Ganin ido complete Novel - Chapter 65
Ganin ido complete Novel Chapter 65: Ganin ido complete Novel Chapter 65. Yana ɗakin sa na je na same shi tsaye jikin window yana Waya. Tsayawa na yi daga…
3,351 words
Yana ɗakin sa na je na same shi tsaye jikin window yana Waya. Tsayawa na yi daga nesa da shi kaɗan wanda duk da cewa ban san mi yake magana a kai ba, Lallai ko miye ɗin mai muhimmanci ne. Wata ƙila da Jadda yake magana oho! Ni dai tun ranar da ya sanar mini wannan maganar cewa daga Jadda ta fito na ji har cikin raina na tsanesu kwata-kwata sam bana marmarin zuwa Sudan ɗin kamar yanda na ke jin ɗoki a baya. Ban sani ba ko ta fahimci halin da nake ciki da ita, domin ta rage yawan kirana kamar yanda take yi a baya, wanda ni ma ɗin har ga Allah na yi baya da su sosai na janye kaina gabaɗaya daga lamarinsu. Na so in sanar wa Ammie, amma ya roƙeni cewa dan Allah na bar wannan magana a tsakaninmu kada na faɗawa kowa. Hakan yasa dole na bar abun a raina, kuma Alhamdulillah! Sosai hankalina ya kwanta domin na sake yarda da shi a yanzu fiye da can baya. Har abada na san ba zai cutar da ni ba.
Duk da cewa ban faɗa masa zancen Ya Jafaru ba, sosai na ɗauki tsatstsauran mataki a kansa, domin tuni na yi blocking ɗinsa a duk wata kafa da nasan zai same ni. Na rasa yanda akayi ya samo Layina na nan ɗin wanda idan ya kira na yi blocking gobe da wata numbern zai kira. Hakan yasa na ba Dayaa wayar na ce aka saka mini ita ta hanyar sai idan ina da numbernka kaɗai za ka iya reaching ɗina. A yanxu na tsane sa, da zan ganshi a gabana tabbas zan iya saka bindiga na harbe shi har lahira.
Yana jin motsina ya yi saurin tsinke kiran sannan ya waigo yana murmushi.
Kallonsa na yi ina murmushin nima na ce.
"Kamar akwai wata damuwa?"
"No...ba matsala. Ya akayi? Kin cinye kifin?"
Ɓata fuska na yi ina wani yatsina cike da tsokana na ce.
"A'a.."
"Why! I suffered a lot kafin na samu na kambala shi.."
Hannu na saka na toshe bakina ina dariya na ce.
"To ai ni wallahy Sam kifin bai mini daɗi ba...kamar an wanke kai haka ya yi..ni amai ma nake ji..da ma ace Madam Amima ce ta yi da ƙila na iya ci da yawa..."
Gefen zuciyar sa ya dafe yana faɗin.
"Wash Allah na! Zuciyata bugawa za ta yi...kece fa kika tilastani..."
"To amma ai yanda na nuna maka ba haka kayi ba..magi ya yi yawa,.."
"Zo..zo nan! Ko za ki yi aman da gaske sai kin cinye shi.."
Hannuna ya kama da gaske, yayin da na fashe da dariya ina faɗin.
"Wasa nake..Allah na cinye gabaɗaya."
"Da gaske?"
"Allah kuwa."
"To miye kike a nan? Ba cewa na yi idan kika kambala ki kwanta ki huta ba?"
Zaunawa na yi a inda ya zauna ina kallon sa na ce.
"Daman tambaya ce dani...miyasa ka daina zuwa aiki? Ko ka ɗauki hutu ne?"
"Uhm! Wani abu makamancin haka.."
Wani kallon na yi masa na mamaki na ce.
"Ban fahimta ba."
"Emraan da Suhaib sun yi taking Over.."
"What? Emraan da Suhaib? Su da za su yi aure kwanan nan..."
"Emraan yana da mata da yara biyu, auren da zai yi ba shi ne na farko ba, kuma aikin ba zai hana masa komai ba...Suhaib ma haka auren da zai yi da Hairiyyah ba zai hana masa komai ba, na sa sun ajiye aikinsu domin ci gaba da tafiyar da Wannan Kamfanin."
Hannuna ya kamo a hankali ya shiga jan yatsuna yaci gaba da cewa.
"Kina ji Bibina...Golden Pathways ƙara Faɗaɗa yake, kullum ayyukansa ƙara bunƙasa suke...Mijin Beenafah yana da buƙatar lokaci tare da matarsa domin kulawa da ɗan da za su haifa...idan na ce zan ci gaba da matsawa...to fa lallai ba zan samu wadataccen lokacin da nake da buƙata ba. Hakan yasa na kira su suka zo muka tsara komai wanda sune za su ci gaba da jan ragamar a yanzu tare da sauran amintattuna kafin zuwa shekara ɗaya mu gani."
Cikin wani irin farin ciki na ce.
"Gaskiya wannan tunanine mai kyau Dayaa. Ubangiji ya taimaka ya dafa ga dukkan al'amarunku. Allah ya ƙara muku danƙon zumunci ya kauda shaiɗan a tsakaninku. Yaci gaba da tallafar wannan kamfani ya ƙaro masa ɗumbin nasarori.."
"Amin yah Allah...kina ji?"
"Uhm!"
Na amsa ina mai kafeshi da kallo.
"Gobe In Sha Allah zan tafi Sudan...but ki yi haƙuri ba zan iya tafiya dake ba a wannan lokacin..."
Wani farin ciki ne ya ratsani tare da gode masa a can ƙasan raina, domin koda ya ce mu tafi ni ba zan tafi ba. Ni da waɗan nan mutanen kuma har abada wallahy.
Shiryawa muka yi muka ɗan fita kaɗan wanda iyaka 7pm muka dawo.
Bayan mun yi shirin kwanciya bacci, ina shirin fita na ɗauko abu a kitchen na ji ya janyoni ta gefen ƙofa na faɗa jikin sa ya ɗora kansa a gefen wuyana har zuwa lips ɗina sannan ya janye yana bina da wani irin fitinanne kallon, murya a ƙasa sosai ya ce.
"BibiLove.."
"Uhm!"
Na wani amsa sa da ƙyar jin yana nema ya ɗorani kan wani sabon network ɗinda muka jima bamu hau ba.
"Kin san dai ni maraya ne ko?"
Waro ido na yi cikin serious face na kallesa a raunane na ce.
"Eh."
" To kuma kin san dai taimakon rayuwar maraya abu ne mai kyau ko? Kuma ma ta wannan dalilin sai kiga kin shiga Aljanna..."
"Eh, na sani..miye ya faru??"
Ƙara matseni ya yi sosai a ƙirjinsa tare da kawo fuskarsa saitin tawa ya ce.
"Dr. Abdallah ya ce zamu iya yi ba matsala amma dai kada mu zure sosai...please ki taimaki rayuwar wannan marayan,..tun a Kaduna fa. Ba..bamu ƙara jin ɗumin juna ba...please."
Ni fa wallahy da gaske har na manta da wannan abun a duniyata domin mun jima...amma tunda har da rainin hankali zai zo min. Nima bari na raina masa irin nawa.
Ɗan juya idanuna na yi alamar mamaki na ce.
"Miye wannan ɗin?"
"Ohh! Da gaske ba ki sani ba?...Ok! zo..zo nan na nuna miki to...."
Sai da muka gama morewa juna sannan muka yi bacci.
Washegari da wuri ya shirya na rakasa mota, sai da ya shiga ya zauna, sannan na kalle shi na ce.
"I will miss you...our baby too..zai yi kewar ka..ka gaishe da su Jadda da kowa da kowa. Allah ya tsare."
"I love you.."
Murmushi na yi tare da ɗaga masa hannu na ce.
"I Love you too."
*******
Gefen su Ammie kuwa, sai da suka ƙara tsawon sati biyu sannan Dr. Basheer ya samu nasarar dawowa daga dogon zagayen da ya yi a wurare daban-daban. Lagos, Canada da kuma Abuja.
Sosai ya tsinci kansa a farin ciki da jin nutsuwa akan nasarar da aka samu na kammala alƙawarin da ya ɗauka; alƙawarin dawowa da dukiyar marigayi Dr. Bello Wazeer ga iyalansa ba tare da an cutar da su ko an karya haƙƙinsu ba.
Sai da ya yi wanka ya ci abinci ya huta sannan ya cim mata a ɗakin ta ya ajiye mata wata Jaka a gaban ta yace.
"Na dawo da duk wani abin da ya kamata."
Murmushi ta yi tare da jinjina kanta ta ce.
"Alhamdulillah! Muna godiya sosai."
Buɗe jakar ya yi ya fito da files yana faɗin.
"Everything is done. Cleared and verified...a WazeerMed pharmaceuticals da ke Lagos...an maido da komai hannun ki, all illegal transfers have been reversed. A NordicBag Industry Kuma, munyi zama da su domin can ɗin haɗaka ce kamar yanda kika sani a baya, an gyara komai an kuma cire sunan Alhaji Mudassir da suke turawa kuɗi da duk wasu bayanai ya dawo hannun ki a yanzu. Kune owners da dokar kamfanin ta amince da shi, wanda sun shirya zama da ku baki ɗaya nan da ɗan wani lokaci. A FruitWave Beverages Ltd ma Haka, Komai ta dawo daidai,..Everything has been restored. Kasafin kuɗi, Kasafin kaya da kuma hulɗar cinikayya duk suna a cikin wannan file ɗin. Wanda duk na tura miki copy a waya."
Daga haka ya miƙa mata clearing letter daga bankuna daban-daban yana faɗin.
"Alhamdulillah! Shima wannan ɗin mun samu nasarar buɗe duk wani asusun banki da aka rufe wanda still ba za'a sahale ga amfani da shi ba dole sai da sa hannunku. Sunayenku ne ku uku a matsayin primary beneficiaries..."
Bata san lokacinda wasu hawaye suka wanke mata fuska ba. Lallai ko a cikin mutane kowa da irin tsarinsa da irin rayuwarsa. Dr. Basheer mutum ne na daban, bayan tsohon Mijinta da ya rasu...ba ta ji ta ƙara samun kyakkyawar nutsuwa ba sai yau ɗin nan..duk wannan lissafin da yake mata, har yanzu ba ta ji wuri ɗaya da yace sunan sa ya shiga ba a matsayin Mijinta wanda yake da haƙƙi da iko a kanta.
Jinjina kanta ta yi bayan ya dasa ya aya yana mai hannun ta mata sauran documents ɗin ta ce.
"Thank you so much...Allah ya saka da alheri. I really appreciate everything you did to us.."
Jinjina kansa ya yi yana kallonta yace.
"Kin cancanci hakan Hajiya Mulaifa. Ko bayan cewa ke ɗin a yanzu matata ce...taimakon waɗannan yaran yana da matuƙar muhimmanci a gare ni."
Share hawayen ta ta yi ta ce.
"Na gode sosai. Amma ka bar komai a hannunka tukun. Idan na je na gana da iyayena, sai mu tattauna abun da ya kamata a tare da su domin tabbatar da ci gaban wannan kasuwancin. Kaga Beenafah mace ce, Bahrain kuma har yanzu yana da sauran lokaci kafin ya gama mallakar hankalin kansa. Dole muna buƙatar lokaci da kuma fito da sabbin hanyoyi..."
"While..that's a very good idea...but ina ga ya kamata a jingine tafiyar nan tukun, haihuwar Beenafah kamar gobe ne, idan Allah ya sauke ta lafiya sai ku tafi a tare kamar zai fi..za ta ba daɗi idan kun tafi ba tare da ita ba, haka zalika suma a can ɗin za su ji ba daɗi idan akace tana can wata duniyar ba ta zo ba.."
Jinjina kanta ta yi, cike da alfahari ta yi murmushi tana kallon sa ta ce.
" Sometimes...Allah sends people not because we deserve them...but because we need them...and you...you came exactly when we needed a real protector. Ina alfahari da kai. Na gode sosai."
Miƙewa ya yi yana murmushi yace.
"Kulawa da rayuwarki haƙƙina ne masoyiyata....ku shirya gobe zamu koma gida. Please kada ki ce sai kinje gidan Maman Fakiha, asuba zamu yi."
Dariya tayi ta ce.
"Ba damuwa Allah ya kaimu ranka ya daɗe."
Yana fita ta ɗauko wayar ta ta kira Hajiya Asma'u ta sanar mata da kuma Hajiyar Dr. Basheer ɗin.
Washegari tun da sassafe Maman Fakiha ta ƙumo sakko ta zo ta yi mata bankwana.
Sosai Hussaina da Humaidah suka shiga damuwa suna koke-koke ba ma kamar Humaida wacce ta ke yi kamar za ta suƙe tsabar yanda take kukan tana ciccika, daman Ita Aunty Aysha itama Yau za ta wuce Abuja ta isko Ahlan su wuce gida.
Kallon su Ammie ta yi tace.
"Ba zan tafi da ku ba Hussaina. Ku wuce gidan Alhaji Baba kafin iyayenku su dawo..beside...aurenki ba jimawa za'a yi, zan dawo in Sha Allahu..."
Wani raunataccen kallo Hussainar ta yi mata tana share hawayenta sannan ta ce.
"Ammie Fahil fa ya fasa...iyayensa sun hana sa ya aureni Ammie..dole na haƙura da shi kamar yanda shima ya haƙura."
Cike da tausayawa ta ce.
"Ki yi haƙuri, wannan duk yana daga cikin ƙaddararki Husaina. In Sha Allahu za ki samu wani wanda ya fi sa alheri. Ba zan tafi da ku ba, domin ban yi da iyayenku ba, and a yanzu bani da wata hujja ko dalilin da zai sa na ɗauke ku na tafi daku inda nake. Ƙanin mahaifinku na aura kuma yanzu baya raye. Saboda haka ku yi haƙuri ku tafi gidan kakanku ko ku tafi gidan Isma'ila."
Daga haka ta wuce ta shiga mota, daman Bahrain shi ya jima a ciki, sosai ya shiga addu'ar Allah yasa kada a zo da Humaida domin ya tsaneta, ko zaman da ya yi da ita gidan nan don kawai bashi da yanda zai yi ne.
Suna tsaye suna kallo motar su Ammie ta sulale tabar gidan wanda Humaida faɗuwa ta yi a ƙasa tana kuka tana birgima tamkar wata yarinyar goye.
Lokaci ɗaya ranar da suka wuce Abuja suka bar Beenafah da Ammie a yashe tsakar gidan ne ya zo mata a rai. Rayuwa kenan! Yau gareka gobe ga ɗan uwanka.
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 54*
Tun da ya shiga gidan komai ya sauya a idanunsa, an gyara shi sosai an yi mishi sabon fenti duk da cewa babu abun da na farkon ya yi, gashi ma harda wani sabon gini aka yi a cikin gidan.
Mukullai aka kawo masa ya buɗe gidan da aka mallaka masa tun farkon zuwansu gidan ya shiga.
Ya jima sosai kafin ya iya samun ƙwarin gwiwar fitowa daga gidan ya nufi cikin gidan.
Bai san ta ina zai fara ba. Har yanzu bai yanke abinda zai faɗa musu wanda zai zama gamsassar hujja ba da za ta hana mi shi auren Noura ɗin, but yasan yana kan bakarsa na alƙawarin da ya ɗaukar mata. Ya yanke a zuciyarsa he won't take another wife Komai zai faru.
Da wannan ya sanya ƙafa ya shiga gidan da sallama ɗauke a bakinsa. Sosai kowa ya yi farin cikin ganinsa, an shirya masa girki na musamman sun kuma tarbeshi cike da kewa. Musamman Jadda wacce ta cika da farin ciki baki har kunne.
Nan suka kewaye shi suka gaggaisa da kuma yi masa godiyar yardar da ya yi da Suhaib har ya ɗora shi akan dukiyarsa.
Tunda ya shigo suka gabatar da masa da abinci amma ya ce su dakata tukun baya jin yunwa.
Sai after ya dawo Isha prayer ɗakin ya rage daga shi sai Jadda wanda daman koda ya iso Jaddi baya nan ya tafi wani taro amma dai yau zai dawo yace komai dare saboda zuwansa. Daga ita sai shi ne sai kuma wata matashiya wacce ke sanye cikin Abaya tayi rolling tana zaune a wuri ɗaya tare da juya baya tana kallon window tana danna wayar ta.
Sai da ta ƙara tambayarsa jikin Beenafah da kuma aikinsa yace mata komai lafiya ƙalau sannan ta waiga ta kalli matashiyar matar nan tana murmushi ta ce.
"Noura..! Ki zo ki yi serving yayanki, tun da ya iso bai ci komai ba..."
Ɗan karkata kansa ya yi kaɗan ya kalle ta da wani irin mamaki a ransa amma dai bai ce komai ba. Sai bai yi expecting ɗin ganinta a nan ba.
Jadda kuwa, kamar tasan abinda yake ransa ta jinjina kanta bayan ta kalle shi sai kuma ta waiga gare ta tana murmushi ta ce.
"Hammodi...saboda kai ne ka ɗai yasa kakanta ya amince ta dawo ƙasar nan. Ta jima bata farin ciki, duk da haka bai amince da ta zo garemu ba. Sai yanzu bayan ta amince da kai, ya kuma fahimci da gaske farin cikinta ya fara dawowa sannan ya amince da ta zo nan ɗin domin ayi hidimar auren..."
Duk a maganganunta, babu kalma ɗaya da ya fahimta ya ɗauke ta sa muhimmanci sai kalmar auren nan da ta ambata.
An turo ta nan akan batun auren su why? Waye aka tambaya kafin ta zo? Wannan dalilin ne yasa ta matsa masa akan cewa lallai sai ya zo yau?
Miƙewa ta yi tana faɗin.
"Bari ni na baku wuri ku tattauna tukun, kafin Kakanku ya iso. Naga kamar har yanzu zancen abincin baya ranka.."
Hmm! Abinci? Wai zancen ma abincin take tsohuwar ban kamar bata san halin da yake ciki ba. Tun da ya iso bata da wani zancen sai na kakansa this...Kakansa that...amma shi kuma ta shaƙewa zaman auren sa zai ti.
Ta ɗauki tsawon lokaci da ficewa daga ɗakin amma ko sau ɗaya bai ɗago kansa ya kalle ta ba.
Matsowa tayi don karanta ta zauna a kujera ɗan nesa da shi ta fara ƙoƙarin yin magana tamkar wacce ake yi wa dole ta ce.
"Welcome..! I...I wanted to great you since..but sai naga mutane sun yi maka yawa..."
Wayarsa yakai a saitin kunnensa a daidai sanda take ƙoƙarin nuna bajintar ta taji yana faɗin.
"Bibi wai ina kika shiga haka?"
Batasan mi ta faɗa masa daga can ɓangaren, sai dai ta ga ya miƙe yana faɗin.
"Allah Bibini?....ai kuwa ban gani ba. But bari na ɗauko na duba. Thank you so much."
Waigowa ya yi ya kalle ta ba tare da ya janye wayar a kunnensa ba ya ce.
"I'm coming please."
Waje yana nufi wanda yana magana yana dariya tamkar ba shi ba. Daman yana da other side da yake farin ciki haka ashe? Wani gefen na zuciyar ta ya bata amsa da cewa, eh Noura...daman ai tun a ranar farko ya faɗa miki cewa yana da matar shi wacce yake tsananin so da ƙauna...za ki sha wahala fa! Sosai za ki sha wahala Noura,domin mijin wata musamman namijin da yake tsayar da zuciyarsa akan Mace ɗaya zai yi matuƙar wahala ki samu kansa cikin sauƙi.
Ta jima sosai a zaune, wanda sai da ta fara tunanin tafiya tana mai jin hawaye sun cicciko Idonta. A haka su Jadda ke cewa shi ne wanda ya dace da ita? A haka ne suke tunanin cewa wai farin cikinta zai dawo? At least ko ba komai ya kamata ya mutun ta presence ɗinta ya jira sai ta tafi sannan ya yi abinda zai yi.
Tana nan a zaune ta takure tamkar tsuntsun da ya rasa mafaka lokacin ruwa sama sai ga shi ya dawo. Bayan ya zauna ya kalle ta kamar ba shi ne wanda ya tafi ya barta kamar kayan wanki ba tsawon lokaci ya ce.
"Miye kike cewa a ɗazun?"
Shiru ta yi tare da saukar da kanta ƙasa. Duk ƙoƙarinta na ganin ta hana kanta fashewa da kuka hakan yaci tura domin ta gama ji a ranta cewa ya wulaƙanta ta ba ɗan ƙaramin ba.
Ganin ta yi ya sake kara wayar a kunnen tare da faɗin.
" Don't Bibi! I will call back, give me a few minutes kinji Ko, ki daure please....uhmmm! Something very Important and special..alright! Thank you, I love you."
Yana sauke wayar ya ci gaba da kallon yanda take kuka na tsawon lokaci. Tambayar sa kansa yake wai miye aka yi mata ne haka?
" Ke...tambaya fa na miki. Why are you crying? Ko na miki wani abun ne kuma?"
Ji tayi ta ƙara ƙuntata ma a yanzu fiye da abinda ya yi mata ɗin. Tabbas su Jadda ne suke ganin wai ya cancanta amma ita kam tasan cewa idan har aka aura mata shi a haka dai da bai san muhimmancinta ba to tabbas wata rana baƙin cikinsa ne ajalinta.
" Wannan kukan da kike bana son sa. Yana bani haushi sosai. Just open your mouth and say your mind. Zan fi fahimtarki fiye da wannan kukan da kike."
Miƙewa ta yi tsaye sannan na ta kalle shi idanun ta cike da ruwan hawayen baƙin ciki ta ce.
"Hasashen su Jadda akanmu sam bai yi daidai ba..."
Jinjina kai ya yi yana mai jin wani irin farin ciki akan yanda ta fahimce shi a yanzu ya ce.
"Na gode sosai da kika fahimta abinda nike ta so su fahimta. Kina da tsohon mijin ki a ranki wanda har ki mutu saboda rasa shi da kika yi ba za ki iya ƙara farin ciki ba har abada, haka nima ina da matata wacce ba zan iya haɗa ta da kowace mace ba ni dai a nawa tsarin har abada. Haƙura da juna a wannan tsakanin shi ne abu mafi muhimmanci da zamu yi mu taimaki juna.."
Juyawa tayi a hankali cikin nutsuwarta ta fice daga parlourn tana mai ji a ranta cewa komai za'a yi ba za ta iya auren shi ba, daman abun da take gudu kenan tsawon lokaci. Zai yi mata ciwo a rai sosai idan ya dinga fifita matarsa a kanta, sannan magana soyayya da matarsa irin haka a gabanta, wannan babban tozarci ne da cin fuska.