Kenza eBookz

Ganin ido complete Novel - Chapter 41

Ganin ido complete Novel - Chapter 41

Ganin ido complete Novel Chapter 41: Ganin ido complete Novel Chapter 41. A gigice ta ɗora hannu a kai tana faɗin.

3,348 words

A gigice ta ɗora hannu a kai tana faɗin.

"Wayyo Allah mun shiga uku mun lalace!!!"

"Haba Mummy dan Allah miye haka? Tun da har ba su yi masa komai ba ya samu ya tsira da ransa ai sai mu godewa Allah."

Cewar Husaina tana mai saukar mata da hannun da ta ɗora a kai.

Girgiza kai ta yi cike da kuka tana kallon Husainar ta ce.

"Husaina kin san ko motar miliyan nawa ce? Wannan mummunan labari da mi ya yi kama? Akan me zai tsaya gefen hanya inda yake da ji ba kowa ya ce wai zai yi waya in ban da dai shafewar basira.."

"Mummy ƙaddara ce! Wallahi babu wanda ya isa ya kauce wa abin da Allah ya rubuta masa. Na san cewa dole rashi bashi ba daɗi to amma abu mafi muhimmanci shi ne yana raye cikin ƙoshin lafiya. Allah da ya bashi shi zai ƙara ba shi wata ta inda bai yi tsammani ba.."

"Haba Husaina! Wannan masifar ta yi mana yawa wallahi..."

"Mummy ki yi haƙuri sai mu yi ta gayawa Allah shi ne zai yi mana mafita."

Daga haka ta juya ta kalli Daddy ta ce.

"Daddy ya jikin?"

Amsawa ya yi da.

"Jiki Alhamdulillahi Husaina..wallahi sai kin gansu, kamar mutanen kirki."

"Allah sarki! Wannan duk jarabawa ce. Allah ya mayar da alheri ya baka lafiya."

"Amin. Kin kira Aysha kin sanar mata halin da nake ciki.."

Wani irin mugun tsaki Mummy ta doka sannan ta ce.

"Wai kai ba za ka daina zancen Ayshar nan ba? Yarinyar da kana cikin halin jimami da damuwa ta saka ƙafa ta wuce ta barka shi ne har kake zancen ta..."

Girgiza kai Husaina ta yi jin irin zancen da Mummyn ke yi na takaici daga nan ta zauna gefen Daddy tana faɗin.

" Zan sanar mata, na fi son sai an sallame ka mun koma gida ina tsoro kada hankalinta ya tashi. Amma dai Yaya Hafiz yana kan hanyar zuwa In Sha Allahu... In zubo maka abincin?"

"Eh. Mi kuka zo da shi?"

"white Rice ce da stew, sai kuma tuwo daban."

"OK to, zuba min shinkafar Amma kar ki sa da yawa kaɗan ya isa."

Ta shi ta yi ta zuba masa kamar yanda ya ce ta zuba mi shi nama sosai sannan ta tsiyaya mishi lemun 5alive a glass cup ta zauna a gefen shi ta miƙa mishi tana faɗin.

"Humaida na makaranta, ka manta baka tambayeta ba.."

"Haka ne. Amma ba mantawa na yi ba nasan yanzu tana makaranta ne..."

Fira suka shiga yi sosai a hankali yana bata labarin abin da ya faru tiryan-tiryan yayin da Mummy ke gefe zuciyarta kamar za ta fashe tsabar baƙin cikin motar da ya bari aka sace, sai kuka take kamar wacce aka yi wa mutuwa.

Bayan Hafiz ya iso ɗin ne ya je ya ga likita ya biya kuɗin magani sannan aka ba su sallama suka tafi gida.

Tun da abin nan ya faru tsawon sati ɗaya Daddy bai san abin da yake masa daɗi a rai ba. Daman ga matsalar Ammie da ta ce wai ta aurar da Beenafah ta gudu. To shin wai tun farko ma wacce haukar ce tace mishi ya kore ta daga gidansa? Kwata-kwata bai yi tsammanin cewa za ta iya yin tunani irin wannan ba, domin ya ɗauka cewa har yanzu ciwon hauka yana damunta wanda ba ta iya fahimtar komai. Ashe yana nan zaune ya sake baki ta gama aiwatar da gaban kanta. Saboda haka, idan har bai yi saurin ɗaukar mata mataki ba, to tabbas ya san za ta iya aikata masa wata muguntar. Shi yasa yake ta neman ta ruwa a jallo domin ta riga Malam masallaci.

Yana zaune da dare kamar wasa Ado ya kira ya sanar da shi cewa aikinsa ya kambala. Take ya ji kaso sittin cikin ɗari na matsalolinsa ya tafi. Ba ɓata lokaci ya tura masa miliyan goma rabin kuɗin da suka yi zai ba shi akan zai turo masa da address ɗinda ya ɓoye su Ammie a nan Gusau a yanzu. Idan ya zo ya bashi su sai ya cika masa cikon kuɗi su zama 20M kamar yan da suka yi.

Bayan ya gama zayyanewa Mummy ta fashe da wata irin dariyar nasara ta ce.

"Alhaji, ina so a wannan karon Mulaifa ta shiga haukar da tafi ta baya muni da hatsari. Dole mu salwantar da su da labarin su matuƙar dai ka na so mu ci gaba da dawwama a cikin wannan daular arzikin har jikokinmu...."

"Ai tun farko ke ce ki ka ja mana duk wannan da ƙaramin tunanin ki. Da ace suna nan a tare damu da yanzu duk haka ba ta faru ba."

Wani irin hura hanci ta yi sannan ta jinjina kai ta ce.

"To ai yanzu za'a yi mai kankat gobe idan Allah ya kai mu na rai....baƙin cikin da Mulaifa ta dasa min na hana auren Ameer da Beenafah dole itama ta ɗanɗana kuɗarta.."

Haka suka gama firarrakinsu sannan daga ƙarshe suka je suka kwanta da zimmar idan gari ya waye su wuce Zamfara.

*******

Muna isa da kansa ya buɗe min ƙofa sannan ya kalleni a hankali yace na yi addu'a kafin na sauko da ƙafata. Bayan na yi yaja hannuna muka shiga cikin gidan,gidan ya cunawa gidan su Hajiyarsa da gidan da muka baro a Abuja nesa ba kusa ba. Duniya ce mai zaman kanta.

Duk inda muka ratsa ni dai biye nake ina rayawa a raina cewa wai ni Beenafah ni ce a nan? Allah mai girma! Mai kuma juya al'amarin bawan sa a duk yanda ya so.

Bayan mun gama ratsa wurare sai ga mu a wani katafaren ɗakin bacci tangameme mai ɗauke da duk wasu abubuwan buƙata na more rayuwa.

Kallona ya yi a hankali ya ce.

"ki yi wanka ki huta. Akwai kayan ki a nan, komai da komai..."

Ya ƙarashe maganar yana mai nuna min wani closets da ke gefena. Jinjina masa kai na na yi sannan ya saka kai ya wuce. Wata ƙofar na nufa na buɗe ta sai ga shi na kuwa canka daidai domin nan ne bathroom ɗin. Hmm! Wato ba gidan ba, ba ɗakin ba, hatta bathroom ɗin wani ƙamshin yake fitarwa na musamman kamar wani ɗakin bacci. Komai ga shi nan gwanin burgewa.

Wanka na yi domin a gajiye nake sosai,bayan na fito na zo jikin vanity mirror na tsaya na shafe jikina da mayuka da turaruka masu daɗin ƙamshi sannan na je closet ɗin na ɗauki wata rigar roba doguwa marar nauyi na saka, sai da na saka na gane ashe bakin Knee ɗina ta tsaya ba ta sauka ƙasa ba. Har na yi nufin canza wa sai kuma na ga wani hijab har ƙasa da hular shi mai kyau na saka na zo inda naga an ɗan zagaye an saka dimlight da sallayah na gabatar da sallar Asuba sannan na je kai tsaye na kwanta idona har wani ya ji suke min a lokacin tsabar yanda na gaji.

Shi kuwa, wani ɗakin ya buɗe ya shiga ya yi wanka ya fito ya yi sallah Sannan ya ɗauko wayarsa ya kunna ta ya shiga karanta texts ɗin su Labiba a natse wanda suka kashe masa jiki gabaɗaya ya kasa wani kataɓus.

Bayan ya kambala duba saƙon ya sake kashe wayar sannan ya janyo wata computer ƙarama ya fara aiki a cikinta na tsawon lokaci wanda yana yi yana tunawa da ni.

Har na gama baccin na na tashi bai dawo ɗakin ba a lokacin har misalin sha ɗaya na safe.

Bayan na tashi na cire hijab ɗin na koma jikin faskaceciyar windown na tsaya ina hango manyan-manyan gine-gine gwanin burgewa.

A hankali na ji takunsa a bayana domin ko ban waigo ba nasan cewa tabbas shi kai ɗai ne wanda zai iya shigowa nan direct. A hankali na waigo na gansa Sanye cikin wata casual white shirt da black trouser.

"Ina kwana?"

Abin da na iya furta masa kenan tare da yin ƙasa da kaina domin wani irin nauyinsa ne ke ɗawainiya da ni a duk lokacin da muka yi ido biyu da shi.

Murmushi ya sakar min tare da ƙarasowa ya rungumoni a jikin sa muna facing windown a tare a hankali ya ce.

"Ban taɓa tunanin cewa rayuwa zata bani irin wannan damar ba Beenafah...wannan gidan da kike gani, shi ne duniyata wacce babu kowa a cikinta sai ni da masu aikina...amma a yau.. Sai gaki a ciki a matsayin matata wace ta zamo tsani ta kuma bani hope ɗin rayuwa a karo na biyu... And from now on... Every sunrise, every night, every heartbeat and every dream.... Will begin and end with only you beside me.. "

Lumshe idanuwana na yi a hankali ina ƙara saukar da kaina akan ƙirjinsa...tabbas ina jin wani sabon abu na daɗa wanzuwa a hankali cikin zuciyata game da wannan mijin nawa da na aura saboda ceto rayuwar shi. A duk lokacin da ya furta kalmar godiya a gareni ko kuma kalaman ƙwarara gwiwar da ya samu saboda ni, sai in ji gabaɗaya na shiga wani yanayin farin ciki tare da jin nutsuwa a cikin ruhi da sassan jikina.

Mun jima a tsaye kowa na jin sabon abu na masa tartsatsi a cikin ƙirji sannan daga ƙarshe a hankali ya juyo ni ina fuskantar sa ya ce.

"Kin yi wanka?"

Jinjina masa kai na kawai na yi ina ƙara yin kasa da kaina.

Da Kansa ya buɗe ya ɗauko min wata Abaya baƙa da gyalen ta ya bani ya ce.

"ki shirya mu fita waje."

Wani tsil-tsil na yi da ido ina kalle-kalle ganin yanda ya ja tunga ya tsaya yana kallona, to nufinsa in saka kayan a gabansa ko me?

"Ya dai?"

Ƙara ƙasa da idona na yi domin ina da buƙatar undies, maimakon ya yi avoiding ɗina kamar yanda ya saba, sai bai yi hakan ba. Ganin yan da na tsaya yasa ya sake Kallona ya ce.

"Do you need something?"

"am! Da..daman ina son undies before na saka wannan ɗin..."

Buɗewa ya yi ya ɗauko sabon pant da bra Sannan ya ɗauko skirt ya miƙo min.. 'Wayyo Allah na!' Abin da na furta kenan jin yanda zuciyata ta yi wani tsalle har ban san lokacin da na sauke kaina a ƙasa ba tare da maƙale hannuna.

" Beenafah!"

Ya furta sunana cikin wata irin muryarda ta ƙara hautsina wani abu a cikin ƙirjina. Maimakon ya ƙyale ni sai wani janyoni ya yi jikin sa yana faɗin.

"Why are you Shy? Huh! Kin manta cewa ni ɗin mijin ki ne kuma ke ɗin matata ce?......Ohh common dear! Ke fa kika yi min alƙawarin zamu haifi yara ma su yawa...Ba haka ba ne kenan?"

Fuskar sa ya kawo saitin tawa wanda har muna iya jiyo numfashin juna dani da shi ya ƙara saukar da murya yana faɗin.

"Ki amsa min, ba haka ba ne kenan?"

Ba shiri na runtse idanuna a raina ina faɗin 'Innalillahi!.....Ya Allahu! Wannan mutumin ya gama dani a yau. Miyasa ba zai ji kunyata kamar yanda na ke ji game da shi ba.'

Jin saukar laɓɓansa akan nawa shi ya dawo dani daga duniyar da na shiga, a daburce jiki na rawa na shiga neman zamewa amma kuma hakan bai hana shi aikata abin ya fara ba sai ma ƙara saukar da hannun sa da ya yi zuwa waist ɗina giving him more access to my lips...hankalinsa kwance ya shiga kissing ɗina gently har zuwa wuyana wanda Shi kanshi na lura yanayin jikin shi ya ɗan sauya yana shaking a hankali da alama shima karon sa na farko kenan.

Saukar ɗumin hawayena akan fuskarsa yasa ya janye bakin nasa still da idanuwansa da suka canja launi ya kalleni yana jinjina kansa muryarsa cikin wani irin yanayi ya ce.

"Na yi laifi ne Beenafah? Har da kuka haka. To ki yi haƙuri, amma bana son kina jin kunya because now... we are one."

Yana gama faɗar haka, ya saka yatsa ya goge min idona sannan ya ja hannuna ya kai ni gaban kayan ya ce na ɗauki size ɗina na saka.

Jiki a sanyaye na miƙa hannu na ɗauko wasu, kafin ya yi wani yunƙuri na shige can ciki ta yanda ba ya iya hango ni na tsaya na saka a gaggauce, ƙirjina ne ya buga tuna cewa to ai rigar tana kan gadon kuma dole sai na fito zan iya sakawa, sannan a inda nake ɓoye only inners ne a ciki.

Ganin da gaske ba zan fito wa ba yasa ya miƙa hannu ya ɗauko rigar ya miƙo mini yana faɗin.

"karɓi!"

Bayan na saka na fito na je jikin mirror na naɗa veil ɗin sannan na matso inda yake wanda har yanzu ƙirjina bai daina ɗagawa. bai ko kalleni ba kamar yanda nima ban kalle sa ba yaja hannuna muka fita inda ma'aikatan gidan ya shiga introducing ɗina a wurin su. Bayan ya gama mu ka je dining room muka yi break fast. Muna kambalawa ya je ya shirya muka fita, ban san a ina muke ba sai da na ganni a asibiti inda aka ɗibi jininmu da ni da shi aka tafi wurin gwaji.

Ina nan zaune wani kyakkyawan office ina kallon drama a TV duk da dai cewa kallon kawai nake amma abin da ya yi min ɗazu ya yi matuƙar tsaya min a zuciyata ba kaɗan ba. Kwata-kwata ban sa rai da tsammanin cewa haka yake ba. Amma an ce baki shi kan yanka wuya. Sai yanxu na yi nadamar furta masa cewa wai zamu haifi yara. kaiii Beenafah! Hmm! In dai ciwon baki ne ai gobe sai in ƙara yi. Hannu na kai akan bakina a hankali ina shafa laɓɓana lokaci ɗaya ina jin kamar yanzu ne abin ya faru a tsakaninmu. Har yanzu ban daina jin abin a ƙwaƙwalwata ba domin ya shigeni ba kaɗan ba. 'Wuya na fa!' na faɗa ina mai ƙara kai hannuna inda ya sumbata a wuyana tare da lumshe idona. Wallahi na ji kunya, na ji kunya sosai kamar ƙasa ta tsage in shige ciki haka na ji....jin an turo ƙofar yasa na yi saurin shiga taitayina tare da saukar da kaina a ƙasa. Waya ya miƙo min kurum ya juya ya fice.

Wayar na kai kunnena ganin tana kan kira na ce.

"Hallo Ammie..."

"Na am Beenafah. Da fatan kun isa lafiya?"

Cike da mamaki na ce.

"Daman kin san cewa zamu zo nan kenan?"

"Eh mana, ya sanar mana. Yanzu ma shi ne ya kirani ya ce kina son Magana dani."

"Allah sarki! Ina Bahrain?"

"Hmm! Bahrain yana makaranta, an kai shi tun jiya. Yanzu ni ka ɗai ce a gidan nan sai masu aiki, amma dai Hamza ya dawo nan da zama..."

Wata irin dariya na yi ta jindadi na ce.

"Ammie Yaya Hamza fa kika ce? Dan Allah ina yake?"

"sun fita tare da Dr. Zai karɓo min saƙo..."

"To ina su Yaya Jafaru?"

"Jafaru yana makaranta. Su Fakiha suna Gusau.."

Fira muka sha sosai inda a nan ne ta bani labarin yanda suka yi da Uncle Isma'il da yanda tace ayi da kuɗin. Duk yanda ta wani zage tana shaidamin irin halin da Aunty Hassana ta shiga ni wallahi ko kaɗan bata bani tausayi ba sam. Yan da nake jin tsanarta a zuciyata duk abun da zai same ta ba zan iya tausaya mata ba. Daman masallaci takai kuɗin tace ayi wa Abbie addu'a da yafi bai wa Aunty Hassana da ta yi. Bayan mun kambala kamar an ce na shiga gidan lambobi kawai naga numbern aunty Labiba. Ai ko jiki na rawa na kirata muka sha firarmu da ita kamar wani abu mai faru ba harda ta tsayawa ta yi ta ƙara bani shawarwari. Haka nake ganin rayuwarta kamar ta Aunty Aysha da Mummy Sameera wurin bai wa mutum shawarwari akan zamantakewa da sauran wasu al'amuran rayuwa.

Bayan na kambala ina nan zaune ina kallon TVn sai ga shi ya shigo. Hannu kawai ya miƙomin alamar in zo mu tafi, ganin hakan yasa na miƙa masa hannun don kada ya ce zai min wani abu idan na yi masa gardama.

********

Gefen su Daddy kuwa, washe gari da sassafe suka shiryo daga shi sai ita bayan sun bar Humaida a wurin Husaina da Biba.

Sun shiga mota kenan driver ya tayar sai ga shi an ce Daddy ya yi baƙi a bakin gate.

Cike da mamaki ya ce.

"Baƙi da sassafen nan? Je kace su shigo..."

Daga haka ya waiga gun Mummy ya ce.

"Bari in je in ji su waye ke nemana."

Wasu mutane ne su huɗu shirye cikin shigar suit baƙaƙe suka shigo tare da bashi hannu su ka gaisa sannan ɗaya daga ciki ya ce masa cikin harshen turanci.

"Daga hukumar cibiyar kasuwanci ta ƙasa muke, mun zo ne domin isar da wannan muhimmin saƙon gareka...."

Hannu ɗaya daga cikin su ya tura a aljihu ya ciro envelope ya miƙawa daddy Sannan suka yi masa sallama suka fi ce.

Hannu na rawa ya buɗe envelope ɗin ya ciro saƙon takardar da ke ciki ya fara karantawa cikin harshen turanci kamar haka:

HUKUMAR KULA DA HARKOKIN KASUWANCI TA ƘASA (FEDERAL BUSINESS COMMISSION)

Office: Plot 48, Commercial Avenue, Garki II, Abuja, Nigeria.

Zuwa ga: Alhaji Mudassir Wazeer. Katamfe Extension, Abuja. Nigeria.

Subject matter: Sanarwar Rufe Dukkan Harkokin Kasuwancin Marigayi Dr. Bello Wazeer Na ɗan Lokaci.

Wannan takarda ce daga Hukumar Kula da Harkokin Kasuwanci ta Ƙasa (FBC).Dukkan kadarori,kamfanonan kasuwanci da suka kasance ƙarƙashin sunan Marigayi Dr. Bello Wazeer:

Bayan ƙarar da aka shigar da sunanka da kuma bin ƙa’idar da ke cikin Dokar Kula da Dukiyar Masu Kasuwanci. Sashi na 12, sakin layi na (b), Hukumar ta yanke hukuncin cewa: dukkan ayyuka, kasuwanci, asusun kuɗi, da mu’amalolin da suka danganci sunan marigayi Dr. Bello Wazeer an dakatar da su na wucin gadi. Wanda ba za a sake buɗe kasuwancin ba, saka kuɗi ko cirewa, canja sunan wani abu ko sauya masa fasali ko ci gaba da gudanar da kowanne daga cikin waɗannan kasuwanci ba har sai an samu rubutacciyar amincewa tare da sa hannun matarsa da ’ya’yansa biyu na cikinsa wanda sai hukumar ta tabbatar da sahihancinsu.

Wannan mataki na nufin tabbatar da gaskiya, adalci, da bin ƙa’idojin doka wajen tafiyar da kadarorin marigayin. Idan kuma aka yi yunkurin buɗe ko yin amfani da dukiyar kasuwancin ba tare da izinin hukuma ba, hakan zai zama an karya doka kuma zai jawo hukunci daga sashen shari’a na hukumar mai tsanani. Kuma kai ma za a rufe komai naka tun daga kan asusun banki, gidaje, motoci ba za ka sake amfani da komai ba har sai an gama binciken da ya kamata.

Ana roƙon haɗin kai da fahimtarka domin gudanar da wannan tsari cikin lumana.

Sign by: Barr. (Mr.) Edward Jonathan. Daraktan Sashen Doka da Bin ƙa'idoji na Hukumar Kula da Harkokin Kasuwanci ta Ƙasa (FBC)

Hannu ya saka ya dafe kai tare da ƙwallara wani irin gigitaccen ihu yana faɗin.

"Wayyo na shiga uku sau uku! asiri na ya tonu ni Mudassiru....Ku nemomin Mulaifa... Dan Allah jama'a ku nemomin Mulaifa ta saka hannu ita da yaranta."

A gigice Mummy ta ɓalle murfin motar ta fito amma kafin ta ƙaraso har ya faɗi ƙasa ya suma.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....

*PAGE 38*

"Mine ne Alhaji? Alhaji....Alhaji!!!"

Mummy ta faɗa tana mai tallafo shi zuwa jikinta a gigice.

Da gudu Husaina ta fito ita da Humaida da Biba suna rige-rigen isowa wurin su.

Takardar Husaina ta rifta jiki na rawa ta shiga karantawa...tana cikin karantawar bata ƙarasa ba ta ji wani sabon gigitaccen ihun Mummy ya sake karaɗe mata dodon kunnenta da cewa.

"Jini!!... Husaina kalli jini ta Baki da Hancin sa? Wayyo Allah na Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wai wannan wace iriyar baƙar wasiƙa ce haka nikam Zaliha na shiga uku na?"

Da sauri Humaida ta ƙwala kiran Ilyas dake mota yana jiran su ta ce.

"Ilyas Please yi sauri ka kawo motar a nan mu kai shi asibiti."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull