Kenza eBookz

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 4

Complete book: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy)Chapter 4 of 21FantasyBy Mamy Kabir (aunty Maamy)

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 4

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 4: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 4. Haka dai sukaci gaba da zama cikin so da qaunar…

3,335 words

Haka dai sukaci gaba da zama cikin so da qaunar juna ,dakuma takura ta bangaren yan uwan mijinta ,ita keyin komai agidan ,ana haka maryam ta fara laulayi ,sosai sukayi murna ita da mijinta ,koda baba ta fahimci cikine da ita gaba daya gyashi da hassada suka cika ta tayi ta azabtar da ita ,itake komai ta hana suje asibiti,sai masifa da balai ,gaba daya maryam ta rame ta lalace inka ganta abin tausayi ,ana haka kuma mahaifiyar maryam ta amsa kiran ubangiji,ta rasu ,lokacin da labari ya riski maryam ,atake naquda ta kamata ,tasha azaba sosai kafin ta haifi yarta kyakyawa mai kkama da ita sak ,saidai tunda ta haifi yarinyar bata da lpy ,

Ga rashin mahaifiya ,ga jinya abin yayi mata yawa sosai,kullum mijinta yana kwantar mata da hankali, lokacin da yarinya takai kwnaa bakwaine aka rada mata suna wato nana khadeeja,sunan mahaifiyar maryam kenan .

ko wata ba ayi da haifar khadeeja ba baba tace ga garinku nan an kwanta da ita lpy washe gari sai gawarta da aka dauko ga alamar saran maciji aqafarta,

Haka dai saka share zaman makoki ,nan kuma baba umar ya fara neman aure shima ,inda ya auro lami ,lami yar masiface ga sa ido da baqin hali ,kullum idonta nakan abinda ,malam musa ya kawowa matarsa ,

Ta takurawa umma sosai kullum cikin habaici take da zage zage ,amma umma bata cemata ci kanki ,

Khadeeja kuwa indai ba umma ko abbanta bane suka dauketa ko zata mutu dan kuka umma bazata kulata ba,

Khadeeja yarinya kyakykyawa mai kama da mahaifiyarta ,ga haquri ga uban gashi irin na hausa fulani ,dan kakar ta bagullatana ce usul,

Khadeeja tayi wayo dan yanzu tana rarrafenta ko ina saidai bata zama guri daya ga barna,kome tayi taro dashi saita barar ,shiyasa ma maryam take kula da ita sosai , mata bari tayi ta wajen dakin inna lami .

Akwai wata rana da khadeeja ta rarrafa ta fita zuwa dakin inna lami,lokacin ummanta na bayi ,

Tana shiga taci karo da manjan da aka siyowa inna lami zatayi taliya yar murji dan lokacin tana fama da laulayine ,

aikuwa khadeeja kota basa ta juye manjan nan tas atsakar dakin inna lami tayi dama dama da jikinta dakuma dakin ,

Shigowa innalami tayi danta dauki manjan ta soya dan yunwa takeji,kawai ta tarar da khadeeja ta gama masa aiki,

Wani uban ashar data qunduma saida khadeeja ta tsorata ta zabura, Yau zakici ubanki wllh manjan nawa kikawa haka?

Cikin rashi imani ta dauke yarinyar da wani mugun mari saida ta tuntsira kafin ta dawo hayyacinta inna lami ta daka mata uban duka a cinya , Gaba daya yarinyar ta rikice ta gigice ,saida ta dauki kusan minti biyu kafin ta tsalle da kuka tana miqowa inna lami hannu ,

Cikin sauri umman khadeeja ta fito daga bayi sakamakon jin kukan khadeeja tasan ba lafiya ba ,tana fitowa yayi daidai da fitowa da inna lami tayi da khadeeja tana janta aqasa kamar kayan wanki bako imani bare tausayi, Tsayawa umma tayi saroro tana kallon ikon Allah, Ita kuwa saida ta direta gaban uwarta sannan ta tsaya cikin neman masifa wllh sai anbiyani manjana da wannan shegiyar yar ta zubarmin mai kamada aljanu ,da sauri umman khadeeja ta durqusa ta dauki yarta da take neman suma ,,gaba daya ciinta ya gurje abin tausayi ,kallonta umma tayi cikin damuwa tace yanzu ko me yarinyar na tayi t Ya kamata kiyi mata haka? Kisani Allah yana kallonki kome kikayi ,tana fadar haka ta shige dakinta ,kuka sosai tayi ganin ciwon data jiwa khaddejan ta ,Allah kana kallo,ta fada ahankali tana share hawayenta,

Haka sukaci gaba da zama cikin wahala da tsangwama ,kuma har yanzu malam musa shike kula da gidan da sauran qannansa ,mata daya aurar da su,

Lokacin da khadeeja ta cika shekara biyune alokacin kuma inna lami ta haifi zainab ,ita kuma umman khadeeja tana laulayin ciki,ita ma ,abin ya taru yayi nata yawa tunda ,yayanta ya bar gari har yau ba labarinsa ,ga damuwa ga laulayi ,haka tayi ta fama ,har cikinta ya isa haihuwa ,

Lokacin data tashi haihuwa ba qaramar wahala tasha ba gashi ita kadai adaki ta ,mijinta ya fita wajen nemansa ,inna lami kuwa tana jinta tayi banza da ita ,khadeeja sai kuka take ganin yadda mahaifiyarta take wani abu,

Ana haka saiga mijinta ya dawo da sauri ya qarsa gurinta lokacin ko motsin kirki bata iyayi sai gumi,

Subhanallah maryam sannu bari na samo abin hawa mutafi asibiti kinji,ya fada yana miqewa dan fita ,

Da gyar maryam ta kamo gefen rigarsa ,juyawa yayi yace kiyi haquri yanzu zan dawo maryama,

Dan Allah karka tafi kayi haquri nasan bazan tashiba zuciyata ciwo take sosai dan Allah ka kulamin da khadeeja ,karka bari tayi kuka ,mijina sannan idan dan uwana ya dawo kace nayi kewarsa tsawon lokacin daya tafi ya barni,malam ka yafemin in nayi maka laifi ,ta fada tana hawaye ,

Zama malam musa yayi cikin fargaba ya riqe hannun matarsa abinsonsa ,

Na yafe miki maryam baki tababata min raiba dama ,ki daina wannan maganar kinasani fargaba ya fada yana kallonta ,murmushi tayi ta kalli khadeeja dake kusa da babanta ta shafa kanta Allah yayi miki albarka ,uwata ,ta fada tana murmushi .

Salati ta fara cikin sauri tana maimaitawa ,saikuma tayi shiru jikinta ya saki gaba daya,cikin rudani malam musa yake tabata ,maryam maryam ,tashima haba maryam ,innalillahi ,dan allah maryam ki karki tafi ki barni ya fada yana taba qirjinta dif ba numfashi ,shikena rai yayi halinsa.....

😥😥😥😥bazan iya ci gaba ba saina dan matse hawayena zuwa gobe,taku anty mammy🙏

Mrs babi 💘

Share and comment plesa. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

GIDAN AIKINA🍒🍒

Na mammy kabeer (anty mammy)

Page. 17/18

Kuka khadeeja ta fashe dashi yace,wllh inna idan na zauna agidan nan watarana gawata za'a kawo muku ,inna basusan darajar dan adam ba ba irin wulaqancin da basamin ,har marina suke , shine kawai na taho ,ta fada tana kuka sosai,

La'ilaha illallahu!! Yau naga muguwar yarinya ,malam kana ina fito kaji wannan salalar tsiyar da yarinyar nan ta ja mana ,shegiya dangin tsiya wanda basu gaji arziqiba,

Babane yafito daga bandaki da buta ahannunsa , Mekike cewane ina bandaki naji kina ta babatu ,hauwa,ya fada yana ajiye butar,

Dagowar dazaiyi kawai yayi ido hudu da khadeeja dake kuka qasa qasa ga uwar bakka ahannu, Ke wanake gani kamar khadeejane ,me kuma kika dawoyi anan ya fada yana hade fuska,

Atoh ka tambayeta dai malam gata nan da ranta harda jaka kamar mai shirin barin qasar ,

Kuka kawai khadeeja takeyi ,cikin tausayawa rayuwarta ,wai shin ina zata taji dadine ? Yaushe zata huta da radadin zuciya ,tasami kwanciyar hankali ,

Dan ubanki ba magana ake mikiba kin tsaya kina kallon mutane da shegun idanuwan nan naki,baba ya fada yana mata daquwa ,

Cikin shashsheqa tace baba koroni sukayi daga gidan ,

Shikenan malam ta kassaramu ta cucemu ,ta maidamu rana ,kai wannan akwai shegiyar yarinya ,wanann tsiya ajikinku take ,inna ta fada tana jeho mata wani murfin kwano , Badan ta kauceba da saiya sameta aqafa,

Kai amma khadeeja kekam akwai muguwar yarinya yanzu saida kikayi abinda suka koroki,ina murnar kudin kayan dakin zainab ya kusa haduwa shine dan baqin ciki kika baro can din ,aikuwa zakici ubanki wllh ,badai kin dawoba ,ga gidan nan ki zauna ,ya fada yana shigewa daki,

Khadeeja kuwa daukar bakkonta tayi ta nufi wani tsohon daki wanda ko qofa babu bare window, gefe guda ma daga sama abude yake ,tunda akayi ruwa gefen ya fadi basu gyara ba ,dama kuma nanne dakin khadeeja ,shiga dakin tayi gaba daya tarkacene adakin ,haka ta marmatsar da kayan dazata iya ta ajiye kayanta agefe ta zauna tana kuka ,ya Allah kazama gatana ,kafitar sani daga wannan tsananin danake ciki ,Allah ka kawomin sauqi acikin rayuwata ,

Inna sai fada takebakinta da kumfa tsabar mugunta shegiyar yarinya r nan kika dawo muna karbar kudinmu duk watan duniya za'a kawo mana dubu talatin amma kin mana buqulu aikuwa wani aikin zansa lami ta nemar miki wllh bazaki zauna min agidaba.

Khadeeja tana jinta batace komai ba , Toh mezatace rayuwacefa inmune yau bamune gobeba,

Kameel kuwa sai wajen 5:30pm ya tashi daga barcin da yake dafe wuyansa yayi dayaji ya riqe yanadan juyashi ahankali,kafin ya zauna abakin gadon yana tuno abinda ya faru,

Dole na dau mataki ,akan yarinyar nan ,amma ta yaya meyasa ma nabarta ta tafine ,me yakamata nayi ,ya fada yana dafe kanshi,

Shiba wani abokine dashiba bare ya nemi shawara ,tsuka yayi tare da lumshe idonsa ,na tsawon lokaci ,can ya bude idonsa da sauri yana sakin wani killer smile yesss!!! Wanann shine hanya mafi sauqi dazan rama abida tayimin cikin ruwan sanyi ,aurenta anyi yess aure ,tabbas idan na aureta in da duk wani dama akanta ,

Ya fada yana dariya sosai irin ta mugunta ,yarinya kin shigo hannun mutuwarki saina wahalar da rayuwrki ta yadda ke da kanki bazaki gane kankiba ,ya fada cikin farin Ciki yana dariya ,toilet ya shiga yayi wanka sannan ya dauro alwala adaki yayi sallar azahar da la'asar ,Allah ya shirya kameel ,sam baidamu da ibada ba,

Falo ya nufo bayan ya shirya cikin wani yadi mai taushi da tsada sai qamshin turare yake kamar anyi barin turare ajikinsa,

Mommy na zaune da yaranta sunyi jigum ,suna tunanin halin da kameel ke ciki ,saigashi ya fito ,cikin sauri mommy ta tareshi son,fatan dai kana lafiya ?ta fada tana kallon idonsa ,kana ganinta kasan adame take,

Kallonta yayi ya danyi murmushi gefen baki yace ,da ancemiki banda lafiyane,cikinraini yayi mata maganar,amma sai cewa tayi alhdllh wllh duk hankalinmu ya tashi ,gashi ka kulle dakin ko abinci baka ciba,ta fada tana shafa kansa,

Muje ki bani yunwa nakeji ,ya fada yana nufar dainning table,zama yayi mommy ta xuba masa abincin ya fara ci,

Can ya dago ya kalleta yace ,inane garinsu ?

Wakenan son?cewar mommy,

Kallonta yayi yace your maid,

ok khadeeja kake nufi ,

cikinbuga table din yace momm i dont bloody care about her name ,i just ask about garinsu,

Ok ok sorry son,yarinyar yar jigawace ,cikin wani gari malam madori , nan lmi ta cemin sunan garinsu ,ta fada dason kwantar masa da hankali,

Zama yayi yaci gaba da cin abincinsa ,can ya dago yace gibe zan tafi garin ,zanje na aurota in dawo da ita nan ,

What 😳😳son kanka daya kuwa ?aure fa kace kuma wai khadeeja,ina bazai yiwuba ban aminceba ,ita aishan fa datake zaman jiranak kayi yaya da ita?momy ta qarasa da son jin qarin bayani,

Murmushi yayi ,yace momm ki daina wahalar da kanki kinsan idan nayi niyar yin abu bawanda ya isa ya hanani ,dan haka gobe zanje neman aurenta ta wannan hanyar kadai zan ladabtar da ita, Sannan batun aisha ai bani nace ta jiranibako ,ku kuka hada ,so idan zata jirani saita jira nan da watanni biyu zan aureta in kuma bazata jiraba fine sai ta qara gana ko ya fada yanakallon mommyn da kuma aishan datayi wani irin zabura jin abinda yace na auren khadeeja, Ya ma za'ahadata da khadeeja kishi ina wllh bazai yiwuba wannan ma ai cin fuskane ,

Amma son ya kamata kayi tunani idan so kake kadauki fansa zaka iya ba saika auretaba ,gaskiya nikam hakan baimim dadiba ta fada da dan bacin rai,

tashi yayi bayan ya gama cin abincinsa ya na dage kafada ,is ok momm dama basai yayi mii dadi ba,nikam na riga na yanke hukunci, Ya fada cikin ko inkula.

Amma son yanzu ko dan ni danace bana so bazaka haqura ba ?

Kai momm ,kawai dan bakison abu ni ina da ra'ayi sai in fasa sabo dake ? Hahhhh ina bazai yiwuba ,niba yaro bane ,ina da uancin kaina dan haka kima bar bata bakinki ya fada yana nufar waje,

Yana fita aisha ta sanya kuka sosai ,dama nasani mommy ba sona yake ba ,amma ya rasa dawa zai hadani sai wannan shegiyar yar aikin wllh bazan yarda ba tafiyata zanyi gida ta fada tana qoqarin barin falon,

Ke sakarya zonan ,dan ubanki inya aurotan saiki bari ta sami sake ? Kema dagewa zakiyi ki tayashi cin ubanta ,ki quntata mata kuma ai badan so zai aureta ba dan haka ki kwantar da hankalinki yata mommy ta fada da nufin kwantar mata da hankali, Nan dai sukayi ta qullawa da kwancewa .

Khadeeja baiwar allah tana daki har magrib sannan ta fito tayi alwala ,rabonta da abinci tun jiya,amma har yanzu ba komai acikinta gashi hannunta sai zogi yaje tama yaji wahala, Bayan tayi salla ne ta zauna har ishsha ,tayi sallar ishshar ta ta zauna tana ta adduar subata tuwo koda loma dayane dan ji take kamar hanjinta zai tsinke dan yunwa,

Tana jinsu sunata hira da cin tsire ,baba da inna dakuma zainab da qanannta umar da habu da kuma mariya, Sai shewa suke suna murna amma ita tana daki cikin duhu da yunwa ,ga zazzabi dake damunta,

Tashi tayi ta fito ko Allah zaisa su tuna da ita su bata abinci,

Laaaaah anty khadeeja kindawo ,mariya ta fada cikin murna taje ta rungumeta,itama rungume yarinyar tayi dan ita kadai ke nuna mata so agidan ,na dawo mariya ,ya makaranta ,

Ina zuwa yanzu ajina uku,ta fada tana kaa hannun khadeeja anty zo muje muci tsire babane ya kawo mana,ta fada tana janta zuwa wajen dasuke,

Tsayawa tayi aa mariya bana cin tsire ni ai ,ta fadatana kallon yadda zainab da ma yaran duka ke mata kallon raini ,inna kuwa sai harararta take,

Toh me zakici anty ko tuwo zakici?mariya ta tambaya , Da sauri ta daga mata kai alamar ehh

Toh bari na zubo miki anty zoki zauna ,

Aa mariya zan koma daki saiki kawomin can kinji?

Toh anty ta fada tana nufar gindin murhu ,ta dau kwano tana zuba tuwon ,

ke mariya dan ubanki ina zaki kaimin tuwon ? Ni bandafa dawata qatuwa ba ta age ta nema mana idan tana son ci.

Cikin zunbura vaki mariya tace ke innan nan saikiyi ta yiwa antu fada ,tih ai yunwa takeji,shine zan kai mata,ta fada tana daukan kwanon ta nufi dakin khadeeja.

Zakici ubanki ai shegiya marar zuciya wannan yarinyar sam bata gadoni ba,

Karba khadeeja tayi cikin sauri ta fara cin tuwon mariya na tsaye ,akusa da ita,

anty bakici abinci bane naga kina ta sauri ,mariya ta fada cikin tausayi duk da yarinyace da bata wuce shekara shida zuwa bakwai ba amma tana da tausayi sosai ,ba kamar yan gidan take ba tana son khadeeja sosai,

Bani ruwa mariya ta,khadeeja ta fada tana zuba loma, Da sauri mriya ta kawo mata ruwan tanaci tana shan ruwa saida taji cikinta yayi qatt sannan. Ta haqura dan dayawa mariya ta zubo mata,

Janyo yarinyar rayi tare da rungumeta ,nagode mariyata AllaH ya barminke,ameen antyna ,

Tadan jima adakin suna hira dan ankawo nefa kuma akwai kwai adakin .kafin ta tafi dakinsu ita kuma ta kwanta akan wani zaninta tsoho ,tana tunanin rayuwa,

wacece khadeeja? Mai karatu ku biyoni dan jin wacece khadeeja ,taku anty mammy🙏

Mrs babi💘

share and comment please. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

GIDAN AIKINA🍒🍒

Na mammy kabeer (anty mammy)

Page. 21/22

Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ,maryama karkiyi min haka ,dan Allah maryam kitashi ,shine abinda malam musa ke ta fada cikin rudu da fargaba ,

Kuka ya sanya ganin da gaske fa maryam ta barshi kenan ,kuka yake sosai kamar qaramin yaro shikenan yayi rashin mace ta gari ,yayi rashin maryam mace kamila mai sanin ya kamata ,Allah ya jiqanki maryam ,Allah ya gafarta miki ,ya sa mutuwa hutuce,ya fada yana rungume khadeeja da take kuka itama ganin mahaifinta na kuka ,

Kafin kace me tuni labarin mutuwar maryam yabazu agari, sosai mutane sukayi alhinin rabuwada ita ,domin duk wanda ya santa yasanta ne dalilin alkhairinta da son mutane ,

Haka aka hadata aka kaita makwancinta ,malam musa yana ta kuka ,jama'a sai tausaya masa suke ,dan sun san alkhairinta gareshi,

Bayan sadakar bakwaine yan uwa suka so daukan khadeeja ,amma sam malam musa ya hana kowa ,yace su bar masa ita idan ya kalleta yana ganin fuskar maryam dinsane atare da ita,

Shiyake mata komai wanka tsifa komai na rayuwarta shike mata ,sosai yake kula da yar tashi yana jin tausayinta aransa,

Haka yayi ta rainon khadeeja baya barinta agida ko kasuwa zai tafi, toh fa da yarsa yake tafi dan yasan idan ya barta ,ba qaramin wahala zata shaba .

Shekarar khadeeja biyar aduniya ,malam musa ya kamu da jinyar ajali ,a wannan lokacin khadeeja bata san wani abu waishi damuwa domin mahaifinta yana mata komai duk abinda take so shiyake mata ,

Shikansa baya son abinda zai taba masa yar tasa ,babbar damuwarsa yanzu shine idan ya mutu wane hali khadeejan sa zata shiga? Haka yayi ta jinya tsawon sati guda, Allah ya dauri ransa , Wayyo zokuga khadeeja duk da qarancin shekarunta tasan ,mutuwa,in akace mutum ya rasu baya dawowa ,

Wayyo abbana dan Allah ya dawo bana son ka mutu ka barni ,wayyo abbana ka tashi,shine abinda khadeeja ke fada tana burgima ,mata da yawa tasasu kuka , Allah sarki yarinya kinyi rashin uba mai sonki ,Allah ya jiqam malam musa mutumin kirki,ba ruwansa da duniya,

Haka dai akayi zaman makoki aka wace khadeeja na kwance zazzabi take na rashin mahaifin nata kullum sai tayi kukan ni abbana nakeso ,yana ina,

Tundaga mutuwar malam musa rayuwar khadeeja ta shiga garari kullum cikin azaba take duk da qarancin shekarunta , ita kadai ke kwana adkinau domin baba uamaru ya hana kowa daukanta wai shi zai riqe yar dan uwansa,wanda kuma ba hakan bane aransa domin dukiyar gadonta ya fadi hakan yana son ya cinye mata,

Rayuwa tayiwa khadeeja qunci gaba daya ta rame tayi baki sai uban gashi yalolo da idanuwa ,yunwa tayi mata mummunan kamu ,itake wanke wanke itake shara komai na wahala wanda yafi qarfinta shi ake sanyata,

Akwai wata rana da ta zubarwa da zainab ruwa bata sani ba ,ranar taga izaya ,domin duka inna lami tayi mata na gaske ,sannan ta daureta atuken awaki ga damuna ga sanyin dare ,ranar kuma aka tsula uban ruwa duk akan khadeeja ya qare,washe gari kuwa asume suka sameta, da gyar inna lami ta yarda aka kaita asibiti liki toci sukayi ta fada ,dan sanyi ya haddasa mata nimonia sosai ,kwananta daya ta farfado ,saidai wani irin nunfashi take da qarfi kamar zata mutu,wanann shine silar kamuwarta da cutar asma, Allah sarki maraya bawan Allah ,koda suka dawo gida ba wanda ya kula da ita ahaka tayi ta warke ,sannan da kanta ta sanya kanta amakaranta,

bayan wasu shekaru masu yawa ,khadeeja ta girma dan har tayi candyn secondary school,lokacin yayan inna lami hudu ,zainab da abdallah da sagir sai kuma auta mariya,

Samari kowa son khadeeja yake saboda kyanta ga haquri da kokari amakaranta ,duk da wahalar da take aha itake yin na daya ,

Ganin samari na fito mata ya sanya inna lami gyashi ya shiga ranta da hassada ,dan ba mai zuwa gurin zainab .

Tuni ta bazama gurin malami tasa akayiwa khadeeja asirin baqin jini ,aikuwa tsafi gaskiyar maiyinsa tuni samarin suka daina zuwa gurin khadeeja ,sai dai ace wai zainab ta zo murna gurin zainab da uwar kuwa baa magana ,sai habaici akewa khadeeja ,ita dama bata kula samarin dan ita karatu take son tayi,samarin na zainab duk bana kirki domin dai hirar bata arziqi ake ba ,lallatseta suke ,subata kudi ,idan ta kawowa inna lami kuwa tayi ta murna abinta.

ana hakane wata qawar inna lami ta kawo batun zuwa gurin aiki ,wannan shine silar zuwan khadeeja garin kano aikatau.

Wanene kameel?

Kameel wani kyakykyawan matashine dan kimanin shekaru28yrs ,mutum ne wanda kallo daya bai ishekaba wajen tantance tsanannin kyan da allah ya bashi,yana da kyau mai daukar hankali ,ga kwarjini da haiba mutum ne da bai fiye sakin fuskaba ,yana da wulaqanci sosai ga wanda ya shiga harkarsa ,baya ragawa kowa ciki harda iyayensa,ataikaice dai kameel cikakken marar mutumcine ,ga shaye shaye wanda ya koyo shi aqasar waje,

Readers Also Read