Garkuwa complete novel - Chapter 15
Garkuwa complete novel Chapter 15: Garkuwa complete novel Chapter 15. Jalal da Jamil kuwa, zama sukayi gefenshi, suna mai bin kofar fita da ido. Haroon…
4,289 words
Jalal da Jamil kuwa, zama sukayi gefenshi, suna mai bin kofar fita da ido. Haroon kuwa cikin rudu da ɗaure war kai yake mgnar zuci. shin wai wannan wacce iriyar fitinenneyar masarautace, mai cike da tsarƙaƙiya, yanzuma dama a irin wannan yanayin Jabeer ke rayuwa da ƙannenshi da yayanshi da mahaifanshi. To meyasa, bazasu bar musu masarautarba, tunda shi Jabeer bama son wannan mulke-mulken yakeba. Sassanyan zazzaƙar Muryar Sheykh Jabeer ne ta katse mushi nazari, jin yana rere karatun Alqur'ani cikin nitsuwa yake, karanta fatiha. Bayan ya kai ƙarshenta ya kuma yi bisimilla, ya fara Suratul Baqra, wanda yakeyi da ɗan ƙarfi, tare da fuskantar inda Juwairiyya ke kwance, Yanayin karatun cike da taƙawa da kekyawan tajwid, shiyasa in ya fidda wani harafin kamarsu Khah sai kaji har ƙasan wurin yana amsa amon sautin." A hankali Juwairiyya ta fara buɗe idanunta, tana mai bin karatun da takejin, Cikin sauƙe ajiyan zuciya Jakadiyarsu tace. "Alhamdulillah Jabeer ta farfaɗo". Ta faɗi hakane sabida tasan duk sansa Juwairiyya ta faɗin in dai zai mata Rugyag rufe idonshi yakeyi. Jin Jakadiyarsu tace ta farfaɗo ne, tasashi, yin hamandala tare da cewa, Jakadiyarsu ta meda Juwairiyya Side ɗin ta, kana ya kalli Jalal tare da cewa. "Jalaluddin kaje, ka kula da Ya Jafar, ka bashi abinci kana ka shirya shi, shirin zuwa sallan jumma'a kaima kaje ka shirya." To sukace kana duk suka fita. har sunje bakin ƙofar fira yace. "Jalaluddin kasa kayan mutunci". Cikin sanyi yace. "To". Sannan suka fita. Kanshi ya ɗan juya ya kalli, Jamil, tare da cewa. "Ka gyara mana bedroom." Yana jin haka ya miƙe ya nufi bedroom ɗin. Shi kuwa Haroon ido ya zuwa Jabeer, sabida gaba ɗaya muryarshi ta tabbatar musu, yana cikin tsananin ɓacin rai, kai Haroon ya jinjina ganin Jabeer yasa hannu ya janye hiramin dake kanshi, ya taune lips ɗinshi, kana ya rufe idanunshi, cikin ƙarfi yasa hannunshi ya fara jan bakin hiramin , da yake sabo fil janshi yakeyi alamun zai yagashi. Shiru Haroon yayi baiyi yunƙurin hanashi ba, domin dama yasan za'a rina, sabida shi Jabeer wannan itace babbar alamar tsananin ɓacin ransa, muddin fushinsa ya hauhawa to, yakan yayyaga abu da karfi. Fass haka Haroon yaji sautin, yagewar sabon hiramin nan. Shi kuwa Jabeer idonshi ya ƙara rumtsewa yanayi mai ci gaba da fatattaka hiramin. Murmushi Haroon yayi cikin tare da fara ɗaukar shi video. Yanayi dan tsokana.
A can sashin Hajia Mama kuwa, ganin shiru-shiru Jabeer bai shigo bane, kamar yadda ya saba in yayi tafiya ya dawo yakan, Batul kuwa, ta gaza zaune ta gaza tsaye, ta ƙenƙesa ado da kwalliya tamkar mai zuwa gasar kyau. A karo na barka tai ta kalli Hajia Mama, cikin zaƙuwa tace. "Yakura, muje, side ɗinshin mana, mu duba lfy kuwa har yanzu bai shigoba." Ajiyar zuciya Hajia Mama ta sauke, tare da miƙewa tace. "Muje Batul ni kaina, na banyi zaton zai kai iwar haka bai shigoba, dole akwai abunda ya tsareshi". Da haka suka fito, suka nufi sashin Jabeer ɗin.
Kasan cewarta matsayin uwa, yasa sam bata da hijabi da sashin, haka yasa, sarkin ƙofar na ganinta suka rusuna tare dayi mata kirari kana ta wuce.
A falon suka samesu, zaune. Haroon ya tasashi gaba da kallo da wayarshi, shi kuwa Jabeer, idonshi a rumtse, bakinshi na motsawa a hankali, yana maimaita, tasbihen daya zame mishi abokan rayuwa. Kana hannunshi nata yage sabon hiraminshi. Haroon ne ya amsawa Mama sallamarta, tare da cewa. "Barka da fitowa Hajia Mama". Da sauri ta ƙarasa gabansu, kujerar dake kusa dasu ta zauna, cikin tarin kula tace. "Haroon da kai ake tafe kenan? Ya yar uwata, yaushe ka dawo?". "Haroon lfy kuwa me akayiwa Jabeer? Waya taɓa minshi? Waya taɓo ɗan lelen Umaymah'nshi Da Sitti'nshi?". Cikin lumshe ido Haroon yace. "To Hajia Mama wacce tamɓaya ɗaya zan amsa miki, ta ƴar uwarki ko ta ɗan rigimarku, mutun in yayi fushi sai yayi ta yage-yage, wannan in ya samu dama in yayi fushi ya samu ya damƙi ƴar mutane a hannunshi tabbas zai yageta, dan ko namiji da kyar zai iya ƙwatar kanshi". Murmushi mai cike da kulawa tayiwa Haroon kana, ta kalli Batul da zauna gefenta, ta zubawa Jabeer idonu tamkar zata cinyeshi ɗanye, wani irin sonshi da ƙaunarshi takeji, jiki da zuciyarta, Kekyawan sumar kanshi ta zuwa, idanu a hankali ta dawo da idon kam tattausan sajen da yayi fuskarshi ƙawanya, har kan gashin gemunshi da ya kai kamu ɗaya, yayi baƙi sitib dashi ya konta lib sai sheƙi yakeyi, jajayen laɓɓan bakinsa, da suke motsawa ne ta zubawa kwayar idanunta.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, sanadin tasbihin da yakeyi ne, yaji zuciyarshi tayi fes, fushin da yakeji duk ya kau. A hankali yakejin tsikar jikinshi na amsa sautin yam-yam tana sanar mishi ana kallonshi. Yunƙurowa yayi ya tashi zaune, kana a hankali ya fara buɗe idanunshi. Da sauri ya kauda ƙwayar idanunshi sabida ganin kwayar idanun Batul cikin nasa, Hajia Mama kuwa, cikin sanyi tace. "Innallaha ma'assabirin". Idonshi ya kuma lumshewa, wannan abu shike ƙara sashi jin ƙarfin guiwar zama cikin masarautarsun. Sabida yayi dace, da uwar da take ƙara bashi tarbiyar da yasan itace dai-dai tana danne dukkan baƙin cikinta, domin ta sama mishi nitsuwa. Duk da kasancewar shi malami. Tana ƙara nusar dashi. A hankali yace. "Barka da safiya Mama". Murmushi tayi kana tace. "Barka dai, Muhammad Jabeer. Garkuwa mai nagarta, Yau na tashi da tsantsar farin ciki , tunda maji muryarka da asuba, meya ɓata maka rai daga dawowa?". Cikin sanyi yace. "Babu komai Mama, Sheykh Abdulkareem, da ahlinshin duk sun gaisheki". Murmushi tayi tare da cewa. "Tsoho mai ran ƙarfe, kakanmu bawan Allah, yana lfy ko?". "Alhamdulillah". Yace mata, yana mai sa hannu ya ɗauki hular da Jamil ya ajiye a kusa dashi ya ɗaura a kanshi, sabida wani irin kallo da yaga Batul nayiwa suman kanshi. Ita kuwa Batul ido ta ɗan lumshe, ganin yadda ya tamƙe fuskarshi ya watsawa gefen da take kallon, ƙasaita. A hankali ta buɗe idonta kana ta sauƙesu kan sajenshi, Wani gajeren tsaki yaja, tare da kauda fuskarshi. Ita kuwa Butul mgnar zuciya takeyi. "Masha Allah, Ya Jabeer, komai kayi kyau kakeyi, ya Allah ka tabbatarmin da mafarkina mana, wannan kekkyawan bawa naka ya zamo mijina, domin shine mijin daya dace dani, mijin kece raini da nunawa sa'a, Uhumm jin kai da ƙasaita ba, kayi naka, kafin ka shigo hannuna, in sha Allah, sai na zama sarauniya ka zama bawana." A hankali tace. "Ya Jabeer ina kwana". Shiru yayi kamar bai jitaba, Allah ya sani ya tsani kallo a rayuwarsa ta duniya, baya kuma son mace, da rashin kamun kai. Hajia Mama kuwa ganin yadda ya takurene yayi kici-kici da fuska, yasa ta ɗan, kalleshi tare da cewa. "Jabeer Batul ke gaidaka, itama jiya tazo". Kanshi ya ɗan rusunar tare da miƙewa tsaye, cikin sanyi yace. "Masha Allah". Daga nan ya ɗanyi taku biyu zuwa uku, kana yace. "Mama barin inje inyi shirin jumma'a". Murmushi tayi tare da cewa to. Dan ta fahimci zillewa yakeyi.
Daga nan shi dai yayi, ciki. Su kuma suka, fita.
Haroon kuwa Data ya kunna, Umaymah ya turawa video ɗin da yayiwa Jabeer da yana cikin fushin.
A can Rugar Bani kuwa, yau tun safe, su Shatu suka baro asibitin, sabida, matasan mayaƙan cikin garin Shikan ɗin sai kai komo sukeyi, cikin asibitin. kana sai zuwa sukeyi maja'iunsu, suna mitin. Bisa dukkan alamu, sunada wata manufa, ganin hakane, yasa likitoci musulmai, suka bada shawarar a kwashi marasa lfyar a medasu cikin asibitin babban birnin Ɓadamaya, sabida su nan babban likitansu ya hanasu duba kowa.
Da wannan shawarar ne, aka kwashi duk marasa lfyan da taimakon yan agaji aka shiga dasu cikin Adamawa. Dan an fara rade-raɗin wai fulanin Rugar Bani sunce zasu ɗauki fansa, to shisa ƙabilar ɓachama suma suketa guzurutsoma, har ta kai da matakin in dare yayi matasan hausa fulani na cikin garin ma zauna cikin garin Numan, sai su futo suyi ta yawo da makawai suna kare amguwanninsu. Kana suma ƙabilar ɓachama sai su fito da makamai suna kare amguwanninsu.
Shatu kuwa basu wuce cikin Ɓadamaya ba, sabida Ummiy ta dawo hayyacina ta, hakama Junainah ta dawo haiyacinta da ƙarfin addu'o'in da Aysha da Bappa keyi. Dan haka su cikin Rugarsu-suka koma.
Shatu kuwa, tunda Junainah ta gaya mata batun ɓacewarsu Ya Giɗi da kuma kashe ya Lado da akayi, har zuwa yanzu bata daina kukaba.
Koda Ba'ana yazo wurinta daren jiya, da yaji lbrin sun dawo babu abinda takeyi sai kuka. Shi kuwa Ba'ana, baƙin cikinsa shine da Ummiy ds Junainah da Bappa suka rayuwa, Shiyasa yanzu, yayi musu nasu shirin mutuwa namu samman.
Inda Bugulu Maman Ma'ans ta gasa zabbbin da Ba'ana ya yanka, kana ta daka musu, yajin borkono, da busasshen kan maciji. Ta barbaɗa musu, kana ta yaryaɗa man shanune da ya gauraya da dafin macijin cikin man shanun da tayi musu gashin dashi, kana ya nufi, bakin garkensu, da akoshin gasassun zabbin. Sannan ya aika aka kira mishi Shatu, cikin kuka Rafi'a tacewa ɗan aiken yaje, ya zazzaɓi ke damunta. Koda yaron yaje ya gaya mishi, sai yace zai a kira mishi Junainah, Koda yazo ya gaya musu, Sai Junainah ta miƙe tabi bayan ɗan aiken. Kasan cewar garken nasu ba nisa, tafiya kaɗan tayi ta isa, ta isa ta zauna a bakin ƴar bukkarsa da yake, cikin. cikin disashewar muryar hawaye na zuba tace. "Ya Ba'ana, kaje ka dubo jikin Ya Junaidun ne?". Juyowa yayi ya fuskanceta da kyau, cikin sanyi yace. "Eh naje na dubashi, jikinshi da sauƙi, ke ya naki jikin? Ya Ummiy da jiki". Cikin sanyi tasa hannu ta share hawayenta dake shatata kana a hankali tace. "Ummiy jikinta da sauƙi sai dai har yanzu bata mgn, Adda Shatu kuma sai kuka takeyi". Hararanta yayi a fakaice, ji yake kamar ya jawota ya caka mata mashi ya mata kisan zahiri sai kuma ya fasa, Kanshi ya kauda tare da tura mata akoshin gasassun zabbin nan kana yace. "Ayyah sannu Junnuna, kiyi haƙuri dena, kuka, kici nama, sai kije kicewa Mata, tazo zan gaya mata inda su ya Giɗi suke". Cikin rawan jikin jin yunwa tace. "Yauwa bani inci dama yunwa nakeji, tun jiya banci komaiba, tunda muka dawo, bamuyi girkiba." Da sauri ya turo mata akoshin tare da buɗe mata fefeyin. Cikin rawan jiki irin na masu jin yunwa tasa hannu ta...!
Uhummm Allah kaimu gobe lfy, mu ƙara sa free page, daga PAGE 15-16 an gama.
By *GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🐄🕊️🌈🦚🐍🤴🏻💘
*GARKUWA*
PAGE 15
NA *AYSHA ALIYU GARKUWA*
📝🍇🐄🌈🦚🤴🏻💘
*Littafin GARKUWA na kuɗine, daga wannan PAGE 15 da 16 FREE PAGE sun ƙare, turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276, ko ki turo dubunki ɗaya rak dan shiga Special Group, wanda anfi yawan posting, ta wannan asusun zaki turo 1k ɗin 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276.*
```Dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenki in dai kin san kin sayi littafina ne ko zaki sayane ɗan ki fitar min dashi na roƙeki da Allah da Manzonsa🙏🏻 kada ki saya, in kuwa har kin sayane kawai gaya min in biyaki kuɗin ki ki barmin littafina, mu rabu innahu annahu.```
Akwai kayyakin gyara namu mata setin amare da masu jego, da masu kwaskwarima, idan kina buƙatar saya ko sari, tuntuɓi wannan number tawa 09097853276.
Hannu tasa ta jawo pepeyin jin yana ce mata. "Kici kije da gudu ki kira Mata, tazo in gaya mata, su Ya Giɗi sun kusa dawowa ta dena kuka, anji lbrin inda suke". Rufe akoshin tayi kana ta miƙe da sauri tace. "Da gaske ya Ba'ana an ji inda suke?". Cikin haɗe fuska yace. "Na taɓa yimiki ƙarya ne?". Da sauri ta jujjuya kanta kana tace. "Bari inje in gaya mata tazo sai inci naman a gida". Da sauri yace. "A a jeki kirata, in tazo sai ki tafi da naman, kije kuci keda Ummiy da Bappa da ita ƙawar Mata, ita kuma zan bata nata a nan". Ai tana jin hakan ta juya ta tafi, da sassarfa.
Tana isa gida, ta kamo hannun Shatu, cikin haki tace. "Adda Shatu taso, taso muje ya Ba'ana zai gaya miki inda su ya Giɗi suke, yace anji lbrinsu". Wani irin zabura tayi, hakama Rafi'a dake bakin ƙofar kitchin ɗinsu. Cikin tarin kaɗuwa tace. "Ke Junainah, kada kiyi mana ƙarya". Cikin haki tace. "Wallahi tallahi, haka yace min zo muje kiji". Da sauri ta kamo hannun Rafi'a tace. "Adda Rafi'a kema zo muje tare". Cikin jin daɗi Rafia tace. "A a Junainah kuje, Ni kuma kafin ku dawo nayi mana abinda zamuci, da sauri tace. "A a Adda Rafi'a ki bari kar kiyi girki, Innar ya Ba'ana ta aiko mana gasassun zabbi yanzu zan amso mana su sai muci". Murmushi tayi kana tace. "To sai kinzo". Ita kam Shatu tuni ta fita, ta nufi Garkensu Ba'ana.
Ita kuwa Ummiy ido kawai ta zuba, musu tana son ta kira Shatu ta hanata zuwa amman ta kasa.
Ita kuwa Rafi'a kitchin ɗin ta shiga.
A can garkensu Ba'ana kuwa. Yana hango Shatu, ya saki wani irin ajiyan zuciya, ido ya zuba mata, Gaba ɗaya ta rame tayi fiyau da ita, fuskarta tayi jazir alamun yawan kuka, kana, ga kumbura da idanunta sukayi. Da sauri take tafiya, sai dai tanayin takun a hankali ne, doguwar rigace a jikinta ta atampa, hijabi da ta saka wanda yazo mata har guiwa. Ta ɗan ja hulan kan hijabin dan ya ɗan kare mata kumburarrun idanunta. Wani zafi yakeji a ransa, Allah ya sani baya son ganin Shatu cikin damuwa duk ƙaƙantar-ta, yakanyi komai na zalumci, amman baya yi kan Shatu, shi kanshi ya yarda shi tantirine, azzalumi, kuma mugu, hakanan kuma ya yarda so gsky ne kuma so ɗaya ne tak kuma ya sani duniya ta sani yana son Shatu, yana son sama mata farin ciki a rayuwarta, yana son su rayu tare. Shiyasa yake son rabata da kowa nata wanda suke ƙoƙarin ganin sun hanasu Kasancewa mata da miji. Wani farin buzu ya shimfiɗa mata a bakin ƴar bukkartasa, tun kafin ta ƙara so. Tana isowa, murya can ƙasa tace. "Assalamu alaikum." Ido ya zubawa fuskarta cikin tausayawa yace. "Mata ki zauna". Murya a disashe tace. "Ya Ba'ana ka amsa sallamar mana". murmushi ya ɗanyi kana yace. "Mata na amsa bakijini bane". A hankali ta zauna bisa buzun, cikin sanyi ta lumshe idonta da takeji sun tsastsafo da zafafan hawaye, murya na rawa tace. "Ya Ba'ana, wai anji lbrin su ya Gaini?". Matsowa yayi bakin bukkar, ido ya ɗan zubawa fuskarta, sabida lumahe idon da tayi batasan yana kallontaba ganin hawayenta na zubowa ne yashi yin mgna, a hankali yace. "Mata, kiyi haƙuri, ki kontar da hankalinki, in dai yayunki suna raye, zan nemisu, ko dan farin cikinki, ki bar kuka Mata, bana son ganin hawayenki inajin ƙuna a raina". Ya ƙarishe mgnar murya can ƙasa. Cikin rawan murya tace. "Ya Ba'ana, ya zanyi? Ina zansa raina in ji sanyi, zuciyata tana ƙuna, Yayuna huɗu kab na rasasu lokaci ɗaya, bani da wa wanda zan nuna a faɗin nahiyar nan ince ga wani na a duniyar, babu ya Giɗi, wanda shine tamkar aboki ƙawa aminiya, abokin faɗata abokin dariyana, Babu ya Seyo, yaya mai kamar uwa, sabida yawan tausayinshi da nuna ƙaunarshi gareni, ko uwa iya abinda zata nunawa ɗanta kenan, babu ya Gaini da yake tamkar uba, babusu babu gawansu babu lbrinsu. An kashe min ya Lado da yake GARKUWA a gareni. Ya Ba'ana, ya zanyi in banyi kukaba, Ina zan fara nemansu, Ni macece inada rauni, ta ina zan nemosu? An kashe mana Innarmu". Ta ƙarishe mgnar tana mai kife kanta bisa guiwowinta ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciya, cikin kuka taci gaba da cewa. "An kashe Inna, sanadin haka Ummiy na ta zama tamkar zautacciya, duk gidan dake cikin Rugar Bani babu gidan da ba'a kashe a ƙalla mutun biyarba a ƙaramin kari, suwaye ne ya Ba'ana, me mukayi musu? Me suke nema damu? Me muka tsare musu? Me laifinmu dan mun kasance Fulani makiyaya?". Karon forko a rayuwarsa da yaji rauni har ta kaishi ga zubda hawaye, koda yake raunin soyayyace, cikin zubda hawaye murya na rawa yace. "Mata gani, zan zame miki madadin uwa, uba, yayunki, Inna, zan zame miki Garkuwa, in sha Allah bazan bari ki cutuba, zan bada raina domin kare naki, zan nema miki farinciki da dukkan abinda na mallaka na duniya, zan zame miki adalin miji, Mata ki dena kuka, kiyi haƙuri". Cikin shessheƙan kuka ta ɗago kanta, ta zuba mishi ido, tabbas kuka yakeyi kamar yadda ta zata, cikin mamaki tace. "Ya Ba'ana meyasa kake kuka?". Hannun yasa ya sharce hawayenshi, karon forko a rayuwarsa da yayi abu ya gommace bayiba karo na forko a rayuwarsa da yayi mugunta yaji dana sani kan sace su Gaini. Da yatsarsa manuniya ya nunata, da mamaki tace. "Nice na saka kuka?". Kanshi ya gyaɗa mata, cikin al'ajab tace. "Me nayi maka?". Motsowa yayi ta bakin bukkar sosai can cikin sassanyan murya yace. "Kukanki ne yasani kuka Mata, farinci bazai samu gurbi a rayuwataba, muddin ke kina cikin ƙunci, dan Allah ki daina kuka,". A hankali tasa tafin hannunta ta share hawayenta. Shi kuwa Ba'ana, wani babban kura tanɗu yajo, cikin sanyi ya ajiyeshi gabanta a tsakiyarsu. Cikin sanyi yace. "Shatu". Da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi domin yauce karo na forko rana ta forko a tarihin rayuwarta da taji ya kirata da Shatu, cikin mamaki tace. "Na'am ya Ba'ana". Girgiza kanshi yayi kana ya fara fito da wasu sabbin aska cikin zabirar da yanzu ya jawota, a hankali ya ɗago ya kalleta cikin yaƙini yace. "Shatu, zan faɗa miki abinda, babu wanda ya sani a kaina a duniya, Shatu zan nuna miki abinda duk duniya ban yarda da in nunawa kowaba, sabida ban yarda da kowaba sai ke ɗaya rak Shatu, nasan zuciyarki ciki da woje, ke mai imanice, bazaki taɓa zalumtata ba, bazaki bari a kuma zalum ceniba. Na amince da soyayyarmu, zamu rayu a tare har gaban abadan." Ido kawai ta iya zuba mishi. Ganin Junainah ta iso wurin ne, yasashi jawo akoshin gasassun zabbin gabanshi. Ita kuwa Junainah da sauri ta kuma sa hannu zata jawo akoshin. Kanshi ya jujjuya mata alamun ta bari. Cikin kwaɓe fuska da ɗan karen kwaɗayi da yunwar da takeji yana azalzalar ƴaƴan hanjin cikinta tace. "Yah Ba'ana ka bani mana yunwa nakeji". Cikin sanyi yace. "Bazan bayar ba". Da sauri tasa hannu ta zari akoshin tayi gaba Shatu ce ta fara kiranta tana. "Junnu! Junnu!!! Junnuhhh!". Ina bata kulata bama bare ta juyo. Shi kuwa Ba'ana ajiyan zuciya yayi tare da mgnar zuci. "Uhummm ƙuda garin kwaɗayi kya mutu, kwaɗayinki ne zai karki". Kai ya gyaɗa wa Shstu kana ya juyar da kanshi. Ita kuwa Aysha shiru tayi tabi Junainah da ido. Shi kuwa Ba'ana cikin sanyi ya wore ƙafafuwan sa, takalmin roba na sau ciki wato, tashi kabi shanun dake ƙafarsa ya zare. Sabbin askan ya ɗauka, kana ya fito da wasu ƴan kananun layu guda biyu. cikin yaƙini yace. "Shatu, kinga waɗannan layun?". Kai ta gyaɗa mishi cikin yin kici-kici da fuska. Jinjina mata kai yayi kana yaci gaba da cewa. "Wadannan sune, maƙurar, mgnin kariya da zan saka a jikina, zan sasu a gaban idonki, wannan ƙaramar ita zan saka a dundunyar ƙafar dama, itace kuma layar, ƙarfe, mudin wannan laya tana jikina, to wlh babu wani ƙarfe dake kan doron duniya da zai shiga jikina". Cikin mamaki tace. "Koda bulet ne!?". Kanshi ya gyaɗa mata tare da cewa. "Koda menene, kuwa su wannan sabbin layune, wanda babu makarinsu, sai dai ina na ciresu a jikina, ita wannan da zan saka a ƙafar hagu, layar zanace. Duk sihirin mutun bazai karyashiba, zan iya ɓacewa inje ko ina, makarinta abu ɗaya ne!". A hankali tace. "To menene makarinta?". Cikin sauƙe wani nannauyan numfashi yace. "Idan wata rana dubuna zaicika za'iya kamani, to ammanfa tabbas, zan iya ɓacewa sai dai in ba'a barni na sha ruwaba, amman muddin akabani ruwa nasha zan iya ɓacewa." Da sauri tace. "Ya Ba'ana dubunka ya cika kuma, kamar wani mugu ko maiyin mugun abu". Da sauri ya fizge mgnar da cewa. "Eh to ai yanzu zan fara fataucin nemo. Suya Yaya Giɗi ne, kinga kuwa, sai yadda hali yayi". Ajiyan zuciya ta sauƙe kana tace. "To ita layar ɓatan da ta ƙarfe menene makarinsu?". Kanshi ya ɗan jingina da bakin bukkar ido ya ɗan zuba mata, kana cikin sanyi yace. "Uhum makarinta sai in an samu maza tagwaye, da matar da bata al'ada sunyi tuwon sabon geron da za'a shuka a tsakiyar garken fulanin kana tuwon za'ayishi da garin dakan hannune, kuma maza tagwayen sune zasu tuƙa tuwon kana matar da mijinta ya tara da ita batayi wonkan tsarkiba, ta kwashi tuwon , to su kam in naci, tuwon gaba ɗaya sihirin jikina zai karye, in kuma ba haka sai dai ina an tsaga dundunyar ƙafar tawa an ciresune kafin makami ya iya min illa". Cikin wani irin sanyi tace. "In sha Allah zaka nemosu lfy ka dawo dasu lfy, zanyi ta addu'a Allah ya baiyanasu." Kanshi ya tanƙwasar kana a hankali yace. "Uhum sai daifa Shatu akwai wasu bulalin da aka bani tabbacin zasu worwore duk wani asiri da kafi da nayiwa jikina, Amman duk da haka bazasu worwore waɗannan layunba, sai dai an bani tabbacin, muddinfa aka dakeni da wannan bulalin zan ji azabar dukan, da zai iya ɗauke raina". Cikin mutuwar jiki tace. "Bazama su dakeka ba, Ya Ba'ana". Kanshi ya mirgina kana, yasa hannu ya ɗauki askarnan, kawai sai ya datsata kan dundunyar ƙafar damanshi, Da ƙarfi Shatu tasa salati tare da rufe idonta, gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi murya na rawa tace. "Innalillahi ya Ba'ana zaka kashe kanka". Cikin harshen fillanci yace. "Ai bazanji zafinba Mata, bari yanzu in ɗinkesu, buɗe idonki ki gani." Cike da tsaro tace. "Bazan iyaba, ina tsoro". Jin hakane yasa bai kuma ce ta buɗe idonba, har saida ya gama cusa layun kana yasa ƙayar aduwa ya rinƙa hudawa yana ɗinkawa da zaren, gashin bindin shanu, saida ya gama yace ta buɗe idonta.
Cikin tsoron ta zubawa wurin ido, ga jini ya ɓata ko ina, Sai kuma ta ƙurawa ƙafafuwan ido ganin yana shafa musu man shanu sai wani tafasa wurin yakeyi, cikin mintuna uku duk wurin yayi tib-tib kamar ba shiba. Cikin tsoro tace. "Ya Ba'ana, ka dena irin wadannan abubuwa, wallahi shirka ne, tsafine babu kyau! Haramunne." Ganin yadda ya haɗe fuska ne yasa tace. "Kayi haƙuri, shiyasa tun forko ina son ince maka ba kyau bana son kana irin wadannan abubuwan". Murmushi ya ɗanyi kana yace. "In kin sake min mgnar, bulala ɗaya zan ɗauko cikin bulalin shaɗi na, in zaneki da ita sau ɗaya kiji irin zafin da masu gangancin cewa suna sonki, sukeji a jikinsu." Cikin tsoro tace. "Bazan sake bama Ya Ba'ana wadannan, bulalin da kake tsumasu da dafin kunama ai Ni kam na sani bulala ɗaya zakamin zan mutu". Da sauri yace. "Azubillah, Mata kada ki sake cewa zaki mutu, domin duk randa kika mutu nima zan mutu, sai dai batun gsky ko Mata, duk mutumin da kikaga ya iya jure bulalin shaɗi na, har ya kai matakin nasara, to wlh ki sani ki shaida, jarumine, irin jaruman da sunyi ƙaranci a duniya." Hannu tasa ta kange fuska daga wani irin kallo mai cike da so da yake mata, Tabbas Ba'ana ba barbarene, amman yanada wani irin kyau mai ban mmki, a hankali tace. "Ya Ba'ana wai da waye kake kamane?". Cikin murmushin da ya bayyana kyawawan haƙoransa yace. "Ni da kakata Maman babana nake kama, ita kuma ba kanuribace, fulatamare ce ita". Cikin sanyi tace.
Murmushi ya ɗanyi kana yace.
Cikin sanyi tace. "Haba shiyasa mana kake da kyau sosai". Wani irin kallo ya mata tare da cewa. "Eyeh ashe Ni kekyawan ne Mata, ke dama shine baki taɓa gaya min ba inji daga bakin wacca nafiso fiye da komai a duniya dan inji daɗi, kin bari sai wasu can keta cemin wai ni kekyawan ne". Da sauri ta miƙe tare da cewa. "Sai anjima, Mai kyau ka tashi kaje ka tafi masallacin kaga lokacin sallan jumma'a yazo anata tafiya". Da murmushi ya rakata. Ita kuwa da haka ta tafi gida, sabida tuni wasu masallatan har sun fara huɗuban sallan jumma'a.
Tana shiga gida ta samu. Rafi'a, Junainah, Ummiy da Bappa, gaba dayansu a.
Cikin Babban birnin Ɓadamaya, a cikin masarautar Joɗa, kuwa. Tuni masallacin Lamiɗo Nuruddee, ya cika yayi maƙil da bani adam tako ina zuwa, akeyi.
Masallacin ya cika tab tamkar zai fashe, shiru kakeji babu wani amon sautin ɗan adam dake tashi, sai sautin muryarsa. Yana tsayene cas kan ƙafafunshi, Wata dan datsetsiyar, shaddar Super Nour ce a jikinshi wacce take Brown color a ƙalla kuɗinta zai kai dubu ɗari da ashirin, shaddar irin mai mai ɗinnane, Yayi kauri cikin kayan ko dan yanayin suturar da ya sakane, boxes ce fara ƙal yasa a ciki, sai snglet itama fara ƙal, kana sai Rigar half jomfar yaddan dake jikinshi sai wonɗota, wanda sunyi cib-cib da madaidaicin jikinsa, Kana sai watta tattausar doguwar al'kyabbar sa, Golding color, sai wani irin sheƙi takeyi, sai hirami fari daja irin mai ɗigo-ɗigo nan, yayi masa sakin manyan Dattawan bai lonƙosashi, ya barshi a zube bisa kafaɗunshi, sai ta gaban goshinsa da ya ɗan matseshi ya bada ɗan tsini dai-dai kan karan hancinsa, Sai baƙin zagayen daya ɗaura bisa kam hiramin. Kana sai wasu takalman shi dake can bakin ƙofar shuga masallacin ta ƙofar liman, takalman irin na sarauta ne half cover, wanda suma fari da ɗigon jane. Yayi wani irin kyau mai ɗaukar hankali haibarsa da kimarsa da dottakunsa sunyiwa fuskarshi ƙawanya, sajen nan nashi yayi lib-lib tamkar anayi wa koren ciyawa bayi, sai wani irin sassanyan ƙamshin turaren OudKareem ɗin sa, dake tashi a jikinsa.