Kenza eBookz

Garkuwa complete Novel - Chapter 7

Garkuwa complete Novel - Chapter 7

Garkuwa complete Novel Chapter 7: Garkuwa complete Novel Chapter 7. Wani faffaɗan corridor mai girma suka ratsa, wanda suka riski wani babbanshi na…

4,467 words

Wani faffaɗan corridor mai girma suka ratsa, wanda suka riski wani babbanshi na musamman, inda gaba ɗaya yayan family suke nan zaune dan mahaifin nasu a tsakiyarsu. Wanda yake tsakiyar gatan duniya, farin dattijone wanda tsabar tsufa har ya juye ya koma tamkar ƙaramin yaro, ya ƙanƙance, yana hango Sitti, ya rinƙa sakin murmushi tare da miƙa mata hannunshi alamun tazo. Da sauri ta nufi inda yake su Sheykh na biye da ita a baya, yayinda duk sauran mutanen ketayi musu barka da zuwa. A gaban tsohon ta rusuna, tare da sunkuyowa, hannunshi ya saka bisa kanta yana jero mata addu'o'in da sanya mata al'barka, ita kam sitti da sauran ƙannenenta wanda a ƙalla sun kai arba'in sai Amin Amin suke amsawa, Koda ya gama da Sitti jawo Sheykh yayi ya manna kanshi da cinyarshi, Shikuwa Sheykh. Motsoshi yayi da kyau Cikin wani irin mashahurin daɗin da sai in yana gaban tsohon nan yakejin daɗi yasa hannunshi biyu ya kamo hannun dattijon ya ɗaura tsakiyar kanshi kana ya ƙara manna kanshi da cinyar tsohon tasbihi yakeyiwa Allah mai rayawa mai kashewa. Ya sani shi kanshi da macece shi da yanzu yanada ya budurwa amman gashi wai a gaban kakan mamanshi, ga kuma kakar tashi da sukewa kallon tsohuwa itama gata gaban mahaifinta wannan abu shine abu ɗaya da yake sashi kuka muddin yana gaban tsohonda kullum in yazo irin gaisuwar da sukeyi kenan. Shi kuwa Sarki Abdulkareem cikin rawan jiki irin na tsoffi yake shafa kan Sheykh tare da kallon taron ahlin naahi cikin muryarsa da bata fita sosai yasa suke sanƙala mishi na'urar ɗaga sauti a jikin alkyabbarsa, shiru sukayi gaba ɗayansu suka dakata da ruggume-ruggumen da sukewa Sitti, Cikin rawan muryan da alamu tsohon kuka yakeyi a hankali yace. "Ku bashi dukkan kulawarku, domin yana cikin Magauta, yanada tarin ƙunci da ƙuna a rayuwarshi, matsalolin rayuwar duniya sun mishi ƙawanya, saukinshi ɗaya Allah yayi mushi dafa'i da hasken imani da riƙo da ibada, damuwar tana daƙushe duk wani farin cikin rayuwarsa rashin fara'a ba izza bace damuwace, yana cike da al'hinin kula da ahlinshi,". Shiru ya ɗanyi tare da zubawa gaba ɗaya ahlin nashi idanu, sawon wasu daƙiƙu shiru falon babu sautin komai sai sassanyan sautin shessheƙan kuka da Sheykh a hankali, sai kuma sautin ƙaran A/C.

A hankali Dottijon yaci gaba da cewa. "Kanshi akwai wani abu mai girma a tare dashi, yanada manyan baiwowi a jikinshi, sai dai kuma akwai tarin ƙalubale, zai ɗauki nauyi da yawa a kanshi". Ya ƙarishe mgnar yana shafa tattausan suman Sheykh. Shiru sukayi baki ɗayansu Sitti kuwa Hannu tasa bisa haɓar Sheykh tana share masa hawaye, Haroon kuwa Umaymah ya kira tun shigarsu tana jin duk kalaman kakan nasu haka yasa taketa kuka.

Sosai yayi jawabai masu ratsa zuciya kafin daga bisani, ma'aikatan gidan suka shigo suka rinƙa gabatar musu da abubuwan ci da sha a nan suka zauna ana ɗan ciye-ciye da taɓa hira, Ganin lokacin salla yayine kab kowa ya miƙe dan yin al'wala su tafi harami.

Kamar koda yaushe Sashin Sitti suka wuce wanda yake a gyare, Jannart da Sitti side ɗaya suka shiga. Haroon da Sheykh kuwa Side ɗaya suka shiga. Ruwa suka ɗan watsa sannan duk sukayi al'wala suka fito suka kimtsa cikin manyan alkyebbars masu taushi da masifar kyau wanda sabbine dal akazo aka shirya musu a drower'n. Koda suka gama a tare duk mazan suku tafi Harami.

Haka dai rayuwa tai ta gudana a cikin kwanakin nan.

Randa suka cika kwana uku da zuwa a ranar ne Sitti ta samu mahaifinta da ƙaninta a kan batun tana son kafin tabar ƙasar nan ayiwa Sheykh aure, ta kuma bada zaɓin yaran yan uwa wanda suke larabawa, nan take kuma Sheykh Aliyu da kanshi yace ya bawa Sheykh Jabeer auren diyarsa Jazrah...

Rugar Bani Ɓadamaya state.

Yau kusan kwanan Shatu biyar da dawowa hutu, kuma kullum da salon da Ba'ana yake zuwar mata dashi, wannan abu shine abinda yafi tada hankalin Malam Liman Bappa kenan, wanda yana yawan tattauna matsalar da Ardo Bani kamar yadda yanzuma haka suke tare su daddatawa biyar, Cikin kamala da harshen fillanci Arɗo Bani yayi gyaran murya tare da cewa. "Koda Hashimu ya rasu, in sha Allahu bazamu zuba ido a aurawa Shatu wannan fasiƙi fajiri mushirkin yaron nanba, Salmanu zai fito zai nemi aurenta,in Allah ya yarda kuma zamu cire batun shaɗi tunda, mun sani cewa, bulalin da Ba'ana yake amfanin dasu wurin shaɗi da manema auren Shatu bulalin sihirine wanda duk wanda ya daka dasu ƙarshe mutuwa yakeyi ko ya haukace, to a karon nan zamuce babu shaɗi domin ai shi shaɗi al'adace ba shariya ba. Zamu kuma bawa salmanu dakarun tsaro masu bibiyar lamuranshi a sirri dan gudun kada ayi mishi yankan rago kamar yadda akayiwa Hashimu duk da dai bamu da sanin shin Ba'ana ne koko kafuran Ɓachamawa ne". Da sauri ɗaya daga cikin dottawan yace. "Yo ai shima Ba'ana kusan kafurin ne, tunda baya salla kuma matsafine". Bappa ne ya nisa tare da jan dogon numfashi mai tsawo sannan yace. "Bazai yardaba duk yadda za'ayi sai yace dole ayi bulalin Shaɗi, kana kuma muddin akace baza'ayi Shaɗi ba to haƙƙun zai kashe Salmanu kisan da bazamu samu huja ko madafaba". Shiru sukayi baki ɗayansu cikin kamala da nitsuwa da rauni Bappa yace. "Kaɗan kenan daga illar riƙo da Al'adar daba addini ne ya tanadar dashi ba". Ardonne yayi gyaran murya cikin sanyi yace. "Ya Allah ka kawo mana mafita kan wannan bawa naka Ba'ana daya zame mana masifa a rayuwarmu". Ɗaya daga cikinsu wanda tunda suka zauna baiyi mgna bane ya gyara zama tare da cewa. "Gashi shi kamar ibilis yake, ya rigada ya gama dafa kanshi wuƙa ko bindiga basa shigarsa bare banzan abu shi bulalan Shaɗi shiyasa kullum shine da nasara a rayuwarsa". Shiru sukayi suna kallon ɗaya daga cikinsu wanda ya kasance malamin da suke sawa yana bincikar musu jikin Ba'ana wato Chubaɗo yana cewa. "Akwai bulalin da zasu shigeshi su kuma karya duk wasu manyan sirrukan dake jikinshi, ta kuma sashi yayi kuka,cur-cur da hawayenshi, to amman bazasu taɓa samuwaba bamu da hanya ko damar samunsu, domin bulaline da a ƙalla sun shekara ɗari biyu a murde kuma suna cikin tsumin ma'jiya mai cikar tarihi da girma bulaline da tsawon shekara ɗari da ashirin da biyar kenan rabon da ayi amfani dasu, kuma an killacesu, killacewa mai tsauri, shi kanshi Ba'ana yana neman bulalin ruwa a jillo domin babban dodon tsafin Bonon ya sanar mishi saida bulalin zai samu nasarar da yake so, to amman bai san bulalin ina bane baisan a ina sukeba bai kuma san ta ina yake nemansuba an dai bashi yaƙini a hannun Fulani yake wannan dalilin ne yasa ya baza jakadunshi duk ƙasar da takeda Fulani." Da sauri Suka zuba mushi idanu baki ɗayansu cikin zaƙuwa sukace. "To Chuɓaɗo kai kasan inda bulalin suke e?". Kanshi ya jinjina musu tare dayin ƙasa da murya yace. "Eh na sani". Cikin sauri sukace. "Bulalin inane a wacce ƙasar suke?". Cikin tsoro yace. "Bazan fadaba bazaiyiwu in faɗaba". Magiya suka fara yi mishi amman fir yaƙi yace mutanen jikinshi sun hanashi faɗa, dole haka suka haƙura suka tashi daga taron ganin dare ya raba tsakiya kowa ya koma gidanshi.

Washe gari da Asuban fari Rasuwar Chubaɗo ya zagaya garin Rugar Bani wanda akayi hira dashi lfy lau kawai washe gari aka riski ya rasu da alamun kuma ɗaure mishi wuya akayi ya rasu har lahira. Wannan rasuwa ya jijjiga zuƙatan dottawan nan huɗu da suka rage Arɗo Yabani da Bappa, da kuma Alhaji Ja'eh da kuma Malam Umaru. Sun shiga jimami mai yawa. A haka dai akayi mishi sutura aka binneshi akayi zaman makoki na tsawon kwana uku, randa akayi sadan uku duk hankali mutane huɗun nan ya ɗan konta ganin ba'a sake kashe wani ba a cikinsu.

Yau tun da yamma Ba'ana ya matsa aka kira mishi Shatu wacce dolece tasa taje, inda yake har rugar shanunsu bata damuba sanin bai taɓa koda yunƙurin cewa zai taɓa koda ƴar yatsartace, Cikin sanyin jiki ta sallami aminiyarta Bintu ƴar gidan malam Umaru, sannan ta tafi bakin rugagen.

Zaune ta sameshi cikin ƴar bukkarshi da yayi a cikin tsakiyar turken garken nasu, A hankali ta ƙaraso wurin ta sunkuya zata zauna ne a saman farin yashin dake wurin yayi maza yace. "Mata a ƙasa kuma? A a gskiya kada ki zauna a ƙasa. Ga buzuna zauna a kai". Kanta kawai ta jinjina shi kuwa shimfiɗa mata buzun yayi, a hankali ta zauna tana fuskantar cikin ƴar bukkar da yake zaune a cikinta ɗin. Shima gyara zama yayi tare da fuskantarta, Kwaryar dake gabanshi ta zubawa ido, shi kuwa. Cikin yin murmushi ya sa hannunshi yana gauraye magungunan dake ciki tare da cewa. "Matar dafaki nakeso inyi, irin dafar da muddin mutun ya tuna zai miki sihiri, misali ya miƙa hannu zai amshi mgnanin da zai samiki to zai kuturce in kuma baki ya buɗe zaiyi mgna kan a miki sihiri to zai kuramce". Cikin sanyi ta kwaɓe fuska tare da cewa. "To ni kuma wa zaimin sihiri a duniya wayama damu dani?". Murmushi mai kama da dariya yayi kana yace. "In an nemi mijinki ba'a sameshiba dole kanki za'a dawo shiyasa nake shiryaki sabida kar Ni in an jefeni bai sameniba ya sauƙa kanki". Ya ƙarishe mgnar da miƙo mata ɗan ƙaramin korya yace. "Ingo ki fara shan wannan". Kai ta gyaɗa ganin madarar shanuce da aka tatsa da ɗuminta. Cikin takaicin halinsa tace. "Me wannan kuma?". dariya yayi tare da cewa. "Baki da yarda ki yarda dani wata rana zaki tuna nayi miki gata, wlh bazan taɓa cutar da keba mata, kisha madarace da zuma nasan kinaso". Cikin sanyi tace. "Sai dai in na koma gida zansha". Murmushi yayi tare da zuba mata ido kana a hankali yace. "Fulaku ko? Nasanku fulanin da kunya wato irin bazakici abu a gabana ba, to ai kafin ki koma gida zaiyi sanyi, bari in tafi can bayan bishiya in barki ke ɗaya kisha abunki da ɗuminshi". Ido kawai ta zuba mishi domin tabbas badon halin banza da Ya Ba'ana yake dashiba ya cancanci ta soshi tabbas tasan ko ba yayi mata alherin da bazata taɓa mancewa ba a rayuwarta. Ko komai nashi na duniya mara kyau ne to soyayyarta kekkyawace a zuciyarshi ya sota tun tana yar mitsitsiyarta kuma bai taɓa yunƙurin cutar da itaba ya kuma yi mata halacci. Murmushi yayi tare da cewa. "Mata nayi miki kyau ne?". Kanta ta gyaɗa mishi alamar eh, cikin jin daɗi ya juya ya tafi, can nesa ya ɓuya, ita kuwa a hankali ta fara shan madarar nonon da yaji zuma mai daɗi, kasan cewar nonon ɗan kaɗanne a take ta shanye. Saida ta goge bakinta tace mishi. "Na shanye kazo". Da sauri ya fito ya dawo gareta cikin bukkar ya koma ya zauna wani nonon ya ɗibo ya miƙa mata amsa tayi cikin sanyi yace. "Me kika gani a ciki?". Murmushi ta ɗanyi tare da cewa. "Nono fari ƙal mana". Amsar ƙoryar yayi ya koma cikin bukkar dashi, jin kaɗan ya kuma fitowa ya miƙa mata tare da cewa. "Me kika gani?". Tura baki tayi tace. "Farin nono mana". Kanshi ya jinjina tare da cewa. "Da kyau, yanzu kiyi kamar zakisha ki gani". Ido ta zuba mishi tare da cewa. "Sha kuma?". Kai ya jijina mata kana yace. "Eh amman ba shan zakiyiba kiyi dai kamar zaki kaishi bakinki da niyar sha zakiga wani abu". Jim kaɗan tayi jin yana ce mata sha mana, yasa ta ɗan ɗago kwaryar ta nufi bakinda kamar zata sha.

Wani irin wawan zabura tayi jiki na tsuma da karkarwa cikin tsananin firgita da tarin tsoro ta sake kwaryar....!

By *GARKUWAR FULANI* 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 8

NA *AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

Kada dai ku mance Free page ne, yana kuma gab da karewa.

*Ga mai buƙatar saya ga number ta, 09097853276 turo ɗari uku ko dubunki ɗaya kacal domin samun damar karantawa cikin salama, Ga Ac ɗina 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, in kin biya sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number 09097853276 in ba halin turawa ta ac bisa dole turo katin mtn.*

Ta saki kwaryar, a sorace, da sauri yasa tafin hannunshi, biyu ya tare kwaryar. Cikin tsoro jiki na rawa ta zazzaro idanunta woje kana murya a hargitse tace. "Innalillahi wa innailaihi rajiun, Ya Ba'ana mekabani? Me ka shayar dani? Na shiga uku me kasa nasha?". Gaba ɗaya ta gigice tana rawan jiki da murya, ga hawaye kuma tuni suke shatata. Ganin yadda ta firgitane ya sashi matsowa gabanta cikin ɗaga murya yace. "Ba komai ba abinda na shayar dake Mata, wallahi Allah ki yarda dani wancan da kikasha babu komai a ciki". Da sauri taja da baya tare da cewa. "Ban yardaba me ka shayar dani?". Sai kuma ta fara kakarin amai da ƙarfi, ganin kamar aman bazai zo bane yasa ta tura yatsunta biyu a baki, amman ina aman yaƙi zuwa sam. Kawai sai tasa mishi kuka. Cikin tashin hankali yace. "Kiyi haƙuri Mata wlhi bazan taɓa shayar dake wani abu na guba, ko na ƙiba, duk abinda nasan bazaki shashi da sanenki ba bazan taɓa bakishi a ɓoyeba. Ki yarda dani wlh ban shayar dake komaiba". Ina taƙi ta saurareshi sabida tayi matuƙar firgita da tsananin razana da ganin abinda ke cikin kwaryar, cikin sauri yasha gabanta tare da cewa. "Ki gani mana ki duba babu komai a ciki fa madarar shanunce". Tsayuwa tayi tare da zubawa cikin kwaryar ido tas farin nonone kamar ko wanne nono da bashi da gamin komai". Hannutasa ta mutstsuke idanunta tare da kuma sake kallon, cikin tuhuma ta maida idanunta kanshi tana mishi kallo mai cike da tuhuma. A hankali ya sunkuya ya ajiye akwaryar kana ya taso ya fuskanceta da kyau fuska ya haɗe tare da cewa. "Sam bakya min adalci Mata, na lura dake, wani mugun zato da zargina kikeyi. A zatonki wai zan iya cutar da kene? Shin kin mance tun kina ƴar tatsitsiyarki nake sonki ne? Da inada mummunar niya a kanki da na cutar dake tun kina ƙarama. Kullum idanunki na nuna min baki yarda dani ba. Me kike nufi? ko dai wani kikeso ba niba?". Ya ƙarshe tambayar da taune bakinshi kana ya tsareta da idanunshi, da sauri ta sunkuyar da kanta tare da cewa. "A a ni kam babu wanda nakeso." Kanshi ya ɗan rausayar kana ya dawo ya zauna a bakin bukkar tashi, cikin kakkausar murya yace. "Dawo ki zauna". A hankali ta dawo gefen gaban bukkar ta zauna, shi kuwa wani ɗan randar ƙasan dake gefenshi ya buɗe, cikin haɗe fuska ya ɗan kalleta tare da cewa. "To zakiyi sabon Saurayi. Salmanun Arɗo Yabani, zai fara nemanki, kamar yadda munafukan tsoffin rugar nan suke tsarawa, dan ana son rabani dake". Da sauri taketa jujjuya kai tare da cewa. "A a Wallahi ni Yaya Salmanu, ba sona yakeba, ka sani tun ina ƙarama duk abinda ya shafi karatuna shike koya min har dai yasa aka sani. Makaranta kai kuma baka hanaba". Cikin haɗe fuska yace. "Ehh ai nasan ke baki san yana sonkiba, amman na lura shi yana sonki, kuma zanci ubanshi da bulalin shaɗi bashi babu sake kallon duk wani abu da nakeso". Cikin tarin tsoron kada a cutar da Yaya Salmanun tace. "Wallahi ƙarya ake mishi, baice yana sona ba, shi yama tsaneni ne yanzu, dan Allah Ya Ba'ana kada ka yarda da ƙaryar mutane". Kai ya rausayar tare da cewa. "Uhum kinga nan cikin ranɗar nan, to bulaline wanda nake shaɗi dasu, yanzu tsawon shekaru biyu kenan da aka hana shaɗi basu samu wanda suka dakaba, na tsumasu da tarin tsumi mai zafi, wanda muddin na zana jikin mutun dashi sai ya fashe, Kuma gasu a ƙalla sun kai tamanin a cikin randar nan kuma a ƙa'ida da guda goma sha bibbiyu kawai zakayi shaɗi to kinga kenan zan iya shadi da mutun sama da shida dasu basu ƙareba". Kanta taketa jujjuya mishi tare da cewa. "Ya Ba'ana kada ka yarda da sharrin mutane kasanfa Yaya Salmanu shike karantar dani, tun ina ƙarama kuma ko yanzu dana girma tunda shi ya rigada ya gama digiri ɗinshi shike fahimtar dani duk abinda ya shige min duhu, kuma tunda nazo hutun nanma ban haɗu dashiba". A hankali yace. "Eh ai yau kam zaki haɗu dashi". Yunƙura tayi ta tashi tare da cewa. "Uhumm, shike nan ni bari in tafi gida an fara kiran salla." Da sauri ya miƙe ya fito yabi bayanta tare da cemata. "To Mata jirani inzo in rakaki Mana". To kawai tace mishi, a haka suka jero suna tafiya yana gaya mata irin tsumin da yayiwa bulalin nashi.

Suna isa dai-dai garken su Shatu, ta ɗan tsaya hango yayunta sun dawo daga kiwo, cikin jin daɗi ta ɗan juyo ta kalleshi tare da cewa. "Bari inje wurinsu Ya Giɗi, in tayasu ɗaure shanun". Murmushi yayi kana yace. "To Mata ki kulan min da kanki kada shanu ya taɓa min ke, dan akan ɗan mai shanun zan rama miki ba kan shanu ba". To tace tare da juyawa ta nufi cikin tsakiyar taron dabobbi su da aƙalla zasu kai guda dubu da yan ɗaruruwa tsakanin shanu, tumaki, awaki, rakuma. Da sassarfa take kutsa tsakiyar dabobbin tana cewa. "Yaya sannunku da dawowa". Da sauri Giɗi da Seyo suka juyo murmushi sukayi tare da cewa. "Yauwa ƴar ƙanwarmu, daga ina kike?". Da ido ta nuna musu Ba'ana dake tsaye can gefe ya zubawa dabbobin nasu idanu tamkar mai ƙidanya su.

Gaini ne da Lado suka zuba mishi ido domin gaba ɗaya ya shagala da kallon da yakeyi, har wani ƙan-ƙance idanu yakeyi. Sam bayaji kiran da Babanshi Bukar ke auna mishi. Har saida Giɗi yace. "Heyy Ya ba'ana Ubanka na kiranka". Ya ƙirishe mgnar da bagwariyar hausarsa. Shi kuwa Ba'ana da sauri ya juya ya nufi wurin babanshin da yanzu ya dawo kiwo.

Cikin sakalci da gajiya Giɗi ya kalli yayunshi mazan tare da tura baki gaba yace. "Wayyoooooooo Allah bayana zai karye, Ni dai na gaji bazan iya sunkuyon ɗaure shanu ba, ga Shatu zata tayaku". Sai ya kuma kalli yadda duk suka sunkuya sunata ɗaure dabobbin suna ɗan dariyar yadda itama Shatu ta dage tana tayasu. Junainah ce wace dama duk lokacin dawowarsu zata kawo musu sassanyan kindirmo susha tun a nan kafin su koma gida. Da saurinta take ratso cikin shanayen tana cewa. "Ya Giɗi tareni, na gaji ga damunku". Da sauri ya nufi inda take kwaryar ya amsa kana suka dawo gaban bukkokin da nanne ma kwancin masu gadin dabobbin suke.

Zama sukayi ludeyayen dumar dake kan fefeyin daya rufe kwaryar ya ɗauke kana ya buɗe kwaryar, ludeyi ɗaya ya sa musu a ciki. Aysha dake kusa da sune ta zauna tare da cewa. "Ya Giɗi kama ka bani". Kai ya gyaɗa mata kana ya cika ludeyin yasha sannan itama ta ɗebo rabin ludeyin tasha, kana ta bawa Junainah itama ta kamfato ta cika ludeyin ko rabinshi bata zuƙaba. Ta miƙawa Ya Seyo dake tsaye gefensu, da murmushi a fuskarshi ya amsa ya sha, sauran nata, Shatu ce ta gyara zamanta ta matso kusa da ɗan uwanta tsokonta Giɗi abokin tsamarta, gyara zamanta tayi kana tace. "Ya Seyo zauna ga fili." To yace kana ya zauna suka fara sha, Lado ne ya kallesu cikin gajiya yace. "To wai mu aka kawowa ko kune?". Shiru babu mai magana sai kamun ludeyin da sukeyi, Gaini ne ya matso gefe shima ya zauna kusa da Junainah yasa hannu ya ɗauki wani ludeyin, nan suka zauna suna sha, ganin hakane, Ya Lado yace. "To ni naci girma". Da sauri Shatu ta mike wurinda ta tashi ta nuna mishi tare da cewa. "A a ya Lado zauna kusha ni na ƙoshi". Murmushi Bappa dake gefensu yayi, wanda yanzu ya iso da jarkan ruwa a hannunshi, Cikin kallon so da tausayin yaran nashi yakeyi, Cikin kula yace. "Sannunku- sannunku da rana, Allah yayi muku al'barka". Amin Amin suka amsa baki ɗayansu, Sai kuma ya kalli Aysha da Junainah yace. "Ayshatu maza kama hannun Junainah ku koma gida, kinji an fara kiran salla".

To tace tare da kamo hannun ƙanwar tata suka nufi gida.

Su kuwa Bappa da yaranshi da makiyayanshi anan sukayi al'wala, kana suka juya suka nufi cikin Rugar tasu dan zuwa masallaci. Yayinda ko wanne garke an bar mutun ɗaya sabida tsaro...

Bayan sallan isha sunci abinci sun ɗan taɓa hira, kaɗan kana Bappa ya tarasu yana karantar dasu kamar yadda ya saba duk dare, da kuma safiya kafin a tafi kiwo shiyasa sam ahlin wannan Rugar Bani ba jahilai bane.

Suna zaune, yaro yayi sallama, yace. "Wai ana kiran Shatu a woje". Ummey ce ta ɗan juyo ta kalli yaron tare da cewa. "Wake kiranta?". "Wai yace ince mata inji Ya Salmanu ne". Yaron ya faɗi. Da sauri Ummey tace. "A a Salmanu ne ya zobe? To maza kace ya iso mana ya zai tsaya a waje kamar baƙo". To yaron yace kana ya juya ya fita. Jim kaɗan sai gashi ya dawo gefen Ummey ya rusuna tare da cewa. "Yace wai ince mata, ta fito woje". "Da mamaki Ummey tace to gata nan zuwa". Sai kuma Inna ta ɗan kalli Shatu tace. "Tashi kije ai mun gama aikin ma". Ita kuwa Aysha dake zaune gaban Inna suna gasa tattabarun da aka yanka tunda yamma, kwano ta ɗauko a konɗonsu kana tasa gasassun tattabarun guda biyu. Tasa yaji a gefe, ta rufe, kana ta gyara wuyan hijabinta sannan ta miƙowa Junainah kwanon. A hankali ta ratsa gefen su Ya Giɗi ta wuce.

Ummey kuwa da ido ta rakasu tana fatan Allah yasa fata da shirin Bappa da Arɗo Yabani ya tabbata.

Suna fita suka sameshi zaune bisa dakalin ƙofar gidan nasu. Da sauri Junainah ta isa gareshi tare da cewa. "Oyoyo yaya Salmanu". Ajiye kwanon tayi a gefenshi. Da sauri yasa hannunshin suka tafa da hannunta data miƙa mishi, cikin sakin fuska da nitsuwa yace. "I miss you ƙanwali". Dariya mai ɗan sauti tayi tare da cewa. "Miss you too my dear". Dariya mai sauti sukayi a tare cikin jin daɗi wanda aka kira da Salmanu ya lakace hancin Junainah tare da cewa. "Alhamdulillah alama ta nuna ƙanwaliya tana zuwa makaranta babu wasa". Cikin jin daɗi tace. "Sosai ma ya Salmanu yanzu ajiyana huɗu fa, yanzuma dan hutu mukeyi, kuma gashi ko a gidama Ina karatu". Jinjina mata yayi da hannunshi kana, ya jawo kwanan data ajiye tare da cewa. "Ƙanwaliya me kika kawo mim ne?". Cikin murmushi tace. "Gasheshen naman tattabarune Ya Salmanu barima in koma ciki inci rabona inci na Addana". Kafin ya ankarama tuni ta juya da sauri tayi cikin gida.

Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da kallon Aysha dake jingini da bakin kofar zauren, Cikin sanyi yace. "Kamar bakiyi farin ciki da zuwana ba? Ko dai in komane?". A hankali tace. "A a Ya Salmanu nadai ga kamar kafi farin cikin ganin Junainah ne akai na". Murmushi yayi tare da cewa. "Kin rama kena". Murmushi sukayi dukansu, cikin sanyi yace. "Ga wuri kizo ki zauna mana". A hankali tace, "A a Ya Salmanu mu shiga cikin gida mana".

"Kina tsoron kada saurayinki yazo ya ganmune?". Salmanu ya faɗa a hankali. Da sauri tace. "Eh". Kanshi ya ɗan rausayar tare da cewa. "Babu abinda zai faru sai al'khairi zoki zauna, ki gayamin me kike tsoron?".

A hankali ta zauna gefenshi ɗan nesa dashi. Shi kuwa juyowa yayi ya fuskanceta a hankali yace. "Gaya min me kike tsoro?". Kallonshi tayi cikin yin ƙasa da murya tace. "Ina tsoron kada Ya Ba'ana ya cutar da kai, ina gudun kada sakaiyar alaƙarmu ya zama cutarwa, sabida Ni kamin rana a rayuwata, rana kuma ta al'khairi shiyasa bana son abinda zai cutar da kai". Murmushi mai yelwa yayi kana a hankali yace. "Ina sonki zan kuma aureki da izinin Ubangiji zan rabaki da wannan taƙadirin, domin baki cancanci zama matar mushurkiba". Da sauri tace. "Kada kace haka Ya Salmanu Wallahi zai cutar da kai, kada ka bari wani yaji, bare mgnar ta koma kunnenshi". Murmushi yayi tare da jawo kwanon ya buɗe. Numfashin yaja jin ƙamshin naman a hankali ya fara ci, saida yaci ɗaya kab sannan ya rufe kwanon yace. "Ga rabonki dan nasan Junainah ta cinye naki rabon". Cikin yanayin nitsuwarta tace. "A a kaci kawai Ya Salmanu". Da sauri yace. "No kada kimin musu". Shiru tayi jin yaci gaba da cewa. "Muddin dai ina raye in sha Allah. wallahi Allah bazan bari Ba'ana ya aureki ya lalata miki rayuwaba, zan jure duk azabar da zai shayar dani na shaɗi in Sha Allah zan aureki". Ido ta zuba mushi tana kallon shi cikin kamalarsa, ganin sam hankalinta ba'a kwance yakeba, yasashi ce mata ta shiga gida zasuyi mgna a waya, haka kuwa akayi, ta juya ta shiga gida shi kuma ya nufi hanyar gidansu.

A dandalin wurin da yake kamar kasuwar garin nasu ya samu abokanshi, kowa da budurwarshi suna ɗan hirarsu Can gefe kuma ga yara nata wasansu, ga farin wata ya fito yayi ras, kana iya ganin komai.

Ita kuwa Shatu, bayan sun gama shirin baccinsu, ta kalli Ummey tare da cewa. "Ummey".

"Na'am". Ta amsa mata cikin kula, sai kuma tayi shiru, ita kuwa Ummey ido ta zuba mata, ganin hakane yasa a hankali tace. "Ummey Ya Salmanu". Still kuma tayi shiru, Cikin kulawa da shaƙuwa wanda ke tsakanin uwa da yarta Ummey tace. "Gaya min mana, me Ya Salmanun yayi?". Konciya tayi gefen Ummi dake bisa sallaya, kana a hankali tace. "Wai yana sona, Ummey ina tsoro Ya Ba'ana zai illata mishi rayuwa, gashi kwanan nan Ya Hashimu ya rasu, kuma shima ance kasheshi akayi, Ummey ki cewa Bappa na, yacewa Baba Arɗo ya hana Ya Salmanu cewa yana sona, kinji ko Ummey?". Kai Ummey ta jinjina mata tare da cewa. "To zaki aureshi kenan duk da kinsan baya salla kuma yana tsafi". Kai ta juya tare da cewa. "Bazan aureshiba Ummey, amman ya Salmanu yayi shiru, bari in gama karatuna, in sha Allah akwai mafita in na gama karatuna, Ummey kin gane ai ko? Kin tuna ko". Murmushi Ummey tayi kana tace. "Eh na gane, yanzu konta kiyi baccinki". da haka suka konta bacci.

Bayan kwanaki, sosai lamarin Ba'ana yake bawa mutane tsoro, mutun kamar ifiritu, dan yanzu yanayin sihirinshi ƙaruwa yakeyi sosai, Wasu lokutan ba hawa ba sauƙa sai dai kawai ka ganshi a gabanka sabida yanzu layan ɓatarshi tama fi ta baya ƙarfi, ya dage wai zai bawa Shatu taƙi fir daya matsama kuka tasa mishi hakanne yasa ya hakura ya barta.

Ya Salmanu kuwa yanzu ya dage kan batun soyayyarsa da Aysha, ita kuwa tsoron abinda zai faru ya hana yarda da kowa, gaba ɗaya kuma yanzu Ƙabilar ɓachamawan nan masifa tuƙuru suke neman fulanin Bani dashi sabida baƙin ciki da hasadar ganin yadda shuke-shuken wurin fulanin yayi kyau, shinkafa, masara, dawa, gero, maiwa, wake, gyaɗa, gujjiya, riɗi, da dai sauransu.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull