Garkuwa complete novel - Chapter 72
Garkuwa complete novel Chapter 72: Garkuwa complete novel Chapter 72. Tuni tayi wani baccin gajiya. Ummi na kwance gefenta. A hankali yace. "Ummi bakuyi…
4,424 words
Tuni tayi wani baccin gajiya. Ummi na kwance gefenta. A hankali yace. "Ummi bakuyi bacci bako?". Gyara konciyarta tayi tare da cewa. "To ita dai mai jego tayi sai nida ƙawar tawane muke hira". Murmushi yayi kana ya matso. Miƙawa mishi yar tayi, amsa yayi, ya zauna a bakin gado gefen Shatu. Addu'o'in ya farayi yana tofa mata. Kana a hankali ya kalli Shatu data buɗe ido a hankali tana kallonsu. fuskar yarinyar ya kalla yadda taketa wawure-wawuren hannunta. Cikin nitsuwa yace. "Ummi yunwa nefa ya hanata bacci". Ya ƙare mgnar yana kallon Shatu. Ita kuwa Ummi da sauri tace. "Yauwa tunda ta tashi ta bata maman ta tsotsa". Kai ya gyaɗa kana yasa hannunshi ya kamo na Shatu ta tashi zaune. Ɗaura mata yar yayi bisa cinyarta, kana yace. "Bata Baloon ɗin tasha". Cikin ɗan yamutsa fuska tace. "Daga yanzu?". Da sauri yace. "Eh". Ya ƙare mgnar yana tattaro rigarta yayi sama dashi, tare da ɗan ɗago kan Baby ya saita bakinta da nimple ɗin ya manna mata. Ai kuwa da ƙarfinta ta damƙi nimple ɗin. Wani irin zillo Shatu tai tare da yarfa hannun cikin sakin ƴar ƙara tace. "Wayyo Allah na Yah Sheykh zafi". Da sauri ya saki dariyar mugunta. Hakama Ummi dariyar suke mata. Ita kuwa cikin kunya ta ɗan sunkuyo tana kallon yadda ƴar taketa zuƙam nonon da har yanzu bai tsastsafo da ruwaba. Haka nan taji wani irin son yarinyar yana shiga ta. Tsawon 5 minute tana tsotsar bakin nimple ɗin ta, wanda saida yayi ja yayi tsami a hankali tace. "Zafi wlh zata cinye min nimple". Murmushi yayi tare da lakace hancinta kana ya janye kan yarinyar. Ya kwantar da ita, ai kuwa gajiya da tsotson yasa tayi bacci. Ita kuma Shatu meda breast ɗinta cikin riga tayi kana ta koma ta konta. Sunkuyowa yayi kansu yayi musu addu'a. Kana ya juya ya fita yana cewa Ummi. "Sai da safe". Allah ya bamu al'khairi tace. Amin yace yana fita.
Yana komawa ɗauki shi yayi shirin bacci kana ya kira Haroon da ibrahima sukayi hira sosai cikin farin cikin.
Daga nan ya kwanta.
Washe gari da safe. Gimbiya Saudatu ce zaune a falon Shatu. A hankali ta fito ruggume da yar a hannunta sunyi kyau sosai cikin shigar tasu. Especially Babyn da aka shiryata cikin wasu kayan sanyi masu taushi red color and white masu masifar kyau da taushi, tayi lib a ciki. A hankali ta kalli Shatu dake miƙo mata ƴar amsa tayi tare da cewa. "Masha Allah, ƴarinya kam kekkyawan sai dai Allah yasa kada ta gaji Rashin kunyar uwarta da ubanta". Sheykh dake shigowa ne yace. "Ai kuwa zata gada dan kyan ɗan ya gaji iyayensa". Cikin watsa mishi harara tace. "Kai matarka ta haihu ka girmama bazaka bar yiwa manya rashin kunya bane wai?". Da sauri ta juyo ta kalli Shatu dake cewa. "Toh ai kema baki bar rashin kunyarba bare mu". Cikin ta kaici tace. "To uwar fitsara ke kiji da jegon ma mana tukun". Murmushi tayi tare dasa hannun ta amshi babyn da take miƙo mata tare da cewa. "Allah ya raya". Karo na forko a rayuwar Sheykh da yaji Gimbiya Saudatu ta mishi addu'a ko mgn mai kyau. Cikin jin daɗi yace. "Amin ngd". Tsaki taja tare da watsa musu harara ta fita. Murmushi yayi mai sauti ƙana ya iso gareta. Ya ruggumeta ita da Babyn cikin raɗa yace. "Ana Uhubbuk ya habibi Da'iman". Murmushi tayi dan bata gane da ita yakeba, a zatonta da yar tasu yakeyi. Shi kuwa ganin bata gane bane sai ya share tare da cewa. "Ɗazu nazo kuna bacci". Kai ta gyaɗa tare da cewa. "Ummi ta gaya min". Da sauri ya janye jikinsa gareta, jin Muryar Mom Maman Imran wacce itace matar Abbansu ta uku. A daƙile ya amsa sallamar tata, sai ya kuma saki fuskarsa ganin harda Abbanshi da cingam ɗinsa amaryarsa kenan. Bayan su zauna ne Shatu ta miƙa musu ƴar ɗaya bayan ɗaya, cikin murmushin Mom tace. "Masha Allah, tana kama da kakarta". Amaryar Abban ta miƙawa amsa tayi tare da cewa. "Kekkyawar Baby Allah ya raya amaryar Habibullah". Da sauri Abba yace. "Uwar gida dai, ai kece amarya kam". Kauda fuska Sheykh yayi kamar baya wurin.
Haka dai sukayi musu Barka suka tafi.
Haka kuma mata da maza bayi da hadimai keta yiwa Sheykh Barka a duk sanda ya gilma cikin masarautar.
Rafi'a kuwa tazo wanda zuwanta yasa Shatu ƙara sakewa sosai gashi Khadija tace mata gobe zasuzo da sassafe, dan jirgin dare zasu biyo da yauma zasu isota.
Alhamdulillah kuma bayan sallan isha'i suka iso. Salmanu ne ya ɗauke su ya kaisu Rugar Bani, shima zai kwana can saida safe zai taho dasu.
A masarautar Joɗa kuwa abin mamaki kowa yazo barka yaga baby ammma. Banda Hajia Mama, Mami Matar Affan kuwa kusan nan Part ɗin Shatu ta wuni dan suna masifar ɗasawa.
Washe gari da safe, Aunty Amina ƙanwar Dedde da Khadijah ƙanwar Shatu da Inna Amarya da Junainah suka shirya zuwa masarautar Joɗa. Inda Ummey ta haɗawa Shatu man shanu, kwan zabbi yajin daddawa dana borkono da zuma da madarar shanu, ko wanne mai yawa suka taho mata dashi.
Ƙarfe tara da rabi dai-dai Salmanu yayi parking a asalin babban gate ɗin masarautar Joɗa. A hankali ya juyo ya kalli Khadija dake gefensa yace. "Kira ta ki gaya mata kun iso a turo masu shiga daku". To tace kana ta kira Shatu. Tana ɗagawa tace. "Assalamu alaikum ƴar uwa rabin jiki kun isone?". Da sauri tace. "Eh mun iso muna babban gate ki turo azo a shigo damu naga masu jajayen rigunar nan sai kallonmu suke tayi". Da sauri tace. "Toh ba matsala bari yanzu Jamil ko Jalal zaizo". Tana faɗin haka ta katse kiran, tana ruggume da Babyn ta nufo falon. Tana fitowa ta hangosu can bisa. Dinning table suna yin breakfast harda Yah Jafar. Da sauri Ummi ta nufi inda take tare da cewa. "Yah dai Shatu kina son wani abune?". Gyara riƙon da tayiwa Babyn tayi tare da cewa. "Eh Ummi dama su Junainah ne suka zo, suna can babban gate to inaso a shigo da sune". Da sauri Ummi tace to kana ta juyo tana ƙwalawa Sara dake kitchin kira. Da sauri ta fito tare da cewa. "Na'am". Cikin kula tace yauwa dan Allah jeki can bakin babban gate ki shigo da baƙi". Da sauri tace to kana ta fita.
Tana isa tace su shigo da motar har Salmanu yace a a sai kuma yace to sabida tuno akwai kaya. A hankali tayi gaba motar na binta a baya suna kutsa hancin motar cikin masarautar Joɗa.
Junainah ta sauƙe wani irin masifeffen ajiyan zuciya kamar dai irin ka dade kana neman abu baka samuba ka samu. Wani irin daɗi takeji na musamman yana ratsa mata jiki da zuciya. Haka nan taji tsikar jikinta yana tashi tsaye.
Har bakin Part ɗin su. Sukayi parking. A hankali suka fito.
Shi kuwa Salmanu kayan nasu ya fitar ya ajiye bisa barandar dake bakin ƙofar falon tare da cewa. "Toh ni zan juya in kin shiga Khadijah kiyi mata barka". Da sauri Khadijah tace to. Kana ta sunkuya ta ɗauki jarkan man Shanu Junainah kuwa galam ɗin zuma ita kuwa Sara ta ɗauki kwaryan ƙoyayen. Inna Amarya kuwa jarkan madarar shanu. Sara ce a gaba Junainah na biye da ita a baya sauran na biye dasu.
A can cikin falon kuwa dai-dai lokacin Sheykh ya fito Falon gefen Shatu ya zauna. Jalal kuwa tsaye yake gefensu yana kallon Babyn dake hannun Sheykh su Jamil Affan Yah Jafar kuwa suna Dinning area. Haka nan sukeji zuƙatansu na harbawa da ƙarfi da ƙarfi.
A hankali Sara ta buɗe ƙofar tare da turo kai tana mai sallama.
A hankali Junainah ta sako ƙafarta cikin falon tare da buɗe muryarta sama tace. "Assalamu alaikum Adda Shatu". Wani irin ratsa amon sautin muryar ta kunnuwansu Jalal Jamil Jafar Sheykh sukayi tare da juyowa da sauri suka fuskanci bakin ƙofar ɗakin. Dai-dai lokacin Junainah ta shigo cikin falon. Cike da mamaki Sheykh Jabeer, Yah Jafar, Jamil, suka zuba mata ido tare da haɗa baki wurin cewa. "....!
Littafin GARKUWA na kuɗine akwai Normal group 300, akwai Special Group 1k babbancinsu a wurin yawan posting ne ga ac no 0005388578 Jaiz Bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai kuyi screenshort na Debit Alert ɗin sai ki turo shaidar biyanki ta whatsApp 09097853276 ƴan Normal group in baki da halin biya ta ac zaki iya sayan katin mtn na ɗari uku kacal ki copy numbers ɗin ki turo min ta whatsApp 09097853276.
By *GARKUWAR FULANI*
Cikin zuba mata ido tare da mamaki muryarta da kamanninta suka haɗa baki wurin cewa. "Wa alaikassalam". Shatu kuwa da sauri ta miƙe tsaye tare da nufosu cikin farin cike take cewa. "Oyoyo Allah sarki My Junnu". Da gudu Junainah ta ƙara sa inda take ruggume juna sukayi suna dariya. Da sauri Shatu ta ɗan ɗago kanta ta kalli Khadija date cewa. "Wato ma Junainah kawai kika gani ko Adda Shatu shekara biyu baki ganniba ko ki kulani". Da sauri ta saki Junainah ta ruggume Khadijah tana dariya tare da cewa. "Oh Dija ƙorafi". Ita kuwa Junainah dariya tayi tare da cewa. "Oh su Adda Dija kishi akeyi dani". Cike da mamaki da kuma farin cikin ganin Junainah Ummi ta kalli Aunty Amina da Inna Amarya tare da cewa. "Lalako jaɓɓama mon poi". Da sauri Shatu ta ture Dija cikin tarin so ta ruggume Aunty Amina da Inna Amarya tare da cewa. "Aunty Amina Inna Amarya marabanku." Da sauri suka ɗan juyo jin Sheykh yana cewa. "Sannunku da zuwa". Cike da kunyar sirkai sukace yauwa. Kana sukabi bayan Ummi dake cewa. "Ku iso mu shiga ciki." To sukace kana sukabi bayanta itama Shatu tabi bayansu. Sara kuma ta kwashi kayan duk ta kaisu kitchin.
Ita kuwa Junainah jin muryar Sheykh ne yasa ta juyo da sauri. Ganinshi riƙe da jaririyar ne yasa ta juyo da sassarfa ta nufi inda yake tare da cewa. "Hamma Jabeer?". Tai mgnar tana zubawa Jalal da Jamil ido, da alamun so take taga wanda zai amsa a cikinsu ta gane waye shi. Cikin sauƙe wata iriyar nannauyan ajiyan zuciya yace. "Na'am Junainah". Da sauri ta ƙara so inda yake, tana isa ta ɗan sunkuyo tana kallon Babyn murmushi mai yalwa tayi tare da cewa. "Ina kwana Hamma". Yana mai kallon yantsun hannunta data miƙo mishi alamun ya bata Babyn yace. "Lfya lau Alhamdulillah Junainah ya Bappa". Da sauri tace. "Yana lfy yace in gaidaku duka, harda Yah Jafar Yah Jalal da Yah Jamil". Da sauri ta ɗan juyo jin Affan na cewa. "Banda ni kenan". Kai ta jujjuya tare da cewa. "A a harda kai mana". Sai kuma ta juyo tana kallon Sheykh tare da yin ƙasa da murya tace. "Hamma Jabeer me sunanshi". Murmushi yayi tare da yin ƙasa da murya kamar yadda tayi yace. "Affan". Cikin gyaɗa kai, ta ƙara matsowa zama tayi gabanshi tare da miƙa sawunta cikin zaƙuwa tace. "Hamma Jabeer bani ita mana". Da sauri yace. "Junainah zaki iya kuwa inafa tsoron kada ki kada ita". Da sauri tace. "Zan iya mana". To yace kana ya sunkuyo ya ɗaura mata yar bisa cinyarta, yasa hannunshi ya tallabe kan Babyn.
A hankali Jalal yayi wani irin rumtse idonshi da ƙarfi. Jamil kuwa cikin sanyi ya taso ya taho kusa da ita, matsawar da yayine yasa Yah Jafar hangota. Miƙewa yayi da sauri ya nufo tsakiyar falon.
Ido suka zuba mishi ganin yadda yazo ya tsuguna gaban Junainah da Babyn da Sheykh ɗin. Da sauri Junainah ta ɗago kanta ta kalleshi cikin zuba mishi ido cikin ido tace. "Ina kwana". Shiru yayi bai amsa ba, sai hannunshi da yasa kan sawunta yatsun ƙafarta ya ɗan kama tare da rumtse idonshi. Da sauri ta kuma cewa. "Ina kwana?". Shiru bai amsaba sai kuma ga hawaye na zubo mishi. Hakane yasa ta juyo da sauri ta kalli Sheykh cikin rauni ido cike da hawaye tace. "Hamma Jabeer baya mgn ne? Meyasa yake kuka." Ta ƙarashe mgnar hawaye na zubo mata. Da sauri Jalal ya tsuguna gabanta tabbas ta tuno mishi abu da yawa kam Mameynsu sabida masifar kamar da sukeyu. Haka nan yaji son yarinyar yana ratsa dukkan sasan jikinshi gaba ɗaya. So irin na ƴan uwataka so irin na wa da ƙanwa Cike da mamaki Sheykh yake kallon Jalal da yasa tafin hannunshi yana share mata hawayenta. Wanda ita kuma haka ya ƙara tunzura zubowar hawayen nata. Cikin rawan murya tace. "Hamma Jabeer meyasa yake kuka?". Cikin wani irin yanayi Jamil ya tsuguna shima ya zama sun zagayeta sun sata a tsakiya. Shi kuwa Sheykh a hankali yasa hannunshin bisa kanta cikin rauni yace. "Nima ban saniba Junainah wata ƙil yana tsoron kada ki kada Baby ne ko kuma muryarki ce tayi iri ɗaya da muryar Mamanshi". Cikin shessheƙan kukan da haka nan taji ya kubce mata tausayin mutumin ya rufeta cikin rauni tace. "A a bazan kada itaba, Ummey na ta koya min yadda ake riƙe yara ai lokacin da mukaje gidan Abboi da yarinyar Maman Idris to Ina Maman nashi". Sai kuma ta ɗan musukuta ta gyara zamanta tare da gyara riƙon yarinyar. Cikin sanyi Jamil yace. "Mamanshi bata nan". Cikin zubda hawaye tace. "Ina take?". Tai mgnar da alamun tausayawa. Sheykh ne ya ɗan sunkuyo ya kalli ƙwayar idonta a hankali yace. "Mugayanen magauta sun sabauta rayuwarta sun ɓadda ita". Kanta ta jingina jikin Jalal dake gefenta cikin sanyi da rauni tace. "Ayyah Allah ya isan mata, Allah zai saka mana". Sai ta kuma kalli Yah Jafar ɗin da tsananin kamanninta da Mameynsu ne da kamar murya ya sashi zubda hawaye a hankali tace. "Kayi haƙuri Yaya zamuyi ta mata addu'o'in, kuna Ummey na zata zama mamanku, kuna so ko?". Da sauri Sheykh ya gyaɗa mata kai ganin yadda ta ƙarashe mgnar da zuba musu ido". Affan kuwa gefen Sheykh ya zauna yana mai kallonsu cike da al'ajabin yanayin da suke ciki Especially Jalal da ba kula yara yakeyi ba.
Ummi kuwa a can cikin ɗakin Shatu, tayiwa su Aunty Amina iso. Bayan sun zauna ne, Sara data kai kaya kitchen ta kawo musu ruwan.
Kana ta fito ta koma Kitchen taci gaba da aikinta Ummi na biye da ita a baya. A falon ta tsaya tare da zubawa ikon Allah ido. Muryar Junainah dake iri ɗaya sak da muryar da bazasu taɓa mancewa da itaba a duniya.
Ita kuwa Junainah a hankali ta kalli Ummi data iso gabansu. Tare da kallon yadda suke a hankali tace. "Uhm autar Mamey kawo ɗiyar taki in kaiwa su Inna Amarya ita". Da sauri tace. "Toh". Ta ƙare zancen tana miƙa mata ƴar.
Jalal kuwa ido ya zubawa Ummi. Sheykh kuwa juya kanshi yayi yana kallonta yana nazartan kalmarta, itama taga kamar kenan." Ya faɗi a ransa.
A fili kuwa murmushi suka ga Jafar yayi tare da miƙewa tsaye murya can ƙasa yace. "Autar Mamey nima haka idona ke sanarwa zuciyata Ummi". Da sauri suka kalleshi. To daga jiya zuwa yau dai sun saba da yayi mgn a fizge sai dai bai kuma ƙarayin wata duk mgnar sa za'ayi mishi. Yana faɗin haka shi kuma ya juya ya tafi.
Da sauri Jalal yabi bayanshi. Affan kuwa a hankali ya miƙe ya fita ya nufi falon Hajia Mama.
Jamil kuwa sashin Gimbiya Aminatu ya nufa. Shi kuwa Sheykh a hankali ya yunƙura ya gyara zamanshi ya koma bisa kujera, kana ya kalli Junainah dake tsaye tana gyara tarhan da tayiwa ɗan kwalin hijab din jikinta. Cikin yin ƙasa da murya yace. "Wannan ɗayar itace Ummey?". Da sauri ta matso kusa dashi a hankali tace. "A a Ummeynmu tana gida bata zoba. Wannan Aunty Amina ce ƙanwar Dedde, ɗayar kuma Inna Amarya ɗayar kuma Adda Khadija ƙanwar Adda Shatu ne. Na fita kyau ko?". Murmushi yayi tare da cewa. "Sosai ma kuwa, ke mai zubin larabawa". Wani irin murmushi tayi tare da cewa. "Yessss my Hamma ka iya gayan gsky". Sai kuma ta juya ta nufi falon Shatu tana cewa. "Bari inje inga Adda na da kyau". Da ido ya rakata.
Jamil kuwa yana shiga ya gayawa Gimbiya Aminatu cewa wasu baƙi sunzo wurin Shatu da wata yarinya mai kama da Mameynsu. Tofa wannan al'amari yasa Gimbiya Aminatu sanarwa Lamiɗo haka, da kanshi yace taje tai musu sannu da zuwa.
Yah Jafar kuwa yana shiga, falon shi ya samu Juwairiyya na tsaye. A hankali yaja hannunta suka wuce bedroom ɗinsa. Haka nan yaita maimaita kiran sunanta tana amsawa.
Shi kuwa Jalal juyawa yayi ya fita.
Affan kuwa a hankali ya kalli Hajia Mama cikin sanyi yace. "Mama ƴan uwan Shatu sun zo, sai kinga wata yarinya mai kama da Mameynmu, ko muryarsu iri ɗaya, anjima kije ki ganta". Cikin tsuke fuska tace. "Toh uban marasa zuciya, kullum kai ke cemin in jene". Da sauri ya kuma juyo ya kalli Rumaisa yayarshi. Dake jan dogon tsaki tare da cewa. "Shi bai san damuwar mutane ba, da kishin uwarsa, kana da rashin kunyar da yarinyar nan kewa Mama kake wani cewa taje taga ƴan uwanta." Idonshi ya kuma juyowa kan Maman tasu jin tana cewa. "Barshi sakarai ni ko ƴar da aka haifanma banje na ganiba bare wata can baƙuwar ba hillatanar daji, mitssssss". Cikin sanyin jiki yace. "Uhumm". Daga nan bai kuma cewa komaiba, baisan komai kan makirci mahaifiyar tashi ba, iya saninsshi tana son su Yah Sheykh fiye da yadda take sonshi sai dai wasu lokutan yana zargin tana da wani manufa a kansu. A hankali ya miƙe ya fita ya nufi Part ɗinsa.
Ita kuwa Hajia Mama cikin fidda numfashi ta kalli Rumaisa tare da cewa. "Sai gobe zanje duba jaririyar, kuma zanje da garin batur, tabbas zan zuba matashi a baki. Tana haɗiyewa zai tsistsinka ƴaƴan hanjita ta mutu kowa ya futa, shegu masu yawan haihuwa". Cikin cin daɗin haka Rumaisa tace. "Dai-dai kenan".
Gimbiya Aminatu kuwa anayi sallan la'asar taje,. Tabbas itama tayi mmkin kamannin. Koda ta dawo ta sanarwa Lamiɗo da Abba da Gimbiya, cikin al'ajabi Lamiɗo yace. "Yarinyar zata kai shekara nawa?". Da sauri Gimbiya Aminatu tace. "To gsky bana ceba dan irin yaran nanne masu jiki ɗan cafal ba wawan girma ku ba ƙaramin ruwa da wuya ka iya ƙiyasce shekarunta kai tsaye". Wani irin dogon numfashi Abba ya sauƙe tare da cewa. "Shi Muhammad ɗin zai tambayi yayar tata". Galadima kuwa cikin nitsuwa yace. "Uhummm babu shakka akwai abinda ke shirin tabbata daga zantu kan Malam Musa, yace ƴa mace mai kama da ita zata fara zuwa kafin ita. Amman bai saniba ƴartace ko ba tataba, ya kuma ce mana a haihuwar matar Muhammad ne zai sanadin zuwanta. Tabbas bawai munyi imani da abubuwan daya faɗa bane. Wasu ma mun mancesu. Sai dai gashi bayan shekaru goma sha biyu abubuwan daya faɗa sun fara baiyana na aure ba fullatar daji. Sai kuma batun haihuwarta da zuwan yarinyar koda banga ƴarba inaji a jikina itace ƴarinyar dayake nufin". Cikin nitsuwa Abba ya gyara zamanshi a hankali yace. "Ni dai yanzu inga yarinya ce damuwa ta, inji shekarunta. Domin na sani tabbas kafin Aisha ta haɗu da ibtila'in juyewar halinta wlh tanada shigar juna biyu wanda ita kanta bata saniba, saida na gaya mata. dan lokacin baifi kwanaki ba. Kuma har bayan ta juye naci gaba da jin abubuwan da nakeji muddin tanada juna". Cikin rauni ya ƙarashe mgnar. Daga nan sukaci gaba da tattaunawa kan batun.
Washe gari yau kwanan Baby uku da zuwa duniya. Ƴan uwa da abokan arziƙi duk sun zo, kab Masarautar Joɗa hatta matar Galadima da take tsohuwa sosai tazo, sai Hajia Mama ce kaɗai bata zoba.
Zaune suke a falon Shatu. Lokacin suka dawo daga yiwa Inna Amarya rakiya dan Salmanu yazo ya ɗauke ta ya meda ita gida. Ya rage Khadijah Aunty Amina da Junainah. Zaune suke a falon Shatu, Ummi ce zaune gaban Shatu ta zuba mata abinci a plate ta bazashi yayi sanyi. Kana tana jujjuya zumar data saka mata cikin kunun tsamiyar data dama mata mai citta. Cikin sauƙe numfashi Aunty Amina tace. "Oh ikon Allah ko ina da al'adarsu mu ai mai jego in dai abinci yayi sanyi to bazata cishi ba". Murmushi Ummi tayi tare da cewa. "Uhum kinga mu kuma nan sai abincin yayi sanyi ƙalau ma kafin mai jego taci, tai wonka da ruwan sanyi, tasha mai sanyi taci mai sanyi kuma babu abinda ke damunsu". Hannu Shatu tasa ta amshi ɗan ƙwaryar da kunun yake ciki ludeyin dumar tasa ta ɗan ɗebi kunun ta kurɓa, ido ta ɗan lumshe dan tana jin daɗin shi a bakinta.
Ita kuwa Aunty Amina riƙon da tayiwa Babyn ta gyara tare da cewa. "Gari banban Allah ɗaya kenan".
Junainah ce ta miƙe tsaye alamun zata fita. Shatu ce ta ɗan kalleta tare da cewa. "Ina zakije Junnu?". Ba tare da ta juyo ba tace. "Zanje kitchen wurin Adda Khadijah da Sara in tayasu girki". Sai kuma tayi sauri ta ɗan ja da baya, ganin Sheykh da sauri tace. "Hamma Jabeer ina kwana". Murmushi ya ɗan yi tare da cewa. "Lfy lau Alhamdulillah". Sai kuma ya ɗan juya tare da cewa. "Yauwa Junainah jeki kira Adda Shatu kice tazo da Baby". To tace kana ta koma ciki shi kuma ya nufi ɗauki sa.
Bayan ta gayawa Shatu saƙon nashinne ta juya zata fita kuma tayi kiciɓis da Hajia Mama da hadimanta. Cikin zuba mata ido Hajia Mama ta ɗan kauda kai ta wuce. Ummi ce ta ɗan miƙe tare da cewa. "Sannu da zuwa". Cikin sakin fuska tace. "Yauwa Ummin Jabeer ina kishiyar tawa kishiya ban haushi". Ta ƙare mgnar tana zama bisa kujerar dake gefen Ummi ya zama suna fuskantar juna da Shatu. Cikin sakin fuska Aunty Amina tace. "Ina kwana?". "Lfy lau Alhamdulillah ya yar jikallena?". Hajia Mama ta faɗa. "Gata lfy lau". Aunty Amina ta faɗa tana yunƙurin tashi zata miƙa mata ƴar. Da sauri Shatu tace. "A a Aunty Amina kada ki bata ita dan Allah". Da sauri tace. "Sabida me?". Ajiye kwaryar hannunta tayi tare da cewa. "Haka kawai". Ta ƙare mgnar tana miƙo hannun ta amshi ƴar. Tare da jan dogon tsaki kana a hankali tace. "Aniyar kura tabi daji aniyar moɗa tabi randa, wannan dai nan gani nan bari da izinin ubangiji". Ta ƙare mgnar tana juyawa ta fita ta nufi falon Sheykh.
Hajia Mama kuwa gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi da masifar takaici da tsanar Shatu da abinda ta haifa dama wanda ya bada cikin dan sune gagararrunta.
Cikin takaici ta miƙe ta fita. Hadiman ta na biye da ita a baya.
Wani irin murmushi Ummi tayi tare da cewa. "Ɗan Adam kenan mugun icce kai dai kaga mutun baka san me accikin zuciya nai ba". Cikin mamaki Aunty Amina tace. "Ikon Allah kai wannan gida naku yana cike da sarƙaƙiya". Da sauri Ummi tace. "Sosai ma kuwa".
Har bedroom ta wuce. Zaune ta sameshi bisa bakin gado. Da sauri ya buɗa mata hannunshi, ba musu ta raɓa jikinshi. Ruggume ta yayi tare da sauƙe numfashi a hankali yace. "I miss you so much". Ƙamshin jikinshi ta shaƙa tare da cewa. "I miss U to". Gyara rungumar da yayi mata yayi, tare da amsar Baby cikin manna mata kiss a goshi yace. "Baki tambayi sunan ta ba". A hankali tace. "Kayi mata huɗuba ne?". Da sauri yace. "Tuntini ma tun randa nace miki ko kinada sunan da kike son saka mats, kikace insa sunan Mamey duk da ban gaya miki wacece itaba". A hankali ta manna kanta da ƙirjinshi tare da cewa. "Toh ai nasan itace mafi ƙololuwar soyuwa da daraja a wurinmu, tunda koda ban santaba baka gaya min komai a kanta ba. Na fahimci tafi ko wacce mace daraja a garemu, tunda in kaji wuya ita kake kira kana raki in kaji daɗi ma ita kake fara tunowa. Nasan tanada matsayi na musamman a rayuwarmu". Murmushi yayi tare da cewa. "Aish sarkin falsafa, to nasa mata sunan Mamey kamar yadda kikace". A hankali tace. "Me sunan?". Murmushi mai sanyi yayi tare da yin ƙasa da murya yace. "Aisha shine sunan Mamey na, kuma sunan matata sunan ƴata ta fari kuma". Cikin murmushi tace. "Masha Allah sunan Ummey nama Aisha ne". Ruggume ta yayi tare da cewa. "Iye zuriyar Aysha's kenan". Da sauri ya zaro ƙaramar wayarshi. Murmushi yayi ganin 3bala'i. Da sauri ya ɗan janye jikinshi gareta. Amsa kiran yayi tare da karawa a kunne tare da cewa. "Uhumm ya akayi ne". Cikin huci Hajia Mama tace. "Jahan wlh zan kashe mutanen nan baki ɗaya in huta". Da sauri ya miƙa ya nufi cikin Bathroom yana juyowa yana kallon Shatu cikin yin ƙasa da murya yace. "Dame zaki kashesu?".
A hankali Shatu ta bishi da ido, fahimtar kamar yana buƙatar sirrine baison tasan abunda zai tattauna a wayar ne yasa ta miƙe a hankali ta nufi side ɗin ta. Bayan ta gyarawa jaririyar kwanciya bisa gadonshi.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya sauƙe ajiyan zuciya jin Hajia Mama na cewa. "Wallahi nayiwa kaina al'ƙawarin tabbas ranar suna zan kashe ƴarinyar nan cikin buzun al'ada da za'a naɗeta, tabbas da ita zan fara kafin inbi ta kan uwar da uban su ƙannen dama a tafin hannuna suke, yayan kuwa majanunine". Cikin danne tashin hankalinsa yace. "To wai meya hatsalaki hakane?." A fusace tace. "Yanzu na baro ƙofar Sheykh wlh naje da garin batur a hannuna zan turawa ƴar shi a baki, wannan fitsarerriyar ƙauyen matar tasa ido cikin ido tace. Kar a bani ƴarta ita bata so. A gabana ta amshi ƴar ta fita inaga ɗakin shegen ustazun ta tafi". Cikin danne dariyarsa yace. "To bari yanzu ina cikin uzuri anjima zanzo muyi mgnar dake". To tace kana ta katse kiran".
Shi kuwa Sheykh a hankali ya fito. Ganin bata ɗakin ne ya sashi sauƙe ajiyan zuciya. Yana murmushin wautar Hajia Mama Ya fito falo.
Dai-dai lokacin kuma Junainah data shigo da tray'n breakfast ɗinshi ta ajiye bisa Dinning table. Shiru tayi tana jin kukan tsuntsayen dake cikin Garden ɗin, a hankali ta juyo ta sauƙa kan steps ɗin. Ganin tsaye ne yana kallonta yasa ta ɗan matsoshi. A hankali tace. "Hamma Jabeer wannan kukan tsuntsayen fa a ina suke?". "Cikin Garden suke nan baya". Da sauri tace. "Ayyah dan Allah ta ina hanyar zuwa wurin yake". Cikin tsareta da ido yace. "Zaki jene?". Kai ta gyaɗa alamar eh. "Toh me zakiyi a can?". Ya kuma tambayarta "Zanje inga tsuntsayen ne ina son kukansu daɗin ji". Kai ya jinjina tare da cewa. "Gacan hanyar muje in rakaki". Yayi mgnar yana yin gaba tana biye dashi a baya. Dai-dai lokacin kuma Lamiɗo da Galadima da Abbanshi suna ciki can bakin ruwan waya sukeyi da Jadda.