Kenza eBookz

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 1

Complete book: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy)Chapter 1 of 21FantasyBy Mamy Kabir (aunty Maamy)

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 1

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 1: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 1. [12/7, 10:30 AM] Saratu Kabir: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

3,362 words

[12/7, 10:30 AM] Saratu Kabir: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

GIDAN AIKINAπŸ’πŸ’

Bismillahir rahmanir rahim.....

Page. 1/2

Barka da hutawa Hajiya na kammala kyaran dakin, Wata yar matashiyace da bazata gaza shekaru 18/19 yrs ba durgushe gaban wata hamshaqiyar mata fara mai dan jiki ,take fadar hakan kanta adurqushe ,cikin ladabi da takatsantsan take maganar,

Saida matar nan ta gama yatsine yatsinen ta kafin ta bude baki tace, Kin tabbata kin gyara komai yayi yadda nakeso ?dan kinsan my son baison qazanta ,ta fadatana kallon yarinyar cikin isa da izza,

Gyara tsugunnonta yarinyar tayi cikin ladabi da sanyin murya tace" Eh hajiya na gyara kamar yadda kika bani umarni,ta fada ta mai fatan Allah ya sa shikenan ta kammala aikin da zatayi,ta samu taje tayi wanka tayi salla sannan ta dan huta yau tun safe bata zauna ba tana ta bauta ,aiki suke sata ba tausayi data gama wannann za ace tayi wannan ,

Kusan minti 5,kafin hajiyar ta dago takalleta cikin ,wulaqanci take kallon nata, Saikije ki samu kiyi wankaki cire wadan nan shegun kayan naki masu wari ,dan bana fatan mai son ya ganki ahaka ,sai yaqi zama agidanma baki daya,

Wani sanyine ya ratsa zuciyarta ,koba komai zata dan huta ,ita inama zata fito ya ganta bare har ce bazai zauna agidan ba saboda ita, Na gode hajiya ta fada tana tashi ta nufi dakin dake,mazaunin nata,

Tana ratsawa babban falon gidan zata wuce ta hangi yan matan gidan su uku azaune afalon,suna ta shewa da alama suna hirar dawowar yayan nasune ,wucewa tazoyi ,taji ance " Keee!!!

Saida ta dan tsorata dan kiran bana wasa akayi mata ba ,juyowa tayi ahankali,tana kallon mai kiran nata ,ba kowa bace face aisha ,dama tasan za arina ,dan itace ke mata irin wannan kiran ,

Zuwa tayi ta tsaya adan nesa da ita tace gani anty,

Kallonta aisha tayi cikin wulaqanci da qasqanci tace ,ke wai mekike nufine damu agidan nan ? Bamu isa kizo wucewa ki ganmu ki gaidamu ba saidai ki wuce kamar kinga sa oinki ,ta qarasa tana harararta,

Sunkuyar da kai khadija tayi cikin girmamawa tace ,kiyi haquri anty inaso inje inyi sallane shiyasa ,

Dan uwarki dukanazakiyi da kika tsaya akaina,sqi wari kike,ina magana kina mayar min saboda raini,

Durqusawa khadija tayi ahankali ,kiyi haquri,ta fada bayan ta durqusa ,

Harararta tayi sannan tace ,ki wuce daki zakiga kayan dana cire ki wanke minsu da hannunki bana son wankin machine kina jina kuma ki tabbatar kin shanyasu arana sun bushe ki goge ki kawomin ,ta qarasa tana wani hura hanci,

Dago kai khadija tayi ta kalli aisha ,cikin yanayi na buqatar taimako,tace toh anty zan wanke amma dan Allah zanje nayi sallah ,ta fada ahankali,

Ban yarda ba ki faramin aikina kafin kije kiyi sallar ,ta fada agadarance,

Kiyi haquri anty amma tabbas saina fara gaisawa da mahaliccina kafin nayi aikinki,ta fada Tana nufar dakinta ,tana ji aisha na ta ihu wai tayi mata rashin kunya , Wllh yau saina ci uban yarinyar nan ni zatayiwa rashin mutunci shegiya yar talakawa ,

Duk abinnan wadan nan yan matan guda biyu sunazaune basu ko tanka musu ci gaba masukayi da hiransu, Kallonsu aisha tayi cikin masifa,yanzu ku kunajin abinda yarinyar nan tayi min amma ko ajikinku,hirama kuke ?

Daya dagacikin yan matan ce ta dago kai tana kallon aisha kafin tace me kikeso muyi mikine aitafiki gaskiya tunda sallah zatayi ,

Dama nasani aike maryam sam baki damu da damuwar dan uwanki ba,wato ko ajikin ki abinda matsiyaciyar yarinyar nan tayimin,ta fada cikin bacin rai ,

Ummice tace kiyi haquri sis idan ta idar saikiyi mata hukunci kawai ama kina bata ranki akan wannan banzar ,

Shiru aisha tayi tanahuci wllh natsani yarinyar nan bana sonta shegiya mai iyawa kamar yar wasu ,

Khadija kuwa saida tayi sallarta cikin nutsuwa ta kai kukanta gurin mahalicci kafin ta fito danyin aikin da aishanta sanyata,

Har lokacin suna falon ba wacce tayi yunqurin tashi dan tayi sallah acikinsu,

Wucewa tayi dan dauko kayan da aishan ta sanyata aikin ,tana tafiya kawai taji an fizgo hijabin jikinta an dawo da ita baya ,kafin ta gama saisaita nutsuwarta ,aishata sharara mata mari har biyu,dafe kuncinta tayi da sauri dan marin ya shigeta , Kllon aishan take cikin mamaki,mari ?menayi miki anty kika mareni,ta fada cikin muryar kuka,

An mareki dan ubanki kozaki rama ne yar talakawa marar gata sai jiji da kai kamar yar sarki , Wllh daga yau idan na sake sanyaki aiki kikamin musu saina tattakaki agidan nan ,

Cikin kuka khadija tace" Duk abinda kikasani nayi miki muddin ya shiga hurumin ubangijina wllh saina fara aikin Allah kafin nayi naki ,kuma ki sani da talaka da mai kudi duk Allah neyayi su ,tana fadin haka ta wuce dakin nasu,ta bar aishatana ta zage zage kamar yar maguzawa.

Ummi ce tazo ta kama hannun aisha dan allah sister kizo muje mu shirya ,kinsan jirgin su yaya 4 zai sauka yanzu kuma muna neman 3,amma kin zauna kina bata ranki abanza,

Haka dai haka suka wuce zuwa dakin ummin anan suka shirya cikin wani haddaden less pink colour dinkin riga fitet ya matse sosai ,sai wani dan siririn mayafi dasuka yafa ,allqh ya kyauta ya shiryi yayan musulmi baki daya,

Suna fitowa itama hajiyar ta sauqo cikin wani ubansun less kai dagani kasan naira tayi kuka,sai qamshi take zubawa ,kai yarana kunyi kyau sosai ta fada cikin murmushi , Dariya sukayi suma mommy kema kinyi kyau sosai wllh ,n

suna cikin zancen saiga abba ya sauqo shima cikin shadda mai matuqar kyau sai kyalli take,

Kamilin dattijo mai fuskar kamaa da yanayi na haquri,

Abba barka da fitowa suka fada dukansu yawwa yace musu ,kana suka dunguma wajen motoci ,yan matan suka hau daya ,abba da mommy suka hau daya , Motoci ne na gani afada hadaddu masu kyau da tsada, Motar security daya na binsu abaya,sai airport.

Allah sarki khadija haka ta fara wanke kayan ba komai bane face inner wears din aisha ,haka ta wanke ta shanya ta zauna tana jiran su bushe, nan takebarci ya dauketa ,tsabar gajiya ,ga yunwa ko abinci bata ciba tana ta bauta,

Qarfe 4:00pm dot jirgi yayi landing,fasinjoji suka fara sauqowa ,daya bayan daya ,cikin izza da isa wani matashi mi kamada dan indiya yake sauqowa ahankali cikin wani farin cikin ganinshi aqasar tashi ta haihuwa, Masha Allah gayen ya hadu ba qarya ,saidai kallo daya zakayi masa kasan baida mutuncin idan ka taboshi,fuskarsa ba yabo ba fallasa,yake sauqowa,

Da gudu qannan nasa suka ruga zuwa gareshi oyoyo yaya oyoyo yaya,tsayawa yayi ya bude musu hannu suka qaraso ya rungumesu dukansu yana mai jin farin ciki ,dariya kawai suke suna murnar ganin yayan nasu ,dagosu yayi yace hi ladies kun girma ,yafada cikin wata hosky voice mai sanyi,

Dariya sukayi dukansu ,aisha sai wani fari take tana maqale masa,

Qarasawa sukayi gurin iyayen nasu dake ta murnar ganin dan dasu suma rungimesu yayi daya bayan daya , I miss you mommy, I miss you abba,ya fada yana lunshe ido Miss you too son ,mommy ta fada tana shafa kansa ,

Mota suka shishshiga dan tafiya gida inyaso aqarasa murnar acan .....

Toh kubiyoni dan jin wace wainar za'a toya agidan , Taku anty mammy πŸ™

mrs babiπŸ’˜

Share and comment Please. [12/7, 10:30 AM] Saratu Kabir: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

GIDAN AIKINAπŸ’πŸ’

Na mammy kabeer (anty mammy)

Page. 3/4

Kai tsaye gida suka nufa cikin tsala tsalan motocinsu ,sosai aka gyara gidan harda sabon fenti,ga abinci kala kala akan danning,gidan sai qamshi yake ta ko ina ,kai hatta ma aikatan gidan sunyi ado,duk na tarbar babban dan gidan ne,

Suna shigowa gidan yan aiki sai daga masu hannu suke alamar sannu da zuwa ,amma basu ko sami arziqin kallo ba sai wani yatsina yake kamar ya ga kashi,

Haka suka sauqa zuwa babban falo wanda yasha gyara qamshi ta ko ina ke tashi,zamasu kayi anata marhabin da lale,

Gaba daya qannan nasa sun zagayeshi sai surutu suke masa ,cikin sangarta ,

Aisha kuwa sai wani shigewa jikinsa take tana kwarkwasa ,da fari da ido, Abba ne yace ku kam bazaku barshi ya dan huta ba duk kun cikashi da surutu,

Kai kameel ka bar yaran nan kazo kaci abinci ka huta kaji ,cewar abba,

Mommy ce ta kalli yaran kunga maza ku tashi muje muci abinci kunga yayyan naku ya dauko gajiya ga yunwa,

Maryam ce qaramar cikinsu ,tadan kalli yayan nasu ,tana murmushi,wllh yaya kamar baza amaka hausa ka amsaba gaba daya ka koma ba indiye,

Dariya yayi tare da jan hancinta ,kema kina nan kamar yar fillonki ,ya fada yana dan dariya,

Turo baki tayi ni wllh yaya banaso. Ana cemin yar fillon nan ta fada tana bubbuga qafa ,dariya sukayi gaba dayansu har abba,yace aikuwa dole akiraki yar fillo tunda ke din yar fillo ce,

Mommy ce ta dan kalli mijin nata sannan tace tubda yarinya bata so sai adena fada mata ai meye hadin ta da filanin yanzu,

Murmushi abba yayi ya girgiza kansa ,ku tashi maza yace duka zamasukayi akan qaton dainning din aisha ce tayi serving nasu cikin rawar kai ta hadawa kameel abincinsa,tana mai murmushi,

Shikam kallonta kawai yake ,yana dan murmushin shima,

Bayan sun kammala cin abincin ne kuma ya nufi bangarensa dan ya watsa ruwa ya dan huta,aikuwa aisha ta bi bayansa ,ya bude dakin kenan ya ganta ,kallonta yayi lpy ishaa ya fada yana tsareta da idanunsa ,

Dan daburcewa tayi ,ummm dama zan tambayeka ne ko kana buqatar wani abu,

Kallonta yayi kadan kafin ya girgiza kanshi bana buqatar komai barvi zanyi ,bana son hayaniya kuma ya fada yana nufar cikin dakin gado,

Danmurmushi tayi kafin tace azuciyarta karka damu nan da wasu lokuta qalilan nice zan rinqa hada maka ruwan wankan ma ,ta fada tana barin dakin,

Sosai ya yaba da tsarin dakin nashi ko ina fes sai qamshi ke tashi,ta ko ina ba datti ko daya ,gaskiya dakin ya burgeshi,

Wanka ya shiga yayi wanda saida ya bata kusan awa guda awanka kadai kafin ya fito ya dan shafa loshion ya fesa turaruka ajikinsa kafin ya fada kan gado sai barci dan ya gaji sosai da sosai,

Khadeeja kuwa hayaniyar suce ta tasheta daga barci ta kwashe kayan data wanke tabi ta qofar kitchen ta shige dakinta ,alwala tayi tayi sallar la'asar ta dan zauna tana tunanin rayuwa ,shikenan shi talaka baida wani gata ,kullum cikin bauta yake,ayita wulaqantashi ,Allah ka karemana imaninmu da mutuncinmu ,tana nan zaune yunwa takeji sosai duk da ita tayi girkin bata sami zarafin ciba tana ta faman bauta,kwanciya tayi tana jiran ajima idan taji sun bar falon saitaje tagyara ,

Can ku tdan leqo taga bakowa afalon dan haka ta fito ta gyara gurin ta goge,sannan ta shiga kitchen ta wanke kwanikan dasuka bata ,ta zubo abincin itama ta koma dakin ta tana ci,

Kee yar qauye ,kina inane ,taji ana kiranta da sauri ta tashi ta fito zuwa falon da hijabinta kamar dai kullum ,aisha ce zaune daga ita sai wani shegen wando pencil,da wata riga ta dan sauqa mazaunan ta kadan ,kan nn yasha qarin gashi ,sai wani yatsina take ,

Zuwa khadeeja tayi ta tsugunna agaban aisha ,anty gani,

Kina jina da shine dan isa da iko kikayi min shiru saboda ga sa arki na magana ko?ta fada cikin wulaqanci,

Kiyi haquri anty dama ina cin abincine shine naji kiranki,ta fada kanta aqasa,

Eh mana ansami na banza ana ci dole kikasa jin kirana ,banza yar matsiyata gadon yunwa ,

Dago da kai khadeeja tayi cikin bacin rai,amma ta danne zuciyarta , Kiyi haquri anty amma dan allah duk abinda zakiyimin ki daina sanyo iyayena domin iyaye ba abin wasa bane ,

Kan bala'i ni kikewa gargadi dan kaza kazan ubanki shegiya mayya mai kwalakwalan idanu,wllh saina ci uwarki yau din nan ta fada tana hankade khadeeja ,

Sosai Khadeeja ta bugu da centre table din falon, Cikin kuka ,me nayi miki anty daga fadar gaskiya shine zaki tunkudeni ,kiyi haquri,ta fada tana kuka,

Kai menene wai nake tajin hayaniya tunda na tunkaro falon nan ,cewar mommy dake sauqowa daga bangaren abba,

Wllh mommy gara akori yarinyar nan domin wllh bata da mutunci waini take yiwa gargadi ,ta fada tana nuna kanta,

Ke khadeeja banason irin wannan abun fa banso ana neman takurawa yarana ,dan haka idan kina ganin bazaki iyaba sai insallameki asamo wata ,ina dalili zaki rinqa bata mata rai ,ta fada cikin fada fada,

dan allah hajiya kiyi haquri wllh bazan sake ba na tuba karki koreni dan Allah ta fada cikin kuka ,

Tashi kiban waje amma idan na sake kamaki da wani laifin saikin bar gidan nan dan naga alama ku talakawa baku iya cin kwan makauniya ba,

Tashi khadeeja tayi ta koma daki tana ta kuka ,ya Allah ka kawomin mafita arayuwata ,wandan nan mutanen sam basu san darajar dan adam ba kowa bashi da buri illa ya wulaqantani agidan nan , Kuka tasha sosai kafin ta tashi ta nufi kitchen dan doramusu girkin dare,

Taliya ta dafa jallof da busashshen kifi,sai farfesun qoda ,sannan ta hada musu lemon kwakwa,

Bayan ta gama jeresune ta koma dakin ta tayi wanka sannan tayi sallah tana zaune har aka kira ishsha tayi sallar ta ta dauko alqur ani tayi karatu sanan ta kwanta,

Shikuwa kameel sai gabdamagrib ya farka ,wanka ya qarayi ya shirya cikin wani bakin wando pencil da riga milk colour ya feshe jikinsa da turare ,sanann ya fito falon lokacin ma anyi ishsha ,kuma ko sallar magrib din baiyiba ,

Kowa yana zaune afalon shi kadai ake jira,abbane kawai baya wajen ,

Hi mom yace yana zama kusa da ita yadan dora kanshi akafadarta,

Son ka tashi sannu, Kai ya gyada mata yana wani yamutsa fuska ,

yaya sannu da tashi ina tsarabarmu ,maryam ta fada cikin zumudi ,

Dan murmushi yayi kai merry kin cika takura ,let me have some time with my mom ,mana,ya fada yana lumshe ido ,

Wllh mukam yaya ka bamu tsarabarmu kawai cewar ummi kenan tana dan buga qafa,

Ok go to my room ,zakigan wani black trolly ki dauko ,ya fada yana kallonta

Yeeeeh suka dau ihun murna dukansu kamar wasu yara,suka nufi dakin nasa,

Mom i miss you sosai wllh ya fada yana bata side huge, Nima haka my son yau shekara biyar baka qasar nan kuma ko saudaya baka zo ganin gidaba,

Mommy ina ta son zuwa amma banson wannan qazantar ta qasar nan neshiyasa nayi zamana amma aike kinje is ok,ya fada yana dan tashi ,mommy am hungry ,

Kama hannunsa tayi kamar wani yaro ta zaunar dashi akan dainning din sannan ta zuba masa abincin ya fara ci ,

Wow mommy is delicious nasan ke kika dafadan wadan nan yaran ba abinda suka iya,

Noo my son bani na dafa ba wata house Maid dinace tayi girkin ,

What mommy ? House maid fa ? Why mommy meyasa zaki bawa maid tayi min girki,mommy kinsan bana son qazanta,ya fada kamar zaiyi kuka,

Kwantar da hankalinka son yarinyar mai tsabtace sosai ,dan ita ta gyara maka dakin kama ,

Really mommy,ya fada kamar wani yaro yana tabe fuska,

Sosai ma kuwa zaka ganta ma ai,

washe gari da asuba khadeeja ta tashi tayi salla sannan tayi azkar ,gari na dan wayewa ta fito tafara gayaran falo ta gana ta shiga kitchen ta dora girki,

Bayan ta kammala girkin ne ta jereshi adanning sannan ta shiga dakin mommy ta gayarshi ,yanzu tasan yaran basu tashi ba dan haka ta sauko dan itama tadan huta kafin su tashi ta gyara musu dakunan,

mommy ce ta fito daga dakin abba ,durgusawa tayi ta gaisheta cikin ladabi ,ko amsawa mommyn batayi ba tace maza kije ki gyara dakin son dan nasan idan ya shigo baa gyara ba sai ranshi ya baci,

Toh tace sannan ta nufi dakin nashi cikin dan sauri gudun kar tayi laifi,

Tana shiga ta fara gyarawa cikin lokaci qanqani ta gama gyarawa ko ina ya dau qamshi ,

Fito tazoyi ,tana bude qofar shi kuma yana sanyo kai saiji kake gummmm sun buga goshi........

Toh fa masu karatu mu hadu next page ,ku bini asannu zaku ilmantu sanan zaku nishadantu sosai acikin littafin nan,taku anty mammy πŸ™

Mrs babi πŸ’˜

comment and share please. [12/7, 10:30 AM] Saratu Kabir: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

GIDAN AIKINAπŸ’πŸ’

Na mammy kabeer (anty mammy)

Page. 5/6

Jikake gummm"sun gwara goshi, da sauri kowa yaja baya yana shafa goshinsa dan ba qaramin gware sukayi ba,

Wash Allah wannan wane mahaukacin ne zai fasa min goshi ,cewar kameel yana shafa goshinsa,

Khadeeja kam ko magana ta kasa sai kwalla daya cika mata ido, wllh zafi gurin yake mata sosai,

Dagowa kameel yayi dan gani wanda yake qoqarin fasa masa goshi,wani zabura yayi gefa can kamar yaga dodo, What ! Ya fada da mugun qarfi , Who the hell are you,? Waye ke ? Me kikeyi anan , Ya fada yana muzurai dan shi har ga Allah ma gani yake kamar bata da hankali ,jibi wani qaton abu data rufe jikinta dashi , Uban me kikemin adaki ,ya daka mata tsawar da sida taji hanjin cikinta ya murda,

Atsorace ta dago dara daran idanunta ta sauke akan kyakykyawar fuskarshi,gabanta ne yayi wata irin muguwar bugawa da sauri ta dafe qirjinta, Haqiqa ganin kameel azahiri ya nunka ganinsa ahoto sau ba adadi,domin hoto yana rage masa kyau ,mutum kamar aljani,masha allah ,ta fada aranta tana kallonsa quri,

Ke mayya daina kallona dan uwarki , Answer my question what are diong in my room,ya qara daka mata tsawa,

Gaba daya khadeeja ta rikice ,tama kasa magana sai rawa jikinta yake ,kwarjininsa gaba daya ya cika dakin , Cikin rawar murya ,tace" Dan Allah ka....kakk...yi..hahhq......qurii, Shine kadai abinda ta iya fada ,zuciyarta na wani irin bugawa non stop,

Kallonta yayi ganin yadda jikinta gaba daya rawa yake sai ajiyar zuciya take kamar wacce tayi tsere,

I said who are,u? Ya qara buga mata tsawa, Khadeeja fa gaba daya ta shiga tsaka mai wuya ,kawai saita sanya kuka dan Allah kayi haquri hajiya ce tace inzo in gyara maka daki kafin ka dawo,ta fada cikin muryar kuka.

Mtssss ,banza qazama jibeki dan Allah ahakan kike min gyaran daki ,kai amma mommy ta kwafsa wllh,ya fada yana buga hannunsa,gaba daya ma ji yayi bazai iya shiga dakin ba.

Fita yayi cikin bacin rai yana kiran mommy !mommy!! Kamar yana kiran sa arsa, Dasauri mommy tafito ta nufo inda yake son lpy kuwa? Menene?

Cikin bacin rai yace momm maiyasa zakimin hakane ,ya zaki tura min wannan mahaukaci yar har cikin daki ,just look at her mom,

Ya fada cikin tsawa, Sorry son yarinyar tana da tsafta shiyasa na zabeta ka kwantar da hankalinka ,zakaji dadin aikinta,cewar mommy cikin rarrashi,

Nooo,Mom Banasonta asakemin wata ,i dont like her at all,ya fada yana zare mata ido kamar ba mahaifiyarsa ba ,

Shikenan son kayi haquri bari yanzun nan zan sa akawomin wata ,just colldown ,ok,ta fada tana dafa kafadarshi,

Zamewa yayi ya nufi kujera ya zauna,yana huci ya ma za ace wannan abun itace zata rinqa kula da dakinsa ,jibeta fa kamar mahaukaciya ta sanya abu buyu buyu yana binta kamar tababbiya,

Khadeeja kuwa yana fita tayi saurin jingina da bango tana kuka ,waisu yan gidan nan halinsune haka ,basu da aiki sai wulaqanta dan adam ,meye laifina dan inayi musu aiki sai suyita wulaqantani kamar baiwa,

Fitowa Tayi daga dakin nasa ta shigo ta corridor zuwa falo , Yana zaune sai huci yake yana yatsina,

Cikin tsoro da fargaba tazo zata wuce ,ya daka mata tsawa, heey you come ya fada yana mata kallon tsana,

Dan firgita tayi kafin ta juyo ahankali ta tako zuwa tsakiyar falon,

Stay there ya fada yana nuna mata inda take tsaye,karki qaraso gurina ki shafamin cuta,wayasani ma yanzu kome na kwasa dililin bugamin wannan qaton kan nakida kikayi,ya fada yana harararta,

Tsayawar tayi jikinta na rawa da sauri tadurgusa,kanta aqasa,

I hate you ,ya fada har cikin ransa kuma, Karki qara yarda ki hada hanya dani dan bana qaunar ganinki ,ko kadan ,banason ganin wanann shegen fuskan naki mai kama dana monkey ,and idan na qara ganin ki koda kusa da dakinane ko ,saina balla miki wannan slim ugly legs din naki ,bace min da gani ya fada cikin tsawa,

Readers Also Read