Ganin ido complete Novel - Chapter 48
Ganin ido complete Novel Chapter 48: Ganin ido complete Novel Chapter 48. Jinjina kai ta yi tare da mayarda idonta akan lambar wayar Alhaji Baba da take…
3,372 words
Jinjina kai ta yi tare da mayarda idonta akan lambar wayar Alhaji Baba da take nema ta ce.
"Allah ya tabbatar da alherinsa a ciki."
Ɗaki Hussaina ta shiga a ranta tana faɗin 'Lallai kura tayi lafiya'! Shi kenan da gaske mummy ta zubar da makaman yaƙinta. To Allah yasa ta ɗaure a hakan.
Suna nan bayan an gama sallar Isha, Salman ya shigo tare da yara suka sauke musu buhun shinkafa da su semovita da sauran kayan buƙatar rayuwa daidai yanda zai yi sannan washe gari ya Juya ya koma ya bar Hassanar nan domin ta ƙara ganin iyayenta.
Alhaji Baba da Uncle Isma'ila sai misalin ƙarfe uku suka iso gidan. Bayan sun ci abinci sun gama gaisawa ya kalli Mummyn ya ce.
"Alhamdulillah! Alhaji Mudassir jiki ya yi kyau wanda babu abin da zamu ce sai dai Allah ya ƙara masa lafiya...Touh! Dan gane da batutuwan da muka tattauna dake tun kuna can dai, mun kai ƙarshe, mutumin da aka siyarwa wannan gidan naku da kuke ciki, kamar yanda muka yi dashi duk ranar mijin ki ya dawo daga jinya za ku tashi ku hannunta masa gidan sa shi kuma ya cika ta muku sauran 3M ɗinda kuka biyo sa. Saboda haka, shi dai kyawon alƙawari cikawa,za ku tattara ku koma gusau ku bashi gidansa. Sannan...maganar da mukayi da Isma'ila itace. Wannan gidan da ya taɓa ararwa iyalan marigayi Bello, to da cewa na yi ya ara muku, amma bayan duba da kuma wani lissafi da na yi, da ace ara muku akayi ku zauna gwanda ace mallakin ku ne, kalmar aro ba kalma ce mai daɗi ba, musamman yanzu yanda zamani ya lalace zumunci ya taɓarɓare. Saboda haka, mun yi magana zai ba ku shi 2M idan ya so sauran 1M ɗin sai ku samu wani abin da kuka yi da ita..."
Ɗan ƙara gyara zamansa ya yi yana kallon yanayin Mummy ya ci gaba da cewa.
" Abin da yasa na yanke wannan hukuncin shi ne...kinga dai yanda abubuwa suka lalace muku, ga yanayin jikin mijin ki yanda ya kasance, sannan ke ɗin nan Mace, ba za ki iya ɗauke nauyin lalurar waɗannan 'ƴa'ƴa na ku ba. Amma idan kuna can cikin dangi duk wani abin da ya gagara...sai en uwa su tallafa muku. "
Jinjina kai ta yi tana wani irin kuka ta ce.
" Ba komai Baba...Allah yasa hakan shi ne mafi alheri...na gode, na gode sosai Allah ya saka da alheri."
A hankali Humaida ta taka taje jikin Hussaina ta kwanta tana mai fashewa da kuka ta ce.
" Shikenan da gaske Aunty Hussaina zan bar karatuna na koma zaman gida...shi kenan ma driver na yaƙi ya dawo, komai mun rasa kenan da gaske..Wallahy abincin da ma ake a gidannan yanzu daurewa kawai nake amma bana iya ci....."
Murmushin yaƙe Hussaina ta yi mata alamar shi dai yaro-yaro ne sannan ta jinjina mata kai ta ce.
"Allah na tuba Humaida..daman wanda bai ga uwar sa ba ai bai isa yaje neman kakar sa ba, ke da ko mota ɗaya babu yanzu a gidanku har kike zancen wani driver da karatun milyoyan kuɗi? Ki yi haƙuri, ki bai wa zuciyar ki magana, yara nawa ne ba su samu damar karatun ba bayan an tauyesu ta ƙarfin tsiya suka haƙura suka ci gaba da rayuwa ballantana ke. Muyi ta addu'a, Allah ya kawo mana alheri ta hanyar da bamu za ta ba ya sanya wa rayuwarmu albarka."
*********
Kyakkyawan sammako muka yi zuwa Airport gabaɗayanmu har da Emraan wanda ni dai tun ranar da suka iso ban ƙara sanya shi a idona ba sai a yau ɗinnan.
Wani lounge muka shiga dagani sai shi muka zauna.
Leƙo fuskata ya yi yana murmushi yace.
"Wai har yanzu ba za ki yi min magana ba kenan Bibi?"
Ƙara rausayar da kaina na yi gefe ina wani ƙara fuskewa ba tare da na Kallesa ba na ce.
"Ni bana magana da wanda idan ya yi alƙawari yake saɓawa...kasan a yau ɗinnan zamu yi wannan tafiyar amma kuma kasa jikina sai ciwo yake..."
Hannuna ya kama cikin rarrashi ya sumbata ya ce.
"To ai dai na yi alƙawari daga wannan ɗin shikenan..."
Janye hannuna na yi ina wani ƙara cuno bakina na ce.
"Ai ko shekaranjiya haka kace...but amma sai da ka karya alƙawarin.."
"To na ji...yanzu ai dai kinga garin mutane zamu tafi, kuma na san ba lallai ma mu ƙara ganin juna da dare ba sai dai idan mun dawo gida. Saboda haka na yi alƙawari ba zan sake miki komai ba tunda bakya so..."
Hannuna ya ɗaga ya ɗora akansa yana dariya ya ce.
"In rantse miki?"
Ban san lokacin da na fashe da dariya ba akan wannan abin da ya yi. Film ɗinda muka kalla na Indiya a daren jiya dani da shi, shi ne wai ya yi min acting ɗinda actor ɗin da ya ɗora hannunsa akan yayarsa ya rantse da Ita. To mu ɗin Indiyawa ne da zai ce ya yi rantsuwa da kaina alhali mu ɗin ba gantalallu ba.
Kissing ɗin lips ɗina yayi lightly ya janye yana dariyar Shima ya ce.
"Yauwa abar ƙaunata ko ke fa."
Kaina na ɗora akan shoulder ɗinsa a hankali na ce.
"Mun yi waya da Ammie ɗazu. Ta ce tana mana fatan sauka lafiya mu gaishe da kowa..."
Jinjina kai ya yi ya ce.
"mun gode sosai. Allah ya saka da alkairi ya ƙara mata lafiya."
"Amin."
Muna nan sai ga Hairi ta shigo tare da samun wuri ta zauna a kusa dani. A haka muka ci gaba da tafiya wanda sai da muka share 4hours 30mnt sannan muka sauka a Khartoum International Airport dake ƙasar ta Sudan.
Wasu tawagar motoci ne jere cikin tsari guda huɗu, Range Rovers ne black convoy guda huɗu masu wani irin sheƙi suna walwali. kowaccen su da Sudanese flag sticker da kuma tambarin sunan MUSDHAPHA SAMI a jiki.
A yanda na cika da tsananin mamaki, na lura ba ni kaɗai ba, hatta uban gayyar da su Aunty Labiba, sun cika da al'ajabi.
Kallon Baba Ustaz Dayaa ya yi yace.
"Baba..ka sanar musu ne?"
Jinjina kai ya yi ya ce.
"Eh, na samu nasarar isar musu da saƙon cewa iyalin Alhaji Attahiru za su zo kawo musu ziyara amma ban sanar musu komai game da kai ba.."
Jinjina kai ya yi alamar gamsuwa, sannan daga nan muka taka mu shiga mota ɗaya dani da shi sannan Baba da Emraan, sai mota ɗaya su uku. Daga nan muka ɗauki hanya sai Oumdurman.
HOUSE NO. 17, SAMI DISTRICT, OUMDURMAN, KHARTOUM STATE, SUDAN.
Bamu ƙara cika da al'ajabi ba sai da muka doso unguwar wacce take ta musamman a cikin yankin. Babban gida ne mai taken Koda me kazo an fi ka duk da dai ba'a faɗamana hakan ba, amma dai daga yanayin manyan gine-gine da tarin dukiyoyin da ke malale a harabar gidan kaɗai ya isa ya tabbatar maka da cewa ba ƙaramin wuri ka zo ba. Domin kuwa, an ƙawata makeken babban filin farfajiyar gidan cikin adon flowers na musamman da kuma flags na Sudan....
Kuyi haƙuri ina cikin uxuri kwana biyu.
✍️ *OUM-AMEER* ✍️
P43
Gidan part-part ne flat gasu nan iri ɗaya sun kai ƙwara biyar wanda an tsara su gwanin sha'awa, sannan wani abun burgewa shi ne;rufin gidajen ba kamar namu na Nigeria ba ne da muka saba gani, gini ne kamar na ƙasa zan ce wanda a saman rufin ɗin shafe yake da ƙasa ba kamar mu da ake rufi da zinc ba. Ga rumfuna nan suma an ƙawata domin zaman shaƙatawa, ga bishiyoyi nan suma sai kaɗa iska suke mai sanyi. Wani irin ƙamshi ne na musamman ke tashi a farfajiyar gidan wanda ya ƙara tabbatar mana da cewa mun zo wuri na musamman.
Kallona Hairi tayi murya a ƙasa sosai cike da nishaɗi tana jinjina kanta ta ce.
"Aunty Beena...wurin ya ƙayatar ko! Gaskiya I'm impressed!"
Gaba na yi na fara taka wa a hankali tare da riƙa hannunta na ja ta ganin su Baba Ustaz ɗin sun yi gaba.
Lokaci ɗaya ahlin suka fito gabaɗaya suka tsaya a balcony ɗin babban gidan. A matsayinmu na baƙi wanda wannan ɗin shi ne karonmu na farko a gidan;Maimakon muga sun yi mana tarba irin ta baƙi da ta 'ƴan gida kamar yanda aka saba yi idan mutum yaje sabon wuri,ba hakan ce ta faru ba, domin kuwa;gabaɗaya yanayin damuwa da baƙin ciki shi ne abin da ya yi wa fuskokinsu ƙawanya.
Kallon tuhuma muka shiga jefawa kanmu, musamman Ya Mohaa da ya ji wani irin faɗuwar gaba na jin tsoron kada ace korarsa za su yi. Sai yanzu yake jin nadama a ransa cewa;dama ace tun farko Baba Ustaz ɗin bai sanar musu ba. Ƙila sam ba su yi murna da zuwan Ahlin Alhaji Attahiru Araam ɗin ba. Ƙila zuwan na su ya tado musu wani miki da raɗaɗin da ya jima kwance a cikin ƙirazan su na tunawa da 'ƴar su da kuma jikan da suka ɗauka cewa za su rayu da shi a matsayin wanda za su riƙa gani ko bayan mutuwar 'ƴar su, amma haka shi ma ya mutu ya bar su. To don mi za su yi farin ciki? Tabbas dole su kasance a baƙin ciki da damuwa a duk lokacin da suka yi ido biyu da familyn Alhaji Attahiru Araam.
Muna kai gangar hawa ɗan matattakalar balcony ɗin muka ja muka tsaya.
Wata kamilalliyar dattijuwa ce wacce ke cikin shigar lafaya fara ta alfarma ta tako zuwa gaban Ya Mohaa ta tsaya a gabansa tare da fashewa da kuka. Hannayenta ta ɗora akan gefen kuncinsa na dama da hagu ta sumbaci goshin da kuma kumatunsa cike da bege sannan ta rungume shi cike da zallar nuna kewa ta ce.
"HAMMODI...Idonka kenan? Idon kenan Hammodi? Ashe daman kana raye tsawon shekarun nan muke ta baƙin ciki da kukan rashinka.."
Cike da mamaki ya janye tare da ƙura ido yana kallonta. A yanda take kukan ne ya yi matuƙar ƙona masa zuciya har bai san lokacin da hawaye shima suka wanke masa fuska ba.
Ganin irin kallon da yake mata yasa ta jinjina masa kanta yayin da take kuka da murmushi a lokacin ɗaya ta ce.
"Ni ce JADDA Hammodi...ni ce nan Kakar ka wacce ta haifi Mahaifiyarka.."
Wani irin abu ne ya ji ya daki ƙirjinsa lokaci ɗaya, jin furucin cewa wai itace Grand Ma ɗin shi. Without second thought ya sake rungumeta sosai yana mai jin wani irin sanyi a ransa duk da cewa ya kasa furta mata ko kalma ɗaya.
" Mun yi kewar ka Hammodi, mun yi kuka mun yi baƙin ciki da labarin mutuwar ka ya riskemu...babu watarana da za ta zo ta wuce ba tare da na saka Jaddin ka a gaba cewa ina so in je ko ƙabarinku kai da mahaifiyarka na sake gani Hammodi..."
Janyewa tayi ta kalle shi sannan ta waigo ga wani dattijo wanda babu abin da yake gani a fuskar sa face zallar zubin fuskar mahaifiyarsa ya ji ta ce.
"Je.. Je wurin Jaddin ka Hammodi..."
Cikin takun da bai gaza huɗu ba ya isa gabansa ya tsaya idanun nan tab da ruwan hawaye.
Sumbatar goshin sa yayi da kumatunsa kamar yanda ta yi wanda da alama ita ce mafi ƙololuwar tarbar da suke yiwa baƙon su.
Shi kam hawaye ne ya zubo masu cike da ɗaci da nuna tsananin kewa. Cikin wasu irin kalamai ya jinjina kansa tare da ɗora hannayen sa akan shoulders ɗin Ya Mohaan ya ce.
"Mutuwa kalma ce wacce duk musulmi na ƙwarai yarda da ita wajibi ce ga kowane ɗan Adam...tabbas mun yarda da kalma ta mutuwa a gareka Hammodi, amma kuma ta yi mana matuƙar wahala da nauyi a Ƙirji...labarin mutuwarka ya riskemu a lokacin da sam bamu tsammata ba. Mun Ƙirga cikakken lokacin da ya kamata ka dawo garemu bayan mun nemi alfarma a wurin mahaifinka ya amince, lokaci ne kaɗan ya rage ka dawo garemu, bayan mun gama duk wani shirye-shirye mun tsara maka komai yanda ya kamata...kwatsam sai mummunan labarin mutuwarka ya riskemu. Mutuwar ce kawai Hammodi...Amma mun rayu tsayin lokaci ba don kai da mahaifiyarka kun mutu a zukatanmu ba..."
Rungumeshi Ya Mohaa ya yi yana mai jin wasu irin hawaye yace.
" JADDI!!! Ban sani ba..ban taɓa sanin cewa ina da wata mahaifiyar ba...ban taɓa sani cewa ina da ku ba duk tsayin lokacin nan JADDI...ku yafe min, ku yafe min dan Allah..."
Ba su ba, hatta mu da muke 'ƴan rakiya sai da muka zubar musu da ruwan hawayen tausayinsu musamman Dayaa...wallahy komai rashin imaninka sai ka tausaya masa.
Bubbuga bayan sa Jaddin ya shiga yi, cikin wata irin wuta da ke ciciyar zuciyarsa ya ce.
" Tabbas! Duk wanda yake da hannu a cikin wannan mummunan aikin sai ya ɗanɗana kuɗarsa...ko duk abin da na mallaka zai ƙare sai na tabbar ya ji a jiki da zuciyarsa irin raɗaɗi da ƙuncin da ya wanzu a cikin zukatanmu tsawon lokaci..."
Hannun shi Jadda ta kamo ta tsaya da shi a gaban wasu mata ta kalle su sannan ta kalle sa ta ce.
" Wannan ita ce Fattoom, wannan kuma Razia, su ne ƙannen mahaifiyarka...sai Mu'aƙƙib ga shi nan.."
Ta faɗa tana mai juyawa wurin wani dattijon mutum amma bai kai Jaddi tsufa ba.
"Na rantse da Allah mai girma! Sai na tarwatsa rayuwar duk wanda ya shirya wannan makircin..."
Rungumar da Mohaa ya yi masa ne ta hana shi ƙarasa zaratan kalaman da yake fitarwa daga bakin sa masu nuna zallar ɗaukar fansa da rashin ɗaga ƙafa da duk wanda yake bayan wannan abun.
"Jadda...Miyasa za ku tsaya a nan? Ya kamata a shigo da su ciki."
Cewar wata matashiya.
Jinjina kai Jadda ta yi tare da faɗin.
"Haka ne, kin yi gaskiya Suwara."
A tare matan suka iso inda muke tsaye. Tabbas ba don girmamawa da karrama baƙo na daga cikin abu mafi muhimmanci da girma ba a wurin su, da tabbas ba zamu Iya gane kan su ba. Ganin yanda suka tsaya suna kallonmu yasa Aunty Labiba ta harɗe hannayenta alamar ban haƙuri ta ce.
" Ku yi haƙuri.."
Janyota Jadda ta yi ta sumbaci goshinta sannan ta jinjina mata kanta da ɗan murmushi ba tare da ta yi magana ba. Haka tabi mu ɗaya bayan ɗaya ta yi mana sannan muka ɗunguma zuwa cikin katafaren parlourn wanda ya ji shimfiɗu da kayayyakin more rayuwa na alfarma.
Wani irin freezing muka yi ganin HAJIYA zaune a tsakiyar parlourn tana kuka.
Gabaɗaya yaran na ta ba ƙaramin kaɗuwa suka yi da ganinta ta ba a irin wannan lokacin.
Ya Mohaa kam dama tun a waje ƙwaƙwalwarsa a toshe take. Tunanin yan da su Jaddi suka san da labarin wai yana raye ne ya tsaya masa a zuciya, musamman da suke iƙirarin cewa wanda duk ya aikata musu haka sai ya ɗanɗana kuɗar sa. Ganin Hajiya da ya yi kenan shi ne amsar tambayar sa.
Cikin wani irin mamaki EMRAAN ya kalle ta ya ce.
"Hajiya!!! Mi kike a nan?"
Sautin kukan ta ya ƙaru jin kalar tambayar Emraan a gare ta.
Miƙewa ta yi ta tsaya tana kallon Muhammad ɗinta wanda zuciyar ta ta cika da kewarsa cikin wata iriyar karaya ta ce.
"Ni ce na ɓata komai Emraan...saboda haka, ya zama dole na gyara da kaina...shiyasa na iso kafin ku..na bayyana musu gaskiyar duk abin da ya faru domin na sauƙaƙ..."
"Babu wani sauƙi a kan ki Hajiya Batula, wallahy dole zamu gurfana dake a gaban kotu...Duk abin da kika Kawo mu a garemu ba dalili ba ne,domin bamu yi gadon talauci ba da har kike tunanin idan kika ce kina son mallakar dukiyar RANIA zamu tsaya jayayya dake..."
Cewar Fattoom tana mai bin ta da wani irin kallon tsana da wutar fansa mai babbaka a cikin ƙirjinta.
Murya cike da nuna zallar karaya da rashin mafita ta kalli Fattoom ɗin ta ce.
" Za ku iya yin duk abinda kuka ga dama, ƙofa a buɗe take... Ni miye ya rage min a duniya?? Dangina, 'ƴa'ƴana da ma sauran mutanen da ke kewaye dani duk sun guje ni akan wannan mummunan aikin da na yi. A yanzu rayuwata ba ta da wani amfani, saboda haka ku kai ni a zartar min da duk wani hukuncin da ya dace dani...Na riga na gama nawa, kuma na gode wa Allah sarki da ya tona asirin nawa na farga na sauke duk wani haƙƙin da na ɗaukarwa kaina na wannan yaron tun kafin na mutu ko kuma yayi min nisan da ba zan iya kamo shi ba...Haƙkin Mim....Mijina kuma da ya yarda da ni..."
Wani irin matsanancin kuka ne ya sarƙeta wanda ya hana ta ƙarasa fitar da sauran abin da yake ranta.
Cikin kaukkausar Murya Jadda ta bi ta da wani irin kallo ta ce.
" Wannan kuma duk ya rage na ki, duk wannan koke-koken da kike wallahy ba zai hanamu shari'a da ke ba...Jami'ai!!! Ku shigo ku wuce mana da ita!"
Ta ƙarasa maganar tana mai ɗaga murya. Cikin ƙiftawar ido, sai ga jami'ai Mata da Maza sanye cikin kaki sun shigo cikin parlourn kai tsaye sun zagaye su.
Rarraba ido ya fara yana mai lissafin maganganun kakar tasa waɗanda suka nuna tsananin zafi da kaifin ɗaukar fansa.
Lokaci ɗaya ya yi wani taku, kafin su kai ga tsayawa gabanta shi har ya riga su isa. Hannun sa ya ɗora a saman kafaɗarta ya rungumota a ƙirjinsa cike da zafi a kalamansa ya ce.
"Ita ɗin fa Mahaifiyata ce!!! Ita ce wacce ta raineni tsawon shekaru....Baba!"
Ya kira sunan Baba Ustaz yana mai kallon inda yake tsaye ya ce.
"Idan za ka iya tuna kalaman mahaifina na ƙarshe a ranar da zai rasu akan gadon asibiti...A wannan ranar, Hairi tana kwance akan kafaɗata tana bacci, a lokacin tana shekaru uku, Nadeeyah tana tsaye a gefen haguna hannunta a cikin nawa, Labiba kuma tana zaune a gefensa hannunta cikin na Alhajin itama tana kuka, Emraan baya nan yana makaranta, Hajiya da kai, kuna tsaye kowa da damuwa baibaye akan fuskarsa. A wannan lokacin, Alhaji ya kira sunana ya ce; Muhammadu! Da ace ba'a fasa auren ka har karo biyu ba, da yanzu kai ɗin magidanci ne wanda yake ɗauke da nauyin iyalinsa....wata ƙila bani da rabon ganin iyalinka Muhammad, amma ga AMANAR ƙannenka nan da mahaifiyarka na ɗora akan kafaɗarka. Ka yi iya yinka wurin kulawa da su kada ka taɓa bari su yi kukan mahaifi..."
Jinjina kai Baba Ustaz ya yi cike da jin sabon tausayinsu ya ce.
" Wannan haka yake Muhammad. Tabbas an yi haka a ranar da marigayi zai bar duniya..."
Waigawa ya yi yana fuskantar dangin mahaifiyar tasa cike da ƙwarin gwiwa ya ce.
" Jaddi! Jadda....Uncle...Auntie...dama sauran dangina da ban sani ba. Haƙiƙa ina jin raɗaɗi sosai a raina kamar yanda kukeji...ban san ku ba tsayin shekaru, amma kuma na rayu, kuma kun ɗauka cewa na mutu tsayin shekaru amma kuma kun rayu..rana tsaka kuma, ba za to ba tsammani sai gashi ƙaddara ta sake haɗamu...wannan kaɗai ya Ishemu farin ciki yasa duk wanda yayi mana wani laifi mu yafe masa Jadda...Ita ɗin matar mahaifina ce, waɗannan kuma ƙannaina ne ubanmu ɗaya, su ɗin amana ce a gareni Jadda...shin idan kuka ce za ku ɗauki fansa, Amanar mahaifina kuke so na banzarar wacce ya bani yana gabanin mutuwa ko kuma tozarta mahaifiyar waɗannan yaran waɗanda bani da tamkar su a duniya. Ina son su...Ina son su sosai kamar yanda nake son kai na Jadda...idan suna cikin farin ciki na fi su kasancewa a farin cikin, idan ma suna baƙin ciki na fi su kasancewa a baƙin ciki....ko don waɗannan abubuwan guda biyu ina so ku dubi girman Allah ku yafe mata. Kuskurenta ɗaya da ta aikata ba shi zai sa mu kasa duba dimɓin alherinta ba....Kuyi haƙuri,Allah da kansa yace yana tare da masu haƙuri masu yafiya..."
Emraan na wani irin tururi ya ƙara so inda yake tsaye ya rungume shi yana mai fashewa da wani sabon kuka ba tare da yayi magana ba. Ganin hakan yasa Labiba matsawa tare da su Hairi suka rungume juna suna ta kuka.
Tabbas wannan Yaya na su shi ɗin mai zuciyar zinari ne. Duk da irin abin da Hajiya ta yi masa bai duba komai ba, ya yafe mata kuma ya hana dangin mahaifiyarsa su hukunta ta.