Kenza eBookz

Ganin ido complete Novel - Chapter 9

Ganin ido complete Novel - Chapter 9

Ganin ido complete Novel Chapter 9: Ganin ido complete Novel Chapter 9. "Eyyah Aunty Beenafah dan Allah kije ki duba, kafin ki dawo na yi copying wannan da…

3,370 words

"Eyyah Aunty Beenafah dan Allah kije ki duba, kafin ki dawo na yi copying wannan da kika nuna mini please."

A hankali na tako na zo na buɗe ba tare da na ce komai ba, domin ni dai ba mai gida, ni ba kowa ba. Wani kallon banza ya yi mini kamar na ranar sannan ya ce.

" Malama ki je ki ce su Adeel su fito muna nema mu makara suna ɓata mana lokaci."

"Yanzu ake kan haɗa musu abincin kari, Mai dafa musu abinci bata da lafiya ba ta zo ba...."

"Ke! ke ce uwar su hala? Banza dake ƙazama 'ƴar aiki...In fact! ke wace ce da har za ki tsaya tsoma min bakinki a maganata? Aikenki na yi, ki wuce ki ce su fito."

Wani irin abu na ji ya tsaya mini a raina tamkar dutse lokaci ɗaya tsabar al'ajabi, mamaki da takaici.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa*

*FREE-BOOK*

*PAGE 12*

A hankali na mayarda ƙofar na rufe na bar shi a tsaye na koma muka ci gaba da abin da muke yi ni da Adeel. Bayani kawai nake masa amma kuma zuciyata cike take maƙil da baƙin ciki tamkar za ta fashe tsabar yanda na ji ya ɓata mini rai. Idan har ya matsu, to ya buɗe gidan ya shigo ko kuma ya tsaya can ya sake ƙwanƙwasowa.

Shima Muhsin ɗin abin da yake nema kenan, bayan ya ƙara some minute yaga Ba su fito, shi ne ya je ya tsarawa Mamansu Ƙarya da gaskiya ita kuma ta yi zuciya ta fito da Key ɗin motar ta taje ta kai su. Ga driver na ta yi mata magana amma ko kallon inda yake tsaye ba ta yi ba.

Aunty Labiba kuwa, sai kusan goma da rabi suka gama karyawa sannan suka tashi na taimaka mata na shirya mata Hanan, Adeel ma ya shirya sannan suka fito ɗauke da kayansu.

Tana isowa Parking lot ta tarar da Driver suka gaisa sannan ta ce.

"Ka ajiye su Tima tun ɗazu ko?"

Da sauri ya girgiza kai ya ce.

"Aa, Hajiyar ce ta kai su da kanta."

Batare da kawo komai a rai ba ta ce yaje ya ajiye su kuma dan Allah ga short note ya kaiwa Malamin su yace in ji ta.

Tana shigowa ta kirani na zo Palour na same ta ta kalleni ta ce.

"Kin iya girki Beenafah?"

Girgiza kaina na yi na ce.

"Gaskiya ba zan ce eh ba ga girki irin wanda Aunty Hajjo ta iya."

"OK to ba damuwa. Ina so don Allah, idan kin koma ki nema mini alfarmar mamanki cewa za ki ɗan riƙa wuce ƙarfe biyu domin ki ɗan riƙa tayani rage wasu abubuwa kafin Hajjo ta ji sauƙi ta dawo. Sai ki ɗan riƙa tsayawa kamar zuwa five haka."

"Ok. To ba damuwa In Sha Allahu zan sanar mata...."

Daga nan na ɗan ƙara yin ƙasa da muryata na ce.

"Nima ina neman alfarma. Gobe ina so zan raka Mamata Asibiti."

"Ba damuwa, ni ma ina da fita gobe...yanzu abin da za'a yi shi ne, zan tura su Adeel can gidanmu in yaso da dare sai a dawo da su."

Ranar Talata, ina shirin tafiya gida sai ga su Hanan sun dawo. Da gudu Adeel ya zo ya rungume ni yana faɗin.

"Thank Aunty Beenafah! Thank you. Wallahi kuwa ashe kin iya sosai. Ina cikin mutum huɗu da suka fi kowa cin maki na wannan home work ɗin...dan Allah zo ki nuna mini yanda zan yi na bokona.."

Ni dariya ma ya bani yan da yake ta wani farin ciki yana jan hannuna.

" Adeel ba fa komai na iya ba, kada na yi maka kaje ka ci zero kaga ba daɗi..."

"Ba wani Zero Aunty Beenafah, Haka kika ce ko ranar kuma ga shi ban ci Zero ba."

"Aji nawa kake?"

"J.s.s one nake going to two..."

Duk yan da nake hango na yi lattin zuwa gida, Adeel bai barni ba sai da muka yi home work ɗin sannan na tafi gida.

****

Bayan sati ɗaya.

Labiba na zaune misalin ƙarfe takwas na dare Mijinta ya shigo gidan. Da gudu su Adeel suka tarbe shi suna masa sannu da zuwa. Kayan da ke hannunsa ta karɓa sannan ta rakashi yaje ya rage kayan jikinsa ya shiga wanka.

Koda ya shirya ya fito har ta gama jera mishi abinci a dining table suka zauna suka ci sannan suka dawo parlourn suka zauna.

Kallon Adeel ya yi ya ce.

"Adeel! Ku tafi da Hanan parlourn ciki ka kunna mata cartoon.."

Miƙewa Hanan ɗin ta yi ɗaɗɗake da Tidy bear ɗinta suka wuce.

"Adeel dan Allah ka kamo mata wanda take so na san halinka."

"In Sha Allah Abba."

Bayan sun wuce ya kalleta cikin tsanaki ya kira sunanta.

"Labiba!"

Cike da nutsuwarta ta amsa.

"Na'am Barrister."

"Ina so ki faɗa min miye abin da ya faru a gidan nan har Hajiya Marwa ke kai yara Islamiyya da boko da kanta."

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta kai hannunta ta ɗora akan na shi ta fara magana.

"Barrister! Ka san halina sarai. Wallahi ban san abin da ya faru ba. Na dai san ranar na kira ka kana gidanta na faɗa maka cewa munyi late saboda Hajjo bata da lafiya idan tafiya za su yi su tafi idan ya dawo sai ya ajiye su,Idan kuma bai dawo ba ni sai na ajiye su da kaina, to ban san miye ya faru ba."

" Shi kenan. Sai magana ta gaba, amma tashi ki fara saka mini system ɗinnan a caji please..."

"Ok to. Daga nan zan duba yaran can har su shiga bacci, ina dawowa yanzu."

****

Tun da na raka Ammie asibiti na dawo, kullum bana fashin zuwa, kuma idan na tafi sai biyar na yamma nake komawa gida. Hakan sai ya ƙara mana kusanci sosai da Aunty Labiba da kuma yaranta. Mace ce mai matuƙar mutunci da kirki...kai ba ita ba, duk wani wanda zai zo daga gefen ta to da wahala ka ganshi ace ba shi da kirki. Ina jin daɗinta kuma har abada bana danasanin haɗuwata da ita domin ita ɗin ta kasance fitila a cikin rayuwarmu. Sati biyu cikin na uku na share idan na zo sai five nike tafiya sannan Aunty Hajjo ta dawo, bayan ta murmure.

Aunty Labiba ta so na ci gaba da kaiwa ƙarfe biyar na yamma ɗin amma na ƙi amincewa domin duk inda nake Ammie tana cikin tunanina, ko kwanakin baya daurewa ce kawai nake don bani da yanda zan yi amma yanzu tun da Aunty Hajjo ta dawo kawai na ce tayi haƙuri.

Sai dai, a yanzu mun ɗan ƙara sake wa juna ba kamar farko ba, musamman yanzu da Adeel ke yawan saka ni a gaba wurin yin assignment ɗinsa idan ya zo da shi daga makaranta.

Muna kitchen tare da Aunty Hajjo, tun ina shara har na kambala na yi duk goge-gogen da zan yi tana nan maƙale da waya a kunnenta tana magana.

Kallonta na yi na ce.

"Wai Aunty Hajjo da wa kike ta magana haka a waya tun ɗazu?"

Kashe wayar tayi tana dariya ta ce.

"Soyayya nake yi mana."

Ƙureta na yi da kallo bakin gaskiyata na ce.

"Soyayya? Kamar ya kenan?"

Wani kallon uku saura kwata ta yi mini sannan ta ce.

"Ban son renin hankali fa Beenafah."

Murmushi na yi mata ina faɗin.

"To Allah ya baki haƙuri."

Daga haka na wuce na wanke Uniform ɗin su Hanan sannan na fito zuwa gida.

Ina zuwa ƙofar gida na tarar da Yaya Jafaru yana zaune. Gaishe shi na yi ya amsa sannan ya kalleni ya ce.

"Beenafah ko za ki ɗan sammin abincin nan ne, wallahi ina jin yunwa."

Da murmushina na ce.

"Ƙwarai kuwa Yaya Jafaru mi zai hana. Bari yanzu na shiga na ɗebo maka, jirani kaɗan."

Koda na fito daga gida na tarar Yaya Jafarun ya ci kwalar abokinsa da na tarar da su zaune a tare kafin na shiga gida mutane sun taru da yawa sai faman rabasu ake. Gefe na ja na tsaya ina jiyo duk abin da ke faruwa wai ashe akanmu ne Yaya Jafaru yake faɗa.

Ina nan tsaye a gefe har aka ci aka suɗe, mutane suka watse sannan na zo inda yake zaune na ajiye masa abincin na juya bance masa komai ba na shige gida.

****

Misalin ƙarfe goma sha ɗaya na dare. Daddy ne zaune a gefen gadonsa yayin da Mummy ke tsaye tana shiryarwa cikin kayan baccin ta.

"Hajiya ke fa nake jira ina so zamuyi magana."

Ɗan ƙara gaggautawa ta yi ta kambala sannan ta zo dab da shi ta zauna tana faɗin.

"Alhaji Allah dai yasa lafiya?"

Jinjina kai ya yi ya ce.

"Lafiya ƙalau, magana ce akan Aysha..."

Lokaci ɗaya annurin fuskarta ya ɓace, cikin kaushi ta ce.

"Miye ya faru?"

Ƙara sassauta muryarsa ya yi sosai ya ce.

"Hajiya Zaliha! Dole lokaci ya yi da ya kamata ki saurareni. Na sani cewa Aysha ta aikata kuskure, kuma na ɗauke shi cikin rashin wayau da kuma sharrin shaiɗan. Saboda haka ki yi haƙuri ki yafe mata...."

"Haba Alhaji! Ayshar ce ba ta da wayau? Shekara ashirin da bakwai a duniya! Ɗauke da igiyoyin aure a kanta! ta haihu tasan zafin haihuwa sannan ka ce mini rashin wayau...komai rashin wayaunta ai ta san cewa ni ce mahaifiyarta kuma ko mahaukaci yasan uwar sa...Ni Aysha za ta nunawa karenta ya kai tsaiko!..."

"Duk na ji Hajiya Zaliha, ki yi haƙuri..Allah ma muna masa laifi kuma ya yafe mana ballantana tsananinmu mu 'ƴan Adam. Ki yi haƙuri ai ta riga ta gane kuskuren ta sai dai a haƙi gaba,kuma In Sha Allahu ba za ta sake ba. Ke fa mahaifiyarta ce ba ta da wata uwa a duniyar nan bayan yake, wannan hukuncin ya isa haka, ina so daga yau ki janye furucinki itama ta dawo cikin sauran en uwanta taci gaba da mu'amala da su da kuma mu, ki bar komai ya wuce."

Ta ɗauki tsawon lokaci tana nazari sannan daga ƙarshe ta sauke ajiyar zuciya ta ce.

" Shikenan! Allah ya yafe mana baki ɗaya."

"Ameeeen! Uwargidan Mudassir Wazeer. Na gode miki, Allah ya ƙara bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali."

"Amin. Ina so zan kwanta."

Ta faɗa tana wani yatsina fuska tamkar wadda taga kashi.

Ɗan janyewa ya yi kaɗan shi kuma yana faɗin.

"Ba matsala, yi kwanciyarki ki huta. Allah ya tashemu lafiya."

Tashi ya yi ya rage mata hasken fitilar ɗakin sannan ya fice ya kira en biyu suka fito parlour suka samesa.

"Daddy lafiya?"

Cewar Hassana tana mai samun wuri ta zauna ido cike da bacci.

Shi kuma cikin farin ciki ya ce.

"Albishir na zo na muku; Mummynku ta yafe wa Auntynku yanzu za ta iya tahowa gida..."

Wani Uban Ihu Husaina ta buga tana laƙe daddy cike da farin ciki ta ce.

"Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Yah Allah. Thank you so much Daddy, ubangiji Allah ya ƙara girma, Allah ya ƙarawa wannan family namu zaman lafiya mai ɗorewa da ci gaban rayuwa."

"Amin Yah Allah. Yanzu kam kuka ya ƙare ko?"

Murmushi ta yi tana mai gyaɗa masa kanta. A ranta kuma, addu'a take 'Allah yanda ya juya al'amarin dake tsakanin Mummy da Aunty Aysha a dare ɗaya, to ko yanzu al'amarin Su Beenafah tana addu'a Allah ya canza zuciyoyin iyayenta yasa su gane gaskiya su dawo da su cikinsu su ci gaba da rayuwa kamar yanda suke a baya'

Tsintar Muryar Hassana suka yi wacce ta ɗauki hanyar komawa ɗakin su tana faɗin.

"Ni dai bacci nake ji, sai dai da safe idan na fito.."

Kallon Husaina Daddy ya yi ya ce.

"To kema ki je ki kwanta ki bar shi sai gobe..."

Cikin sauri ta girgiza kanta tare da duba agogon wayar ta ta ce.

"A'a Daddy! Ba zan iya jira ba,....A wannan yanayin, tazarar hour ɗaya ce tsakaninmu da London kamar yanda Aunty Ayshar ta faɗa mini, saboda haka yanzu muna ƙarfe goma sha biyu saura na dare, kenan su a wurin su ƙarfe ɗaya ne saura, amma gaskiya ba zan iya jira ba dole na kira ta a yanzu na sanar mata."

Girgiza kan shi ya yi yana murmushi kawai ya juya ya koma ciki.

Ringing ɗaya zuwa na biyu ta ji muryar Ayshar ta ɗaga, sauti can ƙasa sosai ta ce.

" Hussy, lafiya kuwa? Ko wani abin ne ya sake faruwa?"

Cike da farin ciki ta ce.

" Aunty Aysha you freed congratulations!"

Daram! Haka ta ji ƙirjinta ya buga, da sauri ta ce.

"Are you serious?"

"Yes... Yes.. Aunty Aysha, wallahi da gaske nake miki. Mummy ta yafe miki, tace you can come home anytime you want. And za ki iya magana da duk wanda kike so a cikinmu"

Wa su hawayen farin ciki ta ji sun wanke mata fuska lokaci ɗaya ta shiga furta kalaman godiya zuwa ga Ubangiji mai girma.

"Hussy!"

"Na'am Aunty Aysha."

"Miye kike so? Faɗa mini duk duniyar nan miye abin da kike so?"

Cikin jin wa su zafafan hawaye ta girgiza kanta tamkar tana a gabanta ta ce.

"Ba komai Aunty...abin da yake raina ba za ki iya cika mini shi ba, sai dai ina so ki tayani da addu'a Allah ya cika mini burina."

"Amin..Hussy, In Sha Allah zan tayaki da addu'a har burin naki ya cika, kuma ko ya cika Hussy Addu'a ta tana tare daku har ƙarshen rayuwata.."

"Na gode Aunty Aysha... Ina Baffa?"

"Baffa ya yi bacci, ya lectures?"

"Alhamdulillah! Lectures tana nan ana ta yinta da zafinta..amma gaskiya yanzu mun fi jin sauƙi saboda muna gida ba kamar da muke hostel ba..."

Nan suka ɓata dare suna fira sai kusan uku na daren agogon Nigeria sannan suka yi sallama.

****

Yau tun asuba Bahrain ya masifeni akan dole sai na bi ta school ɗin su na rakashi mun yi magana da malamin su dake son ganina. Shiyasa na yi saurin kambala duk abin da nake ƙarfe bakwai da rabi muka fito muka je, daman daga school ɗin su zuwa gida bamu da wani nisa sosai. Faɗa mini suka yi wai ana aika mana taron iyayen yara amma bamu taɓa halarta ba shiyasa akace sai ya zo da maga'isan sa,dalilin kiran shi ne wai, bayan sallar azumi dake gabatowa idan Allah ya kaimu Bahrain zai yi walima tare da sauran en makarantar su, saboda haka akwai kuɗaɗen da zamu biya idan lokaci yayi, daman nasan ya yi hizib kusan hamsin da uku. Sai kuma kuɗin exam ɗin ƙare primary school zuwa Jss one da kuma kuɗin graduation.

Godiya na yi musu cikin tsantsar farin ciki na ce musu in sha Allah zamu biya komai da komai kafin lokaci ya yi. Daga nan nayi musu godiya na fito na nufi gidan Aunty Labiba.

Ina kan hanya na ci karo da Yaya Jafaru wanda ba zan ce ga daga inda ya fito ba.

Da murmushi ya tarbeni cike da nutsuwarsa ya ce.

"Beenafah! An tashi lafiya?"

"Lafiya lau Yaya Jafaru ina kwana."

"Lafiya lau, sai ina haka?"

"Gidan aikina zan tafi."

"Allah sarki! Nima na dawo daga raka Farisa makaranta ne."

Shiru muka yi na ɗan lokaci, sannan daga ƙarshe ya ce.

"Muje na raka ki mana."

Da sauri na girgiza kaina na ce.

"A'a Yaya Jafaru ka bar shi nagode."

"Ranar sai kika ji muna ta darga da Shahid, bai da kirki ko kaɗan, idan ba shi ba ina ruwansa da rayuwarku.."

Murmushi na yi na ce.

"Ba komai Yaya Jafaru kada ma wannan ya dame ka. Daman idan ba'a yi da kai ai ba kowa kake ba. Sai an jima."

"To ya yi, Allah ya tsare sai kin dawo."

Ina zuwa gidan yau na tarar da wani mutum zaune parlourn na Aunty Labiba. Duƙawa na yi har ƙasa na ce.

"Ina kwana."

Dauke kansa yayi daga kallon wayar da yake ya ƙare mini kallo tsaf sannan ya amsa gaisuwar da na masa sai kuma ya sake cewa.

"Wace ce ke?"

Ƙara saukar da Idanuna na yi na ce.

"Ni mai aikin Aunty Labiba ce..."

Cike da zallar nuna mamaki a maganar ya maimaita ya ce.

"Mai aiki?"

✍️ *OUM-AMEER* ✍️

*GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa*

*FREE-BOOK*

*PAGE 13*

Muryar Aunty Labiba na ji tana shigowa parlourn tare da su Hanan shirye cikin uniform ɗin su na Islamiyya ta ce.

"Barrister Beenafah ce fa. Mai aikina wacce Adeel ke yawan yin maganarta."

"Oh! Allah sarki. Wannan ita ce Beenafah? Da yake kin san ban taɓa ganin ta ba sai yau.... Sannunki."

Faɗowa Hanan ta yi jikina cike da jin tsagwaron rigimarta da ta saba tace.

"Aunty Beenafah ta shi muje makarantarmu..."

Miƙewa na yi da sauri na nufi ciki janye da hannunta,muna shiga na rungumeta ina shaƙar daddaɗan ƙamshinta na ce.

"Wow...My Hanan! ƙamshinki mai daɗi, uniform wankakku kuma gashi an goge su sun yi kyau, yau kin yi kyau kin ji ko tawan....amma kema kin san cewa ba zan iya zuwa makarantarku ba dan Allah kada ki ci gaba da rigima, ki je makarantarki kin ji ko?"

"To za ki tsaya har na dawo?"

"Sosai ma. Yi maza driver yana jira kar ki yi latti."

Daga haka ta fice tana mini bye-bye yayin da ta bar Adeel nan tsaye yana mai bina da kallo wanda da alama akwai abin da yake so ya tambayeni ko ya faɗa mini.

"Aunty Beenafah amma dai kin taɓa yin makaranta?"

Dariya ce ta suɓuce mini ba tare da na shirya ba sannan na gyaɗa masa kaina na ce.

"Eh, na taɓa yi mana..."

"Aji nawa kike to?"

"Kamar ajin da kake yanzu."

"J.s one kenan?"

"Eh."

"Wace school to?"

"Ban sani ba.."

Ɗan Jim ya yi kaɗan jin amsar da na bashi wanda a zatona zai sa kai ya wuce ne amma sai naji ya sake yi mini wata tambayar da cewa.

"Aunty Beenafah kinga karatun da kika koya mini ranar? Wallahi Uncle Daniel ya ce na iya sosai haka ma a islamiyya kullum yanzu ina cikin waɗanda suke saurin iya karatu saboda kina duba min"

Ina kan cire hijabina kawai na ce.

"To ka ji daɗi..."

"To ke Aunty Beenafah duk ya akayi kika iya komai da komai?"

"Ta hanyar koya mana, kamar kai yanda ka ke yi."

"To ta ya ya?"

Hannayena na saka na riƙe ƙuguna ina kallon sa na ce.

"Ban sani ba Adeel! Ban sani ba na ce. Ka wuce kada ka yi latti."

Na ƙarashe maganar ina mai yi masa nuni da ƙofa.

"Allah baki haƙuri."

Banza na yi masa tare da yin gaba na bar shi a nan. Zuwa gobe bai hana idan muka sake haɗuwa ya ci gaba da damuna da tambayoyin da har zai kai ga ƙureni.

A kitchen na samu Aunty Hajjo na gaisheta sannan na tambayeta na ce.

" Ashe Aunty Hajjo Babansu Adeel a gidannan yake yau? Lissafina ya ɓace wallahi. Allah yasa kada Aunty ta ji haushin cewa na karya mata doka."

Girgiza kanta ta yi ta ce.

"A'a, ba a nan yake ba, ina ga tafiya Maman Tima tayi shiyasa yake nan...Ɗauki ga kaya can ki wanke in ji Aunty Labiba."

Ɗauka na yi naje na wanke mata na dawo da su sannan na wuce wurin aikina.

****

Aysha kuwa, Tun da Husaina ta kira ta, ba su ƙara cikakken wata ɗaya a birnin London ba. Daman faɗuwa ce ta zo dai-dai da zama domin auren ƙanwar Ahlan Firdausi saura kwanaki kaɗan wanda bayan auren iyaka sati biyu zuwa uku azumi.

A Abuja suka sauka kamar yan da ta nemeshi alfarma domin a Sokoto ainahin gidan auren su yake sannan shi Ahlan ɗin ɗan Sokoto ne har iyayensa a can suke zaune. Shi ne ta roƙi alfarma akan ya bari su fara sauka nan in yaso daga baya sai ta taho idan bikin ya tashi.

Sanin irin wahala da ƙuncin da ta shiga sai bai yi yunƙurin hana ta ba, sai dai kuma yace mata ba zai je gidan na su ba a yanzu, sai idan sun tashi komawa zai zo ya gaishe su. Abin da Mummy ta yi har yau ya kasa mantawa, shiyasa yanzu ya ɗauki hanyar yin baya-baya da Ita kada shima laifin Ayshar ya shafeshi.

Driver ne ya zo ɗaukarta tare da Humaida da kuma twins.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull