Garkuwa complete Novel - Chapter 24
Garkuwa complete Novel Chapter 24: Garkuwa complete Novel Chapter 24. Sheykh kuwa ƙasar garin ya zubawa ido, yana tuno irin zafi da ƙunar sashi cire…
4,235 words
Sheykh kuwa ƙasar garin ya zubawa ido, yana tuno irin zafi da ƙunar sashi cire kayanshi da sukayi satin daya gabata, yana tuna raɗaɗin da zuciyarsa ta masa a wannan lokacin. Busar sarewa da akayi azaban ƙarfi ne, tabbacin an bada dama a farane. Yasa Jabeer gyara riƙon da yayiwa bulalar, yana maiji cikin ransa da jikinsa zai rama dukan azaba da wannan ya mishi. Yanajin zai ramane kuma dan tsorotar dashi kan sake dukan wani. Yasani in sha Allah daga kanshi baza'a sake wannan gasar daba adadin bane, yayi niyar yin ramuwar ne dan tare wannan ɓarakar zai ramane ko zai samu ya huce tsanar da yayi mutanen garin, sabida kasan cewarsu Musulmai ƴan uwansa baya son yayi musu irin wannan tsabar lokacin ɗaya fushinsa na ranar ya dawo. Shiyasa ya murza yatsunshi da kyau tare da matsawa gefe kaɗan, Rumtse bubalar yayi a tafin hannunsa da kyau, kana ɗagata tare kuma da cewa Bismillah, ya fara da sunan Allah kana ya ɗaura da fara karanto ayatul shifa sannan ya zabgawa Ba'ana ita a tsakiyar bayanshi.
Gaba ɗaya hankali da idon kowa bisa fuskar ba'ana yake. Shi kuwa ba'ana wani irin murmushi yayi tare da kallon gefe da gefenshi kana, yayi fito alamun babu wani abu da yaji dai yaji tsikar jikinshi yana tashi yar-yar.
Arɗo Bani da sauran dattawan kuwa har ji sukeyi tamkar su kamo hannun Jabeer suyi ta zabgar Ba'ana babu ƙaƙƙautawa.
Shi kuwa Jabeer wani bulalan ya kuma shimfiɗa mishi a tsakiyar bayanshi tare da sunan Allah. Still murmushi yayi sai dai wani irin masifeffen bugawa da zuciyarsa tayi ya tsinke ras. A karo na uku ya tabka mishi bulalar a tsakiyan kafaɗunshi wannan karon baiyi murmushi ba, ƙebta idonsa yayi, tare da gyara tsayuwa sai kace dutse ake tabkawa bulalin. Fargabane ya fara dukan ƙirazan dattawan Fulani, yayinda ƙabilar ɓachama kuwa, suketa ihu da tsalle da fito da kiran ba'ana suna ƙara mishi ƙarsashi. Bulala ta biyar Jabeer ya kuma tsula mishi, still babu sauyi. Cikin sauri Arɗo Bani ya juyo ya kalli Lamiɗo dake zaune. Ko ajikinshi dashi da tawagarsa, Sarkin Shaɗi kuwa murmushi ma yakeyi.
Cikin fargaba, Arɗo Bani yace. "Allah rene Lamiɗo wannan yaron bai iya duka da ƙarfi bane? Ko dai ba bulalin masarautarku bace!?". Wani irin kallo mai cike da mamaki da kuma tuhuma Lamiɗo yayi mishi. Sai kuma dai ya kauda kanshi. Ɗanzagi ne yace. "Hattara dai Arɗo , Masarauta Joɗa sun wuce aro, zuba ido kaga ikon Allah". Bulala ta bakwai ne, Jabeer ya ɗago ya tsulala mishi ita a gadon bayanshi. Da sauri Ba'ana ya rufe ƙwayar idanunshi sabida wani irin tashi da yaji tsikar jikinshi yayi. Tsikar jikinshi bai gama konciya ba, yakuma jin Jabeer ya rausa mushi wata bulaliyar, da sauri ya buɗe idonshi sabida. Wani irin Yar-yar da yaji tsikar jikinshi tana zubawa duk gashin jikinshi ya miƙe tsaye. Bai gama dawowa nazarin meyasa yakejin hakaba ya kuma jin wata bulaliyar. A hankali yaji zufa ya fara keto mishi duk ta inda hudan gashin jiki yake a fatarsa. Murmushi yakeyi har yanzu sabida bawai zafi yakeji ba, sai dai fargaba ta rufeshi, sabida jin alamun sihirurrukan jikinshine ke fecewa. A haka Jabeer yayi ta tsula mishi bulala har zuwa bulala ta goma sha ɗaya. Ata goma sha biyu ne, da ya tsula mishi yayi wani irin gantsarewa sabida wani irin azabebben ƙaiƙayi da yaji wurin yanayi mishi. Da sauri yasa hannunshin a bayanshi alamun zai sosa. Ife-ife da sowan da matasa suka farayi ne da Muryar Barmuji na cewa. "Dokar gasa banda susa". Da sauri ya dawo da hannunshin tare da cewa. "To ya dane karatun da yakeyi, bana so, ya dena kira min sunan Allah". Wata bulalar Sheykh ya zabgawa shege tare da cewa. "Sunan uwarka zan kira maka in ban kira sunan Allah ba?". Arɗo Bani kuwa wani irin ajiyan zuciya mai ƙarfi yaja. Shi kuwa Ba'ana wani irin masifeffen ƙaiƙayi ne yakeji a duk inda Jabeer ya zuba mushi bulala, a bulala ta goma sha biyar ne, da aka zuba mushi. Yayi wani irin gantsarewan da yafi na ɗazu. Wani irin azabebben zafi da raɗadine yakeji yana tsarga mishi jiki da zuciya. Zuface ta ketomishi tako wanne sashi na jikinshi. Cikin sauri Jabeer ya juya bulalar ya amshi ta biyu ya haɗa data forkon. Ya damƙesu a hannun hagunshi. Wanda dama shi badamene kuma bahagone duk abinda hannun damanshi kan iya yi to na hagun yana fi iyawa. Sai dai kasamcewarshi mutun mai ilimi da sanin addini shiyasa yake amfani da hadinsin nan da Manzon Allah ke cewa. A cikin dukkan abinda zamuyi mu wakilta dama a forko, har dai sai in shiga bayan gidane aka ware shiga da ƙafar hagu. To juya hannun yayi da hannun hagunshi, kana ya riƙe mahaɗin al'kyabbar jikinshi da hannun damanshi. Gyara tsayuwarshi yayi kana ya ɗaga bulalar da ƙarfi ya zubawa Ba'ana a tsakiyar bayanshi.
Wani irin azabebben ihu mai ƙarfin amo da karaji Ba'ana ya kurma tare da fara karkarwa kar-kar tamkar mai farfaɗiya. Ihun da ya kurmane yayi masifar tada hankalin dukkan kafurai magoya mayanshi. Arɗo Bani kuwa a gabansu Lamiɗo ya tashi tsaye ya juya ya fuskanci al'ƙibila yayi sujjada. Bappa ma da kanshi wani irin murmushin jin daɗi yakeyi.
Hakama duk sauran dottawan. Shi kuwa Ba'ana wani irin azabebben kuma masifeffen zafi yakeji a dukkan sashin jikinshi. Wani irin tsalle ya buga da ƙarfi lokacin da aka kumayi mishi bulala ta ashirin. Wani irin tsuma da karkarwa jikinshi keyi hatta Ba'anansa miƙewa tayi tana karkarwa, wata tafasashiyar zuface ta sinƙo mishi, zafi yakeji har cikin ƙoƙon kanshi da zuciyarshi. Bulala ta ashirin da biyu akayi mishine yasashi fashewa da wani irin kuka mai azaban ƙarfi wani irin masifeffen fitinenne fitsarin azaba ya fara kwaranyo mishi, ihu mai cike da azaba yayi. Wanda gaba ɗaya rugar saida kowa ya jiyoshi. Ƙabilar ɓachama kuwa gaba ɗaya suma kuka suka saka. Shi kuwa Ba'ana da ƙarfi ya faɗi ƙasa yana burbuwa, tamkar wanda yayi al'janu. faɗuwanshi ƙasane yasa Jabeer rusunowa ya rinƙa tabka mishi bulalar, ihu da burbuwa da rarrafe alamun guduwa Ba'ana yakeyi cikin azaba da karaɗi da kuka yake cewa. "Wayyo! Wayyo!! Wayyo Bonon!!! Ka ceceni zan mutu zai kasheni. Wayyo Bononnnnnn! Yau bakayi min ranaba, ga bulalin karin sihirina sun iso gareni wayyoooooooo Bonon meyasa baka gaya minba na hudu tun kan wannan malamin ya kasheni ya karya min komai na jikina da sunan Allah." Ya ƙarishe mgnar da ƙarfi tare da miƙewa tsaye ya fuskanci kudu. Ya ɗiba a guje ya ari ta kare ya nausa a guje. Wani irin taku Jabeer yayi tare da biyoshi baya da sassarfa abunka da dogon mutun sai gashi ya isoshi a gigice ya fara kai mishi bulalin hagu da dama, Jin azabar ta zarce azabar da yake zatone, yasa Ba'ana kurma ihu da kururuwan da yasa kab mutane suka nufosu. Gudu yakeyi Jabeer na binshi yana zaneshi har ya fiddashi cikin taron gaba ɗaya. Barmuji ne ya riƙe hannun Jabeer tare da cewa. "A dokar gasa Shaɗi in dai ya gudu ka bishi ka korashi cikin farfajiyar shike nan ya faɗi a gasa kaci. Kuma bazai sake samun damar shiga gasarba bazai kuma sake zama a garinba." Wani irin busar sarewa da al'gaita kana da kiɗe-kiɗen tsantsar farin ciki, al'ummar Rugar Bani suka farayi. Sunayi suna zagaye Jabeer. Haroon kuwa da Arɗo Bani da Galadima miƙewa sukayi cikin farin ciki suka ruggumeshi. Jamil, Jalal, Imran, Hashim, Sulaiman. Suma kab farin cikine ya cika musu zuƙata. Laminu kuwa ji yakeyi tamkar ya shaƙo Jabeer ya karshi sai dai tabbas dama ya zaci aha dan shi mari ɗaya nema Sheykh ya masa ya kusan suma, shiyasa ya tausayawa Ba'ana. Lamiɗo kuwa jinjina kai yakeyi yana tattausan murmushi.
Koda su Galadima suka ruggumeshi, Arɗo Bani kuwa kama hannunshi yayi ya ɗaga sama alamun yaci gasar Shaɗin.
A haka suka iso gaban Lamiɗo hannunshi yasa ya dafa kan Jabeer tare da sanya mushi al'barka.
Mutane kuwa duk an kacame da farin ciki. Ya Salmanu kuwa kusan suma yayi tsabar masifar jin daɗi. Alhamdulillah yau dai burinshi ya cika ya samu konciyar hankalin duniya an ɗauka musu fansa, shida masoyan Shatu na baya, harma da yayanshi.
Jan gefe makaɗan suka sabi, da sauran zugar jamar gari.
Jabeer kuwa mamaki yakeyi yadda yaga. Fulani nata shigowa garin tako ina wasu bisa dawakai wasuma ƙan raƙuma. Lamiɗo kuwa waya yakeyi da amalun a sirrance yake mgnar sabida ko Jabeer ɗin dake kusa dashi baya jinshi.
Bisa umarnin Arɗo Bani ne aka rinƙa fito da ƙwaran nono da fura da dambu da ƙwaran zuma, Ana kawowa su Lamiɗo.
Wanda fadawa da dogarai ne sukasha.
A hankali Jabeer ya kalli Lamiɗo cikin gajiya yace. "To ai sai ku tashi mu tafi ko!". Shiru Lamiɗo yayi mishi, ganin hakane, ya gyara hiramin kanshi kana ya kuma cewa. "Mu tafi ko". Galadima ne yace. "Ai bamu gamaba". Cikin sauri Haroon yace. "To meya rage kuma?". Galadima ya buɗe bakin zai bashi amsa kenan. Sai kuma duk suka juyo suna kallon wasu tsala-tsalan motocine masu masifar kyau da tsada, suna shigowa Rugar Bani a jere-a jere. Cikin fidda numfashi Haroon ya ɗan kalli motocine da mamaki yace. "Ha Jabeer kalli wannan kamar tawagar motocin Uncle Abdulkarim da Abudulfata kalli kamarfa harda Jadda". (Sarki Jalaluddin suke cewa Jadda) Sai kuwa ya juyo ya kalli Lamiɗo cikin nitsuwa yace. "Lamiɗo lfy kuwa?". Kanshi ya gyaɗa mishi alamar eh Lfy kau. Shi kuwa Sheykh Jabeer cikin nitsuwa yake kallon ayarin motocin a fakaice tabbas. Su Jalaluddin ne da yaranshi. Kana ga kuma Baban Haroon, ga kuma su Dr Aliyu da Barrister Kamal da su Baba Basiru Baba Nasiru dama duk sauran manyan masarautarsu. Da sauri ya juyo ya kalli Lamiɗo da nufin yin tambaya sai kuma yayi shiru ganin Lamiɗo na mgna da Galadima da kuma wani amintaccen bafadanshi. Tsaki ya ɗan ja tare da cewa. "To wannan ƙus-ƙus du na menene, ku duk abinda babu kyau kuna jin daɗin yinshi." Shiru yayi ganin motoci sama da talatin ne suka shigo Rugar. Kana duk manyan mutanene kuma sun fito cikin motocin sun nufo inda suke zazzaune. Wanda tuni Arɗo Bani yasa an kuma firfito da taburman cikin masallacin su. Kana yasa an fito da sauran dardumai da kilisai anzo an shimfiɗa.
Suna isowa sarki Jalaluddin da Abba suka dafa kafaɗun Jabeer tare da sanya mushi al'barka kana suka zauna gefenshi ya zama sun sakashi a tsakiya. Kusa dashi Abbanshi ya zauna, Kana Jalaluddin ya zauna kusa da Abban. Lamiɗo kuwa na kusa dashi shida Galadima.
Da sauri Haroon dasu Jamil kan sukabi bayan fadawan da suka nufi motocin da sukazo yanzu da ido.
Shi kuwa Sheykh Jabeer ido kawai ya zubawa wayarshi. Yana wasu aiyukanshi a ciki.
A hankali ya ɗago kanshi ya kalli Haroon dake taɓashi. Da yatsa Haroon ya nuna mishi gabanshi. A hankali ya juya kanshi ya kalli inda Haroon ke nuna mishi. Fadawane da hadimansu keta jido katon-katon ɗin sweet ga kuma fufun goro shima sunata jidowa suna ajiyewa a gabansu Arɗo Bani.
Cikin mamaki ya kalli Lamiɗo tare da cewa. "Me za'ayi da wannan kuma? Kamar wanda suka zo ɗaurin aure!". Da sauri Galadima yace. "Eh ashe ka gane ai ɗaurkin auren ne". Cikin mamaki Haroon yace. "Aure kuma? To auren waye?". Lamiɗo ne ya kalleshi cikin isa yace. "Auren Muhammad Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa!". Wani irin yunƙura Jabeer yayi zai miƙe, cikin tsananin haɗe fuskarnan tamkar zatayi aman jini ya kalli Lamiɗo tare da yunƙurin miƙewa yace. "Zancen banza kenan a wurin banza, ai wlh baka isaba, wlh Lamiɗo kafa kiyayeni kanafa shigemin rayuwa, ka fita hanyata ka fice min a ido kar in rintsa da kai fa kadafa ka bari in juyo kanka". Ya ƙarishe mgnar da miƙewa tsaye. Sai kuma ya juyo jin an kamo hannunshi an medashi zaune, a fusace ya kalli inda yaji anja hannun nashi ganin Sarki Jalaluddin ne ya riƙo hannunshi ya sashi kuma tsuke fuskarsa cikin faɗa yace. "Jadda sakarmin hannu bana so! Bana son abinda kuke min da rayuwata, wlh gwarama kun tashi mun tafi, dan babu ruwana dan Ni bazanyi aure ba". Da sauri ya juyo jin muryar Abbanshi yana cewa. "...!
Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276, sai in saki cikin Normal group wanda a kwana talatin za'a gama littafin. Ko kuma kiyi min TRANSFER ɗin dubu ɗaya ta asusuna na Jaiz 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276. Sai in saki a Special Group inda cikin mako biyu kacal za'a gama Part 1 da izinin ubangiji.
By *GARKUWAR FULANI* Wata iriyar zuface ke tsastsafo mishi bisa goshinsa, Kamar an watsa mishi ruwa. Ya kamo lip ɗin shi na ƙasa yana taunewa. Hannunshi dake cikin blanket ta zubawa ido. Dan son gano abinda yakeyi, shiru tayi sawon 5 minute kana, a hankali ta ɗaura tafin hannunta kan goshinta, tare goge mishi zufar, daketa tsastsafowa duk da sanyin A/C dake ratsa ɗakin. Idonshi ya saisaita lumshe su da yayi, ya sani Umaymah ce. sabida babu mai shigar masa ɗaki kai tsaye sai ita. Babu kuma mai taɓa mishi goshi haka sai ita. Cikin kula tace. "Jazlaan!". A hankali ya gama buɗe idanunshi da sukayi jazir alamun tarin ƙuna da yakeji a ransa. A hankali tace. "Jazlaan!." Ta kuma kiranshi a karo na biyu. A hankali ya motsa lips ɗin shi alamun zai amsa mata. Amman Ina zafin da zuciyarshi keyi ya danne harshensa hafimtar hakane yasata, nuna damuwarta a hankali tace. "Kaci abinci?". Ƙarya ba ɗabi'arsa bace ba kuma halittarsa bace, duk ɗacin gsky zai faɗeta, bare a kan kashi. Kanshi ya girgiza alamun baiciba. Cikin sanyi tace. "To Muje kaci koda abu mara nauyi ne!." Da ƙarfin ya fizgo mgnar. "Bazan ci ba". Ta sani yadda yayi mgnar, ta kubce masane, dan in ransa a ɓace yake baya mgna, ɓacin ran mai limini kenan babu faɗe-faɗe bare hargowa ko buge-buge. Sanin ko ya zatayi bazai cin bane, kamar yadda ya faɗa mata yasa, ta miƙe a hankali kanshi ta shafa tare da cewa. "Saida safe". Kai kawai ya iya gyaɗa mata, Haka ta fara tafiya, tana kallon yadda yake motsa hannunshi cikin blanket tabbacin. Wani abun yake yagewa.
Yadda ta bar Haroon haka ta sameshi saida safe tayi mishi kana ta wuce ta tafi.
A can Rugar Bani kuwa. Kamar yadda Ba'ana ya ɗaukarwa kanshi al'ƙawari haka ya bar ƙasar ya nufi ƙasar Cameroon Kai tsaye Yahunde ya nufa, cikin rugagen Fulani, yana tafiyarne da ɗan sauran tsafi da sihirin dake jikinsa.
A haka ya nausa cikin ƙasar Cameroon da yake jihar Ɓadamaya tana bakin bodar ƙasar ne.
Fulanin Rugar Bani kuwa, a daren wannan ranar sukayi gangamin ramuwa, suka faɗawa ƙauyukan kafuran ƙabilun ɓacamawa dake cikin Shikan da kewayenta. Allah ya basu nasarar yaƙan kafuran nan. Har suka samu damar ƙona ƙauyem Bonon wanda shine zuciyar ƙabilar ɓachama, kamar yadda Abuja take zuciyar Nigeria. Cikin daren suka ƙona ƙauye dama dodon tsafinsu Bonon da suka ɗauka a matsayin Ubangiji su sun ƙonashi sun ɓadda shi a doron duniya sai dai tarihinsa.
Wannan labarin shine labarin. Da gidajen rediyo dana tv da jaridu sukayi. Breakfast dashi yayinda akayita kuzuzuta cewar Fulani sun zama ƴan ta'adda sun farma garuwa da yaƙi. Uhummm wannan shine halin da Fulani ke rayuwa a ciki. A zalimcesu, kaji cib duniya babu mai yin mgn su kai ƙorafinsu a koresu. Gwamnatin kasar data jiha suyi kamar basujiba. In fulanin sun rama na lokaci ɗaya sai asa musu sunan ƴan ta'adda ko yan tada zaune tsaye, har ana ikirarin korarmu.😭😭😭
Hankalin ƙabilun Ɓacamawa dake cikin Shikan duk suka ari ta kare. Hausawa da Fulani kuwa kowa ya koma, cikin gidansa. Domin Allah ne yabi kadunsu.
Sarkin Shikan da kanshi yayi masifar girgiza da yawan da Fulani sukayi cikin garinshi da kewaye. Gashi an ƙone dodon tsafinsu nasu kuma babu abinda ya samu fulanin. Hakane yasa shi kanshi ya arce, sai abu ya lafa ya dawo.
Su kuwa Fulani bayan sun gama. Suka tsaya suka bawa yaransu da tsoffinsu mafaka, domin su basu kashe yara da tsoffi da mataba. Anyi an gama, kafin hukuma tazo, ta ƙara sai saita Komai.
A cikin masarautar Joɗa kuwa. Washe gari da safe. Lbrin ya rinski Sarki Nuruddeen, shine ya bada umarnin kada a kama bafulatani ko ɗaya.
Aysha ce zaune gaban Umaymah Aunty Juwairiyya na gefenta ita da Hibba, cikin kula Umaymah tace. "Yauwa Aysha kinga wannan ki ɗauke ta matsayin yayarki ita ɗin yar babban Yayanmu ne wanda na nuna miki jiya. Mijinta kuma ya'yan Jabeer ne, Side ɗinta na kusa da naku. In kinga duk wani abun da baki fahimta ba ki tambayeta, in kin gaji da zaman kaɗaici zaki iya shiga wurinta, da wurin Mamanku, da kuma nan wurin Gimbiya Aminatu". A hankali ta ɗan kalli Aunty Juwairiyya, tare da cewa. "Ina kwana Aunty". Cikin jin daɗi Aunty Juwairiyya tace. "Lfy lau ya baƙunta". A hankali tace. "Alhamdulillah!".Hibba ce ta ɗan tsuke baki cikin sanyi tace. "Shike nan ai, an gabatar mata da kowa sai ni aka ware". Murmushi Aunty Juwairiyya tayi tare da cewa. "To Aysha ga Hibba wutar Umaymah, duk family itace auta a jikokin Sitti na nan ƙasar". Murmushi ta ɗan yi sabida ganin yadda Hibba tayi sai Junainah ta faɗo mata a rai. Ita kuwa Hibba motsata tayi tare da cewa. "My happiness". Cikin murmushi Aysha ta nuna kanta, alamun "Nice my happiness?". Murmushi Hibba tayi tare da cewa. "Yes haka Umaymah tace wai kece farin cikin ahlimu da izinin ubangiji". Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta. Haka nan taji tana jin sonsu a ranta, Especially Umaymah da Hibba. Aunty Juwairiyya kuwa da Ummi breakfast Suka gabatar mata, kana suka fita. Umaymah da kantane ta haɗa mata tea mai kauri ita da Hibba kana ta zuba musu abincin da Aunty Juwairiyya ta kawo musu tare da cewa. "Bismillah kuci abinci". tana faɗin haka ta miƙa ta fita, Ita kuwa Hibba da tsauri ta gyara zamanta tare da ɗaukan Fork ta matso gaban plate ɗin da aka zuba mata soyyyan dankali da kwai, hannun tasa ta soki guda biyu tare da ɗagowa zata kai bakinta, sai kuma ta tsaya tare da zubawa Aysha ido ganin ta riƙe mata hannunta. Cikin sanyi da ɗan sakin jiki da Hibba ta girgiza mata kai tare da cewa. "Kada kici wannan abincin". Cikin juya ido Hibba tace. "Meyasa!?". Kai ta jujjuya mata kana ta gyara zamanta, tare da ɗan kallon ƙofar shigowa ta gefen idonta. Wani kekyawan Foodflaks da aka kawo daga sashin Gimbiya Saudatu ta jawo tare da cewa. "Ki ɗiba a nan kici". Cikin mamaki. Hibba tace. "Aunty Aysha, ai Bama cin abincin gidan Gimbiya Saudatu, kuma naga Hadimanta ne suka kawoshi". Cikin rashin gane manufar zancen Hibba tace. "Meyasa bakwa ci?". Juyawa Hibba tayi ta kalli bayanta kana ta juyo ta kalleta da kyau kana a hankali tace. "Bata son Hamma Jabeer dama duk ƴan uwanshi, cewa take zata kasheshi in ta samu dama, shiyasa Umaymah take hanamu cin abinci ta". Wani irin nannauyan ajiyan zuciya ta sauƙe tare da kallon Hibba cikin cushewar tunani ta kalli jerin kulolin da a ƙalla sun kusa takwas a gabansu. Cikin sanyi tace. "Buɗe su mu gani". Jin hakane yasa Hibba buɗe su ɗaya bayan ɗaya. ita kuwa ido take zubawa duk kular da Hibba ta buɗe. Kular ƙarshe wacce ke ɗauke da Chicken Ball's mai zafi sai turiri yakeyi da ƙamshi. ta nunawa Hibba tare da cewa. "Kici wannan". Murmushi Hibba tayi kana tace. "Yauwa shinema na Gimbiya Aminatu kuma ta iya girki tsohuwar hakana hadimanta, a plate ta zu musu. Kana suka faraci suna ɗan korawa da ruwan tea mai zafi da kauri. Sunaci Hibba nata janta da hira duk da ita Aysha zuciyarta a cushe yake.
Bayan sun gamane, Hadiman Gimbiya Aminatu suka shigo suka tattare komai suka gyara wurin bisa umarni Jakadiya.
Ganin Aysha ta ɗan saki jiki da Hibba ne yasa, Umaymah ta wuce Side ɗinsa ita da Umminshi.
A falo suka samu Jafar, Jalal, Jamil, Haroon. Suna bisa kujerun Dinning area, Aunty Juwairiyya tana zuzzuba musu abincin.
Murmushi Umaymah tayi cikin jin daɗin ganin su, da wal-wala hatta Jalal fuskarshi a sake take. Jamil ne ya kalleta lokacin data ƙara so kusa dasu, cikin murmushi yace. "Umaymah mu sai yaushe za'a nuna mana Amaryar a gabatar mata damu, ta sanmu da kyau". Murmushi Ummi tayi tare da cewa. "Ai ku tun daren jiya nagabatar da sunayenku da matsayinku gareta". Haroon ne ya ɗan kurɓi tea tare da cewa. "Yo ai Ni dai ba sai an gabatar daniba, domin nasanta tun safiyar jiya kafinma a ɗaura auren ko Jalal?". Taɓe baki Jalal yayi tare da cewa. "To ni mamaki nakeyi, ko dai dama ita tazone dan taga wanda za'a aura mata". Umaymah ce ta ɗan zauna kusa da Jafar tare da kallonsu kana tace. "Babu sam ita kanta bata saniba bata zata ba bata tsammaci aurenta a jiyaba. Sai dai arashi kukayi, Ni tun jiya da kuka gayamin nasan arashi ne kawai ya haɗaku a asibitin. Bata san komaiba akan auren nan hakama iyayenta, basu da zaɓine kawai dan sun san ƙa'idar gasar Shaɗi ne hakan yasa sukayi haƙuri." Kai Jalal ya jinjina tare da cewa. "Uhummm mu dai yanzu yan kallone. Dan na sani tabbas yanzu za'a fara buga Game ɗin yanzu wasan zai soma". Cikin yin ƙasa da murya Jamil yace. "Sosai ma, dan kuwa akwai kitimurmurar da za'ayi a masarautar Joɗa, wannan Ustaz Sheykh Malam akarmakallahu Hamma Jabeer ɗin, salonshi na dabanne a dukkan lamuran yauda kullum wannan auren dai zamuga ya zai kasance!". Ya ƙarishe mgnar da yin ƙasa da murya sosai, yanayi kuma yana kallon hanyar falon Sheykh Jabeer. Cikin haɗe fuska na wasa Umaymah tace. "Al'khairi shine zai wanzu". Murmushi Haroon yayi tare da cewa. "Inafa al'khairi a wannan abun da bashi da tushe, ni kaina naji baƙin cikin wannan al'amari, auren Muhammad Jabeer ya zama kamar a munafuce a ɓoye babu wani shiri bare kimtsi kun bari an auro mishi mace kamar auren ƴar tsana". Jafar kam abincinsa yakeci, ba tare da ya kulasuba. Jamil kuwa sai murmushi yakeyi. Jalal kuwa shiru yayi alamun nazari.
Ummi kuwa ware wasu kyawawan Foodflaks takeyi gefe. Tare da abinci a cikinsu.
Bayan ta gamane ta ajiyesu gefe. Tare da cewa Umaymah. "Ga breakfast ɗin Sheykh". Kai Umaymah ta gyaɗa mata.
Nan sukaci gaba da hira.
A can Side ɗin Mama kuwa, Tunda batun auren Jabeer ya basu ya riski kunnuwan ahlin masarautar Joɗa, kowa da abinda ke ransa.
Batool kuwa hankalin Mama in yayi dubu ya tashi, bisa irin kukan da Batool ketayi har cewa takeyi ta gane ai dama Mama bata son ya aureta. Da kyar ta samu tasha kanta,
Gimbiya Saudatu kuwa, da Baba Nasiru da Baba Basiru da Laminu. Zaman gaggawa suka tanada.
Suna tattauwana wannan baƙin lbrin da bai musu daɗi ba.
Zaune yake gaban wani ƙasurƙumin boka matsafi. Cikin tsantsar tashin hankali da kiɗima yace. "Boka Tsitaka haka mukayi da kai? Yaushe ka fara min ƙarya kan aiyukan da nake baka? Ya za'ayi kwatsam rana tsaka ace wannan shegen yaron da nakeji tamkar in kasheshi yayi aure? Da kai mukayi mgna a nan tsawon shekaru kace min ka, kashe min wutsiyar ɗan iska mai jajayen kunnuwa, babushi ba mace har yaumal ta ƙunun nadi. Ka bani tabbacin. Har gobe sihirin na bibiyarshi, kace min duk sanda zanen kan macijin ya isa kan tsaitin ƙahon zuciyarshi zai mutu kowama ya huta. Sai kuma jiya kamar sauƙan aradu ace yayi aure!". Wata iriyar razanenniyar dariya mara daɗin amo boka Tsitaka ya kece da ita, wanda har saida tsaunuka da kwazazzaban dake wurin suka amsa amonta. Dariyar mugunta yakeyi babu ƙaƙƙautawa, har saida baƙon nashi ya fara hatsala cikin tashin hankali yace. "Wannan ai insakanci ne, in bazaka iyaba ina nemo wasu matsafan. Ya zan zo da matsalata da sanyin safiyar nan kai kuma ka kama min dariya, Ni mahaukacin gidanku ne?". Cikin dariyar boka Tsitaka yace. "To ai tashin hankali na banzane, kana kokonto kan aikin da shekaru goma sha biyu yana cinsa yana bin jikinshi. Kana zaton ya karye ne? To bari kaji wannan sihiri yana nan a jikinshi, har kwanan gobe wutsiyarsa bata harbawa, baya jin kanshi a namiji. Ba kuma zaiji yadda maza kejiba har abadan. Iya bincikena banga mai mgnin da zai gani aikin da mukayi mushiba. Auren da akayi mishi, da ya sani tabbas da zai watsa abun. In kuwa kana zaton sihirin yana sauƙa kaje ka dubu, zanen bindin maciciyar da yake tun daga kan ƴar babbar ƴatsar ƙafarshi ta dama, zaka samu kan macijiyar ya ƙetare ƙugunshi. Na kuma gaya maka duk sanda kan macijiyar ya isa kan ƙirjinshi, saman nononshi, zai mutu, kuma yadda zai bar duniya haka ƙannenshi da wanshi zasubar masarautar Joɗa har abada yadda ba'a tambayi yaushe matacce zai dawo duniyaba haka suma baza'a tambaya ba." Cikin ɗan jin daɗi baƙon bokan yace. "To ai dole hankalina ya tashi, kaida kace min bazai wuce shekaru biyar ba zai rasu gashi yanzu shekaru goma sha biyu bai mutuba". Cikin zare ido boka Tsitaka yace. "Kai ai mun ma yi dacen yin asirin da wurine, tun kafin ya gama girma da yanzune sam bazai kamashiba, mutumin da baya rabuwa da sunan Allah a bakinshi. Yaronda ko yaushe da al'wala yake zama, ai badan hakaba da tuni mun hallakashi". Cikin ɗan samun nitsuwa baƙon ya direwa Boka Tsitaka kuɗi kana ya miƙa ya fice.