Kenza eBookz

Garkuwa complete Novel - Chapter 36

Garkuwa complete Novel - Chapter 36

Garkuwa complete Novel Chapter 36: Garkuwa complete Novel Chapter 36. Gaba ɗaya wunin yau aiki Ummi da Shatu da Saratu suka wuni yi, wanda aikin salla ne.…

4,390 words

Gaba ɗaya wunin yau aiki Ummi da Shatu da Saratu suka wuni yi, wanda aikin salla ne. Zabbin da Jalal ya kawo bisa umarnin Hammansun. Da kuma kajin da Lamiɗo yasa aka rabawa al'ummar masarautar Joɗa. Ko wani Side in dai akwai mace kaji goma ake kaiwa. Da tarin kayan miya komi da komi, wanda shi cikin lambun masarautar ake cirewa. Kajin kuma daga gidan Gidan gonar MJ aka kawo, kana zabbin da aka kawo manyan sashin Masarautar Joɗa ma daga gidan gonar MJ aka kwasosu. Haka ƙoyayen kaji. Duk an rarraba ko ina. kuma duk saida aka yanka su aka gyarasu aka rarrabusu, dan haka aiki kawai aka fara babu kama hannun yaro. Hadimai da bayi sunata aiki.

Duk sauran ɗinku nan suma sun dawo.

Kasan cewar kusan a kitchen ɗin suka wuni ne, yasa Shatu ta ɗauki zabbi uku tun da azahar tayi musu gyara na musamman. Hibba kuwa tana Side ɗin Aunty Juwairiyya anayi mata zanen lalle.

Akan sai dare za'ayiwa Shatu shiyasa taketa kimtsa aiyu kanta da wuri. Dama sunje da sassafe an wonke musu kai an gyara musu.

Ummi kuwa tayi lallenta na gargajiya tana kwance a falo. Hakane yasa Shatu ta kira Gimbiya Aminatu. Cikin wasa tace. "Gimbiya a ƙaro min mai taya aiki yau Ummi na tasa lalle, Hibba ma tana can ana zana mata, nida Sara ce kaɗai a kitchen." Dariya Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa. "To Sayyadar Sheykh bari Larai tazo". Cikin jin daɗi tace. "To Gimbiyar Lamiɗo". Dariya sukayi duka kana sukayi sallama.

Juyowa tayi ta kalli Ummi tare da cewa. "Tace zata turo Larai, Ummi ta iya aiki ko?". Kai ta gyaɗa mata tare da cewa. "Sosai ma kuwa". Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa kana ta miƙa wa Ummi wayarta tare da cewa. "Ummi sai mun nitsu ki bani number Gimbiya Aminatu". To tace kana ta koma kitchen ɗin.

Wanke zabbin tayi fes tare da ɗan matsa lemun tsami kaɗan a ciki. Kana ƙara lallaɓeshi. A tukunyar ƙirar ƙasar Cameroon ta zubasu. Kana tasa al'basa, Curry, Maggi, kanamfari, citta, tafarnuwa kaɗan, da gishiri ɗan ƙanƙani. Ta rufe tukunyar da zabbin uku suka cikashi.

Bisa gas ta ɗaurashi kana tasa wutan dai-dai.

Saratu kuwa sa sauran tayi a babbar tukunta tasa kayan ƙamshi da ɗanɗano. Sannan ta ɗaura.

Dai-dai lokacin Larai ta shigo. Bayan sun gaisa ne, ta ɗauki markaɗen waken ƙosan da zasuyi na kaiwa masallaci.

Da markaɗen tattasan da taruhu da al'basan.

Ita kuwa Shatu yau kunun basise ta dama mai kyau, ta cika kulolin. Kana Ta daura ruwan tea Yana tafasa ta ɗura a flaks.

Duk wannan zabbin sunata sulaluwa suna bararraka sai wani irin masifeffen ƙamshi da yake tashi. Har yawunsu na tsinkewa.

Fruits ta ɗebo a Fridge ta gyarasu ta shiryasu a tray biyu shiri mai kyau. Kana ta medasu cikin ƙaramin Fridge ɗin data kashe dan sanyi su ya daidaita.

Larai na dawowa, suka fara suya.

Ita kuma ƙullun waken kaɗan ta ɗiba.

Kana tasa dafaffan ƙan data ɓare. Da al'basan da kifin data tafasa ta murmusa a cikin ƙullun ta sa mai da Maggi curry da dai sauran kayan haɗi ta kulla alala. Ta ɗaura a gefen tukunyar zabbin.

A ƙalla awa ɗaya zabbin na ɓararraka kana tazo. Tasa jajjagen taruhu da al'basan, A ciki. Sai ta ɗan tarfa soyayyan mai kaɗan a ciki ganin kamar man jikin zabbin bazai mata yadda takeso ba. Kayan ɗanɗano ta kuma sawa, da yankekken al'basa mai yawa ta zuwa a ciki. Kana ta maida marfin tukunyar ta rufe. A hankali danderun zabbin ya fara taushi yana lugub cewa, Ƙasusuwan suna saɓulewa daga jikin naman.

Tuni su Sara kuma sun gama soya ƙosan, nan ta ciccika kulolin da za'a fidda kana ta ɗiba musu nasu, daban. Sannan suka tattare mata wurin suka tafi sabida ita ta kusa gama nata aikin.

Koda alalan ya nuna ta kwashe tasa a kuloli biyu. Sai kuma ƙaramar kula daya.

Ya rage zabbin ne kawai a wuta. Rage wutan tayi sosai yadda zasuke jin wutar na ratsasu da kyau.

Tattare wurin tayi ta kimtsa komai. Kana ta fito falo. Ƙarfe biyar da rabi. Tace lokacin data zauna ta ɗauki wayarta Ummi kuwa na cire lallenta. Ya kuwa yi baƙi yayi kyau. Hibba ce ta shigo cikin Langwaɓe kai tace. "Aunty Shatu me ake dafa mana yau tun waje can ake jiyo ƙamshin na fitowa a gidanki". Cikin gajiya tace. "Tuwone miyar taushe". Cikin zumbura baki tace. "Tab wlh bazanci ba, inyi azumi a bani tuwo ta yaya zan haɗiyeshi, yaseen zan koma wurin Aunty Juwairiyya nagama tayi awara, ƙamshin gidanki na jiyo na gudo". Dariya Ummi tayi tare da cewa. "Hibba dai cokali a saki a daɗi ko?". Murmushi sukayi dukansu kana suka konta A kan kujerun. Ganin Ummi ta miƙene yasa Shatu cewa. "Yauwa Ummi duba mana kitchen ɗin kiga ko Danderun yayi". To tace kana ta shiga ta duba. Sannan ta fito tare da cewa. "Yayi sosaima, kai gskyar Hibba nima da bana jin ƙamshi yau naji ƙamshin girkin. Jeki sauƙe kawai kiyi wonka kuzo ki huta kafin a kira salla". To tace kana. Ta miƙa taje ta sauƙe. Binta a baya Hibba tayi tare da cewa. "Wai Aunty Shatu bakuga lallena bane banji kunce yayi kyau ba". Murmushi tayi tare da cewa. "Kayya Hibba ai yanzu kam idanunmu basa gani". Ta ƙarshe mgnar tana sauƙe tukunyar, Kana ta ɗauki Foodflaks guda uku biyu manya ɗaya karami. Gaba ɗaya ƙasusuwan sun saɓule. Romon yayi kaurin diddigin nama. Rabin zabuwa ta sawa Sara da Larai a ƙaramar kular. Kana tasawa Gimbiya Aminatu gudar. Su kuma tasa musu ɗaya da rabin a kularsu. Kular datasa alala data kosai ta jere a babban tray'n. Da tray'n fruits, ɗin a gefe. sannan da flaks ɗin kunu ta bawa Hibba tare da cewa. "Ki kawai Gimbiya Aminatu. Na ƙaramar kular nasu Sara ne". Amsa tayi kana ta fita.

A can ta samu Ya Jafar shida Lamiɗo bisa alamu yau tare zasuyi buɗa baki.

Ita kuwa Shatu Hibba na fita. Ta sauƙe babbar tukunyar tafashen naman kajin ta ajiye gefe. Dama zabbin duk a freezer'n suka sasu.

Ɗan buɗe bakin tukunyar tayi yadda zasu sha iska su kama jikinsu. Jajjageggen Attaruhu da al'basan kuma ta sashi a Fridge.

Kana ta fito da komai ta jere musu a dinning table.

Sannan ta wuce ɗakinta. Wonka tayi da ruwan sanyi duk da bata son sanyi To amman duk jikinta huruwa yake tamkar wuta. Haka yasa tayi da ruwan sanyi. Tana fitowa ko mai bata shafa ba. Wata atamta mai taushi riga da zani, ɗinkin Borno sitayel yayi masifar yi mata kyau. Ɗan kwalin ta ɗaura a sauƙaƙe sabida duk jikinta rawan yunwa da azaba yakeyi.

Cikin falon ta fito nan ta samu Hibba ta dawo. Jalal, Jamil, suma sun zo. Ummi ma ta fito da alamun tayi wonka.

Tana isa ana kiran salla. Nan sukayi buɗe baki da fruits kawai sai kunun suka ɗansha, kana kowa yaje yayi sallan. Sannan sukazo sukaci sauran kayan kwalamarsun.

Suna tashi sukayi sallan isha. Zuwa lokacin kuma anata raɗe-raɗin ba'aga wata bafa. Wannan lbrin shiya tada hankalin Hibba da sauran mutane irinta, a gefe harma da Jamil Sabida azumi ɗayan nan da za'a ƙara wasu ganinshi suke kamar shekara ɗaya za'ayi ana azumin sai kaji anata gunaguni da cewa wai anƙi a faɗa ne. Shatu kuwa murna tayi dan ita bata samu tayi lalle ba. haka yasa gobe zata ƙarisa aikinta a nitse. Jin an kira salla za'ayi Asham ne yasa Hibba zubda hawaye tare da cewa. "Wlh zan kira Umaymah da Hamma Jabeer ina dai saudi sunyi salla Ni babu ruwana salla zanyi". Ta ƙarishe mgnar tana kiran layin Umaymah yanata ringin ba'a ɗagawa. Hamma Jabeer kuwa data kira baya shiga ma gaba ɗaya. Haroon kuma shima yana shiga baya ɗagawa. Dariya Shatu tayi tare da kunna tv tace. "kalli Hibba suma asham sukeyi". Da sauri tace. "A a kam Isha'i ne". Ganinfa da gaske Hibba keyi yasa suka sherata sukaje sukayi asham kana suka dawo. Kitchen suka shiga, soya kajin sukayi suya mai kyau kana suka ajiye. A gefe. Jalal ne ya leƙo kitchen yace. "Ummi azumi talatin zamuyi bana". Dariya tayi tare da cewa. "Aiko gacan Hibba nata fushi." Shigowa yayi plate ya ɗauka ya miƙawa Shatu tare da cewa. "Aunty a samin nan". Amsa tayi tare da saka mishi soyayyen naman kazan. Dakekken yaji ta saminshi a gefen Fridge ya buɗe ya ɗauki Du-du tare da cewa. "Wannan fa yaushe aka fara kawoshi". Ummi ce ta kalleshi tare da cewa. "Naga Shatu tafi sonshi ne yasa nace akawoshi". Kai ya gyaɗa tare da cewa. "To nima bari in taɓa shi". Nan ya fita falon.

Su kuwa suka ƙarisa aikin. Suna ƙoƙarin fitowa ne. Jamil ya leƙo tare da cewa. "To yau kuma meye za'ayi mana na sahur ne". Jalal dake bayanshi ne yace. "Yo azumi ɗaya ai ko tazarce zamuyi". Hararan Jalal yayi tare da cewa. "Hege daka ci kaji kayi tak ba, mutun kamar kura". Murmushi Jalal yayi tare da cewa. "Yes naci in kuma ƙara". Hararanshi Jamil yayi tare da cewa. "Mutun sai son nama kamar ba bafulatani ba sai kace babarbare". Da sauri Jalal yace. "Yo dama aini Arbabarbare ne". Dariya Ummi tayi, Ita kuwa Shatu Jalal ta kalla tare da cewa. "Me zan dafa mana to?". Tsaki ya ɗan ja tare da cewa. "Kiyi mana Coucous da miyar hanta kawai". To tace kana ta juya ta fara aiyin. Cikin sa'a ɗaya ta gama ta fito.

A falo ta samesu suna. Waya da Sheykh yana ce musu kadafa suyi sakaci suyi sallan, dan babu lbrin ganin wata.

Hakan dai suka haƙura. Bayan yaga waya da sune. Umaymah ta shigo ta sameshi zaune yanacin inabi. Gefenshi ta zauna da wata jakar. Miƙa mishi tayi tare da cewa. "Kace ranar salla da safe in an sauƙo idi dai zaku tafi ko?". Kanshi ya gyaɗa tare da cewa. "Haka dai Wannan tsohon Galadiman ya buwayeni da zancen komawar". Murmushi tayi tare da cewa. "Abbanka ma yace min ranar sallan zaku tafi". Kai ya gyaɗa. Ita kuwa gyara zama tayi tare da cewa. "Tsarabar me ka sayawa Shatu da ƴar ɗakinta Hibba". Da sauri ya kalleta tare da cewa. "Umaymah tsaraba kuma. "Yo tsarabar me zanyi sai kace wani sabon zuwa, Ni ibada nazo yi ba tsaraba ba". Jakar ta nuna mishi tare da cewa. "To ni kam ga tsaraba ka kai musu, wannan na Shatune Hibba gobe zan dawo da nata. Kai kuma in kaso ka koma hannu rabbana". Kanshi ya sunkuyar kamar baijiba. Sai kuma tace. "Jazrah tace in gaidaka, wai tunda kazo bata ganka ba". Cikin sanyi yace. "Yoh dama ya zanyi in bari ta ganni yarinya sai kallon masifa". Miƙewa Umaymah tayi ta fita. Tana fita Haroon da Ya Hashim suka shigo. Nan suka ɗanyi hira kafin suka tashi suka tafi masallacin dan shabiyu ta kusa a fara tuhajjudin.

Nan suka tafi. Washe gari aka tashi da azumi na talatin. Allah cikin ikonshi aka kaishi lfy. Watan Shawwal ya baiyana Ramadan ya tafi kuma sai mai nisan kwana.

Shatu kuwa a wunin ranar Yar aikin Aunty Juwairiyya Sato, ta zana mata jan lalle mai ɗan karen kyau.

Koda ta dawo kuma jarakuna madarar shanu data gayawa Gimbiya Aminatu tanaso Aka kawo mata ta tafasashi kana tasashi a manyan kware da ƙananan kwore da kyawawan robobi tasa tsami kaɗan a ko wanne kwarya da roba. Ta rufesh ta jerasu a Fridge a ƙalla sunfi kore goma madaidaitan ƙananan sun kai kore takwas sai robobin su kuma sun kai goma suma.

Bayan sallan magriba ansha ruwa anyi nak. Hibba sai tsalle da farin ciki da kiraye-kirayen ƙawaye da yan uwa da abokai sai tsiya Jamil ke mata.

Bayan sun gama shirya komai na aikin da zasuyi gobene. Suna zaune a falo Ummi ta kalli Jamil tare da cewa. "Jamil wai sai yaushe zaka share Side ɗin Sheykh ne, munyi waya da Umaymah ɗazu tace min gobe fa zasu dawo. Anayi sallan idi a can zasu taso". Gyara zamanshi yayi tare da cewa. "To naga mutun ga matarsa ace Ni in mishi shara". Ko inda suke Shatu bata kalla ba. Ummi kuwa jingina tayi da jikin kujera tace. "Ai bazata san ƙaidar yadda yakeson a gyara mishi ɗakinshi ba. Dole sai ka nuna mata." Cikin gamsuwa da hakan yace. "To ba matsala sai gobe da sasafe mu hau kan aikin abinda ɗakin ba wani ƙura da tarukucene da shiba". Eh hakane Ummi tace tare da kallon Shatu tace. "Gobe in Allah ya kaimu Shatu ku gyara mishi ɗakin nashi". "To Allah ya kaimu. tace ba tare da ta kalli inda sukeba.

A can ƙasa mai tsarki kuwa. Ana idar da sallan isha'i da yawa suka fara ɗawafi. A cikinsu kuwa harda Sheykh Jabeer da mai sunanshi kana da Haroon A nitse bisa tsari suke ɗawafin sunje ƙafa biyu ana uku sun isa dai-dai. Maƙama Ibrahim. Sheykh Jabeer ya juyo kanshi ya kalli gefen damanshi da sauri cikin tarin mamaki al'ajabin Fuskar mutumin da ya ga ya wulgawa a idonshi...!

Littafin GARKUWA na kuɗine idan kina buƙatar saya ga number 09097853276 katin mtn na ɗari uku. Normal group in kuma special Group kikeso 1k zakiyi min TRANSFER ta ac ɗina 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.

By *GARKUWAR FULANI* 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*GARKUWA* NA

*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🐄🕊️🌈🦚🐍🤴🏻💘

ASSALAMU ALAIKUM. MASOYA NA MAKARANTA LITTAFIN GARKUWA, WAƊANDA SUKA BIYA DA WAƊANDA KE KARANTA NA SATA, INA MUKU FATA ALKYAIRI da fatan muna lfy, kana kuma ina mai bawa dubban mutanen da sukayi min mgn ta kafafan sadarwa kamarsu, WHATSAPP, FACEBOOK, INSTAGRAM, WATTPAD, BAKANƊAMIYA, WASUMA A TIKTOK daga jiya da yamma zuwa safiyar yau haƙurin rashin basu amsar tambaya ɗaya dai da aketa memeta min. GARKUWA WAI KIN SAIDAWA ƳAN HAUSA FILM LBRIN GARKUWA? WAI DA GASKENE BAZAKI ƘARASA MANA LITTAFINBA? TO DUK GA AMSARKU NAN. Alhamdulillah, ngd matuƙa da kulawarku. Kana ina mai baku tabbacin EHHH TABBAS NA SAIDA LITTAFIN GARKUWA GA ƳAN HAUSA FILM KAMAR DAI YADDA KUKAGA YAKETA YAWO, TABBAS NA SAIDASHI WA ƊAYA DAGA CIKIN MANYAN INDOSTIRI. DA IZININ UBANGIJI ZASU JUYASHI ZUWA FILM MAI ZAMAN KANSHI, IN LOKACIN YAYI KUMA ZAN SANAR MUKU. DA FARI NASO IN SIRRANTA ZANCEN NE, SABIDA SEDA MUSU DA NAYI BAWAI YANA NUFIN BAZAN ƘARASA LBRIN GARKUWA BANE, ZAN ƘARASA MUKUSHI HAR ƘARSHE DA IZININ UBANGIJI. TO SAI DAI NAYI MATUƘAR MAMAKIN YADDA AKAYI MGNAR TA FITO FILI TA BAIYANA HAR TA BAZU, domin naso barinta sirrin kai da kaina sabida gudun kada hankalin makaranta na ya tashi. To amman ba komi ku kwantar da hankalinku masoya na zan ƙarasa GARKUWA lfy lau. Kana suma ƴan film zasuyi abunsu lfy lau. Duk wacce ta/ya sayi littafin GARKUWA sun san uzurina da yasa kwana biyu bana Update, so ku kwantar da hankali ku, in sha Allah ni AYSHA ɗiyar ALIYU GARKUWA, Jikar Malam Muhammad Babayo mai Murare. Zan ƙarasa mukushi lafiya in Allah ya aramin rai da lfyar. KUYI HAƘURI WAƊANDA SUKAYI MIN MGN TA PC BABU TABBACIN ZAN BIKU ƊAYA BAYAN ƊAYA IN BAKU AMSA.

FATAN AL'KHAIRI MASOYANA MAKARANTA LITTAFIN GARKUWA WAƊANDA SUKA BIYA DA WAƊANDA KE KARANTA NA SATA🤝🏻😘🥰😘🥰😘. Dan naga masu karanta na satan ƙarfin halinsu yawa gareshi, har ƴar guntuwar nasiha sukemin wai kada in zalinci mutane na fara musu ban ƙarasa ba🤣🤣😂. Ɗan Adam kayan Allah ana ɗauke damu muna ɗauke da halayenmu🤗🤗🤗🤗.Cikin sassarfa bisa tsarin addinin yaci gaba da ɗawafin. Yana mai bin bayan tawagar mutanen da yaga fuskar wannan mutumin a cikinsu. Idonshi yaketa karkasawa amman ina ya kasa sake ganinshi. Zuciyarshi nike da mamaki. Haka yaci gaba da ɗawafin. Saida sukayi. Kana suka fito. A hanyarsu ta komawa gidane ya haɗu dasu Jannart da Jazrah da Umaymah da Sitti da kuma Aunty Hafsat ƙanwar Umaymah dake ƙasar Masco. nan Aunty Hafsat tayi ta sayan kayan tsaraba tana bawa Sheykh wai a kaiwa surkarta. Dan dole ya amsa sai kuma Aunty Rahma ƴar autar Sitti itama a gaban Aunty Hafsat ta girma. Kuma sa'ar Sheykh Jabeer ce shiyasa akwai yar tsama a tsakaninsu. Cikin hausarsu data fara basu wuya tace. "Ba dai kayi auren sirri ba, in sha Allah zanzo zamuzo auren Haroon zamuga amaryar, inga surkar tawa ya take"

Taɓe baki yayi tare da cewa. "Ke tafi daga nan da Allah ki bar manya suyi mgna ba irinki ba". Murmushi Umaymah da Aunty Hafsat sukayi dan sun san tsamarsu. Kuma suna masifar shiri. Ammi suke kiranta ita Aunty Rahman.

Jazrah kuwa hakanan take jin daɗi in ta ganshi. Shiyasa taketa murmushi. Haroon kuwa girarshi ya ɗagawa Jannart tare da cewa. "Wai auren ya kusa ko?". Cikin jin kunyar Umaymah tace. "Ban saniba." Haka dai sukaci gaba da tafiya.

Washe gari da safiya. Duk kan al'amur musulmai na duniya suna farin ciki da ranar salla. Manya da yara tsoffi maza da mata duk anata shirin zuwa idi. A dukkan ƙasashen duniya a ko wani saƙon da suke da musulmai.

Hakace ta kasance a ƙasashen Afrika ma. Wanda ciki ƙasar Nigeria yake. Tun daga idar da sallan asuba. Saratu da Larai sukazo. Nan suka samu Ummi da Shatu suna kitchen. Its Ummi fura take kirɓawa mai ɗan karen laushi da ƙamshi yaji sugar. Ita kuwa Shatu dakkeren Couscous tayi, dambu inji hausawa. Bayan sun gamane suka killace shi gefe.

Kana ita Shatu. Ta haɗa kajin nan tayi Pepper Checken mai ɗan karen kyau yaji jajjagen taruhu da al'basa mai yawa ga kayan ɗan-ɗano dana ƙamshi sunji komai yayi maɗau. Su Sara kuwa robobi ta miƙo musu, suka rinƙa mulmula gumbar nan manya manyan mulmulellen masu kyau sai sheƙi da ƙamshi gumbar keyi, dakkeren kuma a robobi Ummi ta rinƙa zubasu. Hibba ce data shigo tare da kuloli a hannunta tace. "Wow Aunty Shatu lallai yau masarautar Joɗa zata amsa sunanta masarautar Fulɓe zata kuma gane an auro mata cikekkiyar ba fulata, gsky tsarin yayi kyau". Cikin jin daɗi Ummi tace. "Gsky nima naji daɗin wannan abu. Dama ace ko wanne yare ranar salla tayi abincin da yarenta keyi ta rabawa maƙota. Hakan zaisa asan cimar juna, kuma yasa aci abincin salla da marmari, amman kayan haushi duk sai a tafi kan shinkafa taliya masa, da dai ire-iresu. Su kuma akeci kullum". Murmushi Shatu tayi tare da cewa. "Ha Ummi ai yanzuma sai nayiwa su Jalal koda dafadukan taliyace, nasan zasuce wannan ai sai mu". Da sauri Hibba tace. "Tab wlh Aunty Shatu karkiyi komai, kinga yanzuma an kawo abincin gidan Barrister Kamal. Ga kuma na gidan Aunty Juwairiyya. Sannan kuma Gimbiya Aminatu ma zata aiko". Cikin sauri tace. "Allah ko Ummi mu huta kawai kenan?". Da sauri tace sosaima. Dan duk yawanci sai an kawo abinci nan wai tunda ke baƙuwace, wannan karamawar masarautar Joɗa akan bago. Kuma koda kin dade ana aikawa juna abincin salla part 2 part". Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa. "Shike nan mu haɗa wannan a kai ko wanne sashin". Ta ƙarishe mgnar tana rufe ƙatuwar Foodflaks ɗin da ta juye Pepper Checken ɗin. Bayan ta ɗebawa sashin Ya Jafar da kuma Lamiɗo da Hajia Mama.

Ƙananan robobin da a ƙalla suma nonon dake cikinsu zai kai kwanon sha ɗaya da rabi ta fara firfitarwa. Kana ta fito da madaidatan ƙoren da zasuci kwanon sha biyu da kaɗan sai manyan da sukaci kwanon sha uku da rabi-rabi. A hankali ta jerasu kan table ɗin dake tsakiyar kitchen ɗin. A hankali ta buɗe ƙwaryar forko dake gabanta. Wani irin murmushi tayi tare da cewa. "Alhamdulillah kunɗirmo ya konta yayi bacci yayi kyau". Leƙowa Ummi tayi tare da buɗe na kusa da ita. Nonon yana konce yayi lib ya daskare yayi fari ƙal-ƙal sai alamun maiƙon man nonon da yayi ɗan yellow-yellow kaɗan. A hankali suka fara bubbuɗe fefeyayen tsakan zaren taburma da aka rufe ƙoren dashi. Gaba ɗaya duk sun konta sunyi kyai Yan madaidai robibin da akasa take ɗauka na fura ɗaya na dakkere ɗaya sai na sugar ɗaya kana da ludayin duma. Sai ta jerasu kan fefeyayen da robobin. Ganin haka yasa Saratu da Laraima suka matso suna taya. Har saida ta jerasu kab. Gwanin sha'awa. Manyan ƙore biyu ta maida cikin Fridge. Kana ta irga sauran tsakanin manya da ƙananan Ƙoren da robobin su Talatin da tara Juyowa tayi ta kalli Ummi tare da cewa. "To Ummi gashi mun gama ki gaya musu duk inda zasu kai. Zasu isar ko". Cikin jin daɗi Ummi tace sosaima kuwa harma da sashin bayi zai isa sabida part-part talatin garemu a cikin masarautar Joɗa. Sai sashin bayi part takwas. Cikin jin gamsuwa da tsarin Shatu tace. "Yanzu a kai ƙore biyu sashin Lamiɗo kana duk manyan iyayen Sheykh akai musu kwarya ɗaɗɗaya, sai sashin Ya Jafar kinga manyan ƙoren sun ƙare sai abin na tsakiyan a kai sauran sashin ƴaƴansu robobin kuma akai sashin bayi".

Haka kuwa akayi su Sara suka fara rabawa. Ita kuwa Ummi ita da kanta da Hibba suka kai na sashin Gimbiya Aminatu. Kana suka dawo da kuloli har uku na abincin sallan da Gimbiya Aminatu ta basu. Kana ɗaya daga cikin tace na Sheykh ne a ajiye mishi. Koda suka dawo samu sukayi su Saratu sun gama rabawa kab. Kamar yadda Ummi ta tsara. Har sun tattare ko ina sun gyara sun share sun goge sun tafi. Zuwa lokacin kuwa gaba ɗaya kan dinning table ɗinsu cike yake da Foodflaks iri da kala abinci kala-kala. Wani irin kallo Shatu tayiwa kulolin kana tayi murmushin da ita kaɗai tasan ma'anarsa ta juya ta nufi tsakiyar falon.

A gaggauce sukayi wonka kowa yayi shirin idi. Ƙarfe tara saura kwata duk suka fito falo. Tuni lokacin kuma liman har ya fara huɗuba. Su Jalal, Jamil Ya Jafar suna tsaye cikin shiga ta al'farma. Karon forko dataga manyan kaya a jikin Jalal. Sai kamanninshi da Hamma Jabeer ɗin nasu ya fito sak-sak kamar an tsaga kara hatta rashin yawan dariyarsu iri ɗaya ne. Sai dai shi Sheykh ko yaushe zakaga lips ɗinshi na motsawa yana tasbihi saɓanin Jalal da zaka ganshi baki a tsuke.

Hibba ce ta fito cikin tarin farin ciki da son Jalal yayi murmushi tare da cewa. "Masha Allah ya Jalal kayi kyau kafisu duka". Ya Jafar dake karatu kamar ko yaushene ya kalli Shatu da Hibba da sukayi shigar atampa iri ɗaya da manyan hijabai har ƙasa ga sallaya da carbi a hannunsu sunyi matuƙar kyau, murmushi yayi musu kana ya juya yayi gaba. Jamil ne yace. "Aunty Shatu sai mun dawo, in munci abinci sai mu sharewa. Oga, Dr, Garkuwa, Malam, akarmakallahu, Sheykh, mijin Sayyada, ɗin ɗakinshi". Dariya sukayi dukansu yadda ya jero masa sunayen nashi. Ummi dake cikin shiga ta al'farma ta miƙa tare da cewa mu tafi.

Suna fita suka rufe ƙofar.

Suka tafi masallacin. Masarautar Joɗa ɗan yin sallan idi. Suna fita su mata sukayi gefen mata su kuwa maza sukayi gefen maza.

Bayan an idar da sallane kuma sai suka zagaya suka shigo ta asalin ƙofar sukayi yadda sunna ta koyar.

Suna dawowa kuwa a falo suka zube nan sukaci suka sha sukayi haniƙan.

A dai-dai lokacin kuma su Sheykh dama sauran al'ummar Annabi duk an sauƙo sallan idi. Suna ɗawafin ban kwana. Sosai Sheykh ke baza ido ko zai sake ganin wancan mutumin amman ina hakan bai samuba.

Koda suka fito daga ɗawafin ban kwana. Kai tsaye gidan Sheykh Abdulkareem suka wuce. Nan yayi musu addu'o'in komawa lfy. Kusan duk baƙin gidan a ranar suka bar gidan. Da su Aunty Hafsat ma ranar suka juya Masco hakama Ibrahim. Koda suka iso Airport kowa da inda ya nufa. A nan Ibrahim ya ruggume Sheykh tare da ɗan dukan bayanshi yace. "In Sha Allah Auren Haroon dani za'ayi". Shima Sheykh ruggumeshi yayi gam-gam tare da cewa. "Allah yasa, ina kewar rashinka a ƙasar mu". Aunty Rahma ne tace. "Kai jirgifa ba jiranku zaiba oga Sheykh". Sakin juna sukayi kana kowa ya nufi inda jirgin ƙasarsa yake.

Bayan duk matafiya sun shiga, jirgin ƙasar Nigeria wanda zai sauƙa jihar Ɓadamaya.

A hankali ya zauna. Ya Hashim na gefenshi. Kasan cewar yana kusa da window ne, ya ɗan juya yana kallon mutanen daketa hada-hadar nufar inda jiragan ƙasar su jihohinsu suke. Can cikin wasu ayarin mutane maza da mata ya hango wannan fuskar da ya gani. Sun nufi can ciki suna tafiya yankin da jiragen ƙasar Cameroon suke. Cikin tarin mamaki ya bishi da kallo tabbas badon jirginsu ya fara ƙugin tashiba da ya fita yaje ya tabbatar da fuskar dattijon da yake hangowa.

A haka dai suka ɓacewa ganinshi. Kana jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasarmu ta haihuwa.

Ana gida Nigeria kuwa cikin Jihar Ɓadamaya a Masarautar Joɗa. Zaune suke a falon. Shatu na waya da Junaidu nan yake ce mata, Sun samu sauƙi dukansu. Ance za'a sallamesu bayan salla. Kuma harda ɗinkunan kayan salla akayi musu.

Bayan sun gama waya da shine ta kira Rafi'a. Nan suka gaisa har ta bawa Ummi su gaisa. Bayan ta bawa Ummi wayarne. Jamil ya ɗan kalli agogon hannunshi a hankali ya miƙe tare da kallon Shatu yace. "Muje mu gyara Side din boss kar ya dawo ya samu da datti". Kai ta gyaɗa mishi kana ta amshi wayarta da Ummi ke miƙa mata. tare da ce mata. "Eh dan Allah Shatu tashi maza-maza kuje share wurin da kyau". A hankali ta miƙe tare da cewa. "To." Hibba ce ta bisu a baya. Jamil na gaba ita Shatu'n tana tsakiya. Hibba na bayanta. A haka suka shigo falon. Da komai na ciki yake fes-fes babu wani daddi ko ƙura ko hargitsewa, sabida an share falon safiyar yau, sai ƙamshi da sanyi ke tashi.

A hankali Jamil ya ɗan sa hannunshi tsakanin ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu sheƙin Daimond dake matsayin labulen Dinning area ɗin shi. Ita dai Shatu ido ta zuba mushi, ganin ya zaro key ɗin a cikinsu. Ƙofar bedroom ɗin ya nufa tare da cewa. "Muje." To sukace kana suka biyo bayanshi. Tana nazarin wurin da suke ajiye key ɗin. Key ɗin ya saka cikin raminshi tare da murzawa.

Da sauri Shatu ta rumtse idanunta. A hankali take jin zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. Shi kuwa Jamil tura ƙofar yayi bayan ya murɗa key ɗin ya buɗe. Wani irin masifeffen harbawa da azaban ƙarfi zuciyar Shatu tayi.

Kutsa kai cikin Jamil yayi. Tare dasa hannunshi jikin ginin a hankali ya kunna wutan ɗakin hasken ya gauraye ko ina, jikin window ya wuce ya yaye labulen tare da buɗeglass ɗin. Iskam cikin Garden ɗin dake bayan window wanda ɗawisu yake ciki. Ya buso ɗakin.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull