Kenza eBookz

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 6

Complete book: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy)Chapter 6 of 21FantasyBy Mamy Kabir (aunty Maamy)

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 6

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 6: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 6. Ba shiri khadeeja ta fada jikinsa tana kuka dan…

3,359 words

Ba shiri khadeeja ta fada jikinsa tana kuka dan sosai yake azabtar da ita ta hannu, Wayyo Allah na ka bari banaso hannuna ciwo mugu kawai azzalumi sai Allah ya sakamin ,ta fada cikin kuka tana juya kanta ,aqirjinsa cikin radadi,

Shikuwa kameel wutace ta dauke masa diff ,na tsawon wasu sakwanni ,sakamakon haduwar jikinsu guri daya, wani irin shock yaji tundaga tsakiyar kansa har zuwa tafin qafarsa ,da sauri ya runtse idonsa ,yana mai sakin wani dan qara,"auchhhh wayyo Allah " Dan shi tunda yake baitaba jin irin wannan abinda yakeji yanzu ba idonaa ya qara lumshewa dan haryanzu bata daina goga kanta aqirjinsaba,

Bugun zuciyarsane ya qara tsananta ,cikin rawar murya ,yacw,kee.....dan..dan u....wwarki da.....gagg.....nii.ya qarasa cikin nunfashi sosai kamar wanda yayi tsere, Wllh ko shakka babu wannan yarinyar mayya ce ji yadda gaba daya najini wani iri daga ta hada jiki dani shegiya kamar wanda ma take jan jinina,ya fada aransa ,

"Kasakemin hannuna",ta fada cikin raunin murya,

Dasauri ya sakemata hannun dan samarwa kansa lpy shima ,wannan dole ya kiyaye abinda zaike hada jikinsu da ita wllh ,banza qazama ko tayaya ma ya riqe hannunta har tawani kwanta masa ajiki ?shegiya taga jiki mai kyau da tsafta ba irin nata ba,ya fada yana harararta bayan ta dagashi .

Jikin qofa ta koma ta jingina kanta da glass tana mai ci gaba da kukanta muryarta har ta dashe,tsabar kuka ,

ni yanzu shikenan haka zan qare rayauwata cikin bauta? Bautar ma kuma qarqashin wadannan mutanen da basu san darajar dan adam ba ? Baba meyesa zakamin haka ? Maiyasa kazabi jin dadin rayuwarka akan farin cikina ? Nifa marainiyace ,kuma manarka , amma ka bayar dani ga mutanen da suka daukeni baiwa ,bakomai na dogara ga Allah shine zai kareni daga sharrinsu.

Kameel fa gaba daya ya shiga yanayi ,dan haryanzu jinta yake tana goga fuskarta a chest dinshi wani jummmmm!!! Yakeji ajikinsa ,gaba daya yanayinsa ya sauya,idonsa suka qanqance ,sunyi jaa sai wani lunshe ido yake ,ji yayi yana buqatar kasancewa da mace sosai,abin ya bashi mamaki dan kafin wannan lokaci shi sam mace bata gabansa , Bawai baijin feeling akan mata bane, aa kawai baya bari abin yayi tasiri ne atare dashi ,

Amma yanzu gashi wannan mayyar tana neman zuqeshi ,danshi baiyarda cewar ba jinisa take zuqaba,

Qara kwanciya yayi jikin kujerar yana mai lunshe ido,cikin yanani na buqatuwa,gaba daya jikinsa yayi wick ,kasala duk ta lullubeshi ,sai ajiyar zuciya yake , Koya ya motsa saiyaji yanayin na qaruwa atare dashi,

Ji yake kamar ya janyota jikinsa ya rungumeta ko zai daina jin yanayin dake tare dashi, Amma tab! Allah ya kiyaye ya qara bari wannan mayyar ta rabi jikinsa ,never wllh nafi qarfinta ,ya fada yana rufe ido da qarfi.

Qarfe uku da kwata suka iso garin kano 3:15pm ,ba bata lokaci suka nufi anguwar g.r.a ,hon driver yayi abakin tangamemen get din,akan bude musu suka kunna kai ciki.

Suna tsayuwa kameel ya bude jajayen idanunsa da cike cike da jarabar daya samu yanzu yanzun nan ,ya kalleta tana zaune kamar gunki ,sai hawayene ke ambaliya a idonta.

wannan shegiya bata gajiya da kuka tunda muka taho daga wancan jejin nasu takekuka,har yanzu,mtsss ya ja tsuka " Ke malam dalla fita kiba mutane guri ko motar ta ubankice,da kika zauna baki fitaba ya fada cikin jin haushin yanayin data sanyashi ,shegiya mugu ya fada aransa.

''Hahhhh malam kameel kenan ,kaida ita aga mugun ai,kuma wllh ka iya bakinka da cewa garinsu khadeeja jeji ehee😏"

ko kallonsa khadeeja batayi ba dan ita yanzu batatashi take ba babbar damuwarta shine komawa wannan baqin gidan.

Cikin haushi ya bude motar ya fito tare da bude bangaren da take ciki ya fizgota ya fara janta har cikin babban falon ,

Yana zuwa ya hankadata ,Allah yasota ma akan kujera ta fada , Sai huci yake, "wlllh wannan shine lokaci na qarshe dazanyi miki magana kiyimin banza ,banza yar matsiyata masu son abin duniya kwadayayyu ,ya fada cikin izgili tare da bin Corridor ya nufi part dinsa,

Kuka sosai khadeeja ta sake cikin baqin ciki da damuwa ,kamar zata mutu haka takejin zuciyarta.

wannan wane irin aure baba ya dauramin ?anya kuwa ba siyar dani din yayi ba da gaske ?inkuwa hakane baba yaci amanar dan uwansa yayimin abinda abbana bazai taba yiwa zainab ba , Bakomai Allah yana tare dani ta fada ahankali,

tana zaune saiga mommy ta shigo gidan da alama bata gidan da,

Kallon shegege tayiwa khadeeja ,kafin tace"kin dawo kenan kinzo girbar abinda kika shuka agidan nan ,yarinya ki kwana da sanin bazaman dadi zakiyi ba ,dan wllh saina san yadda nayi rayuwarki ta daidaice ,kin batamin shiri kinsa dana ya auroki jibeki wata qasqantacciya marar galihu yar matsiyata ,har ace kece surukata ? Kinyi ganganci wllh yar aiki, da ina tunanin batar dakene lokacin da naji son yana batun auroki ,amma danaji qudurinsa na aurokin saina barki dan ki dandani radadin bacin rai har ki hadiyi zuciya ki mutu.

Tana kaiwa nanta nufi dakinta cikin bacin rai .

Kuka kam khadeeja ta shashi awannan rana ba mai rarrashinta sai Allah,tana nan gurin har magrib ,kafin yaran gidan suka dawo da alama daga gurin biki suke dan yanayin shigarsu ya nuna hakan .

Wucewa sukayi batare da sun kula da itaba ,dan tana jikin kujera daga can lungu ,anan tayi sallar ta,ta zauna tana addu'ointa ,ga yunwa dake nuqurqusarta.

Sai bayan sallar ishsha suka fito falon gaba dayansu ,har mommy , Yaran suna sanye da qananan kaya ,kana gani shigar san ba tarbiyya acikinta ,kuma har aisha dan tata shigar ma tafi tasu muni.

Kameel kuwa yana shiga dakinsa kwanciya yayi yana ta juyi akan gado sai tsuka yake yana jan yaji ,sosai yake jin feeling na damunsa,haka yayi ta juyinsa kafin ya samu barci ya daukeshi ,sai gurin biyar ya tashi wanka ya shiga ya dauro alwala,

Sallolinsa ya fara daga azahar ,la'asar zuwa magrib sannan ya shirya cikin wani qanan. Kayan masu masifar kyau ,wow kuzo kuga yadda kayan sukayi masa matuqar kyau kamar kasace shi ka gudu ,barin turare yayiwa jikinsa kamar kullum ,

Kafin yayi sallar ishsha dan ankira alokacin ,shifa baya zuwa masallaci dan karya hada sahu da mutane su shafa masa cuta yan nigeria qazamaine. Kuji dan rainin hankali fa.

falon ya fito shima yanata baza qamshi kamar gonar turare ,zuwa yayi ya zauna kusa da mommy ,cikin murmuahi mommy ke shafa kansa son sannu da hanya ,fatan dai baka sha wahala ba ?

Dan zamewa yayi ya kwanta akan cinyarta ,aransa yake cewa "nikuwa aini nasha wahala wannan mayyar data rinqa zugata , Amma afili kuwa cewa yayi ,no wahala mom.

Tashi yayi cikin sauri momm ina take? Ya fada yana dan dube dube,

Wake nan son?

Ita yarinyar dana kawo mana shegen taurin kaine da ita sai na gyara mata zama sosai mayya ,ya fada yana qarewa falon kallo can ya hangota tana barci aqudundune agefen kujera,tashi yayi yana murmushi ya bude fridge ya dauko ruwa mai shegen sanyi ya nufo inda take ,

Baiyi wani tunaniba kawai ya bude murfin robar ruwan ya fara tsiyaya mata shi ajiki shaaaaa

amugun firgice khadeeja ta tashi tana salati ,dan aduniya bata qaunar ruwan sanyi saboda jinyarta ,

Nan danan jikinta ya dau kyarma kamar mazari dafo kanta tayi cikin rawar jiki tana kallonsa.......

Toh fa masu karatu sai anjima taku anty mammy🙏

mrs babi💘

Share and comment please.

More comment ,more typing. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

GIDAN AIKINA🍒🍒

Na mammy kabeer (anty mammy)

ELEGENT ONLINE WRITER'S

Page. 27/28

Dago kanta tayi cikin rawar jiki tana kallonsa ,

Kameel kuwa rungume hannunsa yayi aqirji ,yana murmushin mugunta kallonta yake amma bai yarda idanunsu sun hadu ba.

Cikin gadara da salon mugunta yace "yane ko kina da magana "

Ajiyar zuciya khadeeja ta sauke tare da kawar da kanta batace komai ba sai qoqarin daga hijabin datake da hannunta dan ya manne aqirjinta,

"oya wuce ki dafamana abinci yanzu ,wane shegen kika ajiye da zai dafa ,ya fada yana komawa inda ya tashi ,

Kana kallon aisha zaka fahimci irin dadin datakeji ,ganin irin wulaqancin da kameel yayiwa khadeeja, Hakan ba qaramin kwantar mata da hankali yayi ba,dan tasan ba batun soyayya anan,

Kallon juna sukayi da mommy sukayi dariya,

Khadeeja kuwa kitchen din ta nufa ta dora girkin jallof din taliya tayi musu da busashshen kifi,sannan tayi musu sobo ,tana kammalawa ta jere musu akan danning table gaba daya ta ajiye musu komai,

Kaha suka taso zoqai zoqai ko kunya suka zauna ita tayi serving dinsu ,ta koma gefe ta zauna ,yunwa takeji sosai ,gashi bata dibi abincin ba bare taci,

Haka sukaci abincinsu suna ta hira ,sunma manta da ita agurin ,ikon Allah tas suka cinye abincin nan tana kallonsu ,amma ba wanda yayi tunanin cewa zo ki diba kema kici ,haka suka gama ,kuma aka bata umarnin gyara gurin haka ta gyara dan sauran wanda suka rage shita samu taci a kitchen din.

Bayan ta kammala neta fito ta nufi hanyar dakinta na da saidai kafin ta yi nisa da tafiyar taji muryarsa ,

"ke gidan ubanwa zaki? Ya fada agadarance ,

Daki zani,ta fada ahankali,

Zaraf aisha tace"to isashshiya bazaki nemi izinin tafiya ba saidai kiyi gaban kanki ko? Ni wllh mommy wannan jiji dakan nata yana bani takaici saikace yar wani, Barni da ita aisha ,aini wllh mamaki abin ma yake bani ko gani take hutu ta dawo yi agidan ne wayasani?

Kameel ne yace "Come back here"

Tahowa tayi cikin takunta na nutsuwa wanda suke dauka ko dan wani dalili takeyinsa ,

Zuwa tayi ta durgusa agefensa ,

Cikin bada umarni yace daga yau kin bar kwana adakin can kinjina ,a part dina zaki koma zama sai inzakiyi aiki zaki fito nan,

Kallon mommy aisha tayi da sauri cikin zaro ido ,sannan ta kalli kameel , Amma baby kana ganin kwananta acan ya dace kuwa ta fada adan shagwabe ,

Kallon aisha yayi kafin yace ,ina ruwanki ,kinsan bana son shishshigi akan harkata ,nariga na yanke hakan araina so ki zubamin ido kawai ,ya fada yana galla mata harara,

Shiru tayi tare da turo baki ,aranta take cewa ,dan rainin hankali dan kaga ana sonka sai kayi tayiwa mutane iskanci ,zakazo hannune wllh saika raina kanka,

kallon khadeeja yayi ,wacce itama shi take kallo cikin mamaki ,lallai ma adakinka kamar wata yar iska ?ashe kuwa zaayita dan wllh bazanyi barci ka cutar dani ba,

Kina jina ko dan haka koma can kijira har saina tashi tafiya part dina sanann muje innuna miki inda zaki zauna ,ya fada yana mai jin dadin yau zai wahalar da ita dan yayi alqawarin bazatayi barciba dan aiki zaiyi ta bata,

Sannan kuma Bana son qazanta dan haka kikiyaye ,ya fada yana mata kallon sama da qasa.banda qaddara mai zai hadashi da wannan kidahumar.

Mommy ce tace son amma dai ba daki daya zaku kwana ba dan banason ta shafa maka cuta ,tayi wannan tbayarne dan jin kodai yana da wata manufane akan khadeejan ,Allah dai yasa ba kusantarta zaiyiba dan bata fata ta sami jika da wannan matsiya ciyar ,

Sarai kameel ya gane mai mommy ke nufi ,kallonta yayi cikin murmushin duniyanci yace "mommy kenan karki damu abinda kike tunani bazai taba faruwa ba har abada,ya fada yana murmushi,

Ajiyar zuciya mommy tayi dan har hankalinta ya kwanta.

Khadeeja na gefe azaune barci takeji sosai amma ta rasa yadda zatayi ,shikuma da gangan yau yayi zaman sa afalon sai wajen 12 sannan ya tashi lokacin duk sun tafi daki har mommy ,sai aisha da take ta karuwancinta dan ta burge kameel shikuwa ko kallonta baiyi ba bare yasan me take.

Kee tashi ,ya fada yana zungurin khadeeja da qafa , Dago kanta tayi ta kalleshi suka hada ido ,damm! damm!! damm!!! Gabansa ya fadi ,da sauri ya kawar da kanshi ke mayya dena kallona karki cinyeni,ya fada yana yin gaba,

tashi tayi ta bi bayansa tazo wucewa ta gaban aisha ,da sauri ta sanya mata qafa,tafiya tayi taga taga zata fadi ,runtse idonta tayi tare da yar qara tana jiran jinta aqasa,kawai saijinta tayi ajikin mutum ,

dan lokacin data yi qara kameel ya juyo yaga zata fada kan wani dan qaramin table na glass da mugun sauri ya taho ya riqota ta fado jikinsa ,

bude ido khadeeja tayi jinta ajikin mutum idontane ya sauqa akan fuskar kameel ,yana riqe da ita.

shikuwa kameel sakinta yayi da sauri ta fadi qasa ,banza mahaukaciya kina tafiya bakya kallon gabanki zakiyimana asarar table ,saboda baki san darajarsa ba ya fada yana harararta,

Khadeeja kuwa cikin ji haushi ta miqe tsaye tana gunguni ,table din banza inbanda mugunta qanwarka ta sanya min qafa zan fadi kazo kana cewa zanyi muku asara mugaye kawai.ta fada tana murguda baki,

Aisha kuwa wani irin bakim ciki da mugun kishine ya turnuqe zuciyarta ganin kjadeeja aqirjin kameel ,ji tayi kamar ana zuba mata wuta aqirjinta.shegiya mayya ,tsinanniya kawai ta fada cikin kwalla tab a idonta,

Khadeeja kuwa tana jinme aishan ta fada ,juyowa tayi ta kalli aishan tace"wllh mutum dai yaji tsoron duniya dan karuwanci ba sana'a bace haka kawai kinzo gaban mutum tsirara dan rashin sanin qimar kanki,banza ballagaza mai bin mazan mutane .

Tana fadar haka tayi saurin bin bayansa dan tasan halin aishan yanzu zata tara gari.

kutu kutun kaza,aisha ta fada tana miqewa da sauri ,wllh yau saian ci uwar ubanki shegiya mai kamada mayu nice karuwar ,dan uwarki ta fada tana bin bayan ta dasauri ,khadeeja kuwa tana ganin haka ta qara sauri ta taro kameel ,ai da sauri aisha ta damqo hijabin khadeeja ta baya ta fizgota ,

Wayyo Allah wuyana menayi miki kuma? Khadeeja ta fada da qarfi yadda kameel zai jiyo ,

Kutun kazan ubanki kikamin yar iska ni zakicewa karuwa mai bin mazan wasu ? Ubanki nabi ko uwarki?

Keee !!! Kameel ya dakawa aisha tsawa saketa dan uwarki, Ya fada yana hararar aishan ,

Yaya kanajin abinda tacemin wai karuwa maibin mazan wasu,

saketa nace agidan uwarwa ta fada miki hakan ni banjiba?

Wllh yaya haka ta fadamin harda cemin banza,

Kallon khadeeja yayi wacce take hawaye dan taji zafin shaqar da aishan tayi mata da gaske.

Ganin hakan yasa yayi tunanin qarya aishan keyi , "Dan uwarki saketa ko nazo na tattakaki ,banza shashasha, ke yanzu dan asara ki rasa dawa zakiyi fadan saida wannan yar cikin taki? Kuma yar aiki ?włlh kinji asara "ya fada cikin jin haushinta .

Sakin wuyan khadeejan aisha tayi cikin bacin rai tana harararta ,zaki fadamin dawa kikene yarinya.ta fada tana juyawa,

Dan dariya khadeeja tayi koba komai taji dadin yadda akayiwa aishan nan mai wulaqanta mutane,

Ke kuma wllh ki kiyayeni ,dan yaran gidan nan ba sa'oinki bane sun cuce da tsaranki ,karki qara shiga harkarsu banza kawai mayya,ya fada yana mata kallon banza ,

Ita kuwa khadeeja daure fuska tayi tare da dan turo baki , Yana kallonta duk abinda takeyi , "kut nikike turowa baki ? Ya fada cikin mamaki

Niba turo baki nayi ba haka bakina yake,ta fada tana qara turowar ,wllh yanzu ba yarda zanyi anacin bulus akaina ba ko yayane saina rama.ta fada aranta,

lallai ma yarinyar nan wai ahaka bakinta yake tsabar rainin wayo ni zata fadawa haka,kwafa yayi tare da tura qofar falon Ya shiga dan dama sunzo bakin qofa,

Itama shiga tayi dauke da sallama,abakinta duk da tasan ba kowa adakin amma ko ba komai akwai mala'ikun rahama adakin.

Zama yayi akan kujera tare da lumshe ido barci yakeji dan shi baya dadewa baiyi barciba ,

Ita kuwa kahdeeja daga wajen bakin qofar ta tsaya abinta ,kusan minti uku ,kafin ya tashi ya dauko abar tashi ta gafo wato sigari ya kunna ya fara zuqa yana fesarwa,

Kasancewar da akwai tazara tsakaninsa da khadeeja shiyasa warin bai dameta sosai ba, kuma ta toshe hancinta da hijabinta, saida yasha kusan kara shida ,sannan khadeeja ta fara dan tari dan tafara isarta ,kallonta yayi danshi yama manta datana dakin,tsaki yaja ,cikin tsawa yace ke dalla daina min tari aka koso kike ki kwasamin cutar qauyen can naku dan da alama da zaazo duba masu dauke da cutar kwalara ,to kaf gidanku sai andaukesu.

Kallonsa tayi ta dauke kai cikin tari tace "dan Allah ka daina hura wannan hayaqin wllh inada asma kuma zata iya tashi,

Keta shafa ina ruwana da asmarki ? Koni na dora miki? Ai abinda yafi asmama zaki samu ,awannan kangon gidan naku mai kama da gidan kaji,

Runtse ido khadeeja tayi cikin bacin rai batace komai ba ,murmushi yayi da ganin abinda tayi ,yasan taji haushi.

tashi yayi ya nufi uwar dakansa ya barta anan tsaye, Wanka yayi ya fito ya sanya kayan barcinsa ,tare da feshe jikinsa da turaruka masu dadin qamshi ,qaba daya part din nashi ya dumame da qamshi.

Kwanciya yayi dan barcine a idonsa sosai.

Khafeeja kuwa ganin shiru shiru bai fitoba yasa itama ta zame akan kafen ta kwanta ,tare da qudundune jikinta .motsi kadan zata zabura ta bude ido tana waige waige ,dan gani take zai iya fitowa ya cutar da ita,

Ba ita ta sami barciba sai wajen uku na dare kafin barci ya dauketa.

Kameel kuwa ko motsi baiyiba yana ta sharar barci shida yace zai hana khadeeja barci da azaba saigashi ko juyi baiyi ba tunda ya kwanta.

Koda asuba da gyar khadeeja ta tashi ,danyin sallah gashi toilet din acikin daki yake ,kuma qofar falon akulle ,gashi tana son tayi sallah,

Tana zaune shiru tarasa madafa ,lokacin salla sai qurewa yake ,jin wasu masallatan har sun idar yasata miqewa ta nufi dakin nashi, Ta jima atsaye tana tsoron shiga ,kusan minti biyar ,kafin tayi qundun bala ta tura qofar ahankali kamar wata barauniya ,

Yana fan tsakiyar wargajejen hadadden gadon nashi ya lullube jikinsa da lallausan bargo sai kanshine kadai awaje,

Barci yake peacefully abinshi. Harara khadeeja ta buga masa tare da cew Mugun mutum maqetaci ganshi ahaka kamar na Allah nan kuwa mugunta ce tab acikinsa.tsayawa tayi jimm to tatasheshine ko kuma kawai tayi shigewarta tayi uzurinta ta fito, Hakan za aiyi bari nayi alwalata kawai na bar dakin kafinma ya ganni yacimin mutunci,

Sadaf sadaf ta nufi bandakin ta kama handle din kenanzata bude tajimuryarsa yanacewa"uban me kika shigo yimim adaki ?ko sata kuma zaki fara ?"

Da sauri khadeeja ta saki handle din qofar ta juyo tana kallonsa idonsa arufe kuma yana nan yadda ta shigo ta ganshi . Qureshi tayi da ido dan itadai tabbas taji muryarsa yana magana amma kuma gashi ko juyi baiyiba, kodai kunnentane?

daina kallona mayya karki cinyeni ya qara fada ,da sauri khadeeja ta dan ja baya ,anya kuwa bashida aljanu,ta fada aranta ,

Bude idonsa yayi ya kalleta suka hada ido ,nan danan gabansa ya fara faduwa sosai tsaki yayi tare da dauke idonsa akanta ,"mayya ba damar ka hada ido da ita yanzu gabanka zai fara faduwa,ya fada aranshi.

Me kika shigo yimin adaki ?ya qara tambayarta

Dama zanyi sallane kuma ba toilet acan falin shine nashigozanyi alwala,ta fada kanta aqasa ,

Karki nemi ki takuramin fa dama yanzu ake sallar ko bakwai batayi ba ,munafuka kedai ki fadi abinda ya shigo dake yafada idonsa arufe.

Sallar asubar ce sai bakwai? Ta fada cikin mamaki ,da al' ajabi,

bude ido yayi jin yadda tayi tambayar ,kin dameni fa kin hanani barci kije kiyi koma menene ki fita ki bani guri kinji,ya fada adan tsawace ,

Ajiyar zuciya tayi tare da nufar bayin Allah ya kyauta ,ashe matsalar taka harda rashin addini ma ,wannan wace irin rayuwace haka?alwala tayi ta fito ta nufi falo tayi sallarta tare da addu'ointa ,duba agogo tayi kusan 6:5200ama amma har yanzu bataji motsin ya tashi yin sallar ba , Wllh bazan zauna dakai adaki daya batare da kayi sallah ba ,kome zaimin saian tasheshi yayi salla ,haba saikace ba musulmiba ,ta fada cikin jin haushi,

Dakin ta koma yana kwance kamar dazu yana barcinsa ,tsayawa tayi akansa tayi shiru ,taya zan tasheshi toni yanzu? Ahankali ta fara buga gefen fillon da yake kwance bugu daya biyu ,ya bude idonsa cikin barci ya kalleta amma ba sosai ba dan idonsa adan rufe yake , "meye wai " Ya fada da qarfi har saida ta dan tsorata ,

Readers Also Read