Kenza eBookz

Garkuwa complete Novel - Chapter 23

Garkuwa complete Novel - Chapter 23

Garkuwa complete Novel Chapter 23: Garkuwa complete Novel Chapter 23. Ita kuwa Shatu tana haurawa sama. Ido take ɗagawa ta duba sunan Office da mai Office…

4,478 words

Ita kuwa Shatu tana haurawa sama. Ido take ɗagawa ta duba sunan Office da mai Office ɗin Office na forko taga musulmine haka yasa ta kutsa kai ciki. Zaune yake babu kowa sabida duk majinyatan sun tafi. Wasu an duba su, wasu kuma korarsu akayi da cewa yau half day ne, sabida haka su tafi. Da mamaki ya ɗago kanshi jin an shigo mishi Office babu sallama. Da sauri yace. "Waye?". Sabida cikin shigar yan matan larabawa take. Arabian gawd ne mai masifar kyau da taushi a jikinta wanda samanshi yake a dai-dai jikinta ƙasa shi kuma yake a buɗe, wasu irin duwatsune a jikin rigar tun daga sama har ƙasa sai wal-wali sukeyi suna ɗaukar ido. Tayi rolling kanta da ɗan kwalin rigar fuskarta ta fito ras a ciki. Wasu takalmi Golding color ne masu ɗan tudu dai-dai misali sai Ƴar ma dai-daiciyar hand bang mai masifar kyau shima Golding color ne, sai wayarta ƙirar iPhone 11. Fuskarta babu kolliya sai dai duk da haka bai hanata yin kyau ba gashin girarta ya konta lib-lib. Sai dai kuma ta rufe fuskar da tattausan Niƙab sai dai bashi da duhu sosai. To wannane ya hana Dr Salim ganin fuskanta, ita kuwa Shatu cikin tsananin ɓacin rai da zafin tozarcin da akayi wa yan uwanta tace. "Dr Salim". Cikin Mamaki yace. "Na'am". Yatsarta tasa tana nuna mishi maraba da baƙi ta wondon shi, cikin rauni tace. "Dr Salim na tabbatar kai musulmine, kuma nasan kasan cew manzon Allah yace shi musulmi ɗan uwan musulmine! Shin ko ka mance hakane, da ka kasa taimakawa yan uwanka musulmai da kafurai sukayi musu rauni akazo aka watsar dasu a nan kuma kuka ƙi dubasu meyasa, ko dan kawai sun kasance fulanin dajine laifinsu?". Cikin sanyi Dr Salim yace. "Wallahi umarni ne ba'a bamuba daga sama". Cikin tafasar zuciya tace. "Umarni wanne irin umarni kuma zaku jira bayan Allah da Manzonsa sun baku dukkan dama da umarnin taimakawa ɗan uwanku musulmi muddin kunada dama". Miƙewa tsaye yayi tare da cewa. "Dim ɗinmu ne ya hanamu dubasu". Cikin kufula tace. "Kan kafurar uwarshi! wato a cikin asibitima sai an mana ƙabilan ci, dan Allah Dr kuje ku taimakawa bayin Allancan".

Cikin jin ƙarfin guiwa ya juya, ya fita, ya nufi can. Ita kuma haka ta rinƙa bin duk Office ɗin da taga na musulmi ne tana shiga.

Tawagar Lamiɗo kuwa suna isa baƙin wani tamfatsetsen Office Sheykh Jabeer, ya ɗan kalli Lamiɗo tare da cewa. "Ni bari in shiga office na, ko mutun biyar in duba kafin ku gama zagayawa". Cikin gamsuwa da hakan Lamiɗo yace. "To bisimilla". Nan ya nufi babban barandar da Nurses suke tare a wurin maza da mata. Jamil kuma na biye dashi da System ɗinshi a hannunshi. Hakama Haroon ya biyoshi.

Nurses ɗin kuwa suna hangoshi duk suka mimmiƙe tare da cewa. "Sir barka da zuwa". Barka dai yake ce musu tare da ratsawa yana wucewa. Su kuwa sun taru a wurin ne dan tawagar Lamiɗo na wucewa su sauƙa ƙasa su duba Fulanin nan kamar yadda Dim ɗinsu ya basu umarni sabida kada Lamiɗo ya gansu a yashe a ƙasa yasan abun bazai mishi daɗi ba. Suna ganin ya shiga Office ɗin suka juya da nufin zasu tafin sai kuma suka tsaya jiyo muryar Shatu na cewa. "Ku tsaya ina kuma zakuje? Baku da aikin yi ko? Amman da yake ba taimako ne a zuƙatankuba kun bar bayin Allah a wulaƙance ko?". Cikin masifar Nurses da su ba komaiba sai iya ciwa mutane zarafi a hatsale tace. "Ke kuma waye". Kallonta Shatu tayi sama da ƙasa tare da kallon rubutun dake saman aljihun rigarta ganin sunan arniyace ga kai da gashin doki ga uban faratu kamar na jaki yasa taja tsaki tare da cewa. "Banyi da keba, da masu hijabi nake mgn". Yadda tayi mgnar da ƙarfi ne yasa, su Jabeer ma jiyo muryarta, wanda shi kuwa zuwa yanzu yana jin zuciyarshi zata iya faɗowa ƙasa dan bugawar da takeyi. Jin muryar wata nurse ɗin tana cewa. "Wannan ma ai iskanci ne". Cikin taɓe fuska ya nunawa Jalal yatsa alamun ya buɗe mushi ƙofar yaga meke faruwa da suka cika mishi kunne da hayaniya. Da sauri Haroon yabiyo bayan Jalal suka fito.

Shi kuma Sheykh Jabeer komawa yayi ya jingina da jikin kujerar shi. Tare da rage girman idonshi ya zubawa bayan Shatu ido.

Ita kuwa Shatu cikin zafi ta kalli arniyar nan da tace mata wannan ma ai iskanci ne tace. "A kul kada ki kuskura ki sake kira min iskanci a gabana, ke kika sanshi ba niba, ke kika taso cikinsa". Sai kuma ta juya harce cikin fillanci tace. "Shegu masu wari". Sai kuma ta juyo ta fuskancesu da kyau, Haroon kuwa da Jalal ido suka zuba mata cikin mamaki. Shima Jabeer idon ya zuba mata so yake yaji meyasata ihun nan. Ita kuwa Shatu cikin sanyi ta fuskanci musulman ciki murya a ɗan tashe tace. "Kada dai ku manta nace daku nakeyi masu hijabi sabida nasan kun san ma'anar Al'muslim akul muslim. Kun kuma san girma da daraja da kuma wanda ya faɗi hakan". Cikin gamsuwa duk suka ɗaga mata kai, rai a ƙuntace tace. "To meyasa kuka bar waɗanan can bayin Allah'n a tozarce a yashe a maraba da baƙi koda dreesing na raunuka su bakuyi musuba, menene laifinsu, kawai dan sun kasance fulanin daji, shiyasa DOCTOR'S da Nurse's kab bazaku jiƙansu ba". Cikin sanyi ɗaya daga cikinsu tace. "Ayyah yanzuma can zamu tafi. Sabida sai yanzu Dim ya bamu umarni". Wani dogon tsaki taja tare da cewa. "Daga baya kenan yau kwanansu goma cib babu wanda daya dubasu, sai da suka gama jigata". Tsaki arnan ciki sukaja tare da juyawa suka tafi.

A hankali Jalal ya juyo ya kalli Hammanshi da yake cewa. "Rufe min ƙofa wannan ta cika min kunne da ihu". Da sauri yace to. Haroon kuwa murmushi yayi tare da juyowa zai shiga ciki kafin Jalal ya rufe ƙofar. Da sauri ta juyo jin takun mutun a bayanta, Cikin muryar umarni tace wa Jalal. "Kai mai kamar larabawa tsaya kada ka rufe ƙofar, Office ɗin na arne ne ko musulmi?". Cikin dariya Haroon yace. "Na musulmi ne". Taku ta fara tare da nufo cikin Office ɗin. Wani irin sunkuyawa Jabeer yayi ya kifa ƙirjinshi kan babban Glass table dake gabanshi, sabida ji yakeyi tamkar kan zuciyarshi take taku. Ji yakeyi zuciyarshi zata fashe tsabar yadda take bugawa da azaban ƙarfi yadda take ƙara matsoshi haka bugawa zuciyarshi ke ƙara tsananta. Cikin mamaki ta zubawa Office ɗin ido. Office ne mai matukar girma da kyau da tsaruwa, kai bakace Dr Office bane in ba ɗan wannan gadon da labulanshi da sauran kayan aiyukansu ka ganiba. Duk da sai sati-sati yake zuwa nan Office ɗin tsab-tsab sai wani irin sanyi da ƙamshi yakeyi, cikin taɓe fuska tace. "Me hakan shima DOCTOR baida lfy ne? Kodai tsabar wulaƙanci ne?". Murmushi mai kama da dariya Haroon yayi sabida yasan babu abinda Jabeer ya tsana yake kuma tsoro kamar a tsaya a kanshi ana mgna da ƙarfi, yo shi ko a hankali kake mgna sai yace kana mishi ihu a kai bare kuma wannan da take tsaye a kusa dashi kuma tana mgna da ƙarfi cewa zaiyi haushi takeyi." Shi kuwa Sheykh Jabeer hannunshi yasa yana dafe ƙahon zuciyarshi da yakejin yana tsalle.

Rafi'a kuwa tsaye tayi a bakin ƙofar tana kallon ikon Allah.

Sauran Nurses ɗin kuwa suma, tuni sun tafi, maraba da baƙin.

Ita ko Shatu a hankali ta ƙara motsowa gaban table ɗin hannunta tasa ta bug...

😂😂😂😂tsawon shekaru labarin littafin GARKUWA yana kimtse a kaina da zuciyata. Ni kaina in na tunoshi sai nayi murmushi nayi shauƙi sarƙaƙiyarsa kan hanani baccin dare inyi ta nazartan lmrin lbrin GARKUWA, nakanji murmushi da daɗi in na tuna lbrin nakan zubda hawaye wasu lokutan wasu lokutan nakanji jikina yayi sanyi da rayuwar duniya, labarin Garkuwa bazaka ganeshi ba, sai in ka karantashi duk iya lbrin mai labartawa bazai labarta maka yadda komai yakeba, Uhummm Allah ya nuna mana ƙarshensa, salon soyayyar Sheykh ta musamman ce..

Masoyan Parvina kuna sani dariya.

Masoyan Shatu kuna burgeni. Ina masoyan Boleru jinjinan girma gareku.

Masoyan Sheykh ina sonku, Sheykh yana gaidaku.

Masoyan Jalal yace ku dena kallonshi.

Masoyan Umaymah tace ku tayata da addu'a Allah ya yaye musu matsalarsu.

Wai Ya Ba'ana baida masoya ne? Allah sarki Ba'ana ina sonshi dan al'khairin da yayiwa Aysha a baya. To wai wane al'khairi yayi mata ne?

Littafin GARKUWA na kuɗine in kina buƙatan Normal group turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276. In kuma special Group kikeso kiyi min TRANSFER ɗin dubu ɗaya rak ta asusun na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276. Masu turo katin mtn numbers ɗin zaki turo ba hotonba.

By *GARKUWAR FULANI* Ta ɗan buga table ɗin, tare da cewa. "Malam ka tashi kaje ka taimakawa yan uwanka musulmai! in kuma baka da lfy ne ka nemi bokaye irinka su duba lfyarka". Zuwa yanzu gaba ɗaya jikinshi tsuma yakeyi ta ciki. Kanshi ne yakeji yana jujjuya mishi sabida yadda ta konkotsa glass table ɗin da kanshi ke kife a kai. Ga kuma sautin muryarta da yake jinshi har tsakiyar kanshi. Da sauri ya ɗago kanshi tare da ware matsakaita kyawawan idanunshi na zaiba. Cikin sauri Haroon ya matsoshi ganin idanunshi sun cika tab da ƙwalla sai sheƙi sukeyi alamun suna iya zubda ƙollan a ko wanne lokacin. Cikin harɗewar murya ta larabci yacewa Haroon. "Please ka fitar da ita a nan, ta matsa kaina zata fasa min dodon kunne".

Ita kuwa Shatu cikin tarin mamaki da al'ajabi ta zaro manyan idanunta tare da cewa. "Laaah!". Sai kuma ta fara ɗan ja da baya tare da cewa. "Afwan baka da lfy ne!?." Wani irin fitinenne murmushi Haroon yayi tare da cewa. "Eh baya jin daɗi ne, ɗan fita zamu kira wasu bokayen suzo su dubashi". Cikin sauri tace. "Subahanallahi bokaye kuma?". Kai ya gyaɗa mata tare da cewa. "Yesss ba haka kikace ba, ya nemi bokaye ƴan uwanshi su dubashi". Kanta ta ɗan dafe tare da cewa. "No kada ka munana min zato, ina nufin likita bokan turai ka gane ko?". Da sauri taja da baya ganin Jabeer ya miƙa tsaye da ƙarfi. Shi kuwa Sheykh Jabeer tsayuwanta kusa dashi barazana ce ga zuciyarshi tabbas zata iya faso ƙirjinshi ta fito. Ganin yadda ya haɗe fuska ya nuna mata hanyar fitane, yasa ta juya ta fita.

Shi kuwa Jabeer komawa yayi ya zauna tare da sauƙe wasu tagwayen ajiyan zuciya a jere a jere. A hankali yake jin bugun zuciyarshin na ɗan dai-dai-ta kamar dai yadda yaji kafin ta shigo.

Sai kuma ya fara jin zuciyarshi na tsinkewa ras-ras kamar dai tana tsoron kada wani abu yayi nesa da itane. "Ya ilahi ya mujibadda'awati ya hayyu ya ƙayyum". Sune kalaman da Jabeer yaketa maimatawa a saman lips ɗinshi.

Haroon kuwa wani irin kallo yakeyi ma Jabeer mai cike da nazari.

Jalal ma kallonshin yake cike da tarin mamaki duk da sun san baya son akeyin mgn da ƙarfi a kanshi, to amman idonshi bai taɓa ciko da hawaye ba, sai yau.

Ita kuwa Shatu, ido ta zubawa Rafi'a da ta tsareta da ido, cikin yin ƙasa da murya tace. "Rafi'a dama, wannan shugaban tuzuran ƙasar nan, yana aiki anan asibitin gwamnatin jihar nema?". Kamo hannunta Rafi'a tayi tajata sukayi gaba. Haroon kuwa dariya yayi sabida, duk da rage muryarta da tayi sunji abinda tace, sabida wurin da suke ɗin yanada amsa kuwar amo.

Cikin yin ƙasa da murya sosai Rafi'a tace. "Garkuwa ki nitsufa ki rufa mana asiri, kin ko san waye wannan?!". Shiru sukayi dukansu lokacin da suka juyo wata kekyawar mata tana bawa wasu ƴan mata Nurses a ƙalla sun kai goma lbri. Ido Rafi'a da Shatu suka zubama wannan matar cewa. "Shi wannan Dr Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa, ba kamar sauran mutane bane, shi mutunne da Allah yayi masa wasu baiwa da nasabobi masu tarin yawa". Wata ƴar kekyawar cikinsu ne ta ɗan lumshe ido tare da cewa. "Allah ya sani Aunty ina sonshi, ina son wa'azin shi, muryarshi kawai in naji yana zuba larabci sai inji bani da sauran damuwa a duniya, sai dai shi kuma yana nan kamar dutse!". Da sauri Matar nan tace. "Ai bazai yiwuba, wlh bazai taɓa kulakiba, duk nacinki da korkosarki, shiyasa wasu ke raɗe-raɗin shi waliyi ne!". Numfashin ta sauƙe tare da ci gaba da cewa. "Duk matsayinki, kyanki, mulki, sarauta, gata, ilimi!. ko da meye kike taƙama dashi a duniya ya fiki abin". Kusan a tare suka haɗa baki wurin cewa. "Kawai dan shi jikan sarkine sai yafi mu komi?". Kanta ta jinjina tare da gyara zaman ta cikin sanyi tace. "Ba haka bane. Bari kuji kaɗan daga cikin nasabarsa. Kunga forko dai shi mutum ne wanda ubangijin yayi mishi baiwar ilimin addini dana zamani. Yana ɗaya daga cikin manyan malam da Afirka gaba ɗaya take ji dashi. Sabida a ƙiyasin malamai babu yaro matashi mai jini a jiki da tarin ilimin addini kamarshi. Tun yanada shekaru takwas a duniya ya haddaci al'ƙur'ani mai girma. Sannan ya fara karatun littafai shine matashin da yakeda haddar hadisai zunzurutunsu a kanshi sama da dubu ashirin. Kunji wannan darajeta da tasa ko manyan mutane suke girmama shi. Sannan shi jinin Masarautar Joɗa ne ta wurin mahaifinshi. Ta wurin mahaifiyarshi kuwa shi jinin sarki Jalaluddin ne, masarautar sarkin Musulmai. Kana ta wurin kakarshi data haifi mamanshi. Asalin balarabiyar saudiya ce, wacce zuriyarta ne limamen Harami. Kunga nasaba kan nasaba kenan. In kyau ne na halitta, babu irin kyan da bai ganiba, In kuwa kuɗine, ku leka ƙasan gidan saman nan zakuga ayarin motocin da sukayi mishi rakiya, to ko kakan nashi Lamiɗo motar da yake hawa bata kai ta Jabeer ba. Uwa uba shi mutun ne da ya ƙoshi da sunna, baya son bidi'a. Shi mutun ne wanda ya samu kekyawan zato a wurin mutanen duniya ake mishi shaidar salihi, mumini, mai tausayi." Da sauri suka ƙatseta da cewa. "To Aunty meya hanashi yin aure har yanzu?". Cikin maida numfashi tace. "Allahu alamu, sai dai ance kamar shi bana miji bane!". Cikin sauri wata tace. "Kai mgnar. Duniya dan Allah kiji zancen ƴan shashi faɗi. Bita da ƙulli har an samo sharrin da aka liƙa mishi bawan Allah." Rafi'a kuwa kai ta jinjinawa Shatu alamun kinji ko, ita kuwa Shatu zuru tayi kamar makahon daya tsinka garaya". Cikin sauri wacce tace tana sonshin tace. "Wlh ni dai ko shi bana miji bane zan iya zama dashi a hakan in da zai yarda muyi aure". A hankali Shatu ta gyara riƙon da tayiwa wayarta tana ɗaukar su video.

A hankali matar nan ta nisa tare da cewa. "Uhum Nafeesat kenan ai kuwa da wuya ya aureki duk abinda zakiyi. Sabida kin ga Dr sugzana yar India ce ƙabilar buramin bautar wuta takeyi. Tace tana sonshin, tace in dai zai aureta zata musulunta, amman yaƙi". Da sauri ɗaya dake cinsu tace. "Sabida me yaƙi duk da tayinta na shiga addinin Allah?". Cikin sanyi matar tace. "Yayi bayani kuma manyan malamai sun gamsu da hujjarsa, inda yace, tace dole sai in zai aureta zata musulunta, kenan badon Allah zata musulunta ba sai dan sonshi. Ta kuma ce in sunyi aure duk yaransu rabasu zasuyi rabi suyi addininshi rabi suyi addininta bi ma'ana wasu suyi bautar wuta wa iyazubillah. Yace wannan dalilin yasa bazai aureta ba, kuma shi baya sonta, ya kuma gargaɗi mata su dena cewa suna sonshi. Dan shi yanzu al'majiri ne sai ya girma zaiyi aure". Dariya sukayi baki ɗayansu. Jin hakane yasa Rafi'a yana Shatu suka ci gaba da tafi.

Su kuma waɗancan sukaci gaba da hirarsu.

Tafiya kaɗan sukayi suka samu wasu yan mata da samari suna hira ɗaya daga cikinsu na cewa "Ni tsarin Sheykh Jabeer yana masifar burgeni a rayuwata. Shifa tunda yake a duniya babu wani mahaluƙin da zaice yaga koda singalalin hannunshi ne a waje. Mutum ne da Allah yayi mishi sutura, yake kuma suturce kanshi." Cikin dariya wani yace. "Kai nima yana burgeni sai dai tsarinshi na wai mata su dena yafa gyale, su rinƙa yin shigar zurmuƙa-zurmuƙan hija baine bai minba, to mu matasa taya zamuyi ta kallonsu munajin daɗi. Ni wlh wani lokacin a kallonma nake biyan buƙatar damuwata sai dai inje inyi wonka". Cikin tashin hankali ɗaya daga cikinsu yace. "Ouzubilla, ka nemi gafar Allah wlh zina kakeyi". Cikin zaro ido yace. "Kai malam dakata ni banyi zinaba". Cikin sanyi babban nasu yace. "Wlh kayi sabida ita zina ai kashi-kashi ce akwai ta ido akwai ta kunne haka kuma akwai ta zahiriya, fisabilillahi ka kalli yar mutane na tafiya har kaji ka biya buƙatar ka?". Kai ya gyaɗa musu cikin sanyin jiki. Nan sukayi ta mishi nasi daya kame idanunshi

Da sauri suka wuce su. Ita kuwa Rafi'a cikin murmushi tace. "To bari in baki amsar tambayar ki. Yana zuwa nan asibitin sau ɗaya cikin ko wanne sati. In yazo kuma ranan duk wanda ya duba magani kyautane, in kuma aikine kyautane. Kinga Hospital ɗin school ɗinmu shi kuma a wata yake zuwa sau ɗaya, Nanam da kyar ya yarda, yanada asibitinshi mai zaman kanshi can yafi maida hankali". Ajiyan zuciya Shatu tayi tare da cewa. "Uhum can yake tara kuɗin bayin Allah ya ƙwamushewa dai". Kai Rafi'a ta jujjuya tare da cewa. "No ba haka bane, duk abinda zan ce miki bazaki gamsuba in sha Allah sai Next month in ciwon mararki ya tashi, zan kaiki can zakiga zahiri. Amman dai daga sunan asibitin zaki iya fahimtar manufarsa". Kallonta ta ɗanyi tare da cewa. "Menene sunan asibitin?". Ƙara saurin tafiyarsu sukayi tare da cewa. "Ballitai Hospital". Kanta ta gyaɗa alamun gamsuwa da sunan asibitin kana taja hannun Rafi'a suka tafi can maraba da baƙi.

Abin mamaki suna isa suka samu. Kusan rabin DOCTOR'S din asibitin duk suna wurin. Duk DOCTOR'S ɗin da Shatu tayiwa mgna sunzo nan sunata basu taimakon gaggawa. Kana ga Nurses tako Ina, sunata tura marasa lfyan ana basu gadaje. Cikin abinda bai gaza awa ɗaya da rabi ba. Komai yayi dai-dai hatta waɗanda za'ayiwa aikin anyi musu.

Bisa umarnin Lamiɗo kana ya rinƙa bin gadajensu yana ajiye musu kuɗi dubu biyar-biyar.

Sosai wannan abun yayi masifar yiwa Shatu daɗi, tana kallon dattijon tamkar wani nata, Godiya sosai sukayi musu da zasu tafi, suna fita nan sukayi kiciɓis da Jabeer da yanzu ya fito ɗakin tiyata.

Ita kuwa Shatu Junaidun Junainah ta kalla lokacin da aka dawo dashi daga ɗakin tiyata, Inda aka ɗinke mishi inda aka sareshi. Cikin murmushin yace. "Adda Shatu zamu kwana ko?". Murmushin jin daɗi tayi tare da cewa. "A a Junaidun yanzuma zan tafi, kasan Ummey ba lfy, amman jibi ma zanzo gobe su ya Salmanu zasu zo, yanzu dai hankalinmu ya konta tunda kun samu kulawar likitocin yanzu sai matsalar abinci". Cikin sanyi Sumaye matar marigayi Sarkin bakansu, tace. "La abinci kam bamu da matsalarshi, tako ina zakiga musulmai na dafo abinci suna kawo mana sadaka, harda kayan zaƙi da kuɗi wasu ke bamu". Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa. "Alhamdulillah yau kam mutanen Rugar Bani zasuji lbri mai daɗi". Cikin kula tace. "Toni yanzu zan tafi in Sha Allah gobe akwai masu zuwa, Allah ya baku lfy". Ta faɗi tana kallon sauran mutanen nasu. Haka Rafi'a ma tayi musu fatan lfy kana suka fita tare. Adaidaita suka shiga, saida ya kai Shatu tasha kafin. Ya wuce da Rafi'a school ɗin su.

A can wurinsu Lamiɗo kuwa ganin lokacin sallan la'asar yayine yasa Jabeer cewa, suyi salla a masallacin asibitin kafin su tafi. Haka kuwa akayi, sai gashi masallaci ya cika maƙil da bani adam, saida suka idarne kana suka kama hanyar tafiya garin Rugar Bani.

A cikin motocin kuwa kowa da abinda yakeyi. Shi kuwa Sheykh Jabeer tsuratul Khaf yake karantawa a hankali. Hakama Lamiɗo.

Su Jalal kuwa kowa na ruggume da waya. Haroon ma waya yakeyi da Umaymah tana tambayarshi sun isane. Nan yake gaya mata inda suke da abinda sukayi.

A cikin Rugar Bani kuwa, kamar ko wacce ranar jumma'a yauma hakane. Tunda aka taso sallan jumma'a suka dawo tsakar garinsu suka zauna suna ƙara jadda mitin ɗin su na ɗaukar fansa. Zuwa yanzu garin yana amsar baƙoncin Fulanin da suka gaiyata tako wani sashi na Afirka. Sunata shirye-shiryen su.

Suna cikin masallaci suna sallan la'asar ne suka rinƙa jiyo, shigowar motoci cikin Rugarsu kamar bazasu ƙare ba.

Cikin nitsuwa sukaci gaba da sallan su.

Su Lamiɗo kuwa suna shiga garin ganin tsit kuma alamun ana salla, sai yace su tsagaita gudun.

Jabeer kuwa zuwa yanzu tuni zuciyarshi ta fara luguden dukan ƙirjinshi ya rasa wannan abu na menene? Yanzu wannan karo na huɗu kenan yana jin wannan abun a rayuwarsa, ya kuma gwada kanshi yaga bashi da BP dan sani BP nayin hakane ya sashi godawa.

A jere a jere sukayi parking motocinsu cikin nitsuwa, Dogarai da fadawa suka fito suka zagaya motocin.

Bayan sun idar da salla sunyi addu'o'insu ne kana suka fito. Gani fadawa da dogarai ma kaɗai ya ganar dasu waye yazo. Dan haka cikin karrama da mutun-tawa Arɗo Bani ya nufi inda suke. Sosai dogarai sukayi mamakin yadda wannan karon kuma yakeyi kamar ya haɗiyesu dan farin cikin zuwansu saɓanin wancan karon da yayi ta aunawa Lamiɗo boma-boman baƙaƙen maganganu. Jiki na rawa ya juyo ya kalli matasan tare da cewa. "Maza ku shiga cikin gidan ku fito da dardumai da kilisai kuzo ki shimfiɗa. Ina sarkin kiɗa maza a fito da gangaguna a fara sanarwa. Mabusa ku fito."

Ai kuwa cikin abinda bai gaza 25 minutes ba aka gama shirya komai. Tuni mutane sun cika sunyi maƙil ko ina ya cika da bani adam. Kiɗe-kiɗen da bushe-bushen sarewa da al'gaita kuwa tuni ya cika illahirin garin tako ina mutane ke shigowa.

Ba'ana da tun jiya yake cikin ɗakin dodon tsafinsu Bonon. Jin al'gaita Shaɗi ne, ya sashi fitowa bayan ya gama shafe magunguna. Dama yayi zaton wannan hegen mai jajayen kunnuwan zaizo shiyasa tun jiya ya shiga ɗakin sirri dan a dafashi da kyau.

Jinsu ne yasa ya fito dashi da tawagarsa suka nufi Rugar Bani.

Lamiɗo kuwa da tawagarsa a hankali cikin ƙasaita da kwarjini suke taku har i zuwa cikin rumfar karan da aka malale musu kujeru da kilisai.

Bayan sun zaunane duk dattawan wurin sukazo suka gaida Lamiɗo da tawagarsa. Jabeer kuwa ji yake tamkar ya kira Sojoji su zo su zazzane mishi mutanen garin gaba ɗayansu ko zaiji ya huce da abinda sukayi mishi. Sam baya son ganin fuskokinsu, ga toshe mishi kunne da sukayi da wannan bushe-bushen sarewa. Ga bugun zuciyarshin dake neman zautar dashi. Allah ya sani baya son ganin ko ƙasar garinne.

Cikin kula da nitsuwa da kamala Bappa ya kalli Jabeer ɗin tare da cewa. "Yaro ya ƙarfin jikin naka". Ba tare daya ɗago kanshiba ya amsa, sabida jin muryar tanada kamala. A hankali yace. "Alhamdulillah". Gaba ɗayansu suna farin cikin ganin Jabeer yazo cikin ƙoshin lfy. Sunyi masifar mamaki ganinshi garau ya worke cikin mako ɗaya tak. Wannane ya ƙara sawa Ya Salmanu wani farin ciki na ban mamaki.

A hankali Bappa yace. "Masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi". Idonshi ya ɗan ɗago ya kalleshi, haka nan yaji dottijon ya cika mishi ido a hankali yace. "Amin ya Allah". Bukar ne ya ɗan kalleshi tare da cewa. "Yanzu yaron nan kaine? Ka sake zuwa garin nan lallai baka son ranka". A daƙile Jabeer yace. "Inuwa tace". Galadima ne ya ɗan kalleshi tare da mishi alamun kada yayi mgna. Kwaffa yayi tare da murtuke fuska.

A hankali su Arɗo bani suka koma wurin zamansu. Kana Barmuji ya fara sanarwan ana son ganin Ba'ana a tsakiyar fili.

Wannan abu shine na forko a tarihin shi a nemeshi yazo tsakiyar fili dan a rama gasar da yayi. Haka yasa cikin karsashi da buɗa ƙwanji yayi wani irin tsalle ya faɗo tsakiyar taron. Juyi ya farayi da ihu da ɗaga hannunshi sama, saida yayi kusan sau goma kafin yacewa Barmuji. "Ka gayawa yan kallo in dai an cini gasa zan tafi in bar ƙasar nan, zan koma ƙasar Cameroon nida ƙasar nan sai dai ziyara, Dan ba'a yin jarumai biyu a gari ɗaya kamar yadda ba'a sarakuna biyu a gari ɗaya." Wani irin ihu da shewa gaba ɗaya mutanen suka ruɗe dashi lokacin da Barmuji ya sanar da ikirarin Ba'ana.

Kana dattawan garin kuma kowa da abinda ke cikin ransa Arɗo Bani dasu Bappa kamar su haɗiye haƙorinsu dan daɗi.

Arɗo Bani ne ya ronƙofo kusa da Lamiɗo cikin nitsuwar datattaku yace. "Allah rene, bisimilla GARKUWA ya fito fage shi ake jira." Kai ya gyaɗa mushi kana ya juyo ya kalli gefen damanshi inda Jabeer ke zaune cikin shigarsa ta al'farma, yayi masifar kyau, yana zaune cikin kamala sai lips ɗinshi ke ɗan motsawa a hankali alamun tasbihi yakeyi. Cikin yanayi girma da bada umarni da tsare fuska Lamiɗo yace. "Jabeer kai ake jira tashi kaje muyi abinda ya kawomu." Fuskarshi ya tsuke tare da lumshe idonshi, muryar Galadima da yajune yasashi buɗe idonshi. Shi kuwa Galadima hannu ya miƙa ya kamo hannun Jabeer, tare da fara ja alamun zai miƙar dashi tsaye. Cikin mamaki Jabeer ya zubawa tsohon ido wanda yake Bappa ne ga Lamiɗo, in banda ƙarfin hali inashi ina iya ɗaga Jabeer. Muryar Lamiɗo yaji yana kuma cewa. "Jabeer DAN ALLAH KA TASHI". Tsaki ya ɗan ja kana ya yunƙura ya miƙa a hankali. Cikin jin daɗi Galadima ya kama hannunshi yaja suka fara taku, zuwa cikin taron. A hankali yake bin bayan Galadima kana fadawa na biye dasu. Al'kyabbar shi ya ɗan gyara mahaɗinta.

Suna isa tsakiyar taron. Mabusa da makaɗa duk suka kaceme wurin da bushe-bushen sarewa da al'gaita kana da kaɗe-kaɗen.

Barmuji ne ya matso bayanshi da alamun zai cire mishi Al'kyabbar shi. Da sauri Barmuji ya dakata sabida ganin wani irin lallo da Jabeer ya watsa mishi cikin tabbatarwa yace. "Kada ka sake gangancin ciremin suturar da Allah yayi min har abadan. In kuwa ka gwada tabbas zakaji yadda raɗaɗin marin tafin hannuna yake, in kunnenka ya kuramce ansan kuramtane yasa bazakaji gargaɗi da kashedi na ba!". Ya ƙarishe mgnar da tafasar zuciya, cikin tsuma Barmuji ya rusuna tare da cewa. "Duk da dokar gasa ce, anyi maka wannan lamunin tunda kaine mai duka ba kai za'a dakaba". Ba'ana kuwa wani murmushi jin daɗi yayi sabida yasan yin duka da ƙatuwar riga haka, zai takurashi bazai samu damar zage ƙarfin shi ya zabga mishi bulaliyar ba. (Allah sarki Ba'ana bai san zafin hannun Sheykh bane. Sarkin Shaɗi ne, ya miƙe tsaye tare da tanɗun shantun da a ciki suka zuro bulalin nasu. Ya nufi wurinsu Jabeer yana zuwa. Yasa hannunshi ya zaro bulala ɗaya daga cikin bulalin ya miƙa mishi. Hannun yasa ya amshi bulalar. Kana ya gyara al'kyabbar jikinshi. Shi kuwa ba'ana gabanshi ya matso ya tsaya ya buɗa sawunshi, kana, yasa hannunshi duka biyu ya riƙe ƙugunshi, ya buɗa ƙwanjinshi da kyau.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull