Ganin ido complete Novel - Chapter 15
Ganin ido complete Novel Chapter 15: Ganin ido complete Novel Chapter 15. "Tun yanzu? Iya ka ƙarfe biyu da wani abu fa, ki bari mu ƙara fira mana. Idan mun…
3,351 words
"Tun yanzu? Iya ka ƙarfe biyu da wani abu fa, ki bari mu ƙara fira mana. Idan mun ci abinci sai ki tafi."
Miƙewa na yi ina girgiza kaina na ce.
"Bari dai in tafi ai gobe zan dawo."
"To shikenan, sai gobe. Akwai hanya ta nan ɓangaren kitchen sai ki bita."
Cike da ɗan fargaba na kalle su na ce.
"Dan Allah ko za ku ɗan rakani zuwa gate."
Miƙewa Haula ta yi tana ninke hijabinta ta ce.
"Sai dai Munira ta rakaki, ni yanzu zan je ne na shirya abinci a ciki. Nasan Aunty Ziza tana can tana baza ido kuma yanzu In Sha Allahu har akai abincin nan a ɗauke shi ba za ta ci wani abin kirki ba."
Gyaɗa kai Munira ta yi ta ce.
"Ko abincin ɗazun haka akayi. Tun suna asibiti Yaa Emraan ya kira Hajiya yace a kawowa Aunty Ziza abinci amma haka aka kwaso ba ta taɓa komai ba."
Nidai tsaye nake na yi shiru ina jiran wacce za ta rakani.
Kallona ta yi ba tare da cire Hijab ɗinta ba ta ce.
" Mu tafi."
Ta gefen Kitchen ɗin muka fito ta rakoni har gate ɗin farko,nan na yi ta rarraba ido ko zan ga motar Aunty Labiba, sai dai kuma ba motar da alama ta wuce kenan. Ma su gadin da ke zaune a ƙarƙashin bishiyar ƙofar gidan waɗanda ke sanye da kaki ta kalla ta ce.
"Ina wunin ku?"
A tare suka amsa sannan ta ce.
"Wannan sunan ta Beenafah, ita ma'aikaciyar Hajiya ce yau ta fara aiki, kullum za ta riƙa zuwa tana komawa."
"Ok! She's welcome."
Murmushi ta yi mini tare da ɗaga mini hannu ta ce.
"To, sai an jima ko?"
Nima hannun na ɗaga mata na ce.
"Yau wa, sai anjima na gode."
Titin na miƙo a hankali har na samu mai Mashin na tare shi na faɗa mishi sunan unguwarmu. Bayan mun shirya na tambaye shi dan Allah idan akwai hanya mai sauƙi da zan iya bi daga nan zuwa gida ƙasa ya bi dani, domin na riƙa zuwa da ƙafa. Haka kuwa ɗan albarkar mai Mashin ɗin nan ya yi ta bi dani hanya nan take sai gamu wurin corner ɗin gidanmu duk da akwai nisa amma ba sosai can-can ba.
Yana ajiye ni na shige gida cike da farin ciki ina mai yi wa Ammie albishir na sabon aikinda na samu.
Murmushi Ammie ta yi ta ce.
"Wannan irin farin ciki haka Beenafah? Masha Allah an yi nasara kenan?"
"An yi Nasara Ammie...sun ɗaukeni daga yau na koma bakin aikina."
Cike da jindaɗi Ammie ta ce.
"To Alhamdulillah! Ina roƙon Allah ubangiji ya tsare ki da tsarewarsa ya kuma bada sa'a. Yanda kiketa ɗawainiya a kaina Beenafah Allah ya bani ikon hidimta miki nima. Allah kada ya jarabceni da ƙuntata miki koda na second ɗaya ne matuƙar ba hanya kika kauce ba. Allah ya yi muku albarka. Allah ya shiryar mini da ku ya ƙara muku tausayin junan ku."
" Amin Ammienmu.... Akwai sauran abinci?"
" Eh, akwai. Amma dai gashi can saura ne a tukunya,ki na gama cinyewa ki ɗora mana wani kada auta ya dawo ba abinci..."
"Kai Ammie dan Allah! Ba komai, nima ai makarantar zan shiga watarana...."
Na iyarda maganar ina mai nufar inda tukunyar take.
"Eh fa! Tun safe yana can yana ta karatu har yamma, to ba zan yarda ya dawo ba abinci ba."
Ina zaune ni da Bahrain After Isha prayer ina taya shi homework sai ga su Ya Jafaru sun shigo, wanda duk dare idan suka dawo kafin su shiga gida sai sun shigo mun yi fira sannan suke wucewa gidan su. Bayan mun gaisa ya Jafaru ya kalleni ya ce.
"Kinje gidan?"
Gyaɗa kaina na yi na ce.
"Sosai, na je."
"To ya suke?"
"Kamar dai yanda halin 'ƴar yake, su ma haka. Suna da kirki."
"Alhamdulillah! Na ji daɗin jin hakan. Allah ya taimaka yasa kin shiga a sa'a."
"Amin. Yah Allah, na gode."
Washe gari koda na tashi sai na shiga tunani akan na yi wauta, domin ya kamata ace na tambayesu lokacinda suke buƙatar zuwana. Hakan yasa Ammie tace na shirya ƙarfe sha ɗaya na tafi, idan yaso daga yau sai na tambayesu lokacin da suke buƙata ta. Ina fitowa Ya Jafaru na fitowa shima daga gida.
"Sai ina haka?"
Hanyar na kama ina faɗin.
"sabon gidan aikina mana."
"A ƙafa za ki?"
Gyaɗa masa kaina na yi tare da faɗin.
"Eh to, da ace na san hanyar da a ƙafa zanje, amma kuma nasan ba zan gane ba sai dai in bari a ƙara kwana biyu."
"Ta ina ne gidan?"
"Uhm!....Can ne cikin G.R.A wurin gidan Yarima..."
"To muje mana.... ina nufin mu taka da ƙafa nasan inda za mu bi yanda zai fi miki sauƙin ganewa."
"Wallahi short cut ɗin sunyi lungu da yawa..."
"sai in yi ta rakaki har ki gane."
Murmushi na yi cikin jindaɗi na ce.
"Ai ko na gode, Allah ya biya."
Tafiye muke muna fira sai gashi ba jimawa mun isa ƙofar gidan. A bakin gate ɗin ya tsaya ya kalleni ya ce.
"Ki kula kin ji ko?"
"In sha Allahu Ya Jafaru, na gode sosai...."
"Da ƙarfe nawa zan dawo?"
"Ummm! To ka dawo zuwa ƙarfe biyu haka."
" shi ke nan, Allah ya kaimu."
Gaishe da masu gadinda ke zaune na yi suka amsa sannan na saka kai na shige ciki. A gate na biyu kuwa, ina tura ƙaramar ƙofar sai ga wani murtuƙaƙƙen Soja ya ta so wanda babu alamun rahama a fuskar sa ya kalleni ya ce.
"Who are you?"
Zaro ido na yi hankali tashe, tuni baki na ya fara rawa domin ban san ma mi zan ce masa ba.
"I said, wacece ke?"
Ƙasa na yi da idona na ce.
"Jiya aka ɗaukeni a aiki.."
"And??"
Mai motar da ya zo ya tsaya shi ne wanda ya ceceni daga hannun dodon da ya tsareni a wannan lokacin, duk da cewa ban san sunan shi ba amma kuma na shaida shi, shi ne wannan na jiya mijin wannan matar da muka iske ni da Aunty Labiba da wani kalar kaki a jikin shi wanda ban san ko na miye ba. Ko yau ma sai da na gaishe shi amma kuma ban ji ya amsa ba kamar dai jiya,sojan kawai ya kira can kusa da shi ya yi mi shi magana wanda ban san mi yace mishi ba, ni dai kawai na ji ya ce mini in wuce.
Tsaye na yi ina nazarin kuma ta ina zan shiga, shin ta ƙofar baya ta jiya ko kuma ta inda muka shiga da Aunty Labiba.
Wasu maza na gani guda biyu sun gifto ɗauke da wasu kayayyaki a hannunsa suna tafe suna magana.
Ganin yanda nake ta rarraba ido yasa ɗaya daga cikin su ya ce mini.
"Malama ya dai?"
Gidan na nuna ina faɗin.
"Nan gidan zan shiga."
Ƙara kallona ya yi daga sama har ƙasa sannan ya ce.
"Zo ki bi ga hanya nan."
Zagawa na yi ta bayan su na wuce ciki. Bakin Kitchen na tarar da su da ƙatuwar MP suna ta shan waƙa suna ta dare-dare hankalin su kwance.
Cike da murna suka tarbeni tamkar sunyi shekaru da sanina musamman Haula da Munira.
Bayan na samu wuri na zauna Munira ta kalleni ta ce.
"Keee! Ai ko mun manta yau dutyn Tayo ne wallahi, ya akayi ya barki kika shigo? Ko ya kira Hajiya ne a waya?"
Jinjina kai na yi na ce.
"Ai kuwa dai ƙila shi ne kam ya tsareni,har ya fara yi mini tambayayo sai ga mutumin nan na jiya ya zo da mota..."
"Ya Emraan ko? Naga ɗazu Haula ta kai mi shi break fast, kamar Kaduna zai koma wurin aikin sa....Ta shi kije ki gaida Hajiya ki dawo."
Miƙewa na yi ina faɗin.
"Ɗan rakani mana.."
Dariya Haula ta yi ta ce.
"Naga sai wani ɗari-ɗari kike Beenafah. Ki saki jikinki gidannan bamu da wata damuwa. Ga ƙofa can je ki shiga, tana nan parlour in dai ba yanzu ta tashi ba."
A hankali na taka steps ɗin na tura babbar ƙofar na shiga har parlourn inda na tarar da ita zaune ita kaɗai taci uban gayu cikin dakakken leshi wanda ya jiƙe sosai da ruwan kuɗi sanye da farin glasses a idanunta sai baza uban ƙamshi take mai daɗin gaske tana zaune a dining table tana cin Abinci. Duƙawa na yi cike da girmamawa na ce.
" Mama Ina kwana?"
Ajiye spoon ɗin hannunta ta yi ta ce.
"Ya ma sunan ki?"
"Beenafah."
"Beenafah. Kin tashi lafiya? Ya jikin Maman ki?"
Cike da mamaki na ce.
"Alhamdulillah. Mai jiki da sauƙi sosai."
Daga haka na miƙe na juyo da nufin fitowa sai ta sake kiran sunana na waigo ina mai amsa ta.
"Ungo Maganin nan ki kaiwa Ziza please, yanzu sai za ta ce ta neme shi ta rasa alhali na gano ta bata son shan magani."
Hannu biyu na saka na karɓa ina faɗin.
"A ina ne?"
Wata ƙofar ta nuna mini a hankali na taka naje na yi nocking, banji an amsa ba hakan yasa na tura kaɗan ina mai tura kaina ciki.
Cikin rashin sa'a ko mukayi ido biyu da ita tana zaune a ƙasa tayi rashe-rashe da plate a gabanta cike da slize fruit.
" Lafiya?"
Ta tambayeni tana mai tsatstsareni da ido wanda har sai da naji wani tsoro ya kamani.
"Ma..Magani Mama tace na kawo miki."
"Mama! Wace ce Mama?"
Kallonta na yi na ce.
"Hajiya!"
"OK to, Hajiya za ki ce ba Mama ba, zo ki ajiye min a nan na gode."
A hankali na tako na zo inda tace na ajiye mata na juya da nufin ficewa na ji tana faɗin.
"Call Munira for me please.."
Waigowa na yi na ce.
"Na'am."
"Cewa na yi ki kira mini Munira, tun ɗazu na ce mata zan aike ta kuma bata dawo ba... Ko kuma ungu keys...."
Ta jefo mini tana faɗin.
"Ki ce taje ta ɗauko mini kayan da nace mata a gida. Sannan akwai wa su Keys a bedside drawer na ɗakin Sama ta ɗauko ta rufe mini part ɗin Emraan ta kawo mini Keys gaba ɗaya"
Ɗauka na yi ina faɗin to sannan na fito na zo na tarar da su na bata sannan na yi mata bayani.
Ɗaki ta shige ta ɗauko hijabi tana faɗin muje ki rakani. Kallonta na yi nace.
"Ban yi aikina ba fa Munira.."
Dariya ta yi mini ta ce.
"Aiki kam na gama sai dai na gobe idan Allah ya kai mana rai. Ki riƙa zuwa Ƙarfe shida da rabi...Ina nufin zuwa dai bakwai na safe kin iso, Hajiya bata son ma sha ɗaya tayi ba'a gama gyara mata gida ba sai dai idan akwai wani ƙwaƙwƙwaran dalili..."
Ina jinjina kaina alamar gamsuwa na ce.
"To in sha Allahu gobe da wuri zan fito, ai na za ta bata son sammako."
Kallona ta yi ta ce.
"Muje mana.."
Girgiza kaina na yi ina murmushi na ce.
"A'a, kije ki daw..."
Hannuna taja da ƙarfi muka yi gaba tana faɗin.
"Wallahi sai kin rakani to kuma kin ji na rantse."
Dole bani da bakin magana haka na yi shiru na bita sai gamu a harabar parking lot tana ƙwala kiran wani wai shi Nuhu.
Muna nan a tsaye sai ga shi yazo ya kalle mu ya ce.
"Ya akayi Munira?"
"Gidan Aunty Ziza za ka kaimu mu ɗauko mata kaya."
"OK."
Juyawa ya yi yaje ya janyo wata mota a hankali yazo ya tsaya a gabanmu ta buɗe muka shiga.
Tafiya muke a hankali tana mini fira da cewa.
"Aunty Ziza kenan, shekara ɗaya yanzu da aurenta ita da Yaa Emraan, er Kebbi State ce amma dai an ce wai ba'a nan ta girma ba, a can kudu ne wurin wan babanta, amma kuma tana da matuƙar kirki da sauƙin kai..."
Ni dai kawai ina sauraren ta ne ba tare da na amsa ba mata ba. Sai da muka yi tafiya mai nisa sosai sai gamu wata unguwa wacce Munira ta ce mini wai sunanta Tudun wada.
Wajen wani katafaren gida ya yi parking tare da danna horn, jim kaɗan sai ga wani ya zo ya buɗe, yana ganin Munira da drivernsu ya koma ya buɗe gate muka shiga.
Masha Allah, gidan ya haɗu iya haɗuwa. Muna shiga babban parlourn gidan, tace in zo mu haura sama na ce mata a'a taje dai ta fito ina jiranta.
Ina nan zaune ina ta bai wa idona abinci har ta kambala mata uzurinta sannan ta fito muka koma gida. Muna shiga sai gata ta fito cikin shiri da alama itama fita za ta yi.
Kallona ta yi ina mai ɗauke da kayan ta sai kuma ta kalli Munira ta ce.
"Tare kuka je?"
Cikin ɗan shakku Munira ta gyaɗa kanta ta ce.
"Eh..."
"To waye ya ce kije da ita? Da zuwan yarinya jiya-jiya sai ki ɗauke ta ki kai mini gidana, kin san halin ta ne?"
Shiru muka yi dukkanmu jin yanda take faɗa kamar wacce akace na aikata mata wani zunubi. Sai dai kuma ni, ko a silifas ɗina ban kawo ta ba, domin wani gefen tana da gaskiya, baƙuwa dani bai cancanci ace na shiga gidanta bada izini ba. Sai da ta dasa Aya sannan Munira ta ce.
"Ki yi haƙuri Aunty Ziza ba za'a koma ba..."
Anshe Keys ɗinta ta yi tana mai wani buga uban tsaki ta taka ta yi wurin inda motar ta take ajiye ta kira drivern Hajiya ya zo suka fita.
Hannuna Munira taja tana mai buga tsaki ta ce.
"Muje dan Allah, kin san zuciyar mai ciki a wuya take, Sai ka ce wani gidan ƙwarai."
Ni dai shiru kawai na yi bance komai ba har muka shige ɗaki muka zauna.
Abinci na tarar an jere da yawa a ƙasan ɗakin. Kallona Haula ta yi ta ce.
" Sai yanzu? Ku zo muci abinci please ni ina jin yunwa.. "
Da mamaki a fuskata na ce.
" Abinci? Tun yanzu kuke cin abinci rana?"
"A'a. Wallahi fa abincin safe ne wai, sai yanzu za mu karya in faɗa miki."
Lafiyayyen breakfast ne kamar wanda na gani a parlourn Hajiya, a raina na ce lallai kuna jin daɗinku kuna sha'aninku.
Duk yanda na so zamewa dole sai da suka matsa mini muka ci. Daga nan suka yi ta fira ni kuma ina kwance ina sauraren su. Haka dai na yi wunin ranar a gantale ba wani aikinda na yi taƙamaime har ƙarfe biyu na rana. Ina shirin tafiya gida Haula taje da kanta ta zubo mini abinci da ma sauran abincin karin safe da yawa ta bani tana faɗin.
"Jiya Aunty Labiba ta kiramu da dare tace an baki abinci da za ki wuce muka ce a'a, shi ne ta yi faɗa. Kuma mantawa dai akayi domin kullum abinci sai dai ayi ta shanyawa a rana ana yin ƙanzo, ki yi haƙuri."
"Haba ba komai, Na gode sai gobenku."
Ko yau ma sai da suka sake rakani har ƙofar gidan sannan suka koma. A nan na tarar Yaa Jafaru na jirana wanda ni wallahi kwata-kwata na manta da shi. A tare muka sake takawa har gida.
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *ArewaPen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 18*
Washe gari kam da wuri na fito tun Bakwai saura wanda nasan a lokacin ma Ya Jafaru bai isa fitowa ba.
Koda na isa gidan iyaka bakwai da mintota,kuma ina zuwa kowane gate aka barni na shige ba tare da wata damuwa ba. Daga Haula sai wata tsohuwa kawai na tarar a bakin Kitchen ɗin suna fere doya da Irish potato a lokaci ɗaya.
Bayan mun gaisa Haula ta kalleni da murmushinta tana mai nuna mini tsohuwar da take gefen ta ce.
"Wannan ita ce Inna Kuluwa, idan ana zancen gargiya to itace a samana, idan kuma ana zancen abincin zamani to ni ce nan a sama.."
Maganar ta ta dariya ta bani wanda har ban san lokacin da na dara ba sannan na ce.
"Allah sarki. Allah ya ƙara basira."
"Amin. Kije ciki Munira na can."
Yau kam tare muka yi komai ni da ita wanda ko da goma ta buga da mintuna mun kambala komai wanda gidan babu abinda yake idan ba tashin ƙamshi ba. Wa su manyan kwalabe ne Munira ta ɗauko wanda babu komai a ciki sai turaruka masu mashahurin ƙamshi da daɗaɗa rai wanda ko alama ba su yi kala da na yankinmu ba, bayan an gama kunna na burner ta ɗauko air fresheners Wanda su ma ɗin da ga jin yanda suke ƙamshi kasan cewa na musamman ne.
Bayan mun kambala muka dawo bakin kitchen muka zauna inda a nan ne Haula ta ɗora mini dubu ɗaya a jikina tana faɗin.
"Ga kuɗin satin ki nan.."
Cike da mamaki na jimƙe kuɗin a hannuna sannan na ce.
"Kuɗin Satina kuma?"
"Eh, duk ranar kasuwa, yau Monday kenan ana bamu dubu ɗaya na cin kasuwa daga Yaya."
Jinjina kaina na yi na ce.
"Allah sarki! Mun gode sosai Allah ya saka da alheri ya ƙara buɗi na alheri."
"Amin. Na san yanzu Hajiya ta fito, kije ki gaisheda ita."
"Tau, in sha Allahu yanzu kuwa."
Miƙewa na yi kamar dai jiya na je na gaishe ta na dawo muka zauna muka ci abincin kari mai rai da motsi wanda ban an kare ba sai wani alamun bacci-bacci da naji yana neman ya sace ni. A hankali na ɗan gincira yayin da su kuma suka ci gaba da aikin surutun na su kamar yanda suka saba.
Ina nan bacci ya fara figata na ji Munira na tashina cewa wai na tashi mu shiga Kitchen, Aunty Ziza tace Haula ta yi mata Cake yanzu ta kai mata da zafin shi take so ta ci.
Tunani na fara ina za'a yi Cake ɗin tunda Hajjo tana yi a gidan Aunty Labiba ina gani, da kayan wuta ake yin sa, to su kuma naga na su kitchen ɗin na itace ce da manyan Murahu waɗanda da su suke girki. Sai dai kuma, tunanina ne ya yanke ganin mun shiga cikin gidan inda suka ja ni wani katafaren Kitchen wanda yake zaman ɗaki biyu na wata macen ta saboda girma da kuma faɗinsa. Ido, baki, hanci, su na buɗe a lokaci ɗaya ina kallon Aljannar Duniya 'Ya salam!' Wannan kitchen ɗin ya ƙawatu sosai da kayayyakin zamani kala da kala. A hankali Idona ya fara sauka akan double door Samsung smart fridge mai touch screen display Wanda ke nuna time, weather da Kuma recipe tips. A gefen fridge ɗin kuma, akwai built in microwave da Kuma Oven da aka saka cikin bangon kitchen ɗin. Sai kuma Six burner electric cooker Mai digital heat control da Kuma smoke extractor. A saman Cooker ɗin akwai hanging rack da ke Cike da shining copper pots and pans an jejjeresu Kamar wasu kayan kwalliya.
A jikin faffaɗan windown Kitchen kuwa, sink ne mai automatic sensor tap. A gefe Kuma, akwai dishwasher, da cabinet drawers masu soft close system.
Komai a kitchen ɗin nan is beautiful. Wani store dake ta ciki Haula ta shiga ta ɗauko dukkan kayan buƙata sannan ta fito ba ɓata lokaci muka hau aiki wanda muna yi suna ta faman surutunsu da suka saba, ni dai kawai ina taya su aikin ina sauraren su har muka kambala.
Bayan ta gama tsara shi a cikin wani haɗaɗɗen bowl na tangaran kawai sai ta miƙo mini tana faɗin.
"Ungo Beenafah, dan Allah ki miƙa mata,nasan tana can tana ta aikin jira, ni zan iyarda haɗa mata Mango juice ɗinne sai na kawo mata."
Kallon Munira na yi wacce ta duƙufa sosai wurin gyara wurin da muka yi aikin wanda hakan yasa dole dai ni ɗin zan je na kai mata ko bana so. Ban san abinda yasa ba, tun abinda tayi mini jiya yasa na ji a raina cewa ina shakkarta.
A parlourn da na fara tarar da ita farkon zuwana gidan a nan na tarar da ita tare da wasu mata guda biyu, en gayu ne suma kamar ita, suna zaune suna fira a hankali ba tare da hayaniya ba.