Garkuwa complete novel - Chapter 12
Garkuwa complete novel Chapter 12: Garkuwa complete novel Chapter 12. Shigowan Hajia Mama da hadimanta ne, yasa Juwairiyya, jin rauni, a take hawaye ya…
4,422 words
Shigowan Hajia Mama da hadimanta ne, yasa Juwairiyya, jin rauni, a take hawaye ya cika mata idanu. A duniya bata da babbar matsala sama da larurar mijinta. Ita kuwa Mama, gefenshi ta zauna, cikin sanyi ta kalli, Jalal da fuskarshi ke murtuƙe kamar ko yaushe, cikin baiyanar damuwa tace. "Ya za'ayi ya samu gamsuwa da kulawarka, a yadda kake haɗe fuskarnan tamkar wanda aka sanarwar labarin mutuwar uwarshi, ba haka Sheykh ke mushiba, yana kula dashi, da tausayawa da sakin fuska tunda yasan larurar haukace dashi, amman kai ko yaushe kana nan kamar boss". Sai ta kuma kalli Jakadiyarsu Kana, ta kalli Jamil dake waya da alamun da budurwarshi yake mgna, hararanshi tayi tare da cewa. "A haka kuke samawa kanku tabon nunawa a rayuwarku, shi wannan ya zama, mahaukaci, shi Jalal ya zama tantiri ɗan shaye-shaye, kai baka da aiki sai bin matan banza. Kuna samin ciwo a raina, shima kanshi Sheykh duniya ta zata fara zargin cewa mazinacine shiyasa yaƙi yin aure ya zauna, sinƙitin fakitin. Shi kuwa Affan in banda shashanci da tarin ƙuruciya babu abinda yasa a gaba. Ya kukeso inyi, ya kuke son mahaifinku yayi? Yana da yaya maza har ku shida, amman ku biyar manyan duk kun zama, ababe masu taɓo a idon duniya, ya za'ayi yayi mararin gadar mulki a hannun mahaifinshi, tunda yasan shi bashi da masu gadarsa, a kusa,ku duba, Imran da yake uwarsa ta tambaɗaku, ta nesan taku da mahaifinku, sai ta kusanta ɗanta da mahaifin naku. Shiyasa mahaifinku keta ƙin amsar sarautar har sai randa Imran ya mallaki hankalinshi, ku kuwa kun zama ababen kyarata. Yaya zanyi da raina. Shiru sukayi gaba ɗayansu, Shi kuwa Ya Jafar sai ƙara sautin karatun yayi. Yanayi yana zubda hawaye.
Shi kuwa Jalal, shiru yayi yana riƙe da hannun Jafar ɗin. Jamil kuwa katse kiran yayi. Affan kuma wanda dama tare suka shigo, fuska ya ɗan kele, cikin irin matsayin da ƴan auta kedashi a wurin iyayensu yace. "Mama, shifa zato zunubine koda ya kasance gsky. Ki dena jifar Mommy da batun wai ita ta tambaɗamu, ya za'ayi keda kanki ki rinƙa suffantamu da marasa nagarta mu dai gsky ba a tamɓaɗe mukeba, Menene a cikin mulki da sarauta, Mama akwai wani mulkine matabbaci a duniya banda mulkin mahaliccin mu, in ma Imran ya gaji sarauta menene a ciki ɗan uwanmu nefa". Cikin sanyi ta girgiza kanta a hankali tace. "Ɗan uba dai ba ɗan uwaba". A tare suka zuba mata ido baki ɗayansu. Aunty Juwairiyya kuwa, ruggume yarta kawai tayi, tana jin ranta na suya.
A cikin fada kuwa, tun tuni Maimartaba ya fito, yana shigowa suka gaisa dasu Bappa ya amshesu a mutunce, cikin kulawa, da mutuntaka, bayan sun gaisa ɗinne suka koro mishi jawabin abinda ke tafe dasu. Shiru mutanen fadar sukayi baki ɗayansu, sai muryar Ardo Bani, da yake ƙare zancensa da cewa. "Babban tashin hankalinmu, kullum ɗauki ɗaɗɗayan da akeyima yaranmu da tsoffinmu. Kana a sace dabobbin mu, in mun kai kukanmu ga hukuma ko masarauta sai ayi burus damu, koma a ƙara mana da cin zarafi ko ƙazafi. To gashi yanzu ankai matakin ana sace mana yara, ko gawarwakinsu ba'a bar mana, shiyasa mukayi tattakin isowa gareka adalin shugaba, ka duba lamarinmu."
Wani irin zafi da ƙuna ne ya cika zuciyar, Maimartaba Lamido, zalumci yayi yawa. Gyara zaman babbar Al'kebbar sarautar dake jikinsa ya ɗan yi, yana maijin ƙuna da tafasa a zuciyarshi, fargaba da tsoron, haƙin bayin Allah'n da aketa kashewa ya cika mishi zuciya, sabida sanin shine sarki kuma shugaba, ga duk wani mutun dake yankin. Wani nannauyan numfashi yaja mai ƙarfi. Juyawa yayi ya fuskanci maga takardar fadar tashi, cikin bada umarni yace. "A rubuta takarda a aikawa Haman-Ɓachama cewar ina bukatar ganinshi, da gaggawa. Kana ya tabbatar kafin ya isoni yankin da yake mulka babu sauran zalumci, ko ƙabilanci!". Cikin cika umarnin da maga takardar ya ɗan rusuna, tare da cewa. "An gama ya Mai alfarma Sarki Adalin Sarki." Waziri, Galadima, Wambai, Sarkin fada, kana da sarkin dogarai, duk, shiru sukayi sabida a zahiri ake iya hanƙo tsantsar tashin hankali da ɓacin rai a fuskar adalin shugaban nasu.
Su kuwa su Bappa sosai sukaji sanyi, a zuƙatansu, sabida nuna kulawarshi garesu, cikin iya sarrafa harshe da tausasan laffuza mai martaba sarkin Nuruddeen Bubayero Joɗa yace. "Kuyi haƙuri, ku gafarceni, bani da labarin dukkan abinda ke faruwa daku, sai yanzu, naji daɗi da kuka nemeni, da matsalarku, In sha Allah ni kuwa zan ɗauki mataki, da izinin ubangiji koda belbelun dake cikin shanunku baza'a sake kashesuba, bare dabobbin ku, bare a kai ga rayukanku. Zan kirayi GARKUWAN FULANI, yanzu, zan sashi maza ya taho ya dawo ƙasar sa, Domin shiga lamuranku nauyin a kanshi yake." Sai kuma ya ɗan numfasa kana ya kalli wani bafadensa dake tsaye bayanshi yanayi mishi fifita da maficin da akayishi da gashin kekkyawan ɗawisu. Cikin bada umarni ya umarceshi daya koma gefe, Da sauri ya rusana ya koma gefen. Shi kuwa Sarki Nuruddeen, wani ɗan kekyawan matashi dake gefen damanshi ya kalla tare da cewa. "Imrana, kiramin Sheykh Jabeer." Kai ya ɗan rusunar kana yasa hannu ya amshi wayar da Kakan nashi ke miƙa mishi. Amsa yayi, kana ya kira Sheykh Jabeer, wanda shi kuma a dai-dai lokacin yana gaban Sheykh Aliyu, Abdulkareem, Jabeer, Sitti, Jazrah, Haroon. Da dai sauran ahlin nasu.
Wanda kiran ne yasa ya samu ya fece daga tarkon da ake naɗa mishi.
Jin wayar tayi ringing har ta katse ba'a ɗaga bane, yasa Imran ɗan rusunar da kanshi tare da cewa. "Wata ƙil baya kusa da wayar." Kai ya jinjina mishi tare da cewa. "A a zai kira, bayan amsa kirana yanzu zai kira". Kai ya gyaɗa alamar gamsuwa. Suko su Bappa duk suna zaune cikin kamala.
Shi kuwa Sheykh kamar yadda ya saba, hakane baya amsa kiran kakan nashi, sai dai ya bari in tayi ta katse sai ya kira, shiyasa, yanzuma ya bari saida ta katsen sannan ya kira.
Gyara zamansa yayi tare da kara wayar a kunnensa na dama.
Imran kuwa yana ganin kiranshi yayi maza ya amsa, cikin tarin girmamawa yace. "Barka da hantsi, Hamma Jabeer". A can gefen Sheykh Jabeer ɗin kuwa, ido ya lumshe cikin yanayinshi da sun rigaya sun saba yayi shiru. Da sauri Imran ya kuma ɗan rusunar da kanshi yace. "Afwan Sheykh Assalamu alaikum ". Murya can ƙasa yace. "Wa alaikassalam". Cikin ɗan tura baki Imran ya kuma maimaita mgnarsa ta forko. "Barka da safiya, Hamma Jabeer ya, Sitti?". A taƙaice yace. "Alhamdulillah". Da sauri Imrana yace. "Masha Allah, ga Lamiɗo". "Na'am". Yace a takaice. Shi kuwa Imran miƙawa kakansu wayar yayi. A hankali Sheykh ya ɗan buɗa laɓɓansa cikin zazzaƙan sautin muryarsa yace. "Assalamu alaikum". Murmushi mai cike da so da ƙaunar jikan, nasa yayi tare da amsa sallamar tasa. Gaisawa sukayi, bayan sun gaisa ya tambayi labarin su Sitti da ƙanennenta da kuma mahaifinta, sai kuma ya kora mishi jawabin abinda ke faruwa a jihar tasu. Kana, ya ɗoro da cewa. "Ka dawo, kayiwa lamarin tubkar hanci". Cikin sanyi yace. "In sha Allah. Ina nan tafe, nanda kwanaki uku. Ina jajanta musu, abinda ya faru, kuma in sha Allah. hakan bazai kuma faruwa ba.
Da haka sukayi sallama.
A can garin Numan kuwa cikin Rugar Kikan.
Gaba ɗaya garin shiru yayi, dan wannan abunda ya faru yayi masifar shiga jikinsu. Da dama maza matasanmu sun tafi kiwo, kamar yadda suka saba, rayuwar yau da kullum. Saura sai irin dattawan da aka bari, da mata da yara maza da mata.
Cikin garin Bonon kuwa, gaba ɗaya, matasan garin dama ƙauyuka gefensu na ƙabulun Ɓachamawa, duk sun hallara wuri ɗaya, suna cike gaban dodon tsafinsu, wato Bonon ɗin, giyar burkutu mai ɗan karen tsami da wari, suketa sha, tamkar zasu fasa cikkunansu. Yayinda gefe guda kuma, maƙerar dake gefe wasu matasa su ne maƙera keta wasa ababen faɗansu, kamarsu wuƙaƙe, Adda, sitaka, barandami, mashi, kibau, da dai sauran mugayen makamai, sai sheƙi sukeyi.
Suna cike a wurin, Ba'ana ya iso, cikin wata shigar rigar saƙi. Hanya suka rinƙa buɗa mishi, hardai ya isa ga sarkinsu, dake zaune gefen dodo sun. Zama yayi kusa da sarkin nasu ya sasu a gaba, Cikin harshen ɓacamancin yace. "Ku hanzarta, ku shiga, duk matasansu majiya ƙarfi, sun tafi kiwo. Dottijan su kuma sun tafi, kai gulmarku, ga Sarkin su wannan karon basu tsaya ga sarkinku na nanba, ina da yaƙinin kuma za'a sauraresu a can. Yanzu matansu da ƴaƴansu, ƙanana mata da mazane suka rage a garin. Sai wasu dattawansu dake, dakon dawowar magulmatan can. Kuyi maza, kushiha kafin su dawo, ku share garin kab. Ku kashesu gaba ɗaya babba da yaro mace dana miji." Da sauri wani daga cikin su yace. "Harda gidansu Shatu?". Cikin izaya yace. "Harda su, domin Mata, bata nan, ku kashe kowa nata, ta hakane zata dogara dani kaɗai tunda bata da kowa nata a duniya, dole Ni zan zama mijinta ubanta yayunta ƙannenta uwarta, in zama Garkuwarta in zame mata duniyarta ta hakane zata yarda nine ɗaya gatanta kuma duniyarta, ba tare da ta zargeniba, a hankali wata rana in sata tayi ridda, musha giya, muyi tsafi tare da ita, bazatayi min musuba, mu haifi ɗanmu na forko mu bawa dodonmu yasha jininshi yasa mana al'barka a aurenmu". Wani irin ihu da sowa na tsantsar jin daɗin bayaninshi sukayi baki ɗayansu. Hakama dodonsun, saida ihunshi ya firgitasu baki ɗayansu. Dariya mai amo mara daɗin ji. Sarkin nasu yayi, kana ya busa ƙahon dodonsun, alamun ya basu izinin tafiya.
Nan fa duk suka rinƙa shiga, cikin maƙerarnan suna ɗaukan makamai, suna nufar garin Rugar Kikan (Rugar Bani) kenan a guje...
Cikin garin Shikan kuwa, Bani rana ta fara tasawa, mata masu zuwa tallan nono cikin garin Numan, suka fara ɗaukar ƙorarensu, suna fita garin. Yara maza da mata kuwa, wasu na wasa wasu na ɗebo ruwa, wasu na ɗebo kayan lamɓu. Yayinda wasu kuma suka dawo break dan tara tayi.
Cikinsu kuwa harda Junainah.
Tafe take da saurinta da ɗan tsalle-tsallenta tana rataye da yar jakarta, da sauri ta tsaya ganin Junaidu a gabanta rike da kwanɗon zabari wanda yake cike da ƴaƴan itatuwa. Murmushi ta ɗanyi tare da sunkuyar da kanta cikin surutunta tace. "Har naji tsoro!". ta ƙarishe mgnar tana kallonshi, Murmushi yayi mata shima cikin son ƴarinyar yace. "Haba dai, tsoron me kuma zakiji, tunda gani, babu abinda zai sameki muddin ina raye, zan zame miki Garkuwa". Da sauri tasa hannu ta rufe bakinta tare da cewa. "Kai! Kai! Ya Junaidu, sunan Babanmufa ka kira". Murmushi mai kama da dariya yayi kana yace. "Au na manta ashe sunan surki nane". Kai ta gyaɗa mishi kana tasa hannu ta amshi, nonon inabin da yake miƙa mata, baki ta buɗe da nufin sawa a baki, sai kuma ta tsaya tare da tura baki jin yana ce mata. "No kada kici ba'a wonke bafa." Sai kuma ya ajiye kondon, ya amshi inabin ya ɗan gangara, gefe kaɗan ya wonkeshi a bakin ruwan wutsiyar Kogin da yayiwa Rugar tasu ƙawanya. Ya tahowa tana kallonshi.
Koda ya iso miƙa mata yayi, kana ya ɗauki kondon, ganin still tanata kallonshi ne ya sashi cewa. "Ya dai?". Kai ta kauda tare da fara tsinkar ƴaƴan inabin tana afawa a baki tana taunawa, Murmushi ya kumayi ganin yadda ta lumshe idonta. A hankali tace. "Ya Junaidu kayi kyau sosai yau, har kamar ka fini kyau". Dariya ya ɗanyi kana yace. "Yo dama ai na fiki kyau". Maƙe kafaɗa tayi tare da cewa. "Uhum a a kam". A haka dai suna tafe suna hira.
Can cikin gida kuwa, Ummiy ce zaune bisa kujera ƴar tsuguno da buta a gabanta, alamun al'walan sallan walaha, zatayi. Inna kuwa, da wasu maƙotansu uku Biba, Hari, da Innawuro. suna zaune bisa taburma a tsakar gidan. Suna amsar gaisuwa.
Can cikin garin kuwa su Alhamdulillah Manu dasu Siddine da dai sauran dattawan garin ne zaune a fada. Sai yara daketa kai komo.
Da sauri su Siddi suka miƙe tsaye ganin, matasan mayaƙan ƙabilar ɓachama, sunata shigowa garin tako ina gabas da yamma kudu da Arewa, bisa dukkan alamu zobe sukayiwa garin Kana ga zurma-zurman makamai masu tsawo tamkar raƙumai. Sai sheƙi sukeyi.
Cikin ɗaga murya, Alhaji Manu yace. "Kai lfy? me haka?". Ganin sun nufosu gadan-gadan ne yasa, suka miƙe gaba ɗayansu, kowa ya fara, neman makari, to amman ina, basu da zato ko sanin za'a far musu, shiyasa basu da shirin komai na kare kai. Ɗaya daga cikin sune, yace. "Mu gudu kashemu sukeda shirin yi ba tare da laifin komaiba". Siddine ya kuma ɗaga murya tare da cewa. "To in mun gudu matanmu da yaranmu fa". Ihun da sukajiyo tako wani sashi na garinne ya tambatar musu, ana karkashe su. Gudu suka farayi kowa ya nufi hanyar gidanshi dan ɗaukar matakan kare kai. Sai dai ina basu da hanya duk inda suka ɓullo sai sunci karo da, mayaƙan.
Lokaci ɗaya garin ya ruɗe ya birkice kota ina sai ife-ife da gudun ceton rai da makiyayan Rugar Kikan keyi.
Wani irin sauti mai baiyana azabar fitan rai Alhaji Manu yayi, lokacin da wani kafurin ya caka mushi sitaka a ƙahon zuciyarshi. Siddine ne ya juyo da azaban razani, amman sai shima ya saki wani sauti mai gigitarwa jin azaban sara da sukan da akeyi mishi. Garifa ya kacame, Hadi ne babban ɗa ga Alhaji Haro mahaifinsu Junaidun Junainah, ya nufi cikin gidansu da azama, Yana cike da fargaba, da tashin hankali domin wasu irin ihu da yake jiyowa a cikin gidan nasu. Yana kusa kai ya samu, makasan suna cike a gidan. Suna ta'addanci, sun kashe kowa na gidan. Ganin haka ya juyo yana juyowa. Yayi kiciɓis da abokinshi Sale, yana tafe jini na zuba an farka mishi ciki. Cikin magagin mutuwa yake cewa. "Hadi sun kashe kowa na garin nan sai wanda baya nan. Hadi na kira Hukumar yan sanda ta nan cikin Numan na shaida musu, amman kafuran nan maƙiya Allah da Manzonsa sai cewa sukayi, A kashe mu mana, ai an rage musu aikine. Na kira su Arɗo Bani, suna ɗagawa katin wayata ya ƙare. Hadi sun kashe kowa na gidanmu. Taroshi Hadi yayi suka faɗa nan suna kuka mai cike da taraddadin rabuwa. Cikin ƙarfin hali Sale ya ture Hadi tare da cewa. "Ka gudu Hadi ku gudu, Ni nasan bazan rayuba. Ka gudu. Sun kashe min Kowa har jariren tagwayen da aka haifa min shekaran jiya, sun kashesu.
Cikin kuka Hadi yace. "Bazan iya guduba Sale su kasheni kawai, ina zanje bayan sunyiwa garin zobe. Da ƙarfi Hadi ya abka jikin Sale Jin ansa gatari an sari kafaɗarsa ta dama, Juyowar da zaiyi kuma aka tsira mishi mashi a ƙirji. Nan take ya cika, hakama Sale.
Cikin gidansu Shatu kuwa. Ummiy ta sallame sallan kenan, taji. Inna dasu Innawuro suna kurma ihu da salati. Yunƙurawa tayi da azama jiki na rawa ta nufo woje. Fitowanta yayi dai-dai da lokacin da aka sare kan Innawuro, wanda kan yayi tsalle ya faɗo kanta, kana ya gangara ya faɗa gabanta. Wani irin ihu mai cike da karaji gauraye da salati ta kurma lokacin da taga an burmawa Inna mashi a ciki. Ihunta da salatinta ya jawo hankalin su, sukayo kanta. Sai dai kafin su isoma ta yanki jiki ta faɗi babu numfarfashi tamkar matacciya.
Koda suka iso, dariya suka kece da ita cikin rashin imani ɗayansu yasa ƙafa, ya taka ruwan cikinta, tare da cewa. "Shegun FULANI ku mutu, mu huta, da ganinku a garinmu, gonakinku da dabobbin ku duk sun zama namu. Mu ɗauke yaranku mata mu maidasu karuwanmu, muyi musu ciki su haihu mu bawa dodo. Muji daɗi dasu.
Ganin kamar ta mutune yasa suka tattakata suka wuce suka fita daga gidan.
Junainah kuwa da Junaidun, suna gab da shigowa garin suka fara jiyo ihun mutanen garin. Cikin azaban firgici Junaidu ya wurgar da kondon ƴaƴan itatuwan dake hannunshi, da gudu yabi bayan Junainah data ruga a guje sabida hango, anata kashe mutane a gabansu. Cikin kuka da tarin kiɗima da fita haiyacinta take cewa. "Wayyo Ummiy Wayyo Inna Wayyo Bappa, zasu kashemu. Wayyoooooooo Adda Shatu zasu kashemu". Riƙo hannunta yayi da ƙarfi cikin rawan jiki da murya yace. "Junainah bazasu kashekiba, zan kareki da izinin ubangiji, zaki rayu, Shatu bazata rasa kowa duniya ba. Junainah zan zame miki Garkuwa zan fanshi ranki da nawa ran. Ki zama tamkar yar tsira, Shatu ta zama tamkar yar jarida, ta rubutawa mutanen duniya su karanta, kisan gillan da akeyiwa Fulani mazauna daji. Da ƙarfi yasa hannu ya zaro wukar dake ƙugunshi wanda da ita ya yayyanki nonunan ayaba dasu inabi. Wayarshi ya kuma zarowa Ya Salmanu ya kira, Salmanu kuma dake, kwance a gadon asibitin nan Genaral Hospital Numan. Wanda bai workeba tun dukan shaɗi da ba'ana ya mishi. A hankali yasa hannunshin ya amsa kiran wayarshi ganin Junaidu ke kiranshi. Cikin kiɗima da firgici Junaidu yace. "Ya Salmanu, mayaƙan ƙabilar ɓachama sun shigo Rugar mu, sunata kashemu, mazanmu da matanmu. Ya Salmanu Junainah ina son ta tsira, ko dan ran Junainah ka kira mana hukumar yan sandan cikin Adamawa, ina son su iso su ceci Junainah kada Shatu ta rasa kowa a duniya. Ban saniba ko zan gazawa bawa Junainah tsaro". Gaba ɗaya jikin Salmanu rawa da tsuma yakeyi, katse kiran yayi da sauri ya kira. "A.S.P Kabiru Nasir. Wanda yake, Hetkotan Adamawa. Koda ya mishi jawabin abinda ke faruwa, a take. A.S.P ya kira. S.P Daniyel dake Numan ya bashi doka da oda maza-maza su bawa fulanin Rugar Kikan tsaro gaggawa, shima yana nan tafe da rundunar sa. Ya bashi umarni mai ƙarfi ya ƙara da cewa, muddin yazo ya samu ba dai-dai ba ta ɓanƙaren tsaro, to akan aikinshi.
Wannan abun na umarni daga samane, yasa mugun kafurin nan. Firgita gudun rasa aikinsa, da tonuwar asirinsu da gudun kada a cireshi asa musulmi a kujerarsa, yasa cikin gaggawa ya haɗa kan rundunar sa ya nufi. Cikin Rugar Kikan.
Junainah kuwa wani irin karkarwa takeyi wanda, tuni fitsari ke tsiyaya yana bin sawunta. Wani irin ihu tayi, ganin wani kafurin ya kaiwa Junaidun sara a bayanshi. Wani irin juyi Junaidun yayi ya farma kafurin da da wuƙarsa dan kare kansa da Junainah. Duk da su biyar suka zagayesu, basuyi nasara a kanshiba, yana kare kanshi da Junainah, har saida suka tsira daga waɗannan. Sai kuma wasu, mutun takwas suka cimmusu. Da ƙarfi suka banƙaren Junaidun, suka fara kiciniyar zare Junainah da ya ruggumeta da azaban ƙarfi da yayi. Wani irin ihu yasa jin an caka mishi. Wuka a gadon baya. Still bai saketaba, sai yaƙin kareta da ya farayi, da iya ƙarfinshi. Ita kuwa Junainah ganin an caka mishi wuƙane yasa ta sume. Dai-dai lokacin kuma rundunar yan sandan suka iso.
Kamar bazasu guduba, dan sun san da bakin hukumar sukeyin aikin, to sai dai ganin musulman cikin yan sandan suna sakin harbine yasa. Suka ari ta kare.
Daga nan suka rinƙa gudu sunayiwa yan uwansu fito alamun su gudu. Cikin ƙanƙanin lokaci duk suka gudu.
Su kuwa yan sandan, suka shiga cikin Rugar Kikan ɗin. Hankalin musulman cikinsu yayi masifar tashi ganin irin kisan gillar da akayiwa bayin Allah'n nan, kisa na rashin imani. Nan take suka kira motocin asibiti. Suka rinƙa jidon masu sauran rai suna sawa a motar ambulance suna kai cikin Genaral Hospital Numan. Kana suna harhaɗa gawakin kuma a tsakiyar garin. Cikin mintuna talatin rundunar A.S.P ta iso. Tare da yan jaridu.
Su Bappa kuwa. Koda suka gama tattaunawa da Maimartaba, sai ya umarci Waziri daya hanasu tafiya a bisa adalcinsa. Yace su tsaya suci abincin rana, kana suyi sallan azahar kafin su tafi. To haka yasa suka zauna. Waziri yasa akayi musu duk ihsanin da Maimartaba ya bada umarnin ayi musu. Sukaci abinci sukasha, Sannan sukayi sallan azahar. Daga nan aka sallesu suka tafi.
Tuni cikin gari kuwa gidajen rediyo sun ɗauka, batun faɗan FULANI makiyaya da Ɓachamawa manoma, wanda akaso a juya rahoton da cewa makiyayan ne sukayiwa manomanne ɓarna.
Bayan. Tafiyan su Bappa da kamar 30 minutes ne. Labari abinda ya faru ya riski Maimartaba. Nan take yasa Waziri da Galadima da hadimai mutun ashirin suka nufi cikin Numan dan suje su tabbar da abinda akace ɗin.
Su Bappa kuwa, sam basuji lbrinba saida suka isa cikin Numan. Ganin garin a hargitse ne yasa Arɗo Bani ya kalli Bappa da Alhaji Haro da suke gefenshi cikin mmki yace. "Lafiya kuwa? Meke faruwane a garin nan?". Cikin kaɗuwa suka haɗa baki wurin cewa. "Allahu alamu". Drivern nasune, ya kallesu a tsorace yace. "Anya kuwa yau ba faɗa akeyiba a garin nan ba".
"Kai ba lfy ba kam!". Cewar Alhaji Umaru Shi kuwa Drivern, bakin titi ya ɗan gangara ya tsaya, ya tambayi wasu yan agaji daketa. Shiga cikin wani babban Pharmacy da alamun magunguna suke saya, koda suka mishi bayanin abinda ya faru. Jiki na rawa yazo ya sanarwa su Arɗo Bani. Lokaci ɗaya hankalinsu. Yayi masifar tashi. Nan sukace ya wuce dasu. Asibitin.
Koda sukaje hanasu shiga akayi. Hakane yasa, sukace to ya wuce dasu Rugarsu. Suga ko canma akwai uban da zai hanasu zuwa.
Nan ya nufi cikin Rugar tasu dasu.
Su Wazirima tuni, sun iso.
A can cikin masarautar kuwa, Sosai hankalin Maimartaba ya tashi.
A can ƙasa mai tsarki kuwa.
Sitti ce tsaye gefen Sheykh lokacin da yake mgna da kakanshi. Zama tayi gefenshi, tare da tsareshi da ido. Baibi ta kantaba, ya ci gaba da sarrafa wayarshi. Wata number, ya dannawa kira kana ya kara wayar a kunne, jim kaɗan aka amsa kiran. Bayan sun gaisane, ya ɗan gyara zamanshi tare da ɗan kallon Sitti ta gefen ido Cikin harshen fillanci yace. "A haɗa min zama da Ƙungiyar TABITAL POOLAKU". Sai kuma ya ɗan shaƙi sanyi da ƙamshin ɗauki ido ya lumshe cikin kamala da nitsuwa yaci gaba da cewa. "A kira min Ƙungiyar MIYETTI ALLAH, da gaggawa, ina da zama dasu. Ranar Jumma'a in sha Allah". Hannun damanshi yasa yana shafa sajenshi, tare da sauraron mgmar da. Arɗon Arɗaɓe keyi. "Ranar jumma'a kuma? Ka dawone?". A takaice yace. "Zan dawo!". Cikin gamsuwa da mgnarshi sanin in yace eh, eh ɗince in kuma yace a a, tofa a ance. Muddin kuma yace zaiyi abu to da izinin ubangiji sai yayi shi. Cikin jin daɗi adalci da kulawarshi ga shugabanci da aka bashi yace. "To Allah ya dawo da kai lfy". Yatsun ƙafarshi ya sunkuyar saida suka ɗan bada sautin ƙaras, kana yace. "Amin ya rabbil izzati". Daga nan ya katse kiran.
Kamar bata wurin haka ya jawo System ɗinshi ya fara daddannata. Kamar babu kowa kusa dashi haka yaci gaba da aikinshi. A system, ita kuwa Sitti ido ta zuba mishi. Tana kallon yatsun hannunshi da yaketa sassarfa, tamkar shiya haaliccin na'ura.
Yanajin idanunta na yawo a sasan jikinshi, hakan yasa, ya ɗan juya kwayar idanunshi, ya ɗan kalleta ta wutsiyar idonshi, murya can ƙasa yace. "Sitti wannan kallonfa, kin san bana son kallo kam ko?". Ajiyar zuciya ta ajiye, kana ta ɗan janye Hiramin kanshi, da sauri yasa hannunshin ya kame hiramin cikin kwaɓe fuska yace. "Sitti ya haka, kinsan Haroon ba kan gadone dashiba, yanzu zai iya shigowa da yaran nan". Ido ta ɗan rufe kana tace. "To su yaran mayune, ko yaushe kana rufe da Al'kyebba da hirami, kasha iska mana, ko nauyi basa makane?". Kanshi ya ɗan juya kana a hankali yaci gaba da aikinshi tare da cewa. "Suturce jiki shine, zaiyiwa ɗan adam nauyi, Sitti, sannan ya za'ayi in bari ko wani Tom and Jerry su kallarmin suman kai, ai shi hula da hirami kamar ɗan kwaline wa mace". Sai ya kuma ɗan juyowa ya kalleta tare da cewa. "Yauwa Sitti, bana son ana sawa Jazrah tana samin abinci, bana so, sai a turrota tazo taita kare min kallo". Fuskarta ta haɗe kana tace. "To yayi kyau, kawai in baka sonta, ka fito fili ka faɗa mana". Kauda mgnar yayi tare da cewa. Ki shirya in sha Allah zuwa ran jumma'a ina son in kasance cikin ƙasata ta haihuwa a jiharmu a kuma masarautarmu". Haroon da yanzu ya shigone ya ɗan kalli ɗan uwan nashi, cikin mmki yace. "Sheykh kawai dan ana mgnar baka matar aure shine kake shirin guduwa zaka bar ƙasar ba?". Bai kalli Haroon ba kuma baice, komai ba, sai rufe system ɗinshi yayi kana ya miƙe a hankali, gaban drower'n gadon ya nufa, buɗewa yayi, wasu E Passport guda biyu ya ɗauko, Kana ya dawo gaban Haroon. Hannun shi ya kamo ya danƙa mishi su, kana yace. "Gasu, ina son zamu bar ƙasar nan ranar al'hamis." Da sauri Sitti tace. "Kaida waye zaku tafi". Ba tare daya kalletaba yace. "Da ke". Kai ta kuma juyawa tace. "A a kam ka koma kai ɗaya, ni ban gaji da ganin ahlinaba". aKanshi ya kaɗa tare da cewa. "Zafa ki koma, don bazan barki a kasar nanba, kiyi ta haɗa min tarko, dole tare zamu tafi, inada zama mai mahimmanci, dole inje inji da matsalar al'ummar da aka naɗani GARKUWANSU, tunda ke kika sa na amince da wannan naɗin, ina zamana lfya, wani mulki ko sarauta basa jadawalin rayuwata, keda waɗancan tsofoffin sarakunan kuka likamin wai GARKUWAN FULANI, To sun samu matsala kuma dole inje in bincika". Shiru kawai Sitti tayi ganin karfin hali ziraran miraran. Zuwa yanzu ta dena mmkin, cewa akan abu biyu Sheykh ke iya doguwar mgna, akan Alqur'ani, wanda shine zaka samu zai iya wuni a zaune yana tabsiri ba gajiya ba yunwa bare ƙishi ko bacci. Sai kuma akan wannan sarautar GARKUWAN FULANI da aka bashi shekarun biyar baya, wanda harga Allah baison wannan Sarautar ko kaɗan sai dai dole da akayi mishi, da fushin da Abbunsu ya nuna a kan haka. Shiyasa duk sanda zaiyi ƙorafi yakan iya jera mgna biyar zuwa bakwai, wanda sam shi tsarin rayuwarsu ba mai doguwar mgna bace.
Kai takaɗa jin yana cewa. "Ku ɗan bani wuri". Basuyi mgna ba suka fita, a tare, domin sun san Sheykh Jabeer mutunne mai tarin tsananin al'kuyya da killace jikinsa, shi kanshi yana kunyar kanshi a rayuwarshi ta duniya shi bai taɓa yin tsirara a kan kanshi wai yaga surar jikinshi ba, Allah yasani yana masifar jin kunyan kanshi. Haka yasa koda wonka zaiyi, baya yin tsirara, yanada wasu tausasan gajerun towel wanda duk rintsi dasu yakeyin wonka a jikinshi.
Suna fita falo, Haroon ya tsaya yana kallon Jazrah, dake konce bisa kujera ta kife kanta a cinyar Jannart tana kuka mai sanyin sauti. Kai Sitti ta juya ta nufi ɗakinta, Allah ya sani Jazrah na son Sheykh, shi kuwa bai nuna ya tsaneta ba, amman dai ya nuna zahirin bazaiyi aureba.
Haroon da Jannart ne suka zauna suna bata baki. Saida ta nitsune suka fita tare.