Kenza eBookz

Garkuwa complete novel - Chapter 44

Garkuwa complete novel - Chapter 44

Garkuwa complete novel Chapter 44: Garkuwa complete novel Chapter 44. Cikin fargaba da tausayawa Mata abinda ke damunta ya kalli ɗaya daga cikin yaransa…

4,477 words

Cikin fargaba da tausayawa Mata abinda ke damunta ya kalli ɗaya daga cikin yaransa wanda ɗan ƙabilar ɓachama ne, cikin waɗanda suka koro shanayen Bappa ne da Alhaji Haro. Cikin Ɓacamancin yace. "Barun zaka tafi ƙasar Nigeria ka wuce jihar Ɓadamaya kai tsaye har cikin masarautar Joɗa". Cikin tsoro Barun yace. "Masarautar Joɗa kuma, ta yaya to?." Numfashi ya fesar tare da cewa. "Duk magungunan da Sarkin bakan masarautar Joɗa yake saka mata da wanda zai sa mata nan gaba, duk na ruruta ciwon ne, sabida shi magautan Jabeer yakewa aiki, to kasan cewar bawai sihiri bane shiyasa Mata bazata ganeba, kawai maganin ingiza ciwon yake shafa mata. Sannan makarin ciwon Ni kaɗai nake dashi. To zan kira Bappa da layinka. In mishi jawabin ciwon da mgnin sannan zance mishi kai yau zaka kama hanya, dan taimaka mata, amman fa sai in zasu biya kuɗin jinyar da shanu hamsin". Cikin mamaki Barun yace. "Shanu hamsin mutumin da muka kwashewa komai ko ɗan tinkiya bamu bar mishiba, ina zai bada shanu hamsin". Murmushi Ba'ana yayi tare da cewa. "Uhumm baka san waye Malam Liman ba kenan Bappa baka san da waye yake tareba, baka san komai game da shiba. Kai dai bani inkirashi yanzu kaji."

Da sauri ya miƙa masa wayar. Shi kuma ya dannawa Bappa kira.

Yana katse kiranshi da Sheykh yaji wani kiran ya shiga wayarshi. Amsa kiran yayi tare da kara wayar a kunne. Sauya murya ba'ana yayi tare da cewa. "Ina mgn da Malam Liman ko baban Aysha mai ciwon hannu". Da mamaki Bappa yace. "Waye ne?". Ciki kaurara muryarshi yace. "Sarkin bakan nufe ne, bincike nane ya nuna min ciwon hannun yarka tana can masarautar Joɗa. An kawo wani sarkin baka yana mata mgni sai dai mugune magautansu yakewa aiki. In har zaku biyani ni Shanu hamsin zan je kuma zan mata aiki a take zataji sauƙin". Cikin sanyi Bappa yace. "To yanzu kai ina kake". A nitse yace. "Ni yanzu haka ina bakin iyakar ƙasar Nufe da Nigeria ne. Yau zuwa gobe zan shiga ƙasar". A hankali cikin sanyi Bappa yace. "To ba matsala, nima jibi zan shigo. Mu haɗu a can in dai kayi mata mgnin ta warke a take zan biyaka da abunda kace". Cikin jin daɗi yace. "To sai mun haɗu."

Katse wayar yayi tare da cewa. "Alhamdulillah Shatuna zata samu lfy. Zan kuma samu shanu hamsin. Sannan zanji lbrinta, zaka kuma isarmin da manufata. Kunga na jefi tsuntsu biyar da dutse ɗaya."

Jinjina mishi sukayi kana ya shiryawa Burun komai nagnin ya nuna mishi yadda zaiyi da yadda zai isar mishi da saƙonshi wurin Aysha.

Bappa kuwa Murmushi yayi dan ya gane Muryar Ba'ana. Dama ya sani bazai rabu dasu haka a sauƙaƙeba yasani yanzu duk motsin Aysha yana tafin hannunshi. Abinda yasa ya yarda su haɗu kuma yasan ba shi da kanshi zai jeba. Sai dai ya wakilta wani. Ya kuma sani tabbas yanada makarin ciwon taɓen sihiri wato ƙetare. Yakuma san bazai cutar da Aysha ba yasan tabbas taimaka mata zaiyi dan baya son abinda zai cutar da ita.

A haka shima ya kira Arɗo Bani suka tattauna kana ya fara shirin tahowa. Ko Ummey bai gaya mata abinda ke faruwa ba.

A can jihar Tsinako kuwa sha ɗaya dai-dai jirginsu Umaymah ya tashi ya nufi jihar Ɓadamaya.

A cikin Rugar Bani kuwa. Tun shekaran jiya su Junaidu suka dawo gida. Alhamdulillah duk sun worke kuma har gida aka dawo dasu.

Sosai Arɗo Bani da sauran dattawan sukayi mamakin jin Sheykh ne ya kaisu sibitinshi ya kuma kula dasu har suka samu lfy. Kana yayi musu komai ya dawo dasu lfy. Alhamdulillah kuma yanzu Rugar Bani basu da matsalar komai. dan ya rigada Allah yasa tsoron fulanin a zuƙatan Ɓacamawan. Yanzu kowa harkar shi yake ba kare bin damo.

Suyi kiwonsu lfyta shanayensu nata habaƙa. Yanzu kuma sun maida hankali kan shuke-shuke amfanin gonakin su. Sabida shigowar damuna.

A cikin masarautar Joɗa kuwa. Sheykh yana gama mgna da Bappa ya shiga bathroom.

Cike da mamaki ya ɗan sunkuyo ya kalli boxes dake jikinsa, wanda dashi zaiyi wonka. hannunshi yasa ya damƙi bnnarshi da tun jiya da safe data harba ta miƙe ta tsaya ta rinƙa kumbura da cika da miƙewa tayi tsawo. Har yau har yanzu harbawa takeyi babu ƙaƙƙautawa yadda zuciyarshi ke harbawa haka itama. Kuma tana tsaye gam tamkar zata faso boxes ɗin ta fito woje. Shiyasa yake jin tsikar jikinshi yana zubawa. A hankali ya sakarwa kanshi ruwan sanyi, wanka yayi kana, ya fito ya kimtsa ya shirya jikinsa cikin manyan kayan.

A falon kuwa Lamiɗo da Galadima da Sarkin bakan. Ne suka shigo bayan. Sallama yayi musu jagora.

A bisa kujera Lamiɗo da suka zauna sarkin baka kuma a ƙasa. Hakama Ummi da Hibba. Jalal da Jamil kuwa tun ɗazu suka fita, suka tafi Side ɗin Mama. A can suka samu Ya Affan.

Cikin girmamawa Ummi ta ɗan rusunar da kanta tare da cewa. "Barka da isowa Lamiɗo shugaba mai adalci". Kanshi ya jinjina tare da cewa. "Barka dai Jakadiya mai gsky, ya jikin ɗiyar taki, ina take". Cikin ƙara rusunar da kai tace. "To jiki dai da asuba da sauƙi amman kwana mukayi babu bacci. To rana na fitowa kuma ciwo ya harzuƙa ya zarta na baya". A hankali Lamiɗo da Galadima sukace "Subahanallahi". Sarkin baka kuwa. sunkuyar da kanshi yayi tare da sakin murmushin mugunta, kana ya gyara riƙon da yayiwa wayarshi yadda, waɗanda suka sashi aikin zasuji bayanin komai da kunnensu. da kiransu da ya haɗa. A can kuwa magautan dariyar jin daɗin lbrin. Sukayi.

A hankali ya kalli Ummi yace. "Sauƙi a hankali yake samuwa, zai nayi yana lafawa har yazo ya bari gaba ɗaya". Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa.

A hankali ta miƙe bayan Lamiɗo yace mata. "Jeki kira min ita tazo". To tace kana ta nufi shashin Sheykh.

Shi kuwa Sheykh yana cikin fesa turare kenan. Ya juyo ya kalli Aysha da ta tashi zaune da sauri tasa hannu a kanta tana yarfa ɗaya tare da cewa. "Wash! Wash! Wayyoooooooo Allah na!'. A hankali ya ajiye kwalban turaren kana yazo gaban gadon. Tare da cewa. "Sauƙo". Cikin rawan jiki ta sauƙo tana yarfa hannunta. Cikin haɗe fuska yace. "In zakiyi kuka fice min a ɗaki". Cikin rauni tace. "Yah Sheykh zafi! zafi!! zafin nakeji yana dawowa". Da sauri ya juyo ya kalli ƙofar ɗakin jin ana bugawa. Jiyo muryar Ummi ne yasa ya juya ya nufi ƙofar. Yana buɗewa tace. "Sheykh, Lamiɗo ne yazo yana son ganin hannun nata". Kanshi ya ɗan gyaɗa kana yace. "Fito kije, Ummi a kawo mata ɗan kwali ta ɗaure wannan dogon gashin da kitseshi ma aikine shiyasa ko yaushe kai a tsefe ai kuwa al'janu kam sayi ta shiga lodi-lodi". Da sauri Ummi ta miƙo mishi ɗan kwalin doguwar rigarta dake hannunta tun sanda ta wurgar dashi. Kanshi ya juya tare da cewa. "Fito". Cikin zubda hawaye ta fito. Gaban Ummi ta tsaya tana cewa. "Wayyo Ummey na". Cikin tausaya mata Ummi tace. "Sannu ko". Ta ƙarishe mgnar tana yafa mata ɗan gyalen. Kana ta kama hannunta na hagu suka nufi falon.

Shi kuwa Sheykh hiraminshi yasa ya dai-dai-ta komai. Sai dai abin da ya sashi jin kunyan kanshi da kanshi ganin. Har yanzu bnnarshi a tsaye ƙiƙam duk da danneta da yayi da boxes. shi da kanshi in ya sunkuyo yana ganin tudunta kaɗan danma manyan kayane a jikinsa. matseta yayi kana ya buɗe al'kyabbar da kyau, sannan ya fito ya nufi falon yanajin yadda take harbawa duk da kai tsaye bawai sha'awa yakeji ko makamancin hakaba.

Wayarshi ce kaɗai a hannunshi ya fito.

A falon ya samesu tana zaune gaban Lamiɗo da Galadima. Gefensu ya zauna. Sarkin bakan dake gabanta yana kwaɓa mgnine ya kalla tare da cewa. "A bar wannan mgin haka, kada a sake shafawa".

Cike da mamaki Sarkin bakan ya ɗago ya kalleshi tare da cewa. "Sabida me?". Idonshi na kan wayarshi yace. "Nace kada a shafa ko". Lamiɗo ne ya juyo ya kalleshi tare da cewa. "Za'a shafa". Shi kuwa Sarkin baka ido ya zura musu. Shi kuwa Sheykh miƙewa tsaye yayi tare da cewa. "Shike nan!". Ya ƙarishe mgnar da kallon hannun Aysha mai ciwon. Kana ya juya ya kalli Ummi tare da cewa. "Bari in ɗauko Umaymah ta iso". Da sauri Hibba ta miƙa tare da bin bayanshi tana cewa. "Hamma Jabeer inzo muje". Kai ya gyaɗa mata, kana suka fita. Ummi na ce musu. "Allah ya kiyaye hanya". Amin Amin sukace sannan suka fice.

Ita kuwa Aysha zuwa yanzu ta fara gigicewa. Sai mutsu-mutsu takeyi, tare da shishita. Galadima ne ya kalli Sarkin baka yace. "Kayi aikinka!". To yace kana ya fuskanceta da kyau yace. "Kawo hannunki". Jiki na rawa ta miƙa mishi hannun tana mai lumshe idonta hawaye na zubowa. "Sannu ko Mamana". Lamiɗo ya faɗa cikin tausayawa sabida sunan mahaifiyarshi Aysha.

Ummi ma sannu ta mata.

Shi kuwa Sarkin bakan da yawa ya daƙumo maganin ya labta a kan hannun. Sannan ya fara shafawa.

Wani irin zillo tayi tare da sunkuyar da kanta ta kifeshi kan hannun kujerar da Lamiɗo ke kai.

Gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi tamkar mazari. A haka ya gama shafe magungunan sannan ya bata wani yace sai dare ta shanye shi.

Ummi ce ta amsa tare da yi mishi godiya. Kana Lamiɗo da Galadima sukayi mata sannu da jiki suka tafi.

Suna fita, ta miƙe da sauri ta nufi falon ta. Da sauri Ummi ma tabi bayanta tana cewa. "Lafiya kuwa." Babu mgna tana shiga kan gado ta faɗa ta kife kanta a filo murya na rawa alamun sanyin zazzaɓi tace. "Ummi rufeni rufeni sanyi zai kasheni a kashe min AC." Da sauri ta ajiye maganin kana ta rufeta da jibgegen blanket ɗin sannan ta juya ta kashe AC'n.

Ta dawo gefenta ta tsaya. Cikin al'hini take cewa. "Sannu! Sannu ko Aysha". Ina babu mgna sai karkarwa takeyi tamkar zata faɗo ƙasa.

Haka yasa hankalin Ummi tashi.

Shigowar Aunty Juwairiyya ce da ta kawo musu abincin rana. Dana tarban Umaymah ne.

Cikin mamaki tace. "Ummi ko dai in kira. Sheykh yazo muje asibitine gafa yadda take rawan sanyi".

Ummi kam tama rasa bakin mgn, shiru kawai tayi tana riƙe da haɓa.

Suna cikin hakane Hajia Mama ta iso. Cikin tashin hankali tace. "Innalillahi wa innailaihi rajiun. Ummin Jabeer ya za'ayi da wannan yariyar ne? Mu tafi asibiti fa, da sauri ta juya ta fita zata kirawo Affan.

Tana fita da miti bakwai. Su Umaymah suka shigo. Kai tsaye suka wuce har cikin ɗakin jiyo mgnar su Ummi a can.

Shi kuwa Sheykh, asibitin Valli ya wuce.

Umaymah na shiga ta isa bakin gadon. Zama tayi a gefe tare dasa hannu ta buɗe borgon. Ganin yadda taketa karkarwa ne, yasa Umaymah ɗagota ta ɗaura kanta bisa cinyarta. Tana cewa. "Innalillahi wannan wane irin sabon al'amari ne mai firgitarwa". Da sauri tace. "Hibba kiyi gudu ki kirawo min Jazlaan kada ya fita." Da sauri Hibba ta juya ta nufi waje.

Ita kuwa Ummi da Aunty Juwairiyya ko sannu da zuwa Allah bai basu ikon yiwa Umaymah ba sabida ruɗani.

Wani irin numfarfashi ta fara fiddawa a jere-a jere sai ga jikinta ya fara lafawa da rawan da yakeyi. Wani irin zufa ya fara tsastsafo mata duk ta inda hudar gashi yake a jikinta.

Cikin sanyi suka fara sauƙe ajiyan zuciya. Suna cewa. "Alhamdulillah".

Gyara mata konciya Umaymah tayi ganin tayi bacci. Buɗe mata borgon tayi kana ta kalli Juwairiyya tare da cewa. "Kunna AC". To tace kana ta kunna.

Ajiyan zuciya ta sauƙe da ƙarfi. Haka yasa Umaymah ta sauƙo kan gadon. Cike da al'hinin abin suka fito falonta suka zauna. Juwairiyya ce taja jakar Umaymah ta kai ɗakin Ummi. Kana ta fito. Cikin sanyi Ummi tace. "Umaymah sannu da zuwa ya hanya". Tallaɓe habarta tayi tare da cewa. "Uhummmm Alhamdulillah Ummi ya mai jiki". Cikin sanyi tace. "To jiki kam dai babu daɗi. Sai dai godiyar Allah". Cikin sanyi tace. "Dukkan tsanani yana tare da sauƙin. Ya iyayenta sunji ko?". Kai ta gyaɗa alamun eh. Juwairiyya ce taje falon ta kawo mata ruwa da abinci. A hankali tace. "Juwairiyya ajiye abin cinnan bazai ciwuba".

Dai-dai lokacin Hajia Mama ta shigo da Affan yana cikin kiɗima.

Ganin Umaymah ne yasa suka zaune kusa da ita tare da cewa. "Ya jikin nata".

"Alhamdulillah ta samu tayi bacci." Umaymah ta basu amsa. Cikin kula Hajia Mama tace. "Sannunki da zuwa, ya hanya". Yauwa sannu Alhamdulillah tace. Hibba ce ta dawo tacewa Umaymah kafin ta fitama ya tafi. To kawai tace.

Daga nan suka zauna suna al'hinin abin.

Har azahar tayi nan suka watse kowa taje tayi salla. Ita Umaymah a ɗakin Aysha tayi salla.

Bayan sunyi sallan ne Ummi ta kawo musu abinci suka ɗan ci.

A nan suka zauna Ummi da Umaymah a ɗakin Aysha. Juwairiyya kuma taja Hibba suka tafi dan yin girkin dare.

Haka suka zauna har la'asar bata tashiba.

Sheykh kuwa sai ƙarfe biyar na yamma ya dawo gida daga asibitinshi.

Nasa falone ya wuce Side ɗinsa kai tsaye.

Biyar da miti bakwai dai-dai ta farka daga nannauyan baccin azabar. Da sauri Umaymah tayi kanta. Ganin tana ƙoƙarin tashine yasa Umaymah taimaka mata. Cikin disashewar muryar tace. "Lah Umaymah yaushe kikazo? Sannu da zuwa". Cikin tausaya mata tace. "Sannu Aysha ai ke za'a cewa sannu. Ya jikin naki". Cikin sanyi tace Alhamdulillah".

Sai kuma ta zuro ƙafafuwan ƙasa tare da cewa. "Umaymah zanyi salla zanyi wonka". To tace da sauri kana ta juya zata shiga bathroom ɗin. Da sauri Ummi tace bari in haɗa mata ruwan wonka."

Umaymah kuwa kamota tayi ta tsayar da ita. Dai-dai lokacin Ummi ta fito hannun ta zubawa ido cikin sanyi tace. "Ya naga kamar hannun ya ƙara kumɓura ne?". Kallon hannun sukayi a tare. Cikin sanyi tace. "Eh kamar ya ƙara kumɓura". Umaymah ce ta ɗan kalli hannun kana tace. "Je kiyi wonka ki fito kizo kiyi salla kici abinci, in baki mgnin da nazo miki dashi."

To tace kana ta nufi Bathroom ɗin tana cewa. "Bana iya gogo sosa a jikina sai sabulu kawai. Shiyasa nakeji kamar ba wonka nakeyi ba". Cikin tausayawa Ummi tace. "Allah sarki in kin samu lfy dai shike nan".

A haka ta shiga bathroom ɗin yau ko sabulun bata iya gogashi da kyauba.

Ita kuma Ummi kaya ta fito mata dashi kamar kullum.

Ita kuwa Umaymah Dinning area taje. Ta ɗauko Foodflaks ɗin da plate ta dawo nan.

A hankali ta fito bathroom ɗin.

Cikin ɗaga hannun sama ta kalli rigar da aka fito mata dashi a hankali tace. "Ummi bazan iya sashi ba, matsastsene a bani mai faɗi".

To Ummi tace ta sauya mata wani. Mai faɗin ita kuwa dogon wondon dake kan gado ta ɗauka ta koma bathroom ta saka da kyar sannan ta fito.

Koda Ummi ta bata rigar sai ta gaza sata. Ido cike da hawaye tace. "Ummi samun hannun rigar a hannu mai ciwon a hankali kada ya taɓa shi, sai kin buɗashi da hannu biyu. Cikin sanyi Umaymah tace. "Bakisa bra ɗinba".

Kanta ta sunkuyar tare da cewa. "Bazan iyaba". Shiru Umaymah tayi tana tunanin dole jinyar hannu sai da mataimaki. Ita da Ummi kuma surkaine Hibba ƙaramace. Shiru dai tayi tana nazari. Bayan Ummi ta taimaka mata tasa rigar ne. Ta saka hijabi tayi sallan a daddafe da taimakon lafiyayyan hannun. Tana idarwa Umaymah tasa mata abinci a plate kasan cewar tuwone da miyar ganye da ɗan tsami. Sai ya zama gaba ɗaya a kaikaice take sa spoon ɗin da niyar gutsuro tuwon. Kuma taji tana son cin miyar. Da kyar ta gutsuro gaya ta ɗan ɗebi miya ta ɗaya zata kaishi bakinta kenan ya faɗi a jikinta.

A hankali ta kallesu cikin sanyi tace. "Umaymah a bani tea kawai bazan iya cin wannan ba, zai tazubewa."

Da sauri Ummi ta gyara zama tare da cewa. "To matso in baki". Ɗan gajeren murmushi tayi cikin jin kunya tace. "A a bari in sake gwadawa to".

Dai-dai lokacin Sheykh da Umaymah ta kirashi a waya ya shigo yanata buɗe al'kyabbar jikinshi gudun kada a iya ganin tudun abinda yake ɓoyewa.

A bakin ƙofar ya tsaya tare da yin sallama. Cikin ɗan ɗaga murya Umaymah tace. "Shigo".

A hankali ya tura ƙofar ya shigo. Tunda tazo gidan tsawon watanni biyu kenan yanzu bai taɓa tako ƙafarsa nan ba sai yanzu.

Ta gefen ido ya kalleta ta sake ɗaukan loma a karo na uku kafin ta kaishi bakinta ya ɓare. Ture plate ɗin tayi tare da cewa. "Bana iya cin abu da hagu gwara tea zan iya kafa kofin insha wani wani ya ɗan zube". Ta ƙarishe mgnar tana shere hawayen da suka zuba mata.

A hankali Ummi taja flaks ta fara haɗa mata tea. Umaymah kuwa. Gefenta kan Bedside drower'n ta nuna mishi tare da cewa. "Zauna". fuska ya ɗan kauda kana ya zauna. A hankali tace. "Me zamuyi kan hannun yarinyar nanne?". Cikin jin haushi yace. "Sai abinda su Lamiɗo sukace ai. Ni Ko nayi mgna sai sun musamin ya rigada sun maidani kamar sa'ansu, bani da ancin mgn kan komai nawa sai yadda suka tsara min in naƙi bin unarninsu keda Abba kuyi faɗa, to ya zanyi?". Murmushi Ummi tayi ganin yadda yayi mgnar a tsare kamar shine babba a kansu ba suba wai sun ɗauke shi sa'ansu. Ita kuwa Umaymah cikin sanyi tace. "Kaga bata iya ko cin abinci tana bukatar kulawa ta musamman. Wonka ma wuya yake bata haka al'wala ko kaya sai an saka mata". A hankali yace. "Toh lallai kam Allah ya baku ladan jinya". Kai ta jinjina tare da cewa. "Amin". A ranta kuma tace. "Zanyi mgninka".

Ganin tayi shiru ne ya sashi miƙewa tare da cewa. "Allah ya sauwaƙa kana ya fita." Yana mai jin zafin katsalandar dasu Lamiɗo ke mishi a kan lamuran rayuwarshi, komai nashi sai sun saka mishi baki. Yace kar asa mgnin amman dan rainin wayo sunce dole sai an saka.

Su Umaymah kuwa nan suka zauna har akayi sallan magriba. Su Jalal Jamil Affan sukazo suka ci abinci aka ɗanyi hira dasu.

Har zuwa ƙarfe goma na dare hannun shiru ba ciwon sosai.

Haka kowa ya shiga yana cemata saida safe Allah ƙara sauƙin. Umaymah tace Ummi ta tafi da Hibba ɗakinta ita zasu kwana tare.

Haka kuwa akayi, har sun fara bacci.

Habawa sha ɗaya dai-dai, Ciwo yace salamu alaikum. Tashin hankali iya tashin hankali Umaymah ta ganshi a ranan. Domin har gabanin asuba basu rintsaba kamar dai yadda ta kwana jiya da Ummi abinma har yafi haka yau. Sau biyar Umaymah na kiran layukanshi duka basa shiga. Kuma Aysha guduwa kawai take nufa. Haka yasa dole tai ta riƙe ta.

Asuba na ƙaratowa tayi bacci kamar na jiya.

Sai da akayi sallan Umaymah ta tada ita. Tayi salla lfy tasha tea. ta koma bacci rana na fitowa ciwo ya dawo.

Gaba ɗayansu sun gigice sun tsorita da lamarin Umaymah ta tura Ummi taje ta gayawa Lamiɗo yazo yaga yadda take.

Hibba kuwa da Saratu sun kasa yin aikin da aka sasu sai kuka.

Hannun kuma yau yayi biyun na jiya. Idanunta sun kaɗa sunyi jazir. tana zaune kan kujera Umaymah na tsaye gefenta gudun kadda ta arce. Ta ɗaura hannun a kai tana kuka iya kuka, kukan azaba haɗe da salati. A haka Sheykh ya shigo ya samesu. Cikin takaici Umaymah ta juya ta nufi falon Ayshan tana kallonshi tana cewa. "Gata ka barta kada ka kula da jinyarta da haƙƙinta ne Allah ya rataya a kan wuyanka ai ka fini sani. Ka sani kana take sani". Ta ƙarishe mgnar tana zubda hawaye sabida duk wanda yaji kukan da Aysha keyi yasan na wahala ne.

Ita kuwa Aysha da sauri ta miƙe ta kife kanta jikin gini tana mai ci gaba da kuka. Jamil, Jalal, Affan, sunata yi mata sannu.

A hankali yabi bayan Umaymah da kallo tabbas ranta yayi matuƙar ɓaci, ga tashin hankali ga rashin bacci.

A hankali ya isa inda take. Hannunshi yasa ya kamo nata. Da sauri ta ɗago jajayen idanunta ta kalleshi, cikin zubda zafafan hawaye tare da cewa. "Yah Sheykh zafi, hannuna zai tsinke." Wani irin masifeffen rauni da tausayinta ne yaji sun rufeshi, kanshi ya juya cikin sanyi, yaja hannuntan. Suka nufi ɗakishi. Ita dai binshi a baya takeyi tana tafiya kamar a sama takejin kanta. Kai tsaye har bedroom ya wuce da ita. Kan gadonshi ya ajiyeta yanajin kukanta na hawa kanshi.

Bakin gadon ya zauna ya bata baya tare da cewa. "Ki kwanta kiyi addu'a zakiji sauƙi."

Ba jinshi takeyi ba bare ta gane abinda yake nufi. Da sauri ta yunƙura zata sauƙa. Juyowa yayi ya kamata ya ajiyeta kusa dashi kana ya juyo suna fuskantar juna.

Cikin kuka ta faɗa jikinshi tana cewa. "Umaymah hannu zai tsinke. Zafi zai kasheni". A hankali ya ruggumeta tare dasa hannunshi ya kamo hannun dake ciwon. Da sauri tayi tsalle zata zille hakan ne yasa ya ƙara ruggumeta gama ya haɗa jikinsu wuri ɗaya. cikin sanyi ya fara mata karatu a kunne yana hura mata iskar bakinshi kan hannun

Ajiyan zuciya mai ƙarfi da numfarfashi ta fara sauƙewa da ƙarfi-ƙarfi.

Umaymah kuwa jin shirune yasa, ta nufo Side ɗinsa. Ganin baya falone. Tace. "To ina suke ina ya kaita?". Ta ƙarishe mgnar tana tura ƙofar Bedroom.

Tana tura ƙofar sai kuma tayi sauri taja da baya sabida hangosu da tayi yana konce lib yayi rigingine ya ɗan jingina da allon kan gadon. Kana ita kuma ya kontar da ita kan jikinshi, ya ɗaura kanta bisa ƙirjinshi hannunshi na kan...!

Jinyar Sheykh ta musamman ce. To ya zata kaya ne in ɗan gidan ba'ana yazo. Hege Sarkin baka wa yakewa aikin.

By

*GARKUWAR FULANI*

Bayanta da ƙirjinshi. Da sauri ta ɗan koma gaba tare da cewa. "Innalillahi". Sai kuma ta tsaya ta juyo ta fuskanceshi da kyau. Idonshi ya rumtse da sauri, Allah yasani bazai iya jurarar ganin waɗannan ababen ba masu masifar tada hankalin da gigita kwakwalwar ɗan adam.

Ido a rufe ya buɗi baki murya can ƙasan maƙoshi yace. "Me hakan?". Da sauri ta fara ja da baya tana cewa. "Ka tafi! Ka tafi!". Buɗe idon yayi a hankali kana yayi taku biyu zuwa uku ya kamota, a hankali yace. "Ke meyasa bakya nitsuwa ne akan komai! Yanzu a hakan ina zakije a tsiraranki". Ya ƙareshe mgnar yana sa hannunshi ya janye rigarta dake cikin hannun ta. A hankali hannunta na hagun ta zaro tare da rufe ƙirjinta da ko rabinsu bai rufuba. Cikin sanyi ya matsota da kyau, a hankali yace. "Me zakiyi ne?".

Murya a kunyace tace. "Zan saka rigatace kuma na kasa shine. Umaymah tace inzo in baka kasamin."

"Uhummmm". Shine abinda ya iya furtawa sabida ji yake kamar bazai iya mgna ba.

Ita kuwa cikin sauri tace. "Wash". Jin ya fara jan hijabin. Da sauri tace. "Kayi min a hankali kunnena".

Ba tare da ya sunkuyo ya kalleta ba yace. "Meya samu kunnen?".

Cike da kunya tace. "Hijabin ya sarƙafe min ɗan kunne".

Bai tanka mata ba, sai hannunshi yasa ya buɗa hijabin. Ya maidashi a hankali yasa yatsunshi biyu, yana cire ɗan kunnen.

Matsota ya kumayi, kana ya samu ya warware garkuwan ɗan kunnen daga jikin yadin hijabin. Sai kuma yasa hannunshi ya cire mata hijabin duka.

Ya zama daga ita sai wondon dake manne a jikinta.

A hankali ya sunkuyo ya ɗauki rigar tata, sannan ya juyo ya zama tanata cikin falon shi yanata baƙin ƙofar shiga, Yayi mata ƙawanya da jikinshi.

Idonta a sunkuye, hannunta na saman caɓɓullenta. Zura mata rigar yayi a wuyanta. Cikin nitsuwa ya buɗe hannun rigar na dama ya sakamata cike da takatsantsan. Sannan a hankali yasa hannunshi ya kamo hannunta na hagun ya saka mata hannun rigar.

Cikin hikima ya sake rigar tayi ƙasa, sannan a hankali ya juyo bayanta, dai-dai ta wuyan rigar yayi kana yaja mata zip ɗin. Ɗan sunkuyowa yayi ta kafaɗanta, ganin gaban rigar bai dai-dai-ta yadda ya kamata bane yasa a hankali yasa hannunshin cikin wuyan rigar. ciki da mamaki da tsoro ta rumtse idanunta. Shi kuwa hannunshi yasa ya dai-dai-ta caɓɓullenta cikin breastcub ɗin. Kana ya dauki ɗan kwalin ya ɗaura mata a kanta kamar mayafi kana ya juya ya nufi. Dinning area yana maijin wani irin yam-yam da tafin hannunshi ke mishi tun sanda ya taɓa caɓɓullenta, hannunshi yasa ya ɗauki goran zam-zam ɗin da ya mata addu'o'in karya sammu. Gabanta ya dawo, ita kuma tana ta son ɗaura ɗan kwalinta. Goran ya miƙa mata tare da cewa. "Gashi wannan shi zakisha duk sanda kikaji ƙishi. In kinsha kuma ki ɗan shafawa hannun ki mai ciwon". Cikin yin ƙasa da idonta ta amshi goran tare da cewa. "Ngd". Bai tanka mata ita kuma ta juya ta tafi.

A falo ta samu Ummi da Umaymah da Hajia Mama, suna zaune. Cikin wani irin yanayi ta kalli Hajia Mama kana tace. "Ina kwana". Fuska cike da fara'a tace. "Lfy lau. Alhamdulillah yau jiki da sauƙi ko?". A taƙaice tace. "E". Daga nan ta wuce. Hajia Mama kuwa Umaymah ta kalla tare da cewa. "Khadijah ya lbrin Auren Haroon ne Kam?". Ajiyan zuciya tayi tare da cewa. "To aure kam yazo ga mai nisan kwana". Bayan sallan layya da kwana goma za'a fara bikin".

"A lallai aure kam yazo ga mai nisan kwana". Hajia Mama ta faɗa.

Ita kuwa Ummi murmushi tayi tare da cewa. "Lallai jihar tsinako zata kwashi baƙi".

Nan dai sukayi ta hira.

Sheykh Jabeer kuwa. A hautsune ya koma bedroom, kan gado ya kwanta tare da yin rubd ciki. Idonshi ya rumtse da ƙarfi wai ko zasu dena harsasho mishi hoton abinda ya gani.

Kiran da akewa wayarshi ne ya sashi jan tsaki Karo na uku yanajin kiran yana shiga. Ya sani babu mai mishi wannan kiran mafarautan sai mutun biyu. Haroon ko Ahmad wani babban abokinshi ɗan kasar Cameroon.

Hannunshi yasa ya amsa kiran tare da danna amsa kuwa. Tsaki yaja jin Haroon na cewa. "Kai kace baka son yawan kira, in an kiraka sau ɗaya kuma baka ɗagawa dan wulaƙanci. Ni kuma gani Sitti ce ta buwayeni da in Kira mata kai taji lbrin jikin amarya." Cikin sanyi yace. "Yaushe kaje lamorde julɓe?".

"Yau kwana biyar".

A hankali yace. "Anya kuwa Haroon in kayi aure bazaka dena aiki ba".

Taɓe fuska yayi tare da cewa. "Babu mamaki in bar aikin ma inji da amaryata".

Ɗan gajeren tsaki yaja tare da cewa. "Bawa Sitti wayar".

Miƙa wa Sitti wayar yayi. Cike da kulawa da so tace. "Muhammad".

"Na'am Sitti ya gida".

Cikin kulawa tace. "Gida lfy lau. Ya jikin iyalin naka?".

A hankali yace. "Alhamdulillah".

Da sauri tace. "Muhammad yaushe zaka kawo min itane?".

"Nima ban sani ba". Ya bata amsa a gyatsine.

Murmushi tayi kana tace. "Shike nan zan zo ai".

Da sauri yace. "A a bance ba, ki bari in ta samu lfy zata zo". To tace tana murmushi tasan yasan in tazo tofa. sa'idonta yafi na akowa. Duk motsinshi zata gayawa Lamiɗo. Nan dai suka ɗan yi hira kana suka ƙatse kiran.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull