Kenza eBookz

Ganin ido complete Novel - Chapter 64

Ganin ido complete Novel - Chapter 64

Ganin ido complete Novel Chapter 64: Ganin ido complete Novel Chapter 64. A yanzu jin shirunsa ya gama ruguza mini zuciya, shirunsa ya bani amsar da nake…

3,349 words

A yanzu jin shirunsa ya gama ruguza mini zuciya, shirunsa ya bani amsar da nake nema ba tare da na sha wahala ba. Ashe Ya Jafaru ya yi gaskiya, shi ɗin fuska biyu ne da shi. Shi ɗin ashe da gaske bai amshe ni ba, shi ɗin bai aminta har cikin ransa cewa mun zamo ɗaya ba kamar yanda ni na gama sakankacewa...da gaske kenan komai da yake mini yana yin sa ne don kawai sadaukarwar da na masa. Komai yana yin sa ne don GANIN IDO na amma akwai abinda yake nufi a zuciyarsa.

Yunƙurawa na yi da ƙyar tamkar wata wacce aka daddane na miƙe ina mai yi masa wani kallon mai ɗauke da abubuwa masu tsaya na ce.

"You break my trust...amma ba komai, Allah zai mini sakayya..."

Takawa na yi zuwa bakin ƙofa sannan na tsaya tare da juyowa na sake kallonsa na ce.

"Kafin gobe...ina so ka rubutamin takardar saki na ka bani..."

Tamkar wanda aka shaƙewa wuya, haka ya furxo kalmomin sunana a gigice ya ce.

"Da...Dan Allah Bibi!! Dan Allah ki tsaya ki saurare ni...Dan Allah!"

Wasu sabbin hawayene masu tsananin zafi na ji sun gangaro mini, a raunane na ce.

"Ka daina kirana a haka..domin kana mini illa sosai..wallahy zuciyata ji nake tamkar za ta fashe...na yarda da kai...yarda mai girma..na ɗauka na samu madogara, na ɗauka na riga na samu shingen da sai mutuwa ce za ta fitar dani daga ciki..."

"Bibi..is not like that! Is not what you think and is not what you have heard...please I beg you for the sake of Allah akan ki tsaya ki saurare ni da kunnen basira ki kuma kalleni da ido na fahimta...."

"Me zan ji daban bayan wannan ɗin? Tabbas kai ɗin babban mutum ne mai babban matsayi, ga kuɗi ga kyakkyawar nasaba ta dangi wanda ni duk bani da su kuma ban kai ka ba..."

Lumshe idanunsa ya yi yana mai jin zuciyarsa na masa nauyi sosai. Wannan wace irin mummunan rana ce? Miye duk wannan yake faruwa tsakaninsa da abar sonsa? Ciki ne da ita fa...jaririn ciki! Ya zai yi da ransa idan wani abu ya same waɗannan mutum biyun da ba shi da tamkar su a duniya. Su ne farin cikinsa, uwa da ɗan cikinta su ne walwalarsa, dariyar sa da kuma rayuwarsa baki ɗaya. Dole ya yi wani abu...tabbas dole ya taɓuka kada ya rasata da gaske.

"Bibi!"

Ya furta kalmomin sunana yana mai tasowa a hankali ya ɗan matso inda nake tsaye kaɗan.

"Wallahy ban taɓa tunanin rayuwata da wata macen ba idan bake ba..da gaske nake faɗa miki wannan..wannan auren ma da ake ta ƙoƙarin ƙullawa wallahy tallahy ba'a son raina ba ne. JADDA ta riƙe wuta Bibi..., bana cikin komai duk su ne suke ƙullawa....i told them a millions times Cewa ke kaɗai kin isheni rayuwa.."

"Auaaaurree? Jadddda?"

Na furxo kalmomin tamkar Wata sabuwar mahaukaciya wacce cutar Echolalia ta kamata, haka na shiga maimaitawa. Runtse idanuna na yi da ƙarfi sai kuma na buɗe..sai kuma na yi gaba sai kuma na dawo baya tare da using hannuna alamar ban gane miyake nufi ba domin na ruɗe na gigice na ɗimauce.

Ganin kamar na daina fahimtar komai yasa a ruɗe ya kamoni tare da neman sanya ni jikinsa. Wata irin zillewa na yi na fara ja da baya ina mai binsa da wani irin kallo na ce.

"Jadda? Aure? Aure za su maka? Ban cancanta ba? Kenan a family group da aka sanya ni ta what'sapp ana ta zuzuta auren Noura da Engineer kai ne ake nufi kenan?..."

Jikina na wata irin ciccira komai ya shiga dawo mini, beat by beat. Wannan ɗin ita ce za'a aura masa suka mayar dani shashasha marar lissafi?

" Bibi...no Bibi please..."

Wani irin mummunan kallo na jefa masa ina mai jin wani irin azababben tashin hankali na ce.

"Ka amsa mini Ya Mohaa!! Kai ne Engineer ɗin Noura kenan???"

Jin ya yi shiru yasa na sake matsawa baya sosai ina mai dafe jikin gini domin jirin da nake ji na saki wani murmushin da yafi kuka ciwo ina wani girgiza kaina na ce.

"HUhmm! Lallai ɗan Adam! Wato sakayyar da su Jadda za su mini kenan? Bayan na gama dawo da kai mutum...bayan na cire ka daga ƙangin da ka yanke ƙauna...akan jindaɗin ka dawo gare su bayan tsawon shekaru...basu ga dami za su saka mini ba sai aura maka er uwar ka ko? Tabbas Ya Jafaru ya yi gaskiya....kai ɗin sam ban cancance ka ba, Noura ce wacce tafi da cewa da kai, mai cikakkiyar nasaba da ilmi...Sai yanzu na yarda da gaske cewa kai ɗin you are just using me, sai yanzu na yarda cewa you are just pretending na kasancewarmu miji da mata but as temporary Ko Mr. Engineer??"

Haukace masa na yi tuburan wanda sai da ya yi nadamar zuwan wannan ranar a rayuwarsa. Duk inda ya taro ni sai na zille, na bushe idona bana ji bana gani tamkar ba ni ba. Bai san cewa haka nake ba sai yau, bai san ina da wata kalar fuskar ba sai yau domin ya rasa gane kai ne. Sai kuka nake ina masa hauka. Daƙyar da taimakomin ubangiji ya samu na tsaya na nutsu bayan ya yi ta magiya akan cewa na tsaya na saurari uzurin sa wanda idan har bai mini ba sai na ɗauki duk wani hukuncinda naga cewa ya fi cancanta.

Wasu irin hawaye ne suka wanke masa fuska domin kalamaina kama suke da saukar ruwan dalma akan dukkan wata gaɓa ta sasssan jikin sa. Ya shiga tashin hankali domin gani yake ma kamar har ya rasa ɗin da gaske. Girgiza kai kawai yake tamkar wani zararre yana ƙoƙarin furta mini kalamai amma ya kasa yin hakan, kalmomi biyu ne zuwa uku yake ta nanatawa domin ya rasa makama.

"No Bibi..Please Bibi...dan Allah ki saurare ni..."

"Na san cewa da ka aure ta, everything will become over between us. Domin ta fini ilmi, wacce take da class, wacce English ɗinta very fluent, ita ce za ka iya zaga duniya da ita ka nuna ta a ko'ina ba tare da jin kunya ba, ita za ka iya hawa jirgi da ita, ita za ka iya kaiwa Office ka nuna ta a gaban kowa,familynka ita ce za su dawo suna so ni kuma na dawo banza, kai ma haka za ka dawo yi mini riƙon sakainar kashi, ƙarshe ka sake ni saki na wulaƙanci..."

" Stop it! Stop it please!"

Ya furta a tsawace yana mai kakkafeni da ido. Haƙiƙa kalmomina sun soke shi ba kaɗan ba. Ya jima shiru wanda bai san mi yake nazari akai ba sannan daga ƙarshe ya jinjina kansa tare da haɗiye wani abu daƙyar a maƙogoronsa sannan ya ce.

" Okay! Zan faɗa miki gaskiya ɗaya Bibi...ba zan ɓoye miki komai ba., Eh, da gaske Su Jadda sun matsa akan sai na auri Noura, sun ce dole sai na aure ta, amma ba don..."

Ban san lokacin da na runtse idanuna ba ina wani girgiza kaina ina ci gaba da zubo da ruwan hawaye, a karye na ce.

" To ka ji fa dan Allah! Kenan duk sadaukarwar da na yi musu na yi ta a banza kenan? A idon su sam ban yi darajar da za su ɗaga mini ƙafa ba su bari na rayu da kai ni kaɗai koda na tsawon shekaru uku ne kacal ba, a misali kenan? Ashe ban cancanci hakan ba? A GANIN IDO na ne ashe suke nuna suna so na amma daga zaran na juya baya ni ce babbar maƙiyayarsu abokiyar gabar su? Sakayyar su a gare ni kenan bayan na ƙwato musu kai a bakin Kura? Za su aura maka wata, watan ma Noura, wacce suke ganin tafi da cewa da kai, domin ta haɗa komai na rayuwa ni kuma ban cancanta ba...ko secondary school ban kambala ba, a islamiyya ma ban yi nisa sosai ba..."

Yanzu kam sosai yake kuka kamar yanda nake yi. Tamkar wani ɗan maye haka ya ƙara kusanto inda nake yana faɗin.

" Stop saying that about me...you know that I will never do that for you...domin ni ɗin ɗan halak ne...a yanzu sai Ince kin fi sanina fiye da kowa, ba zan taɓa aikata miki hakan ba. Idan ma na yi hakan kuma...Allah ma ba zai barni ba, domin na ci amanar marainiyar yarinyar da ta yarda dani.. "

Numfashi ya ja a hankali sannan ya sauke yana mai ƙara matsoni sosai ya ƙara kwantar da murya ya ce.

" Bibi! Yes! Su Jadda sun matsa sun kuma tsaya kai da fata..sun ce idan na aure ta zamu yi farin ciki a tare mu uku...but ba hakan ba ne!"

Bakin gaskiyata har cikin zuciyata na girgiza kaina ina mai jin wani iri game da su na ce.

"Ba zan ɓoye maka ba...sam ban ji daɗin yanda su Jadda suka juya mini baya ba."

Hannuna ya yi nasarar ruƙowa yana mai matso da fuskar sa dab da tawa sosai ya ce.

"ki yi haƙuri dan Allah. Abin da nake ta gudu kenan...but ni kece farin ciki na, ban san kowace mace ba idan bake ba. I'm not a boy, I'm a man...and as a man...i choose only you."

Buɗe idanuna na yi sosai na kallesa ina jin wani iri a zuciyata na ce.

" Idan har ni kaɗai ka zaɓa to me yasa ka yarda da zancen su? Idan har su basu ga cancanta ta ba ai kai ka gani ko ba haka ba?"

Ɗan taune lips ɗinsa ya yi kaɗan yana mai shafa bayan ƙeyar kansa ya ce.

"Saboda sometimes...bin umarnin iyaye shi ne maslaha Bibi..na rasa su na tsawon shekaru, ina jin tsoron bijirewa maganarsu kada su ce don mahaifiyata bata raye ne naƙi yi musu biyayya..amma ki yarda dani cewa tun farko har zuwa yau ban amince ba..bazan iya saka mace biyu a zuciyata ba, domin wurin ki ne ke ɗaya, ina jin tsoron rasa ki Bibina, shiyasa na kasa sanar miki, ina jin tsoro da fargabar aikata wani abun da zai karya miki zuciya.... "

Sama ya yo da hannuna ya ɗora akan saitin zuciyarsa yana faɗin.

" Feel my heart...Does it feel like someone that's wants to hurt you? Har abada ba zan iya cutar da ke ba Bibi, har na mutu...."

Sosai na ji gaɓoɓin jikina sun saki, maganganunsa sun hudani, na ji gabaɗaya kamar na yarda da duk abinda yake faɗa mini. Tabbas a tsorace yake, kuma duk ya birkice kamar ba shi ba. Yanda nake ƙonewa shima haka ya ke ji a ransa. To amma muddin aka ce auren sa zai tabbata da Noura to ni kuma sai dai na haƙura da shi gabaɗaya, saboda ba zan yarda na rayu da dangin mijin da basa so na ba kamar yanda ya faru da Ammiena. Silar hakan ne yasa ta ƙare a matsala.

Hannunsa na janyo nima na saka na share hawayena, amma ba don sun daina kwarara ba. wani kallon na shiga bin sa da shi ina girgiza kaina na ce.

" Dayaa! Ina son ka sosai kamar yanda ka ke ji kaima...zan iya cewa ma na fi ka zurmawa da yawa domin ni da kai kaɗai na fara so, saɓanin da kai da ka taɓa son wasu a baya Allah ne bai nufa ba. Ni kuwa, kai ne kaɗai wanda na fara so, kai ne wanda ya koyar dani komai, ban san wata kalar soyayyar ba idan ba taka ba. Dalilin hakan yasa nake jin tsananin kishin ka wanda nake ji zan iya mutuwa idan kace za ka haɗani da wata macen, zan daina moruwa in daina gane komai idan ta tabbata cewa da gaske kai ɗin ba so na kake yi ba kuma za ka iya rabuwa dani watarana...idan har aurenka ya tabbata da Noura...to tabbas zan haƙura da kai har abada..."

Hannayensa ya saka ya janyoni sosai tare da ɗora kaina akan ƙirjinsa ya rungumeni. Wani irin riƙo ne ya yi mini tamkar wanda akace za'a ƙwace masa ni. Sosai hankalinsa ya tashi da jin irin furucina, tunani ya shiga da kuma neman mafita wa rayuwar aurensa, Bibi itace rayuwar sa da kuma abin da yake cikinta, saboda haka dole ya ɗauki action ɗinda zai ceci aurensa ya hana masa samun tangarɗa.

Haɓata ya ɗago tare da sanya hannunsa ya share mini hawayena sannan ya saita narkakkun idanunsa cikin nawa murya a ƙasa sosai ya ce.

"I love you Bibi...i love you in a way that I can not explain in one language... Saboda babu wani harshen da ya isa ya kwatanta irin yadda kike a zuciyata. Ni mijin ki ne Bibi, da ni kaɗai ya kamata ace kin yarda. Babu wani zancen cewa wai zan auri wata na wulaƙantaki, babu wani abu makamancin cewa wai ke ɗin ba class ɗina ba ce, ke ce Mace mafi daraja da girman da tafi dacewa da Engineer Muhammad Attahiru Araam..kece rayuwata, kece nutsuwata, kece abokiyar tafiyata a duk inda zan sanya gaba, kece addu'ata cikon mafarkina. Ba ki yi zurfi ilmin boko ba...so what? Ke irin ilmin ki, wayonki,hankalinki, basirarki da kuma kaifin tunaninki ya zarta na dubban mata. A haka nake son ki, a haka nake so da burin ƙare rayuwata dake Bibi..wanene yafi dacewa dake idan ba ni ba?"

Kallon sa nake kallon da babu ƙyaftawa a ciki...zuciyata sosai na ji ta ɗauki sanyi a hankali tana samun sarari saɓanin kasancewarta a cunkushe tsawon lokaci.

Hannunsa ya sanya a nawa ya yi twisting sannan ya ɗago sama ya sumbaci bayan hannun nawa yana mai jinjina kansa ya ce.

"Ni Mijin Beenafah...Daddyn babynmu da yake ciki...na yi alƙawari a yau, ina kuma yi wa Bibina Alƙawarin cewa...I will never replace you in my heart, I will not marry another wife...tunda har bakya so..mi zai sa na aikata? I don't care about duk wani abun da za su ce...farin cikin ki..shi ne kaɗai abinda na sani....yes! I choose your smile, I choose your peace and I choose our Marriage over their talks....ina neman gafararki akan barin zancen nan da na yi har yakai kunnenki ya dami zuciyar ki ya hana mata sukuni, maganata ta ƙarshe da zanyi shi ne, ba zan aure ta ba muddin hakan shi ne ci gaban dariyarki da walwalarki..."

A ɗan razane na jinjina kai na na ce.

"Da gaske kake ba za ka aure ta ba?"

"You have my word Bibi...Ba zan yi ba. Komai za su ce, ko wane irin hukunci za su ɗauka, ba zan aure ta ba. Ki yarda dani."

Rungumesa na yi ina mai jin wata nutsuwa da sanyin rahama na ratsani. Wani abu na ke ji mai kama da kunya na kamani tuna irin haukar da na dinga masa duk tsawon kwanakin nan. Tausayin sa ne ma ya kamani da kuma tausayin soyayyarmu. Miyasa nake zarginsa. Shi ne mijina, wanda yake tsananin so na da ƙauna ta. To yanxu ya kuma alaƙa ta da su Jadda za ta kasance kenan? Idan suka ƙullace ni fa? Idan suka tilasta masa fa?

Tsoron hakan ne yasa na ɗago da sauri ina kallon sa a raunane na ce.

"Amma..Su Jadda fa? Idan suka..."

"Zan fuskance su in kuma faɗa musu gaskiya. I will stand for us...i will explain ta yanda za su fahimci matsayin ki da girman ƙaunar ki a gareni. Na yarda za su iya bani shawara, amma ba za su tilasta min auren da zai ruguza farin cikin gidana ba. Dangane da maganar ilmi Kuma...if you want, we can work on that. Duk abin da kike so ki zama, I promise to stand by your side har ki samu cikar burinki.."

Jinjina kaina na yi ina mai jin yarda da kalamansa na ce.

" Ka yi mini alƙawari...cewa ba za ka taɓa wulaƙantani ba kuma ba za ka bari wani naka ya wulaƙantani ba, ka yi min alƙawarin cewa har abada ba za ka taɓa kallona ƙasa da kanka ba."

A hankali ya jani muka koma kan kujera muka zauna tare da ƙara jana a jikin sa still hannun sa a nawa ya jinjina kansa yana kallona ya ce.

" I promise you Bibina...cewa, I will honour you, Ba zan taɓa wulaƙantaki ba ko kuma wani nawa. I will always respect you, I will protect you and your heart, Ba zan taɓa bari ki ji cewa kin yi losing wani position a rayuwata ba..."

Shiru na yi na en wasu daƙiƙu ba tare da na ɗauke idanuna akan sa ba. A hankali na kai fuskata na ɗora karan hancina akan nasa ina mai silalo da ruwan hawaye masu sanyi sosai.

Hannayensa ya saka ya zagayeni a hankali ya janye fuskar tasa yana kallona da wani irin murmushin nasara ya ce.

"Shihhh! It's okay...lets go inside."

Ɗakinsa muka wuce. Tamkar wasu baƙin juna haka muka dawo, a tare muka yi wanka na biyesa na sake yi kamar yanda ya buƙata, bayan mun fito muka shirya...ina ganin ya yi kashe fitilar ɗakin a hankali na kalle sa na ce.

" Ba ka ci abinci ba?"

" Farin cikin da nake ciki ya gama ƙosar dani Bibi..lets rest together kinji.."

Daga haka ya jani muka kwanta. Kamar yanda na tsunduma duniyar tunani na san tabbas shima aikin da yake yi kenan a halin yanzu. Bayan shafe tsawon lokaci wanda duk a zatonsa bacci na yi,na ɗago kaina da sauran hasken ɗakin na kallesa still ina jin hawaye a idona na ce.

"Ka yi haƙuri kaji...na tsorata ne...na tsorata sosai, na ɗauka komai zai faru kamar yanda na ke ji a raina, maganar aurenka ta gigitani.."

"Har abada ba za ki taɓa rasa ni ba. Na rantse miki...da in rasa ki..gwanda na ɓata da kowa a duniyar nan..kuma kada ki damu, domin nasan duk abin da kike kina yinsa ne saboda kina so na."

Cike da jin kunya na ɗan murmusa na ce.

" Ni kawai kishin ka na ke..."

Murmushin ya mayar mini sannan ya jinjina kansa ya ce.

"Ke ce Queen ɗina...har abada ba zan taɓa ba wata damar hawa wannan kujerar ba. Ba'a taɓa sarki biyu a Faɗa ɗaya ba, a kan ki kuma ba za'a fara ba. Bana son ganin hawaye a idon ki ko guda ɗaya, I just want to see your smile, na gaji da ganin kukanki, na gaji da ganin ki a damuwa. Kukan ki yana matuƙar karya mini zuciya, ki yi min alƙawarin cewa ba za ki ƙara kuka ba. "

" In Sha Allahu, na daina...amma kuma har abada ba zan daina kishin ka ba..ba zan iya hana kaina damuwa akan ka ba.."

Dariya ya yi cike da jin farin ciki a ransa irin yanda nake nuna masa yanda nake ƙaunar sa ya ce.

" I know...amma nima koda abubuwa za su zo mana ba yanda muka tsammataba ba...ina fata za ki yi mini uzuri ki kuma yarda dani..koda abubuwa sun canja, ina so ki tuna da wannan daren da kuma alƙawarrunka da muka ɗaukarwa juna..koda yaushe igiyar ƙaddara ta juya damu..ki yi alƙawarin kasancewa dani na har abada."

"Ba zan taɓa bari wani abu makamancin tsoro ko zargi ya sake raɓata ba ballantana har ya yi barazanar rabani da kai ba Mijina..shaiɗan ne ya kutso a tsakaninmu kuma ya yi nasara. In Sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba.Ka yi haƙuri..."

Daga haka na kwantar da kaina a ƙirjinsa a hankali na lumshe idanuna ina mai jin komai yana dawo mini sabo.

********

Washegari gari da wuri muka shirya muka fita asibiti wurin ganin likita. Sai da muka kai kusan ƙarfe uku na rana sannan muka samu aka kambala mini komai lafiya ƙalau sannan muka dawo gida da tarin tulun maganganun masu inganta lafiyata da kuma ta jaririna wanda yau bayan munyi ultrasound scan aka tabbatar mana da cewa namiji ne.

Farin cikin da Dayaa yake ciki baya ma misaltuwa. Kowa kira yake yana faɗa masa, duk yanda nake kwaɓarsa baya ji Sam bai saurare ni ba.

Wani sabon babin muka buɗe na zallar madarar soyayya wanda ba shi da wani aikin sai nawa, motsi kaɗan idan na yi akan idonsa. Ganin ya shafe tsawon kwanaki bai je aiki ba na ƙudura a raina cewa sai na tambayesa dalili.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull