan nan kuma, sai ya sake ɗora sabon burin Aurar da 'ƴa'ƴan nasa, amma sai rai ya yi halin sa...to ina tabbatar miki, wallahy tallahy da za'a sake dawowa da shi duniyar domin ya aurar da yaran, ko da ya cika wannan burin sai ya sake ɗora wani na son ganin 'ya'ƴan 'ƴa' ƴansa ma'ana jikokinsa da kuma sake burin aurar da Zarah da take ƙarama a cikinsu. Zai iya burin sake maimaita wasu shekaru hamsin ko fiye da haka tare da ke da kuma iyalinku. Kowa a haka yake tafiya Beenafah! To kinga ko a haka sai a godewa Allah. Wani ana haihuwarsa yake mutuwa, wani ana ɗaura masa aure amaryar ba ta kai ga tarewa ba zai faɗi ya mutu, wani kuma har ya mutu 'ƴa'ƴa ne ba zai samu ba. Saboda haka ki yi haƙuri, ki ci gaba da yi masa addu'a domin ita ce abun da yafi buƙata a halin yanxu. Hammodi ya rasu ba wai mafarki bane ko gizau abun yake miki, mutuwa gaskiya ce kuma hakan ce ta faru da shi. Ki yi haƙuri ki ƙwarara kanki ko don yaran ku. Idan kin zamto haka su da suke cikin giya da mayen mutuwar su ma ɗin ya kike so su yi?"
Kwantawa na yi a jikinta ina ta rusa kuka tare da jin yanda kalaman ta ke tasiri a cikin ruhi da gangar jikina.
" Ki yi hak'uri! Kowa haka ya ji, mutuwa ba ta daɗi, ita ce mafi girman ƙaddara a cikin rayuwar ɗan adam wanda take ɗauke shi a duk lokacin da Allah yaso, ko da ciwo ko babu ciwo. Mijin ki mutumin kirki ne Beenafah, ya samu yabo sosai. Ki godewa Allah ki ƙara godewa Allah. Ki yi haƙuri. Ki ƙarfafa kanki ko don ni mahaifiyarka da yaran ki. Shi kansa zai fi samun nutsuwar kwanciya idan kika daina koke-koken nan kika duƙufa yi masa addu'a dake da yaran ku.. "
Kalmomin sa ne suka shiga dawo min daki-daki a lokacin da mukayi 15 anniversary wanda muka yi a ɗakin Ka'aba mai tsarki. Shi ne wanda ya kawo tsarin kuma muka tafi baki ɗayanmu muka yi ibada tare da yin addu'o'i...wallahy ji nake tamkar yanzu ne yake furta waɗannan zantukan a gare ni cewa.
" Bibi...ko a haka na mutu Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Na samu mata ta gari, na samu 'ƴa'ƴa na gari, na samu dangi masu so na waɗanda suka tsaya dani a kowane irin yanayi. Rayuwa ta yi mini komai..."
Jinjina kaina na yi ina share hawayena tare da kawar da tunanin ina mai jin wani irin ɗaci na ce.
" Allah ya gafarta maka yasa ka a Aljanna maɗaukakiya, Allah ya bamu haƙuri da juriyar rashin ka, Allah ya shiryar maka da zuriyarka ya sa su zamto masu jinƙai da addu'a a gareka. Na yi alƙawari ba zan ƙara kuka ba, amma ka sani zuciyata za ta mutu da kewarka da kuma ci gaba da begenka har zuwa numfashina na ƙarshe..."
Hannunta ta kai a hankali tana bubbuga bayana tare da ƙara bani kalaman lallami da kwantar da hankali.
Da haka ta samu ta lallaɓani na ɗan ci abinci na yi sallah sannan muka fito inda na tarar Zarah tana kwance jikin Sis Nourah wai jikinta ya yi zafi tana jin zazzaɓi.
Wuri na samu na zauna ina mai saukar da kaina a ƙasa tare da share hawayena ganin yanda Hairiyyah ta yi wani iri duk ta zabge ta fi ce hayyacinta.
Mutane ne ta kowane ɓangare suke zuwa mana gaisuwa wadanda mafi yawa da cikinsu ni ban ma san su ba.
Shi ma Aliyu yana nan maƙale dani a duk inda nake, Su Aryaan ne ke can waje inda iyayen na su maza suke har aka kambala zaman makokin a hankali kowa ya shiga watsewa.
********
Bayan watanni shi da sun shuɗe, haka na ci gaba da ganin mutuwar mijina wasa. Ji nake kamar zai dawo, ji nake kamar komai wasa ne, amma kuma idan har ina son gaskiya...to fa ya tafi har abada ba zai dawo ba. Na yarda duniya ba ta tabbas, babu abin da yake ɗorewa da ci gaba da wanzuwa sai Allah maɗaukakin sarki, shi ne wanda bai haifa ba kuma ba'a haife sa ba. Da yardarsa da amincewarsa komai na duniya yake tafiya.
Shekaru ashirin sai suka zamo mini tamkar kwana ashirin bayan na tabbatar na rasa shi har abada. Na amince da shi ba tare da na taɓa ganin fuskar sa ba. Na so shi so mai tsanani a lokacin da zuciya da ruhi suka amince da shi a matsayin masoyi wanda ya cancanta kamar yanda shi ma ya ɗauke ni. Mun gina rayuwa mai inganci da tarin albarkoki da alkairai waɗanda ba zan taɓa mantawa da su ba.
Kuɗi ko mulki ko sarauta ko talauci babu wanda zai hana maka mutuwa idan lokacin ka ya yi. Da ciwo da babu ciwo idan lokacin ka ya yi sai ka tafi. Da ace lafiya ko kuɗi ne ko wani jindadi zai hana mutuwa, tabbas da Dayaa na bai mutu ba. Domin yana yawan zuwa check up kuma baya yawan rashin lafiya domin sai ya shekara bai yi ciwon kai ba. Amma da yake mutuwa duk bata duba wannan. Sai gashi ta ɗauke shi ta barni da kewa.
Tun last week Ammie ta zo akan cewa tana so ta ji mi na yanke dangane da rayuwa. Ni dai ban ce mata komai ba, domin akwai abubuwan da nake hangowa da haskowa a cikin rayuwar 'ƴa' ƴana.
Yau ma tunda na wayi gari ina kwance a ɗakin sa na kasa tashi ma ko wanka na yi. Ko breakfast ban yi ba.
Hakan yasa Abdallah ya ƙara shigowa ɗakin ya same ni bayan ya nemi izinina ya zauna yana faɗin.
"Grandma ta shigo tana parlourn ki Maami. Yau har yanzu ko breakfast ba ki yi ba. Dan Allah ki daure ki tashi..."
Kallonsa na yi sai kuma na duba agogo ina faɗin.
"Miyasa ka ke gida har yanzu baka fita school ba?"
"Na gayawa driver na cewa ba zan fita school ba tun jiya. Saboda yanayin ki yayi kamar bakya jin daɗi. You are just hiding it Maami....Su Ya Aryaan ma suna duba abinci suka tambayi Miss Mairah ta tabbatar musu cewa baki fito ba kawai suka fice ba tare da sun ci abincin ba...ki na ji ko Maami...yanayin ki is killing us,we are not happy a yanda kike. Ke ce ƙwarin gwiwarmu kuma dogaronmu. Mun rasa Daddy...idan muka rasa ƙarfin gwiwarki zamu susuce rayuwarmu ta samu tangarɗa."
" Zarah fa? Mairah ɗin ta gama shirya mata?"
Na tambaye shi, domin na yi ƙoƙarin kawar da zancen duk da cewa na san gaskiya yake faɗamin.
" Eh, tare suka fita da su Ya Arhaam ɗin, sun ce sune za su ajiye su school ɗin."
Miƙewa na yi na zauna a hankali ina mai share hawayena na jinjina masa kaina ina murmushi na ce.
" Abdallah! Ku yi haƙuri, ni ɗin tabbas na kasance mai tsananin son kai na, damuwata kawai nake dubawa, amma daga yau na yi alƙawari...zan yi iya yina."
Hannuna ya riƙa har bakin toilet yace.
"Ki yi wanka ki shirya kin ji Maami, ni zan je na haɗa miki wani abin karin da kaina. Grand Ma tana jiran ki."
Murmushi na yi tare da jinjina masa kaina ba tare da na yi magana.
Bayan na yi wankan na kambala na fito na shirya sannan na fito inda Ammie ɗin na gaishe ta sannan muka gaisa da Bahrain wanda ya iso ƙasar jiya da dare.
Kallona Ammie ta yi ta kira sunana a hankali ta ce.
"Beenafah!"
Ɗagowa na yi na kalle ta tare da amsa mata sannan ta ce.
"ina ta magana tunda na zo ba ki ce komai ba."
Jinjina kai Bahrain ya yi idonsa a kaina cike da kulawa ya ce.
"Aunty Beena...Life won't continue like this. Dole ki farka ko don goben yaran nan..."
Jinjina kaina na yi ina share hawaye na ce.
"Daman na yanke wata shawara ne. A lokacin da ƙaddara ta haɗamu da Ya Mohaa, a Nigeria rayuwarmu ta fara, sai muka koma Dubai, wanda bamu taɓa kawo ƙaddarar zama a Oumdurman ba. Sai gashi ta kasance gidansa na ƙarshe. Ta dalilin sa ne muka zo nan ɗin, to abunda na yi tunani, idan na ci gaba da zama a nan, zan ci gaba da karyewa ne har abada. Zamu koma UAE tare da su su ci gaba da karatunsu ni kuma na ci gaba da kulawa da su. Akwai abubuwa da dama da yasa na zaɓi na koma can da zama, sannan a tsohon gidanmu zamu zauna inda muka fara rayuwa..."
Murmushi Ammie ta yi tana mai jinjina kanta ta ce.
" Ba komai Beenafah, tunani ne mai kyau, Allah ubangiji ya ci gaba da jiɓantar lamarin rayuwarku damu baki ɗaya. Allah ya ƙara miki haƙuri da juriya ya baki ikon kulawa da Amanar waɗan nan yaran."
"Amin Ammie, na gode sosai."
Ɗan ƙara tattaunawa muka yi sannan daga ƙarshe ta kirasu Uncle Mu'aƙƙib ta sanar musu wanda ta ce ita ce ta kawo wannan shawarar da take tunanin kamar za ta kawo sauyi a cikin rayuwata. Cikin ikon Allah dai gashi kowa ya goyi baya hakan yasa muka shirya cikin wata ɗaya muka koma UAE inda tarihin rayuwarmu ya soma.
Alhamdulillah! Komawarmu sai in ce ta ƙara haske sosai a cikin rayuwata. Domin na ɗan saki raina duk da a gidan komai yana mini watarana kamar zan ga Dayaa na a ciki. Abubuwa da dama idan na tuna sai dai in shige ɗaki na kulle kai na na yi kukana ba tare da sun sani ba. Yarana sun kasance abun alfaharina, domin sun tsaya sosai wurin bani haɗin kai wurin gudanar da rayuwar tamu bisa tsari. Musamman su Aryaan da suka tsaya akan ƙannensu da basu kulawa yanda ya kamata. Sannan Emraan da Suhaib ma sun tsaya sosai a kansu musamman Emraan wanda ya tsaya kai da fata tamkar 'ƴa'ƴansa na cikinsa. Hakan sai ya ƙara kwantar mini da hankalina sosai Alhamdulillah.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar damu a kwana a tashi har su Aryaan ɗin suka kambala Degree ɗin su yayin da Abdallah ya wuce Jami'ar Madina domin karantar fannin larabci kamar yanda ya yi buri da shi da mahaifinsa. Daman shi ɗin rayuwarsa tun tashin sa ya taso ne da son gefen addini wanda a nan rayuwarsa tafi karkata. Tun a shekaru goma ya sauke alƙur'ani sannan yana da sha biyar muka yi masa walimar haddacewa wanda har abada ba zan manta wannan ranar ba, domin Daddynsu yayi matuƙar farin ciki har da kukansa akan yanda abun ya faranta masa rai. Shiyasa bamu hana sa akan abinda yake so ba. Kuma In sha Allahu, a hankali wannan kudurin nasa zai cika.
A shekarar da suka kambala karatunsu, a shekarar na samu Ammie muka tattauna tare da su Emraan akan zancen auren su Aryaan kamar yanda muka tsara. Bayan mun kai ƙarshe ne aka saka rana da lokaci inda Aryaan aka tabbatar da maganar sa da Siyama er Hairiyyah kamar yanda ya zaɓa sannan Arhaam da kuma 'ƴar gidan Raihab da Aunty Husaina wato Amal.
*******
Shiri muka shi ga yi na musamman wanda ta kowane ɓangaren sun ɗauki bukin da muhimmanci, kuma a nan muka yanke za'a yi domin a Oumdurman ma Jadda ta shekara biyu da rasuwa, hakan yasa muka yanke kawai a yi sa a nan ɗin.
Ana saura wata ɗaya Aunty Labiba suka iso da Aunty Nadeeyah domin kawai su kasance a tare dani wanda ba ƙaramin farin ciki ya bani ba.
Ina Zaune ina Gyarawa Zarah kanta wacce a yanzu itama ta fara zamowa Budurwa Aunty Labiba ta shigo.
Kallonta na yi ina murmushi na ce.
"Aunty Labiba kun ji ni shiru ko? Zarah ce ta sakani a gaba..."
"Ba komai ai, daman wata magana ce ke tafe dani."
Kallon Zarahr na yi na ce mata ta bamu wuri sannan na mayarda hankalina ina kallonta sosai na ce.
"Mummy Na'Imatu kuwa za ta zo?"
"Eh, Sun ce sai zuwa nan da sati biyu za su zo."
"Okay! Allah ya kaimu."
"Amin. Daman Beenafah, zance ne dangane da rayuwarki...babu wanda zai tilasta miki, amma zama a haka kamar ya yi wani iri Beenafah. Dole kowa yasan cewa kin yi rashi, amma rayuwa ba za ta ci gaba da a haka ba....ina neman afuwarki idan har maganata ta ɓata miki. Amma Emraan yace yana neman alfarma idan har zai yi yu, yana so zai aure ki...muma haka ɗin idan har ya kasance, to tabbas zamu fi kowa farin ciki, domin mun riga mun zamto ɗaya, idan har kina da buƙatar wani a rayuwarki, to tabbas Emraan ne yafi cancanta. Ya kamata ki ɗaura aure Beenafah ko don yaran nan.."
Wasu irin hawaye ne suka wanke mini fuska masu matuƙar ƙuna da zafi. Tabbas ba ita ce ta farko wacce ta fara mini wannan maganar ba. Ammie ta yi ta bina da zancen wanda har ta ga ji ta zuba mini ido.
Kallonta na yi ina mai jinjina kaina na ce.
" Na gode sosai da kulawa Aunty Labiba. Amma ki yi hak'uri ko Ince ki ce masa ya yi haƙuri. Na riga na gama aure a duniya. Babu wani namijin da yake burgeni, babu wani namijin da zai iya bani farin ciki kamar yanda mijina yake yi. Sai yanxu na fahimci ciwo da tsananin ƙuncinda ya kasance a cikin rayuwar Noura a wancan lokaci. Rasa miji babban ƙalubale ne a rayuwa..."
Cike da tausasawa ta ce.
"But at the end ta ɗauki shawara tayi haƙuri tayi auren, kuma ta yi farin ciki Beenafah..."
Girgiza kaina na yi tare da lumshe idanuna wasu irin zafafan hawaye suka sake sulalo mini na ce.
"I'm sorry Aunty Labiba...amma na riga na gama aure a duniyar nan. Har abada ba zan iya auren Emraan ba."
Ita da ta kawo shawarar...ƙarshe ita ce ta ɓige wurin lallashi da bani haƙuri har sai da na ji ƙuncin da ke zuciyata ya ɗan ragu.
Na san cewa Emraan tsayayye ne ga komai namu, duk wani abun da uwa da Uba za su yi wa 'ƴa'ƴansu, to tare da shi muke gabatar da shi, ko Walimar saukar Zarah wacce ita kaɗai ce Mahaifinsu Allah bai nufe shi da ganin wannan ranar ba, tare da shi muka halarta. Ko Abdallah da zai je Madinah, tare muka tafi gabaɗayanmu har Emraan ɗin wanda idan ba ka tambaya ba ba za ka ce ba shi ne mahaifinsu ba da gaske. Duk da cewa matsayin Uba daban ne a rayuwa, ba su taɓa neman wani abu da sunan mahaifi sun rasa ba, saboda ya tsaya a kansu bisa gaskiya da adalci wanda ba ya iya bambanta su da su Abeer.
******
Wannan hidimar ta tara mini mutanen da ban za ta ba ban kuma yi tsammani ba. Ko gefen Dr. Basheer kaɗai Su Mama Asma'u da su Mummy Sameera sun nuna mini karamcin da ba zan taɓa mantawa da shi ba.
Su Yaya Hafiz suma sun zo gabaɗayansu har Yaya Ahlan mijin Aunty Aysha.
Su ma Maman Fakiha da Baba sun zo har da Barrister Jafar wanda ni tun da suka iso har yanzu ban sanya shi a ido na ba.
Hidima muka shiga yi sosai, inda a nan muke shagalin Su Aryaan ɗin, da kuma gidan Suhaib sai kuma Qatar gidan Raihab wanda a can su Annie suka tsaya har sai da aka kammala ɗaura aure sannan suka iso da Amarya.
Koda aka shigo da su aka ajiye su a gabana tare da su Aryaan ɗin. Kuka nake sosai ina mamaki da al'ajabi wai ni ce yau nake da yara maza da suka yi aure? Ni Beenafah! Allah mai iko da rahama. Ga shi yau wannan ranar ta zo, amma babu Daddyn Abdallah. Ina ma ace yana duniyar? Ina ma ace yana nan zaune a gefena wannan burun na shi ya cika? Haƙiƙa mun rayu, kuma mun yi farin ciki ga albarkar 'ƴa' ƴa Alhamdulillah! Amma duk haka...har yau na kasa sabawa. Dariyar da yanda ya nuna tsantsar farin cikin da nake ji da gani a kunnuwana da idunawana a lokacin da Arhaam ya ce shi zai yi aure a 25yrs ɗin shi. Kamar zai ga wannan ranar da gaske, har ya fara tunani ya fara tsare-tsare, ko a jirgi lokacin da za mu yi tafiyar ƙarshe zuwa Nigeria babu zancen da yake idan ba na auren na su ba. Ya ce zai zan yi gayyata Bibi...zan gayyaci mutane da yawa, wanda duk kuma bai zo auren Mazaje na ni da shi mun datse alaƙa har abada...dariya muka yi dukkanmu. Har Aryaan ya ce, Daddy wannan kalmar Bibin tun muna jin kunyar ta har mun saba da ita. Tun ba mu san mi take nufi ba, har muka fara wayon sani, ga shi mun girma amma kaƙi ka daina ta. Yana jin Aryaan ya dire ya kamo hannuna ya haɗe a cikin nasa yana kallon su yana murmushi ya ce, Cancancacciyar kalma ce da ta cancanci nagartaciyyar Mace kamar Mahaifiyar su. Ita ɗin ta kasance ta musamman kamar yanda na saba faɗa muku, ban san wata kalma da zan kira ta da ita wacce ke bani farin ciki ba Fiye da wannan Kalmar..idan kuma ka ji an daina ambatonta...to ka ƙaddara bana duniyar.
A hankali Aryaan ya ɗaura kansa akan ƙafata, muryar nan cike da nuna zallar karaya ya ce.
"Maami! Daddy kike tunawa ba? Muma ɗin shi ne muke tunawa da irin ɗokin da ya nuna da zuwan wannan ranar...."
Hawayena na share ina mai yin wani irin murmushi na dafa kansu sannan na ce.
"Haka Allah ya nufa, cewa Daddynku ba zai ga wannan ranar ba. Alhamdulillah! Ina farin ciki, domin na cika masa wannan burin nasa, an ɗaura muku auren a ranar da kuka cika shekaru ashirin da biyar a duniyar. Ina muku fatan alheri da fatan zaman lafiya da farin ciki na har abada. Siyama...Amal..dukkan ku 'ƴa'ƴa na ne kuma jinina. Allah ya zaunar da ku lafiya ya baku zuriya ɗayyaba. "
Nan ɗakin ya ɗauka da Amin sannan aka fita da su zuwa gidanje su wanda muke fata su rayu rayuwa ta har abada.
Ina tsaye jikin windown bedroom ɗinsa ina kallon waje, zuciyata cike da marari da kewa na ji an turo ƙofar an shigo. Waigowa na yi sai naga Aryaan ne da Arhaam. Saurin share hawayena na yi ina mai ƙirƙirar wani murmushin na kalle su da alamun nuna mamaki na ce.
"Lafiya kuka dawo?"
A hankali suka tako a tare kowa ya ɗaura kansa a gefen kafaɗata suna faɗin.
"We love you Mammi....thank you for being a good mother to us. Kin tarbiyyantar damu da ke da Daddy, kun bamu farin cikin rayuwa, kun tsaya mana akan cika duk wasu mafarkai na mu, wanda a yau sun juye sun zama gaskiya. Muna alfahari dake, Allah ubangiji ya ji ƙan Daddy ya gafarta masa, ya ƙara jaddada rahamarsa a gare sa ya ƙara yalwata makwancinsa, Allah yasa ki gama da duniya lafiya yasa ki yi kyakkyawan ƙarshe."
Jinjina kaina na yi na ce.
" Amin ya Allah."
Daga nan na ɗago su tare da kama hannun su na koma jikin Window ina kallon waje na ce.