Kenza eBookz

Garkuwa complete Novel - Chapter 16

Garkuwa complete Novel - Chapter 16

Garkuwa complete Novel Chapter 16: Garkuwa complete Novel Chapter 16. Motocin na isowa wurin. Gaba ɗaya mutanen Rugar dama baƙin mutanen maƙotansu sauran…

4,431 words

Motocin na isowa wurin. Gaba ɗaya mutanen Rugar dama baƙin mutanen maƙotansu sauran rugage duk suka miƙe tsaye. Tare da gya tsayuwarsu, suka gyara riƙon da sukayiwa sanduna su. Ba tsoro ba fargaba sukayiwa motoci goma nan zobe, suka sasu a tsakiya. Cikin sauri Sarkin dogarai ya buɗe marfin motar da yake ciki, ya fito tare da zungureriyar bulalarashi. A take kuma Ɗan zagi ma ya fito. Da sauri duk sauran fadawanma suka firfito kowa da zungureriyar bulalarashi. Cikin ɗaga murya ɗanzagi yake cewa. "Ta kawarka lfy Sarki Nuruddeen Bubayero Joɗa, sarki ɗan sarki jikin Sarki,uban sarki kakan sarki. Jama'ar gari sun gaisheka, Da sauri duk sauran fadawan suka, firfito cikin motar. Sarƙin motane yazo ya buɗe wa Sarƙi ƙofar. Dogari kuwa matsowa yayi da sauri ya buɗe wata ƙatuwar laima, gaba ɗaya sukayiwa ƙofar motar labule da mamyan jajayen rigunansu, yayin su duk sawunsu babu takalma, sannan kawu nansu naɗe cikin wasu ƙatti-ƙattin rawanunnuka masu girma babu kunne ko ɗaya a jiki.

Gaba ɗaya mutanen Rugar kuwa, sai ƙara tsuke fuskokinsu sukeyi, cikin jin haushin zuwa sun.

Can cikin motar kuwa Haroon ne saƙale da wayarshi a kunne cikin sanyi yake mgn sabida kada Lamiɗo ya jiyoshi, haka kuwa babu mai jinshi sai Jabeer. Cikin sanyi ya ɗan kalli Jabeer kana yaci gaba da mgna a hankali yace. "Umaymah ni dai hankali na ya tashi, da irin wasu mutane da wasu abubuwan da akeyiwa su Jabeer a masarautar su, Umaymah, meyasa bazasu bar musu sarautar da Masarautar tasu gaba ɗaya bane, sai kinga fa yadda Jazlaan dinki ke fuskanta ƙalubale fa." Cikin wata iriyar murya Umaymah tace. "Yanzu kuna inane?". Kanshi ya ɗan jujjuya kana yace. "Uhum ni ina zan san inda muke, na dai san munzo wata Rugar fulani ce, wai GARKUWAN FULANI nasu ya kawo musu ziyara dan ja-janta musu abinda ya faru, kuma gaba ɗaya mutanen rugar naga sai Wani irin kallo suke mana kamar dai zasu huce a kanmu ne". Cikin wani irin tattausan murmushi mai nuna jin daɗi tace. "Bawa Jazlaan wayar". A hankali ya miƙa Jabeer wayar tare da cewa. "Umaymah ce". Cikin sanyi yace. "Kace tayi haƙuri sai mun koma zan kirata". Da sauri ya like mishi wayar a kunne jin tana cewa. "A a amshi wayar". Ɗan haɗe fuska yayi kana ya amshi sallamar da tayi mishi. Kana ya meda kai jikin kujerar murya can ƙasa yace. "Umaymah, Na gaji tunda muka dawo ban hutaba, yau da sassafe wannan tsohon ya sani shara kamar wani bawanshi haka ya sani na share mishi wannan ɗakin nasu na gado wanda in dan ta nine rusashi za'ayi gashi yanzu kuma ya kwasoni zuwa wata rugar FULANI da duk makamaine a hannunsu, ko wa zasu daka". Cikin wani irin jin daɗin daya bashi mamaki mai yawa tace. "Ko kai zasu dakane Jazlaan, Sheykh Jabeer, yasha zana a hannun Fulani". Cikin sanyi yace. "Su kashe Ni dai Umaymah, ke kin sani tunda nake a duniya, ba'a taɓa dukana ba, sabida koda iba yaroma ban taɓa yiwa Mama da Ummi laifin da zai kaisu ga yimin dukaba, Abba na kuma baya dukanmu, Umaymah kema baki taɓa koda marina ba, to kuma wa kika ga zai dakeni a faɗin duniyar nan banda ruwan sama". Murmushi tayi wanda har saida yaji sautin cikin sanyi tace. "Allah ya tabbatar da al'khairi cikin tafiyar naku, ka dai lura kaine GARKUWAR dole da duk abinda zai cutar da Lamiɗo ko masarautarku ko sunanta dole kai ne zaka zame musu Garkuwa, so dan Allah bana son kayiwa Lamiɗo musu bare gardama a cikin duk abinda zai umarceka". Cikin sanyi yace. "To Umaymah, in na koma zamuyi mgna". Daga nan sukayi sallama, cikin mamaki ya kalli yadda gaba ɗaya manyan hakimai sun firfito, ga Lamiɗo ya fita amman yana tsaye bakin ƙofar motar. Cikin sauri ya kalli Hashim tare da cewa. "Hashim Lfy kuwa naga duk suna tsaye, garin basu da abin zamane daza'a karrama baƙi?". Cikin nitsuwa Hashim yace. "Uhum cewa sukeyi, wai sun yafe ziyara da ja-jantawar Lamiɗo".

A wojen kuwa, cikin ɗaga sauti Danzagi yace. "Hattara dai fulani mai ƙasar ne gaba ɗaya, ke tsaye tsakiyar garinku, maza ku bada masauƙi". Ya ƙarishe mgnar yana jujjuua bulalar hannunshi haka sauran fadawan. Cikin fillanci ɗan aiken Arɗo Bani ya buɗe murya da ƙarfi cikin harshen fillanci tare da cewa. "Maza ku bada hanya mai martaba ya iso fadar Arɗo Bani". Jin haka gaba ɗaya taron al'ummar fulanin suka fara buɗa hanya, Har gaban rumfar da Arɗo Bani ke ɗauke baƙi, inda aka shimfiɗe wurin da manyan taburmaii kana aka malale manyan kilisai irin namu na fulanin dawa. Bappa Malam Liman Alhaji Haro Alhaji Umaru, Musu, da kuma Ardo Duno da Arɗo barwa maƙotansu, duk suka mimmiƙe tsaye sai dai gaba dayansu fuskokinsu babu wal-wala, asalima wasun cikinsu jikinsu har ɓari yakeyi, dan fushi da zafin zuciya.

A can cikin ƙauyen Bonon kuwa, Ba'ana da sauran ƙabilum ɓamawam duk suna gaban dodon tsafinsu Bonon ɗin, Da gudu Maman Ba'ana ta iso wurin cikin Yaren ɓacamancin ta sanar dasu zuwan, sarki Lamiɗo da tawagarsa, jin hakane yasa, Ba'ana ya miƙe jiki na rawa ya nufi rugartasu. Su kuwa sauran yace in yaje yaga da matsala zai kirasu. Nan ya tafi su kuma sukaci gaba da dariyar mugunta.

A cikin Rugar Bani kuwa, Bukar Baban Ba'ana ne yayi wata iriyar fitinenneyar murmushi mai cike da mugunta dan son haddasa fitina, ta yadda zai samu masarauta Joɗo da kanta ta shiga matsala. Kutsawa yayi tayi cikin mutane har ya samu ya shigo gaba-gaba. Lamiɗo kuwa da tawagarsa taku sukeyi cikin al'farma da ƙasaita. Su Waziri, Galadima, Wambai, Ɗan iya, ɗan buram, duk suna biye dashi a baya, Dogari na rike mishi da laima, fadawa kuma na zazzaune a ƙasa, gefe da gefe, Ɗanzagi kuwa muryarsa ce cika wurin baki ɗaya duk da hayaniyar da wurin kedashi. A hankali Jabeer ya sako sawunshi woje, yana taka ƙafarshi ta dama kan ƙasar garin, yaji zuciyarshi ta buga da azaban ƙarfi har saida ta kaishi da rumtse idonshi tare da ambaton. "Innalillahi wa innailaihi rajiun". A saman red lips ɗinshi. da ƙarfi yasa hannunshi ya dafe ƙahon zuciyarshi, tare da kuma maimata. "Hasbunallahiwani'imanwakil". Sabida ji yayi tamkar zuciyarshi zata fasa ƙirjinshi ta faɗo ƙasa. Jalal, Jamil, kuwa ido suka zuba mishi, sabida ganin yadda ya rumtse idonshi, sabida suna bakin ƙofar motar, sune ma suka buɗe mishi marfin. Haroon kuwa da Hashim da Laminu, jira suke ya fita kafin su fita. Cikin mugun tsana Laminu ya kalli Jabeer ɗin da ya yunƙura ya fita, zuwa yanzu, wani irin harbawa da tsalle zuciyarshi keyi, wani irin masifeffen fargaba, da kaɗuwa ne suka dirar masa lokaci ɗaya. A hankali duk suma su Haroon suka fito, a tsakiya sukasa Jabeer kana bayinshi na biye dasu a baya. A hankali ya gyara tattausan al'kyabbar jikinshi, tare gyara hiramin kanshi ya kange kekyawar fuskarshi.

Takun da yakeyi ne ya ƙarawa shigarsa ta al'farma daraja, ya fito tamkar balarabe, gaba da baya, kamalarsa da kwarjini shi ya cika dukkan idanun bani adam dake kan doron ƙasar wannan wurin.

Ya Hashimu ne da ya samu ya dawo gida jikinsa da sauƙine, yayi wani irin kabbara mai ratsa zuciya, cikin sanyi yace. "Ziyararku tayi haske sabida kun zo mana da mai hasken addini a jiki da zuciyarshi". Ga mamakinshi sai yaji Ɗanzagi na cewa. "GARKUWA ya amsa Sheykh Jabeer Jikan sarki tsatson sarki gaba da baya". Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali yake takunda yasa al'kyabbar sa buɗuwa tana bajewa, sabida ɗaga hannunshi da yayi yanai musu sallama irin ta addinin Musulunci. Mafi akasarin mutanen tafukan hannunshin suka zubawa ido, sabida kai da ganin tafin hannunshi kasan ya gauraye da ni'imar ambaton sunan Allah da rike littafi al'ƙur'ani, da kuma jin daɗin. Shi kuwa Jabeer ƙara sarƙafe carɓin shi yayi cikin yatsun hannunshi, kana, ya fuskanci gefen hagunshi, ya ɗanga musu hannu tare dayi musu sallamar kamar yadda yayiwa yan gefen damanshi. A haka har suka isa tsakiyar ƙaton filin. Inda Lamiɗo da sauran tawagarsa ke zaune. Bisa fararen kujerun robar da anka jera musu cikin rumfar suka zazzauna. Bayan sun amsa musu sallamar da sukayi. Cikin nitsuwa Lamiɗo ya kallesu tare gyara zamanshi. Muryar Ɗanzagi ce ta karaɗe wurin da cewa. "Gyara kimtsi. A saurara dai Lamiɗo jikan ɗan Lami Bubayero jikan Lamiɗo Joɗa zaiyi mgna". Wani irin harara suka watsawa Danzagin, shi kuwa Lamiɗo cikin nitsuwar datattaku tace. "Da farko dai zan fara da baku haƙurin zalumcin da akayi, muku, Allah ya jiƙan wanda suka rigamu gidan gsky." Da ƙarfi Ɗanzagi yace. "Amin". Su kuwa dattawan ido kawai suka zuba mishi. Shi kuwa Lamiɗo a hankali yaci gaba da cewa. "Ina mai baku haƙuri da kuma umarnin kada kuce zaku ɗauki mataki domin ramuwa." Kamar daga sama sukaji Muryar Bakur yana cewa. "Babu wani sarkin da ya isa ya hanamu ɗaukar fansa sai, Ubangijin daya busa mana, numfarfashi". Da ƙarfi Wani dogarin ya ɗago zabgegiyar bulalarshi ya zabgawa Bukar. Wanda saida yayi tsalle ya kurma ihu. Cikin tsauri Lamiɗo ya ɗagawa duka fadawanshi da hadimanshi da dogara shi hannu alamun kada su sake dukan kowa. Saura su Waziri kuwa duk shiru sukayi, Jabeer kuwa, a hankali yaci gaba da tasbihin da yakeyi, sabida danne abinda yakeji zuciyarshi nayi. Shi kuwa Lamiɗo cikin sanyi ya fara mgna, dan yasan zafin rashin da sukayi ne yasa sukace sai sun rama, a hankali ya kalli fuskokin dattawan da yasan sunje mishi har fadanshi dan neman zaman lfy, cikin kula ya kalli Arɗo Bani tare da cewa. "Arɗo Bani zaku haƙura, hukuma da masarauta ta bi muku kadun cutar damu da akeyi, ko zaku ɗauki makami dan ramawa?". Cikin tarin kufula da harzuƙa da kuma son cinma wata gagarumar manufar da ya daɗe yana fatan ya samu da sai yau, fuska a haɗe yace. "Babu wani wanda zan kuma hana ɗaukan makami, Dan kare kanshi da ramuwar kisar gillan da akeyi mana." Cikin tarin Mamaki da al'ajabi Bappa da sauran dattawan suka buɗe baki tare da kallon Ardo Bani, Jabeer ma idon ya buɗe cikin sanyi yace. "Baba Ardo kayi haƙuri, muyi aiki da al'ƙalami, domin al'ƙalami yafi tokobi, ina nan inata shirin samar da tsaro na musamman kan FULANIN ƙasarmu da nake shugabanta." Cikin nuna tsantsar fushi da son fusata Lamiɗo Arɗo Bani ya dakawa Jabeer tsawa tare da cewa. "Kada rufe min baki, meka sani akan Fulani? Me ruwanka damu? Damuwarmu ta shafeka ne? Ina kake sanda ake kashe mana mata, yara, jikoki, mu kanmu bamu tsiraba, in munje mun kai kukanmu a koremu tamkar karnuka, sabida duk baku san darajar fulani ba." Cikin sauri Ɗanzagi yace. "Hattara dai Ƙaramin Ardo, wannan sarkine na fulɓe masarautar filɓe ce gaba da bayanta". Cikin ɗaga Muryar Ardo Bani yace. "Tafi can baƙin bawa, bawan banza bawan wofi mai ka sani kan fulɓe, meka sani banda bauta da fadanci, masarautar da kuke bautawa bata san menene fulɓe ba". Cikin sauri Waziri ya yunƙura zaiyi mgna, da sauri Lamiɗo ya dakatar dashi, sabida zuwa yanzu zuciyarshi ta fara tafasa, yaya daga kawowa mutane ziyara dan ja-jantawa suke neman tozarta mushi masarauta. Cikin ɓacin rai ya kalli su Bappa daketa kama hannun Arɗo bani daketa fizge-fizge yana kwaza musu baƙar mgna, cikin fushi yace. "Masarautar Joɗa ɗince bata fulani ba?". A harzuƙe Arɗo Bani yace. "Tabbas dan data fulanice, da an bamu kariya da tsaro, da an duba kukanmu, a kashemu a hanamu ɗaukar fansa, an kuma kasa bamu tsaro. Nan da mukaje ina shi jikan naka da yake matsayin Garkuwan Fulani, yana can ƙasashen woje, da iya dukiyar da ake bashi tsaro da kariya shi rai ɗaya ta kai a kula da fulanin daji dubu a kuma basu tsaro. Yau kwana uku da kashe mana mutane sai yau zaku ɗebo manyan riguna kuzo mana da batun wai kada mu rama, sara da suka da yanka mana mutane da akeyi, Kaida kab zuriyar ka da masarauta ka, babu mutun ɗaya da zai iya jurar koda bulalar *(SHAƊI)* ma bare sara da yanka da suka da wuƙa a hakan kuke ganin kanku Fulani". Cikin tarin zafin ƙuna da tafasar zuciya Waziri yace. "To me kuke so muyi muku, tun randa akayi abun munzo bamu sameku ba". A harzuƙe Bukar yace. "Ƙarya ne babu wanda yazo". A hankali Jabeer ya buɗe baki da nufin zaiyi mgna sai yaji Lamiɗo na cewa. "Uhum jinina kuke cewa ba fulaniba, to ko jaririn da aka haifa yau a jikin masarautar Joɗa zai iya jurarar bulalar SHAƊI bare manya ko ɗan baiwa zai iya bare jinina ƴaƴana ko jikokina, ko kun manta masarautar Joɗa ce tushen Shaɗi?". Cikin son harzuƙa Lamiɗo Arɗo Bani yace. "A da can baya ba, yanzu kuma da aka san lusarai ake haifa a masarautar inji an haramta shaɗi a masarautar, yau in kun isa fulani ka bada ɗan ka ko jikanka ayi gasar Shaɗi dashi, in ya iya jurewa, to mun yarda mun gamsu ku fulanine ku masarautar Fulani, in kuwa kun kasa fidda goninku to, ku ba masarauta fulɓe bace." Wani irin karkarwa jikin Lamiɗo ya fara sabida fusata, wai suda masarautarsuce tushen fulɓe a ƙasar, su ake cewa ba fulani ba, har ake kiransu lusarai, Galadima, Waziri, Wambai, Ɗan iya, Ɗan buram, Ɗan Maliki, Sarkin Dawaki. Gaba ɗaya hankalinsu yayi masifar tashi sabida ganin tsananin fushi da tashin hankalin Sarki Lamiɗo. Jamil Jalal Haroon kuwa , hankalinsu na kan Jabeer bisa alamun yana cikin wani hali. Shi kuwa Jabeer bugun da zuciyarshi keyi ne yasa, Hankalinshi tashi, ƙarfin addu'o'in da yakeyi ne, yashi iya fahimtar abinda suke cewa. Kamar daga sama kamar cikin mafarki, sukaji murya Lamiɗo na cewa. "Ga jikana, Jabeer GARKUWAN FULANI, na badashi a matsayin matashi mai yin gasar Shaɗi ku fito da duk gwanin da kukega shine makurar gwayen yankinku. Ayi Shaɗi dashi yadda zaku samu gamsuwar yakai matsayin ya kasance GARKUWAN FULANI". Tunda ya amɓaci sunan Jabeer, Sarkin Fada yayi wani irin murmushi mai cike da jin daɗin alamun burinshi zai cika. Hakama Arɗo bani wani irin asirtaccen murmushi yayi.

Jala, Jamil, Haroon, Hashim, Imran, Galadima, kuwa wani irin zazzaro ido sukayi. Cikin tsananin kaɗuwa da firgicin batun Lamiɗo suka zuba mishi ido.

Bukar kuwa cikin karaji yace. "Ba'ana Bukar shi zai kara dashi." Ya ƙarishe mgnar da fatan Ba'ana ya kashe wanda aka kira da Jabeer tunda jikan Lamiɗo ne.

Jabeer kuwa wani irin kallo yayi kakan nashi, irin kallon nan. Na lallai kam tsohon nan ka haukace, ka zauce, ai bani bakam ko inuwata bazaku kuma gani a garinkuba bare kuyi wannan gwajin dashi. Ga mamakinsu kab sai sukaji Arɗo Bani na cewa. "A yau ɗinan kuma Yanzun nan, a kuma nan za'ayi gasar Shaɗi in har kun isa fulani." Sosai Lamiɗo yaji hakan bai mishi ba dan a zotonshi za'asa ranane ya koma ya shirya Jabeer kafin ayi gasar, to fahimtar ƙuresu suke neman yi, yasashi gyara zamanshi cikin danne fargabanshi na anya Jabeer zai iya jura yace. "Na Aminc....!

Yau bisa wani uzuri ban samu yin posting da wuriba, kana kuma ba editing a gurguje na watsoshi, bari in nemo PAGE 16 ko zuwa yan da yamma ne.

By *GARKUWAR FULANI* 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🐄🕊️🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 16

NA *AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🐄🌈🦚🤴🏻💘

*FREE PAGE SUN ƘARE DAGA WANNAN PAGE 16 DIN IN DAI KIKAGA LITTAFINA GARKUWA BA TARE DA KIM BIYA NA SAKI A GROUP BA TO NA SATANE, DAN ALLAH DA MANZONSA KADA KU FITARMIN DA LITTAFI DAN ALLAH KU BARI IN SAMU KUƊI zuwa makka😂😂😂*

*Littafin GARKUWA na kuɗine dan Allah da Manzonsa kada ki karanta na sata, kada ki watsamin littafi a sata, turo katin MTN na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276 ki biya ki karanta cikin aminci ba tare da haƙƙi naba. Ko kuma ki biya 1k domin shiga Special Group wanda cikin sati biyu rak za'a gama Part 1, da izinin ubangiji kana a shiga 2, turo dubunki ɗaya ta wannan asusun 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidan biyanki ta wannan number 09097853276 in baki da halin biyan dubu ɗaya ko baki da ra'ayi kina iya turo ɗarinki uku kacal da ban tsauwalaba sabida halin rayuwa da muke ciki. Dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenki kada ki sai littafina in dai kin san niyarki ki saya ki fitar da shine in kuma. Har kin sayane to dan Allah da Manzonsa gaya min in baki kuɗinki in cireki a group na, dan Allah🙏🏻 nace badon niba*

"Na Amince!". Cikin tarin mamaki Jalal, Jamil, Imran, Haroon, Hashim, da duk sauran tawagar Lamiɗo suka, zazzaro ido cikin tarin mamaki da al'ajabi, sam basuyi zaton jin haka daga gareshi ba, Ya Salmanu kuwa wani irin farin cikin mara misaltuwa ne, ya rufewa, domin yana ganin ikon Allah da yake nuna mishi zahirin abinda yake nuna mishi a mafarkansa tsawon kwanakin da yake a gadon asibiti.

Ba'ana kuwa da tun ɗazu ya iso, wani irin ihu yayi mai cike da farin ciki, da jin daɗin yana ganin zaiyi abinda gaba ko kashe mutanen Rugar Bani sukayi gaba ɗaya, masarautar Joɗa bazata kulasuba, Wani irin tsuma da karkarwa jikinshi keyi sabida azabar muguntarsa dake tasowa.

Arɗo Bani ma wani murmushi manufa yayi tare da cewa. "To, ina gwanin naku?". Cikin karaɗi Ɗanzagi, ya kalli Jabeer tare da cewa. "Malami ba faɗen Allah, malamai magada annabawa, Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa, GARKUWAN sarki Lamiɗo, jikan sarki, mai martaba Nuruddee. Jarumin Masarautar Joɗa." Gimtse bakinshi yayi ganin wani irin kallo mai ma'anoni da yawa da Jabeer ke watsa mishi, Cikin yin ƙasa da murya tare da tsuke fuskarsa, ya ɗan ronƙofo kanshi, kusa da Lamiɗo murya a kausashe yace. "Wannan tatsuniyar da kukeyi, bafa koyarwan shariya bace". Da sauri Lamiɗo ya katseshi da cewa. "Eh amman koyarwar Masarautar Joɗa ce". Cikin kufula yace. "Ya ina ce maka Allah kana cemin gadon masarautar Joɗa ce". Cikin haɗe fuska da ƙasaita Lamiɗo yace. "Eh ba addini bane, kuma sai an yishi dan gadon masarautar muce". Kanshi ya kuma motso dashi jikin kakan nashi cikin taɓe fuska yace. "Okay to ai sai ka tashi, ka tsaya su zaneka ciki da woje". Cikin kausasa murya Lamiɗo yace. "Kai ne dai zaka tashi". Cikin watsawa kakan nashi wani kallo na lallai ma tsohon nan kanka ya kwance yace. "Ai bani bane sarkin, kaine sarkin ko?". Cikin faɗa Lamiɗo yace. "To ko Ubanka bai isa in sashi abu yace bazaiyi ba". Jin muryar Lamiɗo ta ɗan yi samane, yasa fadawanshi suka miƙe tsaye, Ware rigunansu sukayi, suka kamgesu da jajayen rugunan nasu, ta yadda babu mai ganinsu, Cikin haɗe fuska Jabeer yace. "Yesss shi bazai ƙiba, tunda kai ubanshi ne, Ni kuwa babu wanda zai sani in zauna in bawa wani ƙaton fatar jikina ya zane, kai jimin zancen son zuciya, kai ni kaɗaine jikanka, a duniya, a nanma baga Ya Hashim ba ai shine babban jikanka, zancen gsky na gaji da wannan tirsashe-tirsashen naku, kanada ƴaƴan ai, ka kira ɗaya daga cikin ya'yan ka yazo ya wakil ceka mana, Amman ni dai kam Muhammad Jabeer babu wani tsohon da zanyiwa mubaya'a in tsaya wani gardin makiyayi ya ɗimeni, tunda ba faɗin Allah bane". Ya ƙarishe mgnar yana yunƙirin tashi tsaye. Da sauri Galadima yasa hannu ya kamo nashi, fuskar ya kwaɓe tare da komawa zaune yana gyara hiramin kanshi da al'kyabbar jikinshi, Cikin tausasa harshe Galadima yace. "Jabeer kafa san ma'anar GARKUWA a masarauta." Cikin sanyi da ganin kima da darajar dottijon Jabeer ya kwaɓe fuska tare da cewa. "Nifa shiyasa wannan mulkin bawai sonshi nakeyi ba, sabida wannan tsarabe-tsaraben daba na addiniba, a buwayi mutun dashi, yaya nasan abu ba Allah ne da manzonsa suka wajabta mana shiba, ace in zauna a cutar dani." Cikin sanyi Waziri ke jujjuya mishi kai a hankali yace. "Jabeer Garkuwa fa, kake dole ka kare martabar Masarautarmu kana ka nunawa su fulanin da kake Garkuwarsu kai Jarumine". Rai a ɓace ganin sufa da gske sukeyi, cikin dakiya yace. "Bana so, ita wannan sarauta ta GARKUWAN FULANI ku bawa duk wanda kukeso, ni ban nemaba dama". Shiru Haroon yayi dan gskya harga Allah shi wannan abun yazo masa a bazata. Jalal kuwa cikin haɗe fuska yace. "Wannan ma ai zancen banza ne, An bawa Ya Jafar Galadima, ko kwana ashirin baiba a kai, aka birkita masa rayuwa, kana yanzu kun likawa Hamma Jabeer wani GARKUWA kun kwasomu kun kawomu Rugar fulani, wai kuna cewa ayi gasar duka dashi." Da sauri yayi shiru ganin Jabeer ya ɗaga mishi hannu. Jamil kuwa tuntuni idonshi ke tsastsafo ruwan hawaye dan gani yake so ake a kashe Hammansu a ƙarar da ƴaƴan ɗakinsu, Laminu kuwa ɗan Gimbiya Saudatu matar bappansu Sheykh kuma Kani ga Yah Hisham wani irin dariyar jin daɗi yakeyi.

Shi kuwa Lamiɗo, wayarshi ya zaro, Mai alfarma Sarki Jalaluddin ya kira wanda yake kane ga Jabeer. Wanda ya haifi Mamanshi. Bayan sun gaisane yayi mishi bayanin abinda ke faruwa, jin haka yasa yace ya bawa Jabeer wayar.

A tsakar filin Rugar Bani kuwa, tuni. Arɗo Bani ya bada dama na suduka yana shekantawa gari cewa. Ana gamgamin Shaɗi yanzu-yanzu tsakanin Ba'ana da kuma jikan Sarki Nuruddeen.

Tuni an firfito da ganguna anata kaɗe-kaɗe da bushe-bushen sarewa, kana ana buga babban gangan dake tsanar da makotan Rugar Bani sauran rugage alamun za'ayi Shaɗi yanzu.

Kafin kace kobo, Rugar Bani ta cika tayi maƙil da mutane, Maza da mata, matasa da tsoffi, sabida an san duk sanda za'ayi Shaɗi ana bada sanarwar, kwana uku kafin nan to jin wannan na gaggawa kuma da jikan Sarki za'ayi yasa, mutane taruwa, gashi ranar jumma'ace, duk matasan rugogin suna, gida tunda suka dawo sallan jamma'a. Rugar Bani ta cika tayi maƙil da bani adam, tako wacce kusurwa tsastsafo akeyi kusufa-kusufa. Jin karan tamɓarin ganganr Shaɗi ne ya ƙara gaiyato mutane harda na cikin garin Shikan, tuni ƙabilun Bonon sun garzayo cikin Rugar Bani.

Bukar kuwa mahaifin Ba'ana shida kanshi yaje, cikin Garkensu ya ɗauko tukunyar tsumin bulalim shaɗin da Ba'ana ke tsumasu da dafin kunamai da sauran sihirurruka, na dodon tsafinsu Bonon.

Matasa majiya karfi ne keta ɗebo ruwa, cikin rijiyoyin garin. Suna jiƙa taron wurin dandamalin, da za'ayi gasar kaɗe-kaɗen duk sun taru sun cika kunnen kowa. Jabeer kuwa bugun da zuciyarshi keyi shiyafi komai tada mishi hankali.

A can cikin gidajen Rugar kuwa, duk yan samari da yara sun firfito. A gidansu Shatu kuwa, Tunda taji Shelan da Nasuduka yakeyi cewa gasar Shaɗi tsakanin Ba'ana da jikan sarki. Kuka ta farayi, cikin tashin hankali da kiɗima ta kamo hannun Ummiy da tayi shiru sai ido take binsu dashi, murya na rawa tace. "Ummiy kijifa, zasuyi ya kashe, wani wanda baijiba bai ganiba, sunfa san illar dake cikin bulalinshi." Ganin Ummiy dai ba mgna zatayi ba, yasa ta kamo hannun Junainah cikin tsananin tashin hankali tace. "Junainah ki gudu, kije kicewa Bappa kada ayi gasar nan, Ni dai a bari na haƙura zan auri ya Ba'ana a yadda yake, zan zauna dashi, zanyi ƙoƙarin gyara mishi, rayuwa na gaji, kada a sake cutar da wani a kaina". Da sauri Rafi'a ta kalleta jin ta kamo hannunta cikin zubda hawaye tace, "Rafi'a wlh ya Ba'ana zai iya kashe mutun a kaina, da dafin kunamai yake tsuma bulalinshi, da wani tsafin, me ribata ayi ta cutar da mutane a dalilina, babu fa wani mahaluƙin da zai iya cin Ya Ba'ana gasar Shaɗi, babu wanda zai iya jurar azabar bulalinshi fa." Cikin sauri ta miƙe tare da miƙar da Junainah, sai kuma duk suka koma suka zauna, Jin muryar maƙocibsu Sarkin aska, yana cewa. "A a Shatu kada ki tura kowa, kada kuma kije kin tsumayi sakamakon gasar yau in sha Allah zata banbanta da na baya . Yanzu ma Arɗo Bani ne ya aikoni da in gargaɗeki." Yana faɗin haka ya juya da sauri ya fita, kana ya nufi wurin gasar.

Da ido suka bishi. Ita kuwa Junainah da sauri ta miƙa ta nufi kitchin ɗin su, tana cewa. "Yauwa Adda Shatu, barin in kawo mana gasassun zabbin da Ya Ba'ana ya kawo mana muci. Ɗazu da nace muci Adda Rafi'a ce, tace mujiraki." Cikin sanyi Rafi'a tace. "Yauwa Junainah kawo mana, muci yau tunda gari ya waye bamuci komaiba." Gyara zansu sukayi, kana ta kalli Shatu cikin kula tace. "Dan Allah Shatu muci abinci, kinga Ummiy ma taƙi cin komai ganin, yadda kiketa kuka tunda kikaji ɓatansu ya Giɗi da rasuwar Ya Lado da Inna." Cikin zubda hawaye ta gyaɗa mata kai, sabida ita kanta tasan tana jin wani irin masifeffen yunwa, tamkar zai kasheta. Da sauri Junainah ta nufosu riƙe da akoshin gasassun zabbin da aka zuba dafin macijin a cikin.

A can cikin tsakiyar garin Rugar Bani kuwa. Tuni su Ba'ana an gama shiryawa zalumci, domin dama ai a ƙa'ida shi zai fara duka, Yana tsaye sai zagaya filin yake yana zane iska, makaɗa da mabusa nata yi mishi kirari.

A cikin wurin da Fadawa suka kange Lamiɗo da tawagarsa kuwa, anata kai ruwa rana da Sheykh Jabeer, Cikin kufula, yake cewa Sarki Jalaluddin da suke waya dashi. "Nifa babbar matsalarta wannan abun da za'ayi ba *Sunna* bace ba kuma *Farilla* bace, ba kuma *Mustahabbibace*, kai ko a babin *Makaruhi* ban taɓa cin karo da wannan banzar al'adar da kukeso in yarda ayita dani ba, Ina kuma da yaƙini in da zan bajeta a babin musulunci, kai tsaye za'a iya karhantashi, sabida ai cutar da kaine kuma, Musulunci bai yarda mutun ya cutar da kanshi ba, haka kurum kuce wai in tsaya a zaneni, inji shi kanshi kakan Lamiɗon Joɗo da yaji haza a gasar Shaɗin shine ya hana wannan al'adar a masarautarsa sannan yanzu ace za'a saketa a kaina bayan tsawon shekaru 145 ba'ayishi ba, tun zamanin jahiliyan ma an bar abu sai yanzu ku tara abu a kaina, to wallahi bafa zai yiwuba." Cikin kufula Sarki Jalaluddin yace. "To ya kakeso ayi ɗan masu ilimi kowa jahiline sai kaine mai ilimi sabida tsabar tsoro da ɗan karen son jiki kana gudun abinda zai taɓa lfyarka shine zakayi ta jawo mana wasu dogin falsafofi, a hir ɗin kafa Jabeer ko uwarka bazan sata abu taimin musuba". Gaba ɗaya sun hautsuna mishi zuciya, Ji yadda suketa zageshi, dan kawai yace bazaiyi abinda al'adace ba addiniba sai wani ce mishi suke ko uwarka ko ubanka, bayan sun san baya kuran hakan, rai a ɓace yace. "Uwata kace ai tunda ita ai ka haifa ba niba ko?, zancen gsky bafa za'ayi wannan abunba, sun daɗe basu ce mana lusaraiba, dolene, sai sun yarda mu fulanine, kai yau nifa ba bafulatani bane. A kirani da ko wacce ƙabilar ma in anga dama aikin kawai!". Yana faɗin haka ya katse kiran. Laminu kuwa da yake cikekken ɗan jarida, tuni yana naɗe komai a faifai jawaban su.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull