Kenza eBookz

Ganin ido complete Novel - Chapter 10

Ganin ido complete Novel - Chapter 10

Ganin ido complete Novel Chapter 10: Ganin ido complete Novel Chapter 10. Tana haɗa ido da su ta wani fashe da kuka da gudu taje ta rungume su. Su ma kukan…

3,368 words

Tana haɗa ido da su ta wani fashe da kuka da gudu taje ta rungume su. Su ma kukan suke kamar yanda ta ke yi tamkar za ta ɗauke numfashi bama kamar Husaina.

Hannu Humaida ta miƙa ta janyo Baffa tana faɗin.

"Come here my boy...Tun kana baby gashi ka dawo babba"

Mota Hassana ta nufa tana faɗin.

"Please every body should hold his tears please.....ku jira idan muka koma gidan sai ku ci gaba."

Motar suka nufa ba tare da kowa ya tanka mata ba suka shige sai gida.

Suna shiga gidan jiki na rawa ta faɗa jikin Mummy Zaliha ta fashe da wani irin kuka tana faɗin.

" Ki yafe mini Mummy...Dan Allah ki yafe mini, I promise you ba zan ƙara yin abin da bakya so ba..."

Taɓe baki tayi still Ayshar na rungume a jikinta ta ce.

"Ah to! Mutum dai ya ga abin da zan iya, ni ba kamar sauran iyaye ba ce, yaro bai isa yace zai takani ba, Ƙaryar sa wallahi, don har yanzu ban haifi wannan ɗan ba, saboda haka sai ki kiyaye na gaba."

"In sha Allah Mummy zan kiyaye."

Zaunawa suka yi a tare sannan ta janyo Baffa a jikinta ta rungume shi tana mi shi murmushi tana faɗin.

"A'ah! Ga mu yau ga mutanen London... Ina Abbanka?"

Cikin jin wani sanyin farin ciki Ayshar ta karɓe zancen da cewa.

"Abban shi ya wuce Sokoto Mummy, sai dai idan ya dawo."

"To Allah ya kai shi lafiya. Shi ma ai Hafiz ya kirani ɗazu ya ce mini in sha Allah satin nan mai zuwa zai dawo ya ganki..."

"Allah sarki! Allah ya dawo da shi lafiya."

"Amin. Ina Salma?"

"Salma tana can na ce Ahlan ya wuce da ita kafin mu zo, ta girma sosai, ina tsoro kada iyayenta su ce za su riƙeta su yi mata aure."

Miƙewa Mummy ta yi tana faɗin.

"To idan sun riƙe ta ba sai ki samo wata ba. Gari da yawa ai maye ba zai ci kansa ba. Ni ɗaukar mai aiki da kuma korarta a wurina tamkar saka riga da cirewa ne...Ku tashi muje mu ci abinci, nasan matafiya na jin yunwa."

Haka suka zauna suna ta cin abinci, faɗar irin farin cikin da Aysha ke ciki ma ɓata baki ne. Duk inda Mummy ta saka ƙafa tana tare da ita a wannan ranar hatta bacci ɗakin Mummy ta yi shi tare da ita, komai ya dawo mata sabo.

****

Haka muka ci gaba da rayuwa komai na tafiyar mana a hankali dai-dai da matsayinmu, wanda shi ne silar farin cikinmu da walwalarmu.

Yau azumi ya rage saura kwana biyu. Ina kan mopping Aunty Hajjo ta shigo ta miƙo mini leda tana faɗin.

"Ga Kayan Azumina nan da aka kawo mini tare da an gani ana so."

"Kayan Azumi da an gani ana so? Miye hakan yake nufi to Aunty Hajjo?"

Kallon sama da ƙasa ta yi mini kamar dai wa can lokacin sannan ta ce.

"Wai ni kam, shekarunki nawa ne Beenafah?"

Kai tsaye na ce.

"Sha shida nake da kamar."

"To yanzu don Allah so kike ki ce mini baki taɓa gani ko jin kayan see I love ba? Da kayan azumi?"

Bakin gaskiyata na ce.

"Da gaske nake Aunty Hajjo."

Gyaɗa kanta tayi ta ce mini.

"To amma kin san aure ai?"

"Eh, munyi auren Aunty Aysha a lokacin."

"Ok to kamar haka, wanda yake so ya aureni ne ya kawo mini kayan azumi da kuma kayan tsaida shi a matsayin wanda zan aura, an yi mana engagement Kenan, daga haka har mu kai ga yin aure.."

"ohh! Na fahimta yanzu, Allah yasa alheri."

"Amin."

Aikina na je na ci gaba da yi. Bayan na kambala ina shirin zuwa gida sai Aunty Labiba ta dawo, daman yau koda na zo bata nan ta fita aiki.

Bayan mun yi mata sannu da zuwa ta kirani waje ni da Aunty Hajjo ta nuna mana kaya ta ce.

"Ga wannan, kowa ya ɗauka ya kai gida. Ke Beenafah ga naki can kema Hajjo ga wanda za ki ɗauka can..."

Godiya muka yi mata sosai sannan na fita har babban titi na samo mai Napep muka dawo gidan na ɗauka na kai gida cike da jindaɗi.

Da muka duba kayan ashe gero ne tiya goma, shinkafa tiya biyar,sugar tiya ɗaya, dabino tiya ɗaya sai kayan Tea wanda In Sha Allah idan muka lallaɓa zai ɗaukemu har ƙarshen azumi sannan da kuɗi dubu goma.

Cikin nuna zallar farin ciki Ammie ta ce.

"Wallahi Beenafah kar ki ji irin yanda zuciyata ta yi sanyi. Mun gode wa Allah mun gode wa wannan baiwar Allah, Allah ya saka mata da mafificin ya raya mata yaranta ya kuma ƙara mata zaman lafiya da Mijinta."

"Bari Ammie! wallahi ni ma daɗi ya hanani ma yin magana. Aunty Labiba mutum ce,Allah ya saka mata da alheri."

"Aunty Beena ni dai bana son Kunu...in dai kina so in yi azumi duka kamar yanda kika ce to ni ba zan sha Kunu ba."

Dariya muka yi ni da Ammie sannan ta ce.

"Kai dai da kunu kam Bahrain akwai tsatstsaurar gaba sosai.."

"ƙyale shi Ammie, samun wuri ne kawai, can da da bai ga kayan Tea ɗin ba ai dole yasha ko baya so..."

Ammie na dariya ta janyo shi jikinta tana faɗin.

"Haba Beenafah...Autan na wa kike wa haka? Ya fa kusa sauke alƙur'ani ga shi kuma zai ƙare primary ya je Js One... Ko don ƙoƙarin nan da ya nuna da ƙwazo ai kya masa abin da yake so ba tare da ƙorafi ba."

"Haka ne kuma Ammie, amma dai hakan ba shi ne zai sa yace ba zai ci abinda yake gaban sa ba."

Nan muka yi ta fira, muka ci abinci sannan Bahrain ya shirya ya wuce islamiyya.

Bayan na kambala sallar magrib, ina zaune da litattafan Bahrain ina dubawa Ammie ta zo ta tsaya a kaina tsawon lokaci ba tare da ta furta mini komai ba.

" Ammie kin yi shiru kina ta kallona..da wata maganar ne?"

Jinjina kai ta yi ta ce.

"Beenafah, kinga dai tsawon shekarun da muka kwashe ina ta fama da ciwo, a hankali aka yi ta magani, sai ciwo ya yi kamar ya tafi sai kuma ya dawo baya, komai ya lalace mana, duniya ta yi mana ƙunci da zafi, a hankali sai ga shi kuma Allah cikin ikon sa yasa na samu waraka wanda a yanzu in sha Allahu, ina fata da roƙon Ubangiji yasa ƙarshen wahalar da za ki yi dani kenan. To Alhamdulillah! Ga shi cikin ikon Allah abubuwa suna ta sauƙaƙa agaremu ba kamar can baya da muka baro ba a lokacin da kuma bamu tsamma ta ba. To ni shawarata a nan ita ce; Idan Ubangiji ya nuna mana bayan sallah lafiya, ya kamata ki koma islamiyya. Karatun boko ba dole ba ne kuma ba addini bane, abu ne mai kyau wanda yin sa yake da matuƙar amfani idan an samu dama da lokacin yin sa. Amma idan damar hakan bata samu ba, sai a haƙura. Tun da har na samu sauƙi haka, ya kamata ki haƙura da bokon tun da kinga yanda rayuwar ke tafiyar damu, sai ki koma islamiyya, idan kin tafi kin gamo aikinki kin dawo ƙarfe biyu, ki yi duk abin da zaki yi ki gama ƙarfe uku ki wuce wurin neman ilimi, domin shi ne gaba da komai kuma shi ne rayuwa ko ince shi ne abin da aka gina ɗan Adam domin shi."

Cike da jindaɗin maganar da tazo mini da ita na ce.

" In sha Allahu yanda kika ce haka za'a yi Ammie. Allah ya ƙara miki lafiya yasa mu dace."

"Amin."

"To amma kuma Ammie...barinki ke kaɗai wuni ɗaya zungur..."

"Haba! Kar ki damu da wannan, ke da ke barina tun ƙarfe tara ko sha ɗaya na safe kikai ƙarfe biyu ko ma fiye da haka, mi zai sa ki damu don kin fita neman ilmi. Yanzu ga Maman Fakiha a kusa dani, sannan kuma ga Jafaru da Hamza dake yawan shigowa akai-akai sun ɗaukeni Uwa suna kulawa dani, suna yawan shigowa muna fira da su ba ma kamar Jafaru. Saboda haka kar ki damu in sha Allah lafiya za ki riƙa dawowa kina tarar da ni babu abin da zai sameni."

" Shi kenan Ammie, Allah ya nuna mana."

" Amin Yah Allah. Ta shi ki jiƙa mana gero tun da yanzu kada a manta gobe a markaɗo shi da wuri a Tace shi."

****

Unguwar Gwaza, Gusau, Zamfara State. Nigeria.

Babban gida ne mai yalwa wanda ke ɗauke da doguwar verandar tare da jerin ɗakuna. A gefen yamma, manyan Bayika ne guda biyu yayin da gefen gabas ke ɗauke da babban madafar abincin gidan baki ɗaya. Ƙasa ce turɓaya ke malale a farfajiyar gidan wacce tayi fes sakamakon sharar da ta samu, ko'ina ya yi zanen tsintsiya ya yi kyau ga wata iskar da ke kaɗawa tare da babban Iccen Mangwaron da ke farfajiyar filin gidan.

Kwance yake ya kinshigiɗa da jikin bishiyar Mangwaron tare da lumshe idanunsa da alama bacci yake yi.

Umma ce ta zo ta tsaya a kan shi cike da mamaki a fuskarta ta ce.

"ASHIRU... Ashiru..kai Ashiru!"

Da sauri ya zabura yana mai share hawayen idanunsa ya kalle ta murya a sanyaye ya ce.

"Na'am Umma.."

Haɓa Umma ta riƙe tana ƙara girmama wannan al'amari na Ashiru ta ce.

"Au! Wai Kuka kake? Lallai Ashiru! Kai shikenan ba za ka haƙura ba kenan? Sai kace ba musulmi ba..."

Bokiti Ayya ta ajiye dai-dai inda suke tsaye suna maganar itama ta ce.

"Hmm! Ni wallahi tun da na yi tozali da su zuciyata ta cika da tababar cewa anya waɗan nan mutanen bil'adama ne kuwa? Sai ga shi a dare ɗaya zargina ya tabbata, labarin su ya zama tamkar an yi ruwa an ɗauke."

Cike da jin wani irin zafi a ƙoƙon ransa ya kalli Ayya ya ce.

" Ni dai dan Allah Ayya ku daina irin waɗan nan maganganun, wallahi bana jin daɗinsu sam! Beenafah yarinya ce ƙarama,kuma ita take ɗauke da nauyin kula da mahaifiyarta da ƙanenta, sannan su ɗin Mutane ne kamar kowa..."

Jinjina kai Ayya ta yi ta ce.

" To naji! Yanzu sai ka faɗa mini ina suke?....Ka tafi neman su an ce ba bu ma wasu masu kama da su da suka taɓa zama gidan, har su Fa'iza sun tafi amma kuma dai maganar ɗaya ce ba'a san wasu masu kama da sunan ba. Wata ƙila kuma sun koma garin su tun da dai kace su kaɗai ne su uku ƙwallin-ƙwal..."

Cikin nuna ɓacin rai Umma ta ce.

"Ai sai ya zauna nan ya yi ta ɓatawa kansa lokaci! Tun da dai ba ya jin shawara. Tun da ka kasa samun su ka haƙura mana! Ka tashi ka shirya ka wuce Kano, yan da ka ɗebo ƙarfar nan ba tare da neman izinin sa ba ka tashi ka shirya ka koma. Tun ranar da ka iso garin nan ya kirani ya sanar mini cewa bada izininsa ka taho ba, saboda haka ka tashi ka koma ka ji na faɗa maka...abu tun ana na marmari har an dawo na ɓacin rai, haba!"

Ta shi ya yi kawai ya ɗauke ledar da ke gaban sa ya nufi ɗakinsa dake ƙofar gida ya bar su Ayya nan suna halaƙoƙo.

Tun ranar da wayarsa ta lalace ya kaita gyara akace gyaranta kusan dubu talatin ne, hakan yasa ya kira Babban Yayansa dake Kano, Yaya Nura akan cewa ya turo masa da kuɗi wayarsa ta lalace, shi kuma Yaya Nuran sosai ya hau shi da faɗa yana faɗin bai ga amfanin Keke-napep ɗinda ya saya masa ba, tun da in dai lalura ta wuce dubu goma baya iya magancewa kansa ita ko kuma wani na cikin gidan to ya tattara ya dawo kusa da shi ya shiga shago shima, idan admission ɗin ya tashi daga can ya riƙa tafiya. Daman tun da ya gama N.C.E yake zaune zaman jiran Admission na zuwa jami'a, ganin yana zaune a banza yasa yayan nasa ya siya masa Napep domin ya dogara da kansa kuma ya riƙa taimakawa iyayen su da 'ƴan wasu lalurori na yau da kullum. Jin babansu da ma sauran mutanen gidan sun goya baya, hakan yasa dolensa ya shirya ya washegarin daren da ya kira Beenafah a waya. Bai ƙara shiga tashin hankali ba sai da ya yi ta kiranta bata shiga abu kamar wasa. Tunda ya tafi da ƙyar ya ga wucewar wata ɗaya lafiya, haka ya roƙi Yaya Nuran alfarma akan ya barshi ya zo gida yana da uzuri. Tun da ya sauka Gusau ya dire jakarsa ko minti ɗaya bai ƙara cikin gidan ba ya fita zuwa gidan su Beenafah. Sai dai kuma! Bai san cewa allon ƙaddara ne zai juya da shi zuwa wani bigire ba bayan ya sauka a ƙofar gidan na su. Haka ya dawo tamkar wani mutum mutumi jin cewa wai babu ma wasu masu kama da wannan sunan a cikin gidan. Tamkar wani mai taɓin hankali haka ya dinga musu da mai gadi yana neman kai masa duka. Haka ya ɗauki tsawon lokaci suna dragging ƙarshe dole dai ya bai wa kansa magana ya juya ya koma gida da tunanin cewa wata ƙila suna asibiti har yanzu ba'a ba su sallama ba. Daman tun farko da za su tafi yaso ya bi su Sokoton Babansa da Umma suka ce ba su amince ba. Haka ya share kusan sati yana zarya gidan su amma magana ɗaya ce dai cewa babu wasu mutane a gidan ma su suna Beenafah.

Haka ya tattara ya koma garin Kano zuciyarsa cunkushe da baƙin ciki da damuwar rashin samun su Beenafah. Kullum kwanan duniya sai ya kira Su Ayya cike da jaje suyi ta aikin ba shi magana mai tausasa zuciya. Sannan kullum su Fa'iza cikin zarya suke wurin neman su amma babu wani labari.

Haka ya rayu tsawon wata huɗu cikin damuwa na rashin su Beenafah, daga ƙarshe shi ne ya sake biyo hanya ya dawo ɗaɗɗake da kayayyakin siyayyar da ya jima yana yi musu musamman Beenafah, ba tare da ma Yaya Nuran ya sani ba.

Shi dai waɗan nan mutane sun zame masa ƙaddara a rayuwar sa, da yana zaune hankalinsa kwance babu abin da yake damunsa, a lokacin da ya same su sai ya ji duniyar sa ta ƙara faɗaɗa, ta yalwata da wani wadataccen farin cikin da shi kaɗai yasan mi yake ji dangane da Beenafah da ahlinta. Sai dai kuma! Daga lokacin da ya rasa su shikenan ya gigice ya ɗimauce, rayuwa ta yi masa ɗaurin kazar kuku. Yarinya ƙarama! Mai ƙaramin tunani; duk da cewa bai san komai dangane da rayuwar su ba, yasan tabbas daga action ɗinta tana da buƙatar matallafi....Tausayinta yake ji, matuƙar-matuƙar tausayinta yake ji har ma Ammien da Bahrain. Kuma in sha Allah muddin ba numfashinsa ne ya yanke daga gangar jikinsa ba, har abada ba zai daina neman su ba.

Bayan Umma ta hasa mishi wuta, dole uwar naƙi ce zaɓi, haka ya tattara ya sake komawa Kano.

****

Tun da muka shiga azumi, tare muke aiki ni da Aunty Hajjo a kitchen bayan kowa ya kambala aikinsa da zai yi na yau da kullum.

Ƙarfe biyu muke farawa wanda watarana zuwa biyar mun gama kambala komai. Kuma tun da aka fara azumi komai na ci da sha idan mukayi sai Aunty Labiba ta bamu shi, wanda kayan amfanin da ta bamu iyaka ga Suhr muke amfani da su domin komai tana bamu.

Azumi na goma sha biyar ta kiramu ta bamu Atamfa bibbiyu da shadda ɗaɗɗaya da kuɗi naira dubu talatin-talatin ta ce kowa ya je ya yi ɗin ki ya sai takalmi.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa*

*FREE-BOOK*

*PAGE 14*

Rabon da muyi sabuwar sutura har mun manta, tun lokacinda mahaifinmu na raye da kuma lokacinda Daddy yake ƙaunarmu. Amma kam rabonmu da sabon ɗinki anyi shekara uku, shiyasa kayan da muke dasu duk sun yi mana kaɗan bama kamar ni da na kasance da tsawo tamkar bishiyar zogale wacce ga tsayi amma ba jiki.

Cikin nuna tsantsar farin ciki na isa gida tamkar zan kife akan murna na zube kayan gaban Ammie ina faɗin.

"Ammie duba ki gani daga Aunty Labibata..."

Ɗaga kayan Ammie ta yi tana ta yabawa tana sakawa Aunty Labiba albarka.

Bayan ta gama duba kayan na kalleta na ce.

"Ammie, kinga sai a ɗinkewa Bahrain wannan shaddar ayi mai har da babbar riga ke kuma a ɗinke miki ɗaya nima in ɗinke ɗaya mu saka muje Idi idan Allah ya yarda..."

Hawayen da suka silalo mata ne suka ɗaga mini hankali lokaci ɗaya. Cikin ruɗewa na ce.

"Ammie lafiya? Miye ya faru?"

Girgiza kanta ta yi a hankali ta ce.

"Ba komai. Kawai dai idan ina tunawa da wasu abubuwan sai in ji zuciyata ta yi mini nauyi sosai..."

Ni ma ban san lokacinda hawaye suka wanke mini fuskata ba, ina kallonta idanuwana cike da rauni na ce.

"Ammie kina tunawa da Abbie ko? Ni ma haka! Ina jin wannan raɗaɗin da zafi a zuciyata. Shin Ammie dole Daddy ne kaɗai danginmu? Na ga wasu suna da dangi da yawa, to mu fa?"

Jinjina kanta ta yi a hankali ta lumshe idanunta ta buɗesu a kaina ba tare da hawayenta sun tsahirta ba ta ce.

" Dr. Bello da Alhaji Mudassir, Yaya guda suke da ita tallin tal wacce suke uwa ɗaya uba ɗaya da ita. Ita ce ta zamto uwa agaresu domin ita ta rainesu su biyu har suka girma wanda aurenmu bai fi shekara biyu ba ta rasu. Shiyasa Alhaji Mudassir ya zamto shi ne komai na mahaifinku..."

Sallamar Yaya Hamza ita ce ta katse mana wannan muhimmiyar firar da na yiwa babbar Register a masarrafar tunanina.

Wuri ya samu ya zauna yana mai kallon Ammie yace.

" Subhanallah! Ammie..ya naga fuskarki ta yi wani iri? Akwai wata damuwa ne?"

Murmushi ta yi tana mai share hawayenta ta ce.

"Ba komai Hamza, an dawo daga shagon?"

"Mts! Wallahi tserowa na yi Ammie na ɗan sarara idan an sha ruwa na koma. Ɗinki ya yi mana yawa kamar zan yi hauka nake ji wllhy..."

"To ina ka baro shi Jafarun?"

"Yana can Shagon, ai ya ce in faɗawa Beenafah ta haɗomai abinci idan kun rage, tuwo yau Mama tayi kuma ba zai ci ba na sani...."

Ya ƙarashe maganar yana kallona.

Nima kallonsa na yi na ce.

"To Yaya Hamza kaima gaka ka zo kuma nasan nan kake so kasha ruwan?"

"Sosai ma! Miƙo mini buta na yi alwala kinga ma lokaci ya ƙarato..." Kallon kayan da ke gaban Ammie ya yi ya ce.

"Ammie wannan ɗinka muku za'a yi?"

Ɗan murmusawa ta yi ta ce.

"Kayan ɗinkinmu ne da aka bamu sadaka a gidan aikin Beenafah."

"Allah sarki! Allah ya saka musu da alheri. Na kun sai a bai wa Yaya Jafaru domin shi ne ke yin ɗinkin Mata ni kuma sai na ɗinka na Bahrain."

Ina dariya na ce.

"Ai kuwa shikenan ta kwana gidan sauƙi...amma dan Allah ka faɗa masa ya yi mini mai kyau na zamani."

Butar da na ajiye masa zuwa gabansa yaja yana faɗin.

"To ki faɗa masa da kanki mana."

"Tau shikenan in sha Allahu zan faɗa masa Yaya Hamza. Daman Fakiha ta taɓa faɗa mini cewa Yaya Jafaru yana ɗin ki ashe kuwa da gaske ne."

Babbar tabarmarmu na ɗauko na baza sannan na ɗauko plate da sauran kayan amfani na ajiye sannan ɗauko mana kayan zuwa masallaci na ajiye a gefe.

****

Washe gari Ammie ta kira Yaya Jafaru ta bashi kayan tare da naira dubu biyar amma ya ce ba zai karɓi kuɗi ba. Babu yanda bata yi ba amma yace shi sam! ba zai karɓa ba ai yanzu an riga an zama ɗaya.

Ina kan hanya sai ga Yaya Jafaru ya cim mini wai in faɗa masa wane kalar ɗinki zai mini.

Kallonsa na yi na ce.

"Ni kam Yaya Jafaru ina nasan ɗinkin da za ka yi mini? Duk wanda ka yi mini ina so..."

"To ni ina nasan wanda kike so."

Haka dai muka yi ta janiniya har muka yi kusan kai gidan Aunty Labiba, kallonsa na yi na ce.

"Yaya Jafaru!"

"Na'am Beenafah."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull