Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 3
Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 3: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 3. Kallonta khadeeja tayi murya ashaqe tace uwarki…
3,290 words
Kallonta khadeeja tayi murya ashaqe tace uwarki nakeyi adakin shiyasa na dade ,tayi wucewarta dakinta hannunta naci gaba da mata azaba,
Kuturun kare ,ni kike zagi ? Lallai yau xakici uwar ubanki yarinyar nan ni zaki zaga ,ta fada tana nufar dakin khadeeja da sauri saidai ta makaro dan khadeeja tuni ta rufe dakin da key ,kwafa tayi zaki fito yarinya zamu hadu wllh saina ci ubanki naga sai wani shigewa yaya kike shegiya mayya,
Khadeeja kuka ta kusan kwana taayi aranan nan idonta yayi jajur ga hannu sai dada aunewa yake ta kasa barci sam sai kuka take wayyo hannuna wayyo umma na ,ya allah ka taimakeni ka fitar dani daga wannan qangin rayuwar,
kamel kuwa tana fita yabita da harara na tsani yarinyar nan for no reasing i just hate her ,ya fada yana nufar dakinsa can ciki sosai yaji dadin gyaran da khadeeja tayiwa dakin wanka yaje yayi zuciyarsa fess dan ya wulaqanta khadeeja kuma yasan zata kiyayeshi yanzu tasan shi ba tsararta bane , kuma yayi alqawarin saiya wulaqanta rayuwarta sannan bazai bari ta bar gidan ba harsai ta zama abin tausayi ita da kanta saita tausayawa kanta .......
Toh fa masu karatu kunji qudirin kameel koya kenan ? kubiyo ni danjin ya zata kaya?
Taku anty mammy🙏
mrs babi💘
share and comment please. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
GlDAN AIKINA🍒🍒
Na mammy kabeer (anty mammy)
Page. 13/14
Haka dai kameel yayi ta shirya salon muguntar da zaiyita ganawa khadeeja ,saikace wata baiwarasa😏,
Washe gari da asuba khadeeja da gyar tayi alwala tayi sallah ,hannu yayi suntun gwanin tausayi haka tayi sallah jikinta kamar wuta dan zazzabi ,kwanciya tayi bayan ta idar da sallar ,ganin bazata iya kwanciyarba yasa ta tashi ta fito zuwa falo bakowa gidan shiru sai hasken kwai kamar rana ,dan kullum abba idan zai fita masallaci yana kunna kwan falon duka,
Wucewa tayi zuwa harabar gidan ta zauna abakin qofar ta jingina kanta da bango ,Allah ne kadai yasan azabar datake sha,tana zaune shiru sai hawaye take ,abba ya dawo daga masallaci, harya dan gota kuma saiyaga kamar mutum azaune
Dawowa yayi yace waye anan,ya fada yana kallon gurin da khadeeja take zaune , Dago kanta tayi cikin azaba tace alhaji barka da asuba nice khadeeja ,yar aiki,ta fada cikin dauriya da cije baki, Aff ,mai sunan mamana kece haka anan me kikeyi ,ya tambaya tana dan matsawa kusa da ita ,dan shi abbamutum ne mai karanci ga sanin ya kamata ,dan dai matar gidan tafi qarfin shine.
Abba bani da lpy hannuna ne yake min ciwo ta fada hawaye na gangarowa daga idonta , Subhanallah sannu sannu mai sunan mama ,mugani ya fada yana duba hannun dan gari yayi haske sosai ,
Yana ganin hannun yace kai wannan ai kamar targade kikayi ko ,garin yaya,ya fada cikin tausayawa,
Faduwa nayi ,ta bashi amsa,
Sannu bati akai ki gurin gyara ,ya fada yana kiran haru driver,da sauri haru ya qaraso kudi ya bashi yace maza yakai khadeeja aduba mata hannun,
Karbar kudin haru yayi khadeeja ta tashi suka fita,
Baqaramin wahala khadeeja tasha ba dan gurin yayi tsami sosai kuka kam khadeeja tasha dan saida matar mai gyaran ta riqeta ,dayake irin manyan matan nan ne,
Ana gamawa kuwa suka taho gida an dan daure hannun da wata igiya tadan rataya awuyanta dan harda tsagewar qashi,
Lokacin da suka dawo kusan qarfe10:00am na safe dan haka duk sun fito dan cin abinci sai dai wayam ba komai akan danning ,gashi kuma sun duba dakin nata ba kowa,suna tsaye cirko cirko ba wanda yayi tunanin shiga kitchen din dan samar musu abinda zasuci kawai baiwarsu suke jira,
Kameel yana zaune akan kujera sai wani huci yake yama kwafa wllh ahiyasa ya tsani yarinyar nan ,jibi yadda ta bar mutane da yunwa ta tafi yawonta.
Shigowa khadeeja tayi da hannu alanqaye awuya ,ganinsu ba qaramin fadar mata da gaba yayi ba ,dan wllh sai yanzu ta tuno batayi girkibama ,amma tasan intayi wa hajiya bayani zata fahimceta tunda harkace ta jinya,
Shigowa tayi ahankali take takawa duk sun zubo mata ido cikin tuhuma, Daga ina kike? Hajiya ta tambayeta,cikin ko inkula,qarasowa tayi ta durqusa agaban hajiyan ,tace Hajiya daga gurin gyara nake ,ta fada kanta aqasa,
Wakika tambaya dazaki fita?, Lokacin duk kuna barci shiyasa kuma jiya kwana nayi da zazzabi hannun yayi tsami ta fada ahankali,
Wllh mommy ba wani nan taje yawon iskancinta dai ta bar mutane da yunwa ,aisha ta fada tana hararar khadeeja,
Dago kai khadeeja tayi ta kalli aisha bata ce komai ba ta mayar da kanta tana rarrashin zuciyarta ,
Dakike kallona koxakiyimim wani abunne idan ba yawon bin mazaba ina kikaje da safen nan wama ya sani ko tun jiya bata gidan dama naji motsi jiya kuma wllh mommy ita na gani ta fice,ta qarasa maganar da nuna ita mai gaskiyace,
Kameel ne ya miqe tsaye ya qaraso kusa da khadeeja yana mata kallom qasqanci yace dama me kuke so agurin irin wadan nan yaran ? Wadan da iyayensu suka kasa daukar dawainiyarsu suka turosu bauta ,ni dama na dade da sanin wannan yarinyar yar barikice kuma qasqantacciya marar kamun kai , Ya fada yana kallonta awulaqance ,
Tashi tsaye khaddeja tayi tana kallonsu daya bayan daya ,sannan ta kalli mommy tace hajiya banda lpy naje gurin gyara sannan hajiya dan Allah kiyimin tsakani da yaranki ,ina musu biyayya kamar yadda ya dace amma kullum burinsu su wulaqantani ,dan Allah hajiya ki rabamu dasu ,sannan ni ba baiwa bace, neman halak dina nake ,ta qarasa hawaye na bin kuncinta ,
Ke kahdeeja ,bana son zancen banza yaran nawa kike cewa in rabaki dasu ? Toh ubanme zakimin agidan bakisan zamansu kikeyi ba ,dan kiyi musu bauta na daukeki aiki kuma nake biyanki duk wata ,idan kinga bazaki iyaba toh gahanya nan ,mommy ta qarasa tana mata kallon wulaganci,
Maryam ce tace mommy ki barta kawai dan naga hannun nata ya kunbura ,ta fada da yanayin dan tausayi,itakam ummi batace komai ba kallonsu kawai take ,dan ita dama bata cika magana ba,
Baza'a bartan ba sallamammiya ,uban waye zaiyi girkin ?ko ke zaki dafa mana abincin ,cewar aisha tana hararar maryam,
Anty aisha kina gani fa hnnunta ya kunbura dan Allah ta yaya zatayi wani girkiyanzu ,ta fada tana turo baki,
Rufemin baki anan maryam kona tattakaki ,waye zaiji tausayin nata ,yarinyar da ke qoqarin kashemu da yunwa,dame meye amfaninta? Tayi mana bauta shine kawai ,itadin tamkar baiwarmuce dan haka dole tayi mana abinda mukeso ,cewar kameel yana zarewa khadeeja ido , Runtse ido khadeeja tayi da qarfi cikin qunar zuciya da bacin rai ji take ahalin yanzu ba abinda bazata iyayi ba saidai su koreta ,ta gwammace ta koma inda ta fito ,idan an azabtar da ita acan tasan yan uwantane,
Kallon kameel tayi ido cikin ido ,duk da mugun faduwar da gabanta keyi hakan bai dakushe mata gwarin gwuiwarta ba ,shima suna hada ido yaji gabansa yayi wata muguwar faduwa ,shegiya mayya dana hada ido da ita sai gabana ya fadi,ya fada yana kauda idonsa ,
Bude baki khadeeja tayi cikin dauriya ta fara magana ,
Kasani niba baiwa bace,sannan kuma ni yar gidan mutumci ce ,iyayena sun bani tarbiyyar danake alfahari da ita ,ina yin aikine agidanku badan komai ba saidan inrufawa kaina da iyayena asiri ,ka guji duniya da cin mutuncin iyayen wasu domin kaima adaraja naka, Tana kaiwa nan tayi shiru tare da kallon aisha dan tayi alqawarin saita amayar musu da dafin da suka cusa mata aranta ,
Ke kuma aisha ,ina mai baki shawara ki guji duniya sannan ki guji cin zarafin dan adam domin darajace dashi ,ke macece idan kika ci gabada hakan abin mazai miki kyauba ,rayuwarki qalilance,sannan wataran zakiyiwa wanda bazai toroleting abinda kikayi mishiba ,dan haka zaibi duk hanyar dayake ganin zaibi dan ya qulaqantaki ,
Ni da kike gani ba baquwar zafi bace ,amma kin takurawa rayuwata why aisha what have i done to you ta fada cikin hawaye sosai ,baki tausayina baki tunanin nima ba yinkaina bane nazamo yar aiki ? Kiyi tunanin idan kena amatsayin danake ciki ya zakiyi,ya zakiji aranki, For God sake ki sararawa rayuwa am tired ,am tired for all this thing ta fada tana fashewa da kuka ,
gaba dayansu kallonta suke ,kowa mamaki yake dama tana magana haka? Lallai kaga mutum kawai domin baka san abinda ke kanshiba ,
Tafi kameel ya faracikin izza yake tafawa ,good lallai sai yau nasan yan aiki suna da dama dazasu tara masu gida suna tuhumarsu ,ya dakata da tafin ya kalli mommy datayi shiru tana kallon khadeejan kamar hoto, Momm did you here ko ? Wannan yarinyar watarana saita danne daya daga cikinku ta yanka domin da gani tana baqin cikin kasancewarku cikin jindadi ,ya fada yana girgiza kai ,sannan ya juyo yana kallon khadeeja ,
Dan uwarki da ubanki ,ki sani ke ba komai bace bace baiwa kuma dolekiyi mana bauta ,and you know what, yau ko karyewa hannunki yayi gida biyu saikin yi mana girki domin ke baiwar mice ya fada yana qureta da ido,
Dariya aisha tayi cikin jin dadin yadda yayan nata ke wuqanta khadeeja yake nuna mata ita ba kowa bace,
Juyawa lhadeeja tayi ta nufi dakinta dan abin nasu kam taga bashida niyar qarewa ,ke gidan ubanwa zaki ,aisha ta daka mata tsawa , Gidan ubanki ,khadeeja ta fada afusace,
😳😳gaba daya zare ido sukayi cikin tsantsar mamaki Khadeeja kuwa juyawa tayi ta ci gaba da tafiya ,kawai taji an janyo hijabinta ta baya ,jikake ,keeeett,ya yage abinka da yasha ruwa dama ,
Kameel kuwa bai tsaya ba saida ya kai hijabin har qasa,ya yaga tare da fincikewa daga jikinta ,garin janne dan kwalin kanta ya fadi gasa,
Ai gaba daya daskarewa sukayi ganin wani shegen baqin gashi mai tsawo kamar na indiya ya wani zubo har gadon bayanta ,
Ga wani hadadden jiki mai kyan diri da qira ,masha Allah Shine abinda maryam ta fada, Gaba daya mamaki ya gama rufesu har wanda ya yaga hijabin wato kameel,wannan wane irin qirane mai kyau da daukar hankali haka ,dama haka yarinyar nan take?
Khdeeja kuwa cikin rudu da mugun bacin ran bude mata jiki da kameel yayi ta juyo afusace ,batayi wata wata ba ta daukeshi da wani mugun marin da saida dakin ya amsa .......
Toh fa masu karatu khadeeja ta tsokano bomb ,baruwana nikam
Sai mun hade next page taku har kullum anty mammy,🙏
mrs babi 💘
share and comment please. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
GIDAN AIKINA🍒🍒
Na mammy kabeer (anty mammy)
Page. 15/16
Batayi wata wata ba ta dauke kameel da wani mugun marin da saida falon ya amsa,cikin tsan tsar bacin rai take kallonsa tana huci kamar mesa,
Mommy,aisha ,ummi,maryam gaba daya bude baki sukayi suna mai zaro ido waje ,cikin dunbin mamaki da al'ajabi ,tab lallai yarinyar nan ta tabowa kanta bala'i yau.
Kameel kuwa kallonta yake cikin shock ,da kuma rashin sanin madafa ,yana dafe da kuncinsa dayasha mari, Mari ,mari ni wannan yarinyar ta mara ?abinda tunda yake arayuwarsa baisan ya zafinsa yake ba danshi ya tabbata ba wanda ya taba marinsa sai dai shi ya mara ,amma yau shine wannan yarinyar ta mara agaban qannan sa ,agaban mahaifiyarsa , Abinda bai taba koda mafarkin faruwarsa ba ,lallai kin tabowa kanki abinda yafi qarfinki,ya fada azuciyarsa,
Mommy ce ta matso ta dauke khadeeja da lafiyayyen mari har guda biyu ,amma tsabar bacin rai khadeeja ko motsi batayi ba,idonta na kan kameel ,tana masa wani irin kallo,tunda take arayuwarta ba wanda ya tana cin mutuncinta irin haka saishi,
Ke yar matsiyata yar talakawa ,harkinyi kwarin dazaki mararmin da agabana ,lallai yau dole ki bar gidan nan shegiya tsinannniya marar mutunci mommy ta fAda cikin bacin rai,
Kallonta khadeeja tayi cikin hawaye tace , Hajiya ko baki fadi hakan ba toh dole zan bar gidan nan domin nan ba gidan mutunci bane ,sam gidan bai kamaceniba ,bazan ci gaba da zama agidan da ake ketawa mace mutunci agaban mace tayi shiru ba ,bazan zauna gidan wadanda kansu kadai suka saniba ,basu damu da damuwar wani ba ,kisani hajiya kun cutar dani agidan nan kuma Allah baya barci zai sakamin,ta danyi shiru kafin ta juya da kallonta kan kameel wanda ya riga ya zama spechless,tunda yasha mari ,
Kai kuma kasani bazan taba yafe maka cin mutuncin dakayimin ba zanci gabada gayawa Allah ya sakamin ,bana fatan sake koda hada yanya ne dakai domin kai azzalumine ,maci amanar Allah,kana da qannai da uwa mace ,amma bakasan darajar mata ba kasani yadda kayi haka za'ayi maka,tana kaiwa nan ta juya da hannunta ariqe ta shige dakin dayake amazaunin nata ada ,kayanta ta hada tana kuka ,duk wani bu datasan agidan ta samu toh anan ta ajiye musu kayansu ,nata kawai ta dauka ta fito sanye da wani hijabin ,
Har yanzu suna falon saidai yanzu kameel azaune yake mommy nata shafa bayansa ,dan wani rin huci yake idonsa yayi jajur dashi jijiyoyin kansa sunyi rudu rudu, Qannan sa suna zaune sunyi zuru ,cikin alhinin abinda yar aiki tayiwa yayan nasu,
Khadeeja fitowa tayi da jakar bakkonta wancce dama da ita tazo gidan ,suna kallonta ta ratsa su ta nufi qofar fita daga falon ,
Mommy yanzu haka zamu barta ta tafi taci bulus kenan,cewar aisha,
Shegiya mai bakin hali jekici uwarta ki balla daya hannunma, cewar mommy, Tashi aisha tayi da sauri zata bita ,, Kameel ya daka mata tsawa , Kee!!! Dakata ki barta kar wanda ya bita,
Amma yaya shikenan taci bul.....
Keeeeeh
Ya isa haka ,nace ya isa haka ke aka mara koni ,ya fada yana miqewa afusace, Da sauri aisha tayo baya ,kayi haquri yaya ta fada ahankali,
Ni ta mara kuma ni zan dauki mataki da kaina ,wllh saina wulaqanta rayuwar yarinyar nan ,saita gwammace bata sanni ba arayuwata bare har tayi gigin marina,saina dai daita rayuwarta ya fada yana dukan wani dan glass mai shgen kyau wanda wasu kyawawan kifi ke yawo acikinsa ai tuni glass din ya tarwatse ,kifayen suka zube suna ta wutsil wutsil ,baya suka ja gaba dayansu cikin tsoro,
Hakan bai asheshiba ya qara dukan wani flower vase na tangaran shima ya tarwatse ,
Zama yayi tare da riqe kansa da mugun qarfi ya kwallah wani qara ahhhhhhh, Ji yake kamar ya sheqa dan baqin ciki ,kamar shi kameel wata qasqantacciyar baiwa yar aiki ta mara ,, na tsaneki , I hate u ya fada da qarfi ,
Mommyce tayi na mijin qoqari ta tunkareshi tare da dafa kafadarshi ,son ka nutsu ka kwantar da hankalinka kaji.....
Leave me alone , I hate u mom kene kika kawota gidan nan harta yimin wanan abin ,i hate u for that ya fada yana zarewa mommy ido ,
Sosai mommy ta tsorata da yanayin dan nata ,dan haka addu'a ta fara tofa masa , Tashi yayi kamar guguwa ya nufi bangarensa yana shiga ya kulle qofar tareda dauko sigari ya kunna yana mata shan kaca zuqa daya yake ya yarda ita ,
Gani yayi hakan bai masa ba ya tashi ya dauko wata yar kwalba a fridge ya buda ta ya kwankwafe duka ya yarda kwalbar ,dubawa nayi naga ansa wine ajiki ,wato dai giyace ,
Zama yayi yaci gaba da busa hayaqinsa kala kala ,can gaba daya ya sauya ya wani horance sai wasu shirme yake ,na tsaneki shegiya ,bana sonki ,amma kina da kyan diri sosai ,da ina neman mata saina bata miki rayuwa ta yadda bazaki amfanuba ,ya fada cikin muryar yan maye yana lumshe ido.
Yayi ta haukarsa kafin barci yayi awon gaba dashi kansa aqasa qafafunsa akan gado.
Khadeeja kuwa tana fita daga gidan ta sami wani guri can nesa da gidan ta zauna taci kukanta ta qoshi yanzu yazan?
Mezance wa inna da baba ? Nasan dole zan fuskanci tashin hankali agurinsu idan sukaji na bar gidan aikina ,amma wllh gara duk abinda zasuyi min suyimin akan in qara koda minti biyune agarinnan ,
Haka ta kama hanya aqafa dan ko kudin adaidaita bata dashi ,ahaka ta je har tasha ,
Wani dan yuniyal ya tareta hajiya ina zaki ?
malam mafori ta bashi amsa, Yawwa dama mutum daya muke jira ,ya fada yana karbar kayan hannunta,
Saida sukaje kusa da motar sannan tace mlm ,amma fa bani da kudi ,
kallonta dan yuniyal din yayi yace,hajiya kamar ya baki da kudi
Tace wllh Bani da ko kwandala dan allah ka taimakamin ta fada tana zubar da kwallah , Tausayintane ya kama dan yuniyal dan yaga ga ciwo ahannunta ,dan haka yace muje hajiya ba komai,
Godiya tayi masa sanan ta shiga.
Qarfe 4:4pm suka isa garin malam madori ,hamdala khadeeja tayi ganinta amahaifarta , Sai kuma fargabar abinda zata tarar agidan ,
Haka ta kama hanya aqafa har gidan nasu,
Da sallama ta shiga gidan ,inna na gindin murhu taji muryarta , Da sauri ta juyo tana kallonta cikin mamaki ,jiya fa aka aiko musu da kudin aikinta na wancan watan , Toh me kuma ta dawoyi yanzu?
Kallonta inna take cikin harara uban me kikazo yi kuma shegiya yar baqin hali naganki da jaka,
Kuka khadeeja ta fashe dashi tace wllh inna.......
Mu hadu next page barci nakeji wllh kuyi haquri da wannan luv u all🥰
taku anty mammy 🙏
mrs babi 💘
share and comment please. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
GIDAN AIKINA🍒🍒
Na mammy kabeer (anty mammy)
Page. 19/20
Wacece khadeeja?
Malam musa dan asalin jahar jigawa ne cikin wata local govenment da ake kira da malam madori,su biyar ne agidansu ,kuma shine babba,sannan iyayensu sun rasu ,shi kadaine adakinsu ,sauran hudun duk yayan kishiyar mahaifiyarsa ne , Mahaifinsu shine ya fara rasuwa ya mutu ne sakamakon ciwon qafa daya takura masa ,lokacin malam musa duk suna yara,shine ma mai dan girma,dan haka shine yake fita yadanyi aikin qarfi sannan su dan sami abinda zasu ci,domin mahaifinsu yana da qaramin qarfi sosai ,
Zamane irin na nuna tsantsar kishi,mahaifiyar malam musa tayi iyaqoqarinta dan ganin sun zauna lpy amma sam dayar taqi amincewa,
Haka itama mahaifiyar malam musa ta kwanta ciwo kafin ta rasu ,
Malam musa ya taso cikin maraici da kuma tsangwamar kishiyar uwa ,amma duk da haka yana son yan uwansa sosai sannan yana taimaka musu iyakar iyawarsa,
Saidai hakan bai hana kishiyar mahaifiyarsa wato baba jimmaiwacce suke kira da baba ,ta cusawa yayanta qiyayyar dan uwansu sosai aransu,duk qoqarinsa akansu basa gani ,suyi ta masa gori da rashin kunya kala kala,
Malam musa ya taso mutum mai zuciyar nema hakan yasa baya zaman banza ,yana nema sosai ,kuma Allah ya taimaka masa yana samun nasara sosai akan kasuwancinsa ,da haka yake taimakawa yan uwansa shine cinsu shine shansu komai shike musu ,
Baisami damar yin karatun boko ba amma ,yayi na addini sosai ,dan haka yasan addininsa sosai.gashi mutum mai tsananin haquri da tawakkali,
Sun hadu da mahaifiyar khadeeja ne agidansu abokinsa wato saddam ,qanwarsa ce kuma su biyune agurin iyayenta ,sosai ta kwanta masa arai dan ta kasance yarinya mai hankali da kuma nutsuwa.
Baiyi wata wata ba ya nunawa abokinsa yana son auren maryam , Sosai yaji dadi dan ya yaba da hankalin musa sosai yasanshi da nutsuwa ga tsoron Allah ,
Dan haka ya sanar da mahaifinsa ,shima ya nuna jin dadinsa akan batun dan haka ,yace ya nemi yardar yarinyar,
Baisha wata wahala ba kuwa maryam ta amince da soyayyarsa ,
Ba bata lokaci akayi biki suka tare agidan su musa inda ya gyara bangaren mahaifiyarsa yasanya amarya adakin ,, Maryam tasha wahala agurin baba domin qiriqiri take nuna mata qiyayya,
Gashi kusan ahekara biyar da auren amma bata sami ciki ba hakan ya qara wa baba samun damar muzguna mata kullum cikin gori take mata da habaici saidai ta shiga daki tasha kukanta ,in mijinta ya dawo ya tambayeta tace ba komai,