Garkuwa complete novel - Chapter 45
Garkuwa complete novel Chapter 45: Garkuwa complete novel Chapter 45. Da daren ranar kuwa koda suka zo konciya Umaymah tace. "Aysha tafi ɗakin mijinki kar…
4,473 words
Da daren ranar kuwa koda suka zo konciya Umaymah tace. "Aysha tafi ɗakin mijinki kar hannun ya tashi dare-dare ya zama kina fita." A hankali tace. "Umaymah yau hannun da sauƙi tunda nasha ruwan addu'o'in nan bana jin zogin sosai".
Cikin jin daɗi tace. "To Allah yasa mu kwana lfy ba tashi". Amin Amin tace kana suka kwanta.
Allah cikin ikonsa da buwayarsa da al'farmar Annabi da al'ƙur'ani a daren sau biyu kawai ta ɗan tashi. Shima in Umaymah ta shafa mata ruwan dai sai ta koma bacci a take.
Washe gari da safe kuwa, Cikin mamaki ta kalli Umaymah dake shafa mata ruwan tace. "Umaymah bakiga kamar kumburin ya raguba".
Siyayan ruwan tayi a tafin hannunta tare da cewa. "Sosai ma kuwa Aysha hannufa Alhamdulillah da sauƙi sosai. Ga mgni kusa dake a bakin mijinki muje anyi ta wahala". Uhumm tace tare da sunkuyar da kanta.
Ummi kuwa Murmushi tayi.
Koda aka gama breakfast.
Ranar a haka a kaikacen ta daure taci. Kafin azahar sosai hannun ya lafa.
Yau kuma tunda safe ko inda hanyar Side ɗinsa yake bata kallaba, in taji zogin ta ɗauko ruwan tasha a shafa mata.
Shi kuwa Sheykh ranar tunda safe ya fita bai dawoba sai tara da rabi na dare.
Still yauma an kwana hannun da sauƙin.
Washe gari da safe.
Sheykh ya kuma ɗauko wani zam-zam ɗin da ganyen magarya guda bakwai, Yazo yana mata tofin cikin ruwan. Yana mgnar zuci. "Uhum jiki yayi sauƙi zamu huta da koken masifa da shogoɓar tsiya".
Koda ya gama yaje ya ajiye a Fridge kana yazo. Ya shiga wonka kasan cewar yau Monday ne tushen aiki ko nasara na tsoronta.
Ya fara kimtsawa.
Ita kuwa a falon bayan sunyi breakfast, suka dawo nan cikin falon, juyowa tayi ta ɗan kalli Umaymah dake shigowa falon tace. "Uhum Umaymah ruwan fa ya ƙare".
Shigowa tayi ta zauna gefenta kana ta kalli hannun ya saɓe sosai. "To kije ki gaya mishi mana, ai bai fitaba, tashi kije da sauri kada ya fita baki gaya mishi ba".
To tace kana ta miƙe ta nufi can.
Tana shiga yana fitowa. A hankali ta koma gefe ta tsaya. "Ina kwana". Tace mishi ido a ƙasa
Ta gefen idonshi ya kalleta tare da cewa "Lfy ya jikin?."
"Da sauki". Tace kana ta ɗan kalleshi tare da cewa. "Yah Sheykh!". Ido ya ɗan zuba mata kana yace. "Na'am!".
hannunta ta ɗan sa ta shafi fuskarta kana tace. "Uhum dama maganin nawa ya ƙarene shiyasa nace bari in gaya maka".
Hannunshi ya miƙo tare da cewa. "Inga hannun".
Ɗago hannun tayi ta miƙa mishi. Amsar hannun yayi kana ya juyo ya nufi tsakiyar falon. Tana biye dashi abaya. Bisa kujera ya zauna tare da nuna mata gefenshi. Zama tayi, duk yana riƙe da hannun, ɗan sunkuyowa yayi ya fara karanta Suratul Baqra yana tofa mata, yana sa yatsunshi biyu yana ɗan murza hannun a hankali-hankali, ido ta ɗan rumtse tare da motsoshi jin yana ɗan jan hannun.
Wash tace a hankali. Ɗan ƙara murza hannun yakeyi yana tofa mata. Hannun hagunta tasa ta damƙi damtsen hannunshi na dama. bai kulata ba yaci gaba da jujjuya mata hannun dan ya lura tana barin hannun a ƙage wuri ɗaya ko yaushe tana naɗe dashi. Murza hannun yakeyi da ɗan janshi yana miƙar dashi da ɗan ƙarfi. Wani irin bubbuga sawunta tayi tare motsoshi da kyau. Tsakanin sawunshi tasa cinyarta ta dama. kana tasa hannun hagun nata ta maƙaleshi.
duk ta kanainayeshi tako ina. zuface ta fara keto mata tako ina na jikinta, Ajiyan zuciya ta fara sauƙewa jin ya sake mata hannun.
Kanta ta manna a damtsen hannunshi tana maida numfashi.
Shi kuwa shiru yayi yana jin yadda take maida numfashi. Kusa 6 minute kana a hankali yace. "To ɗan sakeni in kin gama hutawa ko". A kunyace ta ɗan zame jikinta ta janye cinyarta.
Miƙewa tsaye yayi yana gyara al'kyabbar jikinshi. goran ya ɗauko a Fridge ɗinsa kana ya miƙa mata. Amsa tayi kana suka fito a tare.
Affan suka samu da matarsa Mami.
Suna fitowa Affan ya miƙa tare da miƙa wa Hamman nashi hannu bayan sun gaisane yace. "Ya mai jikin dai?".
"Alhamdulillah jiki da sauƙi". ya bashi amsa
Mami kuwa a hankali ta zame ta ɗan rusuna cikin girmamawa tace. "Barka da safiya Hamma ya mai jiki".
Hannunshi ya kai ya ɗan shafi kan ɗansu Karami Aliyu tare da cewa. "Lfy lau Alhamdulillah jiki da sauƙi. ya yaran?".
Suna lfy tace tare da kallon Aysha dake murmushi jin Affan na cewa. "Aunty Aysha ya jikin dai yanzu kam hannun bazai faɗi bako".
Murmushi tayi tare da cewa. "Alhamdulillah da sauƙi".
Sallaman su Umaymah Sheykh yayi ya tafi.
Murmushi Mami tayi cikin son matar Hamman nasu tace. "Ina kwana Aunty Aysha".
"Lfy lau".
"Ya jikin naki". Tace tana kallon hannunta.
"Alhamdulillah jiki da sauƙi sosai ma". Ta bata amsa. Tana zama kusa da ita, tasa hannun hagun ta amshi Aliyu wanda Dr Aliyu sukayiwa mai suna.
Affan ne ya ɗan kalleta tare da cewa. "My Aunty ga iyalin nawa. Ƙanwar Yusuf aboki nane yayar matarshi Zahra ce kuma."
Cikin fara'a da son Mami tace. "Ayyah yayi kyau Allah ya ƙara zaman lfy da zuriya mai Al'barka".
Murmushi yayi tare da cewa. "Amin tare daku, mu yanzu wannan na uku fa, ai munyi ƙoƙari ko Umaymah". Cikin dariya Hibba tace. "Kai Ya Affan abinma ƙoƙari ne kenan". Dariya sukayi duka kana sukaci gaba da hira. Aysha tana jin gamsuwa da gskyar Mami fiye data Aunty Juwairiyya. Ranan dai anan Mami ta wuni.
Haka dai taci gaba da amfanin da ayatul shifa da zam-zam da ganyen magarya.
Cikin ikon Allah da izininshi. Cikin kwanaki goma sha biyar hannun nan ya warke ya koma garau. Har tana shiga kitchen ayi aiki da ita.
Hakane yasa Umaymah ta fara shirye-shiryen komawa tana mai jin sanyi kaɗan a ranta.
Yau kwananta ashirin da zuwa, kuma yaune zata koma. To fa batun ƙomar da zatayi da Hibba ne yasa. Aysha taji babu daɗi.
Allah yasani ta saba da Hibba sosai. Ganin yadda ta koma ne yasa Umaymah ta ɗan zauna kusa da ita cikin lallami tace. "Kiyi haƙuri Aysha kinga badon makarantar Hibba ba dana bar miki ita. Yanzuma duk an gama mata komai na karatun zata tafi SS1 harma yan uwanta sun fara zuwa.
Kuma kema an kusa janye yajin aikin da University's Suka tafi, nayiwa Jazlaan mgna ana komawa kena zaki koma kici gaba da karatunki kewan zai ragun miki. Rafi'anki zata dawo itama". Cikin sanyi tace. "To Umaymah ki bar mana ita mana, sai in gayawa Yah Sheykh ya sama mata wata makarantar a nan". Murmushi Umaymah tayi tare da cewa. "Abbansu bazai yarda ba Aysha". Cikin sanyi tace. "Uhumm Allah sarki to shikenan Umaymah. Amman wlh gidan zai mana babu daɗi ko Ummi". Murmushi Ummi tayi tare da cewa. "Gsky kam Aysha zamuji kewar Hibba".
Ita kuwa Hibba tana tsaye gefen Jalal ne. Da alamu wani abun yake nuna mata a wayarshi.
Jamil kuwa murmushi yayi tare da cewa. "Uhum in tayi tsami dai maji". Hararanshi Jalal yayi tare da cewa. "Namu ƙamshi zaiyi ba tsamiba, ko Hibba". Murmushi ta ɗanyi tana share hawayenta, duk da rarrashinta da yakeyi kan kada tayi kuka. Har yake nuna mata text message ɗin daya turawa Hamma Jabeer ɗin su cewa. "Yana son Hibba".
Kowa yasan Hibba na masifar son Ya Jalal ɗin. Duk abinda yakeyi burgeta yakeyi.
Tun yana kaucewa har dai shima ya gane yana sonta ne.
Shi kuma Jamil sarkin latsi yaje can yace, i love You yaje can ya kuma cewa haka har yau bai tsaida matsaya ɗaya ba. Kuma soyayya ta hanashi maida hankali kan aikinshi.
A hankali Aysha ta sunkuyar da kanta ganin hawayen Hibba na zuba.
Shi kuwa Sheykh Jabeer ido ya zuba mata.
Lokacin da taga Umaymah ta miƙe tace. "To Ummin Jabeer Allah ya sadamu da al'khairi".
Amin Amin Ummi tace cikin kewarta tun kafin ta tafi.
Hibba kuma ruggume Aysha tayi tare da cewa. "Aunty Aysha zanyi kewarki sosai". Ta ƙarashe mgnar murya na rawa. Tuni hawaye suka tsinkowa Aysha. Aunty Juwairiyya ma sai ga hawaye. cikin danne zuciya Umaymah tace. "Ha Juwairiyya harda ke a kukan so kuke in tafi nima ina kukan ko".
Kai Juwairiyya ta jujjuya.
Ya Jafar kuwa shiru yayi yana kallonsu.
Shi kuwa Sheykh idonshi ya maida kan tab ɗin shi dake hannunshi.
Aysha kuwa. Cikin son danne kukanta tace. "Nima haka Hibba zanyi rashinki sosai. Sai yaushe zaki zo kuma".
Cikin zubda hawaye tace. "Aunty Aysha auren Ya Haroon ya kusa, ai zaki zo, bai cika wata biyu ya rage bama".
Cikin sanyi tace. "Allah ya kaimu".
Amin Amin sukace kana suka fita suka tafi.
Suna fita Aysha ta koma ɗakinta. Tana kuka.
Ummi da Aunty Juwairiyya da ya Jafar kuwa a falon suka zauna.
Sauran kuma duk yan rakiya ne sun fita.
Daga Side ɗinsa, sashin Hajia Mama taje ta sallameta kana ta wuce sashin Lamiɗo suma ta sallamesu sukayi mata fatan isa lfy kana ta tafi.
Ummi da Saratu suka shiga kitchen. Ita kuwa Aunty Juwairiyya ta koma sashinta itama.
Koda suka dawo rakiyar bata fitoba. Kasan cewar magriba tayi ne, sukayi al-wala suka tafi masallacin.
Itama Ummi taje ɗakinta.
Ita kuwa Aysha yau tana hutun sallan. Dan haka taci gaba da konciya.
Har akayi isha'i tana konce.
Koda suka dawo kai tsaye Side ɗinsa ya wuce. Jim kaɗan ya fito yacewa Ummi. "Bari inje Lamiɗo na nemana".
"To sai ka dawo".
To yace ya fita.
Ita kuwa Aysha, kiran da akayi mata a wayane yasa ta ɗanyi murmushi. Muryar Junainah taji tana cewa. "Adda na ya hannunki". Cikin jin daɗi tace. "Alhamdulillah ƙanwali ya worke yanzu kam ina Ummey na". Cikin jin daɗi tace. "Gata nan". A hankali tace. "Ummey na nayi kewarku, ina jina kamar bani da kowa nawa a duniya. Gashi Hibba ma yau ta koma".
Murmushi Ummey tayi tare da cewa. "Ke kuwa kikeda kowa naki a duniya, gaki ga salihin mijinki da Al'amin ya dawo yana yaba mana kamalarsa kowa naki sun gamsu da zaɓin da Bappanki ya miƙi. Gani ga Bappanki ga Abboi ga Ninnanki gasu ya Ahmad sannan ga dengin mijinki masu sonki Gashi kuwa munji lbrin su Ya Gaini". Ta ƙareshe mgnar dan son kontar mata da hankali. sabida basu wani ji lbrin su Gaini ba. Cikin jin daɗi ta gyara konciyarta tare da share hawayenta. "Alhamdulillah Ummey na godewa Allah. Ina suke?". Cikin sanyi tace. "Suna wata rugar FULANI dake ƙasar Senegal, yanzu ana ƙoƙarin a tabbatar ki cire damuwa a ranki ki sasu a addu'a kinji ko". Cikin sanyi tace. "To Ummey na ina sha Allah zan sasu. Kuma zan roƙi Yan Sheykh ma ya samin su a addu'o'in shi".
Cikin jin daɗi tace. "Yauwa to yafi. Ga Bappanki". Murmushi tayi tare da cewa. "Bappa na ina wuni".
"Lfy lau Shatuna ya jikinki".
"Alhamdulillah Bappa na worke".
"Masha Allah, to Allah ya ƙara mana lfy".
"Amin Amin tace."
Kana sukayi saida safe.
Tana katse kiran Ummi dake zaune gefenta tace. "Taso muje kici abinci kinji ko kije ki gayawa Sheykh damuwarki ya saki a addu'o'in shi. Domin addu'ar miji ga matarsa bata da hijabi". Kanta ta gyaɗa cikin gamsuwa kana ta miƙe ta fito.
Kaɗan taci abincin. Sannan taje tayi wonka, tasa doguwar rigar bacci kana ta zurma hijabin ta. Ta nufi falonshi.
Shi kuwa Sheykh lokacin ya dawo daga wurin a Lamiɗo Inda yake gaya mishi, akwai zagayen rangadin da zaiyi rugagen Fulanin ƙasar gaba ɗaya.
A cikin wata mai kamawa.
Koda ya dawo wonka ya shiga, Ya fito ɗaure da towel a ƙirjinshi zuwa saman guiwarshi.
Mai ya shafa tare da fesa turare. Kana yasa wani tattausan gajeren wonɗo mai ɗan faɗi amman ƙasamshi robar a tsuke take. Yana riƙe da rigar bai saba. Yaga kiran Umaymah ya shigo.
Wayar ya ɗaga bayan sun gaisa ne take ce mishi sun isa lfy.
A hankali ita kuma Aysha ta turo ƙafar bedroom ɗin ta shigo.
Ido ta zuba mishi sama da ƙasa a karo na forko kenan da ta ganshi babu riga a jikinsa. Damatsan hannunshi ta zubawa ido zuwa kan ƙirjinshi da tattausan gargasa tsilli-tsilli ya mishi ƙawanya a farar fatarshi.
Shi kuwa ido ya zuba mata dan rabonta da shigowa ɗakinshi yafi kwana goma.
Umaymah kuwa cikin murmushi mai sauti tace. "Ina ɗiyata, tanata kuka ko?".
A hankali yace. "Gata". Wani irin farin cikine ya rufe zuciyar Umaymah tasan burinsu bazai tabbataba muddin babu shaƙuwa da kusanci tsakanin Sheykh da matarsa.
Cikin jin daɗi tace. "Bata wayar".
Uhum yace kana ya miƙo mata wayar. A hankali ta iso gabanshi kusa dashi gab-gab ta tsaya. wayar ya miƙa mata yana kallon yadda take matsoshi. Amsar wayar tayi ta kara a kunne tare da yin sallama. Kana idonta kuma yana kan zanen macijiyar dake konce har kan cikinsa zuwa saman haƙar-ƙarinshi.
Da Ido yabi wurin da take kallon. Fuskarshi ya haɗe tare da ɗaga ƙafarshi zai ja da baya.
Sai kuma ya tsaya cike da mamaki ya kalli hannunta da tasaka ta kamo bakin robar gajeren wondon dake ƙugunshi.
Hannunshi yasa ya bugi hannunta, Amman sai ta ƙara matsoshi. Cikin sanyi ta....!
Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta number nan da nake whatsapp da ita, 09097853276 ba hoton katin zaki turoba, ba kuma TRANSFER ɗin katin zakiyi minba, ba kuma BTU ba, numbers ɗin katin zaki rubuto ki turomin. In kuwa special Group kikeso kiyi min TRANSFER ɗin 1k ta asusuna na Jaiz bank. 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo min screenshort na shaidar biyanki ta wannan number tawa ta whatsapp 09097853276. Kada kiyi min TRANSFER ko BTU na kati wlh in kinyi ba ruwana.
By *GARKUWAR FULANI*
Cikin tsuke fuskarsa da muryar dake nuna zafin abinda ke zuciyarshi yace. "Ummi in ya fito kiyi mishi jagora zuwa wurin sarkin ƙofa ki nunashi kada a sake barin yazo ko kusa da katangar masarautar Joɗa ne, a korashi ya bar jihar Ɓadamaya."
Da sauri Ummi tace. "Toh". Kana tayi gaba tare da cewa. "Mu tafi". Da sauri Barun yabi bayanta.
A can falon Sheykh kuwa komawa yayi ya zauna gaban Bappa cikin sanyi yace. "Bappa kayi haƙuri, ka gafarceni, bisa korarshi da nayi. Wannan sunada manufar data kawoshi, ni zan ji da ciwon hannunta, in sha Allah zata samu lfy. Ka kwantar da hankalinka."
Ido Aysha ta zuba mishi cike da mamakin ta ina ta yaya ya gane meke tafe da Barun har ya gane sunada wata manufa, ta yaya ya gano kuramen bakin da Barun ya karanta mata, ta yaya yayi musu wasali har ya basu cikekkiyar jimla ya karancesu da fassararsu, meya sani a kanta.
Hakama Bappan kallon Mamaki yakeyi mishi amman sai ya gyara zamanshi tare da cewa. "Ba komai Muhammad Allah ya bamu sa'a ya kuma bata lfy".
Amin Amin yace shida Umaymah.
Al'amin ne ya ɗan gyara zama tare da cewa. "To Allah yasa a dace. Amman ko za'a gwada asibiti ne?." Kai ya jujjuya tare da cewa. "Kada ka damu, in sha Allah ba damuwa". Kai ya ɗan gyaɗa cikin gamsuwa. A hankali Umaymah ta miƙe ta fita.
Shi kuwa Sheykh Aysha ya kalla tare da cewa. "Tashi ki barsu suci abinci mana". Da sauri Bappa da Al'amin sukayi mgna kusan a tare sukace. "Alhamdulillah mun ƙoshi". Kanshi ya ɗan juyo ya kalli Al'ameen da kyau kana a hankali yace. "Ba'a zuwa masarautar Joɗa a fita ba'aci komaiba". Murmushi mai cike da gamsuwa Bappa yayi kana yace. "Eh Alhamdulillah munci a wurin Lamiɗo ai". Kanshi ya gyaɗa cikin gamsuwa da hakan yace. "Toh Bappa". Cikin sanyi ita kuma Aysha tace. "Ya Al'amin bani zanci". Murmushi Al'amin yayi kana ya jawo Foodflaks ɗin, a plate ya zuba mata Couscous da biyar hanta. gyara zamanshi yayi ya fuskanceta da kyau itama gyara zamanta tayi. Bappa kuwa Murmushi yayi yana kallonsu.
Shi kuwa Sheykh ido ya zuba musu zaiga dai iya gudun ruwansu duk da zuciyarshi ta gama gano mishi nasabarsu.
Shi kuwa Al'ameen. A hankali yasa spoon ya ɗan ɗibo, kana ya nufi bakinta da spoon ɗin tare da cewa. "Ha, buɗe bakin".
To tace kana ta buɗe bakin ya saka mata. lumshe idonta tayi tare da tauna abincin dan ya mata daɗi. Sake dibowa yayi ya bata, still ta buɗe baki yasa mata.
Cire kanshi yayi a kansu, ya maida dubanshi kan Bappa dake mishi mgna. Umaymah da Ummi ne suka shigo a tare ita Ummi cewa. Sheykh tayi an fidda Barun.
Ita kuwa Umaymah ƙwaryar fura da nono ta kawo musu.
Murmushi sukayi ganin yadda Aysha ta zage tana cin abinci. Shi kuwa Al'amin ya dage yana bata. "Ya Al'amin zan sha ruwa". Tace mishi tana taunar sokar naman da yasa mata a baki. Kanshi ya ɗan juyo ya kalli Umaymah tare da cewa. "Allah rene a sammin ruwa in bata".
To Umaymah tace ta miƙo mishi ruwa. Tana kallon kamanninshi da Aysha ba sai an gaya maka cewar ɗan uwanta jininta bane. Bata ruwan yayi har baki. Tasha sosai. Kana ya kalleta tare da cewa. "In ƙara miki abincin ne?". Kai ta gyaɗa mishi. murmushi yayi tare da cewa. "Bubbuga rumbun Abboi". Murmushi tayi itama tana mai share hawayen da suka silalo mata. Ƙara mata yayi tare da ci gaba da bata. Sosai kuwa taci tayi haniƙan. Sheykh kuwa da wutsiyar idonshi yake kallon dukkan motsinsu. Bayan tayi gyatsa ne, Ummi ta matsar da kwanukan. Babu yadda Sheykh da Umaymah basuyiba, amman Al'amin da Bappa sunƙi suci abinci.
Kiran sallan azahar ne, Yasa duk suka miƙe.
Cikin sanyi Al'amin ya kalli ogogon hannunshi da yaketa sheƙi yace. "Bappa muyi salla mu tafi kada lokacin ya ƙure mana". Cikin kula Umaymah tace. "Ba kwana zamuyi ba". Murmushi Bappa yayi tare da cewa. "A'a zamu koma tunda jiki da sauƙin gata taci ta ƙoshi tana hira." A hankali Ummi tace. "Eh ai dama haka takeyi, anjima kuma in ciwon ya tashi zakace kamar zata shiɗe, sai an mata tofi take ɗan samun sauƙin". Murmushi Al'amin yayi tare da kallon Sheykh cikin nitsuwa da gogewar cikar wayewar dake nuni ba makiyayin daji bane yace. "Sheykh ka samu sabuwar wayar hannu, kenan tunda sai kayi tofi akejin sauki. Dan Allah duk inda kake ta kasance a nan a ƙara kulan mana da Boɗɗin Abbai". Murmushi ya ɗanyi tare da cewa. "In Sha Allah". Cikin karrama Sheykh ya nuna musu wata ƙofar dake gefen ɗakinshi yace. "Ga wuri kuyi al'wala mu tafi masallacin". kai Al'amin ya gyaɗa kana yace. "Bappa je kayi al'wala kazo mu tafi. Cikin nitsuwa Bappa yace da al'wala ta". Shima Al'amin gyara tsayuwarshi yayi tare da cewa. "Nima inada al'wala".
Cikin gamsuwa Sheykh yace. "To bisimilla muje nima da al'wala". To sukace kana duk suka nufi babban falon.
Suna isa tsakiyar falon. Al'amin ya ɗan tsaya tare da cewa. "Parvina zo". Da sauri ta ƙaraso gabanshi. Shiru sukayi jin Al'amin ya juya harshe zuwa wani Yaren ba larabciba ba Turanciba ba hausaba ba fillanciba.
Mgna yakeyi riƙe da hannunta. Ita kuwa Aysha kai taketa gyaɗa mishi ido cike da kwalla. Hannunshi yasa ya share mata hawayen kana yasa hannunshi ya shafa kanta tare da juyawa ya fita. Ita kuwa Aysha cikin sanyi tace. "Bappa dan Allah a kawo min Junainah". Kanshi ya gyaɗa kana shima ya fita. Binsu a baya Sheykh yayi.
Ita kuwa hannunta mai lfyar tasa ta share siraran hawayen da suka zubo mata. Kana ta juya ta nufi ɗakinta. Ummi da Umaymah kuwa kallon juna sukayi suma suka wuce ɗakin su.
Bayan an idar da sallan ne, Sheykh da kanshi ya ɗauki su Bappa ya kaisu tasha kamar yadda sukace.
Bayan ya kaisune. Yayi musu fatan isa lfy ne, yaja motarsa kamar ya tafi. Ya koma can baya ya ajiye motar kana ya kira Ado drevernshi da yake cikin but ya fito. Sannan yace. "Bisu".
Da sauri Ado yabi bayansu.
Shi kuma yayi gida.
A hankali Ado yake binsu. Ga mamakinshi sai yaga sun tari taxi sun shiga. Shima taxi ya tsaida ya shiga, tare da cewa. "Bisu duk inda suka nufa."
To yace, kana yabi bayansu kai tsaye international airport Ɓadamaya suka shiga. Suna shiga.
Kuwa suka fito. Suka biya mai taxi ɗin da kuɗin ma da bana ƙasar Nigeria bane kuɗin ƙasar Cameroon ne. Cikin sanyi Al'amin yace. "Yi haƙuri bamu da canji ne, kaje wurin yan canji za'a canza maka su zuwa Naira". Cikin jin daɗi mai taxi ɗin ya tafi.
Shima Ado ya sallami nasa mai taxi ɗin.
Kana yabi bayansu tafiya kaɗan sukayi yaga wasu mutane a ƙalla su shida, sunbi bayansu duk suna cikin shigar sut.
Al'amin dake gefen Bappa ne ya miƙo wa ɗaya na kusa dashi hannu. Wayar iPhone ƙirar wannan shekarar ya miƙa mishi. Sai kuma system ɗinshi. Daga nan kan tsaye sukaje suka shiga jirgi. Dole Ado ya rakasu da ido.
Su kuma jirgi ya ɗaga dasu.
Tun kafin Ado ya koma gida ya kira Sheykh ya labarta mishi. Murmushi Yayi jin abinda Ado yace mishi. Kai ya jinjina tare da danna wasu ababe a wayarsa. " ?+? ". Murmushi yayi kana ya jefa woyar a al'jihunsa.
Bai shiga gidaba sai bayan sallan isha'i.
Yana shiga kuwa ya samu su Ummi a falo. Aysha da hannunta ya ɗan fara zogin. ta bishi da ido. ganin kamar bazata tashi bane yasa. "Umaymah cewa tashi kije ya miki tofin."
To tace kana ta miƙe, ta nufi Side ɗin nashi. Babu kowa a falon sai dai ta hango shigarsa ɗakin. A hankali tabi bayanshi tura ƙofar Bedroom tayi tare da sallama. Kana ta kutsa kai cikin ɗakin. A hankali ta isa tsakiyar ɗakin babu kowa. cikin sanyi tace. "Ina jiranka dan Allah kamin tofin". Shiru taji ba mgna ba kuma motsin komai a ɗakin.
Cikin sanyi ta ɗan fara hurawa hannunta iskan bakinta. Tana kallon ƙofar Bathroom ɗin.
A hankali kuma ta miƙe tana cewa. "Shyyyuuu hahjjyyyyyyyt". Sai kuma ta matso bakin ƙofar Bathroom ɗin da niyar ta bubbuga ƙofar. Tana sa hannu bisa ƙofar ta buɗu. Da sauri ta ɗan ja da baya. A hankali tace. "Yi haƙuri bansan a buɗe yakeba". Still ba mgn kuma ba motsin ruwa. Hakane yasa ta ɗan leƙa. Ganin ba kowane a ciki ta kutsa kai ciki tare da cewa. "To ina kake ina ka shiga". Shiru wayam ba kowa, komai na bathroom ɗin yana nan fes-fes a kimtse. Da sauri ta fito bedroom ɗin. Waige-waige tayi ba kowa. Haka yasa ta fito falon da sauri tana cewa. "Umaymah ban ganshi bafa, kuma na hangoshi yana shiga ɗakin. Na shiga kuma ban ganshiba." Ummi ce ta amshi zance da cewa. "Ko ya shiga wonka ne". Da sauri tace. "A a baya cikin bathroom". Umaymah ce ta ɗan kalleta tare da cewa. "Ki duba Dinning area ko yana can". Da sauri ta juya tana cewa. "Ɗakin fa ya shiga, kuma ban ganshi ba."
Ummi ce tace. "To kije dai ki ƙara dubawa".
Dube-duben tayi a falon kana ta koma cikin bedroom ɗin wayam fa
A hankali ta ƙarewa wodurob ɗin shi kallo, buɗesu tayi duka, tana cike da mamakin to ina ya shiga, dan tabbas taga shigarsa ya kuma za'ayi baya ciki to ina ya shiga?. A haka duk ta bubbuɗe durowowin babushi babu alamarshi.
Falon ta sake fitowa tana mai jin zohin hannun yana tsananta.
Ɗaura hannun tayi a kanta tana jin idonta na kawo ruwa.
Umaymah ce ta shigo. Ƙofar shiga cikin Garden ɗin su ta duba. A rufe take babu alamun an taɓata ma.
Ƙofar ɗaya ɗakin ta nufa zata buɗe. "Aysha tace. "Allah ko Umaymah bai shiga nanba ɗauki shi ya shiga. Kuma na duba baya ciki tako ina kuma banga fitanshi ba."
"Ikon Allah to ina ya shiga?". Umaymah ta faɗa tana. Shiga ɗakin. Jim kaɗan ta fito. A gefe ta tsaya tana mamaki tabbas dai sunga ya wuce.
Da sauri suka miƙe ganin ya buɗe ƙofar ɗakinshi ya leƙo yana cewa. "Umaymah lfy kuwa? Naji kunata salati". Da sauri tace. "Kai muke nema bamu ganka ba, ina ka shiga Aysha tace baka cikin ɗakin." Kanshi ya ɗan juyo ya kalleta tare da cewa. "Uhumm to dama ya za'ayi ta ganni tanata kuka ta gigita kanta ba dole ta makanceba". Cikin gamsuwa da hakan dan Umaymah ta yarda wata ƙil ciwone ya gigita Aysha shiyasa Bata ganshi ba.
Ita kuwa Aysha cikin zafin tace. "Wlh Umaymah ba ciwo bane na duba ko ina ban ganshi ba". Kai Umaymah ta gyaɗa kana tace. "To kije ya miƙi tofin". Miƙewa tayi ta nufi cikin ɗakin.
Ita kuma Umaymah ta koma falon.
Raɓawa gefe tayi ta shigo. Shi kuwa maida ƙofar yayi tare da cewa. "Zo nan". Matsowa tayi ya fara yi mata tofin tana jingine da ƙofar yanayi yana hura mata iska. A hankali ta fara lumshe ido, ganin zatayi bacci ne yace. "To jeki". Har zata fita sa kuma ya ɗan sha gabanta ido ya zuba mata kana a hankali yace. "Ke komai kika gani sai kinyi mgn ne?". Kai ya jujjuya alamun a a. Gashin girarta ya zubawa ido tare da cewa. "Bubbuga Rumbun Abboi". Baki ta ɗan tura tare da cewa. "Ni dai ba bubbuga Rumbun bace". Matsota ya farayi ganin hakane ta ɗan ja da baya ta jingina da ƙofar, kusa da ita ya kuma matsowa kana a hankali yace. "To ke meyece in ba bubbuga Rumbun ba, ko kunya babu kin zauna gaban wanda ba mijinkiba, yana baki abinci har baki". Gashin tattausan gemshi ta ɗan kalla tare da cewa. "To nida Yayana ɗan uwana, tunda mai bani Allah ya kawoshi ai sai ya bani kada yunwa ta kasheni". Murmushi mai sanyi yayi sabida tambaya ɗaya ya mata cikin amsa tambaya ɗayan kuma ta amsa mishi tarin tambayoyinshi. iskar bakinshi ya ɗan hura mata tare da cewa. "Kince in baki ban baki bane?". Da sauri tace. "Toh sai nace ne?". Ƙara matsowa kusa da ita yayi tare da ɗada mata girarshi ɗaya a hankali yace. "Na'am sai kin ce mana shima ai ce masa kikayi ya bakin". Mutsu-mutsu ta farayi jin ƙirjjinshi na danne nata a hankali tace. "Toh ai shi ɗan uwanane". Ba zato yaji mgnar ta subce mishi. "Toh ai Ni kuma mijinki ne". Sai kuma yayi sauri ya matsa, tare da juya mata baya. Ita kuwa sumar ƙeyarshi ta zuba ido kana a hankali ta juya. Cikin lumshe ido ta fita.
Shi kuwa Sheykh wata iriyar sassayar ajiyar zuciya ya sauƙe mai nauyi. Kana ys cire kayan jikinshi. Sannan ya shiga wonka. Bayan ya fitone yayi shirin baccinsa. Kana ya kwanta.
Ita kuwa Aysha tana shiga ɗakinta ta kwanta sai bacci.
Umaymah kuwa na ɗakin Ummi suna tattauna wata mahimmiyae mgna, sai ƙarfe sha biyu ta shigo. Tayi mamakin ganin Aysha konce tana baccin. A hankali tace, uhum tana tashi zan kai maka ita tunda ka iya kora masu maganin ka kora sarkin bakan masarautar Joɗa kana ka kora wanda iyayenta suka zo dashi.
Daga nan taje tayi al'wala tazo ta kwanta.