Kenza eBookz

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 10

Complete book: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy)Chapter 10 of 21FantasyBy Mamy Kabir (aunty Maamy)

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 10

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 10: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 10. Haka kawai ji yadda yasa na qona abincin ,ina…

3,358 words

Haka kawai ji yadda yasa na qona abincin ,ina girkina yazo yana ta latseni ba dole abinco ya qone ba ,ta fada tana sauqe tukunyar , Kawai mutum Baida aiki sai son ya tabaka yayi ta saka cikin wani hali ,kuma sai anjima yace kaine da laifin wllh .ai bazan qara yarda ba ta fada tana daukar bra dinta da rigarsa ji fa ni nama nata da wata bra,ta fada tana juyowa da bra ahannu ga rigarsa akafadarta ,

Tsak ta tsya tana zaro ido ,mommy ce atsaye abakin qofar kitchen din kuma ga dukkan alamu taji abinda take fada .....

Toh fa sai mun hade danjin me mommy zata ce akan wannan abun data gani... Taku anty mammy🙏

mrs babi💘💘

share and comment please ,

More comment more typing, [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

GIDAN AIKINA🍒🍒

Na mammy kabeer (anty mammy)

ELEGANT ONlINE WRITER'S

Page. 37 /38

Khadeeja!!! Ya fada da qarfi ,cikin mugun gudu ya nufi gurin swimming pool din ,

Cikin wani irin dan bala'in bacin rai, da wani irin qunan zuciya yake kallon aisha ,jikinsa har wani rawa yake ,

Tsoro ,rudani dakuma firgici sune suka bayyana qarara akan fuskar aisha,ja take da baya tana cewa"yaya ka tsaya kaji nayi maka bayani"

Wata damqa da kameel yayiwa aisha saida ta fasa wani uban ihu ,wayyooo mommy ,dan Allah yaya ka tsaya kaji wll....

Dif maganarta da sautinta suka dauke na tsawon wasu daqiqa ,sakamakon wani bahagon mari da kameel ya kifa mata ,

Kafin ta dawo hayyacinta ya qara mata wani marin ,cikin tsabar masifa da bala'ee yake kallon cikin idonta,

Wllh !wllh!! Wllh!!! Idan wani abu yasami matata saina wulaqantaki,saina dai daita rayuwarki ,banza karuwa,ya fada jikinsa na bari ,kuma kijira hukuncin dazan dauka akanki,

Ya fada yana janta qiiii har bakin swimming pool din ,bai jira wani abuba ,ya hankadata da mugun qarfi,yana huci kamar kububuwa.

Khadeeja kuwa lokacin da aisha ta watsata acikin ruwan ba sani ba sabo kawai tajita tsamo tsamo acikin ruwa ,wani irin tsorone ya dabaibaye zucoyarta ,bata son ruwa ko kadan, bare ita da bata iya ruwaba ma,

Ihu taje tana miqo hannu,tana neman dauki ,gaba daya ta tsorata sai shan ruwa take , Kanta harya lume sai hannu take miqowa cikin razani da fidda rai ,

Wata super kameel yayi saigashi acikin ruwan kamar kifi ,kamota yayi yadagota sama ,ya ajiyeta abakin ruwan ,ko hannu bata iya dagawa saboda ta galabaita cikin ruwan .

Fitowa yayi. yarinqa danna cikinta saida ruwan ya fita kafin ya sungumeta ,yayi prat dinsa da ita cikin sauri sauri yake tafiya,

Daki ya wuce da ita ya kashe ac da duk wani abu dazaisa dakin sanyi ya kunna na urar dumama daki ,sannan ya tsaya yana tunanin mafita ,

Gaba daya rawa jikin khadeeja yake kamar mazari tsabar sanyin dake kadata, "Sanyi nakeji ka taimakamin ,ka lullubeni " Khadeeja ta fada cikin rawar murya tana jikinsa,

Yana daga tsayen ya fara cire mata kayan jikinta ,tass ya cire mata bai bar komai ajikinta ba ,kwantar da ita yayi akan gadon snnan shima ya fara cire nashi kayn ,dagashi sai boxer ya hau gadon tare da janyota jikinsa ,ya lullubesu da qaton duvet dinsa mai laushin gaske,

Zare boxern yayi shima ya zama nick ,

Sannan ya matseta ajikinsa sosai yana murza hannayenta .

Wannan itace hanya mafi sauqi dazata sami sauqin sanyin dake damunta ,shine dalilin dayasa yayi musu hakan .

Khadeeja kuwa jin dumin jikinsa yasa ta qara qaqumeshi sosai tana manna jikinta danashi ,dan samin sauqi.

aisha kuwa tsabar baqin ciiki da takaici zamanta tayi acikin ruwan tana rusa kuka kamar ba gobe, wayyo Allah na mommy na shiga uku wllh ya fara sonta ,kalli abinda yayi min danan turata cikin ruwa ,ta fada tana shafa gefen bakinta daya fashe tsabar shigar mari, Ga goshinta yayi qulu ,saboda bigewar datayi lokacin daya turota cikin ruwan .

Khadeeja kuwa tun tana karkarwar sanyin harta daina dumin jikinsu na ratsa juna ,tuni barci yayi gaba da khadeeja tana manne ajikinsa, Shikuwa kameel dumin jikinta da kuma kayan alatunta sune suka sauya masa yanayi sai mutsu mutsu yake yana rufe ido ,

jin yadda hajiya babba ke harbin sa ,yasashi dan mace qafarsa ,"haba ke kuwa karki bayar dani mana ,dan Allah kinutsu please ya fada yana qara matse cinyarsa.

Rufe ido yayi yana tunanim irin hukuncin dazai daukaakan aisha ,wllh ya tsani yarinyar nan yanzu muguwa ce ,tacika qeta ,yanzu da Allah bai kawoshiba fa shikenan saidai ruwa ya cika mata ciki hartamutu?

Dammm ! Gabansa ya fadi nooo in sha Allah hakan mabazata faruba ,ya fada yana qara qanqame khadeeja ajikinsa, Runtse ido yayi aqoqarinsa nayin barci,amma ina !!abokiyar kwarai tace bata san wannan ba,lol

Sai wajen qarfe 3:30pm suka tashi daga barcin ,kamar abin hadin baki atare suka farka , Zare jikinta khadeeja tayi ,zuciya daya ta miqe zata sauka , Kawai tajita ba kaya ,da sauri ta koma ta kwanta tare da janyo bargon zuwa jikinta,gabanta na faduwa dan ita batasan ahaka take bama ,

Dukda dakin akwai duhu ,hakan bai hana kameel ganin abinda tayi ba ,dariya ce taso kamashi ,yace ,"hmmmm abinda na gama tattabawa shine zaki wani rufe ?garama ki tashi danni kunna haske zanyi ," Ya fada yana qoqarin tashi abinsa,

Zaro ido khadeeja tayi na shiga uku wannan wane irin mutum ne? shi sam bayajin kunya arayuwarsa, Qara qudundunewa khadeeja tayi cikin bargo tana kallon ikon Allah ,sai kuma ta kama tari da atshawa,alamar mura ta kama ta. Tunani take aranta wai me tayiwa aisha ne haka da zafi ?take neman rayuwarta,yanzu badan Allah ya kawoshiba fa shikenan mutuwa zatayi ?

Kallonta kameel yayi ,wato har mura ya kamata kenan? Ya fada yana shiga toilet da towel a west dinsa.

Wanka yayi ya fito lokacin harta sanya dogiwar riga ajikinta ta lulluba dan kwali tana zaune ,hawayene keta sintiri akan kyakykyawar fuskarta,

Yana fitowa ya tsaya yana akllon yadda take hawaye,ji yayi ransa yayi wani irin mugun baci ,sosai yakejin kamar ya shaqe aisha ta mutu ,shegiya yar naci ,wllh saina ci ubanta.

Mai yashafa tare da sanya kaya masu dumi dan ana sanyi agarin jiya sun sami ruwa kasancewar farkon damunane.

Har lokacin khadeeja na kuka ,zama yayi abakin gadon tare da dan kallonta ,so yaje ya rrarsheta ,amma ta ina zai fara? Mezaice mata ? Tace meye ya damu na ita haka?kai ina banason raini wllh ,ya fada ranshi yana tabe baki,

Ki tashi kije kiyi wanka zakiji dadin jikinki ,ya fada asauqaqe ,dago kai tayi ta kalleshi yayi saurin kawar da kanshi ,dan bayaso taga yqji tausayinta,ta sami na rainashi,

Tashi tayi ta nufi toilet din jiki asanyaye tana dan tari ,

Binta yayi da kallo haka kawai yake tausayin yarinyar yanzu,harcikin ransa yake jim tausayinta ,ko me yasa oho,dan zaman da yayi da ita ya fahimci akwai tarin damuwa atare da ita ,sannan tana da hankali ga haquri ,tana da son ibada ,dan gashi yanzu sanadinta shima sallar asuba ,bata wuceshi ,duk damadai adaki yakeyinta.

Bayan tayi wankanne ta fito da kayanta ajiki ,wajen jakarta ta nufa ta bude ta dauko wata rigar tare da dauko hoton mahaifiyarta wanda ba ita kadai bace ajiki ta kalla sannan ta mayar cikin jakar ,dan tun wkanaki tace ya bata jakar data taho da ita zata dauki abu amai muhimmanci aciki, shine ta dauko hoton ,ta sanya acikin jakar daya siyo mata kaya.

Yana kallonta har tadau kayan zata koma bayi ,yace" kinga , Dan juyowa tayi , Ya nuna mata sif dinshi yace ,bude can akwai kaya masu dumi saiki sanya,ya fada yana bude laptop dinsa , Sanin bayason musu yasa ta nufi sif din badan tasan yadda ake budewa ba.

tsayawa tayi ta rasa taya zata bude ,jinta shiru yasa ya dan waigo ,tana tsaye jikin sif din sai zare ido take tana kallonta ko zataga inda zata taba ta bude,

Tashi yayi yana cewa ,inband qauyanci idan mutum yaga bai iya abuba tambaya yake bawai ya tsaya yana duru duru ba,matsa ya fada yana latsa wani abu kawai sai glass din ya zuge ,bayan yayi wani dan nishi, zummmmmm,

Da sauri khadeeja taja baya ,jin sif na nishi,dariya kameel yayi yana kallon yadda tayi wiqi wiqi, Dauko kayan yayi ya miqa mata ,ungo yar qauye ,kuma kinga wannan abun ko,ya gada yana nuna sif din ,to cinye mutum yake duk ranar da kikayimin qauyanci nan zan kawoki ya hadiyeki,ya fada cikin sigar tsokana ,

Murmushi khadeeja tayi wanda har saida kumatunta suka loba,

Kallonta kameel yake quri ,dan zai iyacewa wannan shine karo na farko arayuwarsa dayaga tayi murmushi dan raayin kanta ,sosai yaga tayi masifar kyau ,dama tayi ta yin murmushin yana yi mata kyau ya fada aranshi yana kallonta ,

"kyakykyawa" kalmar ta kubce masa bai sani ba ,

Da sauri khadeeja ta dago kanta ,jin abinda ya fada , Shima jin katobarar dayayi yasashi kallon idonta ,aikuwa suka hada ido ,atare gabansu ya wani buga ,rass!!! Da sauri suka basar kowa ya kalli wani gurin ,

Cikin son kawar da abinda ya fada ya ce"wancan turaren ina sonshin kyakykyawane ,ya fada yana dauko wata yar kwalbar turare mai kyawun gaske,

Ajiyar zuciya khadeeja tayi nasan dama saidai idan badani yake ba,ta fada tana juyawa zuwa toilet ,kayan tasanya rigane da wando na maza kayan sanyine masu irin na jikinsa ,saidai nashi sky blue ne nata kuma light green ne,

Wayyo karkuso kuga yadda khadeeja tayi kyau cikin kayan kamar yar america harda safar hannu data qafa duk kalar kayan ,ta tubke gashinta ya zubo gadon bayanta ,sosai tayi kyau ainun ,

Fitowa tayi dan yanzu ta fara sabawa da irin wadannan kayan dayake sanya ta sawa,

Yana zaune agaban laptop dinsa yana aiki ,kawai yaga ta fito ,dan dakatawa yayi da abinda yake ya tsyaa yana kallonta,yarinyar nan classic ce duk kayan datasanya saiya yi mata kyau ,masha Allah Ya fada ahankali,

Tasowa yayi ya qaraso inda take tsaye ,kwalbar turare ya dauko yazo inda take ya fara fesa mata yana kallon jikinta, Kanta asunkuye gabanta sai faduwa yake ,ita wllh wani iri takeji idan yana yi mata irin wanan abun jikinsa sai yayi ta rawa,

Ajiye kwalbar yayi ya dawo tare da kamo hannunta ,yana akllonta,

"Kinyi kyau "ya fada yana kallon fuskarta, Dagowa tayi itama tana kallonsa ,gabanta na ci gaba da faduwa,hade goshinsu yayi guri daya yana jin wani irin yanayi na farinciki atarr dashi ,

Da gaske kayan unyi miki kyau ,yau daya kindanyi kyau kadan ,ya fada yana lakuce hancinta,

Tiro baki tayi ,ni dama da kyauna ,gidankune ya mayar dani hakan,ta fada tana turo baki,

Murushi yayi cikin farin ciki ,yace da gaske gidanmu ne ya mayar dake hakan ? amma yanzu ai ya fara gyaraki ko ,

Turo baki tayi ,hmmmm ana neman kashenin ne ya fara gyarani,ta fada cikin damuwa,

Rungumeta yayi ajikinsa , Karki damu kinji,zan dau mataki mai tsauri akan aisha ,bata sanni bane shiyasa,ya fada da dan damuwa amuryarsa,

Nikam ba ruwana ,karkayi mata komai ,azo ace nashiga tsakanin yan uwa ,nidaba komai ba nifa yar aiki nake agareku ,sannan bani da wani matsayin da dan tayimin wani abu zaa dau mataki ,ta fada tana janyejikinta daga nashi ta nufi falo,

Kamo hannunta yayi yana kallonta , Koda ace ke yar aikice adane ba yanzu ba ,domin yanzu ke matatace kuma dole na kare haqqinki, zan dau mataki akan abinda aisha tayi miki ,yana fadin haka ya sake mata hannu ya bar dakin ya nufi cikin falon gidan.

Dakin aisha ya nufa bata can ,dan haka dakin mommy ya nufa dan yasan tana can ,yana zuwa kuwa ya ganta akan cinyar mommy tana kuka ,

Fincikota yayi tare da kifa mata mari sannan ya nunata da hannu wllh aisha daga yaunayi miki iyaka da matata ,duk sanda tsautsayi yakaiki kika qara tabamin mata sainaci uwar ubanki shegiya marar aji kin biyo saurayi har gidansu kina jiran ya aureki ,ahakan zan aureki ,kina wannan haukan , Tun wuri kije kinemi wani can bani ba dan bazan aureki ba ,shashasha mahaukaciya ,ya fada yana huci,

Mommy kuwa kasaqe tayi tana kallon kameel ,anya kuwa kameel ne wannan shikenan ,wannan shegiyar ta lashe mata kurwar da.

Kai kameel kasan me kake cewa kuwa ? Toh kasani aurenka da aisha ba fashi ,saika aureta ,mommy ta fada cikin jin haushinsa dan yau ya bata mata rai,

Kallonta yayi cikin dage gira ,really ? Da gaske saina aureta ,hmmmm shikenan sai inga wanda ya isa yasani in auretan ,ya fada da qarfi cikin fada,

Wai son kodai ka fara son yarinyar can ne ,mommy ta fada tana kllonsa,

Shima kallon mommyn yayi cikin dariyar gefen baki yace momm kodabana sonta bazan bari aci gaba da cutar da ita ba ,sannna kisani ni ba sonta nakeba ,kawai inason bimata ahqqine akan duk wanda ya cutar da ita kowaye ,nayi alqawarin saina dau mataki akanshi,ya fada yana ficewa dga dakin fuuuuuu ,

Zubewa aisha tayi aqasa tana kuka harda birgima wayyo Allahna mommy kin cuceni kin gama dani wllh saina fadawa mommyna bazan yarda ba ,ta fada tana ramo wayarta, Mommy kuwa zama tayi tana tunani lallai dole ta dau mataki akan wannan shegiyar yarinyar ta fada tana kallon aisha , Zonan aisha ta fada tana janyota,zauna karki damu zansan ta yadda zan bullowa abin kinji ,karki fadawa mommynki Kinsan ranta zai baci,ki bani nanda gobe zan san abinyi,ta fada tana rarrashin aishan,

Shikuwa kameel dakin ya koma ya zauna akan kujera yana huci,tare da dauko tabarshi,yana qoqarin kunnawa ,sai kuma ya kalli khadeeja dake gefe tana kallonshi , Wurgi yayi da tabar yana dafe kanshi tare da yamutsa sumar kanshi So yake ya sha abinda zai sanyaya masa zuciya.

Kallon khadeeja yayi da jajayen ido yace ,come tare da miqa mata hannu,

Jimmm tayi ,kafin ta taho gareshi ,janyota yayi tare da rungumeta tsam ajikinsa yana goga kanshi awuyanta,

kamo kanshi khadeja tayi tare da kallon idonsa ,ta bude baki cikin nutsuwa tace........

Byeeeee Taku anty mammy ,🙏🙏

mrs babi💘💘💘

Share and comment please.

more comment more typing. Luv you guys🥰 [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

GIDAN AIKINA 🍒🍒

Na mammy kabeer (anty mammy)

ELEGANT ONLINE WRITER's

Page 41./42

Mommy ce tsaye aqofar kitchen din ,kuma da alama taji duk abinda take fada,

Zaro ido khadeeja tayi kamar zasu fado qasa, Na shiga uku, wllh taji me nace wayyo ,Allah na, Ta fada tana dafe qirji,

Mommy kuwa binta take da kallo tun daga sama har qasa ,ba shakka lallai kinsami gurin zama ,dan ubanki har irin wanan shigar kikeyi ,ubanwa ma ya baki wannan kayan? Mommy ta fada tana shigowa cikin kitchen din gaba daya,.

Baya baya ,khadeeja ta farayi tana dafe da qirjinta, dan Allah hajiya kiyi haquri ,wllh ba laifina bane ,shine yake taba ni kuma ni banaso ,nace ya daina. Ta fada tana hawaye, Dan ubanki menace miki akan kameel ? Ta fada tana kama kunnen khadeeja ta murdeshi da qarfin gaske ,

Wayyo Allah kunnena ,dan Allaha hajiya kiyi haquri wllh banda laifi , Menece miki? Mommy takuma fada ,

Cewa kikayi kar in sake ya taba ni ko inje inda yake ta fada cikin azaba,

Shine kekuma saboda baki da mutunci kika karya min doka dan ubanki?

Wllh hajiya ba ruwana laifin yallabaine ,shine yake tabani ,ta fada cikin kuka,

Shegiya karuwa qarya kike masa ,nasan ko kallo baki isheshiba bare ya tabaki,wai harkin san kisa namiji adaki kina masa karuwanci,zaki bata min da ko shegiya mai baqar aniya, Ta fada tana sauqe mata rangwashi mai zafi aka ,

Dafe kai khadeeja tayi dan taji zafi sosai ,kuka kawai take tana yarfe hannu dan har yanzu bata cika mata kunnen ba,

Wllh daga yau idan na qara ji ko naqara ganinki kusa da dana saina cire miki wadannan shegun nonuwan masu kama da bishiya ,ta fada tana kai mata duka aqirji,

Da sauri khadeeja ta dafe qirjinta dan ba qarya taji dukn har cikin qahon zuciyarta ,dama zafi suke matadn dazu kameel ya gama lallatse matasu,

Kinajina ko ,idan naga wani abu dayake nuna dana ya kusanceki wllh saina batar dake kona sa akasheshi akashe banza,ta fada tana tunkudata qasa.

Faduwa khadeeja tayi akan tyles ,ta saki kuka mai sauti

,cikin hali na rashin imani mommy ta take mata hannu ,

Ihu ta saka da qarfi ,wayyo hannuna ,hajiya dan Allah kiyi haquri ,ta fada tana ture qafar mommy daga yan yatsunta.

Kameel ne ya bude qofar da sauri ya shigo dan yaji ihun khadeeja,

Mommy!!! Ya fada da mugun qarfi ganin yadda ta take mata hannu kuma dan mugunta sai murza hannun take ,

Zuwa yayi da sauri ya daga khadeeja tsaye ,da jikinta ke matuqar karkarwa,tsabar azaba,

Wani irin tuquqin baqin ciki da bacin raine ke shiga dukkan wani sassan jiki dake tare da kameel ,ji yake da ba mommy bace wllh saiya tattaka ta agurin nan ,

Rungume khadeeja yayi ajikinsa sosai kamar zai maidata cikinsa yana kallon mommy ,kallo irin na kin cutar da zuciyata ,

Mommy what are you doing here,ya fada cikin mugun hade rai,

Son ni kake tambaya me nakeyi abangarenka?

Yesss!!! Momm i ask ,me ya shigo dake nan awannan lokacin ? Infact me ya hadaki da yarinyar nan kike mata wannan muguntar ya fada cikin rashin shayin mahaifiyar tasa ,,

Son, nazo nayi mata kashedine akan ta kiyayeka ,dan naga tana wani shishshige maka , Ta fada tana kallon yadda yake mata wani shegen kallon,

mommy who ask you to do so, Na ce miki tana shishshigemin ne ? Momm kina shiga rayuwata akan me ? Meyasa kike son takuramin ne? Ya fada yana daka mata tsawa kamar wata yarsa , Kokawa khadeeja take dan kwace kanta daga gareshi ,nema yake ya qara jefata cikin matsala ,yana fadawa mommy magana akanta, Shikuwa sai qara riqeta yake yana zazzaga rashin m.

Da qaefi khadeeja ta fuzge jikinta daga gareshi tayi daki da gudu tana kuka ,

Kallon mommy kameel yayi ,ido cikin ido. Ki fita daga harkar data shafi rayuwata mommy ,am not a small boy ,nasan yadda zanyi da rayuwata bana son kishiga rayuwata kingane momm.ya fada yana zare mata ido kamar wata yarsa.

Son ka fahimceni ,nifa mahaifiyarka ce ,dole in kula da rayuwarka ,duk abinda naga zai zame maka matsala dole in zame maka katanga , Nifa banyarda da yarinyar nan ba ma ,ina tsoron kar makircinta yayi tasiri akanka ,har ka kusanceta ,ta shafa maka ,hiv dan bazata rasa ba ,

Mommmm!!! Stop it ,is she not my wife ? Dazakice karna kusanceta,koke zaki bani damar yin abinda naso ? Momm ki fita ahanyar matata ,bake ba ita ,na shirya fito nafito dakowa akan kare mata haqqinta , Ya fada yana kallon mommy cikin tantsar rashin kunya,mommm karku bari fushina ya sauqa akanki ,zan iyayin komai akanta ,domin tana min abinda bazaki taba iya minshiba nasan muhinmancinta agareni. Sannan ni na kawota gidan nan ,nike da iko akanta shiyasa na hanata shiga ,gurinku ,ya fada yana huci.

Mamaki ne danqare azuciyar mommy ,kodai kameel ya fara son yarinyar nan ne? Kai bazai yiwuba nasan son bazai taba wanann kuskurenba ,me zaiyi da wanann yar matsiyatan .

Dan haka cikin alamar rarrashi tace son kasani ni mahaifiyar kace ,kome nene damuwarka arayuwa sai inda qarfina ya qare akanshi ,sannan bazan bari wani abu ya cutar da kai ba ,

Wannan yarinyar ba alkhairi bace agareka ,sam sam ni banga amfanin zamanta agidan nan ba ka sallameta kawai ,idan ma bazaka dauki matakin komai akan abida tayi maka ba ,ga yar uwarka nan aisha ,kuyi aurenku shine burina ,

Wani shegen kallo yabita dashi ,kafin cikin wata dariyar yan duniya, yace really mommm, wannan. Ba alkhairi bace agareni sai waccan shashashar da kika kira aisha,?

Momm har abada bazan taba auren wancan wawar yarinyar ba kozan mutu,i hate her,ya fada da qarfi

Zaro ido mommy tayi cikin alhini,

Son kodai ka fara son wannan yar matsiyatan ne?

kina mamakine ? Komai mai iya faruwane momm. Please leave i need privacy,ya fada yana nuna mata qofar,

Shikenan ta tabbata ya fara son waccan shegiyar ,lallai dole in dauki mataki kwakwkwara akanta shegiya mayya ta lashemin kurwar dana, Ta fada tana nufo inda yake ,

Readers Also Read