Ganin ido complete - Chapter 79
Ganin ido complete Chapter 79: Ganin ido complete Chapter 79. " Kun san ta ya muka fara da mahaifinku? We were met as a strangers, a hankali sai muka fara…
3,274 words
" Kun san ta ya muka fara da mahaifinku? We were met as a strangers, a hankali sai muka fara sabawa da juna, yakan mayar da damuwa ta ta zamto ta shi a kowane irin yanayi, yakan ɗauki farin cikina a matsayin na shi da dukkan al'amura na. Bai taɓa sa na ji cewa na yi taɓa nadamar auren sa ba, kamar yanda shi ma bai taɓa riskar nan wannan lokacin ba a rayuwarsa. Haƙiƙa mun so juna so na domin Allah ba don wani kyawu ko ƙyalƙyalin duniya ba. Mun so juna, mun kuma girmama juna, ya girmama Iyayena da en uwana kamar ya basu muhimmanci sosai kamar yanda ni ma na girmama na sa. Saboda haka, ina muku nasiha da ku ji tsoron Allah, ku daraja auren ku, ku yi rayuwar aure bisa gaskiya da adalci. Ku kula da wannan amanar, kun yi aure a cikin ƙurciya sosai, ina fata da addu'a da kuma roƙon ku akan cewa kada ku zamto masu hange-hange, rayuwar aure duk wanda ya gina ta fata yake ta ɗore har mutuwa. Kada ƙurciya ta ɗebeku ku riƙa tunanin aure-aure. Don Allah ku riƙe amanar en uwanku ku zauna da su tsakaninku da Allah. "
" In Sha Allahu Maami,mun ji duk abin da kika faɗa mana kuma zamu yi aiki da shi gwargwadon iko...."
Jinjina kaina na yi na ce.
"Allah yasa...Kuje, sai da safe. Allah ya bamu alheri."
*******
Wata ɗaya da auren na su aka shirya bukin ƙaddamar da su a matsayin sababbin shugaban nin Golden Pathways kamar yanda Emraan ya tsara, domin sun kawo girman da ya ga cancantar hakan, sannan daman mafarkin Daddynsu kenan da abun da ya tsara matuƙar abubuwa sun tafi daidai.
Bayan sun zamto jagorori muka shirya bayan watanni shi da muka tafi Sokoto wurin auren Kausar wacce zata auri wani matashin likita wanda ke zaune a nan cikin sokoto.
Koda muka isa an gama shirya komai har an shiga hidimar bukin. Muna ɗaki muna tattauna zancen kuɗaɗen da za'a sa yi kayan gara dasu na kalli Ammie na ce.
"Wai dai Ammie shi ke nan kika hanawa Armaan Kausar da gaske?"
Dariya tayi ta ce.
"Bana so ne ta yi nisa dani Beenafah. Sannan Abbun ku ma haka, shi ma ya nuna rashin amincewarsa ya ce ya fi so tana a kusa da shi."
"To Allah yasa albarka yasa ace gwamma da akayi."
"To amin."
Daga haka ta samu wuri ta zauna sannan ta nuna mini gefenta ta ce na zauna. Ina jin ta kira a tausashe na san cewa maganar dai ce kamar kullum.
"Beenafah, kamar yanda na saba faɗa miki, zaman ki a haka sam baya mini daɗi. Beenafah idan kina zaune ke ɗaya, damuwa da tunanina ba za su taɓa barin ki ki zauna lafiya ba. Beenafah aure shi ne cikon kamalar Mace. Ki yi haƙuri ki yi auren nan ko don yaran ki musamman Zarah. Beenafah kada ki manta, na auri Dr. Basheer ne don kawai saboda ke a lokacin. Ke ce dalili domin kawai na ga cewa na cika miki burin ki na son auren mutumin da kika zaɓa. To miyasa ke ma ba za ki jaraba hakan ki gani ba? Na san cewa zuciyarki mijinki kawai take tunani,to amma ki hasko goben yaran ki, har kin aurar da su Aryaan, amma su kan su sun same ni akan cewa suna so ki yi aure, domin zaman ki ke ɗaya yana ƙara miki damuwa..."
Hawayena na share ina kallonta na ce.
" Ammie ba zan iya auren Emraan ba...dalilai da yawa sun sa ba zan iya auren Emraan ba Ammie...and su ma sauran mutanen da suke nuna suna so na ba zan iya ba Ammie ba.."
Hannunta ta ɗora akan kafadata ta ce.
" Beenafah kina ji na? Jafaru yana nan, Jafaru ya kasa aure saboda rasa ki da ya yi, ba komai bane yasa ya aikata duk abin da ya aikata kawai tsabar son da yake miki ne. Ki tausaye shi Beenafah ki ba shi dama dan Allah ko zai samu farin ciki kafin mutuwar sa ta riske shi. Wani lokacin halin da zuciya ke shiga ne yake sa tana aikata ayyukan da ba su kamata ba, amma shi ɗin kin fi kowa sanin cewa mutumin kirki ne. Dan Allah Beenafah ki daure ki ba zuciyar ki magana. Beenafah yanda Jafaru ya ƙare babu wata uwa ko uba mai burin ganin ɗansa a wannan halin, ki daure ko don darajar iyayensa da zumuncin da ke tsakaninmu ki amince ki aure sa."
Jinjina kai na nayi ina mai jin wani irin nauyi a ƙirjina na ce.
" Shi kenan Ammie...idan har hakan shi zai sa ki yi farin ciki zan yi.."
Murmushine ya suɓuce mata jin amsar da ba ta yi tsammaninta ba daga bakina. Hakan yasa ta miƙe cike da farin ciki ta ce.
"Na gode Beenafah. Allah ya yi miki albarka ya ƙara miki kwanciyar hankali da farin ciki mai ɗorewa. In Sha Allahu ana gama ɗaura auren Kausar gobe sai mu tattauna ke ma sai ku tattauna da shi domin ku tsayar da abun da ya dace."
Daga haka ta fice ta barni nan ina mai kwanciya akan gadon na fashe da kuka.
*******
Barrister Jafar kuwa, tun auren su Aryaan bai ƙara yin ido biyu da Ashiru ba sai yau da ta kasance ranar ɗaura auren Kausar wanda suka jima suna tattaunawa.
Jiki sanyaye ya kalli Ashirun ya ce.
"Ko a lokacin auren 'ƴa' ƴanta...na kasa haɗa ido da ita. Ina jin kunyar ta na abin da na aikata mata a lokacin. Amma har yanzu ina son ta..."
Wani murmushin Alhaji Ashirun ya yi sannan ya kalle shi ya ce.
"You made a big mistake Barrister. Tabbas ka aikata kuskure. Wato kasan wani abu? Idan mace ta nuna so akan wani wanda ba kai ba, matuƙar dai kana sonta da gaske kuma kana son farin cikin ta, to lallai ka nuna kana son wanda take so ɗin nan fiye da yanda ma take son shi, sai Kaga an zauna lafiya. A lokacin da na ga hotunansu na a lokacin da aka haifi su Aryaan,...sai a lokacin na gane, na kuma tabbatar da cewa shi ne wanda ya kaɗe mahaifiyarta ya kuma yi tafiyarsa. Sun riga sun yi aure har sun haihu,babu amfanin kawo abin da ba shi da amfani a wannan lokacin. Ta yi kuka, ta yi baƙin ciki ta kuma ci alwashi akan duk wanda ya kaɗe mata Ammienta. Sai daga baya na gan shi ya zo asibitin yana tambaya wanda ita a daren tana can wurin likitan da yake duba Ammienta. Ban san taƙamammen abin da yake tambaya ba domin ɓoyewa ma na yi don kada ya ganni, duk da cewa a rikice yake, na san cewa akwai wani abun da ke damunsa na daban a wannan lokacin, ina nan ina kallon sa ba jimawa ya juya ya wuce. Na gane motar kuma na gane shi, amma tun da har ta aure shi babu buƙatar sanar mata domin haɗa husuma tsakanin miji da mata abu ne wanda Allah da manzonsa ba sa so kuma suka yi hani da shi. To ni na faɗa maka wannan ne domin in baka misali in kuma nuna maka cewa ka aikata kuskure na bibiyarta da kuma furta kalmomin cin zarafi akan Mijinta..."
Jinjina kansa ya yi sannan ya ce.
" Ai komai ya wuce Alhaji Ashiru, domin ko ni yanzu idan na tuna wallahy kunyar kai na nake ji. Allah yasa dai ta amince min."
"To amin."
Daga nan suka wuce wurin ɗaurin auren wanda aka ɗaura ƙarfe biyu na rana.
Ana nan ana ta hidima, Ina tsaye a ɗaki ina magana da Abdallah da ke shaidamin cewa gobe zai koma school na ji wayata ta yi ƙara, ina dubawa naga cewa Ammie ce ke kirana.
Ina ɗagawa ta ce na zo Parlourn Abbu na sama ina da baƙo Jafaru yana jirana a can.
Wani irin yawu ne ya wuce mini da ƙyar sannan na kalli Abdallahn na ce.
"Sai ka shirya ba damuwa, shi ma Aliyu zai bi su Arhaam su koma gida domin exams ɗinsa wannan satin ne, duk da na san cewa ya sanar maka.."
"Eh Maami, ya faɗamin ɗazu da safe."
"To kana da buƙatar kuɗi?"
Girgiza kansa ya yi yana mai mayarda kallon sa akan wayarsa ya ce.
"Nop! Ina da kuɗina, ko last week Daddy Emraan ya tura mini da 500k. And Ya Arhaam ma ya ce idan na sauka zai tura mini wasu."
"Ok to, ka je ka ci abinci dan Allah kafin na zo. Zan je naga wani baƙo a Parlourn Abbu, ka nemo Zarah ka ce ta jirani ina zuwa yanzu, tun ɗazu nake kiranta a waya ba ta ɗagawa."
Yana fita na ɗauko mayafina na lulluɓa na shiga ratsa mutane har na yi nasarar shige wa cikin Parlourn.
Zaune na cim masa ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana sanye cikin shiga ta manyan Kaya na alfarma.
Yanzu tsawon shekaru Ashirin da biyar kenan rabo na da nayi ido biyu da shi. Sosai ya canja a idona amma sam ban ji komai da ganinsa ba. Gyara zamansa ya yi yana mai yi mini murmushi ya ce.
"Hajiya Beenafah! Barka da wannan lokacin?"
Wani kallon na yi masa ina mai jin wani iri a raina na ce.
"Tsawon shekaru ashirin da biyar kenan..amma ko kaɗan ban ji tsana da ƙiyayyar da nake maka sun ragu a zuciyata ba. Komai da nake tunawa ina ganin ka yanzu sai yake min kamar yanzu ne yake faruwa. Kalaman ɓatancin da ka yi akan mijina sun kasa barin zuciyata. Tsananin fushi da ƙiyayyarka ne na gani kwance akan fuskarsa a ranar da ya kama ka a ƙofar gidansa. Jafaru har abada ba zan iya auren ka ba, saboda dalilai da dama..."
"Beenafah na kwashe tsayin shekarun rayuwa ta ba tare da na kula wata macen ba duk don saboda son ki da nake yi..."
"Kai ne ka ɗorawa kan ka, domin Allah bai ɗora maka ba. Wato kasan wani abu....rashin tawakallinka duk shi ne ya kai ka ga wannan Jafaru. Da ace ka yi haƙuri ka karɓi zaɓin Allah da ya rubuta cewa ni ɗin ba rabonka ba ce, da yanzu kana nan kana farin ciki kamar kowa. Amma dagewa da ka yi kace kai lallai sai ka yi fito na fito da ƙaddarar da Allah ya zaɓa maka, shi ne yasa ka ƙare a haka. Mijina ya nuna rashin jin daɗinsa akan bibiyata da ka dinga yi kana faɗin munanan kalamai akan sa, idan har a GANIN IDOn sa na juya maka baya da gaske, to mi zai sa bayan ƙasa ta rufe masa ido na dawo yin alaƙa da kai? Hakan ya nuna cewa na ci amanar sa kenan. Abun da ban yi a GANIN IDON sa ba, har abada ba zan aikata shi bayan shi ba. Ina son mijina sosai, nayi masa so da ƙaunar da ban yi wa wani ɗa namiji ba, kuma har abada ba zan yi ba. Mu ɗin a yanzu ba yara ba ne Jafaru...mun san abin da ya dace da wanda bai da ce ba..."
Wani irin abu ne ya ji mai matuƙar ciwo da raɗaɗin sai da yasa ya miƙe tsaye a zafafe, cikin tsananin kishi ya ce.
" Wai har yanzu ma da ya ji ma da mutuwa ba za ki daina wannan ba Beenafah? Ni fa ban aikata miki wani kuskure ba, kawai ni masoyin ki ne na Haƙiƙa. Ni ban taɓa cutar da ke ko mahaifiyar ki ba, amma shi wanda kike yiwa iƙirarin so idan ba ki sani ba, to shi ne nan wanda ya kaɗe miki mahaifiyarki da Mota har kika kusa rasa ta. Shi ne ya buge ta ya tafi ya barta..."
Wani irin tsalle zuciyata ta yi tsabar baƙin ciki wanda har ban san lokacin da na wanke masa fuska da mari ba ina mai jin yanda wata irin sabuwar tsanarsa ta shiga bijiro min ta kowane sassa na zuciyata.
Baki na na rawa na ce.
" Wai kai dan Allah wane irin mutum ne? To sai me? Sai me na ce don shi ne ya kaɗeta? Wannan mummunar maganar da ka faɗa mini a yanzu kana tunanin shi zai sa na ji tsanar sa ko me? To koma haka ɗin ne na yafe masa duniya da lahira, kuma Ammie ma ai ɗanta ne, kuma na san tabbas za ta yafe masa ita ma, na gode maka sosai da ka sanar da ni wannan, ko banza Kaga wannan nauyin idan har da gaske kake, to ya sauka daga kansa daga yau...Mamaki nake! Har da cewa ya mutu amma ba ka daina jin haushin sa ba. Kada ka bari 'ƴa' ƴansa su ji ka, domin ba za ku ƙarƙare da daɗi ba. Wallahy na tsane ka, tsana ta har abadan abada. Ko maza sun ƙare a duniya...ni ɗin ba zan taɓa auren mutum irin ka ba. Duk da cewa kayi shekaru...amma har yanzu har abada ƙwaƙwalwarka ba ta aiki yanda ya kamata. Ka tafi , kada ka sake dawowa inda nake na roƙe ka..."
Fitowa na yi na barosa a ɗakin, domin wallahy idan na ci gaba da ganinsa tabbas zuciyata bugawa za ta yi na mutu. Na tsane sa ta yanda ban san ma ya zan misalta shi ba.
Sosai na yi ƙoƙarin ɓoye damuwata, domin bana so na wargaza farin cikin mutanen da suka taru domin mu. Hakan yasa na yi tamkar wani abu bai faru ba. Na koma muka ci gaba da hidimarmu.
Da dare bayan an fito da Kausar an sanya ta a motar Alhaji Hashi ne Na ji Bahrain ya riƙo hannuna yana faɗin.
"Aunty Beena please zo ki ji minti biyu dan Allah.."
Kallonsa na yi sai kuma na ce.
"Bahrain koma miye ka bari na kai Kausar na dawo..."
"Noo...Aunty Beena please, it's urgent. Just two minute as I said."
Tun da muka tako bamu tsaya ko'ina ba sai bakin ƙofar Parlourn waje yana mai kallona cike da magiya ya ce.
"Kin ƙi ki saurari kowa Aunty Beena ta...dan Allah ki daure ki saurari wannan ɗin...nobody will force you, but Idan hakan ta faru, zamu yi farin ciki."
Wani irin dokawa ƙirjina ya yi wanda ban san lokacin da na waro ido ina Kallonsa ba na ce.
"Bahrain miye yake faruwa?"
Cikin sigar magiya ya ce.
"Idan kika shiga za ki ga ko miye, Aunty Beena dan Allah ki shiga."
Tura ƙofar na yi a hankali ina mai jera addu'ar neman tsari daga Allah domin ban san waye Bahrain ke ta yi wa wannan magiyar haka ba.
Tsaye yake yana facing window ta waje wanda ko da bai juyo ba nasan kowane ne. Jikina ne ya ɗauki ɓari yayin da na ji zuciyata ta yi wani irin nauyi. Shekaru Ashirin da Shida kenan, rana ta ƙarshe a tsakaninmu ita ce ranar da kunnuwana suka yanke daga jin muryarsa bayan Emraan ya yi nasarar fasa min wayata. A wannan satin ne na yi masa ganin ƙarshe, ganin da ban ƙara sanya shi a ido na ba sai yau. Ko lokacin da Daddyn Abdallah ya rasu cewa ya yi Ammie ta isar mini da gaisuwarsa, auren Su Arhaam da ya zo ni har aka kambala ban gansa a idona ba. Taron gamayyar kamfanoninmu da muke ma, duk da cewa yana cikin manyan ma'aikatanmu bai taɓa halarta ba, matuƙar dai da ni a ciki. Sai dai ya kawo wasu Uzuroran ya shimfiɗa.
Waigowa ya yi a hankali yana mai kallon fuskata zuciyarsa cike da taraddadi wanda ya rasa ma a wanne yanayi yake ciki.
Sautin muryarsa na ji a hankali ta fara sauka a cikin kunnuwana da cewa.
"Beenafah... Dan Allah ki zauna ki saurareni, ba zan taɓa takura miki ba, ba zan ɗaga murya ba, dan Allah ki zauna, ki zauna ki bani mintuna kin ji."
Wuri na samu na zauna ina mai jin yanda hawaye suka cicciko idona wanda ban san dalilin hakan ba.
"Ahm! Da fatan kina lafiya...ya kike ya iyali ya kuma ƙarin haƙuri? Allah ya gafarta masa ya ƙara jaddada rahamarsa a gare shi."
"Amin yah Allah, na gode sosai."
"Wato wata er magana ce ke tafe dani, ina fata ban takura ki ba Beenafah?"
Jinjina kaina na yi camly na ce.
"Ba komai, you can go ahead.."
"Beenafah kin tuna lokacin da muka rabu na ƙarshe a rayuwa? Tabbas a wannan lokacin ban san miye abinda ya yanke maganar da muke yi a waya ba a wannan ranar. But bayan abubuwa sun kasance haka, sai na ɗauka cewa yana daga cikin ƙaddarata. Na so ki tun a wancan lokacin, so mai tsanani wanda yasa na gigice na ɗimauce Beenafah. Kalmomin da na tsara domin faɗa miki a wannan ranar ban yi nasara ba Beenafah. Domin na riga na makaro, sai dai kuma suna kwance a cikin ƙirjina tsawon shekarun nan, ni na yarda da cewa so ɗaya ne,kuma daga lokacin da kika so wani bayan ni sai na hak'ura na kuma ɓoye shi can ƙasan zuciyata domin babu wata macen da ta cancanci kalmomina Beenafah tun a ranar da aka shaidamin zancen auren ki. Na rayu da matata domin bin umarnin Iyayena, amma so ɗaya na ke yi...domin ki na ke yinsa kuma daga lokacin da kika yi aure, a lokacin soyayya ta mutu daga zuciyata. Bana so in yi kuskuren bayar da kalamaina ga macen da ba ita zuciyata take so ba."
Miƙewa ya yi ya dawo kusa dani kaɗan yana mai ƙara kwantar da muryarsa ƙasa sosai yace.
" Beenafah! Ban zo wurin ki don neman soyayya ba a yanxu, na zo ne saboda na san ina son ki, kuma zan furta kalmomin a gare ki wanda shi ne karo na farko bayan na rasa ki a baya, INA SON KI BEENAFAH. Wannam ita ce kalmar da na so furta miki a wannan ranar. Ba lallai sai kin amsani ba, domin nasan cewa tabbas na makara. wanda ya yi nasarar auren ki, shi ne ya cancance su saboda ya kasance jajirtaccen miji na gari kuma uba na gari. Ina so don Allah ki amince ki aureni ko da ba ki jin komai a ranki na So gare ni. Ni ban damu da hakan ba, idan ka rasa masoyi... Abin yana da matuƙar wahala da zafi a zuciya. Mai yiyu wa ka ƙara jin wani son mai yi yu wa kuma ba za ka ƙara ji ba har abada. Ni ba zan taɓa yunƙurin goge tarihin mijin ki a zuciyar ki ba, domin hakan nasan ba abu ne mai yiyu wa ba. Ban zo domin maye gurbin sa ba, na zo ne don in taimaka miki wajen ɗaukar nauyin da ki ka shafe shekaru da dama kina ɗauke da shi ke kaɗai...Beenafah ki ba ni dama, ki ba ni damar da zan tsaya a gefenki domin na zamto inuwa a lokacin rana, mafaka a lokacin ruwan sama sannan kuma san yi a lokacin zafi,sannan na kasance kujera kuma mahutar ki a lokacin gajiya...na rasa damar faɗa miki waɗan nan kalaman na tsawon shekaru ashirin da shida da suka wuce...amma a yau..Allah ya ba ni wannan damar, ki amince dani kin ji. Ba lallai sai a yau ba, ba lallai sai gobe ba. Zan jira na tsawon gobe, jibi, gata har zuwa lokacin da kika ji cewa za ki iya."
Kuka na ke ina mai jin yanda kalamansa ke ratsani. Daman da gaske abun da ya yi niyyar sanar dani kenan a ranar Emraan ya karɓe wayata ya fashe ta a ƙasa? Shiyasa ya yanke wa kansa hukuncin ƙin raɓar duk inda nake?
Lumshe idanuna na yi a hankali sannan na buɗe ina mai jin wasu sabbin hawayen a zuciyata ina faɗin.