Kenza eBookz

Garkuwa complete Novel - Chapter 18

Garkuwa complete Novel - Chapter 18

Garkuwa complete Novel Chapter 18: Garkuwa complete Novel Chapter 18. Hankalin Ba'ana yayi ƙololuwar tashi, ganin har yayi mishi bulala ta arba'in da…

4,487 words

Hankalin Ba'ana yayi ƙololuwar tashi, ganin har yayi mishi bulala ta arba'in da biyar. Baiyi ɗaya daga cikin ababen da zai hanashi cin gasar ba. Ganin hakane ya juya a fusashe, bulalin hannunshin ya wurgar kana ya sunkuyo kam ranɗar bulalin tsafinshi, bulali biyar ya zaro, ya haɗa su ya damƙesu cikin hannunshi. Cikin azaban ƙarfi ya ɗagosu ya yarfawa Jabeer su a tsakiyar kanshi. Wani irin azabane ya ziyarci ƙoƙon ranshi, wanda hakan yasa yaji wani irin fitsarin azaba yana cika mishi mara. Jinine ya tsinko ta kafaɗunshi, yana bin cikinshi, bai gama jin azabar waɗannan ba ya kuma zarma mishi su a cinyoyinshi. Da sauri Arɗo Bani ya miƙa tsaye daga sujjadar da yayi jin ihun mutane, suna cewa. "Ka karya dokar gasa ba'a haɗa bulali biyuma bare biyar kasheshi zakayine. Cikin wani irin isa ta jarumta da jinin sarauta Sheykh ya buɗe kwayar jajayen idanunshi, Barmuji da yayi kansu da nufin kama hannun Ba'ana ne, Ya ɗagawa hannunsa alamun daka dakatarwa alamun ya tsaya kada ya iso ya bar Ba'ana yayi komai ba komai. Cikin tsananin mamaki duk al'ummar wurin suka zuba musu ido ganin jarumta ziraran miraran tana tsaye da sawunta. Shi kuwa Barmuji cikin rauni yaci gaba da nufosu yana cewa. "A a Sheykh bazan barshi ba, ai ya karya ƙaida da dokan gasa". Ya ƙarashe mgnar yana isowa inda suke. Cikin tsananin takaici da firgicin ganin faɗuwa a karo na forko na rayuwarshi, Ba'ana Ya zargawa Barmuji bulalin da ƙarfi. Wani azabebben ihu Barmuji ya narka tare da fara tsalle yana yarfa hannunshi yana zagaya wurin hawaye na shatata mishi sabida azabar da yakeji, cikin ihun azaban bulalin da aka yarfa mishi sau ɗaya, fitsari na tsiyaya a sawunshi yace. "Arba'in da takwas!". Ta gabanshi ya dawo ya shauɗa mishi na arba'in da tara, wanda yasa Jamil yin tsalle yazo gabanshi cikin kuka yace. "Kasheshi zakayi ne?". Cikin tsananin azabar da yakeji ne ya buɗe jajayen idanunshi ya kalli ta inda yaji muryar Jamil. Hannunshi yasa ya ture Jamil gefenshi. Shi kuwa Ba'ana wani irin ihu yayi tare da buga tsalle yayi sama kana ya zabga mishi bulala ta hamsin kuma ta ƙarshe. Wani irin dogon numfashi Jabeer yaja tare da buɗe idonshi kan fuskar Lamiɗo daya iso hango dishi-dishinsa yana nufo inda suke. Wani irin ihu da karaji Ya Salmanu ya kurma da azaban ƙarfi, Wanda ya haɗe ya gauraye da busar sarewa da al'gaita da dukan gamgar jami, aka saki a tare. Wani irin sowa da ihu da hargowane ya cika illahirin gaba ɗaya Rugar Bani, Wanda mutane fulani suketa rawan farin cikin jarumtar Jabeer, Arɗo Bani da sauran dattawan rugar kuwa gaba ɗaya sujjadar godiya sukayi wa Ubangijinmu sarki gagara misali. Gaba ɗaya an zagaye Sheykh Jabeer. Wanda shi kuma ya juyawa Haroon baya alamun yasa mishi suturarsa. Da tsananin rawan jiki. Haroon ya wore al'kyabbar, ya zura mishi ita kan jikinshi daketa zubda jini. Yana jin Haroon ya saka mishi Al'kyabbar ya ɗago kafaɗunshi ya gyara zaman al'kyabbar. Jiki na rawa yasa hannunshi ya kama gefe da gefen bakin al'kyabbar ya hadesu a jikinshi ya suturce kanshi ya kare kanshi. Barmuji na shirin kamo hannunshi yayi maza. Ya ɗaga mishi hannunshin kana ya juya ya nufi inda motoncinsu ke jere. Jalal da na ganin haka yayi maza yayi gabanshi. Marfin motar ya buɗe mushi tun kafin ya iso.

Cikin taron kuwa, tuni Ba'ana da matasan ƙabilar ɓachama, sun ɗauki ranɗar bulalin tsafinshi sun nufi Bonon da tarin baƙin ci dan ganin Sheykh Jabeer bai faɗi gasarba, kuma ga mutanen fulani daketa yi musu dariya da ihun rashin nasarar su. Hakan yasa suka tafi dan sun sani a ƙa'ida sai Jabeer yayi jinya ya worke da azabar da Ba'ana ya shayar dashi kafin ya dawo ɗaukar fansa.

Cikin taron kuwa cikin kukan rauni Arɗo bani ya rusuna gaban Lamiɗo da tawagarsa murya na rawa yace. "Sauran ɗaukar fansar da zaiyi a duk sanda ya worke a duk sanda yaga dama, fatana kuyi shirya bulalin tarihin masarautarku, domin ramuwa akan wancan taƙadirin da baya jin koda harbin bindiga baya shigarsa. Ina yakun farin cikin nasarar da Jabeer yayi a yau, ina kuma fatan yayi nasara a ramuwar da zaiyi a wannan kuma in yayi nasarar mu zaku taya farin ciki, ko ba komai zamu rabu da wancan taƙaɗirin." Cikin wani irin tarin ƙuna Lamiɗo ya gyaɗa kanshi. Kana ya juya yayi gaba Dogari na rike masa da laima ɗanzagi na cewa. "Gyara kimtsi, a bada hanya, sarki ya barku lfy". Waziri da Wambai Ɗan buram Ɗurɓi Da iya duk suka mara mishi baya.

Hakama Arɗo Bani da sauran dottawan wajen sukayo musu rakiya. Sheykh Jabeer kuwa. Yana tafe Galadima na biye dashi a baya. Haroon kuma na gefenshi. Suna isa yasa kai ya shiga cikin motar, kana Haroon da Hashim suka mara mishi baya, da sauri sarkin mota ya maida ƙofar ya rufe. Kana ya buɗewa Lamiɗo motar, gefen bayansu Jabeer ya shiga, kana Galadima ya shiga kusa dashi, sannan aka rufe motar saura duk kowa ya shiga motar da yazo ciki. Sannan duk suka rurrufe motocin.

Kana suma Fadawa da dogarai suka shiga nasu motoci biyun. Ɗaya tayi gaba, sauran motocin suka bisu a baya, ta Lamiɗo na tsakiyarsu, kana ɗaya ta fadawan ta biyo bayan uku da ke bin bayan ta Lamiɗo.

A haka suka ja motocin a jere a jere suka bar cikin Rugar Bani.

Cikin Rugar kuwa kowa ya tafi cikin al'ajabi da farin ciki. Da yawa gani sukeyi kamar dai Jabeer ba mutun bane.

Sauran dottawan kuwa, zama sukayi cikin fadar bayan sunyi sallan la'asar ne, Bukar yazo ya tsaya tsakiyarsu cikin rashin mutunci yace. "Kuyi kuka da kanku akan duk abinda zai faru gaba". Kafin ma su bashi amsa tuni ya juya ya tafi.

Su kuwa nan sukaci gaba da al'ajabi da tuanjidin Jarumtar Jabeer.

A cikin motocin kuwa, mutanen ko wacce mota da abinda kowa ke tunawa. Wani irin azabebben gudu sukeyi tamkar zasu tashi sama, sabida bin umarnin Lamiɗo wanda shi kuwa ya bada izinin gudun ne, dan ganin yadda Jabeer keta zubda jini, ga wani irin masifeffen karkarwa da jikinshi keyi.

Gudu sukeyi a 360 musamman ma da suka samu suka hau kan babban titin Shikan wanda zai sadasu da cikin babban birnin Ɓadamaya.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, wani irin karkarwa jikin shi keyi, idanunshi jinsu yakeyi tamkar zasu zazzago su faɗo ƙasa, sabida wani irin masifeffen azaba da yakeji. Ji yakeyi tamkar ya haɗiyi zuciyarshi sabida masifar fushi da harzuƙa da zafin rai, babban abinda ya tsananta fushinsa shine yadda yaga lokacin sallan la'asar ya gota musu, akan shirmen banza da wofi da zalunci an hanashi yin salla kan lokacin ta. Hannunshi yasa ya fizge rigarshi da ke hannun Haroon dake ta sa hiraminshi yana tare jinin dake zubomishi ta ƙeyanshi. Taune lips ɗinshi yayi tare da sa hannun shi, ya kama wuyan rigar cikin ƙarfi yaja ji kakeyi, Fasss sautin yagewar sabon saddan.

Ido suka zuba mishi gaba ɗayansu, Ya Hashim kuwa jiki narawa ya kira Dr Aliyu wanda yake ƙanine ga mahaifinshi da kuma Abbansu Jabeer ɗin.

A can baya kuwa inda Galadima dake zaune gefen Lamiɗo ne daya bashi umarnin ya kira sarkin gida ya sanar mishi ayi tanadin jinyar Shaɗi cikin gaggawa. Da sauri Galadima ya zaro wayarshi ya kira sarkin gida. Cikin tashin hankali yake mgna a woya bisa alama duk da sarkin gida yake mgn. "Ladodo, kayi maza yanzu ka sanarwa tsohon sarkin Shaɗin masarautar Joɗa yayi maza ya haɗa tsumin igiyar bulalin shaɗi, ya kaiwa Jakadiyarsu Jabeer, A shirya duk wani abun buƙata, domin Jabeer yana zubda jini sosai."

A can masarautar kuwa Sarkin gida yana jin haka ya miƙa ya nufi, sashin kananan sarakuna kai tsaye gefen Sarkin Shaɗin ya nufa, ya sanar mishi umarnin da aka bada, ai nan take Sarkin Shaɗin da sarkin Gida, suka shiga bayan sashin mai martaba Lamiɗo, inda bishiyoyin tarihi dana gargajiya da magunguna suke. Forko bishiyar Goruba suka fara sassaƙan jikinshi. Wanda shine babban makarin dukan shaɗun. Sai kuma suka haɗa da wasu tsirran,. Koda suka gama kai tsaye gefen Jakadiya da sauran ma biyanta suka nufa, Nan suka bata dukkan abinda suka ɗebo, suka kuma yi mata bayani. Kana sukace maza ta haɗa su ta dafa, Sauran kuma sai sun dawo Lamiɗo ya shiga ɗakin sirri ya ɗebosu.

Cikin tsananin tashin hankali da rawan jiki Jakadiyarsu ta amshi magunguna, ta nufi sashin Jabeer ɗin. Cikin gaggawa ta shige kitchin ɗin shi, ta fara harhaɗa magunguna tana dafawa.

A can cikin motar kuwa cikin tashin hankali Ya Hashim yayiwa Dr Aliyu duk bayanin abinda ya faru da halin da Jabeer ke ciki. Ya ƙara da cewa, a shirya komai na bashi taimakon gaggawa. Jin hakane yasa Dr Aliyu tada motar Ambulance wanda take nan cikin asibitin dake cikin makarantar nasu, tazo bakin asalin babban gate ɗin masarautar nasu. Kana ya kira babban abokinshi Dr Sanju wanda ba indiyene wani aikine ya kawoshi ƙasar, tuni suka iso bakin gate ɗin, cikin motar Ambulance ɗin suka shiga suka zauna tare da haɗa duk wani abu na taimakon gaggawa da za'ayi mishi.

A cikin motar kuwa, gaba ɗaya ya gama yage rigarsa ya fizge wonɗonma ya yageshi fata-fata. Ganin wani irin kallo da yayi Haroon ne, yasa Haroon yin maza ya matsa tare da yin mgnar zuci. "Ka gani ko Lamiɗo hegen tsoho kai ka dace ka zauna kusa dashi. Inma yagawarne ya yage ka". A zahiri kuwa fuska ya ɗan haɗe tare da cewa. "Kafa gama yaga kayanka yanzu nawane suka rage a jikina, naga ji kake kamar ka yagamu, yaseen to bamu muka kar zomonba". Dai-dai lokacin kuma, sarkin ƙofa ya buɗe musu ƙofar babban gate ɗin. Kana suka kutsa kai. Suna shiga ko parking basu gama dai-dai tawa ba Jabeer ya sa hannu ya buɗe marfin motar, ƙafarshi ya zuro woje, wanda ganin haka yasa Dr Aliyu ya fito da sauri. Sai dai kafinma ya fito tuni Jabeer ya fito cikin motar ya nufi asalin ƙaramin gate ɗin da zai sadaka da asalin cikin farfajiyar. Kusan a tare suka fito daga motocin gaba ɗayansu. Cikin tsananin tashin hankali Ya Hashim ke ƙwalla mishi kira, amman ina bai ko juyo inda sukeba. Baya kuma jinsu sosai sabida duhu da jirin da yake gani. Da gudu Haroon da Jalal Jamil suka biyoshi a baya cikin rauni Jamil ke cewa. "Hamma Jabeer dan Allah ka tsaya Baba Aliyu zai dubaka, kaga fa har yanzu jinin bai daina zuba ba." Ina ai baya tare dasu tafiya kawai yakeyi, ba tare da yasan inda yake jefa ƙafarsa ba. Ganin hakane Dr Aliyu ya koma cikin Ambulance ɗin ya jata ya nufi inda yake, sai dai tuni har ya shiga cikin asalin farfajiyar.

Haroon, Jalal, Jamil, Hashim, ɗan Barrister Kamal Sulaiman, da Imran, duk suna biye dashi a baya da dudu-gudu da sassarfa. Lamiɗo da tawagarsa kuwa, koma sukayi cikin motocin sukaja, suka nufi cikin gidan.

Shi kuwa Sheykh Jabeer tuni ya isa bakin side ɗinshi. Cikin tsananin rawan jiki da duhu ya kusa kanshi ciki. A babban falon ya samu Jakadiyarsu, tana ganinshi ta miƙe tsaye cikin tsananin tashin hankali ta tsaya ganin ya ɗaga mata hannunshi ɗaya, kana yasa hannunshi ɗaya kuma ya dafe kanshi. Cikin wani irin kerma yake wani irin taku da jan wani irin dogon numfashi ya nufi part ɗin shi. Yana shiga falonshi na musamman, su Haroon na shiga babban falon.

A nan su Jamil kan suka tsaya, shi kuwa Haroon da sassarfa yabi bayanshi. Yana shiga falon nashi ya hangoshi ya shiga bedroom ɗin shi. Ya kuma maida ƙofar ya rufe, kai tsaye bathroom ya wuce yana shiga wani irin duhu ya rufe idanunshi a hankali ya tafi...

A can Rugar Bani kuwa, kuwa Junainah har ta shiga kitchin ta sunkuyo zata ɗauki akoshin naman gasassun zabbin, sai kuma ta fito a guje. Kai tsaye inda ake gasar Shaɗi ta nufa, haka ta rinƙa kutsawa cikin taron, har ta isa gaba-gaba kusa da ya Salmanu, ganin irin dukan da akeyiwa wannan kekyawan mutumin data ganine yasata kuka da ihu. Kukanta ne yasa Salmanu kuka, ya kuma ja hannunta ya fito baya da ita. Hannunta ɗaya riƙene yaji yadda jikinta ke karkarwar kamar mazari, bayan yayi sujjadar ya ɗagone. Yace mata maza ta koma gida.

A haka ta koma tana kuka.

A inda ta bar Shatu dasu Rafi'a da Ummiy anan ta dawo ta samesu. Kai tsaye kitchin ɗin ta nufa, da sauri ta ɗauko akoshin ta fito ta nufi inda suke, cikin rawan jiki ta sunkuyo ta sauƙe musu akoshin ta ajiye a tsakiyarsu, kana itama ta zauna a kusa da Ummiy dake jingine da jikin bishiyar mangoro. Jiki na rawa tasa hannun ta janye fefeyin da aka rufe akoshin da shi.

Wani irin lumshe ido Rafi'a tayi, sabida wani irin ƙamshin daya buɗe hancinta, Ummiy kuwa ido ta zubawa akoshin tana jin yawun bakinta na tsinkewa, Shatu kuwa gyara zamanta tayi sabida wani irin azabebben ƙugin yunwa da cikinta yayi.

Cikin sanyi suka gyara zamansu gaba ɗaya, a hankali Shatu ta riƙe hannun Junainah cikin zubda hawaye tace. "Jeki wonke hannunki sai kizo, da plet da ƙaramin akoshi mu ɗibawa Bappa mu sawa Ummiy a plet ɗin". Cikin sanyi ta tura baki kana ta miƙe tsaye, gindin randunarsu ta matso, yar ƙaramar butarta ta ɗauka ta wonke hannunta, sannan ta nufi cikin madafarsu.

Tana shiga ta ɗauki ludeyi da ƙaramin akoshi kana da pilet sannan ta fito. Tana fitowa tazo ta zauna gabansu, ta miƙa Shatu, cikin sanyin jiki tace. "Bawa Rafi'a ta ɗiba musu, wlh jikina duka rawa yakeyi". Amsar pilet ɗin Rafi'a tayi ta fara ɗibawa Ummiy rabin zabuwa. Kana ta sawa Bappa gudar da romonta, Tana cewa. "Garkuwa yunwace fa, ace mutun ya wuni ya kuma kwana baici komaiba ya kuwa wuni ba abinda yaci ai dole kiji jiri, gashi yawan kukan da kikeyi ne yasa miki zazzaɓi." Ta ƙarishe mgnar tana rufewa Bappa nashi kana tace. "To muci". A tare suka saka hannunsu cikin akoshin. Junainah ce ta fara yago tattausan farin tsokar ƙundun zabuwar cikin haɗiye min yau ta kai hannunta bakin t....!

Dan Allah da Manzonsa kada ku fitarmin da littafina, in kinsan Zaki fitarne gaya min in baki kuɗinki, dan Allah.

By *GARKUWAR FULANI*Ta kai hannun ta, kusa da bakinta kenan Wani ƙaton gadamgare ya faɗo jikinta. Wani irin tsalle tayi tare da rauza ihu, ta faɗa jikin Aysha tuni tayi fatali da akoshin gasassun zabbin nan ya ɓare ƙasa kirib. A firgeci Ummiy ta yunƙuro tare da nufar inda suke, wanda hakan yasa tayi fatali da akoshin da akasawa Bappa zabbuwar da kuma take wanda aka zuba mata a plet ɗin ya ɓare cikin lallausan yashin garin.

Ita kuwa Junainah gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi, fizge-fizge takeyi tana ƙwaƙumar Shatu. Sabida ita ji takeyi kamar dai har yanzu ƙadangaren yana jikinta. Cikin kiɗima Shatu ta ruggume ta, tare da cewa. "Ke Junainah ki bar ihun ƙadangaren ma ya razana da ihun da kika kurma ya sauƙa ya tafi." Jin hakane yasa ta tashi zaune tare da zazzaro ido, Rafi'a kuwa dariya tasa tare da cewa. "Kai Junainah yaseen kin cucemu, kallifa yadda kikayi fatali da akoshin nan". Cikin sanyi Shatu tace. "Haba wannan abu dai Allah yayi ba raban mu bane, Ni dama can haka nan in naga naman sai inji zuciyata ya tsinke ashe ba rabanmu bane, da muncima da mun harar dashi.

Ita kuwa Ummiy jan hannun Junainah tayi kana ta zauna kusa da Shatu. A hankali ta jingina kanta da kafaɗan Shatu, Rafi'a kuwa miƙewa tayi ta shiga kitchin ɗin su. Abincin data dafa musu ta kawo musu. Ta ajiye gefe, sannan ta ɗauko tsintsiyar kwakwa ta share ta kwashi naman kab ta maidashi cikin babban akoshin, ta rufe, sannan taje ta wonke hannunta kana tazo ta zauna suka fara cin abincin.

A can cikin fadar masarautar Joɗa kuwa. Jin jiri na ɗibanshi ga duhu dake rufe mishi ganine ya sashi, tafiya a hankali tare da dafa jikin gini. A haka har ya isa bakin Jakuzin, A hankali ya zare al'kyabbar jikinshi, ya wurgar dashi can gefe, kana ya tura ƙofar ya Jakuzin ya shiga, tsayuwa yayi tsakiyarshi, hannun na rawa ya buɗe shawan ruwan ɗumi. Wani irin numfarfashi wahala ya sauke lokacin da yaji ruwan ɗumi yana ratsa raɗi-raɗin azabobbun bulalin da yasha. Wasu irin hawaye masu masifar zafine yaji suna tsastsafo mishi cikin jijiyoyin kekyawan idanunshi, sai dai basu kai ga damar samun zobowa ba. Wani irin tsuma duk illahirin sashin jikinshi ya fara, zafin ruwan yakeji har cikin ƙoƙon ranshi, wani irin karkarwa haƙoranshi sukeyi har suna dukan juna, kat-kat. Kanshi ya sunkuyar tare da buɗe idanunshi a hankali, ruwan dake gangarowa daga jikinshi yana bin ƙasa in da zai gangara yake kallo, sabida zakace jinine ba ruwaba, Sabida yana wonke mishi jinin jikinshi. Haka ya tsaya a ƙasan ruwan ɗumin har saida yaga jinin ya daina zuba kamar da fari. Sannan yasa hannunshi ya ɗauki daddaɗan sabulun wankan shi, ya fara murza sabulun taki wani sashi na jikinsa, wani irin wahaltaccen ƙara yayi lokacin da sabulun ya ratsa inda ya farfashe a jikinsa, cikin rauni yace. "Wayyo Allah na! Wayyo Mamey na zan mutu, zafi zai kasheni tun kafin cikar burina." Ci gaba yayi da murza sabulun tare daci gaba da cewa. "Wayyo Umaymah wayyo Ummi". Sai kuma ya taune lips ɗinshi kana ya rumtse idanunshi yayi ta murza sabulun tako ina yanayi ruwan ɗumi na dukanshi. A haka yayi wonka ya wonke duk wani jini dake jikinshi yayi fes. Al'wala yayi, kana ya fito cikin Glass ɗin sannan ya ɗauki wanni tattausan baby towel fari ƙal ya ɗaura a ƙirjinshi ya sauƙo har zuwa guiwansa. Hannunshi yasa ya murza farin boxes dake jikinsa wanda ɗazu yake jiƙe da jini yanzu kuma yayi fari tas. Murza boxes ɗin yayi har ƙasa, kana ya ɗaurashi kan al'kyabbar jikinshi da ya cire, Cikin Woshing mashine yasasu, Kana ya fara yin taku a hankali ya iso gaban drower'n glass ɗin dake cikin bathroom ɗin. Wani tattausan gajeren wondo fari tas mai ratsin sky blue ya saka, gajeren wondon yazo mishi har guiwarsa, kuma mai ɗan faɗine, Wata tattaunawar riga mai guntun hannu wacce itama farace da ratsin Sky blue, ya saka, kana ya zaro wata ɓakar tattausar jallabiya doguwa har ƙasa tazo mishi daya zurata, Wani hulan taɓa kaji Hadisi ya kifa kan suman kanshi dake da ɗan damshin ruwan ɗumin.

A hankali yake taku sabida zuwa yanzu wani fitinenne zazzafan zazzaɓi yakeji. Jiki na rawa ya fito, bisa sallayarshi dake shimfiɗe a wata ƴar kusurwa yaje ya hau. Yana hawa kan sallayar ya fuskanci gabas, yaji zuciyarshi tayi wasai, baya tuna komai, baya kuma jin ciwon komai a jiki da zuciyarshi sabida kushi'i da tawakkali da kyutata ibada baya jin komai sai hasken farin cikin ibada. Kabbara ya tada tare da niyar sallan la'asar daya mannata bisa laruri ya makarar dashi.

A falonshi kuwa, hankalin Haroon ya tashi yana nan tsaye bakin ƙofa yana ta magiyar ya buɗe mishi, bai saniba shi yana can har cikin bathroom ɗin shi. Yana nan tsaye, mai Martaba Lamiɗo da Galadima suka iso tare da Sarkin Shaɗi. Cikin sanyi yacewa Lamiɗo. "Ya shiga ciki kuma ya rufe ƙodar ta ciki, inata kiranshi baya amsawa.

Murmushi Lamiɗo yayi kana, yacewa Galadima. "Muje". Kusan a tare suka fito falon. Suka zauna, kana ya kira Abba, yace yazo yasa ɗanshi ya buɗe musu ƙofar.

Jin hakane yasa Abba tahowa da sauri.

A can babban falon kuma. Cikin damuwa Jamil ya labartawa Jakadiyarsu da Aunty Juwairiyya abinda ya faru. Ga mamakinsu sai sukaga Jakadiyarsu tayi wani ƙayataccen dariya cikin sakekkiyar murya tace. "Alhamdulillah wannan shine abinda muka daɗe muna jira tsowon shekaru da dama. Kuma jinyarsa abune mai sauƙin". Cikin ruɗani Jalal yace. "Ummi kuka daɗe kuna jira kuma?". Kai ta jinjina mishi, kana ta miƙe ta nufi kitchin dan harhaɗa aikin da akasata.

A nan Abba yazo ya samesu. Jalal na ganinshi ya kauda kanshi. Hakama Jamil Imran kuma bayanshi yabi suka nufi side ɗin Jabeer ɗin.

A falo ya samu iyayen nashi, Cikin girmamawa ya rusuna yayi Lamiɗo Barka da yammaci kana ya matso kusa da baƙin ƙofar Bedroom ɗin Jabeer cikin ɗaga sauti yace. "Muhammad! Muhammad Jabeer! Jabeer!! Jabeeey!!! Ka taso maza kazo ka buɗe min ƙofar nan ina jiran ka".

Jabeer kuma da yanzu yake raka'ar ƙarshe, sam hankalinshi baya ga jin kiran Abbanshi domin a yanzu yana gaban Ubangijinmu ne.

Haroon kuwa wayar dake kunnenshi ya gyara riƙewa cikin shaƙiyancinsa yace. "Uhumm Umaymah ke dai kicewa Sarki Jalaluddin da Sarki Abubakar baban Daddy na, suyiwa masarauta Joɗo gudumowar suturu. Domin yau dai ran ƴan maza ya ɓaci, nasan sai ya yayyage kab wani abu mai yaguwa a masarautarsu". Cikin wani irin farin cikin wannan labarin da Umaymah taji tayi kekkyawan dariya tare da cewa. "Haroon yayan naka kakeyiwa tsiyako?". Cikin tura baki yace. "Allah ko Umaymah kecema kike sawa Jabeer yana rainani wai yayana". Da sauri tace. "To ba yayanka ɗin bane?". Cikin yamutsa fuska yace. "Yayan kwana arba'in, shiyasa yake min kallon kobo biyu da sisi, sabida yana jin kuna ce mishi yayana, wani lokacin har cemin yaro yakeyi dan tsabar son girma da manyance, Ni mamaki da yake bani kawai sai in zuba mishi ido in naga yana min faɗa kamar wani ɗan cikinsa". Murmushi Umaymah tayi kana, tace. "Gobe zuwa jibi in sha Allah ina nan zuwa Masarauta Joɗo, sabida zanzo in lallashi ɗana nasan yayi zazzafan fushi tunda yaƙi kula Dr Aliyu ma". Daga nan sukayi sallama.

Shi kuwa Sheykh Jabeer saida ya isar da sallameshi yayi addu'o'in shi Kafin ya tashi a hankali ya nufi bakin ƙofar sabida zuwa yanzu zanan bulalin sunyi tsami ga zazzaɓi daya mishi rubdugu. A hankali ya murɗa key ɗin ƙofar ya buɗe ta, kana ya juya ya koma kan gadonshi, sabida rawa da jikinshi keyi na zazzafan zazzaɓi da wahala.

Yana konciya ya lumshe idonshi tare da fara karanta Suratul Khaf kasancewar yau yammacin jumma'a ne.

Su kuwa a falo suna jin sautin buɗe ƙofar, suka zubawa ƙofar ido ganin shiru bai fitobane yasa.

Galadima da Haroon suka nufi cikin ɗakin. Jim kaɗan da shigarsu Galadima ya fito da sauri ya kira sarkin Shaɗi, da Lamiɗo kana da Abba.

A tare suka nufi cikin ɗakin, suna shiga Haroon ya fito. Babban Falon ya koma ya nufa yana kiran Jakadiyarsu da sunan da suke kiranta. "Ummi! Ummi!!". Da sauri ta fito kitchen ɗin riƙe da filas da kofuna, sai kuma wani ɗan kwarya mai kyau ruwan ciki na tururi.

Da sauri ta miƙa mishi tare da cewa. "Yauwa Haroona gashi kai musu da sauri". To yace kana ya amsa ya juya ya koma, can cikin ɗakin Jabeer ɗin.

Zaune suke gaba ɗayansu, shi kuma yana konce ya duƙunƙune cikin wani jibgegen blanket mai masifar kyau da taushi. Sai karkarwa yakeyi tamkar mazari, Cikin sanyi Lamiɗo ya ɗan janye borgon tare da cewa. "Jabeer!". Duk da azaban zafin da yake ciki, bai hanashi buɗe idonshi ba, wani irin mugun kallo ya watsawa Lamiɗo, murmushi sukayi baki ɗayansu kana cikin lallami Galadima yasa hannunshi ya kamo nashi cikin sanyi yace. "Jabeer tashi ko? Tashi kasha mgni". A kufule yace. "Bazan shaba ku barni in mutu tunda hakan shine fatanku". Da sauri Abba ya kauda kai tare da yin wani faffaɗan murmushi kana, ya juyo ya kalleshi cikin bada umarni yace. "Muhammad tashi. Maza tashi kasha mgni". Kanshi ya ɗan gyaɗa kana a hankali ya fara yunƙirin tashi zaune. Ganin hakane Haroon yayi saurin taimaka mishi ya tashi zaune. Idonshi ya rumtse sabida ji yake kamar har cikin ƙasusuwan jikinshi ake tsikara da bakin allurai gashi duk inda hudar gashi yake a jikinsa sai ya ɗan tasa kamar wurin da cinaka ya ciza. Cikin tarin kula da wani mashahurin farin ciki, Lamiɗo da kanshi ya amshi haɗin maganin da sarkin Shaɗi yayi mishi a wani ma dai-dai cin kofi.

Hannunshi yasa ya amshi kofin kana ya kaishi bakinshi, fuska ya kwaɓe sabida gafin mgnin da yaji a jikinshi. Cikin bada umarni Abba yace. "Ka shanye duka". Ido ya rumtse kana ya kafa kanshi ya shanye shi tas. Miƙa musu kofin yayi, kana ya amshi wani kofin da Abbansu ke miƙa mishi, Shima shanye shi yayi tas. Yana miƙa wa Lamiɗo kofin. Ya fara wani irin gyatsa mai ƙarfi, gyatsan a jere a jere. Cikin sanyi Haroon yace. "Sanno my broz". Ina babu halin amsawa dan gyatsan ya tsananta, wani irin zufane ya keto mishi daga tsakiyar kai har kan babbar yatsarshi. Wani irin murɗane ya fara ɗibanshi tamkar zai tsinke mishi ƴaƴan hanji. Cikin wani irin zabura ya fara wani irin yunƙiri. Sai gashi yanata kela wani irin baƙin amai akan tattausan blanket ɗin nan. Murmushi Sarkin Shaɗi yayi tare da kallon aman da kyau kana ya juya ya kalli Lamiɗo da Abba yace. "Da dafin kunamai yake tsuma bulalinshi, ga nan dafin yake amayarwa." Murmushi Galadima yayi tare da cewa. "Uhumm kaji mugun banza ko". Shi kuwa Abba ido ya zubawa Jabeer ganin yadda yaketa kela amai, fuskarshi nan tayi jazir, jijiyar kan goshinsa nan ta tashi ta miƙe samɓal. Haroon kuwa tallafeshi yayi yanata ce mishi sannu.

Sai dai yayi kusan 30 minutes yana kwara amai kafin ya koma ya jingina da jikin Haroon yanata wasu irin zafafan numfarfashi tare da lumshe idonsa. Da sauri Lamiɗo yasa hannunshi ya tattare blanket ɗin ba tare da aman ya ɓata ko maiba. Ya dunƙuleshi ya miƙa wa sarkin Shaɗi.

Da sauri Sarkin Shaɗi ya miƙa Abba wani butan duma. Sannan ya amshi borgon. Shi kuwa Lamiɗo Haroon ya kalla tare da cewa. "Cire mishi wannan rigar". Da sauri Haroon yace to kana ya fara kiciniyar cirewa mishi jallabiyar. Duk da yana galabaice saida ya ɗan ja tsaki tare da ture hannun Haroon cikin muryar dake baiyana a wahalce yake yace. "Bana so ku barmin rigata". Hannunshi Abba ya buge tare da cewa. "Bakinka bazai mutu bako". Shiru yayi yana gani Haroon ya cire mishi rigar cikin murmushin da ganin jarumta da ƙarfin hali irin na Jabeer Galadima yace. "Cire wannan ta cikinma". Ba musu ya bari Haroon ya cire mishi rigar, Wani irin zaro ido Haroon yayi gani duk jikinshi yayi shatin zanen irin manyan kunama nan". Lamiɗo da Galadima da Sarkin Shaɗi kuwa murmushi sukayi tare da haɗa baki wurin cewa. "Uhum dafin ya gama fita, cikin jininshi." Abba kuwa hannun ya haɗa ya miƙa wa Lamiɗo dake mishi alamun zai zuba mishi abu a hannun. Wani haɗin mgnin ya zuba mishi cikin tafin hannunshi. Murzawa yayi kana, ya shafa a duk jikin Jabeer.

Wani irin sassanyan ajiyan zuciya ya sauƙe tare da lumshe idonshi. sabida wani irin sanyin da yaji yana ratsashi har cikin ƙasusuwan jikinshi. Tuni wani bacci mai fitinenne daɗi ya kwasheshi.

Nan suka gama yi mishi komai. Kana suka fita, Dr Aliyu kuwa da Ya Hashim suka shigo bisa umarni Lamiɗo.

Drip and injections Dr Aliyu ya ɗaura mishi tare dasa ruwan alluran a cikin ƙarin ruwan da akeyi mishi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull