Ganin ido complete Novel - Chapter 40
Ganin ido complete Novel Chapter 40: Ganin ido complete Novel Chapter 40. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta jinjina kai tamkar ina a gabanta ta ce.
3,368 words
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta jinjina kai tamkar ina a gabanta ta ce.
"OK."
Shiru ne ya ratsa tsakaninmu wanda a tunanina yanda na rasa abun faɗa itama haka ne a wurin ta. Da ƙyar na ƙaƙalo wata maganar can ƙasan maƙoshina ina mai jin wa su siraran hawaye na jin cewa ban kyauta ba a raina a hankali na furta mata cewa.
"Ku yi haƙuri Aunty Labiba ku yafe mini! Idan har na zama sanadin rugujewar farin cikinku dan Allah ina neman gafararku...."
"Haba Beenafah! Dan Allah ki daina ma wannan maganar...babu abin da kika aikata. Ina matuƙar alfahari dake. Ki kula min da Yayana sosai kin ji ko,shi ɗin tamkar mahaifi yake a gare ni wani ɓangaren. Na san ki, ke ɗin jaruma ce ta gaske, na yarda da cewa za ki iya. Dan Allah kada ki bari ya shiga wani ƙunci, na ba ki amanar sa. Shi ɗin bai san kowa ba idan ba mu ba, idan baya tare damu aikinsa shi ne abokin rayuwar sa, amma yanxu ke ɗin kin maye gurbin komai da kowa...Allah ya ba ki ikon kulawa da shi... In sha Allahu komai zai yi daidai watarana."
Tun ina iya sarrafa sautin kukana har ta kai ga na kasa riƙe kaina, sosai nake kuka ina jinjina kaina tamkar ina a gabanta na ce.
"In Sha Allahu Aunty Labiba..."
Daga haka ta yanke kiran. Wallahi na ji tausayinta sosai har cikin zuciyata. Sai nake jin cewa kamar abin da na yi ban kyauta ba, dama na bari ya sake nin da yanzu hakan ba ta faru ba. Na jima kusan 30mnt sannan ya dawo. Da sauri na goge fuskata ina mai ƙirƙiro murmushi don kada ya fahimci cewa na yi kuka. Shigowa motar ya yi a nutse ya kalleni ya ce.
"Ina fata kina lafiya?"
Jinjina kaina na yi ina mai kawar da kallona gefe na ce.
"Alhamdulillah! Da fatan kaima haka?"
"I'm fine..."
A hankali motocin suka fara tafiya zuwa can cikin sannan muka fito a tare muka wuce. Muna isa wurin wata glass window Haroun ya miƙa wata takarda ya ce.
"She has been cleared under diplomatic Company sponsorship....Manifest will be forwarded to King Khalid private Terminal."
Jinjina kai Officer ɗin ya yi sannan ya miƙo masa takardar clearance muka wuce muka sake shiga motocin. Private Aviation Terminal (Fixed Base Operator) muka nufa inda aka buɗe mana wani gate zuwa tarmac wanda yake private ne ma'ana wuri ne na musamman for special people only. Hannunsa riƙe da nawa muka iso wani haɗaɗɗen lounge mai private check-in counter muka zauna.
Bayan mun yi sallar Magrib da Isha, Iyakar mu 15mnt muka tashi muka wuce wurin wani private jet na musamman da aka rubutawa The 'Golden Falcon X9 MAA' (Muhammad Attahiru Araam). A bakin stairs ɗin hawa jirgin wata flight attendant ta miƙo min hannu tana murmushi ta ce.
"Welcome Ma'am.."
Murmushin na mayar mata na ce.
"thank you."
Daga nan ya jinjina kai yana mai ƙara maƙalƙale hannuna a nasa ya ce.
"Kada ki damu, tare zamu shiga ni da ita....."
Sai da jami'an tsaron sa suka fara shigewa su huɗu sannan su Sharath suka shige sannan mu da kuma wasu guides ɗin sa biyu.
A wani private suite muka shige inda luxurious club seat muka zauna Wanda yake ɗauke da komai na jindaɗi da more rayuwa.
Kallona ya yi a hankali ya jinjina kansa ya ce.
"Wannan jirgi na ne, when ever you wish,he will take you around the world...yanzu zamu tafi inda nake zaune da kasuwanci na a United Arab Emirates, that's Dubai.."
Murmushi kawai na yi masa ina ƙara jinjina girman abin a raina. Wato shi ɗin wai har jirgi yake da shi. No wonder Hajiya da su Hairi suka maida tafiya ba a bakin komai ba.
A hankali bayan an gama komai jirgin ya fara tafiya yayin da na lumshe idanuna na nutsu ina addu'a har ya gama daidaita a sararin samaniya. Nan aka gabatar mana da light meal muka ci Sannan bayan mun kambala ya rungumeni shiru ba tare da ya yi magana ba.
Bayan tafiya mai tsawo wanda har na yi bacci na tashi sai gashi mun isa ƙasar cikin amincin Ubangiji. Flight attendant ɗin nan ta ɗazu ita ce ta sake dawowa ta kawo min Immigration forms na UAE mai ɗauke da landing cards da declaration slip. Nan ya karɓa ya rubuta sunana, passport number, da kuma full address ɗin gidansa da yake zaune a ciki. Muna saukowa muka fito sai ga welcoming delegates daga Golden Pathways Dubai sun tsaya a bouquet da murmushi cike da girmama suka shiga yi mana sannu da zuwa.
A yau babu abin da nake idan ba murmushi ba, duk da cewa wannan tafiyar ba ita ce tafiyata ta farko a jirgi ba, ta bar min wani tarihi na musamman. Daman kuma shekara nawa da hawana jirgin? Komai ganin sa nake tamkar a mafarkina ne yake faruwa. Ga shi duk inda muka saka ƙafa hannuna na maƙale a cikin nasa lokaci bayan lokaci yana tambayata da fatan ina lafiya.
Nan muka shiga motoci exact irin waɗancan da muka hau a Nigeria zuwa gida.
*********
Aunty Aysha kuwa, sai da ta share wata ɗaya gidan Ammie sannan ta shirya daga can ta wuce gidan Hassana. Sosai ta yi farin cikin yanda ta tarar da ita domin Alhamdulillah tana zaune cikin rufin asiri bama kamar yanda suka tsamma ta ba, duk da dai idan da ace Mummy za ta zo to tabbas babu abin da zai hana zuciyarta bugawa akan baƙin ciki, domin gidan ƙofa ƙarama ko gate babu.
Daman Aunty Aysha ta faɗawa Uncle Isma'ila cewa ta samu labarin Ammie,yana jin wannan labarin ya nemi da ta faɗa masa inda take ta ce mishi tayi alƙawari ba za ta faɗa ba. Kawai ta faɗa mai ne idan har zai iya ya faɗamata saƙon sa ita kuma ta yiwa alƙawarin za ta mayarwa Ammie.
Hakan yasa ya tura kuɗin direct babu ya ce ta bata kuma ta roƙa masa gafarar ta.
Bayan ta faɗawa Ammien, murmushi kawai ta yi tana tuna yanda ya wulaƙansu a ranar da suka dawo daga asibiti sannan ta ce mata ta turawa Malam Habibu 5M Babansu Ya Jafaru ya ja kasuwa, sannan idan taje gidan Hassana ta bata 6M ɗin itama ta dogara da kanta kada taje can watarana rayuwa ta yi wahala su Mummy su kasa taimaka mata.
Mamaki ne ya kama Aunty Aysha na cewa wai ga baki ɗaya ta rabe kuɗin kuma ta faɗawa Uncle Isma'ila cewa ta yafe masa duk abin da ya samu sama da kuma duk laifin da ya mata. Hakuri ta bai wa Aunty Ayshar ta ce, duk abinda zai sa ta tuna da zamanta a gidan Daddy Mudassiru to bata ƙaunar sa har abada. Kuma ma ai sadaka ta yi ba wani abu ba.
Baba da mamakin Fakiha Mota suka ɗauka sukutum har Sokoto wurin yi mata godiya har da kukansu. Ga shi daman har da Jafaru suka je da Ya hamza. Ya so ganin Beenafah koda sau ɗaya ya tayata murna amma cikin rashin sa'a akace sun wuce inda Mijinta yake aiki. Yanda ya ji haka ya faɗawa Ashiru wanda yanzu sosai suke abota da juna wanda da kanshi yake bai wa Ammie labarin Ashirun na cewa tun da ya ji labarin auren Beenafah bayan ya gama jimaminsa ya koma Kano ya ci gaba da kasuwancinsa tare da mantawa da wasu abubuwan amma dai ta kasa mantawa da Beenafah.
Hassana kuwa, yi ta yi tamkar za ta yi hauka akan kuɗin da Ammie ta aika mata. Kuka sosai take da hawayenta tana tuna irin gudummawar da ta bada wurin wulaƙanta Ammie da Beenafah. Hatta Bahrain tasha dukan sa haka kawai ba tare da ya yi mata laifin komai ba. Yanzu ga shi ta turo mata kunyarta ta aiko mata da kuɗinda ko mutuwa za ta yi tasan Mummy da Daddy ba za su iya bata ba.
Nan ta ɗauki 4M ta baiwa Salman ɗin ta je ya buɗe private clinic ya zuba magunguna ita ma sai ta shiga juya 2M ɗin su gani.
Suna kan kassafa kuɗin kawai Aunty Aysha ta fashe da kuka tana kallon Salman ɗin ta ce.
"Haƙiƙa ka bani tausayi daga kai har ita, amma kuma ƙwarin gwiwa da jarumtar da ka nuna sun burgeni kuma na ƙara ji a raina cewa ka dace da ƙanwata. Haɗuwarku ne da taimakon Allah yasa ta shirya daga munanan halayen da take. Allah ya baku zaman lafiya ya baku zuriya ɗayyaba sannan ya sa albarka a cikin kasuwancin ku."
Rungumeta Hassana ta yi tana ta wani kuka cike da nadama ta ce.
" Aunty Aysha ku yafe mini dan Allah....yanzu haka ina ɗauke da juna biyu na 6weeks...A yanzu daga ke sai su Hajiya Ermama kawai nike da, ke ce uwata.... Dan Allah ki yi min alƙawarin cewa idan na haihu za ki zo..."
"Insha Allahu na yi alƙawari Hassana.... Ina roƙon ubangiji ya bani ikon cika wannan alƙawarin. Ki kula da kanki kuma ki kula da shan magungunan ciki kin ji ko musamman na ƙarin jini da abinci mai lafiya don gujewa matsala.. Kuma duk abin da kike so kada ki ji shakka kawai ki kirani kin ji ko..."
" In Sha Allahu Aunty Aysha. Na gode sosai Allah ya saka da alheri ya bar zumunci."
Kwana ɗaya ta yi wanda duk sai da suka zaga dangin Salman da ita ta gansu suka gaisa sannan ta juya ta koma Abuja ba tare da sanin Su Mummy ba ta hau jirgi ta yi tafiyar ta London.
********
Daddy kuwa, daman unguwar da Ammie suka bari ta gusau, can yaje tamkar wani taɓaɓɓe yana ta bin mutane duk wanda ya haɗu da shi yana tambayar sa wai ko yasan Hajiya Mulaifa sannan da kuma wanda ya auri Beenafah.
Ya daɗe yana wahala bai samu bayanin komai ba. Sai daga ƙarshe Allah ya taimake shi ya samu wani yaron da ya ce ya san su amma kuma sai idan za su yi jinga ya biyasa shi kuma zai kawo masa Ammie da Beenafah da ma mijin da ta aura.
Kullum yanzu cikin bauta masa yake yana tura masa kudaɗe, ko a katin waya kawai a yini yana tura masa na 10k banda dubu dari biyu dubu dari wai duk na hawa abun hawa ne kafin ma su gama yanke abin zai ba shi.
Bayan ya tabbar masa cewa idan ya samosu zai faɗa masa sannan ya tura masa da kudadensa shi kuma ya zo ya kawo masa su.
Yana kan hanya ya fito daga Kaduna wurin ɗaurin auren ɗiyar abokinsa zai koma Abuja ya kira shi. Wuri ya samu jiki na rawa ya yi parking ya fito ya kira shi back yana faɗin.
"Ado ka samo su ne?"
"Eh Alhaji...aiki ya cika. Ka turo da kaya nima in turo maka su..."
Bai ankare ba ya ji saukar Itace an rabka masa a bayan ƙeyar kansa. Ɗaya daga cikin mutanen da suka Parker mota ne su uku suka buɗe gabanta suna gyara.
Haka Daddy ya zube luuu! Yana kiran. " Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.! An samo min Mulaifa... Dan Allah ku bari a kawo min tsinanniyar matar nan.."
Wani irin wawan naushin ne ya sake kai masa sai ga Daddy ya sume. Cikin uxuri suka karɓe Key ɗin motar tare da lalabe wayoyin sa da duk abunda yake da suka ajiye masa key ɗin kwaraɓaɓɓiyar motar su suka shige tasa motar suka tsere suka bar shi nan kwance a dajin.
*********
Gefen Hajiya kuwa, duniya ta yi mata zafi kowa ya guje ta akan abinda ta aikata. Hairi ma da ta rage mai goyon bayanta ta shirya ta koma makaranta.
Hatta su Hajiya Samiya da ta sanar da su cewa asirinta ya tonu ko kaɗan ba su yi gigin sake tahowa inda take ba, domin sun sani ko Emraan ya ɗaure su sai sun kusa mutuwa kafin a samu mai karɓo su ballantana Muhammad.
Sai yanxu ta tabbatar cewa duk wanda ya biyewa ƙawaye da son zuciya to wallahi tabbas yana cikin halaka...yanzu ga shi sun taimaka mata wurin aikata ɓanna amma yanzu da suka ji asirinta ya tonu sun zame sun barta.
Ta kasa daina kuka...wannan abun kunyar wallahi kullum sabo yake dawo mata a zuciya. Ta yi kewar Muhammad Sosai, gabaɗaya 'ƴa' ƴanta da Hajiya suke kiranta shi kaɗai ke mata 'MOMMA' kuma har yanxu ba daina ba. Haka zai zauna ya ɗora kan shi akan ƙafarta yana kuka wani lokacin akan damuwar sa. Baya cikakken yini ba tare da ya ji muryarta ba. Baya iya jure tsawon lokaci ba tare da ya ganta ba. Sirrin rayuwar shi kaso saba'in cikin ɗari ta fi kowa sanin shi. Komai zai yi sai ya kirata ya nemi shawararta, idan kudi zai bayar sai ya kirata, idan wata kasuwa zai yi sai ya kirata. Amma yau ga shi babu Muhammad a tare da ita saboda zunubinta.
Ganin tsawon lokaci gabaɗaya su Labiba babu wanda ya waiwayeta yasa ta shirya cike da kuka da baƙin ciki ta cire kunya tasa Oga Sule ya ɗauketa Zuwa gidan Baba Ustaz Abuja.
Tun da suka isa take masa kuka, ko ruwa da Mummy Na'imatu ta kawo mata kasa sha tayi. Hankali tashe ya shiga tambayarta dalilin kukanta.
Zamowa ta yi ta zauna ƙasa tana kuka sosai tana faɗin.
"Alhaji Ustazu da kunyar lahira gwanda ta duniya....haƙiƙa na aikata wani zunubi..."
✍️ *OUM-AMEER* ✍️
*GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....
*PAGE 37*
"Na cutar da ɗan da ya yarda dani Alhaji Ustaz, na jefa rayuwar sa cikin hatsari da wahala..."
Nan ta zayyane masa duk abin da ya faru bata ɓoye masa komai ba har abin da ya faru ranar da aka kawo Beenafah. Bayan ta kambala faɗa masa ta kalle shi da wata irin damuwa ta ce.
"Alhaji Ustaz! Kai ɗan uwan mijina ne,tsawon shekarun nan, tun Alhaji na raye da ma bayan ƙasa ta rufe idonsa, daidai da rana ɗaya ba ka taɓa nuna min wani hali na musgunawa ko kuma cutarwa ba......"
A gigice ya miƙe yana mai jin wata iriyar zufa na keto masa ta ko'ina ya ɗaga mata hannu ya ce.
"Ke.. Ke! Hajiya Batula dan Allah dakata! Yanzu kina nufin daga ke har Margayi babu wanda ya taɓa faɗawa yaron nan cewa mahaifiyarsa da ta haife sa ta rasu ba? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
"Wallahi sharrin shaiɗan ne..."
"Sharrin ki dai Hajiya Batula! Sharrin ki dai... Kuma duk abin da ya faru na ɓoye masa wannan maganar da kuka yi tabbas makircin ki ne..."
Share hawayenta ta yi ta shiga gyaɗa kanta kamar wata mai motsin ƙwaƙwalwa tana faɗin.
"Wallahi ba laifinsa ba ne, duk ni ce na shirya hakan, don ya mutu kuma ba zan masa ƙazafi ba. Ni ce nan na shirya hakan na rokesa akan kar mu faɗa masa gaskiya don kada ya wayi gari ya yi kukan maraici ko ya riƙa jin idan ya yi wani laifin na yi masa hukunci kada ya riƙa jin cewa don ba ni na haife sa ba ne....wallahi a farko lafiya ƙalau nake zaune da shi a raina, ban taɓa cutar da shi ba, wannan ne kawai kuma na yi ne saboda.... "
" Kaicon ki Hajiya Batula! Wallahi Kaicon ki! Kinci amanar wannan yaron, kin ci amanar mijinki da ya yarda dake sannan muma kin ci amanar mu kin zubar mana da mutunci....sannan kin san wani abu? Wannan abun da kika aikata zai ɗauka cewar duk da saka hannunmu hakan ta faru don kawai mu gaje dukiyarsa..."
" Na yarda, na kuma amsa laifina amma don Allah Alhaji Ustaz ka taimakeni wurin shawo kansa da basa haƙuri...gabaɗaya su Emraan sun guje ni kuma na san sun tsaneni akan wannan kuskuren da na aikata... Wallahi tallahy bana iya bacci. Zuciyata ciwo take, na rasa ina zan saka kaina. Ka taimakeni wurin daidaita wannan abun... "
Cikin wani irin jin sabuwar tsanarta a zafafe ya nuna mata ƙofa yana faɗin.
" Ta shi ki fice mini daga gida! Ta shi na ce.. "
Cikin tausayawa matar sa Mummy Na'imatu ta saukar da murya ta ce.
" Haba Alhaji! Ka yi haƙuri mana.. "
" Ke! Babu ruwan ki a cikin wannan maganar... Ta je can ta samu en uwanta ta faɗa musu.... Su san yanda za su yi da ita. Ai tasan da cewa akwai irin wannan ranar kul ba daɗe kul ba jima, idan ma nan gidan duniya asirin nata bai tonu ba to akwai gobe alƙiyama inda wani wayonka ko basirar ka ba za su amfana maka komai ba....saboda haka taje can ta ƙara ta..."
Cike da magiya ta haɗe hannayenta ta ce.
" Don Allah ka yi haƙuri ka rufamin asiri kamar yanda Allah ya rufa maka ka taimaka min wurin ba shi hak'uri da shawo kan 'ƴa' ƴana, wallahi tallahi idan har dangina suka ji wannan musamman Alhaji Ɗan-Ladi akwai matsala..."
"Ba dole ki shiga matsala ba Hajiya Batula! Idan baki san halacci ba ai su sun sani tunda ya ɗauke su da muhimmanci da daraja babu abin da suka nema suka rasa na rayuwa...amma ke da yake baki san girman amana ba ga shi son zuciya ya kai ki ya baro ki...."
Ɗan tsahirtawa ya yi da maganar sannan ya girgiza kan shi cike da takai ci da baƙin cikin tuna yanda aka yi ta wahala aka yi ta faɗi tashi wurin neman masa aure da magani, ya ce.
" Kai duniya! Wallahi Hajiya Batula kin ci amana. Ko kaɗan ba ki da imani ba ki da zuciyar musulunci! Kuma zaluncin da kika yi wa wannan yaron ki saurari sakamakon ki daga wurin Allah domin girman haƙƙin sa ba zai bar ki ba..."
Cikin jin wani irin sabon tsoron da ya ta so ya lulluɓe zuciyar ta yasa ta sake fashewa da kuka tana faɗin.
" Wallahi na tuba! Na tuba Alhaji Ustaz... "
Girgiza kansa ya yi ya ce.
" A'a kam! Ba ki tuba ba, domin ba don Allah ya jefa wannan yarinyar ta jiyo bakin zaren ba har ta yi namijin ƙoƙarin taimaka masa ba da yanzu yana nan a yanda yake ba ki yi tunanin daina cutar da shi ba... "
Daga haka ya wuce kai tsaye ya shige ɗakin sa ya barta nan tana ta kiran sunan sa cike da kuka tana roƙonsa.
Mummy Na'imatu ta kalla a rauna ne ta ce.
" Dan Allah Hajiya Na'imatu ki taimaka mini akan wannan maganar. Alhaji Ustaz shi kaɗai ne wanda zai iya taka min na samu na shawo kan wannan matsalar...."
"In sha Allahu zan masa magana. Ki kwantar da hankalinki komai zai dawo ya wuce."
Daga haka ta miƙe taje ɗakin nasa wurin ba shi haƙuri ƙarshe haka ya kore ta itama yana mai balbaleta da masifa. Wasa-wasa sai da ta share kusan kwana uku sannan da ƙyar Hajiya Na'imatu ta samu ta shawo kansa ya amince cewa zai yi magana da Mohaan da kuma su Emraan ɗin. Amma dai ta shirya ta koma gida domin baya ma son yana ganinta a kusa da shi.
********
Gefen Daddy kuwa. Bayan anyi nasarar ce to shi zuwa asibiti sai da ya kwana ɗaya sannan ya farfaɗo daga nan aka samu aka kira Mummy, sai gashi ta iso asibitin a gigice. Ganin yanda ya yi wani shaɓe-shaɓe akan gadon yasa ta ƙara gigicewa tana faɗin.
"Miye ya faru haka Alhaji?"
A hankali ya yunƙura ya miƙe zaune yana mai jin wani sabon zugin a kwankwason sa ya kalle ta a wahalce ya ce.
"Wallahi Ado ne ya kirani akan zancen Mulaifa, shi ne fa na ratse gefen hanya na fito domin yin magana da shi, ashe akwai wa su yaran banza a nan gefena da suka tsaya kamar motar su ce ta lallace suka shamma ce ni suka bugeni suka karɓe mukullin motar da wayoyina da komai suka gudu.... "
Wata irin zabura ta yi a gigice ta bugi ƙirji tana gwalo ido kamar na mota ta ce.
" Wace Motar kake magana Alhaji???"
"Wannan dai motar ta wa wacce Alhaji Mansur Anka ya siya min..."