Ganin ido complete Novel - Chapter 49
Ganin ido complete Novel Chapter 49: Ganin ido complete Novel Chapter 49. Gabaɗayan su babu wanda bai tarfar da ruwan hawaye ba wurin. Jinjina kai Jadda ta…
3,341 words
Gabaɗayan su babu wanda bai tarfar da ruwan hawaye ba wurin. Jinjina kai Jadda ta yi ta ce.
"Shi ke nan Hammodi, tun da kace haka, mun yafe mata,Allah ya yafe mana baki ɗaya..."
Gyaran Murya Jaddi ya yi ya ce.
"Alhamdulillah! Wannan sunna ce mai ƙarfi ta annabinmu annabin rahama da yazo a cikin hadisinsa ingataccen da ya ce, idan an yi maka mummuna ka saka da kyakkyawa. Allah ta'ala yasa mu dace duniya da lahira. Kai da rayuwa tazo maka a haka, ba don Allah baya sonka ba ne, yana daga cikin babin ƙaddarar ka cewa sai hakan ta faru da kai, ko da sanadin Hajiya Batula ko Babu sanadinta...In Sha Allah, wannan kyakkyawan halin da ka nuna na haƙuri Ubangiji zai saka maka da mafificin alherin da baka za ta ba... "
Ji na yi ya janyo hannuna ta baya na zagayo zuwa gabansa. Kallona ya yi, sai kuma ya kalli kakan nasa cike da alfahari ya ce.
" Ubangiji ya saka min Jaddi...domin ya bani wannan... A lokacin da nake cikin tsananin duhu da damuwa...wannan Ita ce matar da ya jeho a cikin rayuwata,... Mace ta gari wacce ta zaɓeni ba don wani abin da nake da shi ba..ita ɗin tana da wata irin baiwa, hikima da kuma hangen nesa. Sunanta Beenafah..."
Jinjina kai Ya yi yace.
" Masha Allah! Allah mai girma! Allah ya sanya wa wannan auren naku albarka ya bada zuriya ɗayyaba...wallahy kunga haƙuri da kuke gani...mu riƙe haƙuri da Addu'a, sannan mu dogara ga Allah. Wallahy duk wanda ya dogara ga Allah har abada ba zai taɓe ba....mu riƙa haƙuri da rayuwa da kuma mutanen da ke zagaye damu, wani zaune kawai kake da shi amma sam baya nufinka da alheri sai sharri a rayuwarka...sai dai kuma, komai zamuyi mu riƙa saka Allah sannan mu yi komai da zuciya ɗaya sannan kuma mu riƙe zumuncinmu da kyau... "
Ya ɗauki tsawon lokaci yana mana nasiha sannan daga ƙarshe ya sallami jami'an suka tafi.
Janyoni Jadda ta yi ta sumbaci goshina a karo na biyu sannan ta sumbaci gefe-gefen kumatuna guda biyu cike da nuna zallar ƙauna. Haka suka yi ta passing-passing suna ta yi min kirari suna saka min albarka.
" Jadda....Mu shiga da su ciki su huta su ci abinci, duk sai a yi wannan daga baya.."
Jinjina kai Jadda ta yi tana mai kallon wacce tayi maganar tana murmushi ta ce.
"Haka ne Taimiyyah, please ku shiga daga ciki."
Wani ƙayataccen parlourn muka tsallaka muka shiga inda aka bamu wurin zama muka zauna har da Hajiya wacce har yanxu ta kasa haɗa ido da kowa har su Labiba ma. Amma su kam sai wani janta suke da fira cike da kewa.
Wasu manyan faskata-faskatan silver tray ne aka shiga jera mana a kan wata kewayayyar shimfiɗa ta lallausar carpet lungun parlourn, wanda da alama shi ne dining area ɗinsu. Da alama dai al'adar su ce a haka, domin a irin matsayinsu da kuɗin da suke da su ba za ka ce wai rashi ne yasa ba'a saka table a wurin ba.
Wata matashiya ce ta zauna a gaban abincin tana Murmushinta mai kyau ta shiga yi mana bayani cikin raha da cewa.
"Ni sunana Suwara, ni er gidan Razia ce ta wannan gida. Yanzu zan muku bayanin wannan Kalolin abincinda aka jera muku domin kuji daɗin cinsa yanda ya kamata. To! Kamar dai yanda kuka ga an jere plate-plate sun fi goma sha biyar a tray ɗaya, Haka ne mu al'adar abincinmu yake. Wannan ɗin...."
Ta faɗa tana nuna mana wani plate a ciki Sannan ta ci gaba da cewa.
" Asida kenan, itace ginshikin abincinmu na Sudanese. Ana yin ta ne da gero ko fulawa sai a jujjuya ta kamar tuwo, sai a zuba mata wannan miyar wacce muke kira da mullah. Sannan wannan kuma, ita ce Mullah bamia, miyar kuɓewa kenan. Sai kuma wannan, Mullah sharmout, miya ce da akayi ta da naman da aka busar. Za ku ji ƙamshinta mai daɗi sosai, ga shi kuna gani har da Man shanu muka saka mata. Sai kuma Kisra da Mullah wanda kuna gani farin fanka ne (flatbread) da muka yi ta da gero, ga miyan Mullah Sharmout nan da ita za'a ci. Ko kuma aci da wannan Miyar Mullah tagalia, wacce miya ce ta nama da albasa, tumatir da ƙamshi. Mullah Rob Kuma, miya ce ta nono da gero,amma dai ita tana da ɗan ɗaci haka da santsi. Wannan kuma....Shi ne Ful medames wanda wake ne gashi kuna gani. Wanda aka tafasa sosai da mai, tafarnuwa da kuma lemon tsami...gashi kuna gani an ƙawata shi da ƙwai, salati da kuma burodi. Sannan ga Shawarma ga kuma grilled meat, Sannan ga Kuma Laham Mashwi wanda kuna gani gasasshen nama ne wanda aka shirya shi da kayan miya akai masa ado. Ga salata da sesame sauce. Ga cake, ga pizza ga Kuma doughnut. Ga kuma nama soyayye. Sai abin sha kuma, mu nan munfi amfani da lemukan da muka haɗa da hannunmu. So... Ga Karkade, zoɓo kenan. Sai Shai bi habahan, wanda shayi ne da aka haɗa da Clove, cinnamon, da kuma cardamom sai sugar. Ga kuma Gahwa, Coffee Kenan. Sannan abu na ƙarshe, ga Basbousa, ma'amoul, ga kuma dabino mai zuma."
Ya salam! Wai Allah ɗaya gari bam-bam inji Bahaushe. Na san dai kamar yan da na rasa bakin magana haka ma su Aunty Labiba, domin babu abin da muke sai murmushi, da mai bayanin da abincin da take mana bayani a kai duk abun burgewa ne.
Ganin yanda muke ta wani murmushi yasa ta jinjina kanta tana mai kallon sauran en uwanta ta ce mana.
"Bismillah.."
Kallon Dayaa na yi ina mai sakar masa murmushi,shima ɗin ganin yanda nake kallon sa yasa ya jinjina mini kansa ya yi min murmushi sannan ya janye daga kusa da Jaddi ya matso gangar tray ɗin.
"Mummy...yawuna tsinkewa yake yi.."
Cewar Hairi tana mai ƙara matsowa kusa dani. Murmushi na yi mata na ce.
"Mu ci."
Zaunawa muka yi muka ci abincin cike da nishaɗi da raha,kuma Alhamdulillah! har Dayaa da Emraan da nake ganin suna da tsantseni basu nuna komai ba.
Bayan mun kambala muka tashi suka wuce masallaci mu kuma muka shiga ciki muka yi salloli. Taimiyyah da Suwara da kuma wata wacce na ji sun kira da Laurat ne ke tare damu suna ta mana fira suna bamu labarai iri-iri.
Bayan sallar Isha ne muka dawo ainahin parlourn da muka fara shigowa muka zauna fira ta dawo ƙasa. Nan suka gabatar masa da dangin su gabaɗayan su da irin dangantar suke da ita. Haka suka yi ta bamu tarihi kala-kala da irin rayuwar da mahaifiyar Ya Mohaa ta yi har zuwa aurenta da kuma irin ziyarar ta ta ƙarshe kafin mutuwarta.
Daga nan kuma aka dawo firar rayuwar Ya Mohaa inda ya basu tarihinsa da irin aikace-aikacen sa. Kallona Suwara ta yi tana murmushi ta ce.
"Aunty Beenafah! Mufa a nan, indai ke matar aure ce, to ya zama dole a riƙa ganin ki da lallen gargajiya...idan kuma baki da lalle a nan to ke budurwa ce...idan kuma ke ba'a ma'abociya son lalle ba ce, to haka za'a riƙa nuna ki ace baki ɗauki aure da daraja ba.."
Dariya muka yi dukkanmu sannan na jinjina kai na ce mata.
"Ci gaba da bamu labaran al'adunku please...abun akwai daɗi..."
Dariya Taimiyyah ta yi ta ce.
"To muma sai ku bamu labarin Nigeria kenan.."
Ɗaki muka koma muka ci gaba da fira. Muna nan sai ga Jadda ta shigo da farantin lalli a hannunta ta zauna a gefena cike da murmushi mai daɗi ta kama hannuna ta fara saka min.
Murmushi na yi jin yanda yake tashin ƙamshi na ce.
" Jadda Lallen nan sai ƙamshi yake.."
Jinjina kai ta yi tana murmushi ta ce.
"Lallen mu ba kamar sauran lalle yake ba, ana mishi haɗi na musamman."
Mu uku, haka ta bimu ɗaya bayan ɗaya ta yi mana ni da Aunty Labiba, da Aunty Nadeeyah Hairi ce kaɗai ba'a yi mata ba kasancewarta budurwa.
Gaskiya a yau, zance wannan ranar ta kasance ta musamman domin mun samu kanmu a wata duniya ta daban mai cike da nishaɗi da barin tarihi a zuciya.
Bayan an kammala kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare aka kawo wani turaren aka Ƙara turarawa sannan Jadda ta kalleni wanda kamar yanda babu wata alamar bacci a idonsu nima haka ne a wurina ta ce.
"Beenafah..tun da ke Allah yasa kin zo da Mijinki. Ki tashi ki tafi kada ki barshi shi ɗaya..."
Da sauri Aunty Labiba ta ce.
"Wallahy haka ne Jadda..dan Allah ki tashi ki tafi.."
Cuno baki na yi na ce.
"Ni dai wallahy ba inda zanje a nan zan kwana kamar kowa. Ai shima tun a jirgi ya ce min yasan cewa gidan mutane muke saboda haka wurin kwananmu ba ɗaya ba.."
Kallon-kallo suka shiga yi a tsakaninsu jin wata irin ɓarusa da na yi. Miƙewa Jadda tayi ta sulale yayin da su Aunty Labiba suka saukar da kansu a ƙasa babu wanda ya sake yi min magana wanda ni kam a tawa haukar a daidai nake.
Ya Mohaa kuwa, ya jima tare da su Jaddi da Uncle Mu'aƙƙib har kusan 2am sannan daga ƙarshe ya je har ɗakin Hajiya inda masaukinta yake ita ɗaya.
Bakin faskekiyar windown glass ya tarar da ita tana tsaye tana kallon hasken da ke ta walwali a waje. Takowa ya yi ya zo har inda take tsaye ya tsaya a gefenta shiru ba tare da yace komai ba.
Ita kuma jin ƙamshinsa yasa ta waigo tare da ƙoƙarin tsayar da hawayenda suka samu gindin zama a kwarmin idanuwanta akan halin take ciki a yanzu ta kalle shi murya a ƙasa sosai ta ce.
"Ka yafe min Muhammad..."
"Momma! Abubuwa fa haka suke zuwa a cikin rayuwarmu kuma suna wucewa. Duk abin da zai zo mana, in ma na daɗi ko na baƙin ciki komai tsananinsa watarana mai gushewa ne. Alfarma ɗaya nake nema a wurin ki dan Allah..."
Hannayen shi ta kama tana mai silalo da wasu sabbin hawayen na damar cike da nuna karaya a kalamanta ta ce.
" wace Alfarma ce wannan Muhammad.?"
Shi ma hawaye cike da idonsa ya ce.
" Kin tsaurara abubuwa Momma...wannan abun bai kamata ace ya fita ko'ina ba. Sam hakan bai Kyautu ba. Dan Allah ki manta komai daga yau ki ɗauka tamkar komai bai faru ba...na yafe miki Momma..dangina ma sun yafe miki.."
Kanta ta ɗora akan kafaɗarshi tana mai ci gaba da raira kuka a hankali har sai da ya kambala maganarsa sannan daga ƙarshe ta ɗago ta kalle shi ta ce.
" Nima alfarma ɗaya nike so a wurin ka Muhammad. Dan Allah ku barni gobe na juya na koma gida. Duk da cewar komai ya wuce a wurin ku..ina jin kunya da nauyin kasancewata a nan..na gode sosai da karamci. Na gode sosai da kuma yafemin..amma dan Allah gobe kada ku hanani tafiya."
Jinjina mata kansa ya yi ya ce.
" Shi ke nan. In sha Allahu gobe za ki tafi, amma dan Allah ki yi min alƙawarin cewa ba za ki sake kuka ba Momma.. "
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana mai jinjina masa kanta alamar ta ɗauka amma kuma tasan cewa wannan alƙawari ne wanda ba zai taɓa ɗaukuwa ba a wurinta. Domin har abada hawayenta ba su daina kwaranya ba dangane da wannan abin da ta aikata, musamman yafe mata da yayi kai tsaye da shi da dangin nasa. Idan ta tuna sai taji Zuciyarta ta ƙara tsinkewa. Duk tsawon shekarun da ta ɗauka tana zaluntar sa ita bata taɓa jin cewa ba a daidai take ba, sai yanzu da asirinta ya tonu shi rana ɗaya yace ya yafe mata.
"Akwai rashin bacci a tare da ke, kuma ga shi kin gaji."
Hannunta ya janyo ya kawota bakin bed ya zaunar da ita sannan ya Juya ya fita jim kaɗan sai ga shi ya dawo hannun sa ɗauke da Tea mai zafi da kuma ruwa ya zauna a ƙasa ya bata yana faɗin.
"Ko abinci kin daina ci, ɗazu ma muka ɗai muka ci ke baki ci ba."
Karɓar Mug ɗin tayi tana sha tana hawaye wanda take jin yana wuce mata a Maƙoshinta tamkar saɓen dalbejiya. Half Kawai ta iya sha,kuma shima bai matsa mata ba. Bayan ta ajiye cup ɗin ya bata ruwa ta sha. Sai da ya tabbatar ta kwanta sannan ya tashi ya kashe wuta ya fita.
Tana ganin ya fita ta sake fashewa da kuka tana wani irin girgiza kai tace.
"Astagfirullah Allah! Mi na aikatawa kai na ni Batula! Ga shi dai na ƙare da jin kunya...oh! Duniya kenan fa! Ya Allah ka karemu daga aikin danasani marar amfani."
Mohaa kuwa, koda ya koma ɗakin da akace an ware masa shi da Beenafah ya ɗauka zai tarar da Ita a ciki. Amma kuma wayam bata nan, agogon wayarsa ya sake dubawa ya ga dare ya tafi sosai amma kuma ace har yanxu ba ta zo neman wurin kwanciya ba. Numbern ta ya lallabo kai tsaye ya kira amma bata ɗaga ba, kira yafi biyar . Haka ya dawo jera mata text still ba respond, dole ba don ransa ya so ba ya cire kayan jikin sa ya shiga ya watso ruwa ya zo ya kwanta da tunaninta fal a ransa.
Ni kam ina ganin kiransa na tura ta a ƙarƙashin pillow na je na yi wanka na zo na kwanta abina.
Aslm, da fatan kuna lafiya Masoya...ina mai baku haƙuri ,kuma in sha Allah zamu riƙa tsallake kwana ɗaya na update.
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 44*
Washegari koda muka gama shiryawa daga masaukinmu muka fito har Hajiya Batula ta gama shiri ta fito domin tafiya.
Wurin breakfast muka hallara muka zauna bayan an gama gaishe-gaishe. Kowa na gidan yana wurin family guda, haka muka zauna ana ta cin abinci ana nishaɗi cikin farin ciki. Ni irin kallon da Ya Mohaa yake min ne ban gane ba,bana jin ma ko gaisuwar da na yi masa ya amsa ni da kyau. Shi dai ba murmushi ba kuma shi ba fushi ba har muka kambala muka fito domin raka Hajiya Mota ita da Baba Ustaz wanda shi ma sai a yau ne ya faɗamana cewa zai tafi gida.
Muna tsayawa bakin motar Emraan ya matso inda Hajiya wacce duk ta shige gashi kamar wata marar lafiya ya yi mata Murmushi ya ce.
"Hajiya! Dan Allah ki saki jikinki...mu fa Ahli ɗaya ne waɗanda muka kasance masu yafiya. Daga ni har su Labiba kowa ya yafe miki, kuma na yi magana jiya da su Uncle Ishaq suma komai ya wuce a wurin su. Saboda haka ki daina wata fargaba, ki kwantar da hankalinki, daga zaran mun kambala ziyarar zamu dawo gida..."
Matsowa na yi a hankali na kama hannunta ina mai share guntun hawaye na na ce.
" Hajiya! Kin riƙeni kin tallafeni ni da mahaifiyata da ƙanina na tsawon shekaru uku, ban san abin da ya kamata na yi ba a wannan lokacin. Dan Allah kada ki riƙe ni ko kiyi tunanin ni ɗin ba alheri ba ce domin na ruguza miki farin cikin iyali tsawon lokaci...ki yi haƙuri ki yafe min..."
Murmushi ta shiga yi tare da jinjina kanta idanunta tab da ruwan hawaye ta ce.
" Beenafah! Ba ke ce da neman gafara ba ni ce...dan Allah ki yafe min, kuma babu laifin da kika aikata domin ni taimakona kika yi...ta sanadin ki, ba Muhammad kaɗai ba, hatta 'ƴa' ƴana suna cikin farin cikin da ban san yan da zan misalta shi ba. A sanadin ki, na samu damar gyara kura-kuran na ɗauki tsawon shekaru ina aikatawa ba tare da tunani irin na ki ba...."
Hannayenta ta harɗe wuri ɗaya alamar roƙo ta shiga kallonsu Jadda ɗaya bayan ɗaya ta ce.
" Na gode sosai da karamcinku, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alheri ya ƙara muku zaman lafiya da farin ciki na har abada. Ba zan taɓa mantawa da ku ba da kuma irin alfarmar da kuka yi a gare ni."
"Ba komai Hajiya Batula, mun gode da zumunci. Allahu ya sauke ku gida lafiya.... Mun gode Alhaji Ustaz, Allah tsare hanya yasa a yi farar tafiya."
Cewar Jadda tana mai juyawa ta koma ciki.
Daga nan shima Jaddi ya yi musu sallama da sauran mutanen gidan suka koma sannan Aunty Labiba ta kalle ta ta ce.
" Na yiwa Barrister Magana Hajiya, idan kin koma zai dawo da su Adeel wurin ki kafin na dawo..."
Jinjina kai tayi tana mai jin yanda zuciyarta ke ƙara sanyaya na jin cewa su Adeel za su dawo wurinta. Wannan shi ya tabbatar mata da cewa sun yafe mata komai ya wuce da gaske. To amma wannan tabon na baƙin fentin da ta shafawa kanta an ya zai iya warkewa kuwa?
Bayan motocin da za su kai tashar jirgi sun ɗaga muka ɗunguma muka koma cikin gidan yayin da su Ya Mohaa suka wuce sashen Jaddi.
Wuni muka yi muna ta firarraki muna nishaɗi. mutanensu na arziki sai shigowa suke wurin yi musu barka da arzikin dawowar Ya mohaa, wanda Ya Muhammad ɗin ma tun da muka shigo ciki bamu ƙara sanya su a ido ba, duk wanda ya shigo sai dai ta nuna masa ni tana cewa Hammodin baya nan ya fita amma ga matarsa sunan ta Beenafah. Ga kuma ƙannen sa wanda suma duk sai ta zayyane sunan su Aunty Labiba cike da alfahari tana nuna su.
Abu kamar wasa har muka kwana muka wuni bamu sanya su a ido ba, sai da yamma ta yi muna wani keɓantaccen wuri ta bayan haraba inda aka keɓance wani lambu na musamman domin shaƙatawa Taimiyyah ta zo ta kiramu.
Koda muka je kaya ne aka kawo mana irin na su na al'ada sun sha kyau har sun gaji kowa da kalar na shi aka ce mu shirya after Isha zamu fita. Wani ɗakin Jadda ta kirani ni ɗaya inda na tarar da wasu mata guda biyu a ciki, wanka na shiga na yi kamar yanda suka umarta sannan na fito. Da towel ɗin jikina suka shiga turarani cikin wani irin hayaƙi mai mashahurin ƙamshi da saka nutsuwa. Bayan sun kambala suka dawo gun lallen hannuna da ƙafata shima suka shiga turarashi na musamman da kuma gashin kaina. Gyara suka yi min na musamman wanda ni karan kaina na ji sabon yanayi a tare dani. Sallar Isha na fara gabatarwa sannan suka shiryani cikin Laffaya ta alfarma wacce ta amsa sunanta Laffaya da kuma manyan gwala-gwalai.
Duk abin da suke min gabaɗaya raina yana wurin su Aunty Labiba, sai nike ji a raina kamar za su ga cewa an nuna musu banbanci an raboni da su an zo ni kaɗai ana shiryani.
A main parlour muka haɗe da su wanda suma sun yi kyau sosai sai tashin ƙamshi suke kamar wasu Amare.
A darare na kalle su ina jin wani iri a raina na ce.
"Aunty Labiba! Daman da Jadda ta kirani ne... Da..daman..."
Murmushi ta yi min mai sanyi tana mai katseni ta ce.
"Ya isa Mummyn Adeel! Ke ɗin fa amarya ce. Ke ɗin ta musamman ce a wurinmu da kuma wurin su Jadda...ke kaɗai ce mai miji a hannu a cikinmu. Kuma duk abin za'a miki muna goyon baya, in ma a Engine za'a saka ki mu hakan ya yi mana. Kada ki ji komai, a tsakaninmu babu hassada ko baƙin ciki, duk ɗaya muke.."
Jinjina kai Nadeeyah ta yi tana dariya ta ce.
"Ni Aunty Labi I'm Eager in ga ina ne zamu tafi cikin daren nan. Ga wannan uban wanka da muka sha kamar ana wani bukin aure...gaskiya familyn nan ya yi, na ji daɗi sosai da kasancewa ta a nan..."
"Uhmm! Idan ana Sallah ba'a magana Aunty Nadee...Hairi kam taga wurin zama.."
Dariya muka kwashe da ita muna kallon Hairi da ta yi wannan maganar na ce.
"Yanzu kenan a nan zamu barki idan mun tashi?."
Wani irin Farr-Farr tayi da ido sannan ta jinjina kai tana murmushi ta ce.