Kenza eBookz

Ganin ido complete Novel - Chapter 36

Ganin ido complete Novel - Chapter 36

Ganin ido complete Novel Chapter 36: Ganin ido complete Novel Chapter 36. "Kada ka sake gigin riƙe hannuna domin ni ɗin matar AURE Ce!!! Idan ba haka kuma..."

3,336 words

"Kada ka sake gigin riƙe hannuna domin ni ɗin matar AURE Ce!!! Idan ba haka kuma..."

A zafafe Hajiya ta kifa mini mari tana faɗin.

"Auren banza auren wofi? Auren da yanzu nan za'a sake ki ki fice mini daga gida! Ina ganin laifin ZIZA akan karan tsana da ta ɗauka ta ɗora miki ashe ban sani ba ita ce da gaskiya..."

Cikin rashin fahimta Emraan ya ce.

"Wai Hajiya miye yake faruwa? Aure Beenafah ta yi? Da wa?"

"Da ɗan uwanka mana! Shegiyar munafuka algunguma kana ganinta simi-simi kamar ta Allah amma fir'auna ne a zuciyarta. Kai da ka nuna kana sonta, ba kai ta so ba, zagawa ta yi tare da wannan shashashar suka haɗa baki ta ce mana Sunanta NANA ta aura masa ita... "

A hankali Emraan ɗin ya lumshe ido sannan ya buɗe yana kallon Hajiya ya ce.

" Alhamdulillah! Wallahi tallahi babu wanda ya kai ni farin ciki da hakan! Kin san dalili? Na so Beenafah sosai a rayuwata, shekara biyu na yi ina dakon soyayyarta. Tun da Labiba ta fahimta ta gano cewa ina sonta na ga ta ɓata rai tana yi mini kashedi wanda idan na fahimta na can ka dai-dai shi ne wanda ta yiwa tanadinta....and Again, ko da ace ba haka ba ne, tun da har ƙaddara tasa ya aure ta, wallahi na yi bankwana da ita da sunan soyayya har abada. And abu mafi muhimmanci da farin ciki yau Yaya Muhammad ya yi aure....Gabaɗaya yau Hajiya a cikin ɗo ki nake da farin ciki....nasan cewa kamar yanda nake mamaki shima haka yake ji, domin gabaɗaya a wunin yau ya kasa yin ko ƙwaƙwƙwaran motsi ballantana magana... "

"Babu ruwana da wannan shirmen banzar Emraan! Wallahi tallahi ba za ta ma kwana ba a daren nan dole sai ya sake ta..."

Cike da shock kowannen su ya shiga kallonta da tsantsar mamaki da al'ajabi.

"Kai Muhammadu! Gata nan furta mata..."

Faɗuwa Aunty Labiba ta yi akan ƙafarsa cike da magiya tana girgiza kanta ta ce.

"Dan Allah Yaya Muhammad dan darajar Allah kar ka daka ta Hajiya! Dalilin ta Sam ba dalili bane, yarinya ce mai tarbiyya da addini, kasantuwarta mai aiki wannan ba hujja ba ce da zai sa ka sake ta... Kada ka taɓa amsa mata na roƙe..."

"Haba Hajiya! Miye laifin Preety...na yi matuƙar farin ciki da auren Yaa Mohaa sannan ganinta yasa farin cikina ya ninku.... Ni wallahi ina sonta...Yaya ni ma ina bayan Aunty Labiba kada ka sake ta..."

Cewar Hairiyya tana mai share hawayen idonta jin wannan irin katoɓara irin ta Hajiya.

Haka suka taru kowa ya yi ta tofa albarkacin bakinsa yayin da Hajiya sai kuka take tamkar wadda aka cewa uwar ta ta mutu. Bayan sun gama faɗin duk abin da za su faɗa ta kira sunan Mohaa a hankali ta ce.

"Muhammad!"

Sai yanzu ya ɗago idanunsa waɗanda suka kaɗa su ka yi ja wanda kallo ɗaya za ka yi masa ka gane baya cikin yanayi mai daɗi ya kalle ta kurum ba tare da ya amsa ba.

"Muhammad wace ce ni a wurin ka??"

Sai da ya lumshe idanunsa for some seconds Sannan ya buɗe su a hankali murya can ƙasan MAƘOSHI ya ce.

"Ke ɗin mahaifiyata ce..."

Jinjina kanta ta yi, cike da alfahari ta ce.

"To idan har ni ɗin na isa da kai ina so ka saki wannan yarinyar yanzu yanzu, bana so ta ƙara ko second ɗaya a cikin parlourn nan da sunan tana amsa sunan matarka...komai lalacewar ka Muhammad kafi ƙarfin auren mai aiki. Saboda haka ka sake ta yanzu..."

Wani irin tsalle na ji zuciyata ta yi tamkar za ta fasa ƙirjina ta fito tsabar yanda maganar ta dake ni. A gigice na kalle shi kamar yanda shima yake kallona ina kuka ina girgiza kaina ina faɗin.

" Please don't! Dan Allah Muhammad kada ka yi... "

" Ka sake ta na ce maka Muhammad!"

Sake girgiza kaina na yi tare da haɗe hannayena a wannan karon alamar roƙo ina wani kalar kuka mai ban tausayi ina faɗin.

"Please don't!! Idan har ka yarda ka furta SAKIN nan to ko yau za ta yi nasara akanka kamar yanda ta saba yi a sauran aurarrakinka na baya!!!"

A take Hajiyar dama sauran yaran na ta su ka ji zuciyarsu ta tsinke. Da wani kallon suka bini jin wani sabon al'amarin da na furzo ba tare da sun yi tsammani ba.

A zafafe na shiga kallon su ɗaya bayan ɗaya ina mai jin wani irin raɗaɗi na jinjina kai na na ce.

"Idan har MUHAMMAD ya furta kalmar SAKI a gareni to haƙiƙa HAJIYA ta yi nasara kuma ta samu abin da take so kamar yanda ta saba yi a baya......"

A hankali na tako na tsaya a gabanta ina mai bin ta da wani kallo kamar yan da ta mutu da mamaki tana kallona na girgiza mata kaina na ce.

" I have no choice Hajiya... Rather than na fallasa wannan asirin naki tun da har kike nema ki ƙure manejin haƙurina...tabbas da ace ba ki matsa kika kafe akan cewa lallai sai ya sakeni ba, da har abadan abada na yi alƙawarin binne wannan sirrin har lokacin da mutuwata wanda hatta uwata ban sanar mata ba..."

"Saboda na ce ɗana ya sake ki za ki ƙalamin sharri??"

"Saboda dai kin yi failing a wannan karon shiyasa kike so ko ta wane hali ki tursasa shi akan dole sai ya sake ni, dalilin ba na zamowa ta mai aiki ba ne....na ga ƙoƙarin ki kuma na ga ƙarfin halin ki na cewa har yanzu kina jayayya da hukuncin Allah...."

Jiki na rawa Aunty Labiba ta janyoni baya a ruɗe ta ce.

"Beenafah! Miye haka..??"

"Aunty Labiba idan har kin yarda dani to ina so ku nutsu ku saurareni..."

Wara idanuwana na yi da kyau na kalle su ɗaya bayan ɗaya, ganin yanda kowa fuskarsa ke ɗauke da tambarin tashin hankali yasa na lumshe idanuna waɗanda suka shabke da ruwan Hawaye na jinjina kaina na ce.

" Ina fata za ku yafe mini! Amma duk abin da yake faruwa da rayuwar Yaya Muhammad ba bu zancen Aljana ko wa su maƙiya...Hajiya ce da kanta..."

"Hajiya Beenafah?? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Cewar Emraan yana mai girgiza kansa cike da mamaki da al'ajabi yana kallona.

Gyaɗa masa kaina na yi kurum ba tare da na kalle shi ba na ce.

"ban san ku ba, ban taɓa sanin su waye ku ba sai da ƙaddara ta ɗaukeni ta jefa gidan Aunty Labiba, daga can ita kuma bayan Mijinta ya kore ni ta dawo dani nan gidan. Ina nan ina aikina kai kuma kace kana sona kana so ka aure ni. A gidanmu, a wannan lokacin kuma Daddyna ya riga ya zaɓa mini mijin da zan aura wanda kwanakine suka rage a ɗaura auren. A ranar da Hajiya ta kirani wanda ban san mi take so ta sanar dani ba...A ranar ne na ji mummunan labarin da ya hanani bacci ya hanani sukuni...waɗannan matan da ta bari a tare dani ta fi ce tana Waya su ne suka zama tsanin da na taka domin taka rawar gani a cikin rayuwar ɗan uwanku da ban taɓa gani ba, ban taɓa jin ko labarinsa ba...."

A rikice Hajiya ta wani fincikoni tana faɗin.

" Ni za ki yiwa Sharri?? Ni za ki ƙalawa sharri ki haɗani faɗa da 'ƴa' ƴa na?? Ka sake ta Muhammad....ka sake ta tun ban tsine maka ba.."

" Muhammad ba zai sake ni ba Hajiya sai ya gama jin irin yanda akayi ya kwance daga ƙullin da ya sarƙe masa zaren ƙaddarar auren sa. In ya so daga baya idan har yana da muradin sakina sai ya sakenin....A ranar da kika kira wayar Haula kika ce ta faɗa mini kina nemana. Ina shigowa kika sa ƙafa kika fi ce kina yin waya. Ɗayar matar da ke zaune akan kujerar 1seater ita ce ta fara fashewa da dariya cikin harshen turanci ta ce; Hajiya Batula ko shaiɗan yana tsoronta....ga shi dai Muhammad ko auren farko ba ta bari ya yi ba amma ga Emraan tana neman aura masa mata ta biyu...ɗayar wacce ke zaune a inda kika tashi ne ta girgiza kanta itama tana dariya ta ce;Kuma wallahi idan ya nemi aure ta lalata ta dawo daga baya tana kuka sai ki rantse da Allah cewa babu hannunta a ciki. Ni babu ma wacce ta bani matuƙar tausayi a last auren da ya nema bai samu ba kamar Labiba. A ranar da Raudah ta mutu yanda ta ga yana kuka na tashin hankali ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba. Kuka fa ta dinga yi tamkar ranta zai cire ya bar gangar jikinta tana faɗin. Da wannan mummunar ƙaddarar da ta sameshi, wallahi da ace tana da wani iko ko wani zarafi....kai! da ace idan ta bada ranta zai zama fansa a gare shi ya samu cikar burinshi, ya yi aure matar ta haifa masa 'ƴa'ƴa da ta yi. Amma haka Hajiya Batula ta ƙeƙashe idanunta da zuciyar ta tayi tamkar ba ta fahimta. Na yi tunanin ko don matsanancin halin da ya shiga na rasa Raudah da taga yayi akan tsananin son da yake mata za ta ɗaga mi shi ƙafa ta bari auren shi ya wakana, amma sam! Ba ta yi ba,ta ce matuƙar dai a Kaga ya yi aure to sai dai a lahira amma ba a nan duniya ba...... "

" What!!!"

Nadeeyah ta furta a gigice tana mai bin Hajiya da kallo. Kamar yanda Nadeeyar ke kallonta, suma haka suka shiga kallonta tare da fata da kuma burin cewa ta buɗe baki ta Ƙaryata wannan zancen da na faɗa a kanta.

Jin tsawon minti biyu ta kasa furta ko kalma ɗaya yasa na kalli Aunty Labiba na ce.

"Ban san waye Muhammad ba, ban san dalilin ta na yin hakan ba, jin sunan ki ya shigo ciki da sunan Raudah, da irin fatan da kika yi akan shi yasa na ji lallai ina so in taimaka. Ke ce ta farkon wadda ta fara tallafawa rayuwata ni da mahaifiyata da ɗan uwana a lokacin da muke cikin matsanancin neman taimako. Kin so ni kin ƙauna ce ni ba tare da kin nuna mini ƙyama ba Aunty Labiba. Hakan yasa na zaɓi taimaka miki da nufin cika miki wannan mafarkin naki. Bayan na zo gidan ki kika ƙara mini haske, daga nan na ƙara jin cewa taimakonki ya zame mini tilas ya zame mini wajibi. Ba tare da sanin kamanni ko yanda kalar ɗan uwanki take ba, haka na yarda na amince domin kawai in ga farin ciki akan fuskar nan taki wacce ba ta rabuwa da son ganin farin cikina nima...idan kuma ba haka akayi ba, ina so ta rantse ta ce ba haka ba ne...."

Cike da wani irin sabon shock wanda ya kama ta a karo na barkatai ta kalli Hajiya ta ce.

" Tabbas a ranar da Raudah ta rasu a asibiti,a ranar Yaya Mohaa ya yi kukan rashin ta wanda duk wanda ke ɗakin sai da ya tsorata. A ranar na yi kuka da kuma burin cewa da ace Raina zai zama fansa da na bayar don ya samu farin ciki...a ranar babu kowa a ɗakin fa ce, ni, ke, Hajiya Samiya, da kuma Hajiya Balki waɗanda su ne ƙawayen ki. Beenafah ba ta san wannan ba muddin ba ji tayi an faɗa ba....a gigice ta zo gidana tun da sassafe ta ce mini tana son auren Ya Mohaa amma tana so a ɓoye kada kowa ya ji sai dai, ni, Ya mohaa da kuma wakilansa. Ba'a yau ɗinnan aka ɗaura masa aure kamar yanda duk kuka tsammata ta a last week Friday ne wacce ta gabata, kuma a nan garin aka ɗaura auren a ƙofar gidan su."

Sulalewa ta yi a hankali ta zube ƙasa tana mai fashewa da kuka tana girgiza kai ta ce.

" Ban taɓa zaton akwai irin wannan ranar ba. Tabbas babu wani dalilin da yake hana masa aure fa ce ni. Wanda ina yin hakan ne ba don komai ba, sai don kada ya yi aure ya samu magada domin bamu da ko Allura a cikin wannan dukiyar..."

Wata irin zabura Mohaa ya yi cike da tashin hankali da gigita ya kalle ta ya ce.

" Hajiya! Da gaske ne wannan maganar kenan???"

" Ka yafe mini Muhammad! Dan Allah ka yafe mini..!!! Labarin ya soma ne ta dalilin rasa mahaifiyarka a ranar da aka haifeka wanda shi ne dalilin aurena da Alhaji Attahiru....Bayan mun yi aure ne yake shaida mini da kuma tabbatar mini cewa duk daular da yake ciki da dukiyar da yake ciki duk ta mahaifiyarka ce... A lokacin da na ji maganar na yi matuƙar mamaki da al'ajabi da ya ce mini wai dukiyar matar shi ce da ta rasu, hakan yasa ya yi mini murmushi a wannan lokacin yace mini ai ba abin mamaki ba ne domin Manzon Allah (S.A.W)ya ce ana auren mace saboda dukiyarta. Saboda haka komai yanzu mallakin ka ne shi bashi da wani kaso mai yawa a ciki. To tun a wannan lokacin na ji cewa hankalina ya tashi domin dole watan watarana za'a wayi gari ka mallake komai da kai da matarka da 'ƴa' ƴanka. Hakan yasa na ce muyi alƙawari da Alhaji cewa kada mu taɓa bari kaji cewa ba ni ce na haifeka ba domin bana so ka yi kukan maraici....."

Wata irin damƙa ya kai wa hannuna wanda ba ni da ya jimƙa ba, hatta su Hairi sai da suka tsorata tsabar yan da suka ga ɓacin randa ba su taɓa sanin yana da shi ba kwance akan fuskarsa, hatta jijiyoyin kansa duk sai da suka hirɗo tsabar yanda ya ke wata irin tafarfasa akan ɓacin rai.

Jana ya shi ga yi da ƙarfi muka nufi hanyar barin parlourn. Cikin wani sabon tashin hankalin Aunty Labiba tace.

"Yaa Mohaa ina za ka tafi da ita cikin daren nan??"

Komai bai ce mata ba har muka fice still tsintsiyar hannuna jimƙe a cikin nasa ya nufi motocinsa ya buɗe ya tura ni ciki shima ya shiga ya zauna. Wayarsa ya fiddo ya yi magana cikin mintuna sai ga masu tsaronsa sun fito suka shigo motocin a cikin daren muka bar gidan.

Cike da tashin hankali ina wani irin kuka na ce.

"Ina za ka kai ni? Dan Allah ka mayar dani wurin Ammie na... Aunty Aysha tana can na baro..."

Cikin wani irin ƙaraji ya daka mini tsawa wacce ta saka ni shiga taitayina lokaci ɗaya ya ce.

"Ya isa!!! Ki rufe min bakinki kin ji ko!"

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....

*PAGE 34*

Duk irin ƙarfin zuciya da Emraan yake da ita sai da ya fashe da kuka tsabar baƙin cikin wannan irin mummunan abun da ya riske su a yau mai cike da baƙin tarihi da abin faɗa a gare su muddin dai wannan maganar ta fita.

Kuka suke sosai wanda ta kai ga babu wanda ke rarrashin ɗan uwansa. A raunane Lababi ta waigo ta kalle ta tana wani irin kuka ta girgiza kanta ta ce.

"Hajiya wannan wane irin mummunan labari ne haka? Wannan abun ya yi muni.... Wallahi ya yi muni Hajiya...Ina ma ace fatan mutuwa na da kyau.. Wallahi tallahi da na roƙi Allah ya ɗauki raina akan wannan mummunan rana da ta riskeni...Yay...yaya Mohaa...bamu taɓa ji ko a mafarki cewa shi ɗin ba ciki ɗaya muka fito ba. Tun tasowarmu har zuwa yau bamu taɓa samunsa da wani abun munanawa agareki ba ballantana mu zarge shi akan cewa yana miki ba daidai ba da har zai sa mu fahimci cewa ba ke ce kika haife sa ba....Wato ashe duk tsananin so da ƙaunar da kike nuna masa ashe duk na GANIN IDO ne Hajiya? Ke ɗin uwa ce a gaban idonsa amma a bayan sa ke ce maƙiyiyarsa ashe....Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Kai duniya! Wai ina za ki damu ne haka??"

Muryar Emraan suka ji yana faɗin.

" Hajiya! Wannan abun da kika aikata son zuciya ne kawai da ra'ayi irin naki! Dalilin da kika kawo Sam ba dalili ba ne. Ni,Labiba, Nadeeyah, Hairiyyah...tun da Alhaji ya faɗi ya mutu yaya Muhammad shi ne ya dawo komai namu, makaranta, magani,abinci, sutura...ya kula damu ya bamu soyayya Hajiya...yanda yake son ki yake ƙaunarki na yi imani ko mu nan iyakar son da muke miki kenan. Shi ne fa ya nema min aikin nan, ya nemawa Labiba ya nemawa Nadeeyah...shi ne yakai Hairi makaranta a Madina. Duk da cewa muna da hanyoyin samu, duk wata sai ya tura mana kuɗaɗe na Musamman. Abinci, motoci, abin hawa gida komai na rayuwa na jindaɗi ya tanada mana kuma bai taɓa yi mana iyaka akan komai ba...Hajiya duk ƙasar da kike so kai tsaye kike samun damar zuwa duk ta dalilin sa, idan kika nuna masa abu kika ce masa wannan fari ne to yafi farin zama fari a wurinsa. Idan kuma kika nuna masa abu kika ce masa wannan abu baƙi ne to wannan baƙin yafi gawayi baƙi a wurinsa...idan kince kin yi hakan ne saboda mu mi muka rasa? Idan kuma kin cutar da shi saboda ƙashin kanki miye ribar ki?.... "

Girgiza kai ta yi cikin gunjin kuka ta ce.

" Babu! Wallahi Babu Emraan! Sharrin shaiɗan ne kawai da zugin ƙawayena.... "

Cike da jin wani irin malolon baƙin ciki Labiba ta girgiza kanta ta ce.

" Idan kika ambaci ƙawaye a nan Hajiya to tabbas kina ƙara munana abun ne ni dai ta gefena,domin ni ɗin nan dai na san cewa ke ce kika haifeni kuma kina sama dani, idan na ce miki wai wata ƙawata ce ta zugani na aikata wani kuskuren to ko ke za ki yi Allah wadai dani ballantana ke da kike mahaifiyata... "

" Wallahi Labiba Sharrin shaiɗan ne da Hajiya Samiya... Ita ce wacce ta ɗorani akan wannan shawarar ta kuma tabbatar mini cewa duk ranar da na bari ya yi aure ya haifi 'ƴa'ƴa watarana sai ya gano cewa ba ni ce wadda na haife sa ba, kuma idan har hakan ta kasance to fa daga ni har yaran da zan haifa ko mutuwa ya yi sisi ba zamu tsira da shi ba... "

Cike da takaice Emraan ya girgiza kai yana faɗin.

" Oh Common Hajiya please Ki daina magana kamar wata ƙaramar yarinya. Ke kike maganar nan amma kuma ni kunya take kamawa wallahi.... Wannan abun da kika yi Hajiya wallahy Hairi gata nan ba za ta iya aikatawa ba Hajiya...Sannan yanzu dan Allah da wanne idon kike son na kalli Ya Muhammad? Da wanne ido kike so duniya ta kallemu idan ta ji abin da kika aikata masa??"

Daga haka ya miƙe shima har yana haɗa hanya ya fice daga parlourn tare da ɗaukar motar sa ya wuce gidansa.

Ajiyar zuciya Labiba ta sauke a hankali tana mai ci gaba da share hawayenta ta kalli Hajiya ta ce.

" Kin san me Hajiya? Mafi munin kuskuren da kika aikata shi ne cutar da ɗan da ya ɗauke ki matsayin uwa. Hajiya duk abin da bawa zai samu Ubangiji ya riga ya rubuta masa tun yana Cikin mahaifiyar sa. Arzikin sa, ajalin sa, aikin sa, wallahi duk Allah ya riga ya gama ƙaddara komai. Wayonki ko kuma dubarar ki, babu ɗaya da zai fishsheki. Ko da Yaa Mohaa, ko babu Yaa Mohaa, arzikin da Allah ya nufeki da shi dole shi za ki samu babu wanda ya isa ya ƙara miki akan haka....... Munyi baƙin ciki da wannan abun,matuƙar baƙin ciki Hajiya. Na sani, da ace Alhaji yana doron duniyar nan da zai fi kowa baƙin ciki da wannan abun da kika aikata. Mun taso cikin haɗin kai da ƙaunar juna yanzu kin ɓata hakan Hajiya...."

Miƙewa ta yi a hankali ta shiga zagan kyakkyawan parlourn tana kewaya tana jinjina kai ta ce.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull