Kenza eBookz

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 8

Complete book: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy)Chapter 8 of 21FantasyBy Mamy Kabir (aunty Maamy)

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 8

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 8: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 8. Kameel kuwa wani irin tausayintane yake qoqarin…

3,340 words

Kameel kuwa wani irin tausayintane yake qoqarin dannan kansa cikin zuciyarsa ,marainiya kuma? Kenan wancan mutumin bashine mahaifinta ba? Ya salam,ya fada yana nufar inda take ,

Tsayawa yayi akanta ya rasa me zai cemata , "Kitashi mutafi gida"ya fada asanyaye,

Kuka kawai khadeeja keyi bata ko kulashiba ,

Ki tashi mana ,kidaina wannan kukan zai iya dawo miki da ciwonki fa ,ya fada adan tausashe ,wannan shne karo na farko da kameel yayiwa khadeeja magana cikin tausasawa.

Ganin batada niyar tashi yasa shi miqa hannu ya riqo hannunta ya tasheta tsaye,

Fizge hannunta tayi cikin masifa,"nace karka qara tabani banaso fatana ayanzu shine mutuwa tazo ta daukeni kamar yadda tadauki iyayena ,har nazama marar gata adunya ka sakemin hannu ,"ta fada tana ture hannunsa da qarfi ,

Kameel kuwa gaba daya ya rasa abinyi dan yaga yau anqure mai haquri ,sai kokawa take dashi saita kwace hannunta.

Kawai janyota yayi ya rungume aqirjinsa ,qam ,

Tureshi khadeeja take tana kuka ,amma ya riqeta qam qam aqirjinsa ,yana hura mata iska akunne yana shiïiiii ,irin yadda ake rarrashin yara.

Gajiya khadeeja tayi da kokawar ta kwanta lubb aqirjinsa tana kukanta, dan azahiri tana buqatar kafadar dazata kwanta akai tayi kukanta son ranta.

Kuka take sosai ta qamqame rigarsa ta baya ,shikuwa yana rungume da ita yana shafa bayanta ,

Tunda yake bai tabajin tausayi ya kamashi irin na yauba ,dagajin kukan da yarinyar nan keyi ta jima da qunci acikin zuciyarta.

Kusan minti talatin suna ahaka ,kameel idonsa aruntse yake dan tsayiwar tasu ta jefashi cikin wani yanayi sai nunfashi yake sauqewa yana qara rungumeta sosai ajikinsa ,

Khadeeja ce ta dawo cikin hayyacinta tajita ruqunqume ajikinsa kamar zai tsaga mata qirji,kicikici take dan ta rabu dajikinsa ,

Jin hakan yasashi bude idanuwansa da suka sauya kala lokaci daya sun qanqance sunyi ja lips dinsa ma yayi ja har wani sheqi yake ,

Tana barin jikinsa ta nufi qofar fita, Binta yayi dakallo cikin kasala,saida ya saisaita kanshi kafin ya bi bayanta ,harta shiga motar , Shiga yayi shima guard yaja motar suka nufi gida.

Mommy ,aisha ummi dakuma,maryam duk suma zaune afalon mommy na waya da abba yana fada mata gobezai dawo dan baya qasar dama.

Kawai saiga khadeeja da kameel sunshigo ,da ledoji ahannunsa,na maganin khadeeja ,

Ko kallonsu batayi ba ta wuce bangarensu kai tsaye ,

Duk kallo suka bita dashi ruuuuu,cikin mamaki lallai yarinyar nan ta sami guri mommy kiga ko gaisuwa baki isa samu agurintaba? Cewar aisha ,

Gaskiya anty aisha akwai abinda ke damunta dan ba halinta bane,nifa wllh yanzu tausayi take bani ,cewar maryam tana bin hanyar da khadeeja tabi da kallo.

Kafin kowa yayi magana kameel ya zauna kusa da mommy yace mommy akawo min abinci ina dakina ,

Son kafita dazu da yarinyar nan ahanunka ranga ramga ,kuma bakayi mana bayani ba meke faruwane? Dan shiru yayi kafin yace "momm bata da lpy ne asma ke damunta,"ya fada yana miqewa.ya nufi dakin nasu,

Tana kwance akan kafet dan sosai takejin kasalaajikinta . Ajiye ledar yayi kafin ya kalleta, Amm kitashi ki koma daki ki kwanta nan akwai sanyi sosai ,ya fada danshi ya rasa me zai cemata ne,

Ko kallonsa batayi ba taci gaba da kwanciyarta,

Ganin yau fa khadeeja asama take itama yasa kameel tattare hannun rigarsa ,kawai saiji tayi anyi sama da ita ,ya nufi dakin da ita .

Kallonsa tayi cikin jin haushi tace sauqeni malam ,ta fada tana cin magani,

Naqi asauqekin ki sauka inzaki iya ,ya fada yana kallon bakinta ,

Kawar dakai tayi tare dadaure fuska ,bai direta ko inaba saikan lapiyayyen gadonsa mai shegen taushi da qamshi, Ya na ajiyeta ya lullubeta da bargonsa mai laushi ,maimakon ya tashi saiya zauna bakin gadon yana mai ci gaba da kallon bakinta ,dan cintar kansa yayi da son yayi mata kiss abakin ,

Hade rai khadeeja tayi tare da turo masa bakin ,ni kadaina kallona bana so,ta fada cikin turo bakin ,

Ai kameel gani yayi kamar ta turo masane dan ya tsotsa ,baiwaniyi nisan tunaniba kawai ya dora bakinsa kan nata ya fara tsotsa ,

Khadeeja kuwa dan zabura tayi tare da zaro ido dan abin yazo matane abazata,hannu tasa dan ta ture kanshi amma ya riqe hannun nata ,yana ci gaba da kisaing dinta,

Lumshe ido khadeeja tayi dan jin abinda ke ratsa kwakwalwarta mai kama da dadine ko mebe oho,sun dauki tsawon lokaci ahaka ,kafin khadeeja tayi yunquri ta kwace bakinta tare da juya masa baya.

Shima da sauri ya nufi toilet yana mamakin kasan, yanzu nema yake ya zama jarababbefa ,motsi kadan zaiji ya farajin feeling yazo yana abin kunya agaban wannan yarinyar ,

Wanka kawai yayi tare da dauro alwala dan baiyi laasarba ,fitowa yayi dagashi sai rigar wanka ajikinsa. Ya zauna gaban mudubi ya fara shafe shafe kamar mace ,khadeeja na kallon ikon Allah mutum sai iyawar tsiya ,ji dan Allah saikace wata mace ya shafa wannan ya shafa wancan ,dan rainin hankali .

"yane haka da kallo kamar zaki cinyeni"

Khadeeja ta cinkayo muryarsa ,ashe yana kallonta ga mudubi, Ai dasauri ta janyo bargo ta rufe fuskarta gabanta na faduwa ,wayyo ya ganni wllh !ta fada tana dafe qirji,

shikuwa kameel murmushi yayi dan tabashi dariya yadda tawani firgita ,batayi zaton yana kallonta ba,

Kayansa ya dauko ya yasanya ko ajikinsa wai khadeeja na dakin dan yasan bazata qara kallonsa bama bare taganshi yana sanya kaya.

Muryar maryam ya jiyo tana sallama ,yace ta jirashi yana fitowa, Abinci ta kawo masa shinkafa da miyar qoda sai lemon kwakwa ,yawwa auta sannu da qoqari ,ya fada yana shafa kan maryam , Murmushi tayi tace yaya ina khadeejan ya jikin nata,

dan jim yayi yana kallonta ,kafin yace tana daki da sauqi maryam, Yaya inje in dubata,ta fada tana kama hannunsa, .tsintar kansa yayi dajin dadin abinda maryam din ta fada ,cikin murmushi yace yes goahead dear.

Tashi maryam tayi ta shiga dakin , Khadeeja ! Ta fada ahankali dan tayi tunanin ko baeci take,

Khadeeja kuwabude fuskarta tayi tana kallon maryam ,

Murmushi maryam tayi ta zauna kusa da khadeejan ,tace ya jikin naki ashe bakiji dadiba ,

Cikin mamaki khadeeja ke kallon maryam ,yau kuma marymce harda tambayarta ya jiki?

Amma saitayi murmushi tace"da sauqi "

toh Allah ya qara sauqi, Ameen tace ,duka sukayi shiru saboda rashin sabo.

Bari na wuce saina dawo ko,maryam ta fada da qoqarin nuna khadeejan kulawa.

Nagode khadeejan tace ,lokacin da maryam zata fita,

Murmuahi kawai maryam tayi ta fice daga dkin.

Maryam zubamin abincin yunwa nakeji fa,yaya toh ita kuma mai jinyar fa, Toh zuba mata itama ,ya fada yana gyara zamansa.

Zubawar tayi ta miqa masa sannan ta kaiwa khadeeja ma .

sosai khadeeja ke mamakin maryam Allah kasa ta shiryu ne ta gane gaskiya.

Bayan kameel ya gama cin nashi abincinne ya leqo dakin dan ganin kota kammala amma yadda aka kai abincin haka yake har yanzun ,ji yayi yadan damu tun safe rabonta da abinci fa,ya fada yana qarasawa cikin dakin .

Zama yayi abakin gado ya yaye bargon ,ido suka hada cikin rashin sani ,gaba dayansu saida gabansu yayi mugun faduwa damm dammm da sauri kowaya janye idonsa daga kan dan uwansa,

Maza tashi kici abincin nan , Ya fada cikin bada umarni, Naqoshi banjin yunwa,ta bashi amsa,

Tashi nace ko kuma wllh indagaki da kaina,ya fada cikin hade rai, Tashi tayi dan ta fahinci daga mutum ba komai bane agurinsa.

Miqo mata plate din yayi ,oya kicinye yanzu ya fada yana kallon bakinta,

Karba tayi ta faraci ahankali ,

Shikuwa sai satar kallonta yake ,dan yaudin gani yayi kamar ta sauya wani tausayinta yakeji da kuma son kallon idonta ,saidai yana tsoron yadda gabansa ke mugun faduwa duk sanda suka hada ido.

Suna zaune shiru kowa da abinda yake tunani aransa ,shikan kameel tausayine ke neman sashi ya manta da qudurinsa , ita kuma khadeeja mamakine ke neman kasheta azaune ,dama yana da kirki haka ? Amma yake abu kamar marar imani kodan ai dole ya nuna min kulawa tunda ya kusan sheqeni,

Kamar abin hadin baki suka dago kai atare suka kalli juna ,da sauri koqa ya dauke kanahi cikin faduwar gaba ,

Amma kameel sai cewa yayi "wai meye kike ta kallona ne kardai kicinyeni"

"Turo baki tayi mezanci anan din ,ta fada tana murguda baki,"

Ke nidinne mezakici anan ? Lallai ma yarinyar nan kin rainani dan bakisan yadda yan mata ke qoqarin cinyenin bane shiya kikace hakan kodan ke ai yarinyace,ya fada yana tabe baki.

"Tab basu da hankaline ni banga abin qoqarin cinyewa nan ba mutum kamar buhun hatsi ," ta fada tana kawar da kanta

kee nine kamar buhun hatsin? Aikuwa yau zakiga buhun hatsi da idonki ,naga alama kina son rainani amma idan kikaji nauyina zki nutsu ,ya fada yana ,qoqarin hawa kan gadom gaba daya,

Da sauri ta ajiye flate din abinci ta ja baya ,wayyo dan Allah kayi haquri da wasa fa neta fada cikin shagwaba ,

Shikuwa kameel bai fasa hawa gadonba tare da janyo ta yana qoqarin kwantar da ita , Ai yau tunda kike min buhun hatsi zan nuna miki buhun hatsinne ni,

Ganin da gaske neman danneta yake yasa da sauri ta fada jikinsa ta qamqameshi sosai dan Allah ka bari natuba ,ta fada tana tura fuskarta cikin rigarsa da maballin ya bude

Dif wutar kameel ta dauke ya wani lunshe ido cikin yanayi na jin dadin abinda takemasa ya rungumeta ajikinsa sosai yana shinshinar wuyanta ,

Nan danan ya fara sauqe nunfashi kamar wanda yayi danbe ,yawo ya fara da hannunda ajikinta yana shafawa ,cikin shauqin buqatuwa ,

Da sauri khadeeja ta janye jikinta jin abinda yake mata ta maza gefe shikuwa miqa mata hannu yayi cikin sarqewar mutya yace come back here!

Noqe kafada khadeja tayi cikin tsoro tace aa banaso ,ta fada tana sauqa daga kan gadon ,taku daya biyu ,kawai taji an rungumeta ta baya ,

Please karki tafi kitsaya i just want huge u ,ya fada yana cusa kansa awuyan khadeeja tare da dora hannunsa kan dukiyar fulaninta ,da sauri duka suka lunshe ido dan jin wani baqon yanayi dake ziyartarsu gaba daya ,

Khadeeja dai tsorone dakuma fargaba sai wani zumm zumm da taji jikinta nayi lokacin da hannunsa ya sauqa akan qirjinta.

Shikuwa kameel rudune da kuma fargabar shima sanna wani rin feeling dake ratsa sassan jikinsa ,sosia ya fara yawo da hannunsa kana qirjinta yana nunfashi idonsa arufe ruf ,

Qoqarin gwacewa khadeeja keyi dan ita bata aon wannan abubuwan da yake mata sam ,

Please kasakeni bana so ta fada da shirin yin kuka , Ko kulata baiyi ba yaci gaba da aikinsa, Kawai tasanya masa kuka sosai ,

Bashiri ya dawo cikin hayyacinsa ya saketa da sauri yana dafa bango idonsa sunyi jajur dasu ,

Am amma .........sorr....ryyyy ya fada ararrabe ,yana nufar qofar dakin ,budewa yyai ya fice daga part din gaba daya,

Yana zuwa falo sukayi kicibis da mommy ,kallo tabishi dashi ganin yadda yake tafiya yana hada hanya kamar wani dan kwaya ,idonsa sai lumshewa suka suna budewa ,

Da dauri ta tareshi son lpy kuwa meke damunka ,baice mata komai ba ya nufi qofar barin falon .

Nashiga uku mommy ta fada dan kallo daya tayiwa kameel ta fahimci halin dayake ciki ,

Cikin fushi ta nufi part din nasa ,yau saina ci uban wanna. shegiyar dake qoqarin sauyamin tunanin yaro ta fada tana bude qofar dakin ,

Dasauri khadeeja ta daqo ta kalli mommy ,tana qoqarin jan rigarta tana zazzabo qasa........

Toh reader masoya ,na barku lpy sai mun hade,danjin hukuncin da mommy zata zartar akan khadenku.inajin dadin comment dinku sosai yana ratsani🥰🥰🥰

Taku anty mammy🙏

mrs babi 💘💘

share and comment please. More comment more ttping. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

GIDAN AIKINA 🍒🍒

Na mammy kabeer (anty mammy)

ELEGANT ONLINE WRITER'S

Page. 36 /36

Da sauri khadeeja ta dago kanta ,ta kalli mommy,tana qoqarin gyara rigarta ,data zazzabo qasa ,

Kallon shegege mommy tabi khadeeja dashi cikin tsana da jin haushi,

Yayi ,ba shakka yar matsiyata kinsami guri ,wato kece har uwar daka ,kina yiwa dana karuwancin ko? tukunnama mwkikwyi masa yanzu na ganshi ya fita aburkice? Kinaso ki iskantamin shi ,shegiya dama daganin idonki wannan kinsan maza ,shine zakisamin nawa dan alungu ki batashi,

Cikin zubar hawayekhadeeja ta kalli mommy, wllh hajiya ba abinda nayi masa ,shine shine ta kasa qarasawa tana kuka,tare da jan rigarta sama,

Fahimtar ba komai ne yasa mommy cewa," Toh wllh idan kika sake koda wasa wani abu ya shiga tsakaninki da kameel ,saina salwantar da rayuwarki,saina batar dake ko insa ayanke miki wuya ,"

Kina jina ko ya zomiki da wata buqata karki sake ki yarda dan ubanki ,kinjini,ta fada tana murdewa khadeeja kunne,

Cikin jin zafi khadeeja ta amsa da "naji "

Rangwashi ta zabga matamai zafi akai ta tureta ,taana harararta,

Saura kadan khadeeja ta fadi Allah dai ya taimaka bata fadinba ta dafa bango ,

Ficewa mommy tayi daga dakin,bakin gado khadeeja ta nema ta zauna ,cikin tunanin wanna wace irin matace haka ? Yanzu har kizo kinayiwa matar danki kashedi akan karta bari ya kusanceta? Lallai qiyayyar tayi nisa ,wato bata son hada zuria dani, Hmmm kikwantar da hankalinki hajiya nima bana fatan danki yasami damar kawarmin da budurci,kuma bana fatan hada zuria da mace irinki mai son kanta ,

Ta jima agurin tana tunanin rayuwa, kafin ta tashi ta shiyi dan taji anfara kiran sallah.

Sai bayan sallar ishsha ,sannan kameel ya dawo gidan ,lokacin khadeeja na sallah,

Zama yayi afalon na dan lokaci kafin ya shiga dakin ,wanka yayi ya dauro alwala shima yayi salla tare da shiryawa,cikin wasu hadaddun riga da wando iri daya sai hula kasancewar garin akwai dan sanyi,

Fitowa yayi zuwa falon tana zaune ta idar da sallar ,tayi shiru da alama tunani take ,

Zama yayi yana dan satar kallonta ,gani yayi kamar tana cikin damuwa ,ta tsurawa guri daya ido,

Samun kansa yayi da son sanin damuwarta,

Baki da lpy ne? Ya fada batare da ya kalleta ba ,

Dago kai tayi ta kalleshi kafin tasunkuyar da kanta ,tace" lpyta qalau"

Kallonta yayi yana son sake tambayarta amma bayaso taga kamar ya damu da itane sosai.

Waya ya dauka ya kira maryam ,tana dauka yace ,maryam abinci fa bazan sauqo nan ba, Ki kawomin yanzu , Ya kashe wayar.

mintuna kadan da gama wayar maryam ta shigo dakin da sallama,ajiye abincin tayi sannan ta zauna kusa da yayan nata ,tadan kwanta ajikinsa ,cikin shagwaba tace"yaya ina khadeejan kuma ?

Kallon inda khadeejan ta takure yayi ,sannan ya nunawa maryam ita da hannu,

Juyowa tayi da sauri dan ita bata ganta ba sanda tashigo dakin,

Sauka tayi tazo kusa da khadeejan ta zauna itama aqasan ,cikin kulawa tace,

Khadeeja ,ya kika zauna anan ?ko jikinne ?

dagowa khadeeja tayi tana kallon maryamdin ganin yanzu kamar ta damu da ita yasa ,tadanyi murmushi tace"ba komai kawai nafijin dadin zama anan dinne"

Noo ! Maryam ta fada tana kama hannun khadeejan ta miqar da ita ,tace kidaina zama aqasa ,nan dinfa gidan kine ,ko kina da damuwar wani abunne yanzu? Ta fada tana riqe hannayen khadeejan bayan ta zaunar da ita akan kujera,

girgiza kai khadeejan tayi , Please khadeeja ki kwantar da hankalinki nann gidankine ,sannan ina mai neman afuwarki akan abinda ya faru abaya ,sharrin shedanne in sha Allah hakan bazata sake faruwa ba kinji,ta fada tana kallon khadeejan .

Sosai khadeeja taji wani sanyi aranta ,koba komai hakan na nuna maryam ta nutsu kuma tasan darajar dan adam ,

Bakomai anty maryam nagode,ta fada ahankali kanta aqasa,

duk abinda suke kameel na kallonsu ,ji yayi yaji dadi sosai daganin murmushinta ,haka kawia yanzu yake son ganinta cikin farin ciki ,

Yaya bari inbarku kuci abincin ko,maryam ta fada tana miqewa. Khadeeja saida safe,ta fada tana mata murmushi , Itama khadeejan murmushi tayi ,ashe haka maryam keda kirki? Alhdllh ,Allah ka qara shiryar damu.

Bayan fitar maryam ne ,suna zune shiru ,sai satar kallonta kameel keyi ,can dai ta dago kanta suka hada ido carab ,da sauri suka janye idonsu daga kan na juna kowa gabansa na bugawa.

Ki zuba mana abincin mana ,ya fada yana qiqarin kunna tabarsa,

Kallonsa khadeeja tayi tare da miqewa da sauri zata bar dakin ,

Inazaki ,ya fada da sauri ,tsayawa tayi ,batare da ta juyoba ,tace "zan fitane idan ka gama sha saina dawo"

Kallon bayanta yayi tare da kallon tabar hannunsa ,yaufa duka baisha tabar nan ba kuma duk sabida itane bayason ya cutar da ita da hayaqin tabar, Ajiyewa yayi ,tare da cewa "noo come back " Na fasa sha ,ya fada yana maidata cikin kwalinta duk da masifar son shan dayake, Dawowa tayi ta zuba masa abincin sanan itama ta xuba ,

Ta faraci ahankali sam bakinta ba dadi,haka takeci,

Shima cin nashi yayi cikin qanqanin lokaci yaci ya gama ,shima dai bawani cine dashiba , Dauke kwanikan tayi ta kaisu kitchen ta wanke ta ajiye ,sannan ta dawo falon ,

Labarai yake kallo ,zama tayi ,can ta fara gyangyadi ,alamar barci takeji,

Kallonta yayi lokacin datake gyangyadin ,kamar wata yar yarinya ,dariya yayi qasa qasa,

Yau kam bazata kwana anan gurin ba dole ta kwana akan gadona ,amma tayaya zan kwanta tareda ita kuma gado daya?

Kee tashi kije ki kwanta mana kina ta faman barci harda munshari yar qauye,ya fada yana kallon qafarta

ni wllh bana wani munshari ta fada ashagwabe tana turo baki ,

Ok qarya nake miki kenan ko ? Wayasani ,ta fada akan lebenta, Me kikace ? Ya tambaya dan yana kallon bakinta ,

bakomai fa ,ta fada again cikin shagwaba , Ji yayi wani abu na tsarga masa dan sai yaga shgwabar tayi mata kyau sosai,,

Oya tashi kishiga daki kikwanta,ya fada yana kallonta ,

Daki kuma ni anan zan kwanta ,

Kee bana son musu fa kona fara wasa dakene? Ya fada a yanayinsa na asalin kameel dan yaga tana son tayi masa musune ,shikuma bazai qara barinta ta kwana anan ba.

Kasancewar khadeeja mai haquri sannan bata iya musu ba yasa ta tashi ta nufi dakin ,kwanciya tayi akan qatuwar dardumar dake cikin sakin daga can gefe ,kasan cewar dakin qatone.

Kameel kuwa saida ya kammala kallosa ya zuqi abar tashi sanna ya shigo dakin taba jinsa tayi lamo kamar mai barci ,kallon gadon yayi bata kai ,dan haka ya fara kallon dakin,

Can ya hangota akan darduma ,ta wani duqunqune ahijab,

Kutt! Ke maye hakan zaki zo ki wani kwanta min anan gurin bakiga gado bane? Ya fada yana tsayawa akanta ,shiru tayi kamar mai barci,

Ok tunda kinyi barci bari na maidake kan gadon dan , bazaki kwantamin anan gurinba,ya fada yana qoqarin daukarta,

Da sauri ta tashi ,zaune , Nikarka tabani zan tashi da kaina ,ta fada ta na turo baki,

Dariyar gefen baki yayi ashe kina jina ,yarinya dakinyi kwanciyarki ai Ya fada yana kallonta,

Tashi tayi tana turo baki ,hak kawai saikace saina kwanta akan gado ,ni bansaba kwana akan gadoba ai,

Kee tsaya ma tukunna ,wai ahaka zaki kwanta bakiyi wanka ba ,toh wllh maza ki wuce kiyi wanka qazama ,ahaka zaki kwanta ga kayan da kika wuni dasu ajikinki,ya fada yana hararar ta.

Toh ni wai wankan me zanyi kawai dan zan kwanta,ta fada tana tura baki ,

Oho miki amam saikinyi wanka zaki kwanta min adaki,

nufar bayin tayi tana qunquni,bayan tayi wankanne tafito dama kuma tana son tayi wanka amma ta rasa tayaya zatayi wankan .

Fitowa tayi da kayanta ajikinta ,ta tsaya ajikin madubi ta dan shafa mai sanan tayi zamanta,

Ke wllh idan baki tashi kinzo kin kwantaba zan bata miki rai ,kuma kicire wadanna kayan qazama kawai ,

Toh bani da kayan barci ,ni da kayana nake kwanciya,

Tashi yayi ya bude sif din kayansa da bazakayi tuananin sif bane bama agurin ,jerin kayan barci kalakala ajere,

Daya ya dauko mata riga da wandone na maza ,ya ajiye mata gashinan kisa wannan amma bazaki kwanta min agado da kaya masu dattiba ,ya fada yana komawa kan laptop dinsa ,dan wani gida yake zanawa ,kasancewar abinda ya karanta kenan,

Readers Also Read