Garkuwa complete Novel - Chapter 6
Garkuwa complete Novel Chapter 6: Garkuwa complete Novel Chapter 6. Al'walan konciya bacci sukayi kana suka shiga, ɗakin Ummey da yake mai girma da faɗi an…
4,492 words
Al'walan konciya bacci sukayi kana suka shiga, ɗakin Ummey da yake mai girma da faɗi an laileyeshi da siminti da leda carpet, kana ga jere da gadajenta biyu masu kyau, Ita da Junainah suna kan babban gadon ita kuwa Ummey tana kan ƙaramin gadon. Hira sukaci gaba da yi irin hira ta tsakanin uwa da ƴarta, cikin sanyi tace. "Aysha, kinji Hashimu ɗan Arɗo ya rasu ko?". Da sauri cikin razana AYSHA ta tashi zaune tare da cewa. "Innalillahi wa innailaihi rajiun Ummey banjiba yaushe ya rasu meya sameshi?". Ta jero tambayoyin a tare kana ga hawaye na kwaranya cikin sanyi Ummey tace. "Kwanan ya rasu, yankan rago akayi mishi sai tsintar gawanshi akayi a burtali ana zaton Ɓachamawa ne suka kasheshi". Cikin shessheƙan kuka tace. "Allah sarki Ya Hashimu Allah ya jiƙanka da rahama yasa ka huta, Allah ya saka maka duk wanda ya kasheka Allah ya toni asirinshi." Sai kuma ta konta tana kuka sosai saida tayi kamar 3 minute tana kuka kafin tace. "Yanzu shike nan Ummey duk wanda zai soni ƙarshensa yankan rago?". Cikin yin ƙasa da murya Ummey tace. "Ba dukaba in sha Allah akwai wanda zai soki ya kuma rayu dake bisa lfy". A hankali tace. "Ummey wa zai soni a irin yadda kullum ya Ba'ana yake kara zama masafi mugu, wa zai tsira da tarkonshi?". Da sauri Ummey tace. "Wanda yake mai ƙare rayuwarsa a amɓaton Allah da kekyawar zuciya." Kai kawai ta kife tana mai kukan rasuwar Yaya Hashimun ta, a haka dai sukayi ta hira har bacci ya sacesu.
A can cikin masarautar Joɗa kuwa. Bayan anyi sallan ishane, Sheykh ya fito cikin shirinsa na tafiya, riga da wondon yaɗin wagambarine a jikinsa sai bakar alkyebbarsa dayasa kana sai hiraminshi fari da kuma bakin tarden dake saman kanshi. Sai takalman sarautar da ya saka, suma farare kalar hiraminshi. Jamil ne ke biye dashi a baya yana riƙe da ƴar madai-daiciyar jakar Hamman nasu, kana hannunshi ɗaya na riƙe da jakar System ɗinshi, shi kuwa Sheykh woyoyinsh ya zura a al'jihunshi.
Tare suka fito, a mashigar ƙofarshi nan sukayi kiciɓis da Jalal, da Jakadiyarsu, cikin muryar da bata cika fara'aba Jalal yace. "Please Hamma Jabeer, dan Allah karka daɗe". Kafaɗanshi ya dafa tare da cewa. "In sha Allah bazan daɗeba Jalaluddin, ka kula da kanka da Yah Jafar". Kanshi ya gyaɗa alamar to, Jakadiya kuwa, ido ta zuma musu tana jin so da ƙaunar yaran kamar itace ta haifesu a cikinta. Cikin girmamawa Sheykh yace. "Ummi bari inje in sallami Yaya Jafar". To tace kana ta juya ta nufi sashin, Hajia Fatima, tsakar gidan Maigirma Habibullah.
Su kuwa suna shiga a falo suka samu Yayan nasu da iyalanshi, a hankali Sheykh ya ƙaraso gaban ɗan uwan nashi, cikin sanyi yace. "Ya Jafar zan tafi Leddi julɓe Sitti ta nemi muje gidansu, can ƙasar saudia, Abba ne da kanshi yace inje badon hakaba babu inda zanje in barka a haka, zanje ƙasa mai tsarki tushen mahaifiyarmu da kakarmu da take jininsu, in sha Allah zan nemi al'farman a buɗe min ka'aba zan shiga har ciki inyi maka addu'o'in samun lfy, kuma bazan daɗe ba zan dawo kajiko Ya Jafar?". Bai kulashiba kana kuma bai bar karatun da yakeyiba, sai dai hawaye daya fara zubdawa a jere-a jere. Jamil kam juyawa yayi ya fita da jakar ɗan uwan nashi dan yasan zaiyi kuka.
Ita kuwa Juwairiyya cikin sanyi tace. "Babu komai Sheykh Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy in sha Allah zanyi ta kula dashi yadda ya kamata". Jalal kuwa tattauna laɓɓa shi kawai yake tamkar zai hudasu, tabbas sunada ciwo a cikin zuƙatansu musamman Sheykh da yasan shike ɗaukan damuwarsu kab harda ta mahaifiyarsu".
Shi kuwa Sheykh hannu yasa yana sharewa Yayan nashi hawayen, a hankali suka juyo suka kalli ƙofar ɗakin Hajia Mama ce, ta shigo hadimanta na biye da ita a baya. Gefen Juwairiyya ta zauna ta zubawa su Sheykh ido, lokacin ɗaya hawaye ya fara kwaranyowa da idanunta, cikin rawan murya tace. "Sheykh lokacin na tafiya, Maimartaba ya aika a kirawo ka a zatonsa kana sashina, tashi kaje, Allah ya kiyaye hanya karka damu yayanku na ƙarƙashin kulawata musamman". A hankali ya miƙe ga mamakinsu sai gashi shima Jafar ya mike hannunshi yasa ya kamo ƙanin nashi, cikin rauni Sheykh yace, "Hajia Mama kodai in tafi dashine, kingafa baya son in tafi in barshine". Hannu tasa ta share hawayenta kana a hankali tace. "Bazai yiwu ka tafi da shiba, karka damu Jabeer komai zai wuce". Kai ya gyaɗa mata, sannan ya juya, ya nufi hanyar fita yana riƙe da hannun yayan nashi, Jalal na biye dasu a baya, Hajia Mama da Juwairiyya da yaranta na biye dasu. Koda suka zo tsakiyar farfajiyar gidan cikin bada umarni Hajia Mama ta kalli Sheykh tare da cewa. "Jabeer kuje sashin Hajia Fatima ka sallamarta". Ɗan jim yayi, a hankali ya kalleta, ita kuwa da sauri tace. "Umarnine ba shawaraba". Kanshi ya gyaɗa alamun to.
Daga nan suka shiga sashin nata, bayan Jakadiya tayi musu iso.
A folon forko suka Sameta, tana hakimce hadimanta na zagaye da ita. Tana ganinsu ta tashi ta zauna, cikin sanyi tace. "A a Sheykh da kanka". Ɗan rusunawa yayi tare da cewa. "Zanyi tafiya Hajia mamace tace inzo in sallameki". Da sauri tace. "Ayyah, to Allah ya kiyaye hanya ya kaika lfy ya dawo da kai lfy". Amin yace a takaice kana ya kama hannun Ya Jafar ɗinshi suka fito.
Nan suka raka'a zuwa sashin Gimbiya Aminatu nan suka sameta a falon, sukayi sallama da ita. Daga nan ya wuce fada, Hajia Mama kuwa ta koma sashinta da hadimanta bayan ta mishi addu'o'in insa lfy.
Juwairiyya kuwa parking lot ɗin su inda ta hango an jera motoci. Ta nufa inda Jamil ke tsaye da alamun waya yakeyi da Malika sahibarsa sabuwar budurwar da yayi.
Shi kuwa Sheykh yana shiga fada ya samu Waziri ne kaɗai da Maimartaba da alamun zaman jiransa sukeyi. A gaban Maimartaba ya rusuna, tare dasa hannu ya tura hularshi ya maidashi baya, Cikin kulawa Sarki Nuruddeen yasa hannu kan tsakiyar kanshi ya dafa tare da cewa. "Allah ya kaika lfy, ya dawo da kai lfy, ya baka sa'an tafiya, ya kareka a duk inda kake". Amin Amin suka amsa baki dayansu, kana Waziri ma ya mishi addu'o'in sannan suka miƙe gaba ɗayansu sukayi woje dan mishi rakiya, Sarki Nuruddeen da bayinshi wazirinsa da bayinshi, shina Sheykh da bayinshi, sai ya zama rakiyar ta samu taron mutane, kana ga bayin Ya Jafar, nan suka shishshiga tsala-tsalan motoci a ƙalla motoci goma sha biyar ne sukayi mishi rakiya zuwa Airport.
A wurin rabuwarsa da Ya Jafar ne yasa zuciyar kowa raunata domin Jafar kuka sosai yayi tayi da kyar dai suka dawo gida bayan jirgin su Sheykh ya tashi zuwa birnin Jalaluddin.
Cikin abinda bai gaza awa ɗaya ba sai gasu a birnin Jalaluddin.
Kafin jirginsu ya sauƙama a ƙalla motoci goma ne suka zo tarbansa, a ciki kuwa harda mai Alfarma Sarkin Musulmai Jalaluddin. Koda yaga jikan nasa mota ɗaya suka shiga, suna isa fadar musulunci, suka fito daga cikin motocin da sauri Sarki Jalaluddin ya zagayo ya kamo hannun jikan nashi, suka nufi sashin Amaryarshi Gimbiya Kulsum, jikanshi Kabir na biye dasu a baya, suna isa falonta gaba ɗaya ma'aikatanta suka fita ganin mai alfarma da kanshi, shi kuwa Jalaluddin cikin ɗan ɗaga murya yake cewa. "UmmuKulsum! UmmuKulsum!! Ga Jazlaan ya iso, gashi na kawo mikishi har ɗauki". Wata kekyawar tsohuwar balarabiyace ta fito da sauri, cikin tsananin soyayyanshi ta ruggumeshi, shima ruggumeta yayi cikin harshen larabci Sheykh yace . "Ana uhubbiki hubban axeeman ya Sitti". Kanshi ta shafa cikin tsananin son jikan nata tace. "Laisa li misluka abadan ya habibee". Murmushi mai faɗi yayi tare da bin bayanta, kai tsaye dinning area ta nufa dashi Kabir da Sarki Jalaluddin na biye dasu, da kallon sha'awa. Kujera taja ta ajiyeshi, kana ta jawa Jalaluddin tasa kujerar nan kabirma ya zauna, Suna zama sai ga wasu dattijan mata su uku sun shigo a jere a jere, suna zuwa duk kanshi suke shafawa shi kuwa sai murmushi yayi tare da kallon Mai alfarma Sarki Jalaluddin yace. "Malam kace su dena shafa min kai haka na gaji". Murmushi sukayi baki ɗayansu kana suka zauna, cikin kulawa babbar cikinsu tace. "Kazo lfy, ya jikin Jafar?". A hankali ya ɗan kalleta tare da cewa. "To Alhamdulillah jiki da sauƙi zance". Allah ya ƙara sauƙi cewar Jalaluddin Amin Amin suka amsa baki ɗayan su, ƙaramar cikinsun ce ta ɗan kalleshi cikin tsokana tace. "Ina mai gidanmu Sarki muminai". Taɓe baki Sheykh yayi tare da cewa . "Uhumm Jalal ne Sarkin Musulmai ko? Baki sanshi bane". Dariya sukayi duka kana suk gaggaisa sannan suka fita gaba ɗayansu, ita kuwa Sitti abinci tayi ta bashi har saida ya kwaɓe fuska tare da cewa. "Na tuba ki barni haka na ƙoshi". Kai ta gyaɗa kana suka dawo falo zata fara hira, yace shi dai ya gaji bacci yakeji hakanne yasa, Jalaluddin da kanshi ya kaishi makwancinsa.
Asuba ta gari al'ummar Sokotawa
A nan Ɓadamaya kuma cikin Rugar Bani Washe gari da hantsi, bayan duk sun karya, kowa makiyaya duk sun tafiya kiwo, manoma kuma duk sun tafi noma, kana mata masu shiga tallan nono cikin gari sun tafi, garin yayi tsit kamar yadda aka saba
Ba'ana kuwa da Shatu suna zaune a ginɗin bishiyar mangoro dake bakin zauren su, ita tanata. Ciki shi kuma yanata woje, cikin sakin fuska ya kalli Junainah dake gefensu yace. "Junainah je cikin gida kice a baki ɗanyen kwai ki kawo mana in dafa mana". Da mmki Shatu tace. "Ka dafa mana kuma?". Kai ya gyaɗa mata, ita kuwa Junainah uwar kwaɗayi tuni ta tafi cikin gida Inna na tambayarta me zatayima Bata kulataba, sai ɗan kwano data ɗauko a konɗonsu kwan zabbi ta ɗebo a kalla sun kai goma, kana da gudu ta dawo wurinsu.
Da sauri yasa hannunshin ya amshi robar, ita dai Shatu Ido ta zuba mishi taga ta ina zai dafa kwan, shi kuwa Ba'ana hannunshi yasa ya fara tona ɗan ma dai-dai cin rami, da mmki Shatu tace. "Ya Ba'ana me zakayi da tona rami kuma?". Cikin murmushi yace. "A ciki zan dafa mana kwan". Junainah kam gabanshi tazo ta zauna, tana kallonshi har ya gama tona ramin. Kana ya zuba kwayayen a ciki ya maida ƙasar ya binnesu. Sannan ya juyo ya kalli Shatu yace. "To musha hirarmu kafin kwan ya nuna". Junainah ce tace. "Ya Ba'ana ta yaya zai nuna kuma babu wuta?". Kamo hannunta yayi tare da cewa. "Ke dai zauna ki jira ki gani ƙaƙara". Kai ta gyaɗa tare da gyara zama, shi kuwa Ba'ana murmushi yake a baiyane a ranshi kuma cewa yakeyi. "Uhummm shi Bappa dan ina son yarsa bazai hanani yashe Garkensa ba, kuma da koyayen gidanshi kawai zan iya karya kafin da yayiwa garkenshi". A zahiri kuwa kallon Shatu a yayi tare da cewa. "Zakiji girkina mai daɗi". Kai ta jinjina tare da cewa. "Uhumm girki ko al'mara." Kanshi kawai ya gyaɗa alamun zaki gani daga nan sukaci gaba da hira.
Bayan kamar 42 minutes ya fara tono wannan ramin daya tona a gabansu babu wuta ko ɗigo ya binne ɗanyen koyaye, sai gashi ramin yana tururi tamkar an bude tukunyar dake tafasa, da sauri Aysha ta waro idonta. Junainah kuwa sai tsalle take, shiko Ba'ana saida ya kwatso ƙoyayen kab kana ya sasu a robar da aka kawosu a ciki, Ɗaya daga ciki yasa a gefen dutsen da yake zaune ya konkotsashi kaɗan kana ya ɗagoshi, yatsunshi biyu yasa yafara ɓarewa.
Cikin mamaki Shatu ta zazzaro idanunta woje tare da cewa. "Hehhhhh...!
Ga masu buƙatar biyan kudi littafin mutanen Niger ga number da zakuyiwa mgn +22799460151 in kun biya ta wurinta ita zata turo min number ku in saku cikin group.
By *GARKUWAR FULANI* 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘
*GARKUWA*
PAGE 7
NA *AYSHA ALIYU GARKUWA*
📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘
*Littafina na kuɗine, turo 1k domin karanta part 1 cikin mako biyu, ko ki turo 300 domin karanta part 1 a kwanaki talatin, da izinin ubangiji. Turosu ta asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank, Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo min shaidar biyanki ta number da nake whatsapp dashi. 09097853276, in da hali bana son kati, amman in babu dama turo katin ba matsala, domin wani baida damar turowa ta bank ac.*
*Ayyah masuyi mun voice note Dan Allah ku rinƙa ɗaga murya, baku saniba ko inada matsalar kunne bayan na idon. In kinga kinyi min mgn ban amsaba wata ƙl fahimceki bane, ko kuma mgnarki bata da amsa a wurina, kana abubuwa suna min yawa, irin asha hira a chart ɗin nan bazai yiwuba, kuyi haƙuri masoya, yawan maimata min slm ince wslm ayi sama da sau goma yana sa in share mutun tsakani da Allah sabida kamar bashi da abin faɗane so Please na tuba,🙏🏻 a ɓari kada kice ina muku wulaƙanci.*
Ido ta zazzaro tare da cewa. "Hihhhhhhh, ya dahu?". Kanshi ya rausayar tare daci gaba da ɓare kwan saida ya ɓaresh tas ya fito subul gwannin ban sha'awa, sai turiri yaketayi, Junainah ya miƙa. "Karɓi kici kiji mana, kwan ya nuna ne Ƙanwaliya". Da sauri tasa hannu, zata amsa, cikin sanyi Aysha tace. "Ke uwar kwaɗayi bazaki ciba". Rau-rau tayi da idanu alamun zatayi kuka, shi kuwa Ba'ana fuskarshi ya haɗa tare da kafeta da ido, da sauri tayi ƙasa da kanta, tana mai wasa da ƴan yatsun hannunta, dubanshi ya maida kan Junainah tare da cewa. "Kici abinki Junainah". Fuskarshi ya ƙara haɗawa jin Aysha ta kuma cewa. "Dan Allah Ya Ba'ana kada taci". Ba tare daya kalleta ba, tace. "Kema zakici ai bare ita". Da sauri ta ɗago kanta tare da girgiza kan tace. "A a ni kam ngd bazanci abinda ban san da me aka dafashi ba". juyowa yayi ya kalli Junainah da tuni ta fara cin kwanta, tana lumshe ido baki cike da kwan tace. "Ya Ba'ana bari inje cikin gida in kawo mana yaji mai daɗi Addana bata cin kwai saida yaji". To yace mata, tuni ta juya tayi cikin gida.
Kallonshi ya maida kan Shatu cikin haɗe fuska yace. "Mata kina tunanin zan cutar da kene?". A hankali ta jujjuya mishi kai alamun a'a, gyara zamanshi, yayi tare da cewa. "To baki yarda dani bane?". A hankali ta buɗi bakinta tace. "A'a ni dai tsoron abun naji, ka toni rami mai danshi da sanyin yashin damina, ka binne ɗanyen kwai mai sanyi ka fito dashi da zafi a dafe ni kam ina tsoro ban san da wutan me ka dafashiba".
Fuskarta-ta yayi da kyau kana, ya fara magana. "Ki yarda dani Mata, bazan taɓa cutar dakeba a rayuwa, duk abinda zakiga inayi, zanyine dan kare lfyarki da kuma baki kariyar. Jikin ki, kici kwannan, babu abinda zai miki". A hankali tace, "Ni bana cin kwai dama, kuma ai shi kariya Allah ke hadashi ga dukkan bayinsa". hannu yasa ya amshi robar dakekken yaji da Junainah ta miƙo mishi, wacce yanzu ta dawo wurin. Wani kwan ya kuma ɓare mata, ya miƙa mata, tanaci tana lumshe ido saida taci biyar, sannan tace. "Ya Ba'ana na ƙoshi". Shatu ya ɗan kalla tare da cewa. "Saura biyar kuma nakine, in kin shiga gida kicishi, sannan kuma akwai wani haɗin maganin da zan kawo miki kiyi amfani dashi. Ni yanzu zan tafi". Kai ta gyaɗa mishi alamar to, kana kuma tace. "Ina zakaje yanzu? Tunda naga lokacin tafiya kiwo dai ya wuce". Miƙewa tsaye yayi tare da cewa. "Zan shiga ƙauyen Bonon ne". Da mmki a fuskarta tace. "Ya Ba'ana me zakayi kuma a ƙauye Bonon garin masafa kafurai ƙabulun Ɓachama". Ido ya zuba mata har saida taji tsoronshi a hankali yace. "Kema watan watarana zakije, ki tuna da kyau Mamata ƙabilar ɓachama ce, ƴar garin Bonon kinga kuwa dole inje can tunda kawuneina ƙannen Mama da yayunta da iyayenta duk suna can". Ya ƙarishe mgnar kamsr yaji zafin zancen ta, ganin hakane yasa a hankali tace. "Kayi haƙuri". Kai ya juya mata alamar babu damuwa.
Daga nan ya juya ya tafi, ita kuwa tacewa Junainah su shiga gida. Suna shiga cikin gidan ta harari Junainah tare da kai mata bugu cikin faɗa tace. "Hegiya kwaɗayayya maza ki zubar da sauran kwanan jakar yarinya ai sai ya ciyar dake guba tunda kince ke kwaɗayayya ce". Ihu Junainah ta kurma tare da cewa. "Wayyoooooooo Inna kin ganta ko tana cin zalina". a guje tayi gaba, ita kuwa Shatu tabi bayanta da sassarfa tana cewa. "Wallahi sai kin zubda ƙoyayen nan". A haka suka isa har gaban Ummey da inna da suketa tafasa nonon da aka tatsa a sanyin safiyar yau, wanda a ƙalla ya kai jarka goms sha uku, so masu gidajen fura da nono na cikin Shikan ɗin nema suke saya, dan matan gidan Bappa kab bai lamunce da zuwansu tallan nono ba.
Inna ce tayi saurin kare Junainah dan saura ƙiris ta abka cikin tafasasshen nono da yanzu aka sauƙeshi, cikin tsoro tace. "Kai ya ilahi ku dai bazaku zauna lfy ba". Cikin nitsuwa Shatu ta zauna gefen Ummey nan ta labarta musu abinda ya faru da yadda ya dafa kwan ta ƙara da cewa. "Amman da yake Junainah uwar kwaɗayi ce, a take a gabanshi taci kwai biyar cas tanaci tana lumshe ido". Cikin tarin mamaki Inna da Ummey sukayi ta salati tare da tafa hannu, a tare sukace. "Innalillahi wa innailaihi rajiun, oh wannan yaron anya kuwa mutun ne ba shaiɗan ba?". Cikin rau-rau da ido, Shatu tace. "Ni ina jin tsoronshi, bana sonshi bazan aureshiba, mutumin da komai nashi na tsafine Inna ki cewa Bappa ya rabani dashi mana". Cikin alhini, Inna tace. "Rashin sani yasa Bappanki dama ke kanki kukayi mishi al'ƙawarin shine mijinki duk rintsi, gashi yanzu ya zame mana masifa. Juyowa sukayi suka kalli Ummey da idonta ya ciki da hawaye a hankali tace. "Dana sani wlh da ban bar haka ta faru ba". Shiru sukayi cirko-cirko a wurin, saida suka jiyo ƙaurin nono na zuba cikin murhune suka dawo haiyacinsu. Kana suka juya suka ci gaba da aikin su.
A birnin Jalaluddin kuwa ƙarfe tara na safiyar ranar, dai-dai jirginsu Sitti da jikanta Sheykh ya tashi zuwa ƙasa mai tsarki da sauran taro al'ummar Annabi masu zuwa Umrah.
Soyayyar da Sitti keyiwa Sheykh soyayyace mai tarin yawa, wanda ko uwa iya son da zatayiwa ɗanta kenan, tana ji dashi tamkar ranta, wata ƙil hakan baya rasa nasaba da tsananin kamanni da yakeyi da mahaifinta wanda shine baida lfy yanzu kuma shine tsohon Limamin Harami yanada zuriya mai tarin yawa yayansa na cikinsa zalla su arba'in da bakwai. Bar jikoki da ƙanne da yaran yan uwa, sai dai ya tsufa sosai tun shekaru ashirin da suka gabata ya ɗaura babban ɗanshi wanda yake ƙanin Sitti ne uwa ɗaya uba ɗaya a matsayin shi. Zuwa yanzu tsotsai tsufa ya kama Sarki Abdulkarim, Hairan wanda yake da shekaru ɗari da biyar a duniya, sai dai sufarsa suface mai tsabta tsuface da ka gani kasan an rainin ƙuruciyarta da tsoron Allah da ibada. Shiyasa babu gigita ko fita haiyaci, yana son diyarsa Sitti kakarsu Sheykh kenan so mai tarin yawa ko dan tayi nesa da shine, wacce ita kuma tun tanada shekaru ashirin da uku, Sarkin Musulmai na ƙasar Kautal na wancan ƙarnin yazo da babban ɗansa, Jalaluddin wanda a nan yaga UmmuKulsum Sitti kenan, ya sota, kuma Allah cikin ikonsa suka dai-dai ta, haka yasa kafin ya koma ma da amaryarshi ya koma dan sitti ta kafe ita dai tana son Bahaushen ga, duk da tasan yanada mata biyu, tace ai a gidansuma bata tashi ta samu mahaifiyarsu ita ɗaya ba.
Tuni ita kam Allah ya mata rasuwa mahaifiyar Sittin kenan, yanzu mahaifinta ne kadai a raye, sai kuma ƙanninta da yake matsayin ɗaya daga cikin manyan limaman harami a yanzu sai sauran zuriyarta da yayu da kannenta. Kowa na ahlinsu yasan Sheykh domin Sitti tana yawan zuwa dashi tun yana ƙarami, kana tana zuwa da sauran ma baki ɗaya, to shi Jabeer anan ƙasar saudia ya haɗa digiri ɗinshi na forko dana biyu. Shiyasa ya zama duk zuriyar an sanshi farin sani, ga kuma tarin kama da yakeyi da mutanen zuriyar wanda da zaran ka ganshi kasan jininsu ne.
Tafiya mai tsowo sukeyi cikin sararin samaniya suna keta gajumare, a ƙalla tsawon aha huɗu kenan suna tafiya. Kafin suka sauƙa cikin babban Airport ɗin jidda, wanda yake tamkar zai fashe da jirage, ko wacce ƙasa ta duniya tanada jirginta cikin wannan babban Airport ɗin, tashin jirage da hawa da sauƙansu tamkar babu wani abun hawa a duniya sai jirgi.
Koda suka fito daga jirgin, wani jirgine na musamman suka shiga wanda yake daga fadar Mai Alfarma masarautar garin. Wanda ya turo a tarɓi ƴar uwar abokinshi da mahaifinsu keta begen gani. A take suka shiga jirgin ya wuce dasu, asalin cikin garin makka, wanda pilot ɗin kuma ɗane ga Umaymah ƙanwar Mamansu Sheykh wato shima jikan Sitti ne ɗan Umaymah sai kuma Jannart wacce ta biyo Haroon Dan tarban kakar tasu wacce ita kuma ƴace ga babban ɗan Sitti wato ƙanwar Juwairiyya ce kuma anan take karatu.
Suna sauƙa a Airport ɗin, suka fito, a jere, yana gaba yana rike da hannun Sitti tana biye dashi a hankali tana taka step ɗin Jannart kuwa tuni itace a gaba. Haroon ne wanda yake biye dasu a baya yana kallon yadda kakar tasu ke taka step da kuma yadda ɗan uwan nashi ke rike da hannun ta, murmushi yayi tare da jingina a ƙofar bakin jirgin cikin harshen larabci yace. "Ko dai zaka goyeta ne ka sauƙar da ita". Sheykh bai kulashi ba, har saida suka sauƙo ya gyarawa Sitti tsayuwarta, kana ya miƙawa Jannart hannun Sitti alamun ta rike musu ita. Cikin jin daɗi Jannart ta riko hannunta tare da cewa. "Ana Uhubbiki ya Sitti". Cikin jin daɗi da son jikokin nata tace. "Ana". Sai kuma suka juyo suna kallon Sheykh dake tsaye cikin shiga ta al'farma shigar salihan bayi, wata dandatsetsiyar al'kyabbace mai masifar kyau ruwan ƙasace al'kyabbar sai surfani da aka sarrafa a jikinshi wanda yake da kalan gold, haka takalmanshi da hiraminshi duk masu ratsin Golding color ne, cikin tsananin jin daɗi Haroon ya fara sauƙowa daga step ɗin, yana kallon ɗan uwan nashi manda suke sa'anni, ruggume juna sukayi, cikin jin daɗi Haroon yace. "Marhabin da zuwa Al'Sheykh, ya gida?, ina ƙannena? Yaya jikin Ya Jafar? Ya Hajja Mama da kowa da kowa." Kwaɓe fuska ya ɗanyi tare da janye jikinshi daga na Haroon cikin sanyinshi yace. "Duk in kana son ganinsu kaje Nigeria zaka gansu, kana nan kullum sai yawo a jirgi kamar turuwa a daji, duk ƙasashen duniya ka gama zagayesu". Murmushi Haroon yayi tare da cewa. "To ai dama na sani bakinka ɗaya da Umaymah'nka, zan koma ne in sha Allah, zan koma inyiwa ƙasarmu aiki, suma ai suna buƙata na". Fuskarshi ya ɗan kauda tare da cewa. "Da yafi kam". Juyowa sukayi jin Sitti na cewa. "Kai Haroon ku taho mu tafi, ka tsareshi da surunka tun daga nan ko?". murmushi Haroon yayi kana ya nufi inda take tare da cewa. "Oyoyo My Sitti". Kai ta juya tare da cewa. "Rabu dani ba kaga ɗan uwanka ka shareni ba". Ruggumeta yayi ta baya tare da cewa. "Na isa in share uwar gida ran gida a gidan Sarki Jalaluddin". Jannart ce tai dariya tare da cewa. "Sitti karki yadda da daɗin bakinshi". Hannunshin yasa ya ɗan dungure kan Jannart tare da cewa. "Kishi ko dan kinga gani ga uwar gida". murmushi Jannart tayi tare da jan hannun Sitti sukayi gaba, shi kuwa Haroon baya ya dawo ya saita da Sheykh suka fara tafiya a jere, duk wanda yaga salo da tsarin tafiyar Sheykh zai gane cewa jini na sarauta na gudana a jikinshi, zai kuma gane nitsuwa ta addinin musulunci da kamala da haiba na hasken imanin ya game jiki da zuciyarshi.
A haka suka jera suna tafe, suna hira wacce ƙarfinta duk Haroon ke yinta. Suna tafiya kaɗan.
Nan suka samu wasu irin zafafan tsala-tsalan motoci masu masifar kyau da tsada, suna jere a ƙalla sun kai goma sha biyu, motocine masu azabar kyau da sabunta da sheƙi da kyelli suna jere. Kana ga kekkyawa fararen larabawa yan uwa da abokai Da sauri suka rinka ɗan rusunawa suna, gaidasu Sitti da jikokinta, wani cikinsu ne da yake jikin wata dan datsetsiyar mota ƙirar Mercedes Benz maybach Exelero wacce kuɗinta zai kai kimanin $8 million dollars. Motace mai masifar kyau da tsada, tana da inƙancin da ko bilet baya shigarta. Bisa dukkan alamu kuma sabuwa ce dal. Direban dake jingine da ita ne yayi maza ya budewa Sitti bayan ta, a hankali suka ƙaraso gaban motar gaba ɗaya ma'akatan sunyi musu ƙawanya, cikin so da ƙaunar jikokin nata, ta yiwa Sheykh nuni daya fara shiga, ba musu kuwa ya shiga, motar, kana itama ta shiga sannan Haroon ya shiga, ya zamana sun sata a tsakiya, Jannart kuma gaba ta shiga gefen drivern, suna gama shiga aka maida ƙofofin motar aka rufe. Kana duk sauran hadiman suka shishiga motocin. Kana suka fara tafiya a jere-a jere, tafiya sukeyi cikin salama da nitsuwa da bin doka da ƙa'idar tuƙi, kai tsaye suka wuce tushen ahlin nasu.
Wanda kafin su zoma, duk labarin zuwansu ya riski al'ummar family, kamar yadda aka saba, haka aka shirya musu tarba ta musamman an gyara sashin na musamman wanda nanne masaukin Sitti asali kuma sashin mahaifiyartace, anan cikin sashin kuma duk ahlinta da zaizo daga ƙasar Kautal nanne masauƙinshi, kuma kullum hadimai da bayin dake kula da wannan wurin suna nan suna tsabtace wurin. Suna isa fadar mai darar Sheikh Aliyu da kanshi ya fito tarbar babbar yayarshi wacce take a madadin uwa a gareshi a yanzu.
A wani falo da yafi dacewa da a kirashi al'jannar duniya, suka haɗu, a hankali Sheykh Aliyu ya ɗaga hannunshi alamun dakatar da ko wanne hadimi, a tare suka rusuna tare da komawa baya gaba ɗaya su. Da sauri ya karaso gaban Sitti Ruggumeta yayi irin ruggumarsu ta jinin larabawa, murmushi mai cike da jin daɗi ƙauna haɗida bege Sitti tayi tare dasa hannunta tsakiyar kanshi tace. "Masha Allah, ɗan uwana na sameku lfy?". Saketa yayi tare da ruggume Sheykh yana murmushi tare da cewa. "Alhamdulillah yar uwata, Barka da zuwa lfy". Cikin kula da zaƙuwa tace. "Yaya jikin Baba". Murmushi ya kumayi still yana ruggume da Sheykh yana shafa bayanshi, yace. "Alhamdulillah jikin baba da sauƙi kewarkice tafi damunshi". Sai kuma ya kalli Sheykh bayan ya sakeshi yace. "Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero, barka da zuwa Doctor, ya gida ina Jafar da ƙannenka". Cikin son dottijon Sheykh ya ɗanyi wani ɗan guntun murmushi wanda shima sai yayi tsawon lokaci bai yishiba, cikin sassanyan murya yace. "Suna lfy, sun gaidaka". Haroon ya tura baki tare da cewa. "Wato mu ko ƴar ruggumar ma ta zumunci baza'ayi manaba, dan mu mun dade, nima zamu koma ƙasarmu mu rinƙa kawo muku ziyara jifa-jifa dan naga baƙi farinjini garesu a ahlinmu". Dariya sukayi baki ɗayansu,. Yayinda duk mgnar da sukeyi da harshen larabci sukeyi.