Kenza eBookz

Ganin ido complete Novel - Chapter 45

Ganin ido complete Novel - Chapter 45

Ganin ido complete Novel Chapter 45: Ganin ido complete Novel Chapter 45. Na daɗe a toilet ɗin wanda sai da na ji na ɗan dawo hayyacina bayan na gama gasa…

3,363 words

Na daɗe a toilet ɗin wanda sai da na ji na ɗan dawo hayyacina bayan na gama gasa kaina sannan na yi wanka na fito. Sosai abin da ya faru a tsakaninmu ya tsaya mini a raina...Wai Yaya Muhammad ne ya tara dani! Tarayyar aure tsakanin mata da miji...Dama wannan shi ne First night ɗin da yake ta yawo da yamaɗiɗi a bakin mutanen duniya? Tabbas na tabbatar kuma na gasgata domin ya bar min tarihin da har abada ba zai goge a ƙwaƙwalwata ba. Lumshe idanuna na yi tare da kai hannu ina shafa jikina ina jin komai kamar yanzu ne yake faruwa tsakanina da datijjon Mijina.

Ajiyar zuciya na sauke daga ƙarshe sannan a hankali na matsa na ja towel na ɗaura na fito. Bakin ƙofar na tarar da shi ya jingina jikin sa tare da tallafe hannayensa a ƙirjinsa. Ɗan ja baya na yi kaɗan tare da noƙe kaina domin ban tsammace sa a wurin ba. Yana ganin na fito ya matsoni tare da riƙo hannuna cike da nuna kulawa, ya ce.

"How are you feeling now?"

Shiru na yi tare da ɗora kaina a ƙirjinsa jin wata irin kunyar sa da ta dawo mini sabuwa.

"ki yi haƙuri kinji...ko kaɗan ban da nufin cutarwa a gare ki....."

Murmushi da kuka ne suka zo min lokaci ɗaya jin yanda ya ruɗe yana ta wani lallashina kamar wanda ya aikata min wani babban laifi. Ɗago kaina na yi da koɗaɗɗun idanuna a hankali na kalle sa a natse muryata a ƙasa sosaina ce.

" Jikinka fa har yanzu da zafi..."

Share maganata ya yi tare da kai hannu ƙarƙashin cinyata a hankali yana mai zame towel ɗin zai tura hannun nasa a HQ ɗina yana faɗin.

"Da zafi ne har yanzu?"

Tashin service!...ai a mugun gigice na kai hannu jiki na rawa na riƙe hannun sa tare da girgiza masa kaina idona a rufe na ce.

"Wayyo ni! wallahy...ni dai dan Allah ka daina.."

Ganin yanda duk na rikice yasa ya janye hannun sa yana murmushi ya ce.

"I'm sorry....Ya jikin to?"

Idona a rufe sosai still ina riƙe da hannun nasa na girgiza kaina na ce.

"Ni dai lafiya ƙalau...."

"Au! Da gaske...! To bari mu kom...."

Ba shiri na ƙanƙamesa tamkar zan shiɗe ina faɗin.

"Dan Allah kayi haƙuri...wallahy wurin zafin sosai..."

Ɗagani ya yi kai tsaye ya bar ɗakin dani. Tafiyar kusan 3mnt sai gamu a wata duniyar wacce tsawon zamana a gidan ban taɓa sani da zaman ta ba.

Wuri ne na musamman wanda zan ce duk kyaun gidan nan nan ɗin yafi ko'ina tsaruwa da kuma jin kayayyakin komai na more rayuwa.

A bakin wani tamfatsetsen gadon ya ajiyeni sannan ya ɗauko wani ƙaramin towel ya tsane mini gashin kaina kamar yanda yaga ina yi sai dai kuma bai zo da hand dryer ba, bayan ya gama tsane ruwan a haka ya bar sa sannan ya ɗauko cream ya shafa mini yana murmushi ya juya ya fice. Duk tsawon lokacin nan da muka shafe babu wanda yayi wa wani magana ta fatar baki amma kuma saƙon da yake Isar min yana isa yanda ya kamata domin wata irin soyayyarsa ce sabuwa nake Jinta tana ƙara huda sassa da ruhin jikina,sam na kasa daina gani da jin abinda ya wakana a tsakaninmu a ido da ƙwaƙwalwata amma kuma gabaɗaya haushinsa da naji ina ji na nemesa na rasa.

Kitchen ɗinda ke cikin keɓantaccen wurin ya shiga ya haɗo min Tea da kansa ya kawo min nasha sannan ya bani magani, bayan na shanye ya ja ni zuwa jikin sa muka kwanta akan gadon wanda bai fi 10mnt ba ya sauka ya shirya ya fice masallaci.

Koda ya dawo ni har na yi sallah na koma na kwanta bacci ya kwashe ni.

Ganina sanye da Hijabi shi ya tabbatar masa da cewa na yi sallah. Hauro wa ya yi a hankali cikin sanɗa ya janyoni jikinsa gudun kada na tashi yaja mana duvet.

Kallon fuskata yake yana jin wani abu na ƙara fisgarsa a zuciya game dani...ji yake tamkar ya tsaga ƙirjinsa gida biyu ya ɗauke ni ya jefa a ciki tsabar yanda yake jina a yau.

Ƙara matso da fuskarsa yayi a hankali yayi kissing saman goshina sannan ya ɗora hannunsa akan gashin kaina a hankali yana shafawa yana addu'a a ransa yana faɗin. 'wannan matar tawa...Allah ya bulbula miki albarka..Allah ya barni dake har mutuwa...Allah ya dauwamar da farin ciki a zuciyarki har abada...Allah ya bani ikon kulawa da ke da dukkan ƙarfina da dukiyata. Haƙiƙa kin bani farin ciki...farin cikin da har na koma ga Allah ba zan daina gode miki da kuma yaba miki ba. A yau na roƙi Allah alkairai masu yawa a tsakaninmu Bibi...Allah ya tabbatar mana da su ya bamu zuria ɗayyaba.'

Haka ya shafe tsawon lokaci yana aikin yaba mini da gode mini a zuciyarsa wanda Sam bacci bai yi nasarar kawo masa farmaki ba.

Muna nan a haka har misalin takwas na safe wanda har yanzu baccina nake hankali kwance ya ji ƙarar saƙo ya shigo wayarsa.

Hannu ya miƙa ya ɗauko ya karanta sannan ya zamar dani gefe a hankali tare da ƙara gyara mini lulluɓi ya sauko ya zura jalabiya ya fita.

Yana shigowa main parlourn gidan suka yi ido biyu da Labiba,waigawa ya yi ya kalli Emraan, Nadeeyah, Hairiyyah da kuma Baba Ustaz.

Wani irin harbawa ya ji ƙirjinsa ya yi lokaci guda. Kafin yayi wani yunƙuri da gudu Labiba ta zo ta Rungumesa sosai ta fashe da kuka ta ce.

"DADDY!!!"

Cikin wani irin jin azabar kewar ƙannen nasa ya ƙanƙemata tare da jin wasu irin zafafan hawaye ya ce.

"I'm sorry my PEACE.....I'm so sorry..Abubuwa sun juye mana yanda bamu tsamma ta ba....dole ce tasa na yi nisa da ku...amma dan Allah ku yafe min..."

Tana kukan ta Ɗago kanta ta kalle shi ta ce.

"Ka yi haƙuri Yaya..mun azabtu da rashinka, wallahi bana iya baccin kirki tun daga ranar da kasa ƙafa ka barmu har zuwa yau, wayarka bata shiga, ka hana kowa na kusa da kai ya mu'amalancemu. Hajiya tabbas ita ce wacce ta haifemu,.... Amma Sam babu adalci idan har ka saka mu a tsakiyar wannan abun da ya faru domin yanda ka tsinci abin muma haka muka tsince sa daga sama... Yaya ba kuɗin ka muke da buƙata KAI....kai ne ubanmu wanda yake tsaya mana a dukkan komai....nisantarmu da ka yi yasa mun zamto marayun ƙarfi da yaji Yaya...kuɗi ba su ne farin ciki ba wani lokacin, kyakkyawar alaƙar zumunci tafi komai muhimmanci..."

Hannayensa ya ware yana kallon su Hairi alamar suma su zo wurin Yayansu.

Da gudu suka shige jikinsa tare da haɗe kai suka yi ta rusa kuka son ran su shi kuma yana ta aikin lallashi da amsa laifinsa yana ta basu hak'uri, musamman irin kukan da ya ji Hairi nayi ya ɗaga masa hankali.

Bayan sun natsa da koke-koken ne suka wuce part ɗin Hajiyarsu inda take sauka idan ta zo ƙasar suka zauna. Emraan sai wani noƙewa yake alamar jin kunya wanda shi Mohaan sam bai kawo hakan ba. Sosai yanzu yake jin rashin kyautawa akan ba su baya da yay na tsawon lokaci. Allah ne fa gatan su shi ne gatan su...amma miyasa zai biyewa zuciya haka har ta kai shi ga saka Masoyan ƙannensa a damuwa. Matsayin Hajiyarsu daban suma matsayinsu daban.

"Emraan....are you still mad at me?"

Ya faɗa yana mai jifar Emraan ɗin da wani irin marayan kallo.

Da sauri Emraan ya Girgiza Kansa cike da jin nauyi ya ce.

"Ba haka bane Yaya..."

"Please kada ka damu kaji ko... Komai ya wuce in sha Allah. Daman ko tsakanin harshe da haƙori da suka fi kowa kusanci da zumunci ana samun saɓani ballantana mu 'ƴan Adam..."

Daga haka ya mayar da kallonsa gun Baba Ustaz a natse ya ce.

"Baba...A farko na ɗauki abin da ya faru dani da zafi sosai wanda har na ji a raina cewa bana buƙatar kowa daga cikinku wanda a ganina tare kuka haɗai kai kuke nema kuga bayana...to amma bayan na zauna na yi nazari, a yanzu na riga na fahimta cewa yana daga cikin ƙaddara ta wanda ban isa na gogewa kaina ba. Saboda haka ni komai ya wuce a gare ni musamman da Allah ya bani Mata ta gari wacce ta zamto haske a cikin rayuwa ta..... A yanzu ni tambayata ɗaya ce a wurin ka...Wace ce mahaifiyata? A ina take? Ina kuma Ahlinta suke?"

Ajiyar zuciya Baba Ustaz ya sauke a hankali yana mai jinjina kansa ya ce.

" Sunanta RANIA MUSDHAPA SAMI...a zuwa tafiyar kasuwanci mahaifin ka ya haɗu da ita a OUMDURMAN da ke ƙasar SUDAN......"

✍️ *OUM-AMEER* ✍️

*GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

*PAGE 41*

ƙaramar jakarsa ya buɗe ya ciro wasu katin hotuna guda biyu irin na da ɗinnan marar colour ya miƙa masa.

Hannu na rawa ya karɓa ya ƙura ido yana Kallo, wasu irin hawaye na bin fuskarsa tsabar yanda ya ji zuciyarsa ta ƙara raunata.

Wannan ɗin mahaifinsa ne tabbas Alhaji Attahiru, wannan kuma...itace kenan mahaifiyar tasa wacce Baba Ustaz ya kira da RANIA. Sanye take cikin shigar alfarma da manyan gwala-gwalai a wuya da kuma hannuwanta, yayin da Alhaji Attahiru ke sanye cikin shigar manyan kaya na er ciki da babbar riga, cikin style na irin hoton da ɗinnan da akeyi sun zauna akan kujera ɗaɗɗaya. Sai ɗayan hoton kuma, Baba Ustaz ɗin ne, Baban sa da kuma kakansa Malam Araam sai wasu guda biyu waɗanda bai shaida su ba.

Jinjina kai Baba Ustaz ya yi ya ce.

"Wannan ita ce Mahaifiyarka, ita ɗin 'ƴar babban gida ce domin iyayenta sun kasance manyan en kasuwa masu hannun Jari da yawa a fannin Zaren auduga, kayan ado, da kayayyakin ƙasashen Larabawa da ake shigowa da su daga ƙasar Masar da Saudiyya, sannan kuma sun mallaki rukunin manyan gonaki na sesame (Gyaɗa) Gishiri da kuma Goro da ake fitarwa zuwa ƙasashen Habasha da Chadi. Mahaifiyarka ta kasance babbar 'ƴa ta farko a wurin mahaifinta Alhaji Musdhapha Sami wanda mutum ne mai daraja da ya shahara ya yi suna a cikin manyan attajiran Sudan. Hakan yasa koda ta taso ta tsayu akan kasuwanci kamar yanda taga iyayenta na yi wanda tun tana yi a cikin gida har ta shahara, ita ce mace ta farko a yankinsu da ta buɗe kasuwa mai suna Suq Rania da taimakon mahaifinta wanda a hankali ta bunƙasata da shaguna ta zuba kayayyakin kasuwanci na kayan gida da kuma wanda ake shigowa da su daga waje. A hankali ta fara bunƙasa har mutane suka riƙa zuwa suna sayen wuri suna buga rumfuna suma suna kasa nasu kayayyaki wanda ita a lokacin ta shahara sosai. A hankali kasuwar tana ƙara suna tana ƙara Faɗaɗa har ta yi shura a Sudan wanda har yanzu akwai kasuwar ta nan a Oumdurman ana ci gaba da kasuwanci a cikinta."

"Shi kuma Mahaifinka a wannan lokacin, shima mutum ne mai jimirin neman na kansa, ƙasashe yake zuwa a wannan lokacin yana saro kaya idan ya saida a Kasuwar Kano, sai ya dawo gida yaga iyayensa ya yi mana sayayya sannan ya juya ya koma a haka har Allah ya jefa shi Sudan inda ya sayi kayan abinci, yaji da sauran abubuwan da basu da shi ya tafi dasu Suq Rania. Yana zuwa aka kaishi Ofishin tattaunawa kan musayar kaya wanda suka ce ba za'a yi komai ba sai dai idan ya ga shugabar su. Sai da ya kwana uku cikin na huɗu sannan ya samu ganinta."

"Ya yi mamaki ganinta Mace budurwa kuma mai ƙananun shekaru ace ita ce ke da wannan Kasuwar. Bayan ya gama gabatar mata da abinda ya kawo shi ba ɓata lokaci ta amince ta bashi rukunin kaya masu yawa daga cikin kowane nau'inda ya buƙata. Bayan an gama suka ƙulla yarjejeniya akan cewa idan ya sayar zai dawo mata da kuɗinda tayi masa ƙarin kaya da kuma ribar ta da zai bata domin kayanta da ta bashi sun ninka waɗanɗa ya zo da su da yawa."

"To bayan ya dawo Nigeria sai da ya shafe shekara ɗaya cif sannan ya juya ya koma mata da kuɗin ta da kuma ɗimbin alherin da aka samu. Jindaɗin gaskiyarsa da amanar da ya nuna yasa ta kai shi wurin iyayenta suka gaisa tasa aka bashi wurin kwana ya kwana biyu sannan ta sake bashi wasu kayan wanda a wannan karon bai fi wata biyar ba ya koma mata cike da alfaharin yin nasara. A hankali suka ƙulla soyyaya da kasuwanci wanda har mahaifinmu a lokacin ya so ya nuna rashin amincewarsa sai daga baya ya samu aka shawo kansa ya yarda ya shirya da wasu en uwa aka tafi aka nema masa aurenta....Wannan hoton guda da kake gani...ranar ɗaurin auren ne, gani nan a ciki, ga mahaifinmu ga Mahaifinka sannan wannan da kake gani na gefen Malam shi ne mahaifinta wato kakan ka na wurin uwa sai ƙaninta Mu'aƙƙib ga shi nan a gefena. Auren ya kasance na alfarma wanda aka haɗa al'adar ƙasar Sudan da kuma tamu ta Hausawa. Bayan an gama bukin muka tattaro harda ita muka dawo Nigeria inda suka ci gaba da gudanar harkokin kasuwancinta ta hanyar wakilinta, wato mahaifinka da saƙonni daga uwayenta da en uwanta."

" Hajiya Rania ta rayu da mahaifinka tsawon shekaru biyar wanda sai a shekara ta shida ne aka haife ka kuma a ranar da ka zo duniya, a ranar ta amsa kiran Mahaliccinta..."

Yana wani irin kuka tamkar wani ƙaramin yaro ya kalli Baba Ustaz ɗin a raunane ya ce.

"A lokacin da ta rasu ɗin...iyayenta ba su zo ba ne?? Miyasa na rayu ba tare da na san su ba?"

Jinjina kai Baba Ustaz ya yi yana kallon sa ya ce.

"Sun zo mana! Sai dai koda suka iso an riga an kawar da ita, bayan an gama gaisuwa an gama jimami sai mahaifiyarta da ƙanwarta suka ce suna so a ba su kai su tafi da kai amma sai Tsohuwar mu da mahaifinka suka tsaya kai da fata suka ce lallai sune waɗanda za su riƙeka. Hakan yasa dole ba su da yanda za su yi suka barka. To a wannan lokacin renonka sai ya dawo hannun mahaifiyar ta mu wanda sai daga baya ne ya auro Hajiya Batula, daga nan kuma ka koma hannunta. Haƙiƙa ta nuna maka so, son da ko mahaifiyarda ta haife ka iya ƙaunar da za ta nuna maka kenan, a hannunta kayi wayau ka girma, a hannun ta ka samu tarbiyya, domin tunda ta auri mahaifinka kai kaɗai ne ke gaban su basu samu wata haihuwar ba sai da ka shekara goma sha biyu a duniya sannan suka haifi Labiba....a yanda ta nuna maka so babu wanda ya kawo cewa za ta iya cutar da kai Muhammad, kuma sanin cewa suna zuwa da kai Sudan babu wanda ya taɓa kawowa cewa wai basu taɓa sanar da kai dangin mahaifiyarka ba. Sai yanzu ne da abu yazo a haka take sanar min da bakinta cewa ai ita ce ta ƙulla makircin da ta sanar wa dangin mahaifiyar taka cewa ka mutu kaima baka duniyar...."

Wani irin nauyi ne ya ji ya ƙara tasowa ya danne masa ƙahon zuciyarsa akan mamaki da al'ajabin hali irin na Hajiyarsu. Hannayensa ya kai ya dafe kansa da ke masa wata irin barazana kamar zai rabu gida biyu tsabar yanda ya ji saukar wannan mummunar maganar da ko a mafarkin sa bai taɓa kawo wa cewa Hajiya za ta iya yi masa haka ba. Daman gabaɗaya jikin sa baya masa daɗi tun daren jiya yanzu kuma ga wannan mugun labari da ya riskesa bagatatan.

Shiru ne ya ratsa tsakaninsu wanda babu abinda suke idan ba kuka ba. A hankali Emraan ya sauko ya dafa ƙafar Yayan na su wanda ya kife kai a tafin hannunsa yana tsiyayar da ruwan hawayen baƙin ciki. Cikin rashin kuzari murya a raunane ya ce.

"Yaya! A faɗin duniyar nan bani da wata kalma guda wacce zan iya amfani da ita wajen furtawa da har ta isa ta zamomin tsani ko yin nasarar tausasa zuciyarka akan wannan kuskuren da Hajiya ta aikata maka...amma ina so ka sani, mu ɗin nan mun rayu mun kuma ta so a matsayin tsintsiya mai maɗauri guda ɗaya...Wanda idan har abin dariya ya zo mana to tare zamu dara, idan kuma abin kuka ya zo mana still a tare zamu koka. Saboda haka, dan Allah kada ka riƙe abinda bamu muka aikata ba, ƙwarin gwiwarka ita ce tamu, idan ka shiga damuwa sai mun fi ka shiga damuwar sau dubu. Ita ɗin da ta zaɓi ta cutar damu wace ribar ta samu? Babu! I'm very sure cewa duk irin halin da muke ciki a yanzu na baƙin ciki da damuwa ta fi mu domin kunyar duniyar nan kaɗai ta isa ta hana mata sukuni...akan abun duniya...Wanda babu abin da ta nema ta rasa za ta zaɓi ta cutar da maraya..."

" Shihhh!"

Abun da ya faɗa kenan tare da kai hannu ya ɗora yatsarsa akan lips ɗin shi alamar yayi shiru.

Bayan ya haɗiye sauran maganar sa ya jinjina masa kai tare da ƙuresa da idanuwansa da suka canja launi sosai, murya cike da nuna mazantaka, ya ce.

" Kai! Kada fa ka manta...ita ɗin Uwa ce Mahaifiya mai daraja...akan kuskurenta ɗaya...ba shi zai sa ka nemi tsallake iyakar ka ba...dukkanmu ajizai ne wanda babu wanda yafi ƙarfin aikata kuskure a cikinmu. Saboda haka kowa ya hutar da zuciyarsa komai ya wuce dan Allah...Ni ta yiwa, kuma na yafe mata...Allah ya yafe mana baki ɗaya.."

Girgiza kai Baba ya yi cike da jin wani sabon tausayinsa ya ce.

" Allah sarki! Allah ya ƙara maka albarka, Allah ya ji ƙan iyayenka ya gafarta musu kusakuransu..."

"Amin Baba...." Daga haka ya waiga ya kalle su ɗaya bayan ɗaya da wani murmushin ƙarfin halin da ya ƙirƙiro ya ɗora akan fuskarsa ya ce.

"My Peace...Nadeen Connel...Hairin Daddy..."

Tasowa Hairi ta yi ta zauna a gefen sa tare da ɗora kanta akan shoulder ɗinsa cike da kewa ta ce.

"I miss you so much Daddy...Zuciyata ta karye fiye da zato..."

A hankali ya kai hannunsa yana share mata hawayenta cike da nuna kulawa ya ce.

"I miss you too Uwar alheri...in sha Allah komai ya wuce."

Ɗagowa Labiba ta yi fuska cike da murmushin da ta jima bata yi kalar sa ba ta ce.

"Yayanmu ina Beenafah.?"

Waigowa ya yi ya kalle ta kai tsaye yace.

"Tana ciki tana bacci."

Sanin cewa safiya ce yanzu, hakan sai baisa suka kawo komai a ransu ba.

Kallon Baba ya yi ya ce.

"Baba yaushe ne kaga ya kamata mu tafi Oumdurman?"

Miƙewa Baba ya yi tare da faɗin.

"Duk san da ka shirya MUHAMMAD, ni a shirye nake....yanzu bari na shiga na ɗan huta."

Baba na wucewa suka ci gaba da tattaunawa. Fira sosai suka yi har kusan sha biyu saura na rana sannan ya miƙe yace su je su huta su ci abinci.

Koda ya dawo ɗakin still baccina kawai nake shaƙa hankali kwance domin tsayin daren ranar ba wani baccin kirki na yi ba, ina nan ba tare da na san budirin da suke sha ba. Ya jima a zaune yana kallon fuskata sannan daga ƙarshe ya janyo ƙafata a hankali ya saka yatsansa yana shafa tafin ƙafar tawa.

A hankali na shiga buɗe idanuna lokaci ɗaya kuma ina janye ƙafata na kallesa a lumshe na yi murmushi kamar yanda naga shima ya yi min.

"Bibi...jikin ne har yanzu?"

Girgiza kaina na yi ina ƙara lumshe idanuwana na ce.

"Alhamdulillah. Zafin ya rage sosai..."

Hannu ya kai ya shafo fuskata zuwa idanuna ya ce.

"Still idanun nan sunƙi su rage kumburin da suka yi...Gaskiya zuciyata ta karye..."

"Hmm!"

Abin da kawai nace kenan tare da kawar da kaina gefe.

"Tashi muje muyi wanka.."

'ƴar dariya ce ta suɓuce min ba tare da na shirya ba, a raina ko faɗin nike ba da ni ba sa lallen Kaza. Ni ɗin zan shiga Wanka da kai? To mu kalli juna yaya kenan..?

"Bibi.."

Ya ambata yana mai kawo fuskarsa saitin tawa, jin hakan yasa na ƙara ƙudundunewa na ce.

"Uh uhm! Ni dai ka je ka fito ba zan iya ba..."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull