Garkuwa complete Novel - Chapter 17
Garkuwa complete Novel Chapter 17: Garkuwa complete Novel Chapter 17. Shi kuwa Sarki Jalaluddin, ido ya zubawa wayar jin jikan nashi ya katse kiran,…
4,122 words
Shi kuwa Sarki Jalaluddin, ido ya zubawa wayar jin jikan nashi ya katse kiran, murmushi yayi, irin nasu na manya, kana da sauri ya kira, Umaymah. A can Babba birnin Katsina, kuwa Gimbiya Khadijah Umaymah kenan , wacce take matar ɗan Sarkin Tsinako, Kekkyawar mata mai cikar haiba nitsuwa, tana kishinɗe, bisa wata tattausar doguwar kujera, yayinda Hadimanta biyu ke mata tausa. Jin wayarta na suwane, yasa ta buɗe idanunta dake lumshe, tunda sukayi waya d, ɗan ta Haroon ke gaya mata inda sukaje da ƴaƴan ƴar uwarta mafi soyuwa a rayuwarsu ne, taketa murmushi. Ganin sunan mahaifinta ne yasa tayi saurin amsa kiran. Bayan sun gaisane, Sarki Jalaluddin ya ɗanyi murmushi cikin nitsuwa yace. "Khadijah, kira ɗan ki, ki bashi umarnin bin umarnin mu, domin yana nuna mana ai bamu muka haifeshi ba, bazamu tirsasashi ba". Cikin tarin girmamawa tace. "Ranka ya daɗe, me kukeso in bashi umarni a kai nasan bazaiyi min musuba". Cikin jin daɗi yace. "Kice dashi ya amince da gasar da za'ayi". Cikin sauri tace. "To An gama yanzu kuwa, in sha Allah zaku sameshi mai biyayya a gareku". Daga nan sukayi sallama, Kana ta kirashi, sau biyu tana kiranshi baya ɗagawa, sabida kanshi ya ɗau zafi yana ganin za'a tirsasashi ya cutar da kanshi. Ga wani irin azabebben tsinkewa da zuciyarshi keyi, Ji yake tamkar zata faso ƙirjinsa ta fito, tayi ta tsalle a doron ƙasa. Gashi duk tsoffin Masarautarsun sun zagayeshi. Kowa da abinda ke ce mishi. Ga uban kiɗen-kiɗen dake hawa mishi kai.
Ita kuwa Umaymah ganin bai amsa kiran bane, yasa ta kira Haroon yana ɗagawa tace. "Ina Jazlaan bashi wayar". Da sauri yace. "To Umaymah uwar Garkuwa gashi nan ido ya raina fata". Cikin barkwancinta da yaron nata tace. "Kaci gidanku Haroon Ni ɗana ba ragobane". Murmushi yayi tare da cewa. "To mu gani a ƙasa mana Umaymah". Yana faɗin haka ya miƙa Jabeer wayar wanda yake cewa Lamiɗo. "Bafa zan yiba, tsohon nan gwara ka miƙe kaje ayi da kai tunda kaine sarkin Masarautar Joɗa, Ni nan babu abinda na sani bayan nonon uwata sai al'ƙur'ani da hadisai, sai likitancin da kuka sani na karanta a dole badon raina yasoba, tun ina yaro kullum Ni a cikin sani dole kuke da tsabar rainin hankali, kaje a jibgeka, Ni kuwa nayi al'ƙawarin zan jinyaceka, Lamiɗo Joɗa." Ya ƙarishe mgnar yana amsar wayar da Haroon ke miƙo mishi cikin faɗa yace. "Mitsss wai meye kaketa tura min wannan argar wayar taka ne?". Cikin mamaki Haroon yace. "Kan uba Jabeer wayar tawace ma arga, wayar da kuɗi ta sun kai rabin million To inma argace Umaymah ce bisa layi". Ba tare da ya kara wayar a kunneba yace. "Hello Umaymah". Cikin tausayi Jalal yace. "Hamma Jabeer baka kai wayar kunneba". Lips ɗinsa ya taune tare da cewa. "Au, zama su sani yin abu da yawa". Haroon kuwa mamaki yakeyi domin karo na forko kenan da yaji Jabeer yace Hello a madadin Assalamu alaikum, da shine abinda yakeyi. Ita kuwa Umaymah tana jin ya kara wayar a kunne shi ya kira sunanta cikin rauni. Murya a kausashe tace. "Jabeer". Da mamaki ya amsa dan sama da shekaru goma sha biyu kenan da Jazlaan take kiranshi, cikin sanyi yace. "Na'am Umaymah". Cikin bada umarni tace. "Jabeer ka tashi maza yanzu ka shiga fagen gasar nan ayishi da kai, bana son musu umarnine ba shawara ba". Cikin sauri ya zaro siraran kyawawan idanunshi, Dai-dai lokacin kuma Lamiɗo ya miƙe tsaye cikin tashin hankali da kiɗima da firgici da baƙin cikin dakatar da gasar Shaɗi da akayi a masarautarsu ya sani da anayi da Jabeer bazai ƙalubanceshi ba, cikin sanyi yace. "Zanje za'ayi dani, zan tabbatar da darajar masarautatarmu bata rusheba." Da ido yabi Dottijon kakan nashi wanda a ƙalla ya kai shekaru 91 a duniya. Cikin kauda kai yace. "To Umaymah yadda kikace haka za'ayi amman bari in kira Sheykh Abdulkareem in sanar mishi in ya amince dai zanyi". Da sauri tace. "A a ban yafe ka kirashi ba, wato don kasan in ka kirashi zai kira Sitti da Mai alfarma Jalaluddin da Sarki Nuruddeen ya dakatar da duk abinda za'ayin, tunda na san cemishi zakayi ba addini bane, al'adace, to ban yardaba maza tashi". Ganin Ya Hashim na miƙa masa wayarshi ne yasashi cewa Umaymah. To cikin sanyi. Yana amsa wayar da Ya Hashim ya miƙa mishi yaki Muryar, mahaifinshi cikin sanyi da kuma alamun yana kukane yace. "Jabeer ashe har kayi girman da Lamiɗo zai umarceka da yin abu kaƙi yi mishi mubaya'a, Ashe har na haifi ɗan da zai ja da mahaifina." Cikin sanyi da rauni yake jujjuya kai murya na rawa yake cewa. "A'a Abba, kayi haƙuri kada kayi kuka a kaina." Bai kulashiba yaci gaba da cewa. "Jabeer Ashe zuciyarka har tayi tauri da kangarewar da kanaji kana gani za'a daki mahaifina a gaban idonka, bazaka zame mishi GARKUWA ba, Jabeer wannan shine tukuicin tsantsar son da mahaifina keyi muka, wanda har ya jazamin ƙiyayya a wurin yan uwana sunaga ya fifitaku kan sauran jikokinsa Especially ma kai Jabeer komu daya haifa baya nuna mana son da yake nuna maka, shine zaka bari a dakeshi mutun mai shekaru 91 da ɗaya a duniya kai me shekaru 30 bazaka iya zame mishi GARKUWA ba?". Cikin rauni da ƙunar zuciya, ya miƙe tsaye hannunshi yasa ya kamo na Lamiɗo cikin tarin ƙuna da zafin rai da takaici yace. "Na Amince, zanyi gasar na yarda, ka koma ka zauna". Wani irin farin ciki ne ya ziyarci, zuƙatansu gaba ɗaya, sai dai kowa da irin manufar farin cikinsa.
Jin haka yasa fadawan janye labulen da sukayi musu. Shi kuwa Lamiɗo hannunshi yasa ya kamo hannun Jabeer, cikin tsantsar farin ciki da al'fahari da ƙasaita ya fara taku, suna ratsawa cikin taron. Kana fadawansu na biye dasu a baya. Ɗanzagi yana. "Takawarka lfy Sarki mai daraja Lamiɗo ɗan Lamiɗo jikan Joɗa. Gyara kimtsi". A haka har suka isa cikin asalin dandamalin da aka jiƙashi jilak da ruwa, sabida hana ƙura wanzuwa.
Gaba ɗaya taron mutanen wurin maza da mata manya da yara, Jabeer suka zubawa ido, sabida duk wanda ya ganshi yaga sahihin Balarabe, mai kamala da nitsuwa, uwa uba kima da haiba, ƙwarjini shi ya cika dukkan idanun magautanshi dake wannan yanki, yayinda masoyanshi ke taraddadin abinda zai faru. A tsakiyar filin suka tsaya, hannunsu dake raƙe dana juna Lamiɗo ya ɗaga tare da fuskantarta gabas, kana ya juya yamma, ya kuma juyawa kudu da Arewa, sannan suka dawo tsakiyar filin, Cikin ƙasaita, yace. "Ga GARKUWAN FULANI, kuma daga Wannan nasarar da zaiyi a gasar nan, Zai tabbatar GARKUWAR Masarautar Joɗa, GARKUWA kuma mai ikon zama inda yaso a cikin fada". Dariya Bukar yayi kana ya ɗaga hannun Ba'ana da yaketa wani abu da ƙirjinshi kamar damisa, Cikin isa da yaƙini da al'fahari yace. "Mu kuma ga namu Garkuwan, da muke da tabbacin bai taɓa gasa ya faɗiba". Sake hannunshi Lamiɗo yayi kana ya juya ya koma ya zauna, cikin rumfar da akayi musu masauƙin. Al'ƙalin gasar ne yazo tsakiyar taro, kamar ko yaushe, hannun Ba'ana ya kamo, ya ɗaga sama, hakan yasa, gaba ɗaya makiɗa da mabusa suka ƙara sautin kiɗe-kiɗen su, wanda Jabeer ke jinsa har tsakiyar kansa, Allah ya sani, baya son hayani koda dai-dai da ƙwayar zarra ne, ga wani masifeffen fargaba da tsinkewar da zuciyarshi keyi, yanaji tamkar yasa hannunshi ya toshe kunnuwanshi. Ɗan wani gajeren tsaki yaja sabida Allah ma ya sani baya son kallo, to kuma yanajin yadda idanun mutane ke yawo a jikinshi.
Shi kuwa al'ƙalin gasar, yana sake hannun Ba'ana yazo ya kamo hannun Jabeer, Da sauri ya juyo ya kalleshi sabida kamo hannunshi da yayi sai yaji tamkar hannun jariri ya kamo dam laushi da taushin fatar, hannun sanyi ƙalau, girgiza kanshi yayi cikin tausayawa, sabisa, ya za'ayi ace mai wannan taushin hannun fatarsa ta iya jurar azababbun bulali masu masifar zafi. Ɗaga hannun Jabeer yayi sama. Yana mai nunawa taron mutanen shi a matsayin dashi za'a gwabza. Shi kuwa Sheykh Jabeer, duk abinda akeyi idonshi na cikin ɗan siririn farin galashi mai garai-garai dake liƙe a fuskarshi, Hannunshi kuma riƙe da carɓinshi, kana bakinshi ambaton sunan Allah.
Cikin tarin mamaki ya kalli, Al'ƙalin gasar tare dasa hannunshi ya riƙe bakin al'kyabbar jikinshi cikin haɗe fuska yace. "Me hakan!?". Cikin saurin rusunar da kai Al'ƙalin gasar yace. "Za'a cire kayan jikin naka ne!". Cikin tarin mamaki ya zazzaro ido waje, a baiyane yace. "Akan me kenan, suturar da Allah yayi min a matsayin mulmi, in killace kaina, shine zaku yayemin a cikin dubban dubatan mutane?". Cikin dakiya Al'ƙalin ya ɗan kalleshi domin kwarjinin Jabeer ya cika masa fuska cikin sanyi yace. "Allah rene, ƙa'idar gasar ce, ba'ayi da kaya a jikin mutun sai ɗan kamfai, kawai ake bari a jikin mutun". Cikin kufula da harzuƙa yace. "To bada niba, Ni nan Muhammad Jabeer wallahi banyi lalacewar da zan tsaya tsirara a gaban jama'a ba". Yana faɗin haka ya juya a fusashe, zai fita cikin taron. Ganin hakane yasa Galadima, yayi saurin tasowa, kana Ɗan buram na biye dashi a baya, tareshi sukayi tare da kamo hannunshi.
Da sauri suka juyo suna. Kallon gungun wasu matasa wanda suka kece da dariyar ƙeta cikin hausarsu ta ƙabilu suke cewa. "To ku ɗan naku ko yadda ake gudanar da gasar ma bai sani bane? Ya zaiyi zaton da wannan shigar tasa za'a dakeshi, to ai ko bulali dubu za'ayi mishi ba jinsu zaiba, Kai Ɗan kazagi, ka gaya mishi nan ba cikin masallaci bane. Nan wurin shaɗi ne". Jiyo hakane ya sa ran dukkan musulman wurin ɓaci. Sabida sun fahimci kafuraine masuyin wannan zancen. Galadima kuwa da Ɗan buram sun ɗauka abin wasane, a zatonsu zasu shawo kan Jabeer a sauƙaƙe, amman ina ya tiƙe yace babu wani zinɗiƙin ƙaton da zai sashi ya yaye suturar dake jikinshi. Dariyar da su Arɗo da sauran mutane keyine ya hautsuna lissafin Lamiɗo. Cikin harzuƙa ya taso, har kamar zaiyi tuntuɓe ya nufi inda su. Waziri, Wambai, Ɗan buram, Ɗurɓi, Da Galadiman, cikin tashin hankalin alamun akwai wata babbar manufa da Galadima ke son cimmawa cikin lamarin ya riƙe hannun Jabeer tare da cewa. "Haba Jabeer kai wanne irin mutun ne mai kafiya da taurin kan tsiya, yaya muna binka kana zillawa, muna haɗaka da Allah da Manzonsa amma kana tunzuramu, wallahi da yau sai anyi gasar nan!". Cikin tsananin ɓacin rai yace. "In tsaya a tozarta ni kuke so. Ayimin tijara kukeso, da wanne idon zan kalli al'ummar Annabi da jiki tsirara". Cikin kufula Waziri yace. "Waya ce maka tsirarane?". Murya a sama yace. "Tsirara ne mana! Tunda sunce wai dagani sai Boxes zan tsaya, ka kuwa san ko Mahaifiyata data haifeni tun ina shekaru shida a duniya bana tsayuwa a gabanta dagani sai ɗan kamfai, tunda nake Mahaifiyata, Mahaifina, Yayuna, Uncles, na Aunty's na, babu wanda ya taɓa dukana, sabida ban cutar dasu da komaiba bare su hukuntani da duka haka kurum rana tsaka kunce in tsaya a dakeni, na yarda, sannan yanzu kuma ace nai tsirara, kai bafa wanda zan yiwa mubaya'a akan hakan..!." Tas! Yaji sauƙan wani irin gigitaccen mari sai dai babu wanda ya ga sauƙan marin sabida suna tsakiyarsu Waziri ne, kuma sauran mutanen garin duk kowa bayan su Waziri suke iya gani. A harzuƙe ya ɗago kanshi, Lamiɗo ne ya gani tsaye a gabanshi. Jan hannunshi yayi da iya ƙarfin shi na tsufa. Tsakiyar filin suka koma, cikin fushi yace. "Galadima zoka cire mishi kayan." Da sauri Galadima ya motso gabanshi.
Su Waziri kuwa duk suka koma cikin Rufarsu masauƙinsu. Wani irin tsuma da karkarwa jikin Jabeer ya farayi, tun sanda yaji sauƙan marin. A take idanunshi nan su kaɗa sunyi wani irin masifeffen juyewa sunyi jazir, Hatta lips ɗinshi karkarwa sukeyi. Wani irin tarin baƙin cikin da bai taɓa jin irinsa ba a duniya ne, ya lulluɓe masa zuciya. Koda randa Ya Jafar ɗinsu ya zauce, baiji makamancin wannan ɓakin cikinba. Ji yakeyi Tamkar ya haɗiyi zuciyarshi ya mace ya bar duniyar kowama ya huta, Rumtse idonshi yayi da azaban ƙarfi lokacin da yaji, Galadima ya gama komce masaƙalan al'kyabbar jikinshi, kana ya buɗe shi, yayi ƙasa dashi, har saida ya cire hannayenshi a ciki. Haroon dake gefensu ya miƙa wa al'kyabbar, kana a hankali ya kuma matsowa gareshi, hannunshi yasa saman kanshi ya ɗage zagayen baƙin abin da yake kan Hiramin, kana yasa hannunshi ya janye hiramin. Kekyawar fuskarshi ta fito ras, tattausan baƙin gashin kansa dake kwance lib-lib ya baiyana, wanda hakan yasa kaso 70 cikin ɗari na dubban mutanen dake wurin suka zuba ƙwayar idanunsu kanshi, da yawa tasbihi da ta'ajjudin irin kyau da haibar da Allah ma ɗauka kin sarki yayi mishi sukeyi.
Jalal kuwa ji yake tamkar ya rinƙa kurma ihu, Allah yasani baya son abinda zai cutar musu da Hammansun, Jamil kuwa tuni hawaye yake zubdawa, Ya Hashim, Imran, Sulaiman, kuwa dukkansu sunkuyar da kawunansu sukayi ƙasa.
Laminu kuwa wani irin masifeffen jin daɗi yakeyi, hakan yasa ya ƙara kutsowa cikin filin hakan ya bashi daman yin viewing da kyau.
Shi kuwa Jabeer tafarfasar da zuciyarshi keyi yayi masifar tsananta lokacin da yaji, Galadima ya zare mishi tattausar rigar shaddar dake jikinshi. jin yasa hannunshi yana shirin zare mishi singlet ɗin jinshi ne yasashi, ƙara ambaton sunan Allah da sauri-sauri, sabida ji yakeyi tamkar ya buɗe ido ya shaƙo moƙoshin Galadima sai ya sumar dashi, tabbas da ace al'ƙalin gasarne ke cire mishi kaya da tuni ya daku. Cak ɓari da karkarwan da jikinshi keyi ya bari, Lokacin da yaji Galadima yasa hannunshi ya kwance zariyar dogon wondon jikinsa. "Innalillahi wa innailaihi rajiun, Hasbunallahiwani'imanwakil. Allahumma ajjirni fi musubati!!.." Ƙasa idawa yayi, jin an saɓule wondon jikinsa yayi ƙasa, da ƙarfi ya buɗe kwayar idanunshi da suka koma tamkar garwashin wuta. Tafarfasar da jininshi keyi shine abu mafi tartsatsi a rayuwarsa. Hannunshi Galadima ya jawo da ƙarfi wanda dole yasa ya ɗaga sawunshi ya tsallake wondon ya zama babu komai a jikinshi dagashi sai Boxes wanda Allah yayi mai ɗan tsawone yazo har kusa da guiwarsa saidai a matse yake.
A tsakiyar filin ya tsaidashi kana ya juya ya koma ya zauna kusa da Lamiɗo. Jalal ne ya sunkuya ya ɗauki wondon da sauri ya miƙa wa, Haroon.
Shi kam Jabeer zuwa yanzu, Ya sani a duniya ba'a taɓa yi mishi tozarci sama da wannan ba, ji yakeyi a duk faɗin duniya babu garin daya tsana sama da garin Rugar Bani, bai taɓa jin haushi da tsanar wani abu a duniya ba sama da mutanen garin Bani, ji yakeyi ya tsanesu gaba ɗayansu, ya tsani komai nasu, baya so da fata da sha'awan komai nasu. ƙasar garin ma da yake tsaye a kai ya zuba mata ido ji yake tamkar ya ƙonata ta sauya launi daga farin yashi zuwa baƙin yashi.
A tsakiyar taron kuwa, da sauri al'ƙalin gasar ya jawo hannun Ba'ana da ya zaro wata asirtaciyar bulalar tsamiya, daga cikin randar bulalinshi sai wani motsi bulalar keyi tamkar tanada rai.
Bayan Jabeer al'ƙalin gasar ya kawoshi. Yana sake hannunshi masu busar al'gaita da sarewa suka farayi da ƙarfin su.
Lokaci ɗaya kuma ranar data take buɗe tarwal ta lumshe. Mutanen kuwa sai tasowa da ife-ife akeyi. Kallo kuma kab ya dawo kan farar kekyawar fatarshi da kekyawan baƙin tattausan gargasa yayi mishi ƙawanya, iya kyan fatarshi kaɗai ya ishi ɗan adam kallo. Da ƙarfi Jabeer ya taune lips ɗinshi, yana maiji tamkar zai hudasu sai ambaton sunan Allah yakeyi, babbar yatsar ƙafarshi ta dama yasa yana caka ƙasar garin, kana yatsunshi na hannun kuwa yasa babban yana zagaye kan ƴar manuniyarshi. A yadda yake jin zafi da ƙuna da baƙin ciki a cikin zuciyarshi ya tabbatar babu wani abu da za'ayi mishi a yanzu yaji zafinsa fiye dashi, to me za'ayi mishi mai zafi sama da tsiraiceshi da akayi.
Ba'ana kuwa cikin dariyar mugunta da sautin amo mara daɗin ji, ya taƙar-kara ya ɗago bulaliyar asirin nan, da iya ƙarfin shi ya zabga mishi ita a tattausar fatar tsakiyar bayanshi. Da ƙarfi su Jalal kab suka rumtse idanunsu. Lamiɗo kuwa wani irin kallo yayiwa Jabeer da yayi. Wani ir.....!
Biya darinki uku kacal domin jin wannan labari har ƙarshe. Dan Allah da Manzonsa kada ku fitarmin da littafina.
Wannan shafin nakune gaba ɗaya waɗanda suka karanta FREE PAGE🤝🏻😘🥰
By *GARKUWAR FULANI*Ido Laminu ya rumtse da ƙarfi. Ganin Sheykh Jabeer yayi wani irin tsayuwa na ingarman, jarumin namiji nitsuwa da kamala, sai lips ɗinshi dake motsawa a hankali yana ambaton Allah. Shi kuwa Ba'ana cikin tsantsar mugunta, ƙeda, da zalumci ya ɗago bulalar nan da azaban karfi ya zabgawa mishi ita a inda ya zabga ta forko. Wanda yasa gaba ɗaya mutanen wurin suka rumtse idanunsu. Especially Lamiɗo da tawagarsa, Shi kuwa Sheykh Jabeer, zuciyarshi ta rigada ta gama tafasa, idonshi baya ganin komai sai wani irin azabebben duhu, kunnuwanshi basa jin komai sai sautin muryar mahaifinshi da kuwa Umaymah. Da suke bashi umarnin cewa dole yayiwa Lamiɗo mubaya'a. Wani irin azaba mai girgiza ran mutun a jikinsa yakeji yana sukarshi har cikin ƙahon zuciyarshi, sai dai duk wani sihiri na jikin bulalar duk baya tasiri a jikinsa illa dai dafin kuna min kam tabbas yana jinsu. Barmuji wanda shine al'ƙalin gasar kuma mai irga bulalin. Da sauri ya rumtse idanunshi lokacin da Ba'ana ya tsulawa Jabeer bulala ta biyar waccee, a take jini ya fara tsastsafo duk inda ta konta.
Arɗo Bani kuwa da Bappa da Alhaji Haro da Alhaji Umaru, da Sarkin aska, da sauran dattawan garin da kewayensa wani irin fargaba ne da taraddadi mai firgitarwa suke ciki. Gaba ɗaya bakunamsu addu'o'in ne a ciki.
Laminu kuwa tuni yanata ɗaukar duk abinda ke faruwa a ƴar ƙaramar na'ura sa. Yanayi yana dariyar farin ciki.
Jalal kuwa da sauri ya rumtse idanunshi kana ya koma baya. Jamil kuwa cur-cur yake zubda hawaye ganin yadda jini ke tsastsafo wa, a tsakiyar bayan Hammansun. Haroon da kanshi tsoro ya rufeshi, yaji ranshi ya fara zargin anya kuwa bada biyu aka haɗa wannan gasarba.
Muryar Barmuji ce ta cika wurin gaba ɗaya da alamun tsananin tausayawa yace. "Goma!". Alamar anyi mishi bulala ta goma kenan. Shi kuwa Sheykh Jabeer Idonshi a buɗe suke, sai dai basa ganin komai sai duhu na tsantsar baƙin cikin abinda sashi yayi cikin bainal nasi a sashi tsayuwa da ɗan kampai, Idanun nashi suna buɗe ras. Launin su kuma ya sauya daga farin zaiba, zuwa jazir tamkar wanda maciji ya watsa dafi a cikinsu. Gaba ɗaya fararen faratun yatsun hannunshi sun rine sunyi jazir tamkar wanda aka ƙunsawa jan lalle. Ji yakeyi tamkar tsikarinshi akeyi da bakin allurai. Tabbas duk da bai san dafin kunama ko macijiba, ya gane cewa akwai gubar dafin wani abu a jikin bulalin da ake tsula mishi tamkar za'a zare ranshi dasu. duk ta inda hudar gashi yake a jikin shi, ji yakeyi tamkar ana soka mishi ƙarin kunamai.
Bukar kuwa, wani irin murmushin farin ciki yakeyi, ji yakeyi kamar ya fito ya taka rawa dan farin cikin ganin halin da jikan Sarki ke ciki.
Muryar na rawa Barmuji yaci ga da irge. "Goma sha ɗaya! Sha biyu! sha uku! sha huɗu! sha biyar!!!." Cikin sauri Haroon ya iso inda suke, hankali a tashe ya kamo hannun Barmuji cikin sanyi yace. "Kai kasheshi zakuyi ne? Bulalin har nawa ne za'ayi?". Cikin rawan murya Barmuji yace. "In sha Allah bazai mutuba, bulali Hamsin za'ayi a ƙa'idar gasar, ba abinda zai sameshi tunda har gashi ya juri bulali 15 wanda a tarihin gasar Ba'ana babu wanda ya taɓa jurar koda bulala biyar ne". Da ƙarfi Hashim ya zaro ido tare da cewa. "50 wannan ai zalumci ne". Da sauri Galadima ya miƙa ya nufi tsakiyar taron ganin Jalal ya nufi inda suke gadan-gadan bisa dukkan alamu kamo hannun ɗan uwan nashi zaiyi yaja su tafi. Da sauri Galadima ya kama hannunshi cikin ɗaga murya yace. "Kai Jalaluddin ina zakaje?". Cikin faɗa yace. "Zan ja ɗan uwana mu tafi, in ku bakwa sonshi bakwa da buƙatar shi, mu muna sonshi munada buƙatar shi, a rayuwarmu domin mu dai shine farin cikinmu, shine silar zamanmu cikin masarautarku, da tuni kun koramu tamkar karnuka, shine kuka haɗa Deel a kashe mana shi, to kuji ku sani zamu bar muku masarautarku in dai ganinmu ne bakwa tson yi." Cikin faɗa Galadima yaja hannunshi yaje ya ajiyeshi gaban Lamiɗo. Yana mai jin tausayin yaran. Da ƙarfi Barmuji yace. "Ashirin da biyar! Ashirin da shida!". Zuwa wannan lokacin gaba ɗaya jikin Al'Sheykh Jabeer Habeebullah yayi ruɗu-ruɗu. Tuni farin boxes dake jikinshi ya cika da jinin dake gangarowa ta bayansa da cikinsa, inda bulalin suke taɓawa duka. Babbar yatsarshi ta ƙafar damanshi da yatsun hannunshi kawai yake motsawa, wanda suke nuna alamun yana nan da rai daram da kuma haiyacinsa. Bayan wannan babu abinda yake motsawa a jikinshi, Cake ƙasar garin yakeyi da yatsar kafar tashi. yatsun hannunshi kuma, motsasu yake yana tasbihi dasu, wanda shima cikin zuciyarshi yake ambaton Allah dayi mishi kirari da kyawawan sunayenshi. Zafin da yakeji a jikinshi tabbas ya wuce zaton mai zato. Taune lips ɗinshi na ƙasa yayi da fararen haƙoranshi tamkar zai hudasu, sai dai har cikin ƙashin haƙoran nashi yake jin azabar dafin dake cikin wadannan bulalin masu masifar siddabaru, sai dai babu wani siddabaru da yayi tasiri a kanshi ko a jikinsa domin shi Allah ya riƙe, Ba'ana kuwa tsafi ya riƙe. Wannan gasace tsakanin gsky da ƙarya, bawai gasar caɗi bane kamar yadda mutanen wurin ke kallo. Haka yasa duk da safin wannan bulalin sam basu kai zafin da yakeji a ranshi na sashi ya tsaya gaban dubban al'ummar garin da ɗan guntun wonɗo a jikinshi ba. Allah ya sani shi mai kunya ne, kuma shi mai suturce kanshine, shida kanshi yana jin kunyar kanshi da kanshi. Baya zama haka ko a ɗaki sabida yana tuna in mafa ya kaɗaice yana tare da Raƙib da Atib Mala'iku makusantan ɗan adam, wanda in ka bar tsiraicinka ma su kauda ido sukeyi daga gareka. Shiyasa shima yake kauda ido daga kan kanshima bare wani. Allah ya sani babu wani abu da aka taɓa yi mishi a duniya ya ƙona mishi rai sama da wannan abun. Tabbas da an barshi hakama, yafi jin zafin hakan sama da waɗanan bulalin. A ranshi yake wani irin kuka mai cin rai yana mgnar zuciya. "Anci min zarafi an wulaƙantani an tozarta ni a gaban waɗan mutanen da wasun cikinsu zindigan kafuraine. An barni tamkar mara kima da galihu, wannan shine iya maƙurar zalumcin da akayiwa rayuwata a karo na biyu". Sam baya jin zuciyarshi tanada raunin da zai iya zubda hawaye kan bulalin nan shiyasa ko zafinsu bai zame mishi abin zubda hawaye ko ihu da bakiba ko gudu ko wani motsi.
Zuwa yanzu hankalin kafuran ƙabilar ɓachama ya yi masifar tashi domin wannan shine karo na forko a rayuwar tarihin Ba'ana da ya zana mutun bulalin shaɗi har talatin da takwas baiyi ihuba bai zubda hawayeba, bai sumaba, bai faɗi ba, bai guduba. Kai wannan abun yayi tsamari wannan wanne irin mutum ne, anya kuwa mutun ne ko al'jan.
Ya Salmanu kuwa, cikin tsanani kuka cur-cur da hawayenshi sabida yasan azabar da Sheykh Jabeer yakeji. Juyawa yayi ya fuskanci gabas, sujjada yayi tare da fashewa da wani masifeffen kuka mai cike da rauni murya na rawa yake cewa. "Ya Haiyu ya ƙaiyum, ya ziljalali wal ikram. Ya Allah ka ƙarawa wannan bawa naka dauriya da jarumta, ya Allah ka bashi ikon jure wannan azabar, ya ubangiji ka sanyaya mishi masifun dake jikin waɗanan bulalin, ya ubangijin taliƙai ka hana wannan mugun mushirkin bawa naka samun nasara, ya Allah ka kare musulminka kan wannan kafurin matsafin da baya salla". Kuka sosai ne yaci ƙarfin Ya Salmanu.
Bappa ma wani irin raunine ya rufeshi tabbas kowa zaiyi tunanin Jabeer yana jin azabar duniya. Sai dai kasan cewarsa Jarumin namiji haka yasa babu wata alama da ya nuna na yana jin zafi ko ciwo. Sosai kuwa hakan ya tada hankalin kafuran.
Lamido da Galadima kuwa kallon juna sukayi tare da yin murmushi irin nasu na manyan fada, murmushi ne mai manufofi.
Jalal kam kife kansa yayi a cinyar Lamiɗo ya saki kuka mai sauti.
Haroon ma hawaye yakeyi zuwa yanzu. Hankalin duk tawagar Lamiɗo yayi masifar tashi, ganin yadda wani irin azabebben zufa ya tsinkowa Jabeer tun daga tsakiyar kanshi, zufar nan take gangarowa har kan jikinshi gaba ɗaya, saida ya jiƙe yayi jilak tamkar an kwaza mishi ruwa bokati ɗaya. Wani irin karkarwa jikin shi, ya farayi yana tsuma yana ɓari, gaba ɗaya jikinshi karkarwa yakeyi. wanda duk fulanin wurin suka fahimci cewa tabbas. Zai iya cinye gasar zai kuma iya faɗuwa.
Shi kuwa Sheykh Jabeer daga can cikin naman jikinshi yake jin jikinshi na rawa tamkar mazari. Zuciyarshi kuwa wani irin duka takeyi, wanda muddin kana kusa dashi zakaji yadda take bada sautin harbawa.