Kenza eBookz

Ganin ido complete Novel - Chapter 63

Ganin ido complete Novel - Chapter 63

Ganin ido complete Novel Chapter 63: Ganin ido complete Novel Chapter 63. Gaskiya da za'a auna BP na a halin yanzu...tabbas za'a cim masa ya haura ɗari…

3,311 words

Gaskiya da za'a auna BP na a halin yanzu...tabbas za'a cim masa ya haura ɗari biyu tsabar yanda na ke cikin tashin hankali da ruɗani.

Ganin bangansu a ko'ina ba, yasa na wuce direct ɗakin da take na shige kai tsaye domin sanar da ita gaskiya. Murmushi ta yi mini tamkar wani abu bai faru ba ta ce.

"Aunty Beena...Yanzu Suhaib ya gama sanar dani cewa su Aunt Fattoom za su zo kawo kayan aure na...yace za'a yi komai kamar yanda muke yi a nan."

Wani irin murmushi na ƙirƙiro wanda dai iyakacin shi kan leɓe na ce.

"Ai kuwa, ya kyauta. Allah ya nuna mana..."

"To wai Aunty Labiba sai tambayata take wai mi nake so. Ni dai na ce ta bari zan yi shawara...kema mi kika gani?"

Jinjina kaina na yi kawai sannan na ce.

"Gaskiya nima dai a yanzu ban sani ba Hairi...ko za ki bari zuwa idan muka koma gida muka nutsu sai muyi tunani a kai...ko ya kika ce?"

Dariya ta yi sannan ta gyaɗa kanta ta ce.

"Haka ne kuma Aunty Beenafah, and again ga Daddy ya dawo yau. Ni sai yanxu na gano cewa na tabka shirme...please ta shi kada ya dawo bakya nan.."

Miƙewa na yi tamkar tasan abun da nafi buƙata kenan na wuce da sauri na koma ɗakina. Ganin irin yanda ta tarbeni ba tare da nuna alamar wata tuhuma ba, hakan yasa na fasa ƙudurina na faɗa mata abinda yake faruwa. To amma shi fa idan ya tambaye ni?

Na jima a zaune inda na kambala sallar Isha ba tare da sanin abin yi ba. Ina kallon sa ta ƙasan idona har ya wuce toilet ya yi wanka ya fito.

Koda ya fito ni har na koma na zauna a bakin Gadon yayin da na sunkuyar da kaina ina wasa da yatsun hannuna. Lallen da aka mini kawai na tsurawa ido ina kallon yanda ya yi maroon ya yi kyau sosai.

Tun da ya gama shiryawa ya tsaya wuri ɗaya tare da resting jikin gini ya harɗe hannayensa yana kallona.

Duk da cewa ni bana kallon sa, jikina ya bani cewa kallona yake. Sosai na ƙara jin wata irin sabuwar karaya ta sake sarƙafe mini zuciyata. Cikin rashin sanin abin yi yasa kawai na fashe masa da kuka.

Wani lallausan murmushi ya saki cike da nutsuwa, yana mai jin wata irin sabuwar ƙaunar da duk abin da zata yi baya tunanin zai iya ganin laifinta ko na second ɗaya,yasan cewa duk abin da zata yi tabbas tana da dalilin yinsa. Macen da take da basirar bin diddigin zance ta kuma jajirce wurin ganin ta tsamo shi daga cikin matsalar da yake cikinta tsawon lokaci tabbas ita ɗin Mace ce ta daban a cikin dubban mata. Ita ce Macen da ta fito da rayuwarshi daga cikin tsananin duhu zuwa haske. Ta sanadinta komai ya daidaita a rayuwar shi. A hankali suka saba, a hankali suka fara samun kusanci, a hankali shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, a hankali soyayya mai sanyi da musulmin daɗi ta shiga tsakanin su..Shi ne kaɗai wanda take so, har kuka fa take yi don zai tafi ya barta, farin ciki ne ya kamata a lokacin da labarin Cikin da ke jikinta ya riske ta....Da waɗan nan tarin dalilan...,Har abada yasan ba za ta taɓa yin fushi da shi haka kawai ba domin jin daɗi. Har abada ba za ta so baƙin cikin sa idan dai ba kamawa ta yi ba. Yasan Bibinsa farin sani...ita ɗin ta yarda da shi sosai domin komai na ta bata ɓoye masa, wannan ma dole akwai wani...Tabbas akwai wani abin da yake tafiya ba daidai ba.

Daga can inda yake tsaye na ji sautin muryarsa mai nakasa duk wani kuzari na jikina yana faɗin.

"Bibina...har yanzu muna cikin faɗan ne? Why are you avoiding my gaze? Saɓani tsakanin miji da mata, is not something new....tabbas zamu saba, kuma zamu shirya matuƙar mun yarda da junanmu..amma kada ki bar fushi ya zama abin da zai ratattake soyayyar da muka gina ta bisa gaskiya da amana. "

Yana gama faɗar haka ya tako a hankali ya zauna a gefena tare da kamo hannuna a hankali na sarƙafe a cikin nasa yana mai ƙara kwantar da murya sosai cike da nutsuwa ya ce.

" Kin san wani abu Bibina.? Idan muka ci gaba da yi wa juna shiru a lokacin da wata matsala ta faru...soyayyarmu tabbas za ta samu mummunan giɓi..kuma ni har bada ba zan so hakan ta faru ba koda kuwa a mafarki ne. Bibi ina miki ƙaunar da ko ni ban yiwa kaina ita. Ina miki sonda baki ba zai iya misalta miki ko kwatanta yanda nake ji a kanki ba. Idan har wani abu mummuna ya shafi alaƙar mu, to tabbas har abada ba zan ƙara moruwa ba.

Wata sassanyar ɓoyayyar ajiyar zuciya na sauke, har can cikin ƙasan zuciyata kalamansa suka taɓo tsabar yanda ya dulmiyani lokaci ɗaya, sosai tunanina ya karkata ya koma only him nake ji da gani.

"Rayuwa dole akwai uzuri wa juna Bibi...amma duk abinda muke mu Riƙa lissafi muna duba haƙƙin abokan zamanmu da ya rataya akan wuyanmu. Ban san laifin da na miki, amma ina nema da roƙon ki alfarma dan Allah ki yi haƙuri ki yafe min. Ina son ki, ina son ki sosai..."

Kwantawa na yi lamo cikin jikin sa ina mai rera wani sabon kukan a hankali ba tare da na yi magana ba. Ina jin rashin kyautawa ta wani ɓangaren amma kuma har yanzu na kasa sauka akan maganganunda zuciyata ta gama aminta da yanke hukunci akan su. Duk yanda na ke jin sonsa a raina dole na haƙura da shi kuma na ja baya, koda zancen Ya Jafaru ya tabbata da gaske..kaɗan zan ji na cutu domin na riga na gama ɗaukar haske kuma na sanya a raina cewa, from today henceforth...komai zai iya faruwa a tsakaninmu idan har ya ci karo da matar da ta dace da tsarinsa da kuma rayuwarsa.

Janyeni ya yi a hankali ya miƙe ya fice mintuna kaɗan sai ga shi ya dawo da tray a hannunsa.

Tamkar wasu kurame haka ya ciyar dani abincin ba tare da munyi magana da juna ba. Bayan ya fitar da kayan ya dawo, ina jin sa yana magana da Emraan a waya yana ce masa kada su zo domin baya gidan kuma ba zai dawo da wuri ba.

Ni dai ina nan na lafe kamar mai bacci da gaske, amma kuma sam ba baccin nake ba. Bayan ya kambala bai jira komai ba ya kashe muna fitila ya hauro kan gadon tare da janyoni jikin sa ya rungumeni a ƙirjinsa. Bai damu da saina canja kaya ba domin yana gudun yayi wata magana cibi ya zama ƙari.

Duk da cewa ina cikin halin damuwa, hakan bai hanani yin bacci ba domin da gaske nayi kewar wannan yanayin. Shi kuma, bayan ya tabbatar na yi bacci, a hankali ya janye ya tashi bayan dare ya raba sosai yaje ya ɗoro alwala ya fara ibada. Sam bai samu bacci ya ɗauke sa ko na second ɗaya ba. Tunanin abinda ya saka ta wannan fushin yake yi. Iya saninsa lafiya ƙalau suka rabu kuma lafiya ƙalau suke waya suke chart. To amma mine ne abin da ya faru a tsakanin kwana biyun nan? Komi ne ne yana fata Allah ya daidaita tsakaninsu domin idan aka ci gaba a haka, har abada ba zai samu nutsuwar zuciya ba.

*******

Jafaru kuwa, wani abu ne ya ji ya ɗalla masa cizo wanda bai san ko mine ne ba, hakan yasa ba shiri ya zabura ya miƙe tsabar azaba ya shiga yarfe hannu a gigice. Kafin kace mi, tuni security alert ya ɗauki saiti bayan wasu mutum biyu sun yi ram da shi.

A yanda suka nuna masa rashin imani har ya riga ya sadaƙar da cewa mutuwar sa ce ta zo,domin ya tsorata ba kaɗan ba. Fitowar Beenafah da yanda ta haƙiƙance ta nuna tsantsar damuwar ta da alfarmar da ta nema masa shi ya tabbatar masa da cewa har yanzu tana ƙaunarsa, kuma da zai ci gaba pushing In Sha Allahu ba jimawa zai cim ma nasara. Yasan cewa da ya riƙe wuta dole za ta matsa ya sake ta saboda ta dawo gare shi. Kuma ba zai sare ba, yana nan akan bakarsa har sai ya samu nasarar ta dawo gareshi.

******

Washe gari, da sassafe Su Emraan suka zo gidan wanda ban san mi suka tattauna akai ba tsawon lokaci. Bayan sun kambala sun wuce muma ba jimawa muka fito. Da ni da shi da Hairi, Biba ce daman yace sai bayan kwana biyu idan an gama shirya mata za'a aika mini da ita daga baya.

Ban yi tsammanin cewa wai zai biya dani ta gidan Ammie ba, domin rabona da magana da shi tun a daren jiya, yanda nake haka ya shiga bi da ni don kawai a zauna lafiya.

Muna isa na sauka na shige ciki. Da su Aunty Husaina na ci karo suna zaune a parlour tare da su Bahrain wai suna buga game ɗin PS.

"Aunty Hussaina! Yanzu dan Allah harda ke a wannan?"

Dariya ta fashe da ita sannan ta ce.

"Beenafah. Ashe za ku biyo ta nan?"

"Eh, wallahy Ina su Ammie da Aunty Aysha?"

"Ammie tana ciki, amma Aunty Aysha ta yi gidan wata ƙawarta."

Ciki na wuce bayan su Bahrain sun gaishe dani na cim mata a ɗaki tana zaune tana waya. Yanke wayar tayi tare da maido da hankalinta wurina ta ce.

"Kun fito kenan?"

Gyaɗa kaina na yi tare da ƙarasowa a hankali na zauna a gefenta na ce.

"Ni zan tafi Ammie..."

Kallona take babu ko ƙyaftawa ta kira sunana a hankali.

"Beenafah!"

Ɗagowa na yi na kalleta ina ƙoƙarin danne hawayena na amsa ta na ce.

"Na'am Ammiena.."

"Miye abinda yake damun ki?"

Hawayenda nake ta ƙoƙarin dannewa ne suka ƙwace mini tamkar an kunna famfo. Kaina na ɗora akan kafaɗarta na ci gaba da kuka. Ganin cewa bani da niyyar buɗe bakina na yi magana yasa ta ci gaba da cewa.

"Idan har ba buɗe baki kika yi ba, ba zan san abinda yake damun ki. Ki buɗe baki ki mini magana kinji? Miye abin da yake damun ki?"

Juyin duniya ta yi, amma ta kasa samun ko kalma ɗaya daga gare ni, duk da haka ba ta sare ba, domin kwantar da murya ta ƙara yi sosai tana mai ƙara jimƙe hannuna a nata ta ce.

"Kin san dai duk duniya daga ni sai mijinki ne wanda baki da kamar su a yanzu ko? To ba zan tilas miki ba, domin ke ɗin ba jaririya bace. Idan har ba zaki faɗa mini ba, to ki faɗawa mijinki, domin shine wanda yafi kusanci dake da kowa a yanzu, shi ne abokinki, amininki, garkuwanki kuma shugabanki. Ki bashi muhimmanci da damar da zai riƙa jin damuwowinki domin nema miki mafita idan har akwai buƙatar hakan, idan kuma na taya addu'a ne sai ya taya ki addu'a,ki riƙe ibada sosai, kuma ki yi ta gayawa Allah dukkan wata matsalar ki, a hakan za ki samu nutsuwa da kwanciyar hankali. Idan kuma matsala ce a tsakaninku..to ki zama mai haƙuri da kuma lissafin rayuwa, domin duk wanda yace zo mu zauna to fa lallai yace zo mu saɓa, gidan miji haƙuri ake yi, kowa da kika gani haƙuri yake muddin yana son aurensa ya ɗore ya yi ƙarko, sai ya yi haƙuri, ya yi ibada, sannan kuma ya yi biyayyar aure..."

"To Ammie idan wanda kake yin komai domin sa watarana ya juya maka baya fa? Idan ya samu wata wadda ta fi ka komai...shin ba aurar ta zai yi ba? Tsoro na ke ji Ammie...ina jin tsoro sosai kada ya juya mini baya watarana, ganin cewa ni ɗin ban cancanta da na zamo matarsa ba. Ammie kinfi kowa sanin cewa bani da wani zurfin ilmi sosai, shi kuma matsayinsa da komai nasa sun wuce nawa nesa ba kusa ba, Ammie shin bakya tunanin watarana zai iya butulce mini? Ammie ni ji nake komai ya fita a kaina....ji nake kamar ba na son ci gaba da rayuwa da shi..domin duk abinda yake yi a kaina duk Ƙarya ce, bab.."

Cike da tsantsar tashin hankali ta saka hannu ta toshe mini baki tana faɗin.

" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Na shiga uku ni Mulaifa! Beenafah a ina kika ji yo wannan masifar kuma?"

Murya cike da kuka na ce.

" Wata ƙawata ta faɗa mini haka...!"

"Wacce ƙawar ce wannan? Faɗa mini a ina take? Dan Allah ki faɗa mini kinji Beenafah!"

Girgiza kaina na yi ina mai jin mummunan faɗuwar gaba na ce.

"Ammie ba'a nan take ba.."

Da sauri ta girgiza kanta ta ce.

"Koda yake sanin ta ba shi ne ma mai muhimmancin ba...gubar da ta shayar da ke ce ya kamata na fara baki maganin ta....kina jina Beenafah? Mijinki mutumin kirki ne sosai, bai jima da muka san shi ba, amma dai duniya da mutanen cikinta da dama sun yi mishi kyakkyawan yabo da shaida ta gari. Har abada ba zai taɓa iya juya miki baya ba Beenafah. Shi ɗan halak ne kuma yasan halacci....Kada ki sake saurarar irin waɗan nan gurbataccin ƙawayen domin babu alheri a cikin tarayya da su. Ciki ne da ke, idan kika ce zaki riƙa damuwa, to tabbas damuwa ce za ta maye miki ƙarshe matsala ta biyo baya, ki dogara ga Allah kuma ki yarda cewa dukkan wani abun da zai same ki, to ikon sa ne kuma yinsa ne ba wani mutum ba. Ki kwantar da hankalinki, ki zauna da mijinki lafiya dan Allah Beenafah ina roƙon ki. Ki daina wannan tunanin sam ba shi da wani amfani. Akan hanya kuke, bai kamata ace na zaunar da ke sosai a nan ba, amma in Sha Allahu zamu tattauna a waya idan kin huta. Allah ya tsare ya ƙara miki lafiya."

"Amin. Na gode sosai."

Daga haka muka fito suka rakoni gabaɗaya har mota sannan suka koma gida.

******

Tunda muka dawo tsawon kwanaki biyar kenan na daina ganinsa a idona,daga ni sai Hairi ne muke budurinmu, to itama a yau ɗin ta koma school. da farko na ɗauka tafiya ya yi. Sai daga baya na gane cewa ashe sai dare ya yi sosai yake shigowa gidan, idan gari ya waye kuma, da wuri yake shiryawa ya fita.

Yanzu kenan yana nufin fushi yake dani kome? Ni ya zan yi da raina? Ya Jafaru ya riga ya cutar dani, ban gane cewa na yi kuskure ba sai da Ammie ta farkar dani daga mummunan baccin da ya ɗauke ni.....kunyar kaina nake ji a yanxu, ina jin kunyar sa shima, ban san ta yanda zan fara kallon sa ba...

Damshin da na ji akan kumatuna shi ya tabbatar mini da cewa ashe kuka nake da gaske. Dole na yi kuka, domin na riga na ɓata rawa ta da tsalle. Yanzu ta ina zan fara.? Ta ina zan fara ni Beenafah? Dole na gyara kuskure na...dole na gyara komai zai faru. Ina da buƙatar mijina,ina jin kewarsa. Wayata na janyo na duba, tunda muka dawo ko sau ɗaya bai kirani ba, bai turo mini text ba. Dole na gyara kuskurena.

Da wannan tunanin na zauna a raina, bayan na gama sallar Isha naje na yi wanka na shirya cikin kayan baccin da yafi so ya ganni a ciki na koma parlour na zauna. Tun ina zaman daɗi har na dawo jin na ga ji, gashi har 11pm ta gota amma bai dawo ba.

Duk da cewa zaman ya gundureni...ko kaɗan ban ji a zuciyata cewa zan iya matsawa ko nan da can ba muddin ba dawowa ya yi ba.

Ina nan a haka har bacci ya fara kama idona sai ga shi ya shigo. Mamakina ne ya kamasa ganina zaune akan kujera na takure tamkar wata marainiya.

Cikin shakka-shakka ya kira sunana a hankali, wanda can ƙasan ransa ji yake tamkar ba gaske bane mafarki ne ko kuma gizau.

"Bibi..."

Tasowa na yi gudu na shige cikin jikin sa ina mai ƙanƙameshi na fashe da kuka ina faɗin.

"I'm Sorry...I'm sorry please..."

Cikin wani jin wani sabon yanayi ya saka hannayensa ya rungumeni a hankali yakai fuskarsa ya binne a cikin gefen wuyana yana na tsawon mintuna, sannan daga ƙarshe ya ɗago yana mai ƙara ƙanƙameni sosai ya ce.

"Ki daina Kukan nan Bibi...Ƙona mini zuciya yake bana so...ki yi haƙuri kin ji?"

Ɗago kaina na yi ba tare da janye jikina daga nasa ba na kalle shi ina kuka mai cike da zallar magiya na ce.

"Ka yi haƙuri...cewa akayi ba da gaske kake so na ba, komai kake mini duk ba na gaskiya ba ne...you are just using me, kana zaune dani ne kawai akan dole saboda na taimakeka, amma daga zaran an kwana biyu zaka samu wata wadda ta fini komai mai babban matsayi irin naka ka aura, a lokacin ne za ka sakeni...da gaske za ka iya yin aure watarana? Da gaske wacce ta fini ilimi, wayewa, da komai ma za ka auro? "

Luu! Haka ya tafi suka zube akan kujera wacce ita ce ta zamto ginshiƙi a gare su, ba don haka ba, da tuni sun rabke daga shi har ita zuwa ƙasa. Wannan wace iriyar mummunar magana ce? A ina ta jiyo wannan maganar? Wane maƙiyin Allah ne masoyin shaiɗan mai warin bakin da ya faɗa mata wannan maganar? Ga shi har yanzu bai gama farfaɗowa daga shock ɗin Jadda ba da ta ce wai an kai kuɗin aure da komai yanzu lokaci kaɗai ake jira. Ga shi ta matsa masa lamba akan dole sai ya sanarwa Beenafahr tun yanzu domin kada tace an yi mata rashin adalci gashi lokacin sai ƙaratowa yake ta yi.

Damuwa da firgici sune suka hana masa tunkararta tsawon kwanakin nan domin har ga Allah bai san ta ina zai fara ba. Kunyar ta yake ji, da nauyin ta. Yanxu kuma ga mummunar maganar ta ta riske shi wacce kwata-kwata bai tsamma ce ta ba. Yanzu ta ina zai fara yi mata bayani kenan? Wane munafukin ne wannan ɗan ƙasa ga wuta? Wanne azzalumi ne mai haɗa gurmi tsakanin mata da miji wanda Allah da manzon sa suka yi hani akan hakan domin mummunan ɗabi'a ce wacce bata da kyau.

Yanxu da ta zo masa da wannan zancen...tabbas ko kwana zai yi yana mata bayani ba za ta yarda cewa auren Noura ba'a son ransa za'a yi sa ba.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

*PAGE 53*

Waye wannan munafukin da ya faɗa mata wannan maganar? Sam bai shirya ba...bai shirya sanar mata..bai san ta ina zai fara ba...ashe duk fushin nan da take akan wannan dalilin ne..sannan kowane ne don kawai ya ƙara ɓata tsakaninsu ya ƙarawa maganar magi da gishiri yace mata zai yi aure don ita ba ta cancanta ba..kowane ne wannan bai masa adalci ba..sam bai masa adalci ba.

Ɗagowa nayi na kallesa cike da karyewar zuciya na ce.

"Haka ne ba? Zancen haka yake ko? Ni ɗin ban cancanta ba..."

Gabaɗaya ya yi resting bayansa jikin kujerar ya jingina tare da zuba mata idanu yana kallon fuskarta, yanda idanunta suka kumbura saboda kuka,karan hancinta ya yi ja, fuskar nan ta yi fayau wanda hakan ba ƙaramin dukan zuciyarsa ya yi ba. Kowane ne wannan bai kyauta masa ba, sam bai kyauta masa ba. Ya zalunce shi ya cutar da shi cuta mai girma..and now...since ta riga ta ji komai...ya zama dole ya fayyace mata komai, duk da cewa yana jin tsoron yanda za ta ɗauki maganar, ga shi an riga an ɓata komai.

Ta hakan ya yanke faɗamata gaskiya wanda shi a tunanin shi zancen auren ne kai tsaye aka samu wani munafukin ya sanar mata, bai san cewa jirwayene ta yi masa mai kamar wanka ba, sai gashi ta yi sara akan gaɓa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull