Kenza eBookz

Ganin ido complete Novel - Chapter 47

Ganin ido complete Novel - Chapter 47

Ganin ido complete Novel Chapter 47: Ganin ido complete Novel Chapter 47. Kwantar da kansa yayi a hankali ya shiga silalo da ruwan hawaye na tsawon lokaci…

3,365 words

Kwantar da kansa yayi a hankali ya shiga silalo da ruwan hawaye na tsawon lokaci ba tare da sauti ba. Hannu na saka cike da jin radaɗi a zuciyata ina shafa Sumar kansa cike da nuna alamun rarrashi. Bayan ya ji raɗaɗin da yake ji ya rage masa sosai ya ɗago tare da nuna min photon murya a rauna ne yace.

" Wannan ita ce Mahaifiyata Bibi...ban taɓa sanin ta ba sai ranar da kika shigo gidana...ban taɓa ganin fuskarta ba sai yau da Baba Ustaz ya zo min da photon ta...."

Girgiza kai ya yi da wasu irin zafafan hawaye masu tsananin ɗaci da ciwo ya ci gaba da cewa.

" A ranar da ta haife ni... A ranar ta ta mutu Bibi... Mem..me na aikatawa Hajiya da za ta saka mini da wannan?na riƙe ta da zuciya ɗaya na raini 'ƴaƴan ta da waɗannan hannayen, kafaɗuna da kuma gadon bayana..na yi aiki tuƙuru, dare da rana, safe da mare ce, ruwa da iska, sanyi da bazara wurin ganin na kula da rayuwarta da ta' Ƴa'ƴanta don kada su yi kukan rashin wani abu kona rana ɗaya....ba abin da tayi min nake dubawa ko tunawa yake sakani gigita da ɗimauta ba Bibi..Asalin mahaifiyata da ta ɓoyemin shi ne abin da yake nakasar da zuciyata...Bibi she told them cewa na mutu bana raye a duniyar nan...waw...wannan wane irin rashin imani ne...yana mini ciwo sosai idan na tuna cewar duk wata soyayya da kulawar da ta nuna min na tsayin shekaru wai duk na GANIN IDO ne,wanda daga zaran na juya baya kuma ni ne maƙiyinta...Mi nai mata da zafi haka?"

Cikin jin wasu irin hawaye na girgiza kaina tare da miƙa hannu na ƙara hasken fitilar bedside lamp ɗin in a kallon cikin idanunsa waɗanda suka cika da zallar karaya da baƙin ciki na ce.

" Babu abin da ka yi mata, Ba komai ba ne wannan fa ce son zuciya da kuma sharrin shaiɗan wanda yayi alƙawarin halakar da duk wanda ya zaɓi tafarkinsa....na sani da ciwo sosai Dayaa...but ka yi haƙuri...ko don su Aunty Labiba dan Allah dan girman Allah ka yi haƙuri...komai na rayuwa kamar yan da na saba faɗa maka yana da dalilin faruwarsa, Ubangiji shi ne mai cikakken sani akan wannan al'amarin kuma shi ne wanda zai yi maka mafita...babu wanda ya isa ya canja abin da Allah ya ƙaddara maka...ba zamu iya maida hannun agogo baya ba Dayaa.. Da zamu iya da duk mun goge munanan ciwukan da ke kwance a cikin ƙirazanmu...but!Sanin cewar bamu da iko akan hakan...dole mu haƙura mu bar komai a hannun Allah wanda baya zalunci kuma bai yarda da zalunci a tsakanin bayin sa ba. Wallahi duk wanda ya cutar da wani daidai da ƙwayar zarra ranar gobe alƙiyama sai Allah ya bi masa haƙƙinsa...ka yi haƙuri...yanzu da kasan da wannan..ka dage da yi mata addu'a daga ita har mahaifinka..Ka yi sadaka ka yi duk wani abun da yake ƙarfinka.. Ubangiji Allah ya sada ku da rahamarsa ya haɗa fuskokin ku a Aljanna firdaus...Ka yafe wa Hajiya dan girman Allah ko don darajar yaranta da ku ka kasance uba ɗaya da su. Ka duba wunin yau irin farin ciki da suka riski kansu a ciki wanda suka rasa tsawon lokaci,.. Motsi kaɗan idan suka yi sai sun ambaci sunanka.. "

Hannayena ya jimƙe a nasa sosai yana jinjina kansa sannan daga ƙarshe yakai bayan hannuna ya share hawayensa yana mini murmushi ya ce.

" Thank you Bibi...as I always said....thank you for existing...da ace babu ke a wannan yanayin..Tabbas rayuwa za ta yi mini wahala sosai..Allah ya saka miki da alheri, Allah ya gafartawa Mahaifinki tare da iyayena, Allah ya ji ƙan mahaifiyarki ba don ta mutu ba ya ƙara mata lafiya mai albarka..Allah ya ƙara mana zaman lafiya....I love you so very much Bibi..."

Har can cikin raina na yi matuƙar jin daɗin waɗannan kalaman nasa masu matuƙar tsada da tasiri a Zuciyata. Toilet ya wuce ya yo wanka ya yo alwala ya zo ya tayar da salla ya shiga jera nafilfili kamar yanda ya saba.

Na daɗe a inda ya barni zuciyata cike da tunane-tunane kala-kala na tsananin tausayinsa akan wannan bahagon al'amarin da ya faru da shi. Tabbas ni Beenafah naga rayuwa amma idan aka buɗa shafin ƙaddarar rayuwar Yaya Muhammad, to tabbas ni nawa farilla ne. Wallahy a yau na yi matuƙar matuƙar tausaya masa. Indai kana numfashi a doron ƙasa, to tabbas ba za ka daina haɗuwa da labarurrukan da za su girgiza maka zuciya ba.wannan fa Iya rayuwata da ta mijina kaɗai na sani, da zan zaga duniya da naji labarurrukan da suka shafe namu, masu al'ajabi da ban tausayi. Allah ubangiji kasa mu dace muyi kyakkyawan ƙarshe. Yah Allah na roƙeka ka bani kariya daga duk wata cuta ta Hassada, girman kai da wulaƙanta al'umma en uwana. Allah na roƙeka...dabba wannan, idan har bata da haƙƙi a kaina, yah Allah ka hanani cutar da ita.

Na daɗe kishingiɗe daga inda nake ina kallon sa sannan daga ƙarshe na miƙe ina mai share hawayen idona na janyo wayata na duba agogo,2:37am haka agogon ya nuna min.

Toilet ɗin na shige nima na yi wanka na ɗoro alwalar na fito na shirya cikin jalabiya, hijabi, hula wanda na ware su na musamman domin bautawa ubangijina cikin tsabta da nutsuwa.

Gabaɗaya sauran ragowar darenmu a nan muka Ƙaresa wurin kai kukanmu ga mahaliccinmu wanda yace mu roƙesa zai amsa mana. Muna nan bamu gushe ba har sai da aka kusa tayar da sallar Asuba sannan ya tashi ya fice masallaci domin gabatar da Jam'i.

Koda ya dawo gidan ni har na kambala azhkar na koma na kwanta na yi bacci. Ficewa ya yi ya ɗauko wani aiki ya dawo ya zauna yana kallon fuskata yana murmushi yana aikin da yake gaban sa.

Koda na farka sha biyu na rana ta riga ta yi. Yana ganin na farka ya tashi ya fice wanda ni duk a zatona wani abun kirkin zai yi. Wani babban dish ya miƙomin tare da brushe ya ce.

"Ga shi ki wanke bakin ki..."

Cike da tsantsar mamaki na hangame baki ina kallon sa na ce.

"Ni fa lafiya ta ƙalau..."

"And ni kuma na ce you won't get out of this bed har sai kin ci abinci.."

Girgiza masa kaina na yi cikin rashin ɗaukar maganar sa da muhimmanci na ce.

"But Dayaa..amma ai marasa lafiya ne a asibiti waɗanda ba su iya sauka daga kan gado ake yi wa wannan...."

"Bibi just obey before complain."

Jin ya ce haka tare da making serious face yasa na karɓa baki alaikum na wanke bakin nawa yana tsaye a kaina na kambala ya karɓa ya juya ya koma tare da faɗin kada na sauko sai ya dawo.

Jim kaɗan sai gashi ya dawo ɗauke da tray a hannunsa ya zauna ya ciyar dani cike da soyayya sannan ya ɗaukeni ya kaini bakin toilet yace.

"ki yi ki shirya, zamu fita da su Labiba...Hairi insist.."

Wani irin lallausan Murmushi na sakar masa ina mai binsa da wani irin narkakken kallon, murya a slow na ce.

"Good morning.."

Rausayarda kansa ya yi gefe lokaci ɗaya yana mai avoiding kallon da nake masa ya ce.

"And don't look at me like that...ki je, muna jiran ki a ƙasa."

Dariya ce ta suɓucemin ganin yanda ya ci wani uban serious Wanda ni sam ban fahimci abin da yake nufi ba.

Koda na kambala shiryawa ko yau 2pm ta yi. Su Aunty Labiba kaɗai na tarar a parlourn tare da shi suna fira. Da murmushi na kalli Aunty Labibar da Aunty Nadeeyah na ce.

"Aunty Labiba, Aunty Nadeeyah ina wunin ku.."

Kallona suka yi dukkan su ba tare da sun amsa ba na ɗan lokaci, sannan daga ƙarshe suka mayarda kallon su gare shi kamar yanda shima yake kallon su, Aunty Labiba ta ce.

"Uhm! Dan Allah Auntyn Adeel kina ji...kada ki sake cewa kowa Aunty wurin nan...ai ido ko bai gani ba yasan ƙima..."

Cike da mamaki na ce.

"But Amma aunty la.."

Hannuna Hairi ta kama tana mai saka idanun ta a nawa tana murmushi ta ce.

"Ahm! Kina ji Mummy...wannan.."

Ta Nuna aunty Labibar tana dariya tana faɗin.

"From today henceforth...sunanta Maman Hanan..Wannam kuma" cewa Da Nadeeyah "Sunanta Maman Dija.Ya Emraan kuma Baban Abeer....waɗannan dai suka ɗai ne za ki ce kina jin kunyar faɗin sunan su kai tsaye, saboda haka duk wanda kike so ki kira sunan sa, you are free, domin girman ki ne da Allah ya baki..don Allah kada ki sa Daddy ya yi alalen Gero damu.."

Dariya muka kwashe da ita sannan daga ƙarshe muka tashi muka fi ce daman suma already a shirye suke.

A hanya na kira Ammie muka gaisa sannan na bata su Aunty Labibar su ma suka gaisa da ita.

Nishaɗi muka shawo na wuni ɗaya zungur gabaɗayanmu wanda har mamakin sa nake irin yanda yake yi da su. Daman ashe haka suke rayuwa da shi? Na tambayi kaina ina mamaki, wanda gaskiya ko ni ce dole na yi kuka idan har akace wani abu ya rabamu. Duk abin da yake min ko kaɗan basu nuna jin kunya ko wani mamakinsa ba. Rayuwarsu gwanin burgewa cike da wayewa da ilmi. Koda muka dawo gida a gajiye muka shigo.

Kallona ya yi a gabansu ya ce.

"Na goya ki a bayana na kaiki ciki??"

Dariya suka fashe da ita sannan Hairi ta wani ɓata fuska tana faɗin.

"Daddy shiyasa ranar na ce bari na hawo bayan ka nasan shi ne na ƙarshe domin nan gaba ba zan samu wannan damar ba, to gashi tun ba'a je ko'ina ba ka watsar dani..."

Dariya muka yi sannan ya janyota cikin sigar rarrashi ya ce.

"Nooo! Ai no one can take your place...Zo...zo ki hawo na fara kaiki.."

Tuma ta yi ta ɗane gadon bayan sa ba kunya, haka na bita da wani kallon mamaki ina dariya,Aunty Labiba tana dariyar ta ce.

"Shegen son jiki kamar mage...Allah ya baki wanda zai iya jimirin goya ki..."

Tsaki Nadeeyah ta yi tana girgiza kai ta ce.

"Wannan ƙatuwa waye wanda bai da aikin yi zai zauna ɗinɗimata a baya..."

Hannayen ta ta saka ta rufe kunnuwanta alamar ma bata son zancen sannan a shagwaɓe ta ce.

"Daddy take me to my room please,...su Aunty Nadee za su fasa mini dodon kunne.."

Wucewa ya yi kamar yanda ta ce ya kaita har kan gadonta ya sauke ta sannan ya kalle ta ya ce.

"Na jira sai kin yi bacci sannan na tafi?"

Girgiza kai ta yi idonta cike da kewar yanayi irin wannan ta ce.

"A'a Daddy...sai na yi wanka, na rage karatu sannan zan kwanta,..."

"Akwai Exams ne?"

"Uhm! But in the Next 3 to 4 weeks haka, kasan mai zurfin ido da wuri yake fara kuka.."

Jinjina kansa ya yi yana kallonta cike da alfahari ya ce.

"I'm proud of you favourite...Allah ya taimaka ya bada sa'a ya nuna min kin kambala lafiya.."

"Amin yah Allah, thank you."

"To, sai da safe."

"Allah ya tashe mu lafiya.."

Yana ficewa ta ɗauki wayarta ta kira Hajiyarsu dake gida Nigeria cike da ƙwarin gwiwa ta ƙara kwantar mata da Hankalinta da cewa ta ƙara haƙuri komai zai zo ya wuce a hankali indai an yi haƙuri.

Koda ya dawo ni har na shige toilet na rage cikina na fara wanka. Ina cikin toilet ɗin ya shigo...wani irin dokawa ƙirjina ya yi, a dururuce na shiga neman yanda zan kare jikina wai don kada ya gani.

"Relaxed Bibi...wannan tsoron da kunyar duk na miye?"

Idona a ƙasa na girgiza kaina a kunya ce na ce.

"Ni dai dan Allah ka fita..."

Ganin yana cire singlet ɗinsa shi ne abin da ya ƙara ruɗani wanda shi Sam ko a jikinsa. Duk yanda nake noƙewa hakan bai hanashi isowa inda nake wankan ba, kai tsaye ya karɓe sponge ya shiga yin son ran sa. Wanda tun a nan na tsinke domin a yanda naga yanayinsa yau kam babu abin ya isa ya ƙwaceni daga hannun sa. hakan ce kuwa ta kasance, domin tun da muka fito muka gama shiryawa bai jira komai ba ya fara kai mini zazzafan farmaki wanda ko a yau ɗinnan daƙyar nasha a hannun sa, da kuka da komai amma bai ɗaga mini ƙafa ba sai da ya gama jin ya kai geji sannan ya dawo rarrashin gulma wanda nake ɗaukar sa kuwwa bayan hari. Wai sai an gama da kai sannan a dawo baka wani haƙurin gulma.

Duk abun da ya rungumeni yana faɗamini ina jinsa sarai, kawai share sa na yi. In banda rashin tausayi kwana ɗaya ne fa ya tsallake...mutum bai ko gama farfaɗowa ba tsabar jaraba a sake saka shi cikin sabon zazzaɓin, da wannan mitar na yi bacci a raina. Sai gashi washe gari yana dawowa daga masallaci abu kamar wasa ya sake lalubeni tas ya shanye daɗinsa ya bar ni da kuka. Wato duk kukan da nake masa da magiya a daren jiya kallon ba ki ma ga komai ba ki jira gobe da safe zan ƙara yake mini.

Da wuri yau ya shirya ya fita ya barmu mu kaɗai a gidan muka yi ta nishaɗinmu sai 6pm ya dawo.

Kayansa na amsa na wuce ciki, bayan ya gama gaisawa da su sun gama yi masa sannu da zuwa ya wuto ciki.

Ganin yanda nake ɗan fuffuskewa yasa ko tsayawa rage kayan jikin sa bai yi ba yazo inda nake tsaye ya rungumeni yana mai lalubo ƙwayar idanuna waɗanda tuni suka fara sheƙin hawaye ya ce.

"Wannan duk fushin ne haka? Duk kiran da nayi miki yinin yau fa a ciki-ciki kika amsa Bibi...to ki yi haƙuri ba zan ƙara ba, na yi alƙawari wannan na yau ɗin shi ne na ƙarshe ba zan sake ba I promise..."

Tafin hannuna na saka na share hawayena ina mai yarda da kalamansa na jinjina kaina wai ni a dole gani na sauko daga dokin fushin da na hau na ce.

" Shi ke nan.."

"To idan kin haƙura ki ɗan murmusa mana.."

"Uhm!"

Abin da kawai na ce kenan ina mai ƙara kawar da kaina gefe.

"Yauwa...thank you. Yanzu muje ki rakani na yi wanka na ci abinci."

A tare na taimaka masa ya rage kayan jikin sa ya shiga wankan ni kuma na je na kawo masa abinci har nan bayan ya fito ya shirya cikin simple wears ya zauna yana cin abinci nima yana bani wanda kamar yasan ban wani ci abincin kirki ba.

Kallona ya yi ya ce.

"Friday, In sha Allah zamu tafi Sudan idan Allah ya kaimu.."

Faɗaɗa murmushina na yi cike da jindaɗin maganar na ce.

"Masha Allah. Nice idea, Allah ya kaimu na rai."

Dire spoon ɗin hannunsa ya yi ya kalleni cike da sagewar gwiwa ya ce.

"Ko ya za su kalleni tsayin shekarun nan?"

Hannuna na ɗora akan nasa ina murmushi na jinjina masa kaina na ce.

"Khairan In Sha Allah...za su yi matuƙar farin ciki da ganin ka kamar yanda kai ma ka kasance cikin ɗoki na son ganin su."

*********

Gefen su Mummy kuwa. Sun sha matuƙar wahala a wurin jinyar Daddy wanda sai da ya gama tatse ɗan sauran abin da ya rage musu tas sannan aka juyo aka dawo da shi gida.

Ranar da suka iso, a motarsa Salman ya ɗauko su zuwa gida wanda suma a ranar suka iso. Daman bayan an yi nasarar fita da shi, gida suka koma daga su har Aunty Aysha, sai Hajiya Er Mama ce ƙanwar Mummy Zaliha ta zo gidan ta zauna da Humaida da Husaina. sai yau da aka ce za su iso suka shirya suka zo amma bada Aunty Aysha ba, ita tana can bata zo ba, amma dai waya kam duk bayan wasu minute ko hour Haka sai ta kira.

Ana shigowa da shi gidan suka ɓarke da wani irin kuka, ganin yanda Daddy ya dawo tamkar wata fatalwa tsabar yanda yasha jinya. Mummy ma kamar ba Mummy er gayu babbar Mace mai aji ba.

Katifa suka fitar veranda suka yi shimfiɗa aka ɗaura shi a kai. Kwance ya yi zuruu! Yana mai binsu da ido ɗaya bayan ɗaya gwanin tausayi.

Hakan shi ne abin da ya ƙara karye musu zuciya suka ci gaba da kuka suna ta mishi sannu ba kamar Hassana wacce sai yanzu take jin wata irin nadama tana ɗawainiya da rayuwarta.

Bayan sun gama yi musu sannu da zuwa an gaggaisa, Salman ya juya ya bar gidan domin ya basu wuri su tattauna.

Kallon Mummy Hajiya Er mama ta yi ta ce.

"Oh! Hajiya ya jikin Alhaji? Daɗa haka ya dawo? halin jinya kamar ba shi ba."

Girgiza kai tayi zuciyarta cunkushe da wani irin raɗaɗi ta ce.

"Ai Alhaji an sha jinya Hajiya Er mama. Allah dai yasa yana da sauran shan ruwa a duniya..ki duba ki ga, magani ake.. Kuɗi ake narkawa..Magani ake amma kamar ana ƙara turara masa turaren ciwo.."

Miƙewa Hassana ta yi tana mai sake fashewa da kuka tana girgiza kai ta ce.

" Kai duniya! Wallahi na ƙara tsinkewa da al'amarin rayuwa...Ina tuna lokacin da Ammie ke cikin tsananin zafin ciwo da raɗaɗi...wanda 70% na daga cikin matsalolinta ku ne sila Mummy da ke da Daddy...kun ɗauka cewa duniyar za ta yi mana girma da faɗin da har abada ba za'a Iya kamo ƙafarmu ba...sai gashi cikin en ƙalilan watannin da ba'a ko shekara ba duniya tayi juyin masa damu...ina amfanin hakan?? Da muka biye son zuciyarmu mi hakan ya tsinana mana? Ammie da gatan ta gaba da baya ita da yaranta amma haka ku ka busar da zuciyoyinku ku ka shiga cutar da su..."

Mummy kam, hawayenda suka kasa tsaya mata ta share tana mai girgiza kai cike da karaya ta ce.

" Astagfirullah Allah! Wal...Wallahy sharrin Zuciya ne kawai..gashi tun ba'a je ko'ina ba rayuwa ta shiga gardama mana.."

Muryar Daddyn suka ji sama-sama cikin sautin da baya fita sosai, yana wani irin tari a Hankali ya ce.

"Ku nemo min Mulaifa dan Allah...Ku nemomin Beenafah da Bahrain dan Allah kada na mutu ba su yafe min ba.."

Waigawa Mummy ta yi ta Kallesa cikin nuna kulawa ta ce.

"In Sha Allahu ba zaka mutu ba Alhaji, sai mun cika burinka na ganawa da Mulaifa da 'Ƴa'ƴanta In Sha Allahu."

Miƙewa Husaina tayi tana mai zura hijabinta ta yi waje tana mai share hawayen Idonta.

Kallonta ya yi wanda ta yi wani irin dagaje-dagaje da kuka ya ce.

" Ya ya dai! Ko wani abun ke Faruwa da Daddyn?"

Girgiza masa kai tayi tare da ƙirƙiro murmushi ta ɗora akan Fuskarta tana kallon shi a sanyaye ta ce.

"Jikin Daddy da sauƙi Fahil..."

"Zan Iya Shiga na gansa?"

"Eh, Bismillah."

Gaba ta shige ya bita a baya har gaban Daddy ya duƙa a ƙasa ya gaishe su ya mai ya jiki sannan ya ciro dubu hamsin ya ajiye a gefen shimfiɗar ya fito waje.

Kallon ta ya yi yana jinjina kai yace.

"In Sha Allahu zai samu lafiya kin ji ko. Addu'a yake Buƙata ba wannan koke-koken ba. Allah ya bashi Lafiya yasa kaffara ne."

Jinjina kai tayi tana mai jin wasu irin sabbin hawaye ta ce.

"Thank you so much Fahil. Haƙiƙa ka shigo rayuwata a lokacin da ya dace, na yarda da cewa komai na rayuwa yana da dalilin faruwarsa...shiyasa a lokacin da maganar aurena ta rushe a baya..Sai na haƙura na kuma yi addu'ar mafi alheri...yanzu kuma kai ɗinnan..kai ne bangon Jinginata Fahil...bangon da ya kasance ƙaƙƙarfan shamaki da ke hana ni karyewa a duk lokacin na ji cewar na gaza. I love you so much Fahil."

Murmushin nan nasa ya yi mata wanda yake nakasa mata duk wani kuzarinta sannan ya jinjina kai ya ce.

" I love you too Hussyn Fahil. Na gode da yarda dani da kika yi. Allah ya cika mana burikanmu na alheri. Allah bashi lafiya..ki je gida. Ni bari in koma. Sai mun yi magana."

Ɗaga masa hannu ta shiga yi tana murmushi har sai da taga ya ɓacewa ganinta sannan ta Juya ta koma gida.

Tana shiga Mummy ta kalle ta da mamaki tace.

" Husaina shi kuma wannan wane ne?"

Kai tsaye ta kalle ta tace.

" Sunan sa Fahil. Shi ne wanda yake so ya aure ni."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull