Ganin ido complete Novel - Chapter 14
Ganin ido complete Novel Chapter 14: Ganin ido complete Novel Chapter 14. "Mama daman cewa na yi ki sanarwa da Maman Abul cewa daga yau na daina yin aiki a…
3,360 words
"Mama daman cewa na yi ki sanarwa da Maman Abul cewa daga yau na daina yin aiki a gidanta ta nemo wata domin na samu wani aikin wanda yafi na gidanta, aikin wannan watan da na yi mata kuma ta ƙiyasti ta biyani duk abin da tayi niyya..."
Dariyar Fakiha na jiyo a bayana tana faɗin.
" Gaskiya Beenafah in dai akan maganar kuɗi ce baki da wasa. Yanzu ma har aikin wannan watan duk da kin canza gida sai ta biya ki ba za ki yafe mata ba? "
Jinjina kaina na yi ina dariyar nima na ce.
" Eh, ba zan iya yafe mata ba gaskiya. Sana'a tafi maula, aiki na yi mata akan zata biyani, ba roƙonta na yi ba, saboda haka dole ta biyani ko aikin kwana ɗaya ne."
Kallona Maman ta su ta yi ta ce.
"Ƙyaleta Beenafah. In sha Allahu zan sanar mata kuma zan amso miki kuɗinki. Halan ina kika samu wani aikin?"
"Gidan iyayen Aunty Labibar ne."
"Eyyah! Allah sarki, wato dai duk tsawon lokacin nan bata manta dake ba tana can tana neman mafita. Allah ubangiji ya saka mata da mafificin alheri ya bada lada. Sai ki kula wannan karon Beenafah. Ki yi ta haƙuri ki kuma zama mai kauda kai ga wasu abubuwan. "
Jinjina kaina na yi cike da jin daɗin maganganun ta na ce.
" In sha Allahu Mama zan kiyaye na gode sosai, sai na dawo.... Bye Fakiha sai na dawo."
Na ƙarashe maganar ina mai ɗaga mata hannu na nufi ƙofa.
"To ya yi, sai kin dawo. Ni ma yanzu ai Islamiyya zan wuce duk da dai na buga uban latti yau."
****
Ban fi minti ashirin da tsayuwa ba sai ga ta tazo ta parker a gabana tare da buɗe mini gaban motar tace na shiga.
Ina shiga na kalle ta na ce.
" Ina kwana Aunty Labiba."
"Lafiya lau Beenafah....kin shirya?"
Kallon jikina na yi a ɗan kaikaice domin in ƙara tabbatarwa sannan daga ƙarshe na gyaɗa mata kaina na ce.
"Eh."
Murmushi kawai ta yi tare da jinjina kanta sannan ta tayar da motar muka fara tafiya.
Kallona tayi a kaikaice ta ce.
"Naga duk kin wani shige gashi Beenafah. Kada ki damu, gidanmu yafi gidana daɗin zama..."
Wani kallon na jefa mata ba tare da na shirya ba, jin wani labari mai kama da ƙanzon kurege. Ta ina gidan su zai fi mini gidanta? Abin da ma ba zai yiyu ba kenan duk da dai banje na gani ba.
Dariya ta yi tana mai jinjina mini kanta ta ce.
" Da gaske nake miki Beenafah, gidanmu yafi gidana domin ni daga ni sai ku, gidanmu kuma gidan mutane ne da yawa..."
Haka dai ta yi ta bani baki domin ta samu na kwantar da hankalina, amma kuma nima abin da yake raina daban.
Ina nan ina baza IDO tamkar wata baƙauyiya duk da ta wani fannin zan iya kiran kaina da hakan, har dai muka iso ƙofar wani katafaren gida abin da ake kira gida wanda masu tsaron ƙofar kaɗai sun isa su sa ka gane cewa ba a ƙaramin wuri kake ba. Bayan mai gadi ya wangale mana gate ɗin gidan mun shiga, nan na ƙara tabbatar da cewa lallai wata jar Miyar sai a maƙota. Duk yanda nake ganin girma da faɗin gidan Aunty Labiba da kuma gidan Daddy, wannan yaci uban na su nesa ba kusa ba. Domin dai it was masterpiece of class and elegance, gidan da duk hassadarka idan ka shigo shi sai ka tsaya kallon sa tsabar burgewa.
Gidan yana da manya-manyan gate guda uku, ɗayan shine gaba ɗaya mai kallon babban titi wanda through nan ake shigowa gidan, sai ɗayan kuma wanda sai ka ƙetareshi sannan zaka kai ga mutanen gidan sai na ukun wanda yake ta baya.
Wani daddaɗan ƙamshi ne ke tashi ta ko'ina na Imported roses and jasmine, ta dalilin flowers ɗinda aka shuka cikin harabar gidan wanda a cikinsu akwai na na'ura masu zaman kan su da suke bada ƙamshi na musamman tare da kaɗa iska mai ɗauke da ƙamshin turaren Oud.
Gidan gaba ɗaya kewaye yake da CCTV Cameras, smart lighting system, da Kuma automatic gate sensors Wanda Idan dare ya yi hasken gidan shi ke kunna kansa idan gari ya waye kuma ya kashe kansa.
A nan harabar first gate parking lot yake inda Aunty Labiba ta wuce kai tsaye ta yi parking. A farfajiyar parking lot ɗin kaɗai;ƙasan shi an yi shi ne da Italian interlock stones, ash and champagne gold, sai wani irin sheƙi suke tamkar glass aka shimfiɗa, Wanda a ƙarshen Layin ginin parking lot ɗin,akwai electric car charger Wanda aka saka don motar BMW i8 hybrid, Sannan akwai motion sensor camera mai lura da duk wanda ya shigo. Hakan kuwa nasan baya rasa nasaba da jibga-jibgan motocin da aka ajiye a harabar ajiye motocin wanda bahaushe ya ce tsaron kaya yafi ban cigiya. Sannan a bangon gefe kuma akwai garden lights da stone bench, inda yawanci suke shan coffee da safe Ko dare a duk sanda suka yi ra'ayi.
A farfajiyar gate na biyu kuma;akwai artificial fountain da ruwa ke ɓuɓɓuga sannu a hankali yana bada wani soothing sound gwanin burgewa.
A hankali nake bin bayanta tamkar wani raƙumi da akala har muka tsallako second gate inda yake ɗauke da manya-manyan mansion guda biyu, ɗaya flat ɗayan kuma Upstairs ne mai hawa uku, sai wa su ƙananun flat a can nesa da su. A hankali na ji na jefa ƙafata ƙasan polished marble tile ɗinda aka yi pathway zuwa main door ɗin babban flat Mansion ɗin Wanda kuma a gefe-gefe akwai automatic lamp posts masu haske da solar sensors suna tsaye a layi wanda suke kunna kansu da zarar hasken rana ya fara gushewa.
Muna jefa ƙafa cikin katafaren parlourn... Oh my God! Lokaci ɗaya naji bugawar zuciyata ya sauya, sanadiyyar wani irin sanyi da ƙamshin daɗinda suka buga ƙofofin hancina zuwa ƙwaƙwalwata. A ƙasan parlourn, Persian rug ne gold and brown yana wani irin sheƙi tamkar an shafe shi da mai. Ceiling ɗin saman ɗakin kuwa, Gypsum ne wanda aka zagaye shi da blue and white LED Light suna wani walƙiya suna shining tamkar taurari a sararin samaniya.
Italian Sofas ne jere a parlourn, beige and gold colour waɗanda aka ƙawata su da adon pillows manya-manya masu kyau da tsari. A tsakiyar parlourn, akwai crystal glass centre table Wanda a ciki akwai Dubai fresh flowers masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali.
Wani Babban photo frame ne jingine a bangon yamma na wani kyakkyawan matashi wanda ke sanye a cikin shigar kaki da ban san ko na miye ba. Sai kuma art painting daban masu kyau da ɗaukar ido na manyan masu kuɗi.
A gefe guda kuma, akwai 85-inc smart TV da home theater system daban. Sai wani kewayayyen wuri wanda akwai mini coffee bar, Inda akwai Coffee machine da Turkish teapots, da Kuma flask masu kyaun gaske. Sai wani katafaren wurin Gym daban wanda babu abinda babu na motsa jiki.
Haka muka ratsa muka shige wani babban parlourn, sai dai shi wannan parlourn bai yi tarkacen wancan na farkon ba amma kuma akwai wani wuri da aka zagaye shi tamkar masallaci inda akwai wata ƙaramar show glass Mai ɗauke da kwalaben humra da kuma litattafan addini a jere wuri ɗaya, sai babbar prayer Mat da aka malale wurin da ita.
Wani haɗaɗɗen matashi ne muka tarar a parlour wanda ya so ya yi mini kama da Guy ɗinda muka baro frame ɗinsa a parlourn farko. Zaune yake tare da wata kyakkyawar Mace wacce ke zaune dab da shi a Kujera ɗaya. Ga abinci nan kala-kala tuttule a gabansu da alama wani bukin ake a gidan. Domin har fruit ga su nan kala-kala da kuma lemukan kwalba.
Murmushi suka sakarwa juna sannan namijin yace.
"Hajiya Aunty Labibatu..!"
Dariya tayi tana mai samun wuri ta zauna a wata kujerar ta ce.
"Ai kai ne Alhaji, ranka ya daɗe."
"Aunty Labiba Ina kwana?"
"Lafiya ƙalau Ziza, ya gidan? Ya jiki-jiki kuma?"
Ɗan sosa bayan ƙeyarsa yayi yana mai yiwa wadda aka kira Ziza wani kallo ya ce.
"Ku daina ce mata ya jikin nan please! Ziza ta hana mini zaman lafiya tun farkon samuwar cikin nan har yau...kullum yanzu ita bata son wannan abun, ita wannan abun take so, idan na dawo don na Huta to ba hutu nake ba because she's always suffering my life all over."
Dariya dukkan su suka fashe da ita sannan Aunty Labiba ta ce.
" Zamowa Baba is not easy at all! So you better shine your eyes. Dukkan iyaye a haka suka fara. Allah ya inganta ya saukar lafiya ya bada kuma rayayye mai albarka."
Ɗan yatsina fuska ya yi kamar wata Macce sannan ya ce.
"To amin, amma please, tell her to stop suffering me. Yanzu haka daga ANC muke, ko yanzu scanning ɗinda muka yi ya nuna akwai kusan two month ahead kafin haihuwar nan amma gata nan sai ta riƙa yin wani abu kamar yanzu za ta haihu..."
Wata dariyar suka sake kwashewa da ita sannan daga baya Ziza ta tsahirta tana mai riƙo hannun sa ta ce.
" Cool down Habibi nima fa ba laifina ba ne... "
Fisge hannun nashi ya yi yana mai canja kujera yace.
" Abeg leave my hand. Kullum ai haka kike cewa."
"To yanzu ni dai duk ba wannan ba. Ina Hajiya...?"
Ta yi tambayar tana mai kallo inda nake tsaye cike da mamaki tace.
"Aa! Wai daman baki zauna ba Beenafah? Dan Allah ki zauna mana."
A hankali na zame daga gefen kujerar da nake tsaye na zauna a ƙasa, Murya a ƙasa sosai na ce.
"Ina kwanan ku?"
"Lafiya."
Wacce aka kira da Ziza ta amsa tana mai bina da kallo yayin da shi kuma mijin nata bai amsa ba bai kuma kalle ni, ban sani ba ko bai ji ni bane oho!
"Ina Hajiya na ce?"
"Hajiya has a visitor fa, but ta ce tana zuwa yanzu."
Cewar Ziza tana mai ɗauke ƙafafunta a hankali ta ɗora su akan gefen kujerar da take zaune.
Fira suka ci gaba da yi sama-sama har lokacin da hajiyar ta fito sannan suka tsahirta, bayan sun gaisa nima na gaishe ta sannan daga baya Aunty Labiba ta kalleni ta ce.
"Hajiya, ga yarinyar da muka yi magana jiya a waya. Sunan ta Beenafah, za ta riƙa yin shara da goge-goge a gidan nan. Idan kinga aikin ya yi kaɗan su biyu, Munira za ta iya joining su Haula a kitchen, idan kuma ya yi miki, sai su riƙa yi a tare, ko kuma a juya mata zuwa wani aikin...."
Sai yanzu ya ajiye wayar hannun sa akan handle ɗin kujerar da yake zaune ya waro idanunsa a kaina ya kalle ni yana murmushi ya ce.
" Wow! Gaskiya Hajiya Labiba wannan kam ba 'ƴar aiki kika kawo ba, matar aure kika kawo min har gida"
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *ArewaPen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 17*
Wata uwar harara Aunty Labibar ta maka mishi tana murmushi ta ce.
"Mts! Ka kiyaye ni Emraan."
Shiru ya yi bai tanka ba, sai ma ya yi tamkar ba shi ne ya yi maganar ba, daga ƙarshe kuma ya miƙe tare da ɗaukar wayarsa ya bi ta wata ƙofa ya shige ciki.
Itama dai matar tasa jin furucin da ya yi yasa ta saurin sauke idanun ta a kaina a karo na biyu ba tare da ta shirya ba wanda a hankali ta sake ƙare mini kallo kawai ba tare da yin magana ba, daga ƙarshe ta mayarda kanta ta ci gaba da abin da take a waya.
Kallona Hajiyar ta yi na ɗan lokaci sannan ta koma ga Aunty Labiba ta ce.
"Kin san fa gidannan akwai yawa sosai..."
"Shiyasa na kawowa Munira Assistant ai. And beside, the girl need help."
"To duk na ji, amma dai Labiba kin san kuma bana shiri da wanda baya son aiki. Naga kuma yanayinta kamar za ta yi son jiki ba ta da alamun kazar-kazar."
Dariya Aunty Labiba ta yi tana girgiza kai ta ce.
"Hajiya, Beenafah ba haka take ba, ni ma abin da na tsammata kenan farkon ganina da ita, sai daga baya na gane ashe yanayin ta ne kawai a haka, amma akwai ta da aiki sosai. Kinga gidana? Idan kika cire ɗaki uku a ciki, gaba ɗaya ita ce take share shi ta goge shi, kuma ko kafin 2pm wani lokacin ta kambala har ma da wasu aikace-aikace."
Jinjina kanta ta yi alamar gamsuwa da maganarta sannan ta ce.
" Tau ya yi kyau, bani wayata gata can na kira Haula inji ina ita Munirar take."
Tashi na yi na ɗauko wayar na miƙa mata sannan na sake samun wuri na zauna wanda ba jimawa bayan ta kira wadda tace sai gasu sun shigo a wata ƙofar a tare.
Ƙasa suka zauna kamar yanda na yi suka gaishe da Aunty Labiba wacce ta amsa musu cikin faram-faram da daɗin rai.
"Haula."
Wadda ta zauna a gefena ce ta amsa kiran hajiyar tare da kallon inda take zaune.
"Ga ta nan, za ta riƙa aiki tare da ku, har can wurin kitchen za ta riƙa sharewa. Sai ku faɗawa Lawan daga yau ya tsaya da sharar tasa can gaban gida. Daman can ba ƙaunar zuwansa inda kuke nake yi ba"
Dariya Aunty Labiba ta yi ta ce.
"Hajiya shi Lawan ɗin? naga fa ba ruwansa..."
"Uhm! Haka za ki gansa shiru-shiru amma shegen iyayi ne da shi da rashin kamun kai.....kin ji dai mi na ce ko Haula?"
"In Sha Allahu Hajiya, naji."
"To tashi kuje ku nuna mata komai yanda yake."
Kallon Aunty Labiba na yi kamar yanda itama take kallona sai ta gyaɗa mini kanta ta ce.
"Ta shi kuje kinji ko Beenafah..... Ga Beenafah nan dan Allah ku zauna lafiya da ita duk da nasan kuma baku da matsala."
Gyaɗa kai Munira ta yi ta ce.
"In Sha Allah Aunty Labiba."
Daga haka muka miƙe a tare muka shige ta ƙofar da suka shigo.
Sake kallon Hajiyar ta yi ta ce.
"To amma fa ban faɗa miki wani abu ba hajiya. Ita ba'a nan za ta riƙa kwana ba, idan ta gama aikinta za ta koma gida gobe ta dawo..."
Cike da mamaki Hajiyar ta ce.
"Miyasa? Gidansu bai da nisa ne da nan?"
"No! Daga ita sai mahaifiyarta sai ƙaninta suke zaune, mahaifinta ya rasu and tana jinyar Maman ne, kinga she need to be around to take care of her."
"Allah sarki! Allah ya bata lafiya."
"Amin yah Allah. Na gode Hajiya..." Daga haka ta girgiza kanta ta ce "Hmm! Hajiya Marwa bata da hankali, ta manta hanyoyin Allah yawa ne da su..."
Sai yanzu Ziza ta tsomo baki tana girgiza kai ta ce.
"Aunty Labiba I hate that woman to the extent...there is a day da naje gidan ku na tarar za ta fita muka yi karo a harabar gidan, sai na gaishe ta amma wallahi haka ta mini as if bata taɓa sanin daga ina na fito ba... That thing pain me, Kamar in kifa mata mari haka na ji."
Dariya Labiba ta yi sannan ta ce.
" Abeg don't mind her. Kawai Don kina baƙuwa ne baki santa ba, amma haka take kuma komai za ki yi mata ba za ta canja ba. Su Nadeeyah har sun riga sun saba da hakan, duk lokacin da ta shigo garin nan taje gidana har ɓangarenta take shiga ta gaidata, so! ki ci gaba da gaishe da ita idan kin ganta ko da ba ta amsa ba wannan ya rage na ta."
" Ni ko wallahi Aunty Labiba ba zan iya ba gaskiya."
Dariya ta yi mata sannan ta ce.
" To ba matsala Ziza, dake da Hairiyyah hali ɗaya gare ku na rashin haƙuri. Allah ya sauke mana ke lafiya."
Rausayar da kanta ta yi gefe tana faɗin.
"Amin.... Hajiya a kira yaran nan su zo su kwashe abincin nan wallahi na ji kuma ba na son komai a ciki."
Jinjina kai Hajiya ta yi ta ce.
"To ya yi, bari na kirasu su kwashe."
Kallonta Labiba ta sake ta ce.
"Yaushe Emraan ɗin zai koma?"
"While! Na ji dai yana cewa gobe, amma ni gaskiya ko bai tashi komawa ba a nan zan ci gaba da zamana."
"Haka ne kuma, to nasan ko ya zauna ma ba zai wuce ya ƙara kwana biyu ba saboda haka ki yi zamanki a nan kawai idan dai har ya yi miki."
"Abin da nace mata kenan, tun da dole tana da buƙatar wani a kusa da ita...."
Cewar Hajiya tana mai danna kiran Haula.
****
Ni kuwa, haka muka yi ta ratsa katafaren gidan, ɗaki-ɗaki tare da su biyun suna nuna mini wuraren aikin nawa.
Daga nan muka fito ta wata babbar ƙofar baya inda wata doguwar verandar mai ɗauke da ɗakuna uku suke, wanda a gefen dama ne babban madafar abincin su yake. Ɗaya daga cikin ɗakunan muka shiga. babban ɗaki ne mai kyau wanda ke ɗauke da madaidaitan kayan buƙatar rayuwa, domin manyan katifu ne guda biyu waɗanda wasu ke kira sauko mu gaisa, an lailaye su da zannuwan gado masu kyau tare da filallukansu. Sai babban madubi mai ɗauke da kayayyakin kwaliya da shafe-shafe. Ga wata wardrobe mai murfi uku a gefe,wacce akwai akwatuna a sama, ga kuma wani rack in da aka zube takalmi kala da kala. Ga Fan, ga Ac ga kuma haske fal ko'ina gwanin sha'awa.
Maganar da Haula ta fara ita ce ta janyo hankilana daga kalle-kallen da na shiga yi ta ce.
"Ni sunana Haula, aikina shi ne dafa abinci, ni ce in charge na girke-girken gidannan gaba ɗaya wanda mu biyar ne a kitchen ɗin da muke aiki a tare."
Jinjina kaina na yi alamar cewa na fahimta sannan ɗayar kuma ta ce mini.
"Ni kuma sunana Munira, aikina shi ne share-share da goge-goge na iya cikin gidan Hajiya kawai..... Nan da kike gani kuma; shi ne ɗakinmu mu kusan biyar, amma ukun sun yi aure saura mu biyu a nan, akwai sauran ɗakuna biyu da masu aiki Mata suke ciki a nan gefenmu. Sannan akwai gefen maza can nesa damu ta gefen Upstairs ɗin can. Saboda haka kema za ki iya zama a nan tare damu."
Jinjina kaina na yi ina mai yi musu murmushi na ce.
" Ni kuma sunana Beenafah, ni ma dai kunji aikin da aka ɗauke ni na share-share. Sai dai kuma; ni ba a nan zan riƙa kwana ba, kullum zan zo in yi aiki, idan na kambala in koma gida."
"Eh to, ba damuwa idan kin zo sai ki sauka a nan ɗin kawai kafin ki gama aikin ki."
"To na gode muku sosai. Allah ya saka da alheri ya bamu haƙurin zama."
"Amin.. Muje, daman ban gama aikin ba. Tun jiya gidan da baƙi yau ma kuma Hajiya sai baƙin take kamar ana turo su. Amma tunda kinzo na san yanzu zan ɗan samu sauƙi."
Cewar Munira tana mai yin gaba, wucewa na yi na bi ta muka shiga yin aikin a tare. Kullum kamar dai ko yaushe, wuri ko bashi da dattin komai dole za'a share a goge. Haka muka yi ta darzaza aiki har kusan sha biyu saura sannan muka kambala.
Bayan mun kambala Munira tace in zo mu tafi kitchen wurin Haula. Nan muka same su ana ta dafa abinci wanda ni wallahi duk a zatona tun farkon zuwana gidan har zuwa yanzu na za ta wani biki ake yi. Barin ma ma'aikatan masu dafa abinci ga su nan birjik! Har da tsofaffi a ciki.
Gasu nan dai sai hada-hada suke suna yi suna fira abinsu hankali kwance, wanda ni ina gefe kawai na zuba ido ina kallon su.
Misalin ƙarfe biyu saura, Haula ta ce mu tashi muje mu yi sallah wanda shi ne abin da ya ƙara burgeni da su. A toilet ɗin cikin ɗakin mukayo alwala muka zo mukayi sallah, bayan mun yi sallar suka zauna suna ta fira suna dare-dare yayinda na dawo 'ƴar kallo a cikin su. Ganin firar ta su ba mai ƙarewa ba ce yasa na ce musu ni dai zan tafi.
Kallona Munira tayi ta ce.