Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 2
Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 2: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 2. Da sauri khadeeja ta miqe ta nufi dakinta ,tana…
3,360 words
Da sauri khadeeja ta miqe ta nufi dakinta ,tana shiga ta fada kan katifa tana kuka sosai ,nima na tsaneka bana sonka ,bai san darajar dan adam ba , ta fada tana kuka sosai,
Ta jima tana kukanta kafin ta share hawayenta ,cikin kwantarwa da kanta hankali ,domin tasan wannan aikin shine gatanta,
wanka tayi ba ko shafa mai tasanya wasu kodaddun riga da zaninta ,ta canza hijabi ,har qasa , Wanke kayan data cire tayi ta shanya ,sannan ta fito dan gyara dakin yan matan gidan ,dakin aishata fara shiga dan tasan itace marar mutuncin yanzu saitayi mata laifi,
Tana shiga dakin ta fara cin karo da kaya atsakar dakin tattarewa ta farayi tana zubawa acikin kwandon wanki,gadon ta gyara ,ta kwashe kayan dakezube gaban sif ,ta gyara dakin ,aisha ta fito daga toilet daga ita sai wani dan qaramin towel, Tana ganin khadeeja ta galla mata harara ,ke yar rainin hankali sai yanzu kikaga damar zuwa ki gyaramin dakin ,isashshita fada tana wata girgiza ,
Kiyi haqiri anty hajiya ce ta sanyani aiki,ta fada kanta aqasa,
Tsaki tayi ta wuce gaban madubi ta fara kwalliya, Toilet din khadeeja ya shiga ta wanke sannan ta fito,anty na gama ba abinda za ayi miki,tatambaya cikin ladabi,
Saida ta gama shan qamshinta tukunna tace,dalla malama fita ki bani guri kin quramin ido ko kina baqin ciki da kyan fftar da nake dashine ,ta fada tana kllonta ta madubi,
Fita khadeeja tayi batace komai ba ,
Shegiyar yarinya tarinqa abu kamar wata yar masu kudi wllh na tsani yarinyar nan,da alama idan ta sami hutu zaayi kyau anan ,aisha ta fada tana hararar qofar,
Dakin ummita shiga ta gyara ,nan dai ko kulata ummi batayi ba dan ita bata fiye magana ba ma, Tana gamawa ta nufi dakin ,maryam nan magyaranta tayita fito maryam bata ma dakin ,
Kitchen ta koma ta dora musu coffee dan tasan suna nemansa ,
Ganin lokacin dora abincin rana baiyiba yasata fito zuwa garden ,ta zauna aqasan bishiyar mangoro ,tana tunanin rayuwa ,
Kamar daga sama ta hango kameel yana nufo gurin da take dan akwai fararen kujeru na hutawa agurin ,da sauri tashige qasan teburin kujerun ta buya gabanta na dukan tara tara,
Qarasowa yayi ya zauna tare da dauko kwalin sigari ya kunna ya fara sha ba tare da ya kula da mutum aqasan gurin ba .
Warin sigarinne ya fara damun khadeeja dake qasa aboye ,sam bata qaunar warin taba ko kadan ,shikuwa shan kayarsa yakehankali kwance
Tarine ya kubcewa khadeeja ta fara yinsa da qarfi ,
Atsorace kameel ya miqe daga kankujerun yayi gefe guda tare da cillar da sigarin hannunsa,dan ya tsorata sosai ,
Nashiga uku shine abinda khadeeja ke fada aranta ,
Waye anan ya fada cikin bacin rai , Shiru khadeeja tayi cikin fargaba,
Komawaye ya fito tun kafin raina ya gamabaci ya fada afusace,
Fitowa khadeeja tayi cikin rawar jiki da faduwar gaba ,
What!!! Ya fada ganin wacce ta fito... Toh masu karatu mu tara a next page taku har kullum anty mammy🙏
mrs babi💘
Comment and share please. [12/7, 10:30 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
DIDAN AIKINA🍒🍒
Na mammy kabeer (anty mammy)
Page. 7/8
What!! You again ,ya fada yana nuna khadeeja kamar yaga dodo, Ohh sheet , I hate ,ke wacece me yakawo cikin gidan nan tell me waya aikoki gareni ? Meyasa kike shiga rayuwata daga dawowan kin fara samin baqin ciki,bana son ganin wannan fuskan naki ,i hate you for the first time i saw you,ya fada cikin fada sosai ,
Rawa kawai jikin khadeja keyi ,tsoron mutumin nan take,me yasa take cin karo dashine koda yaushe ,ya allah save me ,ta fada aranta, Kayi haquri dan Allah,ta fada ahankali muryarta ma rawa take ji takekamar zuciyarta zata fasa qirjinta dan bugu,
Shut up!! Ya daka mata tsawa wannan shine last warning dazanyi miki karki qara hada hanya dani ,qazama irinki kucaka, jaga zaki rinqa hada hanya dani ,bakisan waye kameel ba ko ? Karki bari na nuna miki asalina ,stupid ,ya fada yana barin gurin cikin sauri,
Dafe qirji khadeeja tayi cikin qunan rai da baqin cikin maganganun daya yaba mata ,in sha Allah zata yi qoqarin kaucewa wulaqancinsa ,dan ta fahimci yama fi aisha iya walaqanta dan adam,
Share hawayenta tayi tare da barim wurin kai tsaye kitchen ta nufa dan dora girki,
Tanayi tana share hawaye ,dan wulaqancin yan gidan nan yana damunta,bayan ta kammala ne ta shirya su akan dainning table ,ta dibi nata ta komadaki ,saida akayi sallar azahar kafin suka hallara dan cin abincin ,duk suna zaune amma kowa yana ganin asarar da wahalar ya zubawa kanshi abincin,
Ke yar aiki !!! Aka kwalla mata kira cikin wulaqanci ,
Tana cikin cin abincin taji wannan kiran ,da sauri ta tashi ta fito zuwa falon , Naam anty gani , Ta fada cikin girmamawa, Wannan abincin da kika ajiye uban waye zai zuba ,aisha ta fada cikin gadara,
Kiyi haquri anty ta fada tare da fara zuba musu abincin ,mommy ce ta fito ita da dan lelennata sai wani yatsina fuska yake ,
Zama sukayi batare da ya kula da khadeeja agurin ba ,yanzu haka zancenta yake wa mommy shikam ya tsani yarinyar baya son ganinta acikin gidan . Tace yayi haquri ,zata samo mai kula da gyaran dakinsa kafin ayi bikinsu da aisha,dan itace matardamommynsa tayi masa yar qanwarta ce ,kuma babanta shahararren mai kudine.
Ta gama zubaw kowa ta koma wajen hajiya ta zuba mata ,sannan ta dauki flate ta zubawa kameel,ta tsiyaya lemo tare da ajiyewa dan wani irin faduwa da gabanta keyi,ta rasa dalilin daya duk lokacin data kusanceshi takejin gabanta na mugun faduwa ,har rawa jikinta yakeyi, Garin saurin ta gama tabar gurin ne bisa tsautsayiashe bata ajiye lemon adaidai ba kawai kofin ya sulmiyo sai ajikin kameel dake sanye dafarar shadda ,lemon kuwa ya bata masa jiki tundaga cinyarsa har qafa.
Wata irin zabura yayi tare da jefar da wayar hannunsa mai shegen kyau da tsada ji kake fass gilas din wayar ya fashe, Dago kansa yayi dan ganin wane dan nemawa kai balainne yayi masa wannan aika aikar,
Carab idonsu ya sarqe acikin na juna ,khadeeja sai zare ido take kamar tayiwa sarki qarya,jikinta kuwa ba inda baya rawa ,tsabar rudewa batasan sanda ta miqa hannu ta fara goge masa rigarsa ba,
zaro ido yayi cikin mugun bacin ran dayafi na farko,ya dage iya qarfinsa ya hankadeta ,jikinsa har gyarma yake tsabar masifa bai haqura da hakan dayayi mata ba ya dauko jarkar lemon mai shegen sanyi ya tuttule mata shi ajikinta ya jefa mata robar afuskarta ,i hate you !!! Ya fada da qarfi tare da barin falon cikin sauri,
Sosai khadeeja ta bugu ahannunta dan akanshi ta fada,wani irin zugi da radadi hanun yake mata ga sanyin lemon daya watsa mata ,kuka ta fashe dashi cikin tsantsar tausayin kanta ,
Ke wace irin shashasha ce ne khadeeja,meyasa yanzu kike nema ki zamo irin yaran nan masu rawar kai ,kinsan daya na lallabashi ya barki kici gaba da aiki agidan nan kuwa? Ki kula domin kina gab da rasa aikinki,mommy ta fada tana bin bayan kameel .
Aishace tazo kusa da khadeeja ,batayi wata wata ba ta dauketa da mari ,harke wacece dazaki zubawa kameel lemo ajikinsa,yar matsiyata jikar talauci ,mai qashin tsiya,ahaka zaki qare cikin bauta da qasqanci sakarya kawai,ta fada tana bangaje khadeeja,tare da wucewa,
Sauran ma haka sukayi mata nasu kalan wulaqancin suka kauce,
Tashi khadeeja tayi ta nufi dakinta ,tare da dauko wani tsohon hoto tana kallo cikin kuka , Ummana kin tafi kin barni cikin fararin rayuwa ,umma nasan dakina raye tabbas bazaki barni cikin wadan nan mutanen da basu san darajata ba umma,ta fada tana rungume hotom ajikinta cikin kuka sosai take cewa allah ya jiqanki umma na Allah gafarta miki tare da abbana , Kuka kam khadeeja tashashi awannan ranar kamar ba gobe ,amma taci alwashin daga gau ta daina yarda da cin kashin yan gidan nan dole ta dau mataki .....
Sai mun hade next pagetaku anty mammy 🙏
mrs babi💘
Share and comment. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
GIDAN AIKINA🍒🍒
Na mammy kabeer (anty mammy)
Page. 9/10
Dole in dau matakin kare kaina daga wannan wulaqancin danake fuskanta ,duk da nan aljannace akan inda na baro ,amma nasan qima da darajar kaina ,daga yau na daina yarda ana takani haka,ta fada kallon hannunta dayake mata zogi,
Kameel kuwa yana shiga dakin sa ya dauko sigari ya kunna tsuqa biyu yayi mata ya gama da ita ,kafin ya cire kayan jikinsa ya zauna yana sake kunna wata,itama zuqa biyu ya gama da ita ya yar,ya kunna ta uku kenan mommy ta shigo dakin ,ganinta baisa ya fasa shan abarsa ba sai huci yake idonsa sunyi jazur dasu ,
Zama tayi kusa dashi ,som kayi haquri ka kwantar da hankalinka ,kaji ,nasan wannan abun is mistake dan yarinyar bata da rawar kai har haka,ta qarasa ahankali cikin sigar rarrashi,
Yi yayi kamar baisan me take cewa ba ko kallinta baiyi ba ya jefa abin sigarinsa acikin wani dan kwano na tangaran ya qara zaro wata ,kunnawa yayi yana ta vawa cikinsa hayaqi ,
Mommy nakallonsa batayi yunqurin hanasa ba sam,sai kallonsa datake ita burinta ya sauqo daga fushin dayakeyi,
Son bari in dafa maka wani abincin da kaina kaji,ta fada tana dafa kafadarsa,
Momm please leave me alone,ya fada yana dauke hannunta daga kafadarsa, Son dan Allah ka daina damun kanka zanyi mat....
Momm!!! Ya daka mata tsawa kamar sa'arsa ,ki barni na huta kinji dan Allah banson hayaniya ,please ya fada yana hada hannayensa guri daya ,alamar neman alfarma,
Ok !ok!! Son na tashi inka huce zan dawo muyi magana kaji,ta fada tana barin dakin batare da ta tsawatar masa ko ta nuna bacin ranta akan shan sigarin dayake acikin gidaba ,matsayinta na uwa ,saima haquri take bashi kamar shine uwar itace dan ,Allah ya kyauta ya bamu ikon yiwa yaranmu tarbiyya ta gari.
Haka khadeeja ta zauna adkinta tsawon lokaci tana fama da qunci da damuwar abinda kameel da yan uwansa sukayi mata ,amma taci alwashi fita daga sabgarahi,in sha Allahu bazata qara yarda su hada hanya dashiba.
Can dai ta fito dan gyara musu falon ,gashi ahnnunta sai ciwo yake mata amma ahaka ta gyara ko ina ta sanya turaren wuta ta koma daki ta zauna.
Su aisha basa gidan sun tafi shopping dan haka ta sami sauqin yawan sa aiki,mommy kuma da kanta ta tafi gidan qawarta dan ta sama mata yar aikin dazata kula mata da son dinta mai tsafta,
Cikin sa'a kuwa ta samu yarinya ankawota neman aiki,dan haka tare suka taho da mai aikin,bayani tayi mata irin yadda tsarin kameel yake da abunda baya so ,dan haka tace zata kiyaye, Yarinyace bata wuce sa'ar khadeejan ba itama ,
Dakin kameel mommy ta koma dan gani halin dayake ciki baya dakin da alama ya fitane ,dan haka tacewa yar aikin tazo ta gyara masa dakin ,
Khadeeja kuwa saida akayi la'asar sannan ta fito ta gaida hajiya ,idonta yayi jajur tsabar kukan data sha,
Kije ki dora mana abincin dare tuwon shinkafa miyar danyen kubewa saikuma farfesun kifi da sobo,cewar Mommy ,
Toh kawai khadeeja tace tare da nufar kitchen din ta fara aikinta, Kafin magrib ta gama aikinta tsab ta gyara ko ina ta jera musu abincin ta dibi nata ta shiga daki tayi salla ta dau alqur ani ta fara karantawa ,
Sai magrib yaran gidan suka dawo ashe tare suka fita da kameel, zama sukayi afalon ba tunanin bari muyi sallah ,aa ina dagasu har uwar ba wanda yayi sallar magrib hirama suka kafa.
Saida aka kira ishsha sannan suka tashi ,nan ma ba sallar suka gabatar ba abinci suka fara ci sannan kowa ya nufi dakinsa,
Kameel yana shiga dakinsa ,tundaga falo ya fara ganin ba daidaiba ,domin gashinan ba'ayi mopping ba sannan ga tuqar sigarin dayasha baadaukeba ,kayan shi daya cire ma suna kan kujera,
Cikin dakin ya qarasa ,kan uban nan,shine abinda kameel ya fada yana riqe baki dan ganin gadonsa ahargitse gaba daya dakin ya hautsine ,
Da sauri cikin fushi ya nufo babban falon ,momm !! Ya fara mata kiran yan farauta, Mom kuwa har tayi sallah raka'a biyu,ta fatsar da suri ta sauko zuwa falon , Jin muryara dan lelen nata , Son meke faruwane ?ta tambayeshi adan rude, Kallonta yayi mommy kina son inkoma inda na fitone ,ya fada yana kallonta,
Da sauri ta matso kusa dashi ,haba son ina kuma zaka koma me akama ka anan din , Momm kuna son cuta ta kamani ne in mutu? Noo,son bama fatan hakan , Amma momm aka barmin dakina haka so dirty,why memakon inzoma in ganshi yadda na barshi sai wani qara bata minshi akayi,ya fada yana yatsina fuska,da sauri mommy ta nufi dakin nashi dan tunda adama ta gama gyaran bata je ta dubaba,
sosai mommy ma tayi mamakin haukar gyaran da adama tayi ,fitowa tayi ta dawo gurinsa inda yake zaune gasu aisha akusa dashi sunyi shiru dan idan yana wannan masifar kowa shiga taitayinsa yake,
Sorry son bari nasa yanzu ta qara gyara maka mommy ta fada tana kwallawa adama kira ,da gudu adama tazo gani hajiya ta fada tana sosa kai,
Tunda ta shigo kameel yake kallonta cikin gyama ,yanzu dama wannan ce tayi masa gyaran da hannunta ta tabamasa kan gado ,ina ya fada da qarfi tare da miqewa tsaye , Mommy kina nufi wannan abun shine mai gyaramin dakin ya fada yana nuna adama kamar yaga kashi,
Ita kuwa adama zuba masa ido tayi tana kallon halittar Allah kai amma wannan mutumi da kyau yake ,
Kee !!! Daina kallona shegiya mayya ,wllh mommy wannan idan ta qara minti biyar agidan. Zan iya mutuwa ya fada yana toshe hanci wai wari take,
Tsawa mommy ta daka mata jeki dauko kayanki ki koma can gidan hajiya hafsa ,ta fada tana harararta,
dagudu adama ta fita tana waigen kameel ,
Zama yayi yana maida numfashi,kai wannan wane irin bala'ine , Mom kisa wancan yarinyar ta kwashe bed shit da komai ta samin wani ,ya fada idonsa arufe,
Jin abunda yacene yasa aisha saurin tashi bari na gyara maka yayana,ta fada cikim salon jan hankali,
Kee banaso bake nace ba ko zaki canzamin magana ne?ya fada aza fafe,
Komawa aisha tayi ta zauna gwuiwa asace,
Kiran khadeeja mommy ta shiga yi Khadeeja!!! Khadeeja kuwa nacan kwance zazzabi ya rufeta saboda hannunta daya bugu gashi ba'a duba mata shiba,dan haka ya sauqar mata da zazzabi, Da sauri ta tashi jin muryar mommy na kiranta,
Fitowa tayi cikin tafiyarta ta nutsuwa ta tsugunna agaban mommy , Hajiya barka da dare gani,ta fada kanta asunkuye,
Maza kije ki gyara dakin son,kicire zanin gadon da pillow casa duk ki canza wasu wadan nan din kuma ki kawomin su nan,
Toh hajiya tace tare da tashi ta nufi dakin nasa bata ko kalli inda sukeba ,duk da wani irin bugu da qirjinta keyi,
Sosai khadeeja ta sha gyaran dakin saida ta canza komai ga uban zazzabin dake damunta,
Ta sanya turaren wuta dakin ya dau qamshi da sheqi,fitowa tayi zata bar falon ta ci karo da hoton kameel dake manne ajikin bango hoton yayi masifar kyau kamar me ,kawai cintar kanta tayi da zubawa hoton ido gabanta nawani mugun bugawa,
Shikuwa kameel ya manta cewar bata fito daga dakin nashiba dan haka ya nufi dakin dan wanka yake sonyi ya kwanta,
Yana bude qofar ya hangota gaban hotonsa ta tsura masa ido ,
Kee!!!ya daka mata tsawa,uban me kike kallo ? Gabanta ne ya buga da qarfi jin muryar kameel innalilahi ,wayyo Allah na yazanyi ta fada tana zare ido ,tare da juyowa ..........
Toh masu karatu yanzu aka fara sai kubiyoni dan jin yazata kaya ,takuce dai anty mammy 🙏
Mrs babi💘
share and comment please. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
GIDAN AIKINA🍒🍒
Na mammy kabeer (anty mammy)
Page. 11/12
Juyowa tayi tana zare ido qirjinta sai bugawa yake ,yanzu me zatace masa?meye dalilinta na zubawa hotonsa ido? Na shiga uku Allah ka fitar dani,
Uban me kike kallo ahotona mayya,ya fada cikin tsawa,yana kallon falon dan sai yanzu hankalinsa ya kwanta da dakin,ga qamshi dayake tashi ta ko ina,
Dama...dama. Ina sone ummm,zan gogene naga yayi qura ta qarasa da gyar tsabar bugun da qirjinta yake,
Cikin isa da izza ya qaraso cikin dakin ,kina son gogewa shine kika kafamin ido kina neman cinyeni?
Ko kina da wani damuwane da hoton ina ruwanki dashi,bana son yawan kallo dan daganin alama kedin mayya ce inkika kama mutum saikin cinyeshi ya fada yana balla mata harara,
Dago kanta tayi ta zuba idanunta cikin nasa ,wani irin rass! rass!! rass!!! Yaji gabansa ya fadi sakamakon haduwar idanunsu ,da sauri ya dauke kanda , Dena kallona malama karki cinyeni ya fada fuskarshi na kallon gefe ,
Itama dauke idonta tayi ,daga kallonsa,
Tare da nufar qofa zata fice,
Uban wa ya baki izinin tafiya,? Dan uwarki
Runtse idonta tayi cikin bacin rai ,shi bashi da abin zagi sai uwa da uba,dole ta taka masa burki dan wllh bazata dauki wannan cin kashin ba ya isheta haka,
Juyowa tayi tana kallon cikin kwayar idonsa duk da mugun bugun da qirjinta keyi ,haka ta daure ta bude baki tace,
Ya kamata kasan cewa iyayeba abin wulaqantawa ko zagi bane ,iyayena basu maka komai,nice nake aiki aqarqashinku ,dan haka duk wani wulaqanci da tozarci ya tsaya akaina ,bazan laminci zagarmin iyayena ba dan nasan daraja dakuma zafinsu,tana kaiwa nan tayi shiru,
Kan bala'i kee!! Ni kike fadawa wannan maganar ,kai tsaye ,kinsan dawa kike magana kuwa?anzagi iyayen naki ,nace anzagesu kiyi duk abinda zakiyi dan uwarki da uban ki shegiya mai kama da aljanu, ke har kin isa ki gayamin magana wata kucaka kwaila dake dueki in banda qaddara ke kin isa ko hanyar danabi kibita ,ya fada yana huci dan ransa ya baci baataba maida masa magana ba sai wannan jakar yar matsiyata.
Kanta na qasa ranta in yayi dubu ya gama baci ,
Cikin hawaye ta dago da kanta tana kallonsa ,yallabai kasani Allah da kansa yace mun karrama dan adam ,toh meyasa kai zaka rinqa wulaqanta mutane , Kasani iyaye abune mai daraja wanda baidasu yana kukan rashinsu ,sannan duk da na halak bazaiso awulaqanta masa iyaye ba dan haka mina ina daya daga cikinsu ,bazan iya lamutar cin zarafin iyayena ba ,ta fada tana ci gaba da tafiya , Taku daya biyu taji anwani riqo hannunta da mugun qarfi kuma wanda ta fadi akansa dazu ,runtse idonta tayi cikin azaba da radadi .
Shiruwa fizgota yayi ta dawo cikin falon ya murde hannun da qarfi,
Qara khadeeja ta sanya hawaye na zuba daga idonta ido aruntse ,tsabar azaba, Shikuwa kameel jikinsa har bari yake tsabar bacin rai ,ke din banza ke wacece dazaki maidamin da magana cikin gatsali ? Ko ubanki bai isa ba bareke ke duk kan zuriarkuma basu isa ba ni kameel na fi qarfinsu ,banza yar matsiyata ,shashasha ,marar makun kai ,dama saikun gagari iyayenku sannan suke kawoku gurin aikatau ,wawiya ni nafi qarfinki wllh ya fada yana qara murde mata hannu,
Kuka sosai khadeeja take abun yayi mata yawa ,wannan mutumin nema yake yasanya zuciyarta ta buga ,aduniya ba abinda ta tsana sama da kazagar mata iyaye, Kacikamin hannuna kana jimin ciwo ta fada cikin kuka ,qara murde hannun yayi cikin mugunta , Bazan sakiba ki gwata mana ya fada cikin bacin rai ,
Kuka sosai khadeeja taje amma kameel sam yaqi sakar mata hannu sai qara murdewa yake cikin mugunta,
Khaddeja muwa sai gumi takedan ba qaramar azaba take ji ahannun nata ba,
Saida yaga tana neman suma sannan ya hankadata ,ta qara faduwa akan hannun ,
wani wahalalle ihu ta saki tana riqe hannun tana cikin kuka ta miqe tana kallonsa ,tama kasa magana ,
Sai jan zuciya take, shikuwa yana tsaye yana kallonta cikin ko inkula ,kuma yasan cewa dole tayi targade dan da niyya yayi mata hakan, Ficemin adaki mayya kawai ,kuma wllh azaba yanzu kika farashanta agurina i hate u,ya fada da qarfi,
Juyawa khadeeja tayi cikin azaba ta bar dakin tana ,zuwa falon aisha ta tareta ,
Ke dan uwarki mekikeyi adakim kika dade haka ,shegiya mai kama da mayu,