Kenza eBookz

Garkuwa complete novel - Chapter 14

Garkuwa complete novel - Chapter 14

Garkuwa complete novel Chapter 14: Garkuwa complete novel Chapter 14. Jakadiyarsu kuwa da Jamil da Jalal da Affan Haroon suna falon sunata hirarsu.

4,125 words

Jakadiyarsu kuwa da Jamil da Jalal da Affan Haroon suna falon sunata hirarsu.

A tare hadiman Mama dana Juwairiyya suka kawo, abin kari. Suna fita ba da ɗewa, hadiman Gimbiya Aminatu kakarsu kenan. Suka shigo suma da abun kari.

Suka jera komai kan babban dinning table dake dinning area'n dake falon. Bayan sun fitane.

Suna cikin hira, sarƙin ƙofa, ya shigo, ya shaida musu, ga saƙo an kuma kawowa. Jamil ne ya bada daman a shigo. Nan ya juya ya fita, jim kaɗan, aka turo ƙofar.

Cikin mamaki suka zuwa ƙofar ido. Ganin M....!

*Wannan shafin nakine ke ɗaya MRS SARDAUNA, Sheykh yana godiya da soyayyarki gareshi. Domin duk masoyanshi bayanki sunka biyo*

By *GARKUWAR FULANI*

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🐄🕊️🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 14

NA *AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🐄🌈🦚🤴🏻💘

*Daga gobe ne, FREE PAGE zai ƙare, in da zan saki page 15-16 daga su kuma in kin sake ganin littafin GARKUWA a woje ba cikin groups ɗin da na buɗe nasa wanda suka biya ba, To na satane, na waɗanda basu san darajar iyayenka da girman Allah da Manzonsa suka fitar ne, to ke kuwa in kin san darajan iyayenki da girman Allah da Manzonsa, kada ki karanta na sata, akwai group ɗin ɗari uku kacal ban tsauwala ba dan nasan halin TLC da muke ciki a ƙasar nan ga mai wadata wacce take da dama taga zata iya biyan na Special Group 1k ne rak. Zaki turo ta asusuna 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276, kuma ƴan 300 zaku iya turowa ta ac na ɗin, in kuma baki da dama to turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number dai 09097853276. Dan Allah da Manzonsa in kin san zaki fitarmin da littafi biyoni PC ki gaya min wlh zan baki kuɗinki in fiddaki group salum-alum, ina kuma jin san saya zakiyi ki fidda na roƙeki da Allah da Manzonsa wanda bayansu babu wani kada ki saya ki riƙe kudinki ki barni in riƙe littafina🤗*

FREE PAGE, daga gobe dai zasu ƙare ki biya kuɗin ki in kinada niyan saya.

Ganin Mom ce, yasa fuskokinsu ya baiyana abinda ke cikin zuƙatansu. Cikin ƙasaita, Mom ke tafiya, hadimanta biyu na biye da ita da manyan kuloli na al'farma. Jakadiyarsu ce tayi murmushi mai kama da yaƙe, tare da rusunar da kai, cikin girmamawa tace. "Barka da shigowa, Gimbiyar ahlin masarautar Joɗa. Cikin isa da ƙasaita ta gyaɗa mata kai bayan ta zauna, gefen Jamil dake ruggume da waya kamar, abin masifa, Kanta ta ɗan juyo ta kalli Jalal daya haɗe fuska, Juwairiyya yace ta ɗan gyara zamanta tare da cewa. "Barka da safiya Mom". Murmushi mai wuyar fassarawa tayi, tare da taɓe baki, a gyatsine tace. "Barka dai". Sai ta kuma juya ta kalli inda Jakadiyarsu ke zaune, cikin isa tace. "GARKUWAN YA FITANE?". A daƙile Jalal yace. "Yana ciki kuma hutawa yakeyi". Ko inda yake bata kallaba tace. "Jakadiya ina buƙatar ganinshi, yanzu". Cikin biyeyyarta tace. "Ranki ya daɗe, in zaton bacci yakeyi". A taƙaice tace. "A tadoshi". Haroon dai ido ya zuba musu yana ganin ikon Allah, kowa ji da kai da ƙasaita. Juwairiyya ce ta ɗan kalli Haroon ɗin cikin sanyi tace. "Ukhti, shiga ka sanar mishi". To kawai yace, kana ya miƙe ya shiga bedroom ɗin, da Sheykh ya shiga mituna ashirin baya, kasake yayi a bakin kofar ganin babu kowa a cikin bedroom ɗin. A hankali ya tako ya shiga ciki, bakin ƙofar bathroom ya ɗan matso, kunnenshi ya kasa wai a lissafinshi ko zaiji mitsin ruwa. Shiru babu kowa a ɗakin da kuma bathroom ɗin. Ko ina yayi tsit sai wani fitinenne sanyi daya cika ɗakin, wanda sai sautin A/C dake busawa shuuuuu a hankali. Waige-waige yayi ganin babushi babu, motsinshi ne, ya sashi ɗan ɗaga murya yace. "Jabeer! Jabeer!! Jabeer!!!". Jin shirune yasashi sa hannunshin ya ɗan ƙonƙosa ƙofar bathroom, still shiru. Hakane yasa ya ɗan tura ƙofar, wayam baya ciki. Ganin hakane ya sashi juyawa, shima ɗin cikin takun ƙasaitar ya fito gefen Jalal ya zauna tare da kallon Juwairiyya,kana yace. "Baya cikifa". Wani irin kallo Mom tayi mishi, wanda yake nuna abinda ke bakinta, cikin ɗan sakin fuska yace. "Allah kuwa Mom baya ciki". Kanta ta gyaɗa tare da yunƙura ta tashi tsaye. Kana a hankali tace. "Uhummm". Sai kuma ta juya ta kama hanyar fita, hadimanta na biye da ita a baya. Har yaje bakin ƙofa ta juyo tare da cewa, Ga breakfast ɗin Garkuwa". Haroon ne yayi godiya kana ta juya ta fita.

Cikin mmki Haroon ya kalli Jamil tare da cewa. "Jamil baya cikifa". Murmushi Juwairiyya tayi tare da cewa. "Kun dai haɗa baki, kunƙi ya fito, ya gaisa da Mamanshi". Jalal ne ya ƙara tsuke fuskarsa tare da cewa. "Mamarshi ko makirarshi". Jakadiyarsu ta ɗan gyara zama tare da cewa. "Uhummm, sanin halin mutum sai Allah". Sai kuma ta kalli Haroon tace. "Haroona kace mishi yazo yayi karin kumallo, kace mishi daga sashin Gimbiya Aminatu ce, ga kuma na Juwairiyya". Cikin jaddawa yace. "Allah kuwa Ummi baya cikifa". Da mamaki a fuskokinsu suka ɗan kalleshi, Jamil ne yace. "Bai fita bafa". Juwairiyya ce, ta amshi zancen da cewa. "To kuma dai bai biyo nanba, tunda ya shiga bai fitoba". Shi dai Haroon Ido ya zuba musu, ganin kamar basu yarda Jabeer baya cikiba. Kuwa hakanne, saida Jamil yaje ya duba babu shi a ciki babu alamarsa.

Cikin tarin mamaki ya sanar musu, baya nan ɗinfa. Jalal ne ya ɗan kauda tunaninsu da cewa. "To kunata surutu, ta ina zakuga sanda ya fita, kai Jamil hankalinka duk na kan waya ina zaka ganshi." Cikin kula Jakadiyarsu tace. "Kaga fitarsane?". Baki ya ɗan taɓe tare da cewa. "Ni ban ganiba, na dai san shi ba kuɗi bane bare ya ɓata, ku jira zaku ganshi". Da haka sukayi amanna dan a zatonsu yaga fitarshi kawai bauɗewarshi ne yasa bazai sanar musuba.

A can cikin fadar Masarautar Joɗa kuwa, falon sashin mai martaba Lamiɗo, cike yake da ƴaƴanshi maza, ziryan, wanda kullum iwar hakan suke haɗuwa domin gaidashi kana su gaisa da juna, ya tambayi lfyar ko wanne ɗanshi da ahlinshin. To yau ta kasance jumma'atu babbar rana, wanda kuma, duk safiyar jumma'a. Cikin wani ɗakin gadon sarautarsu, yakan shiga shida kanshi, yake tsabtace wannan ɗakin duk ran jumma'ar duniya, a tarihi da tsarin masarautarsun babu wanda zai shiga ɗakin sai wanda yake, matsayin Sarki. Babu wani wanda ya taɓa shiga wannan ɗakin, sai wanda yake sarki.

Suna cike a falon a ƙalla sun kai su bakwai dukansu. Manyan mutanene masu tarin wadatar duniya, jinin sarauta na yawo a jikinsu. Suna zaune kamar yadda kullum suke zama, suna ɗan hira a tsakaninsu.

Habibullah ne, zaune a can tsakiyarsu a matsayinsa na shine babban ɗa ga Lamiɗo, hannunsa riƙe da. Carɓi, sai gefen damansa, Alhaji Sani, sai kuma Barrister Kamal, kana sai. Dr Aliyu, kana sai, Badamasi, Nasiru, basiru. Dr Aliyu ne, ke gefen daman Habibullah, bisa alamu duk mgna yakeyi mishi a kan lfyarsa. Bappa Nasiru, wanda shine, yake bin Habibullah a girma sai dai uwarsu ba ɗaya ba, gyara zama yayi tare da jan dogon tsakin da yasa duk suka meda idonsu kanshi. Cikin kula Habibullah yace. "Lfy dai Nasiru?." Wani irin kallo mara daɗin gani ya watsa mishi tare da cewa. "Yes lfy lau, sai dai mu nan duk muna da aiki, ba zauna gari banza, irinka bane, kowa yanada hidimar yi gashi har yanzu, Lamiɗo bai fitoba". Murmushi yayi ba tare da yaji ciwon abinda ya gaya mishibs, a hankali yace. "To Nasiru, ai duk saurinka kayi haƙuri dai ya fito, kaga lfyarsa yaga taka, tunda shi bai gajiya da bincikar lfyarmuba, ai muku wa bazamu gazaba. Domin abune mai wucewa". Wani irin kallo mai cike da tsana da tsoggoma ya mishi tare da kauda kanshi. Basiru ne yayi dariya alamar jin daɗin kallon da ɗan uwanshi yayiwa Babban yayansu da suke ƴan uba. shi kuwa Habibullah Abbansu Sheykh, kauda kai yayi kar bai ganiba.

Kusan a tare suka miƙe gaba ɗayansu, tare da haɗa baki wurin cewa. "Barka da fitowa, Mai alfarma Lamiɗon Joɗa." Murmushi yayi tare da kallon ƴaƴan nashi ɗaya bayan ɗaya, a hankali ya ƙarasa fitowa, hannunshi sarƙafe da hannun Jabeer. Wanda baiyanarsa yasa, gaba ɗaya suka zazzaro ido. Cikin tarin mamaki, al'ajabi, firgici, kaɗuwa, gamida tsayawar idanunsu kan ɗan babban yayan nasu, cikin wani irin daskarewa, suka juyo suka fuskaci, junansu wannan ya kalli Wannan wannan ya kalli wancan. Murya a daburce, Nasiru ya nuna Jabeer dake tsaye, cikin wani masifeffen al'kyabbar mai masifar kyau da zadan gaske, cikin ƙafewan yawun baki yace. "Ka gafarceni Lamiɗo, me idonuna ke gani, daga ina ka fito da Jabeer? Me kayi dashi? Meye ma'anar hakan? Mu duk ƴaƴan ka bamu kai ka shiga damu ba sai shi?". Cikin tsare fuska irin ta manyan sarakai dattawan, ya zubawa, Nasiru idanu, wanda dole tasa ya hadiye rahowar maganar tasa. Habibullah kuwa, wani irin rawa da karkarwa jikinsa ya fara. Wani masifeffen tsoro da fargabane ya rufeshi akan ɗan nashi, koda dai baya jinsu a ranshi kamar sauran ƴaƴanshi, hakan bai hanashi tsoro da fargabar abinda zai cutar dasuba. Barrister Kamal kuwa. Wata irinyar madifeffiyar zuface ta keto mishi daga saman kanshi har tsakiyar tafin sawunshi. Lokaci ɗaya yaji wani irin abu ya saki ƙahon zuciyarshi, Maƙoƙoronshi ya bushe ƙamas, duhun daya rufe mishi idone yasashi komawa zaune. Dr Aliyu kuwa, wani irin murmushi yakeyi yana kallon ɗan babban wansun. Shi kuwa Lamiɗo hannun Jabeer ya kuma ja, wanda yake motsa laɓɓansa a hankali yana tasbihi kamar yadda ya saba. Zama yayi kujerarsa ta musamman, kana Jabeer kuwa ya zauna gabanshi. Cikin tattaro yawun baki Barrister Kamal yace. "Barka da safiya. Sarkin Joɗo. Sai ya kuma danne tarin baƙin cikinsa yayi mishi rumfa da fuskarsa ta zahiri kana ya kalli Jabeer da ya ɗan sunkuyar da kanshi tare da gaidashi. Cikin dakiya yace. "Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Joɗa. Yaushe a gari". Kanshi ya ɗan kauda tare da cewa. "Daren jiya". Nasiru ne ya katsesu da cewa. "Lamiɗo, ɗakin sarautar sarakunan Joɗa kuma ya zama kowa zai iya shigane?". Bai kulashi ba, har saida suka gaisa gaba ɗayansu, kana, ya fuskancesu, duka cikin hikima da, kaifin basira yace. "Rigar sarautarsu ta GARKUWAN FULANI, na bashi. Sabida akwai tafiyar gaggawa da zamuyi zuwa, Rugar Bani, da ƙaɓilun wurin suka far musu da kisa." Kai suka gyaɗa alamun gamsuwa, kana duk, ya sallamesu.

Duk suka fita kowa da abinda ke cikin ransa, da zuciyarsa.

Bayan fitansu ne ya kalli Jabeer cikin, tarin kula yace. "Kaje ka shirya kazo mu tafi". Kanshi ya kuma rusunarwa cikin ladab yace. "Allah saine, mu bari sai bayan sallan, jumma'a ina munyi jam'i anan, mu tafi gudun kada muje bamu dawoba kafin lokacin sallan." Gyara zamanshi yayi tare da gyaɗa kai kana yace. "Haƙƙun kayi, gsky to mu bari sai an sauƙo mutafi, in yaso muyi sallan la'asar a can." Da Wannan shawarar suka bari sai bayan sallan, azahar ɗin su tafi. Sun daɗe suna tattaunawa kafin, ya sallameshi ya tafi, shi kuma ya nufi fada.

A falonshi kuwa, yana shigowa duk suka zuba mishi ido, da mamaki cikin zaƙuwa Jamil yace. "Hamma Jabeer wai ta ina kabi ka fitane? Duk bamuga fitankaba". Kanshi ya mirgina, alamun gajiya, kana a fakaice ya kallesu baki ɗayansu, tare da cewa. "Sama". Murmushi sukayi baki ɗayansu, sabida fahimtar amsar daya basu, na nuni basuga sanda ya fita bane.

Bisa wata tattausar doguwar kujera ya zauna. Kana ya fuskanci ƙannen nashi da kyau. Jalal ne ya ɗan sunkuyar da kanshi, ganin yadda Hammanshi ya zuba mishi ido, Jamil kuwa, kanshi ya ɗan rausayar tare da katse wayar da yakeyi, ya fuskanci ɗan uwan nasu, Cikin yin fiki-fiki da idanu yace. "Barka da safiya Hamma Jabeer, ya hanya?". Alhamdulillah, yace mushi a taƙaice, kana ya ɗan gyara, hiramin dake bisa kafaɗunshi. Jalal ne ya ɗanyi baya tare da lumshe idonshi cikin saisaita muryar da indai da Hammanshi zaiyi mgna to sai ya nitsu ya gyarata, Domin yakanji yanada rauni duk sanda yake gaban Hammanshi, yana ji tamkar a gaban mahaifinshi yake. Cikin sanyi yace. "Ina kwana? Hamma Jabeer, ka dawo lfy t yasu Sitti?". Ido ya ɗan kauda kana yace . "Alhamdulillah, Jalal ya jikin Ya Jafar?". Kanshi ya ɗan jujjuya kana a hankali yace. "Kalmace dai ta musulmi, koda cuta babu sauƙi ya zame mana ɗa'a muce, da sauƙin, amman a zahirin gsky ciwon Ya Jafar babu sauƙin, komai yaci tura, abubuwan sun yawaita". Ya ƙarishe mgnar tamkar zaiyi kuka, ganin hakane yasa Jabeer ɗan kauda kanshi, Allah yasani, baya son ganin ƙunci ko baƙinci ko wata damu a fuskarsu, sabida ya ɗauka cewa Allah ya barshi da rai da lfy ne a tsakiyarsu, su da akewa kallon marasa lfy ya zame musu Garkuwa. A hankali ya miƙe cikin kula ya kallesu, murya a ɗan macce yace. "Kuzu kuci abinci". To sukace baki ɗayansu, kana duk suka nufi, dinning table ɗin. Wanda yake cike da abinci kala-kala. Juwairiyya ce ta sakawa kowa abinda yake buƙatar ci, Shi kuwa Sheykh sai jujjuya mata kai yayi alamar babu abinda zaici. Ya dai zauna yana kallonsu, Ummi kuwa, tana gefenshi. Kanshi ya ɗan juya ya kalli Haroon dake shan tea kuma still wayarshi na kunne yana, mgna da Jannart, ɗan gajeren tsaki Jabeer ya ja, jin Haroon na cewa. "Ina yin breakfast ne, ke me kikeyi? Bacci? Ko kwaliya? Ko kallo?". hannunshi yasa ya zare wayar kana ya katse kiran tare da mishi nuni yaci abinci kafin ya tsaya yin waya. Cikin haɗe fuska Haroon yace. "Ka ganka ko? Ni shiyasa har tsoron zama kusa da kai nakeyi, sabida tsarabe-tsarabenka nada yawa, yanzu zaka fara jawowa mutum aya da hadisai, kana wani, abu kaza ba laduban kaza bane, in an jika kayi doguwar mgn to an sosa maka wuri biyu, ko ayar Allah, ko wannan mulkin da kake cewa an liƙa maka jaraba". Jamil ne yayi ƴar dariya tare da cewa. "Mulkin nema jaraba a wurin shi ko? Gacan wasu na neman, zaunece sabida Garkuwan da aka bashi". Jalal ne ya ɗan tsuke fuskarsa tare da cewa. "Ni kaina Wannan GARKUWAN bai wani burgeniba, sabida baya cikin, masu iya gadar mulki, sabida shi ai ba jikan sarki ta wurin ƴa mace bane, jikanshi nefa ta wurin ɗa namiji ta yaya zai bashi Garkuwa?". Ummi ce taja wani dogon ajiyan zuciya tare da cewa. "Uhummm ta yaro kyau take bata ƙarko, to kai Jalaluddin, yanzu Jafar da aka bashi Galadima, wani hali yake ciki? Tun randa aka naɗa masa sarautar me mutane suke kallon ya zama? Dukfa duniya kallon majanun akeyiwa Jafar". Juwairiyya ce ta ɗan rumtse idonta tare da cewa. "Ni banyi fataba, banso a sake bawa Kowa wani mulkin da nasan baza'a barku lfy ba, shi Lamiɗo, meyasa ko ƴaƴan nashi babu wanda ya bawa mulkin komai?". Da sauri Ummi tace. "Sabida muddin yace zai basu sarautu, to wasu zasu hallaka wasu". Cikin daƙilewa Jalal yace. "Ok shine sai ya zaɓi ƴan ɗakinmu a matakan zakarorin gwajin dafi? Ya bawa Ya Jafar Galadima, yaga yadda aka medashi dare ɗaya, da rashi da bazamu samu madadinshiba a duniya, an cire hankalin mahaifinmu a kanmu, sannan ya kuma bawa Hamma Jabeer wani mulkin, salon a sabautashi kenan, nest target nasu kuna, wato a kanshi ne?". Shiru sukayi jin Jabeer na cewa. "Azzannu zambu walau kana haƙƙun, na haneku da irin waɗanan zantukan, babu wanda ya isa, ya cutar da wani sai Allah, domin shine mai rayawa, kuma mai kashewa, mai badawa, mai hanawa, mai cuta mai waraka. Ummi har kema, ya zakiyi ki zauna kina gaya musu hakan, to waye zai cutar damu, acikin ahlinmu, daga ƙannen mahaifinmu fa, sai ƙannen kakanmu, sai matasansu da jikokinsu, sai kuma ƴan uwanmu, dan Allah ku bar munanawa mutane zato." Juwairiyya ce ta ɗan girgiza kai. Shi kuwa Jabeer, cikin bada umarni yace. "Juwairiyya jeki duba Ya Jafar, nasan zuwa yanzu ya tashi daga baccin." To tace, kana ta miƙe ta nufi tsakiyar falon. da sauri ta tsaya tare da ɗan raɓawa gefe, sabida ganin Gimbiya Saudatu, na tsakiyar falon. Da sauri ta ɗan rusuna tare da cewa, "Barka da fitowa Gimbiya Saudatu". Zama tayi bisa kujerar da Jabeer ke zama, ɗaura kafarta tayi ɗaya kan ɗaya. Hadimanta, biyu ne suka zauna gefe da gefenta. Fuskarta babu wata alamar annuri, sai tsantsar tijara, cikin isa da ƙasaita tace. "Kai Jabeer!." Ido Jakadiyarsu ta zazzaro cikin firgici da tsoro ta kalli Jabeer da a take fuskarshi ta sauya launi, cikin rawan jiki da tsoro tayi ƙasa da murya tare da cewa. "Jabeer ka amsa, Gimbiya Saudatu ce, da kanta." Jalal ne da Jamil suka kalli juna, kana suka maida idonsu, kan Hamman nasu, da ya lumshe idonshi ya koma ya jingina tamkar badashi akeyi ba, kamar daga sama suka jiyo muryar Gimbiya Saudatu tana ratsa kunnuwansu. "Kai Jabeer, ka fito kazo nan, ina nemanka". Still bai buɗe idanunshi bama, bare ya amsa ko yunƙurin tashi, sai dai laɓɓan bakinshi da suke motsawa yana maimaita sunan Allah a zuciyarshi da harshenshi.

Zuwa yanzu Gimbiya Saudatu tayi masifar kufula, cikin wani irin mugun kallo ta kalli Juwairiyya da jikinta ke baiyana tashin hankali ta, cikin isa da ƙasaita tace. "Ke maza wuce, kije tun wancan karen larabawan da suka turo ahlin masarautun Fulɓe, dan samun damar maida masarautun a hannunsu, kice mishi yazo dan kan uwarshi". Da ƙarfi Jabeer ya rumtse idanunshi, wani irin bugawa zuciyarshi ta farayi a saba'in. Ita kuwa Juwairiyya kasa motsawa tayi daga inda take tsayen. Ummi kuwa cikin firgici, ta kalli Jalal daya miƙe tsaye tamkar wanda aka tsabura. Jiki na rawa ya ture kujerarshi, zaiyi baya ya fita ya nufi inda taken. da sauri ya juyo cikin tarin zafin rai jin an riƙe mishi, hannunshi. ganin Hamma Jabeer ɗinsune ya damƙi hannunshi ne ya sashi, taune lips ɗinshi da masifan karfi. Jamil kuwa ido ya zubawa Hamman nasu yana ganin yadda jikinshi ke karkarwa, kowa ya sani duk duniya babu abinda yake saurin harzuƙa Sheykh sama da a zagar mishi iyaye Especially uwa! Haroon kuwa zuru yayi da idanu yana kallon ikon Allah.

Ummi kuwa cikin rawan murya da tsoro da firgici ta kallesu murya na rawa, tace. "Dan Allah Jabeer, kaje, tashi muje ka amsa kiranta dan Allah badon niba, dan darajar Manzon Allah". Ta ƙarishe mgnar tana ƙoƙarin zubewa kan guiwowinta, Jin kalaman da tayi mishi da gane nufinta na rusuna mushine ya sashi saurin miƙewa tsaye. da sauri suma duk suka miƙe tsaye. Gyara kekyawar al'kyabbar jikinshi yayi wacce take ta limamaice bawai ta sarautaba, jam hiraminshi yayi ya rufe sajenshi da kyau ya rage iya shatin fuskarshi dan yasan dole tazo da hadimanta mata. Jalal ne ya tsaya gefen damanshi, kana Jamil a gefen hagunshi, Haroon kuwa na bayanshi, Jakadiyarsu kuwa tana gaba tanayi musu jagora. A haka suka fara taki kan stpes ɗin sauƙowa daga kan dinning area ɗin, wani irin taku sukeyi mai cike da ƙasaita da kwarjini. Yana tsakiyarsu tamkar sarki da fadawanshi. A haka suka nufo tsakiyar babban falon da ya kai wasu faluka huɗu. Ita kuwa Gimbiya Saudatu, wani irin hushi da numfarfashi takeyi tamkar wacce tayi gudun fanfalaƙi, cikin izaya da isa, take zaune bisa mazauninshi. Tare da cewa. "Ina karen Larabawan yakene, Dan kan uwark?". Bata ƙarishe mgnar tataba, sabida ganinsu sun nufota gadan-gadan, wani irin kwarjini yayi mata, wanda yasa ta haɗiye ragowar mgnar tata, shi kuwa Sheykh Jabeer, cikin wani irin taku naƙasaita suka karaso tsakiyar falon. Ido ta zuba musu kana cikin tijara tace. "Me zaka zo ka tsaya min a ka, ka zauna inada mgna da kai". Cikin wata iriyar dakekkiyar murya mai cike da ƙasaita yace. "Ai ba sai kince na zaunaba, dama dole in zauna, tunda ni ba bawanki bane, bazan tsaya a kankiba, sabida Ni ba dogari bane". Ido ta zazzaro woje alamun tarin mamaki, ajiyan zuciya ta sauke a ranta tace. "Ehe mai jajayen kunnuwa, uwarka zanci". Shi kuwa Jabeer, wani irin taku yayi mai cike da izza, bisa kujerar dake fuskantar wacce take zaune a kai ya zauna, da sauri ta tsareshi da ido tare da cewa. "Kai ina sama kana sama, haka aka koya maka irin tasu tarbiyar ta larabawan kenan". Ƙafarshi ɗaya ya ɗaura ya ɗaurs kan ɗaya, kana ya gyara zamanshi da kyau, cikin muryar ƙasaita yace. "Ki dena yimin ihu a kai, nan ba fadar masarautar waɗancan surutattun bane, nan fadace mai daraja masarautar Joɗa ce, kiyi hattara da lafuzanki, na baki mituna biyar daga cikin wunin yau gaya min damuwarki in baki mgninta". Jakadiya dai gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi. Haroon kuwa, bayan kujerar da Jabeer ke zaune ya tsaya, Jalal kuma yana gefenshi hakama Jamil. Juwairiyya kuwa, tana inda take tun ɗazu.

Wani irin mugun kallo ta watsa musu, kana cikin zafi da azalzalar zuciya da jin tarin tsanarsu ta gyara zama tare da cewa. "Naji yau an ganka ka fito ɗakin sirri na masarautar Joɗa kaida mai martaba Lamiɗo, me hakan yake nufi?". Ba tare da ta gama rufe bakintaba yace mata. "Ina ɗakin sirrin masarautar Joɗa akace miki na fito, ba ɗakin sirrin masarautar kuba na fito?". Cikin kufula tace. "Itama ɗin wannan masarautar ai tamuce, tunda ƴaƴanane manyan jikokin sarkin Nuruddeen, kuma babansune Galadima, shine kuka kasheshi, aka bawa wancan majanunin yayan naki mulkin Galadiman, to yanzuma kuma ɗan tsurfa da tsiri uwar me kukayi a cikin ɗakin sirrin? Me ya gaya maka? Me kuke shiryawa?". Still harshenta ma bai gama komawa zaune ba ya jefa mata amsa. "Ɗakin sirri mgnar sirri, tunda shi jakin daya kai miki rahoton, bai sanar miki me muka tattaunaba, Ni sai in miki jagora zuwa wurin Lamiɗo ki samu ki ganshi yanzu sai ki tambayeshi me yace min me mukayi, tunda kinsan in bani nai miki isoba sai ki kai sati nan gaba baki samu damar ganinshi ba". Ya ƙarishe mgnar yana tsareta da fitinennun idanunshi wanda babu tsoro a cikinsu. Cikin kufula tace. "Ba girin-girin ba tayi mai, ta yaro kyau take bata ƙarko". Amsa ya kuma bata. "Surkin nakine yaron? Mutumin daya haifa miki miji, kika aura har kika haifi yayan da kike son su gajeshi, shine yaron? To asheko masarautar duk yarace, ke mulkarta, tunda nasan ko tsohonki bai kai, Lamiɗo ba". Ohoho ina wuta ta faɗa ciki, cikin kausasa murya tace. "Ina mai umurtarka da kada ka kuskura ka amshi wani mulkin daya wuce Garkuwa". Cikin taɓe fuska yace. "Anƙi bin umarnin naki". Wani irin Murmushi mai baiyana jin daɗi da tarin Mamaki Haroon da Jamil sukayi. Jalal da kanshi yau Hamma Jabeer ɗinsu ya shayar dashi tarin mamaki, ashe shi nashi ƙarfin halin da ake gani wasane, ga Jarumin da jarumtarsa ta girgiza, zuciyar Jalal. Dan harga Allah shi dai ya sani bazai taɓa iya yiwa Gimbiya Saudatu abinda Haammanshi keyi mata yanzuba, ashe dama haka yake, da kafiya da bada amsa tun kafin ta huta. Muryar Gimbiya Saudatu ce ta kuma katse mishi tunani. "Yanzu bakinka ke iya furta ka haka,, yaro zakaci kan uwark".. da sauri ta zaro mishi ido jin yace mata. "Kul kada ki ƙarasa, in kuwa kikayi gangancin ƙarasawa, zan". Katseshi tayi da cewa. "Zakayi me? Gaya min isshe ɗan fitsara me zakayi". Jalal ne ya amshi zancen da cewa. "Zan datse miki harshe, kika kuma zagar mana uwa". Cikin tsananin tsana ta watsawa Jalal harara tare da cewa. "Zaka aikata! Babu musu! Menene ɗan giya bazai iya yiba, menene, ɗan iska ɗan daba bazaiyiba, banza ɗan sara suka, gwada datse min harshen ka gani, in akwai wanda zai rage da harshe a zuriyar uwarku". Jabeer ne ya ɗan taune leɓenshi tare da kaɗa mata yatsa kana yace. "Kulfa, ki raba kanki da zagin mace mai daraja". Cikin isa da ƙasaita tayi wani irin dariya, kana ta miƙe tsaye, gabansu ta ɗan matso kana cikin izaya tace. "Eh daraja ko? Uhummm lallai kam, aifa sai dai mace mai daraja." Sai kuma ta ɗan ja da baya kana tace. "Mace mai daraja ko mai zunubi, ai dai kun fara ganin sakayyar Allah tun a duniya, waya san metayiwa ubangiji, y...." Juwairiyya ce, tasaki wani irin ƙara da yasa duk sukayi shiru. Ita kuwa ta faɗi kasa a sume alamun makaranta sun dawo. Ganin haka yasa Jakadiyarsu tayi kanta da gudu. Ita kuwa Gimbiya Saudatu murmushin jin daɗi tayi tare da cewa. "Haka dai. Duk a haka zaku ƙare, mulki kuwa sai dai ku ga anayi, GARKUWAN da aka bakanma, zakaga me zai sameka dashi". Tana faɗin haka ta juya ta nufi hanyar fita Hadimanta na biye da ita a baya. Shi kuwa Sheykh Jabeer murya ya ɗan ɗaga a hankali yadda zata iya jinshi yace. "Babu abinda zai sameni face dama Allah ya ƙaddara zai sameni, domin baki isa ki cutar daniba". Cikin harshen fillanci tace. "A laran ai, zaka gani ai". Bai kulataba. Ita kuma fita tayi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull