Kenza eBookz

Ganin ido complete Novel - Chapter 46

Ganin ido complete Novel - Chapter 46

Ganin ido complete Novel Chapter 46: Ganin ido complete Novel Chapter 46. Wucewa ya yi yaje yayo wankan ya fito sannan na sauko da ƙyar na lallaɓa na shige…

3,321 words

Wucewa ya yi yaje yayo wankan ya fito sannan na sauko da ƙyar na lallaɓa na shige toilet ɗin a daddafe. Ba na wani jin alamar zazzaɓi ko wani abu, kawai dai ƙafafuna ne suka min nauyi da kuma zafin da ƙasa na ke min wanda shima ba sosai ɗinnan ba amma kuma bana iya haɗe ƙafafuna da kyau idan zan yi tafiya.

Tun da na sauko har na shige toilet ɗin kallona yake yana ƙara jin abin a ransa yan da nake tafiya da kuma yanayin fuskata da ta koɗe fes tsabar yan da nasha kuka.

Ko yanxu sai da na jima a toilet ɗin, domin sai da na ƙara gasa wurin da ruwan ɗumi wanda na ji daɗin hakan ba kaɗan ba, because na ƙara samun salama ba kamar yanda na shigo ba.

Koda na fito na tarar ya kawo mana abinci da kansa bayan ya shirya cikin wani 3quater da Tshirt wanda suka ƙara fito min da tsantsar kyaunsa da nake ƙara gani.

Tare ya tayani na shirya, bayan na gama gyara gashin kaina da kanshi ya karɓi ribbons ɗin yace na faɗi yanda zai min domin ya cika mini alƙawarinsa da ya ɗauka. Ina dariya na nuna masa ya yi sannan daga ƙarshe na kwance na sake kamawa da kyau na naɗiɗiyeshi wuri ɗaya.

Kallonsa na yi ta cikin mirror na ce.

"Yau ba za ka fita ba ne.??"

Hannayensa yakai ya zagayeni yana murmushi yace.

"Mi kika gani Bibina..."

"Uhm! Naga ka yi wannan shigar ne.."

"Da me kuma?"

Ina wani murmushi na jinjina kaina tare da ƙara Kallonsa ta mudubin na ce.

"And ka yi kyau sosai..."

Juyoni ya yi muna fuskantar juna ya saƙala hannun sa da kyau ya riƙo kwankwasona ya kai lips ɗinsa a hankali akan nawa ya fara kissing ɗina...

Jin abin na neman zauce tunanina yasa a tsorace na ɗan tura shi baya na ce.

"Uh uhm! Dan Allah ka bari..."

Murmushi ya yi yana ƙara kawo fuskarsa saitin ta wa yace.

"Kin tsorata ne?? Is just a kiss fa!"

Hannunsa na ja ina faɗin.

"Muje muci abinci, gwanda ni nasha Tea kai kuwa tun daren jiya bakaci komai ba.."

Abincin muke ci amma gabaɗaya yau yanayin tsokana yake ji har muka gama. Bayan mun gama muka yi sallar azahar sannan ya zaɓomin kaya na musamman yace min na shirya mu sauka ƙasa.

Wani irin freezing nayi naja na tsaya ganin su Aunty Labiba zaune a parlour a lokacin da banyi tsammani ba. Hairi na wani irin blushing ta rugo da gudu ta rungumeni tana faɗin.

"Mummyn Daddy.."

********

Gefen su Mummy kuwa, Aunty Aysha da ƙyar ta yi nasarar shawo kan Alhaji Baba da Uncle Isma'ila suka ce za su zo washe gari.

Suna nan har sai da aka fito da ita zuwa wani ɗakin sannan suka ɗunguma zuwa can amma har yanzu bata farfaɗo ba.

Kallon Husaina Mummy ta yi jiki a sanyaye ta ce.

"Husaina ki je gida ki dafa mana abinci da ruwan zafi kafin ta farfaɗo, idan kin kambala sai ki fara biyawa ki kaiwa su Humaida sannan ki kawo mana nan, zuwa dare ke Aysha sai ki wuce can wurin Alhajin ki kwana tare da ita...."

Zumbur ta miƙe hankalinta a tashe tana faɗin.

" Innalillahi! Mota! Mommota tana can hannun wani.. "

Daga haka ta fito da gudu tayo harabar gate ɗin asibitin a gigice tana addu'ar Allah yasa bai mayaudari bane ta haɗu da shi.

Yana hangota ya fito motar sa ransa a matuƙar ɓace, tana isowa ya jefa mata mukullin motar a masife ya ce.

"Ke! An faɗa miki bana da aikin yi ne da zan zauna yi miki gadin mota ko me? Ni za ki mayar shashasha ki shige ki bar ni nan kamar wani kayan wanki. Kin san wanene ni?"

Jin yanda yake masifa yasa ta sulalowa da ruwan hawaye ta ce.

"Dan Allah ka yi haƙuri..."

Wani guntun tsaki yaja tare da juyawa ya shige motar sa yace Miftab yaja su tafi.

Jiki sanyaye ta shiga motar ta zauna tare da kifa kanta a kan starring motar tana jin taratsin da yayi mata yana yawo a ƙwaƙwalwarta. Bayan ta ɗauki tsawon lokaci tana tunani ƙarshe ta kunna motar ta wuce ganin wankin hula na neman ya kaita dare.

Washegari sai wuraren ƙarfe biyu na rana su Alhaji Baba suka iso wanda a lokacin Salman ya jima da isowa.

Bayan Alhaji Baba ya ƙara natsawa ya zauna ya saurari bayanin komai da kyau wanda Asyha da Husaina suka feɗe masa biri har wutsiya sannan daga baya ya kalli Mummy wacce ke ta keta uban kuka yace.

"Ni duk wannan kukan naki ko kaɗan ban kawo shi a kaina ba Zaliha...haƙƙin marayu! Matar da ba ta ji ba bata gani ba kuka cutar da Ita miye ribar ku? Wallahi tunda har kuka ce wannan hanyar kuka zaɓa to fa masifu yanzu kuka fara gani..."

Cikin gunjin kuka ta ƙara marairaice murya ta ce.

" wallahi na tuba Baba...wannan masifar da muka janyowa kanmu tafi ƙarfinmu...dan Allah ka taimaka..."

"Wallahi darajar waɗannan 'ƴa' ƴan naki kawai kika ci,amma da ba dan su ba da ko dafaki ɗanye nama za'a yi sai dai a dafaki.."

Nan suka ƙara tattaunawa da kuma yanke shawarar tafiya Lagos wurin belin Hafiz.

Bayan su Baba sun fito ta biyo baya su domin ta ƙaro musu ruwa kwatsam ta hangosa tsaye ya jingina jikin motar sa yana Kallonta.

Ɗan ƙara ware idonta tayi tare da murza su a hankali tunanin ko dai gizo ne yake mata ba shi ɗin bane.

"Miye kika tsaya kallo? ko na koma ne?"

matso wa tayi tare da dire carton ɗin ruwan gorar da ta ɗauko cike da jin daɗin sake ganin sa da tayi tacce.

"Welcome!"

Jinjina kansa ya yi yana mai ƙure Kallonta ya ce.

"Ya mai jikin?"

"Alhamdulillah! Ta samu sauƙi."

"I...I'm sorry for yesterday...abun ne ya bani haushi that's why I react that way...suna na Fahil Kabeer Abba.."

Jinjina kanta ta yi tana murmushi tace.

"Husaina Mudassir Wazeer..."

Da ɗan alamun mamaki ya kalle ta ya ce.

"Thesame family with Late Dr. Bello Wazeer?

Da sauri ta jinjina kanta tana ƙara Faɗaɗa murmushinta ta ce.

" Eh."

Wayarsa ƙarama ya miƙa mata yace ta saka mishi Numbernta. Bayan ta saka ya Kalleta yana jinjina kai ya ce.

" Ƙila nafi shekara biyar ban taka ƙafata asibiti ba. Amma ta dalilin ki lokaci ɗaya yasa na zo har sau biyu. Allah ya ƙara mata lafiya."

"Amin. Thank you."

Murmushi ya yi mata tare da jinjina kansa sannan ya juya ya shige motar sa ya wuce.

Ta jima tsaye tana Kallonsa tana ta wani blushing har sai da ya ɓacewa ganinta sannan Daga ƙarshe ta duƙa ta ɗauki ruwanta ta shige.

Duk yanda su Mummy ke ɗaukar al'amarin Hafiz ya wuce nan domin wani ne wanda ya fisu ƙarfin iko ya riƙe wuta a wannan maganar. Kuɗinda aka tana da don fitar da Daddy ƙasar Waje wurin nema masa magani ƙarshe su aka ɗauka har da ciko sannan da ƙyar aka samu aka kashe case ɗin Hafiz ɗin.

Daga baya aka sake ɗaga babban gidan su na gusau aka sayar da wasu filayen Mummyn guda uku aka samu aka haɗa kan kuɗaɗe sannan sukayi nasarar fitar da shi.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

*PAGE 42*

"Hey! Are you sick? Naga fuskanki tayi wani iri."

Cewar Aunty Labiba tana mai ƙara tsatstsareni da ido. Murmushi na yi tare da gyaɗa mata kaina ina ƙara lafewa jikinta na ce.

"Na kwana da zazzaɓi ne Aunty Labiba, but Alhamdulillah na ji sauƙi...and ni idan ina ciwo na rasa mi yake damuna sai na yi ta kuka..."

Cike da tausayawa ta ce.

"Allah sarki! To ya jikin?"

"Alhamdulillah. Nasha magani na ji sauƙi...Yah Emraan ina wuni."

Na ambata ina mai bin sa da ido ganin yanda yake ta kallon mu muna magana.

Jinjina kai yayi ba yabo ba fallasa ya ce.

"Lafiya lau. Ya jiki?"

"Alhamdulillah. Ina Aunty Ziza?"

"She's fine."

Haka na bisu ɗaya bayan ɗaya muka gaisa dasu cike da mutuntawa wanda na lura dai tun da na zuro ƙafa na shigo suke min wani kallo tamkar waɗanda suka ga wata sabuwar halitta, hakan sai da ya saka na ji na tsargu. Shi ma Ya Mohaa ɗin tun da muka shigo ya samu wuri ya zauna babu abin da yake sai aikin murmushi musamman da yaga irin yanda suka tarbeni suna nuna min kulawa.

Hairi kam kasa daurewa tayi, hakan yasa ta taso ta kama hannuna tana wani irin murmushi tana kallon ƙwayar idona ta ce.

"Kinga muna ta kallon ki ko Preety? Wallahi ba komai bane tsabar farin ciki ne. Ashe wai akwai watarana irin wannan da za'a wayi gari ya kasance matar Daddy za ta zo cikin gidannan ta tsaya a gaban mu haka..Alhamdulillah ya Rabb! Shi ne ka ɗai abinda zamu ce. Ki sani,wallahy Kina da wata ƙima da girma a idon mu Beenafah. Yanda kika taimaki Yayanmu kika zama sanadin yaye duhu da damuwa da kuma ƙuncin da yake tare da shi tsawon lokaci, kema muna miki addu'ar Allah ya ninka miki alherin da yafi wanda kika masa..."

Hawaye Aunty Labiba ta share tare da jinjina kanta tana wani murmushi tace.

" Bari kawai Hairi! Komai a duniya yana da dalili yana da kuma sanadi. A duk lokacin da Allah ya baka aron dama da lokaci, to kayi aiki da ita da kyau yanda ya dace kada ka tsaya shirme da shiririta ka bar wannan damar ta tafi a banza. A lokacin da Beenafah ta zo gareni ban taɓa kawo komai a raina ba, kawai ji nayi har cikin zuciyata ina so in taimaketa saboda Allah...."

Nadeeyah ta gyaɗa kanta alamar gamsuwa da kalaman Labibar ta ce.

" Mafi girman kuskure da ɗan Adam zai tabka a rayuwarsa idan har ya samu aron dama da lokaci shi ne wulaƙanta wanda yake ƙasa dashi. Wallahi daga lokacin da ka ɗauki girman kai da jiji da kai ka shiga rigar wulaƙanta mutane wai don ka na da wani arziki ko mulki to ka shiga uku kuma ka nemi hanyar halakar da kanka da kanka domin Allah ma da kansa yace baya son mai girman kai mai alfahari..."

"A lokacin da na yi buri da nufin aurenta ko kaɗan ban yi nufin ja baya ba, domin gani ɗaya da nayi mata sai naji cewa ta cancanta. Daga baya kuma Girmanta a idona da kuma matsayin ta sun ninku ne daga lokacin da ta tsayu a gabana a matsayin wacce ta sadaukar da kanta da rayuwarta domin ceton ɗan uwana. She make a great Woman wacce ta kai ƙololuwar girma da nagartacciyar haiba. Allah ya sanyawa wannan auren naku albarka ya baku zuri'a ɗayyaba."

Cewar Emraan yana mai kallon ɗan uwansa cike da nuna ƙwarin gwiwa.

Cikin wani irin yanayin farin ciki Yayan nasu ya jinjina kansa yana wani irin murmushi yana kallona yace.

" Amin.. Amin yah Allah."

Daga nan ya riƙo hannuna a gaban su wanda har sai da naji kunya ta kamani yana murmushi ya ce.

" Shiyasa komai a rayuwa yana da sanadi...ga shi sanadin Labiba na samu canjin rayuwa. Allah ubangiji ya ƙara ƙarfafa mana zumuncinmu ya ƙara mana haƙuri da juna."

Nan muka wuni har dare muna fira muna ta nishaɗi tamkar wani abu bai faru ba, musamman Hairiyya wacce ta zage take ta bani labarin rayuwarsu iri-iri wanda sallah ce kaɗai ke ta da mu. Bayan mun kambala sallar isha, a tare muka yi dinner har Baba Ustaz Wanda Emraan ne kawai baya wurin ya fita wurin wata sabgar gaban sa, a wani gefen kuma sai nake tunanin kamar dai baya so yana ganina kamar hakan yana masa ba daɗi. Domin duk zaman firar da mukayi maganar sa ɗaɗɗaya ce a ciki kuma gabaɗaya ya ɗauke kallon sa daga gare ni.

Suna miƙewa nima na miƙe ina kallon Aunty Labiba na ce.

"Aunty Labiba zan kwana tare daku muci gaba da fira.."

Zaro ido tayi da sauri ta kalli direction ɗinda Yayan nasu ke zaune domin taga reaction ɗinsa, sai dai ga mamakinta koma alamar ya ji zancen da muke bai nuna ba. Ganin ta kalle shin sai nima na waiga na kalle shi amma har yanzu idonsa na kan wayarsa da alama akwai abin da yake mai muhimmanci.

"Kar ki damu, ai muna nan tare tsawon sati ɗaya har sai kin gaji damu.."

Girgiza mata kaina nayi ina dariya nace.

"Gaskiya ba zan taɓa gajiya daku ba."

"To kiyi haƙuri kije sai da safe kin ji, again kinga daman bakya jin daɗi. Allah ya bamu alheri. ."

Bayan sun shige ne na ɗan kalle sa kaɗan, har yanzu bai ɗago daga abin da yake ba, hakan yasa na wuce ciki abina tare da cire kayan jikina na shige wanka.

Sai da na gama duk buƙatar da zanyi sannan daga ƙarshe na tsala wanka na na fito wanda babu abin da nake tunani sai moment ɗinmu na yau. Haƙiƙa komai yayi farko tabbas watarana yana da Ƙarshe. Gashi dai yanda abubuwa suka lalace a tsakaninsu amma kuma gashi yau Allah ya daidaita su cike da soyayya da kulawar juna.

Ina fitowa ban an kare ba kawai na ji na yi karo da mutum har sai da naji na tsorata na ja baya sosai tare da jingina jikina da bangon ɗakin ina mai runtse idanuwana.

Hannunsa yakai jikin ginin ya sanyani a tsakiya yayi trapping ɗina tare da lalubo ƙwayar idona ya mini wannan kallon mai karya duk wata gaɓa ta jikina da murya a ƙasa sosai ya ce.

"mi ma kika ce? Uhm!..."

"Ni wallahy ban ce komai ba, to ni yaushe ma na ganka...wanka fa nake.."

A yanda na yi maganar ba ƙaramin burgesa na yi ba hakan yasa ya yi murmushi tare da ƙara kusantoni sosai ya ce.

"mi kika cewa Labiba...za ki bita ki kwana ko ba haka ba?"

Zaro ido na yi tare da faɗin Innalillahi! A raina. Wato ashe yana jinmu yayi kamar bai ji ba mutumin nan.

"Ki amsa min maganata Bibi...yanzu ga mijin ki amma kike mararin kwana da wata kawai don kuyi fira..."

Girgiza kaina na yi da sauri ina mai runtse idanunawa na ce.

"A'a, ka yi haƙuri dan Allah, wasa fa nake mata...."

Bansan miye abun da ya zo masa a rai ba da yasa ya janye, kawai ji na yi na daina jin daddaɗan ƙamshinsa da yake gab dani, ina buɗe idona yaja hannuna muka je kan gado. Kallon sa na yi because I'm not comfortable with the towel da nake sanye da shi a bakin thigh ɗina na ce.

"kaga fa yanzu na fito wanka...bari na saka sleeping dress ɗina.."

Jinjina kansa ya yi kamar da gaske ya kalleni ya ce.

"Uzurin Shafe-shafe kaɗai zan miki.."

Daga haka ya ja hannuna har bakin dressing mirror ɗin ya ja ya tsaya ba tare da na fahimce ba, na tsaya na yi duk shafe-shafen da zan yi yana gefe ya harɗe hannayensa yana Kallona. Bayan na kambala na juya domin zuwa na ɗauko kayana kawai na ji ya riƙo hannuna ya janyoni.

A hankali ya matso saitin kunnena ya raɗa min.

"Shin akwai wata illa idan muka kwanta a haka?"

Shiru na yi mai tare da saukar da kaina a ƙasa ina jin wasu abubuwa na yi mini yawo a cikin ƙirjina waɗanda ke saka duk wata jijiya mai saka kuzari a jikina tsinkewa.

Within seconds na ƙare masa kallo from head to toe. Gajeren wando ne a jikin sa sai singlet, hakan yasa na ji na ƙara tsorata. Zan iya cewa a ɗaiɗaikun rana ne na taɓa ganinsa a haka, kuma ko shi sai idan ya gama wanka zai shirya a manyan kaya ne, ko bacci zamuyi da kayan baccinsa wadatacci yake kwantawa amma shi ne yau yazo min a haka. Ni fa wannan maganar ma da ya yi min ta ƙara rikitani da yanayin, domin wallahy ban gama farfaɗowa daga sabuwar duniyar da ya jefa ni a cikinta ba.

Tashi ya yi ya kashe fitilar ɗakin ya dawo ya janyoni muka kwanta tare da ja mana duvet ya rufemu. A hankali naji ya shiga janye towel ɗin wanda Bansan lokacinda na saka hannuna na riƙe gam ba a rikice ina faɗin.

"Dan Allah ka yi haƙuri..."

"Ba abin da zan miki Bibi...kawai ina son ki yi min alfarmar jin ɗumin jikin ki a jikina wataƙil hakan ya bada haɗin kai wurin samar da sassauci ga abin da ke damun zuciyata...."

Shiru na yi na koma laƙwas tare da sakar masa towel ɗin kamar wanda ya yi using remote control a kaina. Lokaci ɗaya na ji tunanina ya harba akan neman sanin abin da yake damunsa because daga yanayin maganar sa, shi ya tabbatar da cewa akwai abin da yake damunsa da gaske. Musamman ko yanayin wuninsa a yau, ganin yanda yake sukuku ya tabbatar min da cewa akwai abin da yake damunsa. Kawai dai yana daurewa ne dalilin su Aunty Labiba.

Cikin siyasa ya yi nasarar rabani da towel ɗin a hankali shima ya zare singlet ɗinsa ya manna ni a jikin sa. Ajiyar zuciya na sauke a hankali jin wani sabon abu dake circulating cikin jini da jijiyoyin jikina. A hankali yanayin numfashina ya shiga sauya jin wani irin sabon yanayin da ban taɓa riskar kaina a ciki ba.

Duk yanda nake ji a jikina yanayinsa yafi nawa sauyawa domin tamkar wanda aka jona shocking haka jikinsa ya shiga kakkarwa yayin da ya shiga sauke numfarfashin da suka sa ƙirjinsa ya shiga yin sama da ƙasa.

Hannayensa ya saka ya rungumeni sosai yana mai sai ta zafafan lips ɗina akan wuyana a hankali ya shiga kissing ɗina. Hanunsa yakai ya zame ribbon ɗin kaina, abinda na lura yana matuƙar sanya shi nishaɗi da jefa shi wata duniya ta daban. Hannun sa ya saka ya shiga hautsinasa sai gashi cikin lokaci ƙanƙani ya baje ko'ina akan fuskarsa da fuskata wanda shi ne dalilin ƙara kunna wata wutar a zuciyarsa.

Duk da ina a tsorace, ko kaɗan ban yi yunƙurin hana sa romancing ɗina yanda yake so ba. Sai da ya gama bin duk wata gaɓa ta jikina son ran sa har sai da ya ji cewar he's fully satisfied sannan daga ƙarshe ya mayarda kaina akan ƙirjinsa muna sauke numfashi ya rufemu muka yi bacci.

Can cikin baccin koda na motsa sai na ji ni kamar akan pillow, hakan yasa ido cike da bacci na shiga lalubawa amma kuma baya nan, buɗe idona nayi sai naga ashe ya saka pillow ne ya tare ta ko'ina ya yi min matashi don kada in gane cewar baya nan.

Duk da cewa fitilar hasken ɗakin a kashe ta sai bedside lamp da tayi ƙasa sosai, hakan bai hana ni hango sa ba. Zaune yake a bakin gadon ya saukar da ƙafafunsa a ƙasa yana mai bani baya. Miƙewa na yi tare da lalubo towel ɗina na ɗaura sannan na matso a hankali na leƙasa.

Photo ne riƙe a hannunsa ya ƙura ido yana kallo. Hannuna na kai a hankali na ɗora akan shoulder ɗinsa na dafa sa, murya a ƙasa sosai na kira sunansa dana zaɓa masa a zuciyata da wani kalar Yaruka guda biyu. Ba kalma ce gama-gari ba,domin na zaɓe ta ne na musamman domin kasancewarsa na musamman a cikin rayuwata kamar yanda ya zaɓi kalma ta musamman yana kirana da ita.

"Dayaa!"

Ɗagowa ya yi ya kalleni da ruwan hawaye a idonsa,cikin wani irin mummunan yanayi, murya a karye ya ce.

"Bibi..."

A ruɗe na tallafo fuskarsa na ɗora shi akan ƙirjina na rungumeta tightly ina faɗin.

"Ka yi haƙuri...ka ƙara haƙuri da rayuwa a duk yanda ta zo maka, kuma ka ƙara haƙuri da mutanen da suke kewaye da kai a wannan ƙaramar duniyar Dayaa. Allah yana tare da kai....idan kuma ka ji ƙirjinka ya yi maka nauyi sosai please ka yi Kuka...Yes..ka yi kuka ka rage nauyin zafin da yake zuciyarka..."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull