Kenza eBookz

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 5

Complete book: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy)Chapter 5 of 21FantasyBy Mamy Kabir (aunty Maamy)

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 5

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 5: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 5. Su ukune agurin iyayensu , yan gatane na gaske dan…

3,357 words

Su ukune agurin iyayensu , yan gatane na gaske dan mahaifinsu shahararren mai kudi dan kasuwa mai ji da naira yana da kamfanoni kusan biyar ,duk abinda yaran ke so suna samu arayuwarsu ,sam basu da tarbiyya ga wulaqanci,, wanda suka samoshi gurin mahaifiyarsu , Yar asalin garin edoce bayerabiyace kyakykyawar gaske iyayenta suna da kudi sosai ,sun hadu da abbane agarin abuja anan suka fara soyayya har takaisu ga aure ,sam mommy bata son mutane bata son talaka ,gaba daya ta shanye abba domin ta rabashi da danginsa ,sai yadda tayi dashi,

Abba kuwa mutumne mai matuqar kirki ga haquri da ibada ,ga son jama'a , Sam bayason rayuwar da yaran nashi sukeyi amma ,bashi dadamar da zai tsawatar musu yanzu mommy zata yi masa tatas agaban yaran ,shiyasa maya haqura yakemusu addua.

Kameel yayi karatunsane aqasar indiya ,birnin munbai,acan ya koyo shaye shaye ,har giya yaek korawa ,saida baya neman mata sam ,mata basa gabansa ,shidai kawai yasha kayan mayensa shine,damuwarsa,kuma baya shakkar sha agaban koma waye,

Wannan shine taqaitaccen labarin su gaba daya ,yanzu zamu koma asalin labarin.

Washegari da safe kameel ya shiray cikin wani hadadden yadi mai shegen tsada da kyau sai daukar ido yake ,harda malum.malum,yayi masifar kyau kamar wani ango,

Kai tsaye dakin momy ya nufa ,yana zuwa ya isketa tana daura agogo ,

Bako gaisuwa yace mommy na shirya bani addrees din zan wuce,ya fada yana wani hade rai kamar ubanta ,

Kallonshi mommy tayi yayi kyau sosai ,tana son tayi masa magana amma tana tsoron karya birkice mata ,dauko takardar data rubuta address din tayi ta miqa masa gashi son amma dan Allah ka kula kaji,ta fada tana shafa kansa .

Gaba yayi batare da yace mata komai ba ,ya fice dama ya cewa baba audu ha shirya zasu tafi anguwa ,shikadai amotar sai driver da motar security guda daya,suka shilla sai jigawa state dan shi so yake nan da azahar ma inso samune sun juyo, Duk wanna abinda ake abba baima sani ba dan ko mommy bata sanar dashi ba.

Khadeeja kuwa koda ta tashi hannunta yayi sauqi sosai dan haka shara tayi tare da wanke kwanikan ,sannan ta hura wuta ta dora ruwan zafi,

Tana zaune agaban murhun gabanta sai bugawa yake kamar zai tsage ,ta rasa dalili,sai innalillahi take aranta,

Inna lami ce ta fito ta dauki buta ta nufi bayi ,bayan ta fitone khadeeja ta gaisheta ,tace inna mai zandora muku? Uwarki da ubanki zaki dora mana shegiya mayya ,gadon tsiya ,wato adafa kici ko ? Mai baqin hali irin na uwa gadon tsiya da basu gaji arziqiba ,ta qarasa taba hararar khadeejan ,

Sunkuyar da kai khadeja tayi tana share kwallah Allah kashirya inna lami ,ta soni kamar yayanta,ta fada ranta,

Zainab ce ta fito cikin wata shegiyar riga matsatstsiya ,ajikinta daga ita sai wani dan mitsitsin mayafi ajikinta tana waya ,zuwa tayi ta tsaya kan inna lami,tana tauna cingam qass qass qarass,tace inna nikam na wuce sai na dawo ,ta fada tana maida wayar cikin jaka ,

Toh yar albarka har kin fito nace yau badan nacin goronne,ta fada tana washe baki,

Kai wllh kekem inna kincika zalama akan kudi jiya fa dubu uku na baki ,amma yau ma kike tamvayata ,kudin nan fa saian sha wahala nake samu,ta fada tana miqa mata dubu biyu,ai da sauri inna lami ta wafce kudin ,yawwa yar albarka , Allah ya karemin ke yakuma bada sa'a,ta fada tana soke kudin ,yau kwai zamuci yaseen ta fada tana dariya ,

Nikam na wuce inna ,zainab ta fada tana barin gidan cikin wata irin tafiya kamar karuwa,

Kallon khadeeja ta bita dashi cikin jin takaicin halin da yar uwar tata takeci,

Kinga yadda ake harkar arziqi bata tsiyaba ,inna lami ta fada tana hararar khadeeja ,shegiyar yarinya mai baqin jini ,karbi kije ki siyomin kwai guda biyar da bread dn tari biyu ta fada tana bata dubu ,

Karba khadeeja tayi ta nufi qafar gidan gabanta na tsananta faduwa,

bayan ta dawo daga siyo kwan ita ta soya ta hada musu tea din amma ko dandane ba abata ba, Guntun tuwon jiya ta dumama ta ci ta koma akurkinta.

can wajen shudewar awa guda inna lami ta bata kudi taje kasuwa ta siyo mata kayan miya ,

Alhalin duk ga yara nan agidan dan yau asabarce ba makaranta, Amma ita aka akai kasuwa haka ta karbi kudin ta fita zuwa kasuwa ,

Kameel kuwa basu iso ba sai wajen 11:00am na rana basu wani sha wahala ba suka zo har anguwar ,kameel ji yake kamar ya koma ya fasa auren da yazo dan gaskiya bazai iya sauka qasan wannan gurin ba haba ai saiya mutu wannan yarinya dole yaci ubanta tunda ta kawoshi wanann gurin wllh,

Daya daga cikin guard din ya aika akan yaje yayi sallama da maigidan yana kallon gidan ayatsine ,wannan sunfi uban kowa ma talauci wllh shegiyar yarinya kawai.

Aikuwa da sauri baba umaru yafito jin cewar wasu motocine sukazo qofar gidan nashi,kuma ake sallama dashi,

Yana fitowa babbar rigarma abaibai yasanyata ,yana rawar jiki, kallo kameel ya qare masa dama wannan shine uban nata har ta daga hannu ta mareni ? Zakuci ubanku dagake har wanann tsohon dan naga alama zalamammene,

Har gaban motar da kameel ke ciki wannan guard din ya kawo baba umaru,yana zuwa ya wani zube aqasa ,kamar yazo gaban sarki,

Allah ya taimakeka alhaji barka da zuwa ,sannun ku da zuwa ,yake fada yana daga hannu danahi yayi tunanin ma shugaban qasane yazo nemansa,

kallon wulaqanci kameel yayi masa tsawon kusan minti goma kafin ya bude baki yana daga cikin mota yace malam kaine baban wata yar aiki a kano?

eh nine wllh yaro nine ya fada yana rawar baki .

Bude baki kameel yayi yace......

Sai mun hadu anjima ,anty mammy🙏

Mrs babi💘

Share and comment [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

GIDAN AIKINA🍒🍒

Na mammy kabeer (anty mammy )

Page. 23/24

Bude baki kameel yayi cikin isa da izza ka tabbata kaine ubanta?

Kwarai alhaji nine komai nata yata ce wllh ,kuma yarinya ce mai hankali Allah dai yasa wajen aikin za'a mayar da ita ,dan wllh da dan kudin aikin muka dogara alhaji ataimaka mana,ya fada yana hade hannunsa alamun tsoro ,

Kallonsa kameel yake cikin raini da kuma kuma tunanin bazai sha wahala ba tabbas dan dagani mutumin mayen kudine,

Wata jaka kameel ya dauke dake gefensa ya miqowa guard din tare dayi masa alama ya bawa baba umaru,duk wannan abun da ake fa kameel baiko bude murfin motar ba bare ya taka qafarsa aqasar gurin.

Karba guard din yayi ya miqawa baba umaru,har neman hantsalawa yake wajen karbar yakar ,bude ,kameel yace masa ayatsine , Ai hannu na rawa baba umaru ya fara kici kicin bude jakar ,gaba daya yama kasa budewar.

Saida guard din ya taimaka masa sannan ya bude, Cikin mugun tsoro da faduwar gaba baba umaru yake kallon makudan kudin dake cikin jakar jikinsa na rawa ,bandir ne na yan dubu dubu kusan guda goma,,da sauri ya dago kansa akarkon farko ya kalli kameel baki na rawa yace, Alhaji wannan kudin na menene?

Saida kameel ya gama hararar baba Umaru kafin yace so nake ka aura min yarka yanzun nan inkoma kano da ita,

Cikin sauri baba umaru ya dago kansa yana qara kallon kameel ,alhaji bangane me kake nufiba ,kasa so kacemin kazo neman auren yata khadeeja ne kome? Ya fada cikin ladabi.

Ashe ma ka gane abinda nake nufi kake tambayata kuma ,kameel ya fada yana yatsina fuska, Allah Allah yake subar gurin nan ,dan ji yake kamar yayi amai duk da face mask dake fuskarshi,

Shiru baba umaru yayi nadan wani lokaci ,sannan yace toh alhaji inaso kadan bani lokaci domin in gayyato yan uwa da abokan arxiqi sai adaura auren in sha Allah duk bazai gagara ba.ya fada yana sunkuyar da kanshi kamar wani dan koren sarki,

Murmushin qeta kameel yayi ,kudi maganin walaqanci, maganin damuwa , gaskiya bai yarda talakawa zulama;u bane sai yau din nan,jibi wannan banzan tsohon zai aurar da yarsa ba tare da sanin waye wanda zata aura ba daga ganin kudi duk ya gigice,

Shikenan na baka minti goma dan sauri nake zan koma ,kameel ya fada cikin isa,

Toh toh alhaji baza abata lokaciba in sha allah yanzu zan dawo ya fada yana tashi da sauri ,ya ruqunqume jakar har tuntube yake ya shiga gida ,

Lami lami ,zokiga abin arziqi yau kakarmu ta yanke saqa,ya fada yana zama akan tabarma ,inna lami ce ta fito tana mita ,kai wllh malam kacika damu wllh yanzu haka ba wani abun kirki bane kake ta......ai kasa qarasawa tayi sakamakon arba datayi da uban kudi ,aibashiri ta nemi kusa dashi ta zauna malam a ina ka tsinci wanan kudin haka ? Ta fada tana daukan dauri daya,

Kedai bari hajiya yanzu sauri nake ,zan je in gayyato liman da sauran yan uwa za ayi daurin auren khadeeja ne yanzun nan,ya fada yana tashi tsaye ,

Malam wace khadeejan kuma? Inna ta tambaya , Khadeeja nawa garemu ta nan gidan mana ,ai mai neman auren natane ya kawo wannan kudin kuma yace yanzu yake son adaura auren zasu wucene,

Malam Amma ka bani mamaki yanzu mutum da wannan uban kudin ka aura masa wannan shegiyar bayan ga taka yar ta cikinka?

Kai lami kina da matsa in bai auri tamuba bagashi ya bamu yanke talauciba yanzu wannan kudin ai ya ishemu rayuwar duniya,ya fada yana ficewa da sauri,

Zama inna lami tayi cikin alhini inama ace yartace ta sami wannan mutumin mai uban kudi haka ,kai gaskiya data more wllh ,amma bari in leqa in masa bayanin zainab ko zai fasa da khadwejan ,ya auri zainab din.

fita tayi da lullubi akai ta nufi gurin dalla dallan motocin ,tana uwa guard suka tareta,ina zaki suka tambayeta ,

nice uwar yarinyar dakukazo neman aure waye mai son nata anan ,ta fada cikin qosawa,

Yana ciki bari asanar dashi,cewar daya daga cikin guard din.

Muje yace mata bayan ya sanar da kameel uwanta ,zuge glass yayi yana kallonta ayatsine ,

Sannu alhaji sannu kaji ,munga abin arziqi muna godiya ,amma nace amma bakasan halin yarinyar bane halan ,da gaskiya yarinyar bata da kirki sam gashi tana yawon banza tasan maza ,mutuniyar banzace, Amma akwai yar uwarta ,tana da hankali idan kanaso sai a aura maka ita ta qarasa tana wage baki,

Kee dalla malam bana son shirme kedin wacece haka ,ke kin isa kisani nayi abinda banyi niya ba shashasha ,idan neman sadaka kike gara ki fadamin in baki ,mezanyi da yarki qazamai kawai ,ya fada yana rufe glass din tare da yiwa guard inkiyar ya koreta daga gurin,

Allah ya qara nikuwa nace ina tsalle dan murna,

Ai kafinma su koreta tayi saurin barin gurin dan ta fahimci kameel baida mutunci ,shegen yaro mai baqun hali ta fada ,amma duk da haka naji dadin cewa da alama shegiyar yarinyar nan ba dadin zama zataji da wannan yaron ba ta fada tana shigewa gida.

kankice me mutane sun taru amasallaci dan daurin auren khadeeja da kameel baba audu shine ya karbarwa kameel auren khadeeja ,akan sadaki naira dubu dari,100.000 Cikin lokaci qanqani aka daura auren amma fa kameel yana cikin mota dan ya rantse bazai fitoba,har aka gama daurin auren yana mota kawai fatansa abashi khadeeja ya tafi da ita domin ya matsu ya fara koya mata hankali,

Wai ina khadeejane ?

Tana can ta gama cefane ,ta taho gida amma gabanta sai mugun faduwa yake kamar zata shide ita tsorontama kar asmarta ta tashi,

Haka ta nufo gida tanajin faduwar gabanta na qara tsananta,

Kasancewar ta gaban gidansu masallacin yake shiyasa ta hangi taron mutane anata fitowa daga masallacin gida ta qarasa bata kula da motarsu kameel ba dan tana can kusa da masallacin ne ,

Shiga tayi da sallamarta ta ajiye kayan ta fara qoqarin dora musu girki dan taga rana tayi ,tana cikin hura wutane baba umaru ya shigo gidan yana baza babbar riga ga kudin sadakim khadeeja ahannunsa,yana ta qirgawa,

Ina khadeejan takene ,maza kizo ki shirya zaku tafi ne fa yanzun nan ,

Dagowa khadeeja tayi tana kallon baba umaru danshi ko kula da ita ma baiyiba yana ta lala kudinsa,

Tafiya kuma? Ina zamu tafi ? Kuma da suwa zamu tafi? Shine tambayar da khadeeja keyi cikin zuciyarta,saidai ba amsa,

Lami zo maza ki kirata zasu tafi, Inna lamice ta fito daga daki uo malam har andaura kenan ,wana suka bada sadakin ne ,ta fada tana kallon hannunsa,

Dubu dari cas kingansu ahannuna ya fada yana nuna mata ,

dari malam yanzu akan wanna. shegiyar ake barnatar da kudi har haka lallai wanna shima dan rakiyar asarane ta fada cike da gyashi,

Ke dan ubanki tashi ki sanya hijabinki ki dauko kayani zaku tafi yana jiranki,

Cikin neman qarin bayani khadeeja tace , Amma baba ina zan tafi ? Kuma wake jirannawa? Ta fada tanankallonsu ,

Mijin da na daura muku aure dashi yanzu ,shine yake jiran naki dan ubanki ,dakike tambayata kina wani kafeni da wadannan idanun naki kamar na mayu ,baba umaru ya fada,

Cikin zaro ido da kuma tsantsar fargaba khadeeja tace ,baba aure kuma? Ni aka daurawa auren ? Ta fada jikinta na karkarwa cikin tsoro,

Dan ubanki dadawa nake magan inbakeba kena daurawa auren mana ,shegiya ,mai baqin jini keda allah ya taimakeki ma kika sami mai abin hannu,ya fada yana cusa kudinsa cikin aljihun babbar rigarsa,

Nashiga ukuna!! Shine abinda khadeeja ta fada tare da dora hannunta akai ta fashe da wani matsanancin kuka ,kukan da bata tabayin irinsaba ,

Wayyo Allah baba dan Allah karkamin haka ,karka daura min aure da wanda bansani ba baba ,nifa yarkace dan Allah baba kataimakamin wallahi bana son nayi aure yanzu karatu zanyi baba wayyo Allah na ta fada tana kuka wiwi,

Laaaah malam kagji shegiyar yarinyar nanko ? Wai kuka take dan ubanki idan bamu aurar dake ba ubanki zamuyi dake shegiya mai baqin hali wllh yau saikin bi mijinki inyaso ko dan yankan kaine ma ya yanke miki kan kowama ya hutata fada tana kai mata duka.

Durqusawa tayi har qasa dan Allah baba kuyi min rai wllh banason wannan auren ku taimakamin dan Allah karkuce inbishi,ta fada tana riqe gefen rigar baba umaru ,

Mari ya taska mata akuncinta ,tashi dan ubanki kona karyaki yanzunnan shegiya ,marar amfani ,ya fada yana qara kaata duka ,

Dan Allah baba ka taimakamin ,baba ni marainiyace ,kuma anama agareka karkaci amanar dan uwanka baba ,dan Allah na roqeka ,ta fada tana tashi daga faduwar datayi

Wllh yau ko gawarkice saita bar gidannan wllh kiji yarinya zatayi mana asara,

maza lami dauko mata kayanta bazata shiga dakin bama,ya fada yana kallon Inna lami, Shiga kuwa dakin inna lami tayi ta dauko mata yar jakar kayanta ta fito ta jefa mata ita tare da cewa zaki tashi kosaina lakada miki dukan mutuwa,

Wayyo inna dan Allah kuyi haquri ku barni innayi muku laifineku yafemin dan allah ta fada cikin kuka kamar zata shide ,

wani icce inna ta dauko ta buga mata abaya ,saida ta gantsare cikin azaba ta kwalla qara wayyo Allah bayana inna kiyi haquri ,ta fada tana daukan hijabinta dake lanqaye ajikin igiya, Ta sanya tare da daukar jakar da inna ta qara jeho mata ita,

,cikin kuka ta kalli baba umaru ,tace baba ,zan tafi kamar yadda ka buqata zanbi wanda ka auraminkoda hakan na nufin nayi tafiya ta har abada ,amma kasani baba ni amanace agurinka ,kuma Allah zai tambayeka akaina ,

Baba duk halinda zanshiga agidan aurena kasani kaine sila kuma Allah baya bin bayan zalinci , Inna na barmiki gidan na tafi zan zauna duk tsanani duk wuya kodazasurinqa yankan naman jikina ne zan zauna har sai naman jikin nawa ya qare,sannan ku sani da mahaifina ne amatsayinku bazai yiwa yayanku hakaba,

tana fadin hakan ta kama hanuyar qofar gida tana kuka,

Baba ne ya kalli inna lami da dan mutuwar jiki yace ammafa yarinyar nan ta kashemin jiki wllh harna fara tsoron karfa siyar da ita mukayi,

Kai kaji kadai malam da wata magana yo ba taimakonta mukayi baaurefa akace bawani abuba ,karka yarda da wanna kalaman nata har suyi maka tasiri ta fada tana qoqarin kawar masa da tunani dayazo zucoyarsa yanzu,

Kuma fa hakane ,ya fada yana nufar qofar gidan shima ,

Kameel kuwa yana zaune ya jingina kansa da jikin kujera wani irin farin ciki yakeji aransa ji yake kamar ya shiga ya dauko yarinyar nan ya fada gwada mata halinsa ,

Kawai saigasu sun fito kuwa ,dariya yasaki cikin qeta ,yarinya ki. Shigo hannu,ya fada daidai lokacin da baba ya kawota har cikin motar ,budewa yayi ta shiga ciki tana kuka bata ko kalli wanda ke cikin motar ba,

Haka tanaji tana gani suka bar garin suka dauki hanyar kano ,kuka take kamar zata mutu ,yanzu haka rayuwa zatayi ta gware dani ya Allah ya kareni daga sharrin masharranta.

Kee! Dan uwarki kin cikamin kunne da ihu,

Cak kukanta ya tsaya sakamakon muryar daji ta ratsa dodon kunnenta ,

Da sauri ta juyo da kanta carab suka hada ido da kameel ..,.......

Toh fa qaqa qara qaqa,

Sai mun hade

Taku anty mammy🙏

mrs babi 💘

Share and commeny please. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

GIDAN AIKINA🍒🍒

Na ammmy kabeer (anty mammy)

ELEGENT ONLINE WRITER'S

Page. 25/26

Da sauri ta juyo da kanta ,aikuwa carab idanunsu ya sarqe cikin na juna.

Damm!dammm!!dammm!!! Haka gaban khadeeja ke bugawa da mugun sauri, Hannunta na karkarwa take nunashi"cikin rawar murya take cewa ' "me kakeyi anan?me ya kawoni cikin motanka" Ta fada cikin rawar murya da faduwar gaba ,Allah kasa kada tunanina yazama gaskiya,no no bazai yiwuba yallabai kameel bazai taba aurena ba ,amma meyasa kuma na ganshi cikin motar ? Kodai satoni yayi?ta fada cikin ramta tana mai zaro ido waje sosai , "menakeyi cikin motarka" Ta fada atsawace tana kallon kameel,

Kameel kuwa gabansa ne yake faduwa da mugun sauri tun lokacin dasuka hada ido,yace toh mayya ta kalleni shikenan gabana zaiyi ta faduwa ,ya fada azuciyarsa.

Cikin isgili yace "au uban naki bai fada miki ya siyarmin dakebane"?

What!!! Ta fada da qarfi," kana nufin kaine mijin da baba ya daura aurena dashi"ta fada cikin karayar zuciya,

Kee!!! Ya daka mata tsawar da saida ta zabura, "ni nafi qarfin in aureki wllh saidai insiyeki,kuma na siyokine don in nuna miki banbanci tsakanin talaka da mai kudi " Ya fada cikin mugun hade rai ,

Sosai khadeeja taji zuciyar ta ta karye ,shikenan tata taqare ,baba umaru ya bayar da ita gurin mutum mugu marar sanin darajar dan adam ,har yana iqirarin ya siyotane ,wayyo Allah rayuwata,Ya Allah ka dafamin ,ta fada aranta ,tare da fashewa da kuka ,tana buga qofar,"bana sonka bana son aurenka ,ka budemin na koma gida na tsani halayya irin taka ,kaiba mutum bane kai shedanine ,meyasa ka takurawa rayuwa ? Menayi maka haka da zafi kake fatan jefani cikin uquba? Ka budemin qofa infita wayyo Allahna wayyo ummana ,wayyo abbana, Abinda khadeeja ke ta fada kenan cikin qunar rai da radadin zuciya , Duk tsawar da kameel ke mata hakan baisa ta daina.ba,dan gaba daya bata cikin hayyacinta,

Ganin tana takura masa da ihune yasa kameel ya ruqo hannayentaduka biyu,yace "ke wllh ki nutsu ko yanzu in mammareki shegiya mayya mai idon mayu"ya fada gabansa na ci gaba da bugawa non stop,

Kokawa khadeeja ta fara tana qoqarin kwace hannunta daga cikin nasa, "ni kasakemin hannu bana sonka bazan bikaba kai mugune wayyo Allahna" ta fada tana mai cigaba da kukanta cikin rudu ,

Kameel kuwa haushine da takaici suka cika masa ciki,'wai bata sonshi ? Kamarni wannan baun zatace nata sona? Lallai wllh saina koya miki hankali zakigane kurenki,ya fada acikin zuciyarsa yana kwafa,

Khadeeja kuwa gaba daya ta tashi hankalinta da kuka tana qoqarin kwace hannunta daga riqon dyayi mata ,zafi hannun ke mata dan ba riqon wasa yayi ma hannunba,

shikuwa kameel saboda salon mugunta sai qara murde hannun yake , Runtse ido khadeeja tayi cikin azaba ,tace"ka sakemin hannu kana famamin ciwona"

Ai kamar ta zugashi ya qara murdawa yace "anqi asakedin kiyi abinda zakiyi ,bake maiqarfi ba toh ki kwace mugani"ya qarasa yana qara matse hannun .

Readers Also Read