Kenza eBookz

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 21

Complete book: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy)Chapter 21 of 21FantasyBy Mamy Kabir (aunty Maamy)

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 21

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 21: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 21. Dagowa tayi cike da murna da jin dadi ta bude…

512 words

Dagowa tayi cike da murna da jin dadi ta bude musu hannu ,oyoyo my kids,ta fada tana rungumesu. Babansune ya shigo rike da ledoji ahannunsa ,yana murmushi. Kallonsa tayi tare da tashi daga jikin yaran taje ta rungumeshi oyoyo my habibi,my life.

Shikuwa daga ta yayi yana juyi da ita,oyoyo deejena kinzama yar lukata fa da alama wannan cikinma zaisa kizama katuwa fa ya fada yana dariya .

Turo baki tayi ni wllh kadaina cemin yar lukuta kaima fa kayi kiba sosai , Dariya yayi yace ba dole nayi kiba ba ina tare da sarautar mata,sannan nayi maganin makiyana suna can suna zaman gidan kaso.

Dan tuni aka yankewasu hajiya talatu daurin shekara goma agidan kaso tare da horo mai tsanani, Kameel tuni ya bude katafaren kamfaninsa na sarrafa larafuna dakuma na kwangilar gine gine , Inda khadeeja ta kamala karatunta yanzu haka itama ya budemata wani gidan marayu da take kula dasu.

Su baba umaru annutsu an komaga Allah ya nemi yafiyar khadeeja tuni kuma ta yafe masa ,an bude masa katon shago anzuba masa kayan masarufi ,yanzu haka yaransa maza duk suna makaranta.zainab ma ta hadu da wani malami ya aureta ,suna zamansu lafiya,mariya ma tuni khadeeja ta sanyata a makaranta mai tsada .

Gidan abbama yanzu ya cika dafarin ciki sosai suke zaman lafiya doctor ya haifi yaranta maza yan biyu .

Khadeeja duk karshen wata sai sunje malam madori ,sun gaisa da yan uwa.tayi musu abin alheri sosai .

Dariya khadeeja tayi ina sonka mijina ka zame min komai arayuwata,

Kissing dinta yayi cikin farinciki nima ina sonki matata,ina alfahari dake kece rayuwata.

Daddy nima fa ,mama ta fada tana turo baki,ganin yayiwa mommynta kiss akumatu, Dariya kameel yayi ya dauki yatinyar da yake jinta har cikin ransa.gaba daya halayenta da kamanninta iri. Na khadeeja ne.kece rayuwata ai mama nafi sonki fiye da komai mamana,ya fada yana mata kiss akumatu.dariya yarinyar tayi dan aduniya tana son daddyn tana yace mata mamana.

Khadeeja ma dariya tayi tana lakutar hancin mama kekam mamako kin fiye kishi daga ganin ammin abu shine kema wai sai anyi miki ko ta fada tana mata hararar wasa. Dariya mama tayi tace mommy ai daddy ni yake so bake ba ko daddyna,ta fada tana rike fuskar kameel.

Kallon khadeeja yayi wacce ta kankance ido tana jiran jin me zaice,

Dariya yayi yace kai mamana kinga mommy fa ta hade rai karna fada ta zanemu mu duka,amma ina sonku gaba dayanku kunar rayuwata. Suma su aeman mazowa sukayi tare da rungume mommynsu mommy we luv you daddy we luv you too.

Hadasu yayi gaba daya ya rungumesu ajikinsa .ina sonku nima gaba dayanku kune rayuwata Allah yayi muku albarka.

Alhamdulillah ,ina godiya ga Allah daya bani ikon kammala wannan littafin mai suna gidan aikina .Allah yasa mu amfana da darasusan dake cikinsa. Ina godiya gareku masoya dakukayi jumirin bibiyata tundaga farko har karshe🥰🥰🥰

sai mun hade alillafina mai suna dakai na dace .karku sake abaku labari domin littagine mai cike da abubu acikinsa kudai saikun karanta daga alkalamin anty mammynku🙏 Mrs babi💘💘💘💘

luv you all masoyana.

Readers Also Read