Garkuwa complete novel - Chapter 71
Garkuwa complete novel Chapter 71: Garkuwa complete novel Chapter 71. Murmushi mai yelwa Gimbiya Aminatu tayi ganin yadda Sheykh ke ruggume da matarsa da…
4,223 words
Murmushi mai yelwa Gimbiya Aminatu tayi ganin yadda Sheykh ke ruggume da matarsa da yartsu a tsakiyarsu wace taketa wawure-wawuren hannunta. Kusa dasu ta zauna daɓas, kana tasa hannun ta amshi yarinyar tana cewa Shatu. "Sannu Gimbiya Aysha surkar Gimbiya Aisha mai sunan Maman Lamiɗo, uwa kuma ga AYSHA masha Allah." Shi dai Sheykh sai murmushi yakeyi Ita kuwa Gimbiya Aminatu amsar yarinyar tayi, Kana ta ɗan kamo zariyar cibiyar, ta saita da ƴar ƙaramar yatsarta ƴar ƙuri, wanda hakan yayi dai-dai da kan mahaɗan da alamun kamar ƙari a wurin wanda dai-dai kan ƙarin ta ƙasa tasa zaren ɗinki ta zagaye ta ɗaure cibiyar kana tasa reza ta yanke. Miƙa Ummi yar tayi tare da cewa. "Kin amshi haihuwar Babanta tsawon shekaru talatin da lokacin tun kina ƙaramar ki, yau kuma kin amshi haihuwarta, kiyiwa babanta jakadanci itama kiyi mata". Da sauri Sheykh yace. "A a kam shiyasa ban bari ƴar ta faɗo a hannuntaba, dan Ummi na ayntacciyace nima bazata min jakadanciba bare ɗiyata, jika ta samu wannan shine tukuicin forko da zanwa Ummi a masarautar Joɗa daga yau wannan sunan Jakadiya ya bar kanta". Ruggume ƴar Ummi tayi tare da sakin wani irin murmushi mai haɗe da hawaye tana sa yar cikin mayafin nan tana cewa. "Masha Allah, zuwanki ya iso mana da al'khairai". Shi kuwa Sheykh cikin sanyi yace. "Ummi ni wannan al'adarfa ba sonta nakeba, kada asa min ƴa a kwarya". Da sauri Gimbiya Aminatu tace. "Jakadiya fita harkar shi ɗauki ƴar ki kaiwa Lamiɗo gashi tafi da mabiyiyar kije ki benneta inda ake binne na ƴaƴan ɗakinsu". Da sauri tace. To. Shi kuwa Sheykh a hankali yace. "Ummi a bari in mata wonka". Bata kulashi ba ta fita. Ganin haka ya miƙe ya kamo hannun Shatu. Bedroom ɗinta Suka shiga, kai tsaye Bathroom Suka wuce, suna shiga ya ajiyeta kan toilet, ai kuwa sai ga jinin yana zubowa.
Ita kuwa Gimbiya Aminatu tattare wurin tayi kana da sauri tabi bayansu. Tana zuwa bakin ƙofar tace. "Kai buɗe ƙofar ka fito". Cikin nitsuwa yace. "Wonka zatayi." Tura ƙofar tayi ta shiga tare da cewa. "Bani wuri". Shiru yayi ya koma gefe, ita kuwa Gimbiya Aminatu a nitse ta juyo ta kalli Shatu dake zaune. "Yanzu taso kizo kiyi wonka". Cikin sanyi tace. "Toh a haɗa min ruwan zafi". Da sauri Gimbiya Aminatu ta girgiza mata kai tare da cewa. "A a ai mu al'adar masarautar Joɗa mace in ta haihu bata wonka da ruwan zafi bazataci abinci mai zafiba bazatasha abin sha mai zafiba. Komai da abu mai sanyi zatayi amfani. Jaririnma muddin na mijine to da ruwan sanyi za'ayi mishi wonka in macece muke ɗan tarfa na ɗumi kaɗan sabida bamu sai ita ina rabo zai kaitaba". "Ikon Allah sai kallo waito wasu tsarabe-tsaraben sai yaushe za'a barsune a saki al'ada a kama gsky". Ya hafaɗa yana taimakawa Shatu ta shiga wurin wonkan. Kana yayi gefe.
Ita kuwa Shatu kasan cewar ta gaji yasa bata ce komaiba. Wonka tayi kana ta fito. Suna fitowa Gimbiya Aminatu ta koma falo, shi kuwa a hankali ya jawo hannunta, bakin gado ya akiyeta, kana a hankali yace. "Ɗan gyara inga ko baby ta ƙaraki". A hankali ta ɗan kwaɓe fuska, kanshi ya jujjuya alamun kiyi haƙuri. A hankali ta ɗan zame ta konta, towel ɗin ya ɗan ja, kana ya sunkuyo, da sauri yace. "Akwai ƙarin amman ɗan ƙanƙanine ɗan kaɗan yanzu kici abinci mu tafi Valli muyi ɗinki". Ya ƙare mgnar yana gyara mata towel ɗin. Da sauri Ummi dake bakin ƙofar tace. "A a ba'a buƙatar ɗinki zai haɗe da kanshi". Shiru yayi yana kallon Ummi sai kuma ya miƙo hannunsa ya amshi Babyn. Wacce anyi mata wonka an naɗeta cikin rawanin Lamiɗo. Murmushi yayi, tare da matsowa gefe ya zauna a bakin gadon.
Ita kuwa Ummi taya Shatu kimtsawa tayi. Kana tace. "To zauna bari in kawo miki abinci". Da sauri ta kwanta tare da lumshe ido kana tace. "A a Ummi barshi wlh bacci nakeji sai nayi in na tashi zanci". Jin haka yasa tace. "Toh."
Har zata fita sai kuma ta tsaye jin yana cewa. "Uhummm Ayyah Ummi a bani zam-zam da dabino mana". Da sauri tace. "Toh". Ba kowa a falon haka yasa taje ta ɗauko danino da zam-zam ta kawo mishi kana ta juya ta fita.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya ɗan malle marfin zam-zam ɗin yasa a bakinshi yasha da kyau. Kana ya buɗe kwalin dabinon. "Bismillah". Yace kana yasa dabinon a baki, ya tattaunashi da kyau. Ya haɗe da damshin zam-zam da yawunshi ya tsastsafo da ruwan zaƙi da ɗan-ɗanon da binon. A hankali ya sunkuyo ya kawo bakinshi kusa dana yarinyar, ita kuwa Shatu ido kawai ta zuba musu. Da sauri ta kalleshi jin an fara kiran sallan magriba. Shi kuwa bakinshi ya manna kan na yarinyar ya rinƙa tura mata ruwan dabinon, ai kuwa sai gashi tana laluma tana haɗiyewa, murmushi yayi tare da juyowa ya kalli Shatu a hankali yace. "Uhumm Bubbuga Rumbun Abboi ta haifo bubbuga Rumbun Sheykh dan ke ta gado da ciye-ciye". Murmushi mai cike da jin daɗi tayi tare da cewa. "Allah Junainah ce uwar kwaɗayi da kuma Jamil to ta gaji ƙanin ka da ƙanwata". Murmushi ya kumayi yanaji a ransa yanzu dai sun gama zama abu ɗaya. Haka yayi ta taunar dabino yana bata ruwan saida ya tauni tabino bakwai.
Amfanin fara bawo yaro dabino a matsayin abinci na forko da zai fara ci a duniya yana da yawa. Ɗaya daga cikin wanda manyan likitocin duniya sunyi ittifaƙi a kai kuma sun gamsu dashi shine. Sun gano duk wani abinci da na sha a duniya kab in ɗan adam yaci, sai sun fara zama a ciki uwar hanji ta bambance ta fidda mai kyau da mara kyau kana ya sarrafu ya zama jini kafin nan zuciya kuma ta harba ta rabashi ko wani sashi da saƙo na jikin ɗan adam. Sai dabino ne abinci ɗaya da likitocin suka tabbatar da cewa. Shi muddin ka cishi kai tsaye ƙoƙolwar ɗan adam yake wuce, ya wonketa ya in ƙantata. So bada ruwan dabino ga jariri yana sa yaro ya tashi mai kaifin basira da ilimi da kwarin ƙoƙolwa. Yayinda mutane kuwa ke cewa. Yaro zaiji mgnar wanda ya shayar dashi ruwan dabinon da yawunsa fiye data kowa. Wannan shine bayanin da Sheykh yakewa Shatu yana mai kontar mata da jaririyar kusa da ita. Murmushi tayi tare da cewa. "Masha Allah". A hankali ya ɗan shafa kanta kana yace. "Bari in tafi masallaci". Ya ƙare mgnar yana fita.
Ita kuwa ido ta zuwaba ƴar tasu. Shi kuwa tv ya kashe kana ya nufi falonshi.
Ummi kuwa tana kitchen zabbi take gasawa waya na saƙale a kunneta Umaymah taketa kira tun ɗazu amman bata ɗagawa.
Katse kiran tayi ta kira Juwairiyya tana ɗagawa tace. "Juwairiyya Shatu fa ta haihu". Cikin tsananin jin daɗi Juwairiyya dake bisa sallaya tace. "Kai Ummi Alhamdulillah masha Allah me muka samu?".
"Ɗiya mace".
"Masha Allah bari inyi salla inzo".
Galadima kuwa yana komawa Side ɗinsa ya gayawa matarsa.
Ita kuwa Ummi Umaymah ta kuma kira, bugu ɗaya ta ɗaza da sauri tace. "Assalamu alaikum al'bishirinki Umaymah". Cikin dariya mai cike da zallar jin daɗi da farin ciki tace. "Goro Ummin Jabeer amman Lamiɗo ya rigaki, yanzu yake gayawa Jaddanmu kinsan su Mamma da Aunty Rahma sun zo shekaran jiya, nima tun jiya ina Katsina. To yanzufa Jadda ya shigo yake gaya mana kai Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!." Cikin dariyar jin daɗi Ummi tace. "Eh lallai Lamiɗo yamin shigar saurin". Sitti ce ta amshi wayar tare da cewa. "A a kada ki damu goron Al'bishir ɗinki na musamman ne". Aunty Rahma dake gefene tace. "Ummi yar da waye take kama". Da sauri Ummi tace. "Wlh da Ishma take kama". Mamma ce ta amshi zancen da cewa. "Allah sarki yadda take son Ishma haka Allah ya bata mai kama da ita". Dariyar jin daɗi sukayi dukansu da yake wayar a amsakuwa take". Daga nan Ummi ta ƙatse kiran ta nufi falon. Ɗakin Shatu ta fara shiga murmushi tayi ganin Shatun na konce tanata kallon yarinyar tana mata tofi. Fita tayi ganin bata gantaba.
Ana idar da sallan isha'i suna fitowa Sheykh yayi sauri yabi bayan Abbanshi. Kana ya bar Jalal Jamil Yah Jafar, Yah Hashim Affan Laminu Sulaiman a bayanshi. Da sauri yace. "Assalamu alaikum, Abba". Da sauri Abban ya juyo wanda Dr Aliyu da Baba Basiru Baba Kamal Baba Nasiru da sauran ƙannen Abban nasu suka tsaya da sauri jin yana cewa. "Alhamdulillah Aysha ta sauƙa lfy". Yayi mgnar a hankali ne cike da nitsuwa da zallan farin cikinsa daya kasa ɓoyuwa. Cikin sauri Dr Aliyu ya juyo tare da cewa. "A a masha Allah, Masha Allah". Baba Kamal ma kalmar yake faɗi. Baba Nasiru kuwa cikin wani irin masifeffen tashin hankali da tsana yace. "Me aka haifa maka?". Da sauri Baba Basiru yayi wani irin murmushi tare da cewa. "Sa ranka a inuwa ƴan macece ba mai gadan mulki aka haifa mishi ba". Karo na forko a lokaci na forko Abbansu yasa hannunshi ya jawoshi jikinshi ya ruggume shi, gam a jikinshi tare da cewa. "Alhamdulillah Muhammad Allah ya raya mana ita bisa imani ya bawa mahaifiyarta lfyar shayarwa da bata kekyawar tarbiya, nayi farin ciki mai tarin yawan da jin wannan Magauta zasuyi rabkanuwar aiyukansu".
Ya ƙare mgnar tare da sakeshi. Tabbas shi kam haihuwar nan tazo mishi da wasu abubuwa manya, wai yau shine har Abbansu ya ruggume shi. Su kuwa gaba ɗaya tafiya sukayi.
Shima binsu a baya yayi. Su Jalal kuwa da Yah Jafar da Jamil da Affan da sauri sukabi Yah Sheykh ɗin nasu a baya. Sabida suna cike da mamakin yadda suka hango Abbansu ya ruggume shi.
Kusan a tare suka kutsa kai cikin falon.
Ummi dake riƙe da babban kular da tasa gasassun zabbin ne ta juyo da sauri, ta kalli Juwairiyya dake bayanta tana cewa. "Iye gafa Daddyn Baby da Uncles ɗinta". Da sauri Jamil ya shigo cikin falon yana cewa. "Kai haba dai My Adda Shatu ne ta haihu?". Yayi mgnar cikin zumuɗi suma sauran gaba ɗaya ido suka zuma mata jiran amsarta. Shi kuwa Sheykh murmushi mai cike da yelwa yake, tare da zaro wayarshi a aljihu.
Ummi ce tayi dariyar jin daɗi tare da cewa. "Wlh kuwa Alhamdulillah Shatu ta haifo mana Kekkyawar ɗiyar fulani fara ƙal". Kusan a tare Jamil da Affan sukace. "Yesssss masha Allah Alhamdulillah". Jalal kuwa wani irin murmushi yayi mai baiyana farin cikinsa a hankali yace. " A a kai Alhamdulillah Allah mun gode maka, Allah ka raya mana ita bisa imani".
Yah Jafar kuwa da sauri ya juyo ya kalli Sheykh ga mamakinsu babu zato babu tsammani sukaji yace. "La'ilahaillaha Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam. Alhamdulillah Allah na gode maka, daka c nuna min wannan ranar Alhamdulillah ni Muhammad Jafar Allah na gode maka". Wani irin juyowa da ƙarfi Sheykh da zai shige falonsa yayi cikin tsananin kaɗuwa da tarin al'ajabi da mamaki da rantsar kokonton shin muryar Yah Jafar ce kuwa da tsawon shekaru 13 baiyi mgnaba yake mgn?. Jalal kuwa da sauri ya koma da baya ya faɗa kan kujera sabida rawan da jikinsa keyi. Jamil da Affan da sauri suka matso kusa dashi. Ummi kuwa da sauri ta saki kular dake hannunta. Ita kuwa Juwairiyya cikin tsananin kaɗuwa da tsoro ta matso gabanshi bakinshi take kallo tamkar zata cire idonta ta mannasu jikin lips ɗinsa gaba ɗaya sun kasa mgn.
Shi kuwa Sheykh da sauri ya iso gabansa hannunshi ya kamo ya riko gam gam tare da cewa. "Yah Jafar mai-maita abinda kace Yah Jafar sake mgn inji maimata". Yayi mgnar da ƙarfi cike da kaɗuwa. Ga mamkinsu sai ga Yah Jafar ɗin yayi shiru yana kallonsu Tamkar kurma. Cikin wani irin tsuma da kaɗuwa duk suka zagayeshi. Cikin tsananin farin ciki Sheykh ya ruggume shi gam-gam a jikinshi murya cike da al'hini da hamdala yake cewa. "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!. Yah Jafar kayi mgna ka sake yin mgn dan Allah kayi mgn". Ya ƙarashe mgnar yana mai janye jikinshi daga jikin Yah Jafar ɗin tare dasa hannunsa bisa kafaɗunsa duka biyu yana jijjigawa. Itama Juwairiyya cikin rauni murya na rawa cike da kukan hamdala tace. "Yah ilahi ya mujibadda'awati ya Allah idan mafarki nakeyi ka tabbatar min dashi". Cikin sauri Jalal dake zaune yace. "Ba mafarki bane Aunty Juwairiyya". Affan ne ya matsosu tare da haɗe su duka ya ruggume sai kawai ya saki kuka. Ummi kuwa cikin shassheƙan kuka tace. "Sheykh ku barshi mu bishi a hankali tabbas mgn yayi kuma in sha Allah zai kumayin mgn". Jamil kuwa gaba ɗaya jikinshi kerma yakeyi wayarshi ya zaro Umaymah ya kira tana ɗagawa ya fashe da sassayan kuka tare da cewa. "Umaymah! Umaymah!!". Cikin tsananin ruɗani da kiɗima tace. "Innalillahi Jamil mene! Jamil gaya min meyasa ka kuka". Da ƙarfi yace. "Umaymah kukan farin cikine. Yau Yah Jafar yayi mgna kuma ya maimaita Umaymah farin cikine ya samu kuka". Cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa Umaymah ta saki wayar tare da juyowa ta kalli Sitti da Jaddansu da sauran ƙannenta da babban yayansu baban Aunty Juwairiyya da Ibrahim kenan. Cikin wani irin murmushi mai haɗe da hawaye tace. "Sitti Jadda Jafar ya fara mgn". Gaba ɗaya salati suka ɗauka a tare, suka direshi da kalmar. "Alhamdulillah ala kulli halin, Alhamdulillah lallai tabbas dukkan tsanani yana tare da sauƙin." Kawai sai kuma duk suka matso gaban Jaddansu da ya saki kuka kamar ƙaramin yaro cikin rawan murya yace. "Ɗaya daga cikin burukana ya cika, kafin mutuwata ko yanzu na kwanta dama nasan bakin Jafar ya buɗu. Sai dai har yanzu ina da wani babban buri Yah Allah ka bani aron rai da lfy ka ka baiya na min ƴata Aisha ka tsare min ita a duk inda take ka dawo da ita kan ƴaƴan ta al'farmar Annabi da al'ƙur'ani". Cikin zubda hawaye suka amsa da Amin Amin gaba ɗayansu.
A nan masarautar Joɗa kuwa, Cikin tsananin tarin farin ciki Sheykh ya kamo hannun Yah Jafar ya zaunar dashi bisa kujera kana da sauri ya juya ya nufi ɗakin Shatu. Konce ya sameta da alamun bacci takeyi. Hannunshi yasa ya ɗauki Jaririyar kana da sauri ya juyo ya fito.
Yana fitowa kuma dai-dai lokacin Lamiɗo da Galadima da Abbanshi suka shigo falon. Cikin sauri ya matso gaban Yah Jafar miƙa mishi ƴar yayi ga mamakinsu sai sukaji yace. "Bismillahi". Cikin tsananin kaɗuwa da mamaki Lamiɗo Galadima da Abba suka zauna, Lamiɗo da Galadima da Yah Jafar bisa kan kujeru sauran kuma duk kowa na ƙasa harda Abbansu. Kallon kallo sukayiwa juna lokacin da suka ga yana shafa kan yarinyar tare da buɗe baki a hankali yace. "Masha Allah. Allah ya raya mana ke bisa imani yayi miki al'barka". Zuwa yanzu Lamiɗo da Galadima cikin kaɗuwa suke cewa. "Jafar". Da sauri Sheykh ya juyo ya kalli Abbansu da tuni hawaye suke tsastsafo mishi ya kasa cewa komai sai tallabe haɓarsa yayi da hannu bibbiyu yana kallonshi. A hankali Sheykh ya juyo kamar ƙaramin yaro haka ya iso da rarrafe. Ya zauna gaban mahaifin nasu ya fuskanceshi da kyau hannunshi yasa ya kamo hannun Abban nasu ya zare mishi tagumin da yayi, kana yasa tafin hannunshi ɗaya ya share mishi hawayen da yakega suna zubo mishi cikin ƙarfin zuciya da tsananin farin ciki kan farin ciki murya cike da girmamawa yace. "Abbanmu kace Alhamdulillah kada kayi kuka, Abba kaga ikon Allah ko Yah Jafar yayi mgn a yau yayi hamdala yace ya godewa Allah daya nuna masa wannan ranar muma muce mun godewa Allah mana sai ya ƙara mana wata ni'imar domin indan Allah yayi maka wata ni'imar ka gode mishi sai ya ƙara maka da wata, muce Alhamdulillah". Kusan a tare gaba ɗayansu sukace. "Alhamdulillah". Harda shi Yah Jafar ɗin. Ya ilahi wannan shine kyautar Allah. Juwairiyya kam hawayenta yaƙi barin zubowa.
Lamiɗo kuwa a hankali ya dawo kusa dashi hakama Galadima, sai ya zama sun sashi a tsakiyarsu. Abban da Sheykh kuwa suna gabansu da sauran Juwairiyya da Ummi kuwa suna gefe". Cikin nitsuwa Abba yace. "Jafar! Jafar!! Jafar!!!". Shiru babu amsa. Da sauri Lamiɗo ya jujjuya mishi kai tare da cewa. "A a barshi, dole sai a hankali komai zaiyi dai-dai." Sai kuma ya gyara zamanshi ya kalli jikokin nashi ya juya dama da hauni kana cikin yin ƙasa da murya yace. "Toh wannan al'amari ya zama sirri tsakaninmu har zuwa ɗan wani lokaci kada ku gayawa kowa na cikin masarautar Joɗa". Da sauri sukace "To". Shi kuwa Sheykh a hankali yasa hannunshin ya ɗauki Jaririyar ya miƙa Lamiɗo ita. Addu'o'in yayi mata sosai kana ya miƙawa Galadima ita, sannan Sheykh ya ɗauƙeta ya miƙa Abba ita cikin murmushi yace. "Aisha ta tafi Aisha ta dawo". Murmushi Ummi tayi sabida tuno irin tarin son da Abba kewa Mamey wanda shiga goma zai zaka jishi yana kira Aisha! kaxa Aisha kaza da kaza yayi kaza ko?,". Shima addu'o'in yayi mata kana, suka ɗan tattauna kaɗan suka tafi.
Su Jamil kuwa suma ɗaya bayan ɗaya suka amsheta. Cikin murmushi da tarin son yarinyar Jalal yace. "Masha Allah da Ishma take kama". Da sauri Jamil ya amsheta tare da cewa. "Kace da Mamey take kama tunda Ishma dai da Aunty Rahma take kama Aunty Rahma Kuma da Mameynmu take kama". Da sauri Affan ya amsheta tare da cewa. "Masha Allah wlh da Mamey take kama, Alhamdulillah Yusuf ƙarami yayi kamu". Ɗan shi kenan takwaran Hamma Yusuf ɗin Zahra dariya sukayi baki ɗayansu. Kana Aunty Juwairiyya ta amshi yarinyar ita da Ummi suka nufi ɗakin Shatu.
Suna shiga suka sameta zaune bakin gado da alamun waya takeyi da Rafi'a. "A a bazan gaya miki ba sai kinzo kiga mai aka samu". Tayi mgnar tana amsar Babyn da Aunty Juwairiyya ke miƙo mata. Ita kuwa Rafi'a cikin tarin jin daɗi tace. "Ai kuwa gobe da sassafe zan muku sammako". Da sauri tace. "Rafi'a baza kizo mu kwana ba". Cikin dariyar jin daɗi ta e. "Zan dai zo gobe kam da wuri". Daga nan sukayi sallama. Ita kuwa Ummi abinci ta zuba mata mai rai da lfy cimar jegon gaske. Tuƙeƙƙen tuwon shinkafa da miyar ɗanyar kuɓewa tasha man shanu da yajin daddawa da nama. Sosai ta tasata gaba taci. Ita kuma Juwairiyya tana riƙe da Ƴar.
Bayan taci tuwon ne kuma Ummi tasa mata gashin da yaketa tururi yaji yaji tana fifita matashi dan yayi sanyi. Kana ta haɗa mata kunu da zuma ta bata, tanaci tana ɗan korawa. A hankali ta ɗan jingina bayanta da gado a hankali tace. "Ummi na ƙoshi". Da sauri tace. "A a Shatu ƙara sashi kada kice zakiyi jegonku na yaran zamani jego da soyayyan Arish da tea". Cikin sanyi tace. "Allah Ummi cikina zai fashe". Jin hakane tace. "To sai anjima ki ƙara". Gyaɗa kai tayi kana ta gyara zamanta.
A can falon kuwa su Jamil duk Dinning area Suka nufa, suka zauna suka fara cin abinci.
Yah Sheykh kuwa falonshi ya wuce, wayarshi liƙe a kunne wanda Bappa yake kira.
Shi kuwa Bappa a can Rugar Bani yana zaune a tsakar gida Junainah na gefenshi su Ummey na gefenta.
Da sauri Junainah ta miƙo mishi wayar da dama Game takeyi da ita. Amsa yayi da sauri ya amsa kiran. Gyara zamanshi yayi jin muryar Sheykh na cewa. "Assalamu alaikum". Cikin kulawa yace. "Wa alaikassalam Muhammad". Da sauri ya zauna bisa kujera cikin tarin jin daɗi da son tsohon da tausayinsa yace. "Na'am Bappa na Ina wuni". Fuska ɗauke da murmushi yace. "Lfy lau Alhamdulillah Muhammad ya su Lamiɗo ya Abbanka dasu Jalal duk suna lfy koma?".
"Alhamdulillah Bappa duk suna lfy cikin farin ciki". Ya bashi amsa yana murmushi. Shi kuwa Bappa cikin kula yace. "Yah Shatu na?". Murmushi Sosai yayi kana yace. "Alhamdulillah Bappa Shatunka ta girma yau ɗazu da yamma gabanin magriba ta zama uwa". Cike da tsananin farin ciki Bappa yace. "Masha Allah! Alhamdulillah yaushe ta haifu mata na samu ko aboki mai tayani kiwo?". Murmushi yayi tare da cewa. "A a Bappa wannan Gimbiya ce amrya ka samu". Cike da farin ciki Bappa yace. "Alhamdulillah Allah ya raya mana bisa imani". "Amin Amin". Yace yana mai jin muryar Junainah tana cewa. "Ayyah Bappa bani shi Adda Shatu ce ta haihu?". Cikin kula yace. "Bappa a bawa Junainah waya". To yace kana ya miƙa mata wayar, tare da juyowa ya kalli Ummey cikin murmushin yace. "Alhamdulillah Shatu ta sauƙa lfy an samu ƴa mace yanzu da yamman nan". Wani irin ajiyan zuciya mai sanyi Ummey ta sauƙe tare da cewa. "Alhamdulillah yau kam zanyi bacci hankali na konce Shatuna ta haihu lfy". Murmushi Inna Amarya tayi tare da cewa. "Wlh kuwa kai Alhamdulillah Metai fi haka daɗi kaji kawai ɗan ka ya haihu lfy".
"Wlh kuwa fa". Cewar Bappa. Sai kuma suka juyo suna kallon Junainah dake tsalle tana cewa. "Alhamdulillah Hamma Jabeer kace dani takeyin kama?." Murmushi yayi tare da cewa. "Sosai ma kuwa Junainah". Cikin dariya tace. "Allah shi ƙara dama kullum Addana sai tace wai ta fini kyau wai inada dogon bakin kwaɗayi, ni kuma kullum ince Allah yasa ta haifi irina ai zata dena cemin mummunan". Dariya yayi sosai kana yace. "Toh gobe dai zaki zo mana ko?". Da sauri tace. "Eh zanzo Bappa na da Ummey ma zasu zo". Katse kiran tayi kana ta miƙawa Bappa wayar. Shi kuwa kiran Abboi yayi ya kara wayar a kunne tare da cewa. "Assalamu alaikum".
"Wa alaikassalam".
"Barka da dare Abboi".
"Barka dai Bappa Shatu." Abboi yace yana murmushi tare da kallon Dedde dake gefensa.
Cikin jin daɗi Bappa yace. "Alhamdulillah yau Shatu na ta hau matakin uwa ta sauƙa lfy mun samu ɗiya mace". Wani irin yalwataccen murmushi mai cike da jin daɗi Abboi yayi tare da cewa. "Alhamdulillah kai yau naji labari mai daɗi masha Allah. Kace lallai zuwa Nigeria ya kamani". Da sauri Bappa yace. "Sosai ma kuwa, yanzu dai su waye zasu fara zuwa". Da sauri yace. "Khadijah da Amina ƙanwar Deddena Shatun, dama nayi mgnar da mijinta tun kwanaki to yanzu kuwa zan kirashi in sanar mishi anfa yi haihuwar ba mamaki gobe ko jibi su taho da safe zuwa gidan naka. Kaga da azahar sai su wuce masarautar da iyalin taka". Cikin gamsuwa Bappa yace eh hakan yayi. Yana katse kiran yayiwa Ummey bayani cikin gamsuwa tace. "Eh hakan yayi amman in Amina da Khadijah sun zo suje da Junainah ni sai bayan suna sai inje ko". Cikin gamsuwa yace. "Eh amman bayan suna da kwana ɗaya zakije in anyi suna kamar yau sai gebe kije ko". "Eh hakanma yayi". Tace cikin jin daɗi.
Shi kuwa Abboi a ya juyo ya kalli Dedde ya mata bayani. Sosai ta shiga cikin farin ciki a take ta miƙe ta nufi ɗakinta. Nan ta gaya Khadijah ta fara shiri Addanta ta haifu.
A masarautar Joɗa kuwa gaba ɗaya a daren labarin haihuwar Shatu ya karaɗe ko ina lungu da saƙo na masarautar.
Riskar wannan lbrin a kumnunwan Magauta yayi masifar tada musu hankali. Hajia Mama kuwa a dare cikin masifar tashin hankali ta wuce gidan bokanta.
Tana shiga tace. "Meyasa ne wai ku bokaye babu wasu maƙaryata a duniya sama daku, ya mukayi da kai da shaiɗanun makaranka maƙaryata. Shin ba cewa sukayi randa aka haifi yarinyar a wurin yanke cibiya zasu kashe min itaba". Cikin wani irin masifeffen razana ta daka tsalle tayi baya, sabida wani irin razanenne tsawa da bokan ya daka mata da ƙarfi. Cikin ɗaga amo yace. "Ke tafi daga can waya isa ya cutar da wanda Allah ya kare, dama ai na gaya miki babu abinda da zai samu cikin nan sai al'khairi. Amma da yake ke tinkiyace ƙidahuma kikazo kina min ihu a kai in zaki iya cutar da itan ke kije ki gwada mana". Cikin tashin hankali gano tayi asarar kuɗaɗenta a banza ta juya ta fita tana cewa. "Tabbas sai na kashe yar nan babu shakka bazata rayuba". Shi dai boka tsaki yaja. Ita kuma ta juyo ta dawo hankali a masifar tashe.
Shi kuwa Sheykh yana gama mgn da Bappa DSS ɗinsu ya kira. Cikin hikima da iya sarrafa harshe yace. "Sir naga wasu yaran da akayi nasarar kamasu da laifin kinnafin ko?". Jim kaɗan yayi tare da cewa. "Eh yaran fulani masu kiwo ko?". Da sauri yace. "Eh su waɗanda akasa suka amsa laifin da ba nasuba akan dole." Da sauri yace. "A a kamar yaya laifin da ba nasuba?". Cikin nutsawa ya gyara zamanshi kana yayi mishi duk bayanin da Sulaiman yayi mishi ɗazu. Cike da al'hini irin yanayin nan na ba'a mugun sarki sai mugun bafade ogan nashi yace. "Kai Malam ni bansan da zancen nanba, kawai nasan kotu ta bada beli babu batun a nemo wasu a basu laifin da ba nasuba". Da sauri Sheykh yace. "Ni nasan baka saniba dan na yarda da adalci ka yanzu me abun yi a kan lamarin yaran nan?". Cikin takaicin yadda wasu jami'an tsaron kasar nan suka zama azzalumai yace. "Dole zamu kai zancen kotu ayi bayani a gaban al'ƙali a kawo Sulaiman ya bada shaida, da kuma sauran ma zauna magarƙamar". Cikin wani irin jin daɗi sanin muddin mgnar taje kotu. Komai zai iya dai-dai yace. "To ka taimaka musu a meda case ɗin yaran zuwa kotu". Cikin nitsuwa yace. "Toh ba matsala". Suna gama wayar kuwa ya fara bincikan lmrin a afaren ya turawa wani al'ƙali rahoton.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya miƙe ya nufi ɗakin Shatu.