Ganin ido complete - Chapter 80
Ganin ido complete Chapter 80: Ganin ido complete Chapter 80. Haƙiƙa ba ka yi Ƙarya ba Yaya Ashiru da kace ka Makara. Tabbas ka makara ɗin na tsawon…
2,572 words
Haƙiƙa ba ka yi Ƙarya ba Yaya Ashiru da kace ka Makara. Tabbas ka makara ɗin na tsawon shekaru ashirin da shida, ka riga ka mara domin Dayaa ne kaɗai wanda yake zuciyata. Ya bani farin ciki da duk wani gatan da mace take buƙata a wurin mijinta. to amma nauyin da ka ajiye a ƙirjinka tare da haƙuri da ka nuna. A yanda ka girmama ni ka girmama Mijina, ka kuma jure tsawon shekarun nan ko bana jin son ka ba zan ƙi amincewa auren ka ba. Ko don na saka Ammie na farin ciki zan amince da kai. Ko don 'ƴa' ƴana da suka ga cancantar ya kamata ace na yi aure zan amince maka. Ko don Bahrain da ya cire nauyin da yake ji nawa ya yi mini maganar ka ba zan ƙi amincewa ba. Kalmomin Ammie ne a raina, wanda ta taɓa faɗamin cewa, ta aure Dr. Basheer ne ba don soyayya ba, sai don cike wani gurbi da ta rasa.
"Beenafah! Idan har na faɗa miki wata kalma wacce ba ta yi miki daɗi ba, dan Allah ki yi hak'uri. Ban ji daɗi ba Sam yanda ki ke ta wannan kukan haka. Da ace na san za ki zubar da hawaye haka, da tabbas ban aikata ba....Hawayenki na ƙona ni, dan Allah ki yi hak'uri."
Girgixa kaina na yi ina mai share hawayena na ce.
" Ba ka yi kuskure ba Yaya Ashiru...da in auri wani wanda bai cancance ni ba, gwanda na aure ka ɗin domin kai ne wanda yasan zafina bayan mijina. Ba kuɗi ko wani matsayi nake nema ba. Ina so na auri wanda zai kula dani da taimakamin wurin kulawa da yarana ba tare da jin na takura masa ba nima kuma ba tare da na takura ba. Wanda zamu girmama juna mu mututunta juna ba don wani abu da ɗaya yake da shi ba...."
"I promise you Beenafah… ba zan taɓa cutar da ke ba. Ba zan taɓa ɗora miki nauyin da ya wuce ƙarfin ki ba. Kuma ba zan taɓa neman ki goge tarihin wanda kika aura kafin ni ba. In sha Allahu zan kasance a yanda kike so na, zan kula da yaranmu da dai gwargwadon iya wa ta. Ba zan taɓa barin ki ki yi kuka ba, ba zan taɓa bari ki cutu ba."
Miƙewa na yi ina Kallonsa a hankali na ce.
" I will go now...domin ana jirana. In Sha Allahu zamu tattauna da Ammie da su Bahrain. "
Cikin farin ciki ya jinjina kansa yana murmushi ya ce.
" Take your time. Allah ya sanya alheri da albarka ya basu zaman lafiya."
"Amin. Thank you."
Ina fitowa na zuba ido ina kallon yanda kowa yayi cirko-cirko ana jirana,domin Kausar ta ce ba za'a ɗaga da ita ko'ina ba sai idan na zo. Hakan yasa na yi ƙoƙarin daidaita kaina na shige motar muka tafi muka rakata ɗakin ta wanda ya sha kaya na alfarma,sai dai mu yi addu'ar Allah ya bada zaman lafiya da zuriya ɗayyaba.
Bayan mun dawo, a daren Ammie ta same ni a ɗakina ta ce.
"Beenafah! Miye kike yanke akan Jafaru?"
Kallonta na yi, sai kuma na Girgixa kaina na ce.
"Ammie ba zan iya auren Barrister Jafaru ba. Amma na yanke zan auri Alhaji Ashiru Ammie..."
Cikin wani irin farin ciki ta zo ta zauna a kusa dani tana murmushi ta ce.
"Kai Alhamdulillah! Gaskiya na ji daɗin wannan shawarar da kika yanke. Tabbas babu wanda ya fi dacewa dake idan ba Ashiru ba..."
"To amma miyasa a farko kika ce Jafaru ne yafi dacewa Ammie?"
"Saboda ya dawo ya nuna mini da shi da iyayensa yana so ya aure ki, and Ashiru shi bai ce yana son ya aure ki ba a yanxu...kin ce kuma bakya son Emraan da duk wani wanda ya zo domin ki. Hakan yasa na ga cancancarta sa, amma idan har Ashiru ya zo da zancen auren ki, to tabbas hankalina zai fi kwanciya da shi. Sai dai shi Jafaru ina masa addu'a Allah ya bashi wata wacce zai aura ko don farin cikin iyayensa. "
" Ba zan iya auren Jafaru ba Ammie..ina fata da addu'ar iyayensa da shi kansa su yafe mini. "
" In Sha Allahu zan yi magana da su kada ki damu. Yaushe kike ganin auren ya kamata?"
" Daga zaran na tattauna da su Aryaan..In Sha Allahu sai ku yanke lokacin da kuka ga cewa ya yi muku, sai a yi. "
Cikin farin ciki ta ce.
" Masha Allah. Allah na gode maka, Allah ya amintar dake yasa albarka a cikin wannan auren da za ki yi Beenafah."
"Amin Ammie."
Washegari da muka zauna muna tattauna maganar da su Aryaan na yi mamaki da suka ce wai an sun san da zancen domin Bahrain ya sanar da su labarin yanda Ashiru ya je neman aurena da kuma yanda na auri babansu. Hakan yasa suka ga dacewarmu tunda na ƙi ƙanin Mahaifin su cewa da Emraan.
Bayan Ammie ta gama jin ra'ayoyin kowa ta tattauna da Abbu da kuma su Annie da Raihab aka saka auren wata biyu mai zuwa.
Ashiru ya yi matuƙar mamaki da farin ciki domin bai kawo komai a nan kusa ba. Sam bai ɗauka cewar abin zai faru da sauri haka ba. Ya ɓoye so da ƙaunar da yake mata tsawon shekaru, ya Karɓi Sabila domin itace xaɓin iyayensa bayan ya rasa Beenafah, ya ɗauki soyayyarta ya binne a zuciyarsa ya rufe domin ya cire rai da sake samunta har abada. So ɗaya ne kuma ya gama so akan ta. Ko a yanzu...ya yi buri da saka ran cewa zai iya samunta bayan Mijinta ya rasu. To amma a yanda yake jin cewa ta ce ba za ta ƙara aure ba a wurin Bahrain. Sai ya cire rai sai kuma gashi Bahrain ya same sa akan cewa shi ka ɗai ne wanda yafi dacewa da yayarsa, saboda haka ina ba shi shawara akan ya je gareta. Hakan yasa lokaci ɗaya So da ƙaunar da yake ji suka motso masa zuciya, take duk wani sirrin da ya binne ya shiga fitowa a hankali yana sarƙafe masa zuciya. Sai ga shi cikin ikon Allah ya yi nasara. Da ya shaidawa Su Umma Ayya har da kuka tayi na al'ajabin wannan so da yake yi wa Beenafah. Nan suka yi masa addu'a da fatan alheri na cewa ko yanxu ɗin Allah yasa ita ɗin rabon sa ce.
Bayan na koma gida tare da yara na shirya kamar yanda muka tsara muka tattaro ni da Zarah da Aliyu muka dawo, wanda su Aryaan suka yanke cewa idan lokaci yayi ana saura kwana biyu za su zo.
Ana gobe ɗaura auren ya zo yasa aka kira ni.
Yanda yake ta farin ciki ni abin har mamaki yake bani, domin ni Sam bana jin wani ɗoki ko marmarin abun a raina. Amma shi sai murna yake yana bayyanar da farin cikin sa a fili.
Kallonsa na yi sai kuma na ɗan murmusa na ce.
"Na zo sai kallona kake ka ƙi ka ce komai Yaya Ashiru..."
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"Maman Zarah har yanxu sai nike jin komai yana mini tamkar a mafarki."
"Allah ke nan! Shi ne mai yin yanda ya so a lokacin da ya so."
Ɗan ƙara gyara zaman sa ya yi yana mai ci gaba da kallona ya ce.
"Haka ne. To, daman dalilin kiran na ki shi ne, ina so mu tattauna wata magana ce mai muhimmanci ne Maman Zarah."
Kallonsa nake a hankali ina mai bashi dukkan nutsuwata na ce.
"Allah yasa lafiya.."
"Lafiya lau In sha Allah Uwar Abdullahi...daman alfarma nake ne ma. Na san cewa kinfi ƙarfin komai da nake da shi. Kuɗi, gida, jin daɗi da more rayuwa...duk kin yi mini rata nesa ba kusa ba. Da wannan nake neman alfarmarki, dan Allah ki daure ki zauna a gidan da na sama miki a Abuja, na san dai rayuwar nan ɗin da can ba ɗaya bane... "
Girgixa kaina na yi ina mai jin tausayinsa a raina na ce masa.
" Ai rayuwa ba za ta taɓa tabbata ba har abada, a duk lokacin da muka samu canjin ƙaddara, to dole abubuwan rayuwarmu su sauya Yaya Ashiru. Kai ne wanda zai aure ni a yanzu, kai ne kake da haƙƙin nema mini wurin zama, abinci da kuma sutura, nauyin ka ne kuma ba zan hana ka wannan ba. Zamu bika a duk inda kake da ni da 'ƴa'ƴana kuma zamu zauna da kai lafiya tare da iyalanka In Sha Allahu..."
Cikin wani jin wani irin sabon farin cikin ya ce.
" Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Na gode Beenafah, Allah ya saka miki da alheri. Allah ya bani ikon sauke nauyin da Allah ya ɗora mini...magana ta gaba kuma, a gaskiya ba gida ɗaya na tsara za ku zauna da Sabila, gidanta daban naki daban In Sha Allahu."
Jinjina kaina na yi ina mai jin wani sanyi a raina na ce.
" Na gode sosai Allah ya saka da alheri. Ni zan shiga ciki,sai goben idan Allah ya nuna mana."
"Allah ya bamu alheri Hajiya Beenafah, na gode sosai, ki gaishe da yaran."
Washegari kamar wasan 'ƴan yara aka shigo ana shaidamin cewa an ɗaura aurena a karo na biyu da Yaya Ashiru.
Su Aunty Labiba, duk da cewa ban zaɓi ɗan uwansu ba. Sun yi matuƙar farin ciki da yi mini fatan alheri. Wanda har Emraan ɗin sai da ya kirani a waya domin bai zo ba. Amma dai su Hairi duk sun zo tare da Aunty Ziza.
Haka kowa ya shiga fatan alheri a gareni wai har da su da Arhaam a faɗin Congratulations Maami. Allah yasa albarka ya bada zaman lafiya. Su kaɗai ne suke farin ciki amma Aliyu sam baya murna, da bakin sa ya faɗa min cewa shi baya son na auri wani, kawai na zauna abina a haka, Zarah kuwa sai murna take tana faɗin ai ko Daddy ba zai so zaman Maami a haka ba.
Sai da aka cika kwana biyu da ɗaura auren sannan muka hau jirgi zuwa Abuja. Kuka nake har muka shiga cikin gidan wanda ni kaɗai na san irin abun da yake damuna. Wai ni Beenafah ni ce yau na aka rako gidan wani wanda ba Dayaa ɗina ba. Rayuwa matuƙar kana numfashi to har abada baka rabuwa da jarrabawa, domin a hakan ni sai in godewa Allah. Saboda wata sai tayi aure uku huɗu a rayuwarta wata ma fiye da haka.
Ashiru kam duk ya ruɗe sai rawar ƙafa yake kamar shi ne auren sa na farko, bayan yana da matarsa har da yara huɗu wanda har ya aurar da ɗaya daga cikin su ta farkon mai 23yrs.
Gida ne babban gida wanda ni sam ban tsammata ba, akan ganin girman shi da tsaruwarshi ne sai dai shi flat Mansion ne amma yana da yawan ɗakuna masu tsari mai kyau. Kayan da ma aka saka sun yi daidai da gidan wanda Bahrain ne da Ammie suka siya komai da komai daga waje.
****** Finale....
A hankali na fara sabawa yayin da rayuwa ta sauya mini a gidan Alhaji Ashiru,wanda ya ƙauna ce ni ya kuma nuna mini irin son da yake mini wanda ya yi ta dakonsa a zuciyar sa na tsawon shekaru.
Hakan yasa na samu nutsuwa daga ni har yara na wanda suke zaune a Dubai ɗin gidan Daddysu Emraan, idan kuma sun samu hutu sai su dawo gida inda nake. Suma su Aryaan suna yawan zuwa dubani tare da matansu waɗanda ke da yara ɗaɗɗaya a yanxu.
Abdallahna bawan Allah shi ma yana Madina wanda sai idan ya samu hutu ko wani sarari yake zuwa ya ganni har ya samu kambala Alhamdulillah wanda muka shirya muka je har Madinar aka yi taron ƙarewarsa, sannan su Arhaam suka shirya masa buki na musamman a Dubai ɗin muka je! Yanzu ya dawo inda nake kuma a nan Abujar yake neman auren wata yarinya wacce suka yi karatu a tare.
Sannan Aunty Aysha tana tare dani ga Baba Ustaz wanda ya tsufa sosai domin a yanzu yana gida ma ko'ina baya fita.
Idan na zauna wani lokacin ina tunani, sai in yi ta lissafin yanda muka faro da irin yanda rayuwa ta shiga sauyawa da irin jarabawowin da muka yi ta tsallakewa. Wani abun na kan yi murmushi, wani ya saka ni dariya, wani kuma ya sakani Kuka.
Yau ma koda muka wayi gari da labarin mutuwar Umma muka farka wadda tayi matuƙar girgixa Baban Muhammad.
Tunda ya fita masallacin asuba ma bai dawo ba. Gani ni har na kambala shiryawa Little Muhammad ma haka. Shigowar Abdallah na ji yana faɗin. "Maami kin gama shiryawar?." Kallon sa na yi da alamar tambaya na ce. "Na gama. To amma in Abban na ku yake?" "Bai dawo daga masallaci ba?" "A'a, bai dawo ba...ina ka baro shi kai?" Sallamarsa muka ji yana faɗin. "Ina ciki Maman Zarah, koda na shigo kina cikin toilet..." Jinjina kaina na yi na ce. "Ga abincin karyawa an gama haɗawa..." Girgixa kansa ya yi ya ce. "A'a, na gode. Amma ba zan iya cin abincin ba, idan kun gama shiryawa ku fito mu tafi." Sosai nake tausaya masa, domin na riga na ɗanɗana zafin mutuwa na san ciwon ta. Mahaifiyarka ta rasu ai kam dole akwai raɗaɗi. Da haka muka kambala muka fito muka kama hanya sai Gusau. Bayan an gama makoki na shirya tare da Abdallah muka je muka duba Mummy da Yaya Hafiz sannan muka je gidan su Maman Fakiha. Yanda take bani labarin Jafaru akwai matuƙar tausayi a ciki, amma ni sam ban ɗauke shi komai ba. Domin shi ne wanda ya ɗaurawa kan sa. Da yace ya zaɓi ya mutu bai yi aure ba, wannan kuma damuwar sa matuƙar dai zai kiyaye kansa da dokokin Allah. Sai da muka biya gidan Fakiha sannan muka zarce gidan Aunty Labiba wacce ta cike da farin cikin ganinmu. Bayan mun kambala zumuncinmu muka shirya muka dawo gida. Inda muka tarar Zarah da Aliyu sun zo wai a matsayin surprise wanda naji daɗin zuwan na su sosai. Daman haka suke mini, sai ina zaune kwatsam sai na gansu sun zo dubani wai sun yi kewata. Komai na rayuwa sai in ce Alhamdulillah! Domin ko a yanda en uwana da yara na suke ƙaunata da damuwa da dukkan al'amura na sai dai in ce Alhamdulillah! Gina Masallatai, rijiyoyi, ɗaukar nauyin marayu da tallafawa bayin Allah shi ne aikina a yanzu wanda kullum bana gajiya da yi wa mahaifina da kuma Dayaa na hidima domin Allah ya kai ladar ƙabarinsu ya kuma gafarta musu. Addu'a ta har abada ba za ta taɓa yankewa ba zuwa gare su In Sha Allahu sai idan mutuwa ce ta riskeni. Haka ma 'ƴan' ƴansa kullum ina musu nasiha da su dinga yi masa addu'a a koda yaushe suna tunawa da shi.
Tammat Bi Hamdulillah!!! A nan na kawo ƙarshen wannan Novel ɗin nawa wanda ya kasance ƙirƙirarre. Ina addu'ar Allah yasa albarka ga darasin da ke ciki. Kuskuren da na rubuta ba daidai ba kuma ALLAH ka yafe mini amin. Na gode sosai masoyana da jimirin bibiyar wannan littafin. Allah yasa mu amfana da darasin da yake ciki. Ganin Ido comment group. Taskar gurinjo novels. Wattpadians Arewapen Da sauran mabiya wannan littafin ina godiya sosai, Allah ya saka da alheri ya bar zumunci. Sai mun haɗu a littafi na gaba In Sha Allah. Ku kasance dani a koda yaushe. #Aminaibrahim #OumAmeer #08068974831 #9,December2025