Kenza eBookz

Ganin ido complete Novel - Chapter 39

Ganin ido complete Novel - Chapter 39

Ganin ido complete Novel Chapter 39: Ganin ido complete Novel Chapter 39. Gefen su Daddy kuwa, babu wani abin da ya canja game da su. Maimakon su ɗauki…

3,368 words

Gefen su Daddy kuwa, babu wani abin da ya canja game da su. Maimakon su ɗauki darasi akan abun da ya faru ba su yi ba. Suna dawowa Abuja ya ɗauki Hafiz ya jefa shi a kamfanin buga magungunan Wazeer da ke Lagos.

Normal suka dawo rayuwar su kamar babu wani abin da ya faru. Mummy ma tayi nasarar buɗe wani babban shopping complex a Abujar Wanda ya ƙara mata jin wata irin sabuwar izza da ƙafafa, ta faɗa ta ƙara faɗa ta ce duk wanda yace bai son kuɗi to shi ɗin matsiyaci ne marar rabo. Shiyasa har abada ta yi hannun riga da duk wanda baya son su da arziki. Hassana tundaga taga hakan ya fi mata ta je can ta ƙarata da rayuwar ta.

Yau ma ta kasance ranar wani taron su na Group ɗin su na en kasuwa su shida da suka haɗa kai suke komai a tare. Bayan ta shirya ta fito suka ci karo da Daddy ya shigo ya nata wani murmushin nasara.

Itama da murmushin akan fuskarta ta kalle shi ta ce.

"Na Zalihatu Zaki! Mudassiru uban Humaidah da Hafiz..."

Wata irin dariya ya yi harda kekkewa sannan ya jinjina kai ya ce.

"Albishirin ki uwar gida!"

"Goro fari ƙal Yana ƙyalƙyali..."

"To na samo mana wata hanyar Kawar da Mulaifa cikin sauƙi da rahusa.....Wallahi ina tabbata miki daga ita har yaran na ta ƙarshen su ya zo... Daman ni babu wanda ya isa ya ja dani ya zauna lafiya Ƙarya ne wallahi..."

Cikin jin wani irin farin ciki.

"Dan Allah Alhaji da gaske kake?"

"Ƙwarrai kuwa da gaske? Mutumin ya tabbatar min da cewa idan na bashi abin da ya lissafa min to shi kuma ya yi alƙawarin kawo min su da ransu su duka ukun... Kuma Ƙarya take yi tana ƙasar nan babu inda ta je....sannan an sanar mini cewa wani shegen matsiyaci ne ta aurawa Beenafahr kuma har shi na ce a haɗa da shi a kawo min wanda na yi alƙawarin ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi."

"Miye mutumin ya ce ka ba shi to??"

Girgiza kansa ya yi ya ce.

"A'a! Na san halin ki in dai akan abun duniya ne. Ina iya faɗa miki ki ce abin da ya nema ya yi yawa. Ni kuma abun da nake gani, biyan buƙata ai yafi dogon buri..."

Tashi ta yi da sauri ta nufi waje tana faɗin.

"Wannan labari ne mai dadi. Kuma in dai akan wannan ne to ka bar shakkata domin ni ma nafi son in bada ko nawa ne muddin dai za'a kawo mana su gabanmu. Na tafi sauri nake sai na dawo mu ƙara tattaunawa ana jirana a yanxu."

Tashi yayi ya shige ciki ya cire kayan jikinsa ya shiga wanka zuciyarsa fes tamkar wanda aka yiwa wani albishir ɗin albarka.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....

*PAGE 36*

Washegari, har ya tashi ya fita masallaci ya dawo bata ko motsa ba. Zaunawa ya yi gefenta a hankali bayan ya dawo tare da ƙura ido yana kallonta. 'Wannan yarinyar! Ita ɗin a yanzu gabaɗaya rayuwar sa ce, tabbas ta kasance duniyar sa mafi girma da daraja a yanzu..... A yanzu gabaɗaya ji yake ya koma wani ƙaramin yaron da baya gane komai sai ita da kuma abin da ta ce masa. Ta fiye masa komai a rayuwar sa kuma har abada ba zai taɓa iya barin inuwar ta ba. A kwana biyun da kawai suka yi tare, idan ya tafi ji yake ba zai iya ɗaukar wani lokacin a wani wuri ba tare da ita ba. Yarinya ce ƙarama amma tana da nutsuwa, ta iya magana, tana da kaifin basira da hangen nesan da ko wata babbar mace mai shekarun hamsin bata da su.....domin ita ce ta tsamo shi daga sarƙafaffen tarkon da ya ɗauka cewa ya riga ya rufta har ƙarshen rayuwar sa.

Sai ga wannan yarinya ƙarama da ita, ita ce ta tsaya akan dugaduganta domin ceton shi bayan Mahaifinsa da en uwansa sun cutar da shi, cutar wa mai muni da barin mugun tabon da har ya kwanta daman shi ba zai manta ba!

Hajiyarsa da ya ɗauketa da muhimmancin da bai haɗata da kowa ba....wai ita ce ta yi uwa ta yi makarɓiya wurin lalata masa rayuwa, ta sanya shi a matsanancin ƙunci da baƙin ciki....haka za ta zauna ta yi ta kuka tana lallashinsa tana cewa ya yi haƙuri da kalar ƙaddarar sa mai yiyu wa rabon auren ne ba shi da shi a duniya ashe wai ita ce.... Ita ce silar rugujewar rayuwar sa...wallahi idan ya tuna sau dubu mutuwa yake da baƙin ciki da dana sanin zuwa duniyar ta hannun su.

Ina ma ace a wata al'ummar, a wata ƙabilar ko wata ƙasar ce aka haife shi ba a hannun Hajiya ba. Yanda yake ƙaunarta ko kansa baya ƙauna haka. Idan ta faɗa masa magana ɗaya! To ko ba ta yi masa daɗi ba ya ɗauka kuma ko a fuska ba za ta fahimci rashin daɗin ta ba a wurin shi...wai amma ita ce silar ƙunci da baƙin cikinsa tsawon shekaru.

Ta ya ya zai iya haɗa ido da su Labiba? Haƙiƙa ya ji kunya sosai akan wannan abun! Ina ma ace wannan maganar ba a gaban su ne aka yi ta ba...ina ma ace daga shi sai ita ne sai Beenafahr kawai suka san da wannan? Da har abadan abada ba zai taɓa bari su ji wannan irin mummunan labarin da yasan cewa ba za su taɓa daina baƙin ciki da kukan takaici ba, yana jin kunyar wai yanda waɗannan ƙannen nasa da yafi ƙaunar su fiye da komai a duniya za su fuskance shi akan kalmar haƙuri akan abin da ba su da masaniya akai kamar yanda shima ba shi da ma saniyar.

Haƙiƙa Hajiya, Alhajin su, Baba Ustaz, da ma sauran dangin su kaf da suka san wannan maganar suka ɓoye masa ita ba su yi masa adalci ba.....to shi ɗin wai ina mahaifiyar sa kenan? Wacece ita? Idan har ace ta mutu to bata da dangi ko ɗaya na kusa ko na nesa da bai taɓa sanin ko mutum guda ba? Ya san dangin Alhajinsa ya san dangin Hajiya ƙwansu da ƙwarƙwatarsu, to shi ina nashi dangin mahaifiyar suke? Idan sau nawa zai tuna maganar nan cewa wai tsawon shekarun da ya shafe a duniya sai yanzu yasan cewa mahaifiyar da ta kawo shi duniya ta rasu amma bai taɓa sani ba sai yanzu sai ya ji hankalin shi ya yi mummunan ta shi? Mine ne amfanin rayuwar sa tsawon lokacin nan da bai taɓa yin addu'a koda ta rana ɗaya ce a gareta ba ko da cewa ne Allah ya gafarta mata ya bata Aljanna! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!! Manzon Allah (S.A.W) fa ya faɗa cewa a duk lokacin da ɗan Adam ya mutu gabaɗaya ayyukansa yankewa suke sai abu uku kawai da za su rage masa a bayan ƙasa su ne;Sadaƙatul jariya da ya yi wacce Allah ya karɓeta da za ta ci gaba da gudana bayan mutuwarsa ladar tana kai wa zuwa gare shi, sai ilmin da ya bayar ga al'umma ya ci gaba da amfanuwa da wanzuwa shima ladar na kaiwa gare shi, sai kuma na ukun yace Al-waladun salih! Idan ya bar Yaro na gari a duniyar wanda zai riƙa yi masa addu'a...sannan ga ayoyin Allah nan a cikin alƙur'ani mai girma da Allah yace a yiwa iyaye biyayya kuma a yi musu addu'a musamman idan ya tuna a cikin suratul Isra'i Ayar da ta ce; Ka sassauta musu fuka-fukan ƙasƙantawa saboda jinƙai. Sannan ya ce Ya Ubangiji, ka yi musu rahama kaji ƙansu kamar yanda suka raine ni sanda nake ƙarami.!

Koda ace tana haihuwar shi ta mutu ai ta ɗauki zafi da wahala na laulayi da naƙuda har lokacin da ta haife shi kuma....kuma ga shi ma a lokacin haihuwar ta sa ne ta mutu...Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! A yanzu ina amfanin rayuwar sa? Shekaru arba'in da wani abu a duniya amma bai taɓa yi mata addu'a ba! Shi ɗin kwana nawa ne ya rage masa a duniyar? Kai co!'

Wani irin firgigit na yi cikin tashin hankali na miƙe zaune jin ƙarar sautin kuka a saman kaina.

Zaune na gansa a gabana yasa hannayensa ya dafe kansa tamkar wanda saƙon mutuwar sa ya riske sa a yanzu.

Cikin zafin nama na janyo hannayensa ina jin wani sabon tausayinsa na ƙara yi wa zuciyata, murya a raunane na ce.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ka yi haƙuri! Dan Allah ka yi haƙuri Yaya Muhammad! Ka tuna fa kai musulmi ne wanda ya yi imani da ƙaddara....halin da kake ciki yana ɗaga hankalina yana sa ina jin raɗaɗi da ƙuna a cikin zuciyata.....Dukkan wata rayuwa tana tafiya ne tare da jarabawa wanda duk wata dukiya, mulki, talauci ko sarauta wallahi ba su isa su hana abinda Ya rubuta maka ya same ka ba.... Shin ka ɗauka cewa kai ka ɗai ne allon ƙaddara ya taɓa birkitawa haka? Ba kai ka ɗai bane Yaa Muhammad....... "

Daga hana na zuro Ƙafafuwana ƙasa na sauka na je banɗaki na yo alwala na zo na gabatar da sallahr Asuba, ina kambalawa ban tsaya doguwar addu'a ba na miƙe na je na kwanta jikin sa a hankali na ce.

" Ka yi haƙuri....Idan kana kuka, ji nake kamar zuciyata za ta fashe akan ƙunci da takaicin jin cewa na gaza wurin kulawa da kai. Ka riƙa tunawa cewa mutane da yawa a duniya suna cikin jarrabawowin da idan ka ji labarin wani sai ka ji cewa kai duk da haka a Aljanna ka ke. Ka yi haƙuri, Allah da kansa ya cewa manzon Allah (S.A.W); Ka yi haƙuri, haƙuri mai kyau. Kuma sai ya yi haƙurin ya ci riba mai girma. To saboda haka, ina so ka yi koyi da masoyinmu, shugabanmu annabin Rahma (S.A.W) ka yi haƙuri kuma ka mayarda al'amarinka ga Allah, in sha Allahu ya isar maka...Sannan kai fa ɗin nan jajirtaccen Yaya ne kuma Uba, idan ba ka ƙwarara kanka ba ta ya ya za ka iya ƙwarara waɗanda suka ɗauke ka jigo kuma tsayayyen Uba a gare su....."

Haka na yi ta faɗa masa kalamai ma su daɗi da sanyaya rai har Allah ya ɗorani a kansa na ji yayi shiru.

Muna nan a haka daga ni har shi babu wanda ya sake runtsawa har misalin ƙarfe bakwai da wani abu sannan ya miƙe a hankali ya zameni yana faɗin.

" Ta shi ki je ki shirya za mu fita."

Saukowa na yi a hankali na wuce ɗakina na yi wanka na fito na mulke jikina da mayukan da ya kawo masu daɗin ƙamshi da sanya nutsuwa, sannan na ɗauko sabuwar bra na buɗe na zaɓa size ɗina saka, daman tun da muka iso da na yi wanka na cire wadda na zo da ita ban sake sakawa ba sai yanzu, Allah na tuba breast ɗin nawa ma gudawa nawa ne? Akwai su amma ba lallai ina buƙatar bra ɗin ba tun da ba wani girma ne da su sosai ba kuma ga su a tsaye....bayan na saka na saka pant da wani cotton under skirt mai azabar laushi da kyau sannan na shirya cikin wata rantsatsiyar Abaya C-green wacce ta yi matuƙar amsar jikina. Bayan na kambala na sake buɗe wasu turarrukan bayan wanda na buɗe jiya na tuttulasu a jikina domin da alama yana masifar son ƙamshi... Ko da yake waye baya son ƙamshi ma a duniyar nan? Amma dai shi ɗin na musamman ne domin turaruka ne wanda ban taɓa sani ma da akwai su ba a faɗin duniyar nan ba.

Fitowa na yi naje na karɓo abin kari na dawo ɗakinsa inda na cimma sa shima ya shirya cikin manyan kayansa na wani rantsatstsen yadi fari ƙal da hula da takalmi ya fito shar da shi wanda muna haɗa ido lokaci ɗaya na ji zuciyata ta tsinke ba shiri na yi ƙasa da kaina domin ba ƙaramin ƙwarjini ya mini ba sosai haibarsa ta cika idona.

Zaunawa ya yi akan Sofa wanda da alama zaman yana da nasaba da shigowar da na yi ganina ɗauke da tray. Wani ƙaramin glass table na janyo na ɗora a kai a hankali na ɗan kalle sa na ce.

"Bismillahi!"

Kafin ya yi maganar da ke bakinsa don da alamar kallon da yake mini yana da ra'aya yasa na miƙa hannu na ɗauki ɗayan Tea cup ɗin na shanye Sannan na ɗauki spoon na ɗan tsakuri sauce ɗin Indomien da aka haɗata da nama da kuma veggies na kai bakina. Jin yanda ta yi daɗi yasa na zage ina ta kaiwa a hankali wanda tun ɗazu shima yana shan Tea ɗin da toast bread yana kallona. Bayan ya cinye one piece na toast bread ɗin ya ci yam ball ƙwaya biyu sannan ya ɗauki bottle water ya buɗe yasha sannan ya ajiye ya kalleni karon farko ya jinjina kansa da ɗan murmushi a hankali ya ce.

"Thank you."

Daga haka ya miƙe ya shige banɗaki. Nima dai bayan na gama na tashi na fice da kayan sannan na koma ɗakina na wanke bakina na ɗan ƙara gyara hulata da ke ta zamewa sannan na gyara rolling ɗinda na yi na fito muka haɗe a parlour muna nufi hanyar fita wanda yana gaba ina bayan sa har muka isa mota. Nan muka tarar da guides ɗinsa tsaye tamkar wasu saƙagai suna ta kwasar gaisuwa da muka fito sannan suka buɗe mana muka shiga.

Shiru ne ya ratsa tsakaninmu wanda yana kallon wata 'ƴar computer da ke gaban sa yana aiki ni kuma ina kallon waje har muka isa Nigerian Immigration Service (VIP Channel) muna shiga wani office muka nufi wani table inda aka rubuta VIP Consular Desk inda muka tarar da wani managern sa na reshen kamfaninsa Golden pathways dake nan Abuja Abdul-Kareem wanda suke kira da Mr. Kareem har ya riga mu zuwa yana zaune yana tattaunawa da Jami'in.

Cike da girmamawa suka gaisa wanda ni dai ban yunƙurin gaishe su ba, domin idan akwai buƙatar hakan wata ƙil da yace na gaishe su a fahimtata.

Bayan sun gama gaisawa ne ya faɗa mishi cewa an cike application form na E-passport da bayanan biometric yanzu thumbprint zan yi da kuma ɗaukar hoton fuskata. Ya faɗa masa cewa an biya service fee Sannan ya miƙo masa receipt mai ɗauke da official stamp. Sannan ya ce an duba identity document, birth certificate da letter of sponsorship daga Golden pathways Wanda ya nuna dalilin tafiyar na business and residency a Dubai.

Nan suka ci gaba da tattaunawa, bayan na gama komai da ake buƙata sai ga wani ya shigo ya miƙawa Mr. Kareem ɗin letter to authorization daga kamfanin Dubai branch tare da e-visa confirmation da aka fitar ta Hanyar MISA/Government liaison na kamfaninsa na Golden pathways.

Bayan mun kambala muka fito muka je offishin Customs for Checks-up wanda a nan ma already Mr. Kareem ya gama komai, nan aka bamu wasu takardu muka cike tare sannan na yi signing shi ma ya yi, sai kuma health clearance letter da ya karɓo daga prestige Clinic a matsayin proof of fitness for traveling. Nan suka sake yi min general health screening da Komai da komai sannan daga ƙarshe aka bamu travelling declaration. Bayan mun kambala sai misalin 2pm muka koma gida.

Haka muka rayu tsawon wasu kwana yana ta min shirye-shiyen ni dai iya ka ta ido sai idan an ce in yi sannan zan yi. Haka muke zaune kamar wa su kurame domin sai abu ɗaɗɗaya ne yake sa muna yin magana da juna. Amma kuma a tare muke bacci baya taɓa barina ni kaɗai kuma ko zaune muke wani lokacin yafi son ya jini ina cikin jikin sa koda kuwa magana bata haɗamu ba. Idan ka ji maganata to waya nake da su Ammie amma shi tunda muka taho banga ya yi magana a waya ko ta second ɗaya ba, wannan wayar number ɗaya ce a cikinta ta Ammie wanda ban sani ba ko yana da wata wayar daban da yake magana da su Aunty Labiba.

Yau ma muna tashi bayan mun yi sallah ya shirya ya fita ko karyawa bai yi ba kuma bai dawo gidan ba sai misalin ƙarfe biyar na yamma. Yana shigowa karo na farko kenan da na buɗe baki na ce.

"Sannu da zuwa!"

Jinjina kansa ya yi yana ɗan murmushi ƙasa-ƙasa ya ce.

"Na barki ke ɗaya ko? I'm sorry...."

Nima murmushin na mayar masa, cike da ƙarfin hali na ce.

"Ya kamata ka ci abinci..."

Hannuna ya janyo yana faɗin.

"Thank you...but I'm sorry,kan hanya muke a yanzu, idan mun samu dama sai muci a hanya. Ya yi miki?"

Jinjina kaina na yi na ce.

"Ba laifi. Duk yanda ka yi dai-dai ne."

"Ok to! Bari in ɗan yi wanka, kema idan kina buƙata ki je ki shirya kafin na fito...."

Girgiza kaina na yi na ce.

"Ban ji ma da yin wanka ba...za ka iya zuwa ka fito...."

Ɗan tsagaitawa na yi kaɗan har ya juya sannan na ce.

"Ina so in yi magana da Aunty Labiba..."

Wata irin faɗuwar gaba ya ji lokaci ɗaya jin kalmar sunan Labiba... Labibar sa, ƙanwar sa mai son ganin farin cikinsa. Ita ɗin bayan Hajiyarsa tana da wani irin matsayi ne a zuciyar sa. Tana da matuƙar kirki da hankalin da har abada ba zai daina alfahari da ita ba. A lokacin da ya cika 40years ya shirya buki a Dubai inda ya gayyace kowa da kowa aka yi shagali sannan ya bata Kambu (award) ya naɗata jakadiyar wanzar da zaman lafiya na kamfanin sa na GOLDEN PATHWAYS (Peace Ambassador).

'A yanzu ko a wanne irin hali take ciki bayan ya baro ta? Yanda za su nun karaya su ji kunya akan al'amarin Hajiya shi ne abin da baya son gani a rayuwar sa. Ya zai yi idan Labiba ta durƙusa a gabansa da kuka a idonta wai da sunan ba shi haƙuri...! 'Kai duniya! Wallahi Hajiya ta cutar damu. Ta rusa mana gida ta rusa mana farin ciki. Emraan,' ƴar rigimarsa Nadeeyah sannan masoyiyar er Auta Hairiyya.' Ya tuna ranar auren da ta tuma ta ɗane bayan sa wai bari ta ƙara shanye daɗin bayan Daddy kafin yaran da Mummy NANA za ta haifa musu su yi mata cin layi.....

Ganin yan da hawaye suka cicciko idonsa yasa na yi saurin girgiza kaina na ce.

"Ka yi haƙuri idan maganata ba ta yi maka daɗi ba.."

Janyoni ya yi a hankali ya yi kissing forehead ɗina lightly Sannan ya wuce ɗakinsa ya buɗe bedside drawer ya ɗauko wayar da yake magana da su ya kunnata ya cire mata passwords gabaɗaya ya miƙa mini sannan ya juya ya koma ciki.

Tun da ya miƙo min messages suka shiga shigowa ɗaya bayan ɗaya sun kai guda talatin wanda babu suna guda ɗaya da na gane a ciki.

Ban buɗe ba domin ba hurumina ba ne. Contact na shiga ina neman sunan Labiba amma kuma ban gani ba. Hakan yasa dole na haƙura. Koda ya fito batun ƙarfe shida ake. Hakan yasa a gaggauce ya kalleni ya ce.

"Zamu iya tafiya.?"

Jakar hannun sa na karɓa ina jinjina masa kaina alamar eh.

Bayan mun shiga mota mun zauna na miƙa masa wayar ina faɗin.

"Banga numbern ta Aunty Labiba ba..."

"Ok."

Abin ya ce kenan tare da karɓa wayar ya ajiye ta a gefen sa wanda sai da muka isa Airport ɗin ne sannan ya kama hannuna ya sanya wayar yace na zauna a motar yana dawowa yanzu.

Bayan ya fita na danna wayar sai naga an rubuta 'my peace' akan wata number, hakan yasa na danna kiranta wacce da alama ita ce ya kamo mini.

Ringing ɗaya zuwa biyu na ji muryar Aunty Labiba cike da kuka ta ce.

"Yayah..!!"

Wata irin doka wa ƙirjina ya yi. hankalina a tashe na ce.

"Aunty Labiba..."

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali itama ta ce.

"Beenafah...! Beenafah ina Yaya?"

"Ga shi can ya fita yanzu, ina zaune a mota ne ina jiran sa, ya ce min yana zuwa yanzu....."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull