Ganin ido complete Novel - Chapter 38
Ganin ido complete Novel Chapter 38: Ganin ido complete Novel Chapter 38. "To hajiya Sameera na ga kina neman rabani da 'ƴata."
3,360 words
"To hajiya Sameera na ga kina neman rabani da 'ƴata."
Ta shi ta yi tana jinjina kai ta ɗauki Jakarta tana faɗin.
"Ya yi daidai. Bari ki gani na tashi na san inda dare ya mini. Sai Anjimanku Aysha asha nono da kyau."
Tana ficewa Ammie ta zauna a bakin gado tana fuskantar Aunty Aysha ta ce.
"Aysha wallahi da Mijin Beenafah ya kira Dr. Ya ce wai tafiyar gaggawa ta kama shi sun wuce gabaɗaya sai na ji hankalina ya tashi. Lokaci ɗaya na ji na rasa nutsuwata. To amma wani abin mamaki shi ne, da ta kirani ɗazu da safe in faɗa miki hankalinta kwance tamkar ba wacce aka ɗauke a ka tafi wata uwa duniya da ita ba...Ko alamar mutum ya nuna ya ɗan damu ɗin nan ba ta yi ba...."
Murmushi Aysha ta yi tana jinjina kanta ta ce.
" Ammie! Wallahi Beenafah ita ɗin jaruma ce ta gaske.... Duk irin abubuwan da ta yi going through a lokacin baya na yi matuƙar jinjina mata domin ita ɗin tana da kaifin tunani da ƙarfin zuciya...."
Dariya ce ta sake suɓuce mata tana jinjina kai ta ce.
"Ammie kin san ma abin da ta yi jiya wanda ya bamu dariya ni da Aunty Sameera?"
Girgiza kai Ammie ta yi tana murmushi alamar A'a sannan Aunty Ayshar ta ce.
"Bayan magrib ta yi mun shiga ɗakin ta mun yi sallar magrib da isha sai muka sake shiryata cikin Atamfa da mayafinta muka fito Parlour muka ce mata za mu wuce sai da safe, kawai ce mana ta yi to sai Mama Asma'u ta ce; yanzu ke Beenafah shikenan kukan ya tsaya gabaɗaya? Ba ma irin alamar ki ɗan yi kukan nan ki ce dan Allah kada ku tafi ku barni..... Wallahi ƙarshe dariya ta yi mana kawai ta ce wai ita ta gaji da kukan ne. Bayan sun gaba sun bar ni dada ni sai ita na ce mata Beenafah ki kula sosai kinji ko kuma ki zama mai juriya da riƙe sirri wai sai ta kalle ni kawai ta ce mini ita ta yi imani cewa har abada ba zai taɓa cutar da ita ba.... "
A tare suka yi dariya sannan Ammie ta ce.
" Wautar ƙurciya da yarinta ina za su barta ta fahimci abin da kike nufi. Allah dai ya amintar da su a wannan zama na su ya ba su zaman lafiya damu da su baki ɗaya....."
Kallon wayar Aunty Ayshar ta yi da ke ta ringing tun ɗazu tana basarwa ta ce.
"Aysha ki ɗaga wayar nan mana, waye yake kiran ki?"
A ɗan darare ta kalli wayar sai kuma ta kalli Ammien ta ce.
"Hussaina ce Ammie.."
"Allah sarki to ki ɗaga mana!"
Jin hakan yasa ta ɗauki wayar ta kira ta back domin har kiran ya sake yankewa. Tana ɗagawa daga can ɓangaren Hussainar ta ji ta fashe da kuka ta ce.
"Aunty Ayshaaa! Aunty Aysha mi nayi miki da bakya ɗaga kirana?? Miyasa kika tafi kika barni a lokacin da nake cike da tsananin buƙatar ki a kusa dani??"
Wasu irin hawaye ta ji sun shararo mata ba tare da ta shirya ba ta shiga girgiza kanta ta ce.
"Hussaina dole in tafi...idan ban tafi ba ya zan yi? Zuciyata ta kasa daurewa Hassy that's why naga cewar tafiyar ita ce masalaha a gare ni..."
Cikin sheshsheka ta ce.
"Aunty Aysha Su Daddy ba za su canja ba! Ba za su taɓa canjawa ba. A ranar da kika barmu the next day muka juyo muka dawo Abuja ko kaɗan ba su can ja ba Aunty Aysha, musamman Mummy,sam ta ƙi yarda da cewa ba'a daidai take ba, Daddy ma ya ce bai san wani kuskure da ya aikata ba kawai dai rashin fahimta ne yasa kuka ɗauki abun a haka. Kuma sai ya binciko duk inda Ammie take a faɗin duniyar nan ya yi shari'a da ita akan su Beenafah... "
A matuƙar kunyace Aunty Ayshar ta ɗago kanta ta kalli inda Ammie take zaune, sai dai kuma Wayam ba kowa wato kenan ta shi ta yi ta bar mata ɗakin.
Jinjina kai ta yi a hankali tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ta kira sunan Husainar ta ce.
" Hussy!"
"Naam Aunty Aysha!"
"Hussy za su canza in sha Allahu! Addu'ar ba ta bar komai ba muci gaba da yi musu ita in sha Allah za su gane gaskiya watarana. Ki yi hak'uri kamar yanda Hassy ta yi aurenta ke ma watarana in sha Allahu za ki samu mijin da ya dace dake wanda zai kula da ke sosai."
"Allah yasa Aunty Aysha. Jiya na je na yi register wani shagon make-up da gyaran jiki zan fara zuwa training domin idan na ci gaba da zama a gida watarana zuciyata na iya yin bindiga na faɗi na mutu."
"In sha Allahu ma hakan ba zai faru ba. Ke dai ki riƙe ibada ki yi ta addu'a...Ko jiya mun gaisa da Alhaji Baba ya ce mu ci gaba da addu'a in sha Allahu watarana komai zai wuce. Allah ya taimaka ya bada sa'a."
"Amin Aunty Aysha na gode.... Allah sarki! Ko waye Ammie ta aurawa Beenafah? Allah yasa duk inda suke suna lafiya!"
Jinjina kai Aunty Aysha ta yi ta ce.
"Amin Yah Allah. Khairan In Sha Allah. Shi kaɗai zamu ce a yanxu. Sai an jima."
Gabaɗaya tun da ta kambala wayar a sukuku take domin ko tantanma babu idan har Ammie ba ta ji wata maganar ba to tabbas ta ji wata. Ita kuma Ammie ko kaɗan ba ta nuna mata cewa wai abin ya dameta haka suka ci gaba da al'amuran su.
*********
Ni kuwa, ina nan zaune ina ta kallo a TVn har misalin ƙarfe ɗaya da rabi,hakan yasa na miƙe naje na yu sallah a ɗaki, ina fitowa na tarar da Launch an ajiye mini wanda na tabbata shi ne wanda ya shigo ya ajiye min.
Zaunawa na yi na ci abincin sosai domin ba ƙaramin daɗi ya mini ba, sannan daman gashi ina jin yunwa duk kwanakin nan ba wani abincin kirki na samu na na ci ba.
Ina nan zaune bayan na kambala na ci gaba da kallo har lokacin Asr ya yi sannan na tashi na sake shigewa ciki na yi na sallah na haye kan gado na kwanta ina tunanin ina ya shiga haka tun safen nan ban ƙara sanya shi a idona ba. Wasa-wasa har dare ya yi ban ji motsin sa ba. Koda na fito daga ɗaki har goma na dare ta gota inda na tarar an ajiye min dinner Kamar na ɗa zu.
Jiki sanyaye na koma ɗaki na kwanta ina hawaye a hankali domin a yanzu na gama tsorota da yanayin da nake ciki. Tun safe bai dawo ba sannan babu mutum ɗaya da ya shigo inda nake. Tun ina kukan kaɗan-kaɗan har ya ci ƙarfina sosai ina ta yi harda sheshsheka sai daga ƙarshe bacci ya yi nasarar sace ni.
Washe gari tun ƙarfe biyar da rabi na farka na je na yi sallah sannan na zauna na yi azhkar sai misalin shida da rabi na fito still babu alamun shi a parlourn.
Wani ɗakinda ke kusa da nawa na je a hankali na murɗa na tura ƙofar na shiga. Kwance na same shi a ƙasa ga gadon ya zama so scattered da alama faɗowa ya yi daga sama.
Cikin matsanancin tashin hankali na ruga da gudu na tallafoshi na juyo shi daga kifen da yake zuwa jikina ina ta tattaɓa jikin shi a ruɗe ina faɗin.
"Yaa Mohaa miye ya sameka!! Baka da lafiya ne??"
Na ambata ina ƙara tattaɓa wuyan shi zuwa kan goshin shi. Jin wani irin zafi da jikin na shi ya ɗauka yasa na fashe masa da kuka ina faɗin.
"Miye ya sameka haka? Na ji jikinka ya yi zafi sosai! Wayyo Allah na! Dan Allah ka taimakeni ka tashi ka ji..."
A hankali ya buɗe idanunsa sama-sama ya riƙo hannayena ya jimƙe a nasa cike da raɗaɗi cikin muryar da kana ji za ka tabbatar cewa yana cikin zafin ciwo ya ce.
" karki damu, bada jimawa ba I will take you far away from here.... I promise you.....Ke ka ɗai ce ni ke da ita a duniya wacce ta rage min a duniya...Sun cutar dani. Gabaɗaya ɗayan su sun ci amanata sun cutar dani...ko da ace na mutu a yanzu haka. To zan yi godiya ga ubangiji domin ya bani mutum ɗaya mai ƙaunata ba don wani abin da nake da shi ba..."
"Dan Allah ka yi shiru ka tashi mu tafi asibita...in sha Allah babu abin da zai faru da kai... In sha Allah zamu haifi yara ma su albarka, waɗanda za su nuna maka ƙauna kuma za ka yi farin ciki da matuƙar yin alfahari da su..."
Tallafo shi na yi don na mayar da shi akan gadon amma na kasa yin hakan... Murya cike da kuka na ce.
" Don Allah ka ɗan ƙoƙarta ka ji. Ka daure na ɗaga ka ka koma kan gadon, nan ƙasan san yi zai yi maka yawa..."
A haka na cicciɓa sa kamar wata mai bala'in ƙarfi da ƙyar na yi nasarar mayar da shi kan gadon. Cikin zafin nama karon farko na buɗe ƙofar na nufi ƙasa.
" Hajiya akwai abin da kike buƙata ne??"
Cewar wa su mutum biyu da suke sanye da uniform ɗin aiki. Da sauri na jinjina musu kai ina faɗin.
" Eh! Eh!....Dan Allah ku bani ruwa da towel yanzu dan Allah."
Cikin en mintuna kaɗan sai ga shi sun yi providing mini abin da na buƙata da gudu na koma ciki na ajiye bowl ɗin a gefen bedside drawer Sannan na haura gadon na shiga kicaniyar rage masa kayan da suke jikin sa wanda kaftan ne na shadda fara da alama tun da ya dawo jiya bai ko tsaya can ja kayan jikinsa ba ya kwanta a haka.
Da ƙyar na yi nasarar cire masa rigar leaving him with only Vest a hankali na matse towel ɗin na shiga goge masa jikinsa ina yi ina masa sannu wanda a wannan lokacin babu abin da ya zo min a rai fa ce lokacin da Ammie ta ke cikin matsananciyar jinya.
Ina nan ban daina ba har sa dai na ji zafin jikin nasa ya suranye sosai sannan na ajiye kayan a gefe na dawo gefensa tare da janyo hannun sa na saƙala a nawa ina murza masa a hankali tamkar yan da nake yiwa Ammie na idan tana zazzaɓi wanda duk na ko yi waɗannan techniques ɗin ne sanadiyyar abin da aka koyar dani idan tana zazzaɓi yanda zan kula da Ita kafin na kai ta asibiti, domin ba'a yarda a bata kowane irin magani ba matuƙar dai ba daga likita ba ne.
A hankali numfashi shi ya fara daidaita yana sauya wa wanda hakan ya tabbatar min cewa ya samu bacci. Bayan na tabbatar cewa ya yi baccin da gaske na sauka daga kan gadon na fito har waje na ce ina Sir Haroun.
Matsowa ya yi daga angle ɗinda yake tsaye cike da girmamawa ya ce.
"Gani nan madam!"
Jinjina kai na yi ina kallon sa na ce.
"Yaya Muhammad ne ba shi da lafiya. Dan Allah ko akwai likitan da za'a iya kira masa ko kuma sai dai mu kai shi asibiti?"
"Akwai likita Hajiya, ki koma ciki yanzu in sha Allah za'a zo da shi."
Dawowa na yi na zauna ina ƙare masa kallo wanda a yanayin jikinsa da fuskar sa ba zan kira sa da saurayi ba, domin yanayin manyanta ya fara bayyana a fuskar sa. Ba ya daga cikin mazajen da za'a kira giant domin bai cika tsayi sosai ba sannan yana da kakkauran jikin da ba za a kirasa da siriri ba. Mutum ne har mutum wanda daga yanayin maganar sa da ɗabi'arsa za ka fahimci cewa shi ɗin kamilallen mutum ne.
Fuskarsa na dawo kallo wacce ta yi luf da kamilalliyar ƙasumba da ta kwanta ta ƙara fitowa da shi. Girman abun nake dubawa a raina wai ni ɗin da ban kambala ma shekara ashirin ba amma kuma na amince da auren babban mutum irin wannan, wanda hatta a cikin Sumar kansa ma akwai zare-zaren furfura da ta fara fitowa ɗaɗɗaya....Tashi na yi tare da share hawayen idona da tafin hannuna na yo waje jin ƙarar door bell da na ji.
Ina ganin Haroun da Doctor Ɗin na ba su hanya suka shigo sannan ya shiga duddubashi yana tambaya mata miye abinda ya same sa.
"Zazzaɓi ne mai zafi ya kwana da shi. Hakan ma na masa tepidsponge ne shiyasa zafin jikin ya rage."
Jinjina kansa likitan ya yi sannan ya shiga ba shi taimakon da ya dace tsawon lokaci. Bayan ya kambala ya yi mini sallama ya tafi tare da Haroun wanda ya shigo da shi.
Bayan na kambala sallar Azahar ne na ɗauki wayar da naga ya kira da ita jiya na kunnata kuma cikin sa'a na tarar ba ta ɗauke da kowane Password. A mamakina lamba ɗaya na tarar a cikin contact ɗinsa. Waro ido na yi tare da ƙasa kashe wayar na kunna still dai ita ce ko a gidan kiran. Cike da rashin tabbas ɗin waye zan kira na ɗauki danna call. Ringing ɗaya zuwa na biyu na ji sautin muryar Ammie tayi mini sallama. A hankali wasu sabbin hawayen suka ƙwace mini a raunane na ce.
"Ammie ba shi da lafiya... Ya mohaa ba shi da lafiya Ammie.."
"Subhanallah! Miye abun da ya same sa? Kunje asibiti kuwa?"
"Eh! Na kira masa likita ya zo ya duba shi har drip ga shi nan ya ɗaura mishi..."
Cike da nuna kulawa ta ce.
"Ubangiji Allah ya bashi lafiya...ki yi hakuri ki kwantar da hankalinki kin ji ko."
Girgiza kaina na yi murya a karye na ce.
"Ammie al'amarin ba mai sauƙi ba ne! Ba mai sauƙi ba ne Ammie.... Dole zan faɗa miki dalilin da yasa yake cikin wannan halin..."
Ban tsaya nauyin baki ba na feɗe mata tun daga biri har wutsiya na duk abin da ya faru da kuma ainahin dalilin da yasa na auri Ya Mohaa.
Hankali a tashe ta ce.
" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Hasbunallahu wa niimal wakil! Mun shiga uku da irin wannan al'ummar da muke ciki a yanzu....Beenafah ita Hajiya Batula ta aikatawa Muhammad ɗin haka?"
Jinjina kaina na yi ina mai ƙara ji a raina cewa na tsani al'amarin mutane waɗanda suka kasance azzalumai masu fuska biyu. Cikin sheshsheka na jinjina kaina na ce.
"Ita da kanta ta amsa hakan Ammie. Zaluncinta da cin amanarta ni a gareni yama fi na su Daddy muni da hatsari....Ammie Uwa fa! Ita ɗin uwa ce Ammie, babu abin da ya rage ta da shi daga ita har 'ƴaƴan ta.."
"kina ji Beenafah! Yanxu ba lokacin yin wannan maganar ba ce. Abin da zan faɗa miki shi ne; ki mayar da hankali sosai domin mijin ki yana da buƙatar kulawar ki, don Allah ki kula da shi domin Allah kamar yanda kika ɗaukarwa kanki alƙawarin kare shi. Ubangiji Allah ya bashi lafiya mai amfani. Kada ki riƙa yi masa firarrakin da ba su da wani amfani a rayuwarsa...."
Nan dai ta yi ta bani shawarwari sannan daga baya Aunty Aysha ta karɓa itama ta yi nata tare da yi masa addu'ar samun waraka.
Bayan mun kambala magana still na sake shiga wayar wai ko zan ga numbern Aunty Labibar na kira amma na kasa samun numbern ko mutum ɗaya.
Ina nan misalin ƙarfe uku na rana naga ya farka a hankali ya miƙe zaune tare da saukar da ƙafafunsa ya kashe magudanar ruwan sannan ya zare Cannula ɗin a hankali ya tashi ya shige toilet.
Ina ganin ya shiga toilet na sauka naje na kawo mi shi abin ci da sha wanda cooks suka gama dafawa a tray na dawo ɗakin na gyara shimfiɗar gadon da kyau sannan na samu wuri na zauna.
Ƙirjina ne ya buga ganin yanda ya fito daga shi sai towel ɗaure a kwankwasonsa. Cikin sauri na sadaukar da kaina ƙasa ina faɗin 'Subhanallah' a cikin raina. Kamar yanda ya yi mini a cikin mota ko yau hakan ce ta kasance domin bai ma nuna alamar ina nan wurin ba ballantana ya ji ya tsargu. Nic and vest ya saka Sababbi bayan ya gama shirya a jikinsa, sannan ya zura jalabiya ya zo kan sallaya ya yi Sallah a hankali bayan ya kambala ya sake komawa kan gadon ya kwanta.
Tashi na yi na je dab da shi Ƙirjina na wani ɗagawa a hankali na ce.
"Am! Ga abinci na kawo maka ka daure ka taɓa koda kaɗan ne kasha maganin da likitan ya bayar yace idan ka ta shi ka ci abinci kasha...."
A hankali ya buɗe lumsassun idanunsa ya kalleni sannan ya murmusa kaɗan yana gyaɗa kansa ya miƙa hannu ya janyoni yasa na kwanta a gefensa ya ƙanƙameni sosai yana mai cusa fuskar sa a gefen wuyana. Da zai saurari bugun zuciyata tabbas da ya ji yanda ta ke tsalle tsabar yanda na ji ni a cikin wani yanayin. Jin yanda jikina yake ƙyarma a hankali ya raɗa mini a kunnena.
"Relaxed... I just want to feel you around me. Thank you for existing."
Luf na yi jin abunda ya faɗa tare da ƙara kwantar da kaina akan damtsen hannun damansa da ya ɗorani na yi shiru tare da lumshe idanuna a hankali bacci mai cike da tarihi ya yi awon agaba da mu wanda bai farka ba sai misalin ƙarfe biyar ya tashi ya je yayo alwala wanda koda ya fito bai tarar da ni a ɗakin ba. Sai da na yi sallah sannan na sake fitowa na sauka ƙasa na sake amso masa wani abincin tare da umartar wata daga cikin masu aikin na ce ta biyo ta karɓi wanda bai taɓa ba.
Yana zaune akan sallayah ya ga na shigo ɗauke da wani trayn a hannuna na ajiye sannan na ɗauki wancan na fita na miƙa mata. Ban zauna ba sai da na ɗauko magungunan na kalle sa murya a hankali na ce.
"Ya kamata ka ci abinci kasha magani..."
Jinjina kansa ya yi calmly yana kallona ya ce.
"I will. But a tare zamu ci saboda kema baki ci ba."
Yatsun hannuna na jefa a cikin haɗaɗɗiyar shinkafar jallop ɗin wacce tasha kaya da nama har ta gaji na ɗebo kaɗan na kai bakina. Ganin na kasa sake wa yasa ya ajiye spoon ɗin hanunsa ya kama hannuna yasa na ɗebo yakai bakina sannan na sake ɗebowa ya kai bakinsa ya haɗa har da siraran yatsuna ya tura a bakinsa cike da jin wani irin shock na yi saurin janyewa ina mai jin tsikar jikina tana tashi. Hmm! Wannan mutumin mugun ɗan renin wayau ne na ƙarshe. Yanzu wai yana nufin shi bai ji komai ba kenan?.
Katse min tunanina ya yi da faɗin.
"Ki ɓallamin maganin..."
Ɗaukowa na yi na ɓalla masa ya sha sannan na tattara kayan na kai waje na dawo.
Hannuna ya janyo muka dawo parlour muka zauna ya jani cikin shi still tare da rungumeni a hankali ya ce.
"Kuka ki ke ɗazu saboda ni ko? Jiya ma kin yi kuka saboda ni?....Thank you."
Daga haka bai sake cewa komai ba nima kuma ban ce ba muka ci gaba da kallo har magrib sannan ya shiga ya yi alwala ya fito yaje masallacin gidansa ya yi sallah bai dawo ba sai da aka kambala Isha sannan muka sake cin abinci wanda ko shi ba mai yawa ba. Muna nan zaune har kusan ƙarfe tara sannan na miƙa a hankali na taka zan shige ɗakina na ji ya kira sunana ya ce.
"Beenafah!"
Cak! Na ja na tsaya ba tare da na waigo ba.
"Bacci za ki yi?"
Still shiru ban amsa ba, hakan yasa ya tashi ya kashe TVn sannan ya ƙara so ya ja hannuna muka shige ɗakinsa ya cire mini hijabina da kansa sannan ya zaunar dani bakin gadon ya je ya yi wanka ya fito ya shirya sannan bayan ya kammala ya kashe wutar ɗakin gabaɗaya ya zo ya kwanta a hankali ya janyo ni jikinsa na kwanta a darare har bacci ya ɗaukemu.
********