Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 7
Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 7: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 7. Bakayi sallaba kuma lokaci ya qure , Shine kikazo…
3,356 words
Bakayi sallaba kuma lokaci ya qure , Shine kikazo kika katsemin barcina akan banyi sallaba ,? Ya fada azafafe ,
Turo baki tayi aigani nayi sallar tafi barcin da kake shiyasa , Ta fada tana kauda idonta gefe ,
Wllh saina ci uwarki zakisan kin katsemin barci ,ya fada yana miqewa afusace baiyi wata wata ba ya dauketa da lafiyayyen mari tassss......
Saida wayar ta fafi ahannuna sakamakon jin qarar marin danayi,
Dan haka dai mun hadu next page taku anty mammy🙏
Inajin dadin comment dinku sosai masoya,ina gaisheku gidan aikina fans 🍒🍒🍒🍒🍒
dama wadanda basayin comment duk ina kallonku .
Mrs babi 💘💘
share and comment please,
more comment more typing , [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
GIDAN AIKINA🍒🍒
Na mammay kabeer (anty mammy)
ELEGENT ON LINE WRITER'S
Page 29/30
Wannan paging sadaukarwane ga matan gidan aikina group ,luv you much,comment dinku na jefani zundum cikin qaunarku🥰😘.
Baiyi wata wata ba ya dauke ta da mari tasssss, Yana nunata da dan yatsan,wllh kika qara tashina ina barci saina kakkaryaki nonsence,
Kallonshi khadeeja keyi dafa da kunci, "dan na fada maka gaskiya shine ka mareni ? Toh ina so kasani wllh koda zaka dinga yanka naman jikina ne akan na yasheka kayi sallah ,toh bazan fasa ba,domin haqqine akaina.
Kaji tsoron Allah ,kasani sallah itake banbance tsakanin musulmi da kafiri, Kuma itace mafubin farko aranar lahira,idan sallarka ta gyaru ,toh aiyukan kama sun gyaru, Idan sallarka ta baci ,hmmm wllh banu da tabewa ta sameka , Kuma wllh rayuwarka bata da wani amfani idan har zaka manta da gaida ubangijinka alokacin daya dace,harsai lokacin da kai kaga dama," Tadan tsaya tana maida nunfashi.sannan taci gaba.
"duk wani musulmin kwarai kamar ka bazai taba barin sallah ta euceshiba idan har yana tsoron Allah,shin kasan lokacin da mutuwa zata riskeka? Kana da tabbacin zaka rama sallar data wuceka kafin ajali ya riskeka? Shin mutuwa na sanar damu lokacin da zatazo garemu?
Amsa anan shine ,aa Dukkanmu ba wanda yasan lokacin zuwan ajalinsa,dan haka gara muyi qoqarin kyautata rayuwarmu da ibadar Allah . Kaji tsoron Allah ka kyautata tsakaninka dashi.
Tanagama fadar hakan tayi ficewarta dagadakin ta koma falo,ta bar kameel atsaye ,jikinsa yayi sanyi sosai, Zama yayi abakin gado tare da dafe kansa, Wata zuciyar na gada masa cewar gaskiya fa yarinyar nan ta fada maka ,wllh mutuwa zata iya riskarka akowane lokaci ,wata zuciyar kuma tana fada masacewar ,ba wani nan wllh rainine yasa ta tsaya agabanka tana fada maka wadannan magan ganun karka yarda da batunta ,ka koma barcinka kawai idan lokacin tashinka yayi kayi sallar.
Komawar kuwa yayi ya kwanta tare da jan bargo ya rufe jikinsa,rufe ido yayi ,dab komawa barci,amma ko kadan ya kasa dainatuna maganganunta , Zuruf ya tashi ,"kai gara dai nayi sallar kawai" Ya fada yana nufar toilet,,
Bayan yayi sallar ne yayi wanka ya shirya cikin qananan kaya ,kamar dai kullum yayi kyau sosai da sosai ,haka yayiwa jikinsa barin turare ,tare da gyara sumar kansa ,
Fitowa yayi falon ,masha Allah ko ina agyare ta gyara sai qamshi ke tashi ,lunshe ido yayi dan yana son tsafta arayuwarsa.
Tana zaune aqasan kafet ta duqunqune jikinta da hijabi, Zama yayi shima ya dauko abar tashi ya fara zuqa ,tashi khadeeja tayi dasauri ta nufi cikin dakin ,ke ina zaki ? Ya fada batare da ya kalleta ba ,
Zan gyara dakinne ,ta bashi amsa.ganin baice komaiba yasa ta shige , ita kuwa harga Allah tayi gudun warin sigarinne.
Bayan ta gama gyaran ne ta dan leqo ko ya gama shaye shayen nashi ,aikuwa ya gama din ,dan haka ta fito ta koma can ta zauna tana jiran ya bude qofar ta fita dn dora girki,
Kallon gefen datake yayi batare da ya kalli fuskarta ba,waike qazantar taki takai matsayin da wanka ma bakyayi saidai ki zauna da kaya masu datti kina wari ? Ya fada yana yatsine fuska ,
Turo baki tayi wanda ya zaka sararta ayanzu ,tace "toh a ina zanyi wankan kuma ai kayana suna cikin motarka acan na barsu,
Tab Ai wadannan tummokaran kike kira da kaya ?wllh bazasu shigomin dakiba ,wayasani ma ko kwarkwata ce ajikinsu ,ya fada cikin wulaqanci, Banza tayi dashi tana kallon gefenta. Aranta tace kamanta kudin cizone ba kwarkwata ba ,koda nake qara banyi kwarkwata ba bare yanzu,
bazakije kiyi wankan ba saina taso ,danni duk kin isheni da wari saura kadan nayi amai,
Banda soso da sabulu ,ta fada tana daure fuska dan taga alama tijara yake son yi mata,
Banza kije toilet din ai zakiga sabon soso sai wanda kika dauka ,zakiyi wanka dashi ,ni qazamine kamarke aka fada miki inzauna d soso guda daya ,ya fada yana harararta ,
Tashi tayi ta shiga dakin harta shiga ta fito ,tace"kayana fa"?
Dalla malama kije kiyi wanka ,ya fada cikin tsawa ,
Dakin ta koma ta shiga bayin, komai tsaf tsaf dashi ga soso nan kusan guda ashirin a lanqaye,wani abu mai turiri yana ta fesowa ajikinsu ,sabulai kuwa kamar shagon siyar dasu ne ,ga mayukan wanka iri iri ,acikin wata gatuwar gwaba,ruwan ta hada mai zafi acikin kwamin wanka ,mayukan ta zuzzuba ,itama,aa yo ayi banda itane , Ga mayukan wanke kai sunfi kala ashirin haka tayi ta wanke kanta da mayuka ta sanya wanna ta sanya wancan ,tayi wanka kusan sau biyar saida taji fatar ta har wani sulbi take ,ga qamshi sannan ta haqura ,wanke kayanta tayi tass ta zuba acikin boket idan ta fita saita shanya.
Wani towel ta dauko acikin jerin towels din dake cikin kwabar ,ta daura, Sannan ta dora daya akanta,
Fitowa tayi dan tasan bazai shigo dakin ba harsaita gama qilama yace saita gyara toilet da dakim zai iya shigowa,
Wllh yau kadai har wani harke khadeeja ta qara tayi kyau,su khadeeja ansamu kayan wanka hadaddu, lol😜
Daga ita sai wannan towel dinda ya dan wuce mazaunanta kadan ta fito ,dan tudun mazaunann nata sun dauke tsayin towel din,
Gaban madubinsa taje ta zauna ta shafa wanann ta shafa wancan ,haka ta shafe jikinta tass da mayukansa masu kyau ,tsada da kuma qamshi.
Wani turare ta dauka tana dubawa ,tana so ta fesa tana tsoron karya ji qamshin yace maiyasa ta shafa masa turare, Wllh saina shafa ,da wayace ya kawoni dakin nasa,ta fada tana fesawa ajikinta ,
Gaba dayafa khadeeja ta rikice da qamshi ita kanta wani dadi tajejin jikinta yayi mata, kai yaAllah ka rabamu da wahala,tafada tana taje kanta da kum dinsa ta shafeshi da mayuka sai sheqi yake, wayyo dan Allah fans kuzo kuga khadeeja ,kamar ba itaba ,gashinnan ya zubo har gadon bayanta.
Kameel kuwa tana shiga ya tashi ya fita dole saiyaje boutique Ya samo mata kaya ko kala biyar ne shegiya wllh bazata sanya min wadannan tsummo karanba ,
Dogayen riguna ya zabo mata kusan guda biyar da riga da siket guda biyu,har zai fita matar tace ,muna da pant add bra masu kyau ,ya danyi jimm toni ina nasan wannene zaiyi mata toh ,
Yace ki bani masu dan girma haka ,,
Ok sa guda nawa ? Yace koma nawane ki bani ,haka ta hada masa dozin dozin ,harda su always ,ya kashe kudi dayawa ,ya kamo hanya ya taho gida ,zakiyi bayani wannan kudin da kikasa na kashe saina fanshe abuna ta hanyar baki horo. Ya fada yana shigewa part din nashi,
khadeeja kuwa tana nan zaune dan ta leqa bata ganshi afalon ba ,
Shikuwa kameel yana shigowa ya nufi cikin dakin dan yasan wannan qazamar tananan ta maida kayan jikinta ,baisan khadeeja bata iya maimaita kayaba .
Kai tsaye ya tura qofar dakin ya shiga ,batare da sallama ba ,darararammm!!! Gaban kameel yayi wata mummunar faduwar da saida ledojin hannunsa sukazube,shikuma yayi baya zai fadi ,Allah yasoshi yana kusa da bango dan haka bangon ya kareshi daga faduwa. Sakamakon arba da yayi da khadeeja atsaye gaban madubi tana qara tahe kanta da wanann dan guntun towel din wanda sakamakon daga hannun datake yasa towel din ya qara janyewa sama sosai , Wayyo Allahna kameel ya fada da qarfi yana runtse idonsa tare da damqe mararsa data wani irin murda masa lokaci guda.
Khadeeja kuwa jin qarar faduwar abu dakuma maganar kameel yasata juyowa adan firgice dan batasan lokacin daya shigo dakin ba.
Daidai lokacin data juyo shikuma ya daqo da kansa dan gasgata abinda idanunsa suka nuna masa ,
Ya ilahi ya fada cikin wata shegiyar murya data koma kamar ta mai mura ,quri ya qure khadeeja da ido jikinsa ya fara rawa ,tunda yake bai taba ganin sura mai daukar hanakali da ruda mutum lokaci daya ba irin ta khadeja ,gaba daya kanshi ya kulle tuni ,jarabar yan maza ta motsa ,jikinsa rawa kawai yake ,yama manta dawayake tare,
Zuciyarsa ce kawia ke turashi zuwa gareta, ji yake idan bai tabata ba wllh zai iya mutuwa ko ya zauce ,
Cikin bacewar basira da tunani ya tunkari khadeeja gadan gadan .idonsa yana kan qirjinta dayafi komai dauke masa hankali,
Khadeeja kuwa tana ganinsa itama jikinta ya dau rawa tsoro fargaba da kuma danasani suka dirar mata wayyo Allahna yau kashina ya bushe meyasa na daukar masa kaya ,ganin ya tunkarota gadan gadan ,yasa ta fara ja da baya ,"dan Allah kayi haquri wllh bani da kaya anan kuma na fada maka shiyasa na daura maka towel zan wanke dan Allah Ta fada cikinn muryar shagwaba irin ta mai son yin kuka, Wanda batasan hakan qara haukata kameel yayi ba ,yana zuwa gareta kafin ta ankare kawai taji ya janyota zuwa jikinsa ya wani qanqameta ajikinsa ,sai wani irin numfashi yake sauqewa kamar wanda yayi tsere,
Zaro ido tayi cikin tsoro da al'ajabinsa toh meye hakan kuma? Na shiga uku mezaiyi min ?ta fada tana qoqarin kwace jikinta daga gareshi,
Shikuwa ai tuni ya lula wata duniyar da baisan ina bace ,cikin zafin nama ya dago fuskarta ya hade bakinsu guri daya ya fara tsotsa kamar ya sami alawa lolli pop ,
Khadeeja kuwa gaba daya ta rude [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
GIDAN AIKINA🍒🍒
Na mammy kabeer (anty mammy)
ELEGENT ONLINE WRITER'S
Page. 31/32
Kallon aisha yake cikin son cusa mata haushi yana murmushi ,dan ya fahimci tana da shishshigi ,shikuma bayasan katsalandan aharkarsa,
Kallonsa mommy tayi cikin dan zaro ido da faduwar gaba ,badai yaron nan ya kwanta da wannan shegiyar bane, Kameel ma kallon mommy yayi ganin yadda ta qura masa ido ,murmushinsa yayi ,kana yace "mommy ya dai ko kinga na canzane ?"karki damu kayanne ya baci shine nayi wanka na sauya wasu ba abinda kike tunani bane,ya fada yana dan murmushi,amma ahankali ya fada yadda aisha bazata jiba.
Ajiyar zuciya mommy tayi dan jin ba abinda take tunani bane,
Amma son har yanzu bata fito ba domin dora mana girki ,mommy ta fada tana kallon kameel , Zaraf aisha ma tace wllh mommy nima yunwa nakeji,ummi ma da maryam haka suka fita school,yaya dan Allah ka kirata tafito tamana girki,
Wani shegen kallo yabi aisha dashi ,yace "ke baki iya girkin bane ? Koke ba mace bace ? Toh daga yau ta daina dafawa ko wace shegiya abinci ,idan bazaku dafa da kanku ba saidaikuyi ta zama da yunwa, qartin banza cima zaune ya fada yana hararar aisha ,
Turo baki tayi cikin sangarta ,girki ? Ni wllh bazan iya girkiba baga yar aiki nan ba,kawai sai mushiga kitchen ,ta fada tana turo baki ,wllh bazan shiga kitchen ba .
Ubanki ne ya kawota aiki gidan dan uwarki? Toh vazatayi girkinba ,wllh ta daina yi muku girki saidai ko wace shegiya ta shiga tayi da kanta,ko kunemi mai yi muku, Ko na auro muku itane dan tazama yar aikinku ? Fansa tawace ni na aurowa kaina ita ba ruwanku da ita ,dan haka ki kiyaye . Ya fada cikin fada yana harararta ,
Kuka aisha tasanya ta bar falon ta nufi dakinta ,wllh bazan yarda ba haka kawai ya auro wata shegiya yazo yana min wulaqanci dan kawai yaga ana sonshi.
Mommy ce ta kalli kameel tace "haba son danme zaka fada mata wannan maganar kasan fa zaman ka take , Cikin tsawa yace ,for God sake momm ki barni na huta mana ,ni nace ta jirani ko nace ki ajiyeta ta zauna zaman jirana ? Banason takura fa,ya fada yana tashi yayi hanyar waje fuuuuu.
Kallo mommy tabishi dashi tana mamakin hali irin na kameel ,
Dakin aishan mommy ta nufa ta sameta tana kuka da waya ahannu tana qoqarin kiran mommyn ta ,zama tayi tana bata haquri ,ta rarrasheta akan zatayiwa tufkar hanci,
Khadeeja kuwa dankalin turawa ta dafa, da farfesun kifi sai tea data hada ,zama tayi taci abinta ta qoshi sannan ta zauna ,tana so tafita amma qofar akulle.
Tana zaune kusan awa guda saigashi ya shigo bako sallama ,ya jeho mata ,wata leda gashinan ki duba kigani wllh in basuyi miki ba saidai ki zauna haka ya fada yana zama,tare da kunna taba.
Dauka tayi batare da ta bude ba ta cusa cikin ledar kayan daya siyo mata ,tace nagode ,kallonta yayi ko meye na godiyar ? banza yar qauye.ya fada yana jan sigarinsa ,
da sauri ta toshe hancinta tana tari dan suna dan kusa ,
Ke ni kike toshewa hanci ,ya fada cikin masifa,
wllh bana son warin taba ne ,ta fada kamar zatayi kuka.
Murmushi yayi aikuwa yau zakisha warin taba ,ya fada aransa yana dariyar mugunta ," Zonan "
Ya fada yana hade ransa ,
Dan Allah kayi haquri bana son warin taba bana son hayaqi wllh, Ina da asmah ta fada amarairaice, Ok bazaki zoba kenan?
Kayi haquri dan Allah ,ta sake fada ,
Wllh idan kika bari na taso jikinkine zai fada miki ya fada cikin shan kunu,
Tashi tashi tayi ta matso dan nesa dashi kadan ,
Nan nace kizo,ya fada yana nuna kusa da qafarsa,
matsowa tayi tana toshe hanci har ta fara tari , hannunsa yasanya ya dauke nata data kare hancinta daahi ya zuqi tabar sosai ,sannan ya feso mata hayaqi ,yayi haka har saubiyu,
tari sosai ta fara kamar zatayi amai tana girgiza masa kai ,alamar ya bari bata so, Amma tsabar mugunta irin ta kameel sake kunnawa yayi ya zuqa ya feso mata, Aikuwa tuni ta fara shidewa tana tari nunfashinta yana sama sama ,sakinta yayi yaci gaba da zuqar tabarsa hankali kwance ,dan shi harga Allah yayi tunanin dan ya bartane tace tana da asma,
Khadeeja kuwa gaba daya ta fara fita hayyacinta da tari nunfashinta sai hawa yake yana sauqa idonta yana kakkafewa ,
jin abinnata yaqi qarewa ne yasa ya dago da niyar yayi mata masifa ,saodai halin daya ganta acikine ya dan tsoratashi,da sauri ya sauqo daga kan kujerar,ya durqusa agabanta ,ke ,meye hakan ? Tashi mana ,ya fada yana dan daga hannunta , Amma ina bata ma sanin abinda yake sai jan numfashi take irin na masu asma idonta akakkafe,
Innalillahi!ke meye hakan wai ?ya fada yana jijjigata,miqa masa hannu take cikin neman dauki tana kakkafewa, tashi yayi da sauri ya shiga daki ya dauko waya ,ya dawo yana jijjigata ke kitashi menene hakan wai ?
Ya fada yana jijjigata ,khadeeja fa gaba daya ta fice ahayyacinta sai nunfashi take ja tana nishi sosai ,ai wani cilli da yayi da wayar bai tsaya wata wata ba ya kinkimeta kamar jaririya yayi waje da ita, da gudu yake tafiya yana kiran,kee kitashi mana ,menene ke ,damunki? Haka ya ratsa falon da ita ahannunsa , mommy da aisha ne azaune afalon suna tufka da warwara,kawai sukaga kameel ya fito da khadeeja ahannu ranga ranga, cikin sauri suka tashi tsaye ,son meye hakan lpy kuwa ?
mommy tabi kameel tana tambayarsa,
Ko kallonta baiyi ba ya fice daga falon ya nufi waje ,
Gudu yake da ita ahannunsa ,gaba daya ya tsorata baiyi tunanin abin zaikai haka ba ,tu daga nesa yake kwalawa guard dinshi kira da gudu suka bude motar yana zuwa ya sanyata aciki shima ya shiga ,
Kanta ya dora akan cinyarsa yana dan bubbuga kumatunta, Sai kakkafewa take tana jannajiyar zuciya,
Kai tsaye wani tsadadden asibiti suka nufa ,suna zuwa aka shiga da ita emergency,
tsayawa yayi abakin qofar yana ta sintiri , Harga Allah shi ya aurotane dan ya dau fansar marin datayi masa amma bada nufin kisa ba ,baisan tana da asmah ba da bazai fesa mata iskar taba ba ,
Kusan shudewar awa guda likitocin suka fito tare da neman kameel ya bisa office , bin bayansa kameel yayi bayan sun gaisa dan da sanayya atsani shine likitan dake duba yan gidan ,
Am wato kameel yarinyar tana fama da cronic asma ne ta yadda ko yaya ta shaqi abu mai hayaqi zata iya tashi ,dan haka sai an kula da ita sosai ,ya fada yana miqa masa wata takadda ga wannan magun gunane da kuma kalar inhelar dazata kinqa amfani daita ,kasiyo ,
Karba kameel yayi tare da tambayar liktan" ya jikin nata likita"
Ba wata matsala nunfashinya ya daidaita yanzu ta dawo nml kawai mun daura mata ruwane dan ta jigata, Zaka iya zuwa ka ganta ma.
Godiy yayi sanna ya fita ya miqawa guard din takardar magaanin shi kuma ya wuce zuwa dakin da khadeejan ke kwance,
Tura qofar yayi ahanakli ya shiga ,tana kwance ga ruwa ahannunta,da alama barci ma take.
Kallonta yayi yana jin ba dadi game da abinda yayi mata ,matsawa yayi kusa da gadon datake ya qura mata ido , Hannun ya miqa ya dan shafa gefen fuskarta ,zuwa wajen lips dinta ,saikuma yayi saurin dauke hannunsa tare dafita daga dakin .
Sai wajen laasar aka sallami khadeeja dan ta warke sai rashin gwarin jiki kawai dake damunta.
Shigowa kameel yayi cikin dakin tana zaune abakin gado tayi shiru tana tuna rabon da asmar ta ta tashi sai yanzu ,dalilin wanann azzalumin mutumin, Allah shine zaiyimin sakayya,tsakanina dakai ta fada tana kawar da kanta daga kallonsa ,
Shima kawar da kannashi yayi tare da cewa tashi mu tafi ,
Kawar da kanta tayi bata kulashiba ,
Ke malama dake nake fa kinyi banza dani yar rainin wayo kai,ya fada ahasale .
kallonsa tayi tare da gallamasa harara,ta kawar da kanta ,
Ke nikike harara ya fada yana nufota cikin jin haushi......
Wllh agajiye nake yau kuyi haquri da wannan , Taku anty mammy🙏
mrs babi 💘
share and comment More comment more typing. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
GIDAN AIKINA 🍒🍒
Na mammy kabeer (anty mammy)
ELEGENT ONLINE WRITER'S
Page 33/34
Kee! Ni kike harara? Ya fada yana nufota cikin jin haushi,
Yana zuwa ya fizgo hannunta ,yana nufar qofa da ita ,
Da mugun sauri kuma afusace khadeeja ta fizge hannunta ,tana kallonsa ido cikin ido,
Kameel kuwa ji yayi gabansa ya fari ,rass! rass!! rass!!!
Da sauri ya kwar da idonsa daga cikin nata , Ke dalla kizo mutafi karki bata min lokaci , ya fada yana qoqarin qara riqo hannunta,
Karka kuskura ka qara tabani ,mugu azzalumi,ta fada cikin tsananin fushi sosai tana nunfashi da sauri,
Kai azzalumine ,baka da imani ,nayi dana sanin sanin ahalinka gaba daya ,baka tsoron Allah, Tunda har zaluncinka yakai matsayi kayi qoqqarin kisan kai,
Menayi maka ? Me natsare maka arayuwa ? Meyasa kuke qoqarin ganin bayana kaida ahalainka ? Dan Allah kubar rayuwata ta huta ,wannan azabtarwar taku tayimin yawa ,nimafa mutum ce ba dabbaba,ina buqatar hutu arayuwata kamar yadda kuma kuke buqata ,ta dan tsaya sakamakon nunfashinta dake cikowa dan cikin fushi da bacin rai take maganar,
Kameel kuwa ya zama speechless,ido kawai ya zuba mata cikin mamaki ,ashe ta iya masifa haka itama?
Khadeeja kuwa ci gaba tayi ,kai ba mutum bane ,kai wata halittace tadaban mai izgilanci da tatin qeta, Ba abinda kasani arayuwarka sai cin zarafin dan adam ,kana ganin hakan shine zai banbanta tsakaninka da talaka? Kayi kuskure ,wannann halayyar taka saidai ta kaika wuta , Baka kula da ibadarka ,baka bawa mahaifanka daraja ,sannan baka bawa al'umma daraja ,me kake buqata arayuwarka ? Kasani Allah shibe ziyimin sakayya atsanina daku , Ni marainiyacemai qaranci gata ,bani da kowa sai Allah ,kuma dashi na dogara Shine gatana ,kuma shne gatan mai gata,Allah yana sane dani,ta qarasa tana fashewa da kuka dan sosai zuciyarta tayi rauni. Durqushewa tayi agurin tana kukanta ma tsuma zucyar mai sauraro.