Kenza eBookz

Ganin ido complete Novel - Chapter 35

Ganin ido complete Novel - Chapter 35

Ganin ido complete Novel Chapter 35: Ganin ido complete Novel Chapter 35. Lallai sai yanzu na tabbatar na kuma fahimci abin da Dr. Basheer yake nufi da ya…

3,362 words

Lallai sai yanzu na tabbatar na kuma fahimci abin da Dr. Basheer yake nufi da ya ce ya kamata nima inji cewar ni ɗin amarya ce wanda a cikin kwanakin nan na fahimci hakan. Wani irin abu nake ji na musamman a cikin raina especially ranar yau da aka taru gidan namu ana ta hidima. An yi mini lalle wanda ya kwanta ya yi luf a fatar jikina ya yi kyau musamman da aka yi mini wannan gyaran jikin sai ya ƙara fitowa dani shar-shar kamar ka sace ka gudu. Ina zaune bayan na gama wanka tare da wasu mata guda biyu da Mummy Sameera ta kawo da Fakiha ana shirya mini Ammie ta shigo da wayar Abbu ta ce mini wai ga Aunty Labiba ta na son Magana da ni. Wata irin dokawa ƙirjina ya yi wanda ban san dalili ba. A darare na kai wayar saitin kunnena ɗauke da siririyar sallama a bakina.

Sautin murmushin ta na ji daga can ɓangarenta tana faɗin.

"Amarya er shagali.."

"Uhm! Ina wuni Aunty Labiba?"

"Lafiya lau alhamdllh Amarya ya niyya?"

"Uhm!"

Abin da na ce kenan tare da ƙara saukar da idona ina wasa da yatsun hannuna. Muryar Hairi na ji ta warce wayar tana faɗin.

"Allah sarki Amaryar Yaa Mohaa na...muna hanya gobe In Sha Allahu, hours kaɗan ne suka rage gobe tayi. Allah yasa albarka....Ga Aunty Nadee itama.."

"Hallo Amarya....ki ji daɗinki kinji! Allah ya tsare mana ke ya kare ki daga dukkan sharri...Ga ƙanwar ki Ziza tana gaishe dake"

Har suka gama surutunsu komai bance musu ba wanda daga ƙarshe da suka gaji suka yanke wayar don kansu.

Muna gama wayar sai ga Mummy Sameera ta shigo da fara'arta tace.

" Beenafah! Kin ganni yau sai yanzu ko? Wallahi baƙuwa na yi tun Jiya matar ƙanin mijina ce ta zo,to yau ina ta so in fito Allah bai nufa ba sai yanzu. Kuma ban iya fitowa in baro ta gashi ta kafe wai ba za ta zo ba sai da na janyo ta da ƙarfi..."

Janyewar da tayi da nufin ta zauna ne kwatsam idanuna suka sauka akan Aunty Aysha ta.

Cike da jin wani irin faɗuwar gaba na kalle ta na ce.

" Aunty Aysha!!!"

Itama a mamakance ta kalle ni ta ce.

" Murya da fuskar kamar na Beenaf..."

Wani irin kukan Kura na yi tare da buga tsalle na ɗane mata wuya a ruɗe na ce.

"Aunty Ayshahhh! Oyoyo Aunty Aysha..."

Breaking hug ɗin na yi ina mai yi mata wani kallon mai cike da kewa na cewa.

"Aunty Aysha daman ashe za ki zo buki na??"

Hannu ta saka tare da sake ƙanƙameni a jikinta ta fashe da wani kukan al'ajabi da mamaki tana faɗin.

"Allah mai iko da buwaya! Beenafah kece yau Allah ya haɗani dake ba za to ba tsammani! Wallahi ko kaɗan ban kawo a raina wai cewa zan ganki nan kusa ba...Alhamdulillah ya Allah Alhamdulillah!"

Hannunta na ja da sauri muka fi ce ban tsaya a ko'ina ba sai tsakiyar ɗakin Ammie inda na tarar da ita tare da Mama Asma'u da Maman su Fakiha... Wani irin freezing ta yi ganina tare da Aunty Aysha a lokacin da ba ta tsammata ba.

Jikin Aunty Aysha na wani ɓari ta zo da gudu ta rungume Ammie tare da fashewa da sabon kuka tana faɗin.

"Please forgive me.... Forgive me Ammie...na yi iya yina in ga cewar na tsamar dake daga cikin halin da kike ciki... But I fail!!..."

Wani irin ture ta Ammie ta yi da ƙarfi tana faɗin.

"Wane ne ya kawo ku inda nake? Na samu farin ciki da kwanciyar hankali miye abin da ya sake dawo da ku a cikin rayuwarmu...wane ne na ce miki ya kawo ki nan???"

Ta ƙarashe maganar cike da ƙaraji da wani sabon tashin hankali.

Faɗuwa ta yi akan gwiwoyinta ta kalli Ammien tana jinjina kanta ta ce.

" Allah ne! Allah shi ne wanda ya kawo ni gare ki Ammie...ban san zan haɗu dake ba wallahi tallahi ban san zan haɗu dake ba..."

Mummy Sameera dake tsaye jiki a sanyaye ta ce.

"Aunty Mulaifa ki yi hak'uri. Duk da cewa ban san abin da yake tsakaninku ba; ni ce nan na zo tare da ita. Amma wallahi tallahi ba mu yi wata magana da ta dangance ku ba. Hasalima ba ta yi niyyan zuwa ba ni ce nan na tursasa mata. Ita ɗin matar Ahlan ce ƙanin Mijina, jiya ta iso daga Gusau idan ta kwana biyu za ta koma London, na yi na yi ta zo mu tafi tace mini naje kawai bata da buƙatar zuwa ko'ina. Bata yi niyya ba ko kaɗan ni ce na tilasta mata na ce mata yau ake wunin bukin ɗiyar Yayana saboda haka sai ta zo. Kin ji dalilin zuwan ta nan.... "

Jinjina kai Ammie ta yi ta ce.

" To na ji, amma duk da haka ta tashi ta fice... "

Ƙafarta Aysha ta kama tana wani irin kuka tana faɗin.

" Ki gafarceni Ammie...ki tuna fa kece kike faɗa mini cewa ke ɗin mahaifiyata ce....wallahi tallahi babu ni a cikin duk abin da ya faru...ƙarshe da na dage akan lallai sai na ɗaukeki...furucin tsinuwa ta yi mini tare da cewa idan ban yi nisa da su ba ko lahira bata fata da burin haɗa fuska da ni.... Yanxu ma na zo ne bukin su Hassy amma hakan bai yiyu ba akan wani dalili da ya taso marar daɗi. Hakan yasa na baro su cikin baƙin ciki zan koma London. Babu wata rana da za ta zo ta wuce ba tare da na tuna daku ba Ammie... A ina kuke? Mi kuka ci? Wace rayuwa kuke yi? Waɗannan su ne tambayoyin da na kasa daina yi wa kaina har ila yau da kike tsaye a gabana..."

A hankali ta saka hannayenta ta ɗago kafaɗarta ta rungumeta a hankali tana hawaye sannan daga ƙarshe ta janye tana faɗin.

" Mahaƙurci mawadaci Aysha! Allah ya musanya mana da mafificin alheri. Na sake wani auren na auri yayan Sameera, Beenafah kuma ita na aurar da ita gobe za'a kai ta ɗakin Mijinta."

Jinjina kanta tayi cike da farin ciki ta ce.

"Alhamdulillah! Na ji daɗin jin hakan. Allah ya sanya alheri da albarka. Tunda na karanta wasiƙarki da kika aikawa Daddy tun ranar nake cikin farin cikin. Allah ya nufa da ni za'a kai Beenafah ɗakin Mijinta. Allah sarki rayuwa!"

Nan maganar wunin buki ta shashace inda aka barmu daga ni sai ita sai Ammie da kuma Bahrain har kusan magariba sannan muka fito, a lokacin har mutane sun shiga watsewa ba tare da ganin Amarya ba.

A daren ranar ma tare muka kwana ɗakin Ammie muna ta firarraki har gari ya waye bamu runtsa ba.

Washegari, da wuri aka shiga shirye-shirye wanda Su Aunty Ayshar ne a gidan gaba yayinda duk na bi na yi wani iri kamar bani ba tsabar fargaba.

Ina cikin ɗaki misalin sha biyu na rana bayan an gama shirya mini cikin wani lace na alfarma, ga make up ta ji raɗau na fito fes dani wai ni Amarya. Aunty Aysha ce ta zo ta ja hannuna tana faɗin in zo ga dangin mijina na nan sun iso.

Tun da muka nufo ta parlourn naji ƙirjina na wani yin sama ƙasa tamkar numfashina zai ɗauke tsabar yanda nake neman diriricewa.

"Kwantar da hankalinki mana ki nutsu Beenafah..."

"La'ilaha Illa Anta Subhanaka Inniy Kuntu Minazlimin!!"

Addu'ar da na shiga maimaitawa kenan. Yayin da na ke ta jin ƙarar guɗa da surutai sosai yana tashi.

Ana ajiyeni a tsakiyar parlourn na ƙara jin wata irin sabuwar guɗar a saman kaina tamkar na tashi na ruga da gudu tsabar yanda na tsorata.

A hankali Aunty Labiba ta sauko daga kan kujera ta zauna a gabana tare da kai hannuwanta ta ya ye veil ɗinda yake saman kaina kaɗan ta ce.

"Barakallah Masha Allah da Amaryarmu NANA!"

Kaina da yake sunkuye a ƙasa da kuma uwar make-up ɗinda nasha ne yasa gabaɗayansu babu wanda ya ganeni.

Manyan hamƙashan mata ne su biyar tare da su Hairiyya. Duk girman parlourn nan sai da ya tumbatse da kayan see I love, kayan sa rana, kayan akwatuna da wasu kayayyakin gift ɗinda suka bai wa Su Hajiya Asma'u mamaki. Haƙiƙa babu irin kalar kayan amaryar da ba su gani ba, amma kam waɗannan kayan sun zarce tunaninsu matuƙa.

Kowa a parlourn sai fatan alheri yake, murna a wurin su Nadeeyah abun ba'a ma magana duk cewa akwai wani irin tsoro da ya yi gini babba a cikin ƙirazansu na cewa za'a iya fasa ɗaura auren a kowane lokaci. Muryar Ziza na ji tana faɗin.

"Allah ya sa albarka Amaryar Yaya Muhammad kuma uwar Muhammad.."

"Amin. Ai kam abun yayi daɗi wallahi Allah ya tabbatar mana da alheri."

Cewar Hairi tana mai janyo wayarta a yanda nake tana ta zuba mini hotuna. Hajiya da tayi zugudum tunɗazu ne Mummy Na'ima da suka zo tare ta kalle ta tace.

"Hajiya tun ɗazu kin zauna kin wani shige gashi...Dan Allah ki saki ranki in Sha Allahu wannan karon akwai alheri... Lafiya lau za'a ɗaura auren..."

Kafin ta iyarda rufe baki sai ga shi Mummy Sameera da Aunty Aysha sun yi hamdala suna faɗin an ɗaura aurenmu da Muhammad..

A gigice suka dinga faɗuwa suna sujjada ga Allah... Kafin ka ce mi koke-koke ya ɓarke tsakanin su Hairiyya. Da masu kukan murna da kuma masu kukan baƙin duk sun taru suna ta yi.

Hajiyarsa ma wani irin kukan farin ciki ne ya kubce mata sai gashi a hankali ta tafi luuu! Ta faɗi ta suma saboda tsabar yanda farin ciki ya cika mata zuciya.

Kanta suka yo da gudu har da su Ammie ana ta faɗin Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.

"Dole ta yi suman farin ciki... Dan Allah ku barta. Allah ne ya nuna mata wannan ranar..." Cewar wata ƙawarta da suka zo tare.

Ni dai ina nan ina ta kallon ikon Allah a can ƙasan IDO saboda tsabar mamakin da ya kamani na irin farin ciki da suke. Aunty Aysha ce ta ɗagoni ita da Aunty Labiba suka kira Ammie muka fi ce zuwa parlourn Abbu tunda har yanxu Hajiya bata da hayyacinta da kyau ba.

Fuskata a lulluɓe aka ajiyeni kusa da wani wanda ban san wanene ba. Lokaci ɗaya na ji bugun zuciyata ya ƙaru fiye da ƙima, ga wani iri ciri da jikina ya ɗauka tamkar ana kiɗa mini mazari. Bana iya hango komai nasa sanadiyyar lullube kaina da akayi da veil sai kyawawan zaratan ƙafafunsa da ya tanƙwashe a kusa da inda aka ajiye ni. Lumshe idanuwana na yi jin yanda daddaɗan ƙamshinsa ya shiga hautsina ƙwaƙwalwata.

Abbu na zaune akan kujera, sai Ammie, Mama Asma'u. Baba Uztaz, Uncle Ishaq, Aunty Aysha da kuma Aunty Labiba.

Hankalina ne ya ƙara tashi a lokacin da na ji sautin nasihar zaman aure ya fara karaɗe kunnuwa na. Jin kowa ya gama tofa albarkacin bakin sai Ammie dake magana yasa na shiga tunani. 'Yanzu ana nufin kenan mijin nawa ne ya zo da gaske? Daman zai zo ashe? Ni ɗinnan wai matar aure ce kenan? Da gaske tafiya za'a yi dani? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..'

Tamkar wacce a zulawa wata azababbiyar bulala haka na fashe da wani irin gigitaccen kuka...cikin tsananin ruɗewa ya janyoni jikin sa a gigice tare da yaye veil ɗinda yake kaina ya ce.

"Miye ya faru dake? Mine ne?? Hey! Are okay??....talk to me please!!"

Jin yanda ya wani gigice lokaci ɗaya yasa na yi saurin haɗe kukanda nake ba tare da na shirya ba. Domin a tunanina tsoro yake kada ace wani mummunan abun ne ya faru dani, alhali ba komai tsabar tsoron da ya kamani ne.

" Hey! Are you okay?"

" Yaya Mohaa remembered you people are not alone.."

Cewar Aunty Labiba muryarta a ƙasa sosai ganin yanda kowa ya yi shiru ya zuba mana IDO yana kallon mu. Jin furucin da ta yi yasa a hankali na janye da sauri tare da sake mayarda mayafina na matsa gefe sosai cike da kunya.

Muryar Abbu na ji yana faɗin.

"To ai ina ga Alhaji Ustazu mun riga mun gama faɗin duk abinda ya kamata ace mun sanar musu. Fatanmu shi ne Allah ubangiji ya bada zaman lafiya. Allah yasa ace gwanda da akayi. Allah ya kare su daga dukkan wani sharri na mutum ko aljan."

Tare muka fito da su Aunty Aysha suka sake mayar dani ciki. Ɗaki muka shige direct tare da Mummy Sameera da Aunty Aysha na sake yin wanka na wanke gabaɗaya make-up ɗin na fito suka sake shiryani cikin Atamfa da babban mayafinta muka fito...wai tashin hankalin gobarar geme.! Motoci ne aka jera sun fi goma sha biyar. Gabaɗaya an fito da duk wani abinda aka san mallakina ne an lodesu a wasu motocin. Duk da ina cikin mayafi ina Iya ganin komai yanda yake.

Rirriƙe Ammie na yi ina ta kuka ina faɗin babu inda zanje na bar Ammiena. Da ƙyar da lallashi da komai aka yi nasarar turani mota wacce daga ni sai Mama Asma'u da Maman su Fakiha, Aunty Aysha kuma a gaba tare da Yaa Emraan wanda da alama motar ce shi domin murya shi na ji a mazaunin driver.

Mummy Sameera da sauran mutane da kuma sauran dangin Angon suka je suka shige motocinsu da suka zo da su muka hau hanyar Gusau.

Koda muka isa gidan shima mutane birjik waɗanda sun ma fi waɗanda muka baro Sokoto yawa sai shagali suke. Ga gidan ya ɗauki saiti ya yi kyau gwanin burgewa.

Wani abun mamaki har muka iso Hajiya ba ta daina kuka ba, lallashin duniyar nan an yi amma har yanzu ta kasa daina kukan farin ciki. Da muka sauka aka tambaye ta ina ne za'a shigar dani sai ta ce kawai a wuce dani gidana direct.

Muna isa bakin ƙofar shiga parlourn gidan nawa Aunty Labiba ta sha gabana ta karanta mini addu'o'i ta tofa mini sannan ta sake karanta wasu ta ce na maimaita sannan daga nan ta shiga muka bi bayanta.

Misalin ƙarfe tara saura bayan kowa ya watse daga ɓangarena kamar yanda suka nema, suka sake gyara komai yanda yake sannan na sake yin wanka na shirya tsab na fito amaryata.

Can ɓangaren Hajiya Kuwa, duk yanda su Uncle Ishaq suka yi da shi akan ya tashi su rakashi ƙin amincewa ya yi yace sai dai Hajiya ta rakashi tare da Labiba. Hakan yasa ta shiryo cikin hijabinta fuskar nan suntum tsabar yanda tasha kuma ta riƙo hannun shi tamkar wani ƙaramin yaro suka shigo sashena.

Mamakine shimfiɗe akan fuskata ganin angona tare da mahaifiyarsa. Wannan kuma wane irin sabon salo ne? Madadin abokai uwar miji ce za ta rakoshi ɗakin auren sa??

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....

*PAGE 33*

Shiru na yi tare da sadda kaina a ƙasa wasu sabbin hawaye na ci gaba da kwaranya daga kwarmin idona ina jira in ji dame ta zo.

Sautin muryar Hajiyar na ji wacce ta daɗe da sarƙewa da kuka tana faɗin.

"Alhamdulillah! Haƙiƙa na godewa Allah da ya nuna mini wannan babbar ranar. Mafi darajar rana a cikin ranakun sati wato Juma'a, rana mai albarka wacce kuma a cikinta a yau aka ɗaura maka aure. Rana ce mai muhimmanci da ɗumbin tarihi a cikin rayuwata da ba zan taɓa mantawa da ita ba. Allahu ta'ala ya sa albarka yasa NANA ta zamto alheri a cikin rayuwarka."

A hankali Aunty Labiba ta zo ta yaye veil ɗinda yake saman kaina sannan ta ɗagoni zuwa gaban Hajiya ta ajiyeni a ƙasan lallausan carpet ɗinda ke malalen a tsakiyar parlourn....ta juya kenan domin ta ɗago Ya Mohaa ta zaunar da shi a kusa dani, ta ji Hajiya ta zabura da ƙarfi tare da buga wata irin Taslima wacce gaba ɗayan su sai da suka razana suka miƙe tsaye a gigice musamman Aunty Labiba tana faɗin.

"Hajiya Lafiya? Miye ya faru.??"

Hannunta da laɓɓanta cike da tashin hankali suka shiga wani irin ɓari tana nuna ni da yatsa a rikice tana faɗin.

"BB... Beenafah!"

Yunƙurawa na yi a hankali na miƙe tsaye da hawaye still akan fuskata na amsa mata a sanyaye na ce.

"Na'am Hajiya!"

Ta shafe tsawon mintuna biyu masu kyau tana ƙare mini kallo tun daga sama har ƙasa. Bayan ta tabbatar dai cewa ni ɗin ce da gaske amma kuma wani ɓarayi na zuciyarta ya shiga gardama mata, cike da waswasi ta kalli Aunty Labiba cike da shock ta ce.

" Labiba! Shin Wannan wai da gaske Beenafah ce ko kuma idanuwana ne ke mini gardama??"

Wani murmushin daman surprised Nike so in miki ta yi sannan ta jinjina kai cike da alfahari ta ce.

"BEENAFAH ce Hajiya...daman surprising ɗin ki na ke so na yi, that's why I planed it this way...."

Wani irin gigitaccen marin ba zata ne itama Hajiyar ta kifa mata cike da baƙin ciki ta shiga nuna ni da yatsa tana kallon Aunty Labibar ta ce.

"Yaushe sunan ta ya tashi daga BEENAFAH ya koma NANA??.....iyeh? Na ce yaushe ne sunanta ya koma NANA?"

Da wani irin maɗaukakin mamaki Labiba ta dafe kunce tana kallonta ta ce.

"Hajiya!!! Yarinyar nan fa taimakonmu ta yi?...."

Wani marin ta sake kifa mata a karo na biyu sannan ta nuna ta da yatsa ta ce.

"Ashe ba ki da hankali ba ki da tunani Labiba? Saboda kawai ƙaddara ta faɗa masa shi ne kike tunanin kowace ballagaza bankaura Jaka ta da ce da ɗana.... Ina Muhammad ina 'ƴar aiki???"

Idan hankali Labiba ya yi dubu yau ya tashi akan irin wannan sabon al'amarin da Hajiya ta fito da shi. Cike da al'ajabi ta kalli Hajiyar ranta na yi mata wani irin tuƙuƙi tamkar an watsa mata gawurtattun garwasu ta ce.

" Hajiya! Kin san kuwa irin abin da kike faɗa? Beenafahr ce ballagaza Jaka? Kar ki manta fa a nan na zo na iske ɗanki ya yi furucin so a gareta kuma kika ce kin amince....To akan wane dalili a yanzu musamman ma ga shi tana matsayin suruka a gareki za ki kirata da 'ƴar aiki? Miye ne bambancin mai aikatau da wacce ba mai aikatau ba???"

A zafafe ta matso daidai fuskarta ta ce.

" Rashin kunya za ki yi min? Na ce rashin kunya za ki min Labiba?? Mutum mai daraja da girma ta ya ya za ki yi tunanin cewa in amince masa don kawai jarabawa ta abka masa in aura masa er aikin da ko darajar mai goge takalmin sa ba ta kai ba? Ko da take mai aiki; har yanzu alkadarinta bai kai ko na mai aikin goge takalmin Mohaa ba.... "

Wayar ta da ta ajiye inda take zaune ne ta warto da ƙarfi ta daddana ta kira.

" Ka zo! Har su Hairi ina son ganin su ku taho a tare...."

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wannan shi ake kira ga ƙoshi ga kwanan yunwa. A yan da hankalina yake tashi da ni da Aunty Labiba, na lura da gogan nawa ko ɗar! Bai yi ba, gefe ma ya ja tare da samun wuri ya zauna kawai ya ɗora ƙafarsa kan ɗaya yana binmu da kallo wanda ni sam na kasa gane ma a wanne hali yake ciki. Shi da nake ƙoƙarin taimakawa shi ne wanda ya nuna rashin amfanina a wurinsa, domin da ya ɗauki auren nan yanda na ɗauke sa, da yanzu hankalinsa ya tashi kamar yanda na wa ya tashi...ban ƙara shiga wani sabon ruɗun da tashin hankali ba sai da naga Emraan ya yi sallama ya shigo tare da su Hairi a bayan sa.

"BEENAFAH!!!"

Emraan ya furta suna na a hankali yana mai ƙureni da kallon mamaki da al'ajabi. Ganin na ƙi amsa shi na saukar da kaina ƙasa ina ci gaba da kuka yasa ya wani damƙi hannuna kamar yanda ya yi mini a wancan ranar ya ce.

"Miye kike a nan?"

Wani irin fisgewa na yi domin lokaci ɗaya na ji wani irin ɓacin rai ya lullɓeni na watsa masa wani kallon cike da zafi na ce.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull