Garkuwa complete Novel - Chapter 37
Garkuwa complete Novel Chapter 37: Garkuwa complete Novel Chapter 37. Juyowa yayi ya kalli Shatu da ke tsaye bakin ƙofar. "Ku shigo, in nuna miki yadda…
4,447 words
Juyowa yayi ya kalli Shatu da ke tsaye bakin ƙofar. "Ku shigo, in nuna miki yadda zakiyi mishi". A hankali Hibba ta ratsa gefenta tare da cewa. "Aunty Shatu mushiga". Ido ta buɗe a hankali tare da bin bayan Hibba da kallo. Kana ta ɗaga ƙafarta da kyar ta. Taka cikin ɗakin, wani irin azabebben sarawa kanta yayi tamkar ana buga mata guduma a tsakiyar kan. Cikin rawan ƙafa ta ɗaga ƙafafuwan ta, Tayi taku huɗu zuwa biyar. Ta kusa isa tsakiyar ɗakin. Kenan. Wani irin jujjuyawa taga kanta nayi. Wasu irin ababe masu ban tsoro ta fara gani suna gilmawa cikin ƙwayar idanunta, shiyasa taketa jujjuya kanta. Ta kalli gabas ta kalli yamma ta kalli kudu ta kalli arewa. Hibba ce ta juyo tana kallonta jin Jamil nata mgna bata bashi amsaba. Cikin sauri ta matso kusa da ita ganin yadda taketa jujjuya kai, ga idanunta da suka juye suka zama kamar harari garke, kana sai Rollin ball eyes ɗin ta take da sauri-sauri. Cikin Mamaki Hibba tace. "Aunty Shatu! Aunty Shatu!!". Shiru ba amsa hakane yasa. Jamil juyo kanshi ya kalli inda suke, da sauri ya juyo gaba ɗaya jikinshi ganin. Wani irin karkarwa da jikin Shatu keyi. Hibba kuwa da ƙarfi cikin tsoro tace. "Aunty Shatu lfy kuwa?". Ita kuwa Shatu, zuwa yanzu bata jinsu bata kuma fahimtar me suke faɗa hankalinta ya juye.
Cikin wani irin layi da rawan jiki tamkar mazari ta nufi tsakiyar ɗakin.
A nan ta tsaya gis gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi. Cikin tsananin tsoro da firgita. "Hibba ta juya a guje tana cewa. "Wayyo Ummi! Ummi!! Ummi!!! Kizo zakiga yadda Aunty Shatu keyi." Ummi dake falo ita da Aunty Juwairiyya, Kamar daga sama suke jiyo muryar Hibba tana rabka musu kira cikin firgici da razani. Haka yasa Ummi da Aunty Juwairiyya miƙewa da sauri suka nufi corridor'n da suke jiyo muryar Hibba na fitowa. Kiciɓis sukayi a bakin ƙofar falon. Cikin sauri Ummi ta ture Hibba ta wuce da gudu ta nufi cikin ɗakin. Sabida jiyo muryar Jamil na cewa. "Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahuwani'imal wakil. Ummi! Ummi!! Kizoooo". Kusan a tare Ummi da Aunty Juwairiyya suka shigo. "Dai-dai lokacin kuma rawan da jikin Shatu keyi ya tsananta. Wani irin kuka tasa tare da tafiya ƙasa luuu zata faɗi
Kusan a tare Ummi da Aunty Juwairiyya suka tarota. Bisa jikin Ummi ta faɗi hakan yasa itama Ummi tayi ƙasa ta zauna.
Babu abinda suke maimaitawa sai innalillahi wa innailaihi rajiun. A kiɗime cikin tsananin gigita Jamil yace. "Subahanallahi Ummi ta sumafa". Jiki na rawa Aunty Juwairiyya ta juya da gudu babban falon ta fito tare da ɗauko goran ruwan sanyi. Kana ta juyo a da sassarfa ta nufi can.
Hibba kuwa a gigice take gayawa Jalal da Ya Jafar abinda ke faru. Da sauri ya Jafar ya tashi ya nufi can.
Jalal kuwa ya zauna dan ya lura Hibba tayi masifar tsorita.
A ɗakin nashi kuwa, Shiru ta lafe jikin Ummi kamar babu rai koda. Ummi ta yayyafa mata ruwan sanyi a fuskarta, a banza saida ta kuma watsa mata a karo na uku ne. Kafin taja wani dogon numfashi cikin sanyi da tsoro Ummi tace. "Alhamdulillah". Sai kuma ta sunkuyo kanta tana ɗan kiranta. "Shatu! Shatu!! Shatu!!!". Ba amsawa kuma bata buɗe ido ba,
A hankali ya Jafar ya zauna gefensu, karatun da yakeyi yaci gaba dayi.
Cikin sanyi ta buɗe idanunta.
Sai kuma ta yunƙura a hankali ta tashi zaune. Da sauri Ummi ta zaro ido ganin yadda idanunta suka juye a murɗe.
Ita kuwa Shatu miƙewa tsaye tayi, cikin rawan sanyi da karkarwa, ta fara zagaya ɗakin a hankali taje baki Bathroom nanma buɗe ƙofar tayi ta shiga. Jim kaɗan ta fito. Idanun suna yadda suke sai dai. Yanzu hawayene keta shatata babu ƙaƙƙautawa. A hankali tazo bakin gadon. Sai kuma kawai sukaga ta faɗa kan gadon a sune! Wannan shine tashin hankali da ba'a samishi rana. Da gudu suka kumayi kanta, cikin firgici da tsananin tsoro Ummi ta ƙara yayyafa mata ruwan. Amman shiru, haka suka tsaya cirko-cirko, shi kuwa Ya Jafar sai gashi yana karatu yana kuka kamar dai yadda yakeyi kafin a auro Shatu a masarautar Joɗa in Sheykh baya nan.
Gaba ɗaya sun birkice sunma rasa me zasuyi.
Aunty Juwairiyya kuwa itama kuka ta farayi. Jiyo kukanta da na Ya Jafar ne yasa, su Jalal da Hibba shigowa. Ganin tana can yashe kan gado a sumene yasa Hibba ma kuka. Cikin ƙarfin hali Jamil yace. "Aunty Juwairiyya Hibba kada kuyi kuka, kuja hankalin mutane nan. Gashi yau salla ba mamaki akwai mutane a cikin Garden." Cikin tashin hankali Ummi tace. "Bari inje in sanarwa Gimbiya Aminatu abinda ke faruwa, ta sanarwa Lamiɗo, sai in biya in sanarwa Hajia Mama." Da sauri Aunty Juwairiyya tace. "Eh yafi kam". Ta juya zata fita kenan sai sukaji tayi wani irin nakasheshen dogon numfashi mai sassanyan sauti. Da sauri Ummi ta juyo ta dawo jikin sanyi tace. "Shatu! Shatu!! Shatu!!!". Shiru babu amsa sai binsu da ido tayi ɗaya bayan ɗaya. Ganin hakane Jamil ya matso. Tofi ya farayi mata.
Ummi kuwa ci gaba da kiran sunanta tayi. Cikin tsoro Hibba tace. "Ummi kinga idonta ya koma dai-dai." A tare sukace Alhamdulillah. Sai kuma Ummi ta kuma kiranta. "Shatu!". A hankali tace. "Na'am Ummi". Sai kuma ta kalli inda take, kana ta juya ta kallesu baki ɗayansu, cikin mutuwar jiki ta yunƙura ta tashi. Murya a sanyaye tace. "Jamil sharan kenan ka tsaya kanata kallona. Gaya min ya za'ayi sharar". Cikin sauƙe tagwayen numfarfashi suka kalli juna, Cikin mamaki Jamil yace. "No ki huta kawai my Aunty zan share". Bata da ƙarfi a jikinta ko ta dage tace sai tayi sharar. Bazata iyaba jikinta duk a mace. Hakane yasa tace to. Hannu ta miƙa Ummi tare da cewa. "Ummi ɗan jamin hannuna mana". To tace tare da kamo hannun. Ta tsaida ita, cikin tafiyar sanɗa ta juya ta nufi hanyar fita. Binta sukayi a baya gaba ɗayansu.
Jamil kuwa dube-dube yayi a cikin ɗakin kana. Ya fara tattarewa da kimtsawa da sherawa, ya canza mishi beshit and blanket, da rigunan pillows. Kana ya goge ko ina fes Sannan ya shiga bathroom ya wonke ya goge mishi.
Su kuwa suna biye da ita har falonta. Ganin ta wuce bedroom ɗinta ne yasa Hibba da Juwairiyya suka tsaya.
Ita kuma Ummi tabi bayanta.
Ganin tana shiga ta hau gado ta kwanta ne a take sai bacci yasa Ummi ta juyo ta fito.
Can babban falon suka koma suka zauna. "Ikon Allah sai kallo wannan abu da ban tsoro da ban mamaki".
Ummi ta faɗa cikin al'hini.
Jiki a mace Aunty Juwairiyya tace. "Sosai kam wannan al'amari ya firgitani". Hibba dai sai zuru-zuru tayi da ido.
Nan sukayi ta mamakin wannan abin.
Jamil na fito shida Jalal suka tafi.
Shi kuwa Ya Jafar bayan matarsa yabi suka tafi.
Hibba kuwa da Ummi nan suka zauna. Ummi ce ta kalli Hibba tare da cewa. "Sai anjima zan kira Umaymah na sanar mata abinda ya faru".
Kai kawai Hibba ta kaɗan mata.
Ita kuwa Shatu baccin tayi mai nauyi sai kiran sallan azahar ne ya tasheta.
Su Sheykh Jabeer kuwa suna can sunata keta hazo. Tafiya awa huɗu ne zai kawosu ƙasar mun.
A hankali ta buɗe idonta, miƙa tayi tare da yin salati. Kana ta tashi zaune. Bathroom ta shiga, wonka tayi da ruwan ɗumi. Kana tayi al'wa tana fitowa. Ta zura Hijabi tayi salla. Bayan ta idarne, ta zauna gaban dreesing mirror. Simple makeup tayiwa fuskarta. Sannan ta sauya shiga, wani tattausan lace mai ɗan karen kyau da tsada tasaka duguwar rigace tayi cib-cib da jikinta. Kasan cewarta kalar pink guava da ɗigo-ɗigin mint green ne yasa tayi masifar dacewa da kalar jikinta. Gyara gashin kanta tayi ta tubƙeshi tare da kitsen jelar. Ta saketa bisa kafaɗunta. Ɗaurin asseta tayi ya zauna ɗas a kanta, tattausan gyale minti green color ta yafa a kafaɗunta. Kana ta fesa turarukan ta masu daddaɗan ƙamshi.
Sosai jan lallen gargajiya dake kan ƴan fararen yatsun hannunta yayi masifar kyau. Ga kuma zanen da akayi a saman hannun hakama ƙafafun ta, suma sun sha zanen jan lalle tayi kyau sosai, Ta fito ras da ita.
Baki ɗauke da sallama ta foto falon. Cikin murmushi Ummi ta amsa sallamar tana mai kallonta, Hakama Hibba da Ummi ta kokkontar mata da hankali taji tsoron ya ragu. Gefen Ummi ta zauna, tana kallon Hibba na ɗaukarta hoto tana cewa. "My Happiness Aunty kinyi kyau". Murmushi tayi tare da cewa. "Na kaiki ne?". Da sauri Hibba tace. "Kin fini ma". Murmushi ta kumayi tare da cewa. "Ngd matuƙa". Sai kuma ta kalli Ummi tare da cewa. "Ummi me zamuyi abincin dare". Cikin jin tausayinta Ummi tace. "A a akwai abinci harda na gobe da safe ma, yanzu kam ki huta, sai dai in akwai abinda kikeso ki gaya min in yi miki". Kai ta jujjuya alamar a a kana tace. "To Ummi a kaiwa Hadimai wani abincin kada ya lalace a banza ko". Cikin gamsuwa Ummi tace to.
A can Airport kuwa ƙarfe uku dai-dai jirgin Ahlin masarautar Joɗa ta sauƙa. Nan motoci suka kwatsosu. Suna isa masarautar ana kiran sallan la'asar hakane yasa matan cikine kawai suka shiga cikin gida su mazan. Masallaci suka wuce. Ana idar da salla kuwa fada suka wuce baki ɗayansu.
A sashin Gimbiya Saudatu kuwa wani irin dariya mai cike da masifar jin daɗi tayi tare da cewa. "Dai-dai kenan yaro zai dawo ya taradda da mummunan lbrin matarsa ta zama zautacciyar mata...!
By *GARKUWAR FULANI* "Mummunam labarin amarya ta haukace. Ai kaɗan ma kenan, kowa yaci tuwo dani miya yasha. Hegen yaro mai jajayen kunnuwan da shegen baki mutun nace masa cuta zai ce ajali, kana ce mishi cas zaice maka kulle, wannan bakin nashi mai zaro zance da inada hali dana rufeshi kirib".
Hadimarta dake zaune gabanta wacce taji cikekken bayanin abinda ya faru da Shatu a sashin Hajia Mama da itama yar rahotontace ta kamo mata. Shiyasa itama ta kawo mata rahoto. Cikin jin daɗi ta kalli Laminu dake gefe yanata murmushin jin daɗi tace. "Shiga ɗaki zaka samu kuɗi a kan gadona, kazo ka bata tukuicin wannan daddaɗan labari mai armashi". To yace kana ya miƙa ya ɗauki kuɗin yazo ya bata, tayi godiya kana ta miƙe ta fita.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu Baba Basiru da Baba Nasiru ta kira ta shaida musu abinda ya faru. Nan sukayi ta murnar abun, da shirya yadda abin zai ɗunguzuma yaci gaba.
A can su Sheykh kuwa saida aka idar da sallan isha'i kana kowa ya nufi Side ɗinsa kamar yadda sukeyi duk shekara in sunje umrah sun dawo.
A Babban falon sashin Jabeer kuwa. Ummi ce zaune bisa kujera Hibba na gefenta. suna mgn da Umaymah a wayar Hibbab nan Ummi ke sanarwa Umaymah abinda ya faru ɗazu da hantsi na firgitarwa. Cikin tarin mamaki da al'ajabi da tsoro tace. "Ummin Jabeer to yanzu ina take? Kuma ya jikin nata? Meya jawo hakan ne?". Juyawa Ummi tayi ta kalli bayanta a hankali tace. "Tana ɗakinta tunda tayi sallan isha'i ta konta, yau ko abinci babu abinda taci, tunda gari ya waye, dan koda muka dawo idi munci dukanmu amman ita ko ruwa bata shaba, kuma har yanzu babu abinda taci". Cikin fargaba Umaymah tace. "Jazlaan ɗin ya shigo wurinku ne? Ya sanine ko bai saniba?". "A a bai shigoba, eh gsky babu wanda yasan da wannan zancen duk Masarautar Joɗa, saini, da Jamil, Jalal, Hibba, Juwairiyya, Jafar. Mune kaɗai muka san da zancen". Ajiyar zuciya mai ƙarfi Umaymah ta sauƙe cikin sanyi tace. "Kada ku damu zanyi mgna da Jazlaan, kada ku gaya mishi, in lokacin saninshi yayi zai iya sani". Ta tace tare cewa. "Masha Allah gashi ma sai yanzu ya shigo". Tana faɗin haka ta katse kiran. Ta miƙe da sauri hakama Hibba cikin jin daɗi suke cewa. "Oyoyo mutanen saudia garin Manzon Allah, Barka da zuwa lfy da dawowa lfy". Ɗan gajeren. Murmushi yayi tare da ƙarasowa cikin falon. Jalal, Jamil, Ya Jafar na biye dashi a baya. Bisa kujera ya zauna tare da kallon Ummi fuska ƙunshe da annuri yace. "Barka dai Ummi na sameku lfy!?". "Lfy lau Alhamdulillah Sheykh ya kuka baro Sheykh Abdulkareem da ahlinshin. Ina mai sunanka Sheykh Jabir Ali". Cikin jin daɗin kulawarta ga yan uwan mahaifiyarshi yace. "Alhamdulillah suna lfy, Sheykh Jabir Ali yace in gaidaku gaba ɗaya".
Cikin jin daɗi tace. "Ina amsawa kuwa ngd matuƙa". Jamil dake riƙe da jakukkunan da Sheykh yace ya ɗauko a motarsa ne ya wuce dasu. Yaje ya ajiyesu a bedroom ɗin shi kana ya dawo falon.
Hibba kuwa ruwa ta kawo mishi. Murmushi yayi tare da amsar goran zam-zam ɗin yace. "Baku shanye tsohon ba Ummi ni gashi na samo sabo". Hibba ce ta ɗan kalleshi tare da cewa. "Hamma Jabeer, su Sitti ma sun dawo ne?". Kai ya gyaɗa mata alamar eh. Kana ya miƙe tare da cewa. "Ummi bari inje in ɗan huta". Kai ta gyaɗa tare da cewa. "Ai dole kam saida hutu dan gajiya da rashin bacci kam ka kwasosu dole kayi ramuwar bacci". Ta ƙarishe mgnar tana kollonshi tuni ya shiga corridor'n shiga cikin falonshi.
Dama kuma tuni ita da kanta ta kai mishi abinci a Dinning table ɗinshi.
Nan sukaci gaba da hira. Hibba na cewa. "Umaymah na ta dawo na kusa komawa". Cikin taɓe fuska Jalal ya kalleta a fakaice. Jamil kuwa dariya yayi tare da cewa. "Za dai ki gudu yarinya faɗi gskyarki". Murmushi Ummi tayi tare da cewa. "Ba wani tsoro ai na gaya mata ta kontar da hankalinta." Jafar kuwa karatunshi yakeyi. A hankali saɓanin baya da in zai karatun da ɗan ƙarfi yakeyi.
Sosai suka ɗan yi hira kana suka watse kowa ya tafi makoncinsa.
Shi kuwa Sheykh yana shiga. Ya rinƙa sauƙe numfashin gajiya tare da rage kayan jikinshi. Wonka ya shiga yayi kana yasa wasu riga da wondo masu taushi yazo ya konta. Ba tare da yasha ko ruwaba, sabida tarin gajiya da bacci. Gaba ɗaya wunin yau a zaune yayi yishi ko a ɗan tsaye. Gashi rabonsa da bacci tun jiya da safe da ya ɗanyi kaɗan kafin ya tafi harami sallan walaha.
Yana konciya kuwa yayi addu'o'in ya shafa jikinsa. Kana ya fuskanci allon majigi dake liƙe a bongon ɗakin wanda yake ɗauke da full ƙura'an. Karatu ya farayi daga ƙasa zuwa sama wato nasi. Ɗaga nan bacci yayi awon gaba dashi ko inna'alzzan bai jeba.
Ummi da Hibba kuwa suna isa falon Shatu cikin kula Ummi tace. "Kije ku kwana kinji ko Hibba babu abinda zai sameki, Bazata miki komaiba, bata da lfy bai dace mu barta ita ɗaya ba". Cikin sanyi Hibba tace. "Gsky Ummi bazan iyaba wlh ina tsoro". Cikin hikima Ummi tace. "To muje ki hau gado ku kwanta ni kuma sai in kwanta a ƙasa kam carpet ɗin. Gyada tayi cikin gamsuwa da hakan.
Haka sukayi Ummi ta kwanta a ƙasa ita kuma Hibba ta konta gefenta a ɗan tsorace.
Ita kam Shatu batama san sunayi ba, domin bacci mai nauyi takeyi.
Haka dai Ummi tai shiru saida ta tabbatar Hibba tayi bacci kana ta koma ɗakinta.
Washe gari da safe bayan Ummi, Saratu, da Hibba sun gama karyawa ne. Shatu da tunda tai sallan asuba ta koma ta konta kan sallayar sai yanzu ta fito. Tayi wonkanta fes ta ƙenƙesa ado da kolliyar ta ba irin mai ramɓatsau ɗin nan ba. Komai dai-dai tayi abunta. Riga da siket ne na Mateyal mai taushin gaske, White Coffee mai kyau. sai ɗan ƙaramin gyale ta yafa a kanta, cikin nitsuwa ta fito. A falo ta zauna tare da juyowa ta kalli Ummi dake shirya abinci a Dinning table. "Ina kwana Ummi". Tace cikin muryarta Normal. Cikin kulawa Ummi ta juyo tare da cewa. "Lafiya lau Shatu. Kin taso kenan". Murmushi ta ɗan yi tare da cewa. "Ummi meyasa baki tadani ba, kika shiga kitchen da kanki". Kai ta jinjina tare da ɗaukan cup mai ɗan girma, Tea mai kauri ta haɗa a ciki kana, ta taho inda take miƙa mata cup ɗin tayi tare da cewa. "Gashi amshi kisha, aiki kam ai saida lfy". Amsa tayi tana murmushi a hankali tace. "Lfyata lau ai Ummi kawai dai baccin ne ban san meyasa nake ta yinshi ba". Kai kawai Ummi ta gyaɗa mata, Kana ta juyo tace. "Hibba kawo mana namu abincin nan muci.
Najiyo Muryar Jamil suna zuwa, kuwa wata ƙil dasu Imran zasu zo". To tace kana ta ɗauko musu nasu Foodflaks ɗin da plate and spoons da ta kawo musu.
Jolof ɗin taliyace da kifin banɗa dasu Kabeji da karas da green beans da dai sauran kayan haɗin. Sai kuma, ferfesun kayan ciki. A plate ɗaya Hibba tasa musu, da ita kana ta sawa Ummi. Kana tasa musu fork, tare da cewa. "Bismillah Aunty Shatu sauƙo muci ko". To tace kana ta sauƙo, suka fara cin abincin. Amman ina tayi loma ɗaya sai ta kusan 4 minute bata kuma sawa a bakiba. Sai dai ta shanye tea ɗin ganin hakane yasa Ummi ta ƙara haɗa mata wani shayin. Shima ta shanye abinta fes, taliyar kuma baifi cokali biyar ba tayi.
Su Jalal kuwa suna shiga suka wuce Dinning area suma sukayi breakfast ɗin kana suka fita, sabida hidimomin salla. Domin yau za'ayi hawan daba, Jalal kuma mayene mai zaman kanshi a kan sarrafa, doki, ɗan daga Affan sai shi. Bayan Sheykh a iya sarrafa doki kab Masarautar Joɗa . Amman shi Sheykh ya daɗe da cewa shi ya girma da yin wannan sakarcin.
Su Ummi kuwa, kitchen Suka kuma shiga. Sanin yau tabbas akwai baƙi masu ɗimbin yawa da masarautar Joɗa zata amshi baƙoncinsu. Domun ƙananan sarakunan wasu garuruwanma duk zasu zo da tawagar su. Haka yasa suka shiryawa taron haiƙan ƙadaran ko wani Side dake gidan za'ayi abinci a ciccika manyan kuloli a kai fadar Lamiɗo, wani a kai sashin bayi. Kana kuma ko wani Side da baƙin su. Haka yasa su Ummi da Saratu da Larai zagewa. Sukayi abinci kala-kala kana suka ciccika kulolin aka kai fada akai wurin bayi. Sannan sukayi nasu kuma suka sassaka a Foodflaks masu ɗan karen kyau suka jera a Dinning table, tare da plate, spoons, and forks. Kana sun cika Fridge kuma da drinks kala-kala. Sun kuma yi Pepper Checken mai zafi na zabbi.
Sai kusan ƙarfe ɗaya suka gama komai, Su Saratu suka kimtsa komai kana suka tafi.
Su kuma duk suka shiga ɗaki da nufin yin wonka. Tuni zuwa lokacin Masarautar Joɗa ta fara ɗinkewa da baƙi tako wani sashin.
Sheykh Jabeer kuwa, tunda ya tashi. Ya nufi cikin Garden ɗin nan da ababen tarihin masarautar Joɗa yake.
Zazzagayawa yakeyi yana dubawa, dan tabbatar da babu wani abun da zai cutar da wani ko wata. Sabida yasan yau manyan baƙi zasu shigo ciki. A nuna musu ababen tarihi da dai sauransu.
Gefen da curin da macijiyar nan yake ya nufa. Ya dudduba ƙofofin ba hayaƙi ba komai. Sai dai in mutun ya kasa kunne zaiji sautin numfashin macijiyar ka da ƴan ƙanana kuka irin na ƙananan macizai. A hankali ya ƙara matsowa bakin curin. Cikin nitsuwa yayi gyaran murya. sai kuma yaji sautin kukansu da kuma numfashin uwar ya ƙaru sosai. A hankali yace. "Assalamu alaikum, ya ke wannan halittar Ubangijin sammai da ƙasai". Gyara tsayuwarshi yayi jin numfashin na ƙara matsowa. A hankali yace. "Ba cewa nayi ki fitoba, nazo in roƙeki ne kamar yadda Manzon Allah ya sanar mana, dukkan halitta tanaji. Kuma ina kaga wani abun cutarwa a gidanka ka haɗashi da Allah da Manzonsa kace ya fita. Manzon Allah ya bamu tabbacin. Muddin ba mai cutarwa bane zai fita. In yaƙi fita kuwa ka kasheshi". Ɗan zagaitawa yayi jin kukansu ya kuma tsananta, cikin sanyi yace. "Ni bazan roƙeku kan ku fita ku bar muhallin zamanku da ban san tsawon shekara nawa kuke rayuwa a wurinba. Kuma bansan dalilin zamanku a wurinba. Shiyasa bazance ku bar Masarautar Joɗa ba. Kuma bazan kasheku ba, Sai dai roƙana garemu. Munada baƙi a Masarautar Joɗa kuma yau zasu shigo, dan Allah da Manzonsa, kada ku fito ku baiyana kanku ga baƙinmu kada ku razana mana baƙi kada ku cutar mana da mutanenmu. Kuyi zamanku a muhallin ku".
Shiru sukayi tsit alamun sun jishi kuma sun gamsu". Fahimtar hakane yasashi cewa. "Na barku lfy". Yana faɗin haka ya juya, Lamiɗo da Galadima ya gani tsaye a bayanshi. Murmushi sukayi tare da matsowa inda suke. Galadima ne yace. "Kada ka damu da fitarshi da zamanshi da yaranshi Domin kai ke ganinshi a nan, amman duk in da wani mugu ya shigo masarautar Joɗa da nufin yiwa Lamiɗo wani abun zai ganta da yaranta a gabanshi.
Amman wanda yake jinin wannan gidan bazai ganshiba. In kaga mutun ya ganshi saida sahalewar Lamiɗo". Shiru yayi yana kallonsu. Shi kuwa Lamiɗo a hankali yace. "A ƙalla yafi shekaru ɗari biyu da arba'in a cikin wannan curi a wannan Masarautar tun zamanin baban kakana Joɗo yake nan, ba kuma tsafi bane, ba sihiri bane, kamar yadda kowa ya sani shi maciji curi gidan zamansa ne, to bulalin caɗin masarautar Joɗa kuwa suma asali nan suke da zama curin ne ya binnesu, kana macijiyar ta shiga ciki, shine ma dalilin hana shaɗi to sai dai lokaci zuwa lokaci in an sarki maici yazo wurin yayi sallama macijiyar kan fito, in zata fito takan fito da balalin a binɗinta. Sai daga baya ta fara fita ita da ƴaƴanta suna yawo cikin masarautar Joɗa ne, muka gane yunwa ke sata fitowa, sai ta shiga cikin kaji tasha kwayaye ta haɗi ƙananan kaji. Lokacin da muka fuskanci haka sai muka fara kawo mata kwai a matsayin abincinta. Daga baya muka fahimci in mutun ya shigo da mugun nufi tana razanashi". Taɓa bakinshi yayi cikin rashin yarda bare gamsuwa yace. "Ni dai ban tambayeka ba, inma tsafine kaidashi Ni nan Muhammad Jabeer bani dalaifi a ciki nayi-iya yina in rabaku da wannan tsarabe-tsaraben na masarauta kun ƙiya". Ya ƙarishe mgnar yana juyawa ya nufi wurin da tsuntsayen wurin suke. Gefenda aku yake ya nufa. Tana ganinshi ta kaɗan fiffigenta tare da cewa. "Sheykh Jabeer ya dawo". Murmushi yayi tare da shafa kan akun yace. "Ya dai tsuntsuwa mai daraja ya gida". Cikin irin mgnarsu na Ali tace. "Lfy Sheykh ya madina garin Manzon Allah". Ta ƙarishe mgnar tana kaɗa kanta da jelarta alamun yiwa sauran tsuntsaye rigimar ance mata tsuntsuwa mai daraja. Murmushi mai faɗin Sheykh yayi ganin. Ɗawisun nan tazo gabanshi ta tsaya ta buɗe dogon jelanta ta kaɗashi tayi sama dashi. har yana taɓa gemunshi cikin sanyi yace. "A a kekyawar tsuntsuwa mai kyan ado da tafiya". A hankali ta karkaɗa jelan kana ta fara zagayashi. Tana nuna mishi kyan tafiyar. Su kuwa sauran tsuntsaye kuka suka farayi. Murmushi mai faɗi ya kumayi tare da cewa. "Tsuntsaye masu zaƙin murya da sauƙin firewa". Aifa nan suka tashi sama suna shawagi a wurin. A hankali ya juyo ya kalli tarin tattabarun dake gabanshi mazan ciki suna ƙotowa wa matansu. Kai ya rausayar tare da cewa. "Iyayen soyayya duk cikin tsuntsaye bayaku a soyayya". Ai sai suka fara irin kukansu nan guggdu-gudduu guuu". A hankali ya fita yankin tsuntsayen bakin ƙoramar dake gudana a tsakiyar Garden ɗin ya nufa. Inda agwagin ruwa keta shawagi a bakin wurin.
Zama yayi yana nazartan lamuran halittun ɗan adam. Ko wanne halitta akwai mace akwai na miji. Kuma ko wanne halitta namiji baya iya rayuwa saida macce. To shi menene matsalarsa da duk manyan likitocin duniya suka kasa ganowa, kowa sai yace mishi lafiyarshi lau. Shi kuma yasan baida lfyar maza, tunda bai taɓa jin wani abu ya motsa a zuciyarshi bare yasa wani sashi na jikinsa motsawa ba yana dai jin shi wasu lokutan a namiji jim kadan lbri zai sauya. Gefenshi Lamiɗo da Galadima sukazo suka zauna. Bisa wani carpet da hadimin da ya shigo yanzu ya shimfiɗa musu. Yana fita wani ya shigo da kayan abinci. Cikin kula Lamiɗo yace. "Taho nan muci abinci Ustazu". Hannunshi yasa ya shafa cikinsa. Sosai yakejin yunwa hakane ya sashi gyara zama nan sukaci abinci su ukum su.
Gani. Ƙarfe ɗaya tayine, lokacin salla ya ƙara to. Ga ɓaki nata shigowa masarautar Joɗa. Yasa suka tafi.
Shi yana shigowa bathroom ya wuce. Wonka ya fesa mai rai da lfy kana yayi al'wala. Kana ya fito ya kimtsa cikin wasu tattausan riga da gajeren wondo 3 qtr yasaka kana yasa tattausar rigar mai guntun hannun. Duk kalarsu Royal blue ne, sai ya ɗauka farar jallabiya. Fara mai ɗan karen kyau. Kana yasa baƙar al'kyabbar jikinshi tare, dasa hirami mai fari da ja, yayinda hakama takalmanshi fari da ja.
Wasu sabbin turaran da ya seyo ya fesa a kan sabbin kayan da ya saka masu ɗan karen kyau.
Wani irin ƙamshi yakeyi mai daɗin shaƙa.
A hankali ya fito falonshi, kallon abinci dake jere kan Dinnin yayi kana ya wuce ya fita. A falon ya samu su Jalal da alamun da al'wala a jikinsu. Can falon Shatu yajiyo muryarta tana kiran Hibba dake ɗakin Mama. Sai yanzu da yaji muryarta ne ma shi ya tuno da ita a gidan. Kai ya kaɗa yasa ƙannenshi a gaba suka tafi. Suna isa masallacin akayi sallan azahar.
Ƙarfe ɗaya da mintu arba'in suka firfito masallacin da ya cika yayi maƙil mafi akasarin matasa suna cikin shigar sukuwane.
Yana fitowa gida ya nufa sabida bai son yawan hayaniya, kuma zaiyi baccinsa da ya saba dashi, baccin tsakanin azahar da la'asar.
Su Jalal kuma cikin abokansu suka nufa.
Yana dawowa Falon Hibba kaɗai ya samu ta kunna tv tana kallon Film ɗin India kamar zai hanata kuma dai sai ya wuce. Bayan tayi mishi sannu da dawowa.
Yana shiga ɗakin ya tura ƙofar ɗakin ya rufe ba tare dasa key ba. Kana yasa hannunshi ya kashe fankar, tare da kashe wutan ɗakin. A hankali ya iso bakin gadon. Zare Al'kyabbar ajikinshi yayi ya ajiyeshi bisa gadon. Kana ya zare jallabiyar jikinshi itama ya ajeta kan gadon ya rage dagashi sai 3 qtr da ƙaramar rigar. Dan sosai yake jin bacci, sanadin ɗan zafin hadarin dake haɗuwa yayi yawane yasa ya ƙara gudun AC kana. A hankali yayi taku zuwa, gefen gadon agogon hannunshi ya cire ya ajiye a kan Bedside drower'n dake kusa dashi. Konciya yayi a nan a ƙasa bisa tayis babu shimfiɗan komai bare pillow. Wannan tsarinshi ne da yakeyi, wanda yanayin hakane dan tuna konciyar ƙabarin da wata rana zai riskeshi. Wani lokacin ma, harda AC'n yake kashewa. Yana konciya ya fara tasbihi yanayi a hankali idonshi na rufuwa, wannene yasa yakeyin bacci a lokacin da yaso.
A can cikin masarautar Joɗa kuwa. Cikin wani irin farin ciki Jalal Jamil suka nufi Side ɗin Hajia Mama jin labarin Ya Affan ya dawo daren jiya karfe biyun dare, a bakin Imran